Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
hana, kome. Dake zuciyarshi ta gama rike dan daudun take kuwa Aamil ya juya tare da gargad'in shi yana fad'in. _Kai da kake ɗan daudu, me zaka yi da mace irin wannan! Tawa ce ita din_ Daga fadar haka yaja hannun my Baby ya tafi da ita, yana son bin su ya kasa, itama my Baby. Tirjiya take tare da mika mishi hannu, karshe ta juya ta gantsara mishi cizo, kawai ya sake ta, ta dawo gurin Allison da gudu. Bude mata hannun yayi ta shige jikin shi, duk yadda yaso ya amsheta kin zuwa tayi tare da rungume Allison sosai, tana kuka. A zahiran kuwa, shida Emily ce tana rungume a kirjin shi, sai cewa yake. 'Karka raba ni da ita, itace burina karka shiga tsakanin mu" Kallon shi Emily tayi haushi yana kamata, bata san lokacin da ta kai mishi maka a cinya ba, tare da cewa. "Dalla bude ido, ka kuma sake ni. Daga ranka ya b'aci kake shan giya. Ko waye ya b'ata maka rai Oho kazo kana shirmen mafarkai marasa dad'i." Sake baki yayi yana kallon inda ta make shi. Tashi yayi ya zauna tare da kura mata ido. Kafin ya gyada mata kai. "Fita kafin na fitar dake!" Banza tayi dashi, ta zauna ganin yadda ya mik'e tsaye, tare da ɗaukar.. Wani igiyar cajin laptop din shi..da gudu ta fice mishi a daki, ya bita da Zungurerren harara, dan ji yaƙe kamar yana duniyar zungura ta dawo dashi. Musamman mafarkin My Baby. *** Dutse.. Da safiyar yau Alhaji Ma'aruf, ya tashi da wani irin nutsuwa, sannan ya sanya aka fitar da kayan cikin gidan Aamil, ya tsaya da kanshi aka kwashe kome zuwa cikin shashin sa, ya sanya aka fasa cikin gidan, tare da gyara tsarin gidan. Kudi ya zuba a kasa, tare da jin dadi a ranshi ya kuma yi imani idan ya gyara gidan ya zamanantar dashi, Aamil zai sauko daga fushin da yake dashi. Duk wani nau'i na more rayuwa, sai da yaje Shagon Alhaji Abubakar ya sayo dan ya samu ya kawo wasu Jacuzzi masu kyau, dan haka ya sayi kala biyu. D'aya fari kal, daya kuma ya barwa Sidrah Pink, duk wani abinda yake bukata na cikin gidan, ya sayo. Hatta paint din da za ayi a cikin gidan, duk ya zab'a musu, kasancewar yasan Aamil yana son combinet color, dan haka ya haɗa mishi da Black And Whiter. Ita kuma Sidrah d'akin ta, yadda ya hada mata kome, sai ka zata yar tsana, haka ya kira me tsara daki, daga kano yazo ya tsara mata d'akinta. Da yadda zata iya rayuwarta babu damuwar kowa. Kitchen ɗinta kuwa, wani irin tsara shi aka yi kamar yadda ake tsarewa babbar mace kitchen ɗinta, an shirya zuba mata kome. Yadda zata sake da rayuwarta babu kowa da zata takura.. A iya yanzun ya gama gajiya da girkin da ake na cikin gidan shi, badan kome ba, sai da. Zunzurutun ta'asar da ake mishi. Ana wani irin b'arna me mugun cin rai, buhun shinkafa da yake wata biyu, amma abun mamaki ko wata daya bata yi, last da yakare sati uku da kwanaki. Yana son ya dakatar da girkin amma sabida gudun tashin hankali ya sanya shi zuba musu ido, yana kuma Addu'a Allah ya dawo mishi da Aamil, Ubangiji ya bude mishi hankalin shi da nutsuwar shi ya fahimci kuskuren da yake aikatawa, ya fahimci cutar dashi da ake. Babban tashin hankalin shi , shine yadda suke niman karya dukiyar da yake tattalin arzikin Mahaifiyar shi, gashi ya tafi, yabar baya da kura. Tun yana musu magana, yanzun ya daina magana ya zuba musu ido, domin kwanaki da ya cika magana. Ido da ido Ali yace mishi. "Wato Abba idan da Aamil ne, ba zaka mishi magana ba, amma dake mune kake mana fada, Duk da wahalar da muke sha, domin sanyawa dukiyar hannu ta bunkasa baka gani ba, shi kenan. Zamu bar maka dukiyar ku, sabida kar ya kare, tunda naku ne." Ranar Alhaji Ma'aruf, sai da ya kwana zaune gashi ranar yana dakin Hajiya Surayyah ne, koda ya gaya mata abinda Ali yayi mishi budar bakin ta, tace.. "Ai yayi maka ma magana mai taushi domin bazai yiwu suna wahala baka gani ba, gwara su bar dukiyar kayi yadda kake bukata dashi." Kuka ne bawan Allah nan bai yi ba, amma tabbas ya kwana cikin damuwa da b'acin rai, a duk lokacin da ya tuna abinda ya faru sai yaji kirjin shi yayi mishi zafi, washi gari dole ya tafi yaga likita, ya gaya mishi jinin shi yayi mugun hawa, dole suka bashi gado. Faruwar haka ya kuma sanyawa suka kuma rub da ciki akan Dukiyar, gashi likita ya hana shi fita kasuwa, gashi idan yana gida baya samun nutsuwa, tashin hankali kwaraniya, hayaniyar mutane. Dan haka ya koma dakin Hajiya Uwani, domin d'akinta yana can karshen gidan ne, baka sanin me ake a cikin gidan, idan baka fita ba. Wannan abin ya kuma kara mishi tashin hankali, domin matan sun daina girki kowa sai ta girka daga ita sai y'ayanta, dalilin da ya janyo ake mishi.satar fitar hankali kenan. Koda yaji sauki ya fara fita kasuwa Alhaji Ahmed ya same shi akan su fara shigowa da keke napep, cikin farin ciki su uku suka shiga da kudaden su, aka sayo napep daga India, kira biyu wato da TvS da kuma Qualia, dukkansu masu mabanbanta priza. Abun mamaki da tashin hankali, kowani dan kasuwa yana burin ya sayar da kaya ya kuma sari, amma banda Alhaji Ma'aruf bai san haka ba, saboda koda yayi sarin, karshe keke napep din suna zaune saboda tsuga musu kudin da aka yi, tvS ana sayar dashi 770k sai kuma Qualia 700k, madadin haka sai karshe suka mai da TvS 970, Qualia 900k, abin da ya hana kowa saya kenan. Koda ya tambayi Alhaji Ahmed, ya gaya mishi zai tafi sari na uku kenan, nan ya gaya mishi ai tun satin farko bai koma ba, nan ya Alhaji Ahmed ya wakilci wani makocinshi ya je yaji yadda priza din keken yake, ya zo ya gaya musu. Abin ya kada. Alhaji Ma'aruf, cire hular shi yayi tare da safe kanshi.dama haka mutane suke. Gyara zama Alhaji Abubakar yayi sannan yace mishi.. "Ina gani me zai hana kazo na kaika gurin Baffana a can Auyo. Insha Allah zai tsaya maka akan matsalar Aamil, babu musu suka nufi garin. ....... Shiru Baba Malam, bayan ya gama jin bayanin Alhaji Ma'aruf, ranshi ya b'aci amma bai nuna musu haka ba, "Wato duk abin da ya faru, kai ne mai laifi, duk abinda ya faru. Kai ka fara, baka ja shi a jiki ba, sannan ka dauko mishi abinda baya so ka bashi, taya zai iya rike musu ita, bayan tayi kankanta da fahimtar shi, amma tunda aure ne babu abinda baya faruwa. Karka kuma irin abinda kayi Insha Allah zai dawo cikin nan da wani lokaci, karka kuskura ka ce zaka sanya mishi tashin hankali ka barshi da izinin Ubangiji zai kawo mishi dauki, kayi hakuri da halayyar shi, domin kai ne ka samar da kome, Insha Allah kome na gab da zuwa karshe su kuma masu kama wasa da dukiya karka damu dasu Insha ALLAH zasu wayi gari dukiyar sai tafi karfin su. Ka kuma Cigaba da hakuri kana hidima dasu." Haka yayi ta musu nasiha, tare da bashi addu'o'in da zai cigaba dayi har Allah ya dawo mishi da Aamil. Sannan ya gaya mishi. Sannan ya saka ana mishi sadaka, domin ita kanta maganin masifa ce. Kuma haka ce ya kasance. Bayan sun dawo ya saka aka fara abincin sadaka, ana kaiwa waje tare da almajirai. Haka ya cigaba da wannan aikin gidan Aamil yanzun haka an kusan kammalawa. Kowa sai jin haushin abinda yayi yake, musamman Ali wanda yake ganin kamar son kai da wariya Baban su yake musu, shi kuma a nashi bangaren yana yin haka ne domin idan Aamil ya dawo ya ga yadda ya tsara mishi ko ina, hankalin shi zai kwanta yayi Na'am da dukiyar Mahaifiyarshi. Sabida yadda yake jin Yaron a a ranshi, hatta tsakar gidan intelock aka saka, cikin gidan kuwa an bishi da tiles, har jikin bango, kitchen din wajen ayi shi kamar na zamani, duk cikin gidajen babu inda yayi musu wannan gatar kamar na Aamil sannan ya kuma fitar mishi da dakin wanki ya saka a kawo mishi injin wanki. Duk yadda ake bukatar gyara yayi mishi sabida bukatar shi yazo ya ga yadda zai fahimtar dashi ya tallafi dukiyar Mahaifiyarshi, kullum da wannan tunanin yake kwana yake tashi. A cikin sati biyu da suka rage aka gama gyara kome dake akwai kudi na gwamna masu gidan rana, babu wanda zai ga gidan bai yi maganar shi ba, sannan ya fitar da tsarin kofar gidan biyu, akwai kofa daya ta wajen gidan, wanda yake hade da gareji, akwai kuma a cikin gida wanda Sidrah zata iya shigowa cikin gidan, sai dakin baki da aka yi shi a waje, sabida karsu sawa matar gidan ido, ( 🤔🤭 Irin su Oo, masu zuwa gashin amarya 🤣󰢇 Jar ubancan Aamil da Sidrah, kwamacala..) Duk yadda ake bukatar kome yayi karewa ma, har da Inverte Yasaka a gidan Aamil tare da solar shi, sabida yasan tunda ya dandana zaman kasar waje, zai yi wuya bai bukaci masuburbudar sanyi ba, dan rayuwar su da mu akwai banbanci. Kuma duk wanda ya zauna acan sai ka ganshi baya son zafi.... Bai zama tilas na kai talatin da biyar ba.. 󰚥 Wannan book din na kuɗi ne akan 300₦ haka ma katin mtn 300₦ 0472282105 Ramlat Abdulrahman Manga GTBNK, zaku iya tura shaidan ku ga Zahrah +2347035133148. Yan Nijar su sami Nana Aicha+22784506476 #Mai_Dambu. [11/13, 8:06 PM] My Zahrah: https://my.w.tt/YlEwi83Nkbb 𝐔𝐖𝐀 𝐁𝐈𝐘𝐔 <𝑲𝒂 𝒔𝒂𝒚𝒊 𝑫𝒂𝒚𝒂 𝒌𝒂 𝒔𝒂𝒎𝒊 𝒅𝒂𝒚𝒂 𝑲𝒚𝒂𝒖𝒕𝒂> ℍ𝔸ℤ𝔸𝕂𝔸 𝕎ℝ𝕀𝕋𝔼ℝ'𝕊 𝔸𝕊𝕊𝕆... ᴍ𝐚𝐢_ᴅ𝐚𝐦𝐛𝐮 Bismillah Rahmani Raheem A wise woman wishes to be no one’s enemy, a wise woman refuses to be anyone’s victim. *Shin har yanzu kuna sayan data,airtime, TV subscription da biyan kudin wuta diga banki???* Ya kamata ku dena *wadatar da bankuna kuxo ku sayi VTU portal a kudi kalilan (5k) sannan kudinga samun akalla 1k zuwa 20k a rana. Mai buqatar karin bayani tayi min magana 😃󰛛 ga masu bukata zasu iya tuntubar Mimiqueens ta wannan Number+2348036319148* #Waye kai? 1⃣9⃣ Cikin nutsuwa yake shiryawa, hankalin shi da nutsuwar shi yana ga shawarar da zuciyar shi ta bashi,kuma ya amshi shawarar hannu bibbiyu, domin yayi na'am da ita. Kara wayar shi yayi, cikin sanyi jiki ya ɗauka tare da sakawa a kunne. A hankali yace. "Mom!" "Allison! Naji ance an kama wannan mutumin! Shin da gaske ne?" Ta tambaye shi a kage, Ajiyar zuciya ya sauke sannan ya lumshe idanunshi kafin yace mata. "Karya ne! Asalima nine na fita Zanga-zangar " "Allison!!" Ta daka mishi tsawa, A shagwaɓe yace. "Mom! Kiyi hakuri ba zan kuma ba." Yadda yake maganar sai jikinta yayi mugun sanyi, nan ta shiga mishi nasiha, tare da mishi faɗa kamar tana gaban shi, lumshe idanun shi yayi cikin damuwa sannan ya bude baki yace. "Nagode Mom!" Sannan ya kashe kiran, tare da fesar da iskan bakin shi, yana gyara neck tie din shi, yana gamawa ba, ya shiga saka links din hannun shi. Tare da makala agogon hannun shi. Daukar bluetooth speakers, ta manna a kunnen shi. Gyara gashin shi yayi tare da fesa turare. A hankali ya saka cap toe Oxford shoe, wacce ta dace da suit din jikin shi, zama yayi a bakin gadon shi yana kallon closet d'inshi, cikin nutsuwa kafin ya mike daga zaunen ya nufi hanyar waje, a sanyayye yake sauka daga step din gidan, yana kuma kallon wayar hannun shi tare da tab'a bluetooth din kunnen shi. Yana iso falon duk suka zuba mishi ido, kafin ya nufi hanyar waje, suka rufa mishi baya, idanun shi lumshe bayan ya zauna cikin motar yayinda zuciyarshi take tsananin Bugawa. Yau bai duba paint work din shi ba, amma tabbas yana bukatar hakan, lumshashen idanun shi ya kuma ware su akan fuskar Emily da bai san shigowar ta ba. A ranshi yace.. "Wannan ba dai bakar naci ba,". Kallon ina zaki yayi mata, take ta shiga hankalin ta, tace mishi. "Zan.." "Sauka!" Babu musu ta sauka domin ta san halin shi tunda yace mata sauka, matukar bata dauka ba, zai iya fidda ita da kanshi ba tare da yaji ko dar ba, haka halin shi yaƙe bai cika so ana mishi shishigi ba. Idan kuma zaka iya tafiya dashi babu kai babu gwatselewa, musamman ita yafi gwatsaleta, amma dake bata da zuciya, sam haka bai damunta, idan zai shekara yana ɓata mata rai toh ba zata tab'a nuna mishi ba. Shi yasa wani lokaci, idan ya koro wulakancin shi, sai ta yi sati Uku bata leko gidan ba, sabida rashin mutuncin da yake mata, amma da kanshi zai je niman ta, idan kuma ya nimota ya shiga shareta, kamar ba shi yazo da kan shi ba. Idan tayi zuciya zata bar gurin ya janyo ta jikin shi dan dole take zama, tunda shi dai idan yaso zai. Mata hira idan bai so ba kuwa, kirb'a mata wulakancin yake tana fara damun shi zai ce mata. "Fita can kiyi surutunki, tunda ke hakan ba wani bakon abu bane a gurinki, ni kuma takurani yake." Idanun tane suke cika da kwalla, ta rike hannun shi sannan tace mishi. "Nasan watan wata rana zaka so na zauna da kai, nayi ta maka." "Kinga dauko min abin sosai kunnen idan kin gama zaki iya tafiya." Bata tab'a fushi ba, bawai dan bata da abun yi bane sai dai kuma tayi imani da cewa, dole wata rana zai so ta. Da wannan take kuma shige mishi, amma bai hana shi buga mata rashin mutunci ba, kuma bata da zuciya. Wani sirrittacen ajiyar zuciya ya sauke, wanda ya boye duk wani damuwar da yake tattarar dashi, Cizon lip shi yayi cikin jin kewar wani abun da bai san dashi ba, amma tabbas yana missing wani moment, bai da wani abu da zai ce ya sashi nishadi but yayi kewar wani abu me muhimmanci. Musamman My Baby wacce take kuka. Amma cikin mafarkin shi ba ta, kuka. Kiran shi aka yi yaga Number na Australia, sakawa yayi a kunne tare da cewa. "Mom! Kina bukatar wani abu ne?" "Son kana boye min wani abu, ina zaka da ka kore Emily daga motar ka?" Ta tambaye shi, Shiru yayi cikin nutsuwa, kafin yace mata. "Mom tun ban aure ta ba, ta fara kawo miki gulma na, lallai dole na rabu da ita, na fasa auren." "Son baka da kirki, meye na fasa auren daga cewa zaka fita ka kore ta, shine abin gulma toh shi kenan, kayi abinda kake so amma batun fasa aure bai taso ba." Aikuwa kamar wanda yake jiran tayi mishi magana ya kuma ririta alamarin, inda ya shiga botsare mata, tana taro shi tanan yana kaucewa ta can, karshe dai kashe wayar yayi, kusan yaran turawa kamar Ƴaƴan agwagi ne. Suna gaba uwar na baya, wasu na bayanta. Wasu na karkata hanya, zata bisu, na bayan na juyawa zata juya gare su. Haka yaran turawa suke, ba a musu fada musamman Allison da bai san fada ba a rayuwar shi, duk abinda yake bukata ya samu. Toh me ya rage mishi. Kawai cikar burin shi ne ya fita yayi yawon duniya, tunda aka haife shi a U.S Bai taɓa barin kasar ba, karewa karatun shima anan yayi tun daga farkon har yanzun. Yana bukatar Fresh air, So yake ya zaga kasashen duniya har da Afrika, domin ko kwana biyu da suka wuce wani abokin kasuwancin shi ya gaya mishi ana samun irin yarinyar da ya zana, a kasashen Afrika. Kama daga South africa, Central republic Africa, sai Kenya, Niger da kuma yankunar Nigeria, can yankin arewa maso yammacin kasar, musamman yankin da aka samu hausawa asalin original Hausa ba, mix Hausa Fulani ba. Ya kuma gamsu da da bayanin mutumin, dan haka yake shirya wani project, da zai kai yammacin Afirka, ko Allah zai sanya ya tsinci wannan bakar zinariyar da ta samu damar ya zanata. Matukar ya same ta, ba zai tab'a kasa a gwiwa ba, zai dauko ta cak ya kawo nan. Domin yayi alƙawarin shirya mata duniyarta ita daya. Murmushi ya sake kamar bai da wata damuwa burin shi kawai yake hangowa. Kuma yana jin a ranshi zai cika, lumshe idanunshi yayi lokacin da suka tsaya a kofar Office din yan sanda, bude mishi motar aka yi, ya fito a sanyayye, yana kallon yadda ake gudanar da al'amuran yau da kullum, a hankali ya gyara zaman rigar shi, sannan ya saka kai suka shiga p.a na biye da shi. Har cikin office din, samun guri yayi cikin nutsuwa, ya tsaya bayan ya mikawa Babban supeto na Office din hannu, sun gaisa sannan ya isa gaban dakin da Aamil yake ciki, suna kallon shi ta glass. "Ko zaku iya nuna min, wasu bayanai na na'urar daukar hoton garin nan da wasu madakatai?" Allison ya bukaci hakan, Kallon shi dan sandan yayi sannan yace mishi. "Yallabai wannan ba hurumin ka bane" A fusace ya juya gare shi, tare da mishi kallon banza sannan ya gyara mishi kwalar rigarshi, yace mishi. "Hurumina ne! Na binciki waye shi, me yasa da kuka yi ta kamo ni kun tab'a bincikar taya haka ke faruwa? Da saka hannunku ake ta b'ata min suna, idan na shigar da kara kotun dole a kwatar min hakkina, dan haka kayi abinda nace ko kuma nayi abinda zai dami kowa, kasan dokar shi yasa na nime muyi magana cikin doka.'" Babu musu, suka wuce zuwa dakina da ake ajiye na'uran,a hankali ake bibiyar duk abinda ya faru, daga ranar da aka fara kama shi, zuwa ranar da aka kawo mishi hari, tabbas Aamil ne a cikin madaukar, sai dai shi yana taka sawun shi ne, fita yayi tare da sawa aka bude mishi kofar da Aamil yake ciki. Da mamaki a fuskar su suke kallon juna. "Waye kai?" Cikin tsannanin tsokana da zolaya Aamil yace mishi. "Ni da kuma ni." Cikin tsannanin b'acin rai, Allison ya cukume wuyar Aamil, tare da kai mishi naushi. Dariya ya saka mishi tare da cewa. "Kai WAYE kai?" " Sake haushin sa yayi, tare da zaunar da shi da karfin tsiya,, mik'ewa Aamil yayi cikin fusata ya cikomo wuyar Allison, yana zare mishi idanu, Da sauri Yan sanda suka nufi dakin, Allison ya hana su, ya kuma rike hannun Aamil. "Waye kai?" "Ban sani ba!" "Wannan zancen banza ne! Taya zaka yi kana aikata laifi ana tuhumata da su? Kasan yadda ka nemi lalata mana sunan Zuri'ar mu kuwa, sabida banzan fuskarka da take kama da nawa." "Dalla sake ni! Banza mara amfani, wanda zuciyar shi bata da amfani kasan ni hatsari nawa na tsallake saboda banzan fuskar ka take kama da nawa." "Ka gaya min waye kai? Zan saka a sake ka ka tafi kayi rayuwarka, amma idan baka fada ba, zaka mutu a banza." "Kai ne kake tsoron mutuwa, tun daga ranar da aka haife ni nasan nazo duniya ne domin dalilai masu yawa, kai kuma lusarancin ka ya sanya ka kasa fita." "Kai dan gidan Uban waye da zaka kirani da lusari? Uban waye ya gaya maka ni.." "Dalla sake ni, idan ka kuma dukana zan baka mamaki." Cikin fushi sosai yace. "Mamakin kaniyar ka, waye ya tsaya maka fadin garin nan. Sabida Shashanci ka, ka sanya waje tayi mini nisa, ina raye kamar matacce, ka san iya adadin bakin ciki da nayi, ga dukiya amma ya zame min mara amfani kazo kana ta kashe mutane tare da amfani da fuskana, banza kawai mara mutunci ka gaya min waye kai, idan ma turoka aka yi zan baka, miliyan dubu biyu, ka fita a rayuwata." Murmushi Aamil yayi tare da ce mishi. "Banza dama kana da miliyan dubu biyu kake ihu, zauna mu fahimci juna, kasan a duniya ina martaba abubuwa guda biyu! Abu me Kyau! Da kuma kuɗi, akan su zan iya kome, amma koda yake tunda ka iya saka, kayan dubu dari biyar da talatin na dallar Amurka tare da agogon miliyan daya, tare da takalmin dubu dari uku, ka hadu turaren miliyan saba'in wanda kampanin Omar Dubai, suka yi kaga ai ba wani abu bane! Ni rayuwata bani da wasu buriruka, amma ina son kudi da abu me kyau, kuma zan yi tafiyata idan ka cika min aljuhuna da makudan kudade, na tafi nayi ta shagali." Cike da takaici yake kallon Aamil yadda yake bashi labarin kaunar shi da kudi. Amma yana gamawa ya gaya mishi bakakken magana, suka kuma kaurewa da faɗa kamar zasu daki juna, karshe haka P.A yazo ya fidda Allison Aamil yana gaya mishi cewa. "Banza dan daudu, daga ganin ka kai dan daudu ne, shi yasa kullum kake toshe a cikin gida. Baka da katabus, sai yadda akayi da kai. Sha-sha-sha banza, lusari kawai, maza an sansu da kare kansu da dukiyar su, kai ka ajiye naka jarumtar ka boya a bayan babarka koda yake ai bata da laifi,kuma ka jawa mutanen da suke niman kashe ka kunne kar su kuma biyo ni domin zan ta karya mutane ne ina ajiye su a gurin, banza wawa." .ya karshe maganar yana wani cizon lip din shi tare da nuna mishi hanyar fita. Kasa hakuri Allison yayi. A fusace yayo kan Aamil, a bika da wanda bai san tashin hankali, koda yazo mangaje shi Aamil yayi yawani tafi can ya bugu da bango, Aamil ya kuma ɗaukar kujeran da yake cikin dakin zai buga mishi, kurawa juna

Chapter 12 of 13