sauran yan uwanta, idan ka cire masifa. Amma bayan nan bata
da matsala dan wani lokaci idan taga Sidrah bata ci abinci ba kawo mata nata take, a boye dan
Sahiya bata kaunar taga Sidrah tana walwala.
Da gudu ta sheko da kumfar. Ta ajiye tare da washe hakori tana cewa.
"Innah ta kara mana gyara, wai nima nayi da nace mata za a wankewa Sidrah kai ne sabida
aurenta, shine tace ashe ni babbar kawa."
Tsaki Lantana tayi sannan ta dangware goshinta tana faษin.
"Karki dame ni, yar banza mara zuciya."
Tura baki tayi sannan tace .
"Toh ni ina ruwana, meye na rashin zuciya, aure da abin taya murna ne. Sidrah Kinga wallahi
muka je dutse sai na haura gadonki me shegen kyau dan nasan ba mamaki..."
Make mata baki uwar tayi cikin jin haushi, sam Yarinyar bata da zuciya.
Karshe ma tayi zuciya tace ba zata saka mata kumfar ba, taje mijin yazo ya saya mata.
***
Cike da jin kunyar abinda zai gayawa D'an uwan shi, amma haka ya daure ya koro mishi
jawabi, tare da niman a d'aga auren zuwa nan da shekara daya ko biyu, Insha Allah.
"Toh babu damuwa, kamar gobe ne sai ka ga abin yazo kamar ba a tab'a samun jinkiri ba."
Sun tattauna sosai, kafin suka yi sallama.
......
Da sallama ya shiga ya samu ana taje kan Sidrah sai yarfe hannu take, Lantana tana
rankwashinta, zama yayi kafin ya fara bayani wa Lantana. Wani uban shewa ta buga tare da
dukar cinyata, tace mishi.
"Ba dai ya tafi yaki auren kazamar mata ba? Toh ai abu yayi kyau"
Daga nan aka shiga yadawa Sidrah,(
๐คญ๓ฐฃธ๐คฃ๐๐คฃ
) ita kuwa baiwar Allah bata san meye ake
nufi da aurenta ba ma. Wallahi, haka suka yita haukar su. Har zuwa lokacin da maganar ya
gana yawo a cikin gidan, abu daya kawai yarinyar ta nuna shine bata iya koda shiga yan uwan
ta, ba sabida tayi kuka, sabida ta gaji da damuwar gidan
***
Ranar Juma'a aka yi walimar mata, Ranar Asabar aka yi na maza bayan an daura aure, kafin
aka Cigaba da hidimar biki, amma ta bangaren Alhaji Ma'aruf daurewa yake, sai da aka
dangana dashi asibiti, jinin shine Ya haura sosai, dole aka kafa mishi sharudda da zai k'iyayye
sabida ciwon shi.
Dole aka rage wasu shagalin, tare da hakura da su. Aamil kuwa ya sha tsinuwa sabida, jin
haushin ya b'ata musu shagali, haka a ciki gaba da hidimar har aka gama bikin. Kowa burin shi
yace ya tsinewa Aamil, amma yaki yace kome,asalima blaming kan shi yake da laifin duk
abinda ya faru.
.... "Ai Hajiya wato Magret ta gama da zuciyar Ma'aruf har yau yana jin sonta a ranshi.
Gashi wancan dan banzan da muka hana ta tafi dashi ya zame mana karfen kafa, tunda gashi
nan ya kuma raunana mana kome. Wallahi nayi bakin cikin yadda yaki tsine mishi."
Ga baki daya hankalin su ya tashi burin su, kawai su ji ya tsinewa yaron, shi kuma bai ce
musu qala ba.
..... Bayan bikin da sati biyu, ne aka samu wani karamin tashin hankali a cikin gidan,
tsakanin Hajiya da Hajiya Surayyah, badan kome ba. Sai dan tace ba za'a yi mata iko da
surukatan ba, matar ali da Matar Ghali. Nan tone tone ya tashi aka kare babu dad'i, abin dai sai
a hankali. Dan haka Alhaji Ma'aruf yace musu.
"Suna zuwa amsar abinci kafin su fara nasu girkin,"
"Haka yayi kaga dole wasu su hakura da aikin su. Tunda gidan dai bamu kadai bane!" Inji
Hajiya Surayyah,
Gyara zama Hajiya Uwani tayi sanan tace mishi.
"Abban Aamil! Haka sam bazai yi ba! Idan aka yi dubi da yawan abincin da ake girkawa, ana
daga musu takwas, sannan da dare shinkafar tuwo mudu biyar, yanzun kuwa dole zamu kara
yawan abincin sannan maganar gaskiya nice zan cutu, sabida bazan iya barin aikina sabida
girki ba, tunda da abuna ka same ni.
Idan su matan zasu iya fitowa su girka na rana a ci baki daya,. Da dare kuma matar gida
tayi toh bismillah, ai munyi na sati biyu, idan kuma bai musu ba kowacce ta kama girkinta babu
kare bin damo,domin ba zan kashe aikina sabida su ba idan yayi muku toh bismillah."
Shiru falon ya dauko, daga bakin kofar shigowa Hajiya tace.
"Amma Rabi kin kawo shawara, ai suma mata ne, idan bai musu ba sai su bari su girka abin su,
sannan ita Surayyah da take fadar haka, ina ce sabida matan yaran ta take wannan ihun,wato
ga bayi ku girka ku basu su ci. Kar Allah yasa ko wacce yar bujen uwa ta shiga kitchen tayi
girki."
Shiru falon ya dauka, sannan Alhaji Ma'aruf, ya dauki wayar shi ya kira yaran shi maza tare
dasu Muhmood, suka iso. Aka yi maganar a gaban su. Tuni Ali ya zare kan shi tare da cewa.
"Ni bana ra'ayin abincin gamayya, mata na zata girka min."
"Abba na amince Ummita zata shigo ayi da ita." Inji Ghali, Bala da Isah, sale da Faruq,
Muhmood, duk sun amince. Daga nan Alhaji Ma'aruf yace musu.
"Uwani kiyiwa matar da take kawo muku yan aiki. A kawo me wanke wanke, koda su uku ne,
zan na baki kudin su. Sai Alamajirin da zai na sharar gidan da sauran bangarorin ku nemi yara
biyar maza, sai a basu aikin. Uwani idan suka zo ki nuna musu yadda za ayi aikin. Karki Barsu
kara zub'e."
"Insha Allah! Zaka same ni da zama me adalci akan kome."
Tsaki Hajiya Surayyah tayi sannan ta tashi zata fita, kamar zata bangaje Hajiya Uwani, bata
hanya tayi tare da cewa.
"Allah ya kyauta, wannan al'amarin ya kamata ya tsaya haka sabida akwai surukai ga kuma ciki
ake jikinki,fada ba namu bane, tunda mun girma muna dab da ajiye jikoki."
"Kina bakin ciki ne da cikin jikina? Dan ke baki samu ba."
Wannan book din na kuษi ne akan 300โฆ haka ma katin mtn 300โฆ
0472282105 Ramlat Abdulrahman Manga GTBNK, zaku iya tura shaidan ku ga Zahrah
+2347035133148. Yan Nijar su sami Nana Aicha+22784506476
[11/13, 8:05 PM] My Zahrah: https://my.w.tt/ucS0zPJzcbb
๐๐๐ ๐๐๐๐
<๐ฒ๐ ๐๐๐๐ ๐ซ๐๐๐ ๐๐ ๐๐๐๐ ๐
๐๐๐ ๐ฒ๐๐๐๐๐>
https://my.w.tt/pvpSrJ4R5ab
โ๐ธโค๐ธ๐๐ธ ๐โ๐๐๐ผโ'๐ ๐ธ๐๐๐...
แด๐๐ข_แด
๐๐ฆ๐๐ฎ
Bismillah Rahmani Raheem
#Sawun Barawo
1โฃ0โฃ
A hankali yake kurb'an tea din jikin shi da zuciyar shi tana ingiza shi, zuwa wani guri na
daban. Bai gama sha ba, ya ajiye kudi da cup din ya bar gurin. Cikin sauri.
Mamaki ya kama su, wannan mutumin da baudaddiyar hali yake, share batun suka yi. Yana
tafiya wani mutum ya tare shi. Yana kallon shi, yace mishi..
"Yallabai!" Kafin ya amsa mishi AM rufe Aamil da duka, sosai fa. Suna fadin..
"Mara mutunci, shi ne ya dakar mana Yan uwan, dole shi ma mu dake shi." Zuwan yan sanda
ya sasu suka bar gurin. Da gudu suna zuwa suka tambayi abinda ya faru. Cikin jin jiki yace
musu.
."babu kome" ran shin son maganar shi ta karu fiyye da baya ma, kawai yana abu kamar ba shi
ba.
Haka suka rabu ya wuce gida. --- yana tsaye gurin aikin motar su, Ya mike zai dauki abu, kamar ance ya juya tana zuwa ta
kifa mishi mari, sake baki yayi tare da kallon ta.
"Ka same ni a gida, tunda abin da ka zab'a kenan!" Ta juya ta shiga BMW dinta, tana huci har
zata wuce tace mishi.
"Zan rufa maka asiri amma yau sai mun je casu!."
Cikin jin haushi ya nufi inda take zai bude motar ta ja motar da mugun gudu, tare da saka
sunglass dinta, tana dariya. ----
A hankali yake fitowa daga Station na yan sanda bayan ya an mishi gargad'i kar a kuma samun
shi da laifi, cikin jin haushi da takaici wanda yake kwance bisa fuskar shi. Yake tafiya. Mota aka
bude mishi ya shiga ya zauna.
"Mr George! Meke faruwa dani ne? Ban san me yake faru ba, sai dai kawai yanzun muje titin
Church, ina son zuwa gurin"
Da sauri aka ja motar, koda suka isa. Sun sami wasu matasa irin kartin nan, suna rike hannun
su. A hankali yaji zuciyar shi tana tilasta mishi ya fita daga motar, ya rufe su da duka, koda ya
fito suka yi ido biyu dashi. Guduwa wasu suka yi dan sun san ko minti biyar ba ayi da suka sha
mazgar shi ba, amma ya kuma dawowa sabida ya mai dasu jakuna. Da gudu suka bar gurin.
Gayen ya fitina su gaba daya garin washington, babu layin da bai sani ba. Bin dayan su yayi da
gudu, ai kuwa ya kamo wandon shi. Mutumin na juyawa ya zabga mishi naushi a fuska yadda
zai kwace. Aikuwa nan ya zube hancin shi ya fara zuba da jini.
Da sauri Mr George ya fito yana me rike shi, ya tashi zaune. Yana faษin.
"Ban dan meke faruwa dani ba! Yanzun zan yi abu zuwa an jima zai zama kamar bani ba. Idan
zaka fahimta ina wasu abubuwa kamar me mutum biyu a tare dashi, ina jin tsoro sosai."
"Yallabai ana jiranka muje daga baya zamu tattauna akan batun."
---
A garejin da Aamil yake aiki kuwa, yau Lahadi babu aiki. Dake da shi daya ne, sai yaji yana
sha'awar ya nufi Church abinda yazo mishi kenan. Dan haka ya dauki key din motar Max, yana
tafiya tare da niman Church din da yayi mishi yaga wasu guda biyu amma bashi yaji zuciyar shi
ya aminta da su ba. Dan haka ya cigaba da tafiya har ya isa wani babbar Church me suna santi
mary, anan yayi parking hango wannan yarinyar da ta mare shi yayi da sauri ya tsallaka, yana
zuwa inda take kawai ya tsinka mata mari, dukda akwai jami'an tsaron da suke kula da ita bai
hanata su mishi caaa ba. Juyawa yayi tare da zabga musu harara.
Sannan ya bar gurin.
Ko minti biyar bai yi ba, da barin gurin sai ga shi sun kuma dawowa da Mr George
tare da Mahaifin yarinyar suna isowa ta kuma kifa mishi mari, rike fuskar shi yayi tare da jan
hannunta suka bar gurin.
..
"Meye matsalar?" Ya tambaye ta. Sanyayye, kai bakinta tayi ta sumbaci bakin shi tana kuka,
kauda kan shi yayi sannan yace mata.
"Kinga ni bana son irin wannan abu,nasha gaya miki rayuwata da taki a kwai, banbanci don
Allah ki bari zamu sami matsala akan haka!"
."amma mari na kayi." Kafeta yayi da ido, sannan yayi kasa da murya yana fadin "kinyi hauka
ne?"
Cikin hasala tace mishi,
"Ga zahiri! Idan baka daina min rashin mutunci ba, zan cire maka zobensa!"
"Toh sai me?"
"Kunga ku daina wannan shirmen, kun kusan zama guri guda."
Bai idda rufe baki ba, sai ga yan sanda, mika musu shaidar kama shi yayi dafe goshinsa yayi
cikin gajiya da damuwa yace.
"Toh muje!"
Haka suka tasa keyar shi har ofishin yan sanda suka fara bincike.
***
Jigawa state
Dutse.
Wai-waiye Ummita tayi sannan ta saka hannu ta kwashe namar miyar da ake, ta juye a cikin
kwano, sannan ta rufe murfin tukunyar ta taso zata fita suka haษu da Ya Hindatu, kamar zata
sake kwanon, amma cikin karfin hali ta daure fuskarta ta wuce.
Tana fita itama Ya Hindatu, ta bude zata fita sai ga Raliyah matar Mahmoud, da sauri ta
sauke murfin miyar a kafarta.
"Innalillahi! Dama Goggo kece kike kwashe mana naman biya ake zargin mune muka
kwashewa da kan mu?" Ta faษa da karfi yadda kowa na gidan zai ji.
"Ke Yar nan, dubi kaina cike yake da furfura, me zanyi da namar miyar kuma?"
"Ai Sharri nayi miki? Wato karya nayi miki a kafar waye murfin tukunyar ta fado?"
Cike da bakin cikin Ya Hindatu take kallon Raliyah ga sauran matan gidan sun zo.
"Amma Yarinyar nan Allah ya isa tsakanin mu! Yar banza ina namar yake da nadiba."
Ya Hindatu ta tambaya a fusace, lokacin da yar ta Hasnah tazo. Bude tukunyar Amarya tayi
taga an kwashe namar Sosai.
"Toh gashi nan dai! Babu namar an kwashe rabin namar."
Wani malolon bakin ciki ne ya kama ta, tare da jin kunyar da bata tab'a jin irin shi ba. Idanunta
na cika da kwalla tace musu.
"Wallahi na rantse muku da!"
"Babu rantsuwar da zaki yi mana, sabida Allah da. Mu girka ke da wadancan Yaranki kuna
zaune. Gyaran albasa baku mana balle bare maggi, baku da aiki sai gulmar wancan da fadar
wannan. Mu dai Allah ya isar mana?" Daga haka suka ja tsaki suka fita daga cikin Kitchen din..
Kusan abinda ke faruwa kenan a cikin gidan, da can baya ba a sata. Amma yanzun gidan
wallahi ko bera sai haka, Ummita da Fa'iza matar Faruq. Idanun su bakan abun mutane, suna
gani zasu dauka. Na Ummita ya b'aci domin kuwa ita har dakin mata idan tafita tana shiga ta
diba mata abinci tafito.
Amma dake sun rena matar Isah, ita suke daurawa sata domin ita irin mutanen nan ne, masu
shishigi bala'in.
..... Bayan kome ya lafa, Ummita ta shekawa mijinta tuwo miyar eguzi, tare da tsokar
nama,da za a kai kasuwa ta haษa har da na mijinta, haka ya taro abokan shi, suka ci. Sai murna
yske matar shi ta sheka miya me dad'i.
***
Hadeja
An shera mata kitso me shegen yawa, gashi bakin gashin nan siษi, har bayanta. Kuka take
idanunta madaidaita, sun kumbura, dan bakinta nan sai wani bari yake kamar an jefata cikin
ruwan ฦanฦara, tana zaune ta saka abinci a gaba, tana shasheka.
Su kansu tausayinta suke ji, dan har ga Allah basu kaunar rabuwa da Yar mareniyar su.
"Sidrah!"
D'ago jajjayen Idanunta tayi sannan ta maida shi akan abincinta, idan aka cire kwayar idanun ta,
da hakorinta, da tafin hannunta. Kome na Sidrah baki ne wuluk ma kuwa, gata da kyau me
sanyi, tare da nutsuwa a tare da ita, gashin giranta wanda ya kasance mai laushi da sheki ya
kwanta, kwalla ne ya jika Eyelashe ษinta, sai suka wani fito zarara, matsa lumshashen idanunta
tayi sannan ta dan ciji lips dinta, kafin ta sauke wasu kwalla masu zafi.
"Innah! Don Allah karku kai ni, ku bar ni anan gidan, wallahi duka ake min."
"Toh Sidrah ya zamu yi, sunce lallai amai dake, sabida akwai baikon Yayanki akanki, kuma
babu amfanin mu barki kar wani abu ya taso." Inji Kanwar Mamanta.
Cikin kuka tace mata.
"Ni bana son zuwa gurin su, kawai ku barni anan mana!" Tasowa tayi ta zauna a gabanta,
sannan tace mata.
"Kiyi hakuri! Wata rana sai labari, kiyi kokarin rike mairaicinki." Gyada kai tayi sannan Kanwar
Mamarta ta fara bata abinci tana karb'a wanda tayi imanin daga yau tayi adabo dashi tana ci
tana kuka har ta gama.
Sannan aka wanke mata kafarta, da hannun ta wanda, wanda aka mata lallen yayi kyau sosai,
sai har yayi kyau da ita. Jaka guda suka hada mata na kayan sawa, sannan suka tattara ta,
bayan sun saka mata. Hijab ษinta yar Karamar, yayi mata Kyau. Haka suka tawo da Kanwar
Mamarta me suna Sabuwa, kafarta sanye da takalmin Sino, kai Yarinyar taga gata babu iyaka,
Tunda suka doshi kofar gidan, gabanta ya fad'i, rike hannun Kanwar Mamarta tayi, jikinta
yana sanyi zuciyarta yana girgiza.
Idan baka tab'a fuskarta halin da, Sidrah take ciki ba, ba zaka tab'a gane yadda take ji ba, ji
take wani tsoro da laifin da bata san tayi shi ba, take zargin ta aikata. Duk sai ta fara tsarguwa
da kanta, har suka shiga cikin gidan da sallama, wani irin kuka ne ya zo mata, amma haka ta
had'iye, har suka shiga shashin Lantana.
"Lale maraba, da zuwanku Sidira, kece haka. Lallai kin sha gida yarinya kinyi kyau da kiba
abinki, sannu Sabuwa, an dawo min da ita"
"Eh Lantana gata nan, kin san da D'a da dukiya ba a musu,, mugunta, koda Uwan Baba ta haifi
Sidrah tasaka rai zata moreta, amma da Allah ya tashi ikon shi sai ya dauke ta, gashi irin
wandanan zaki samu. Su fitina ce a cikin al'umma. Su din kamar haske ne a idanun duniya, shi
yasa ba a cika kuntatta wa maraya ba sai ka ga an sami matsala, ga amanarta dan nasan wata
rana goyon guba, zata iya sonki sama da mu, kin ga kenan ka shirya mai kyau kaga me kyau
duk yadda kika shirya al'amarin ki sai ki samu Ubangiji ya shirya nashi. Shi Alkhairi ko sharri
yan aike ne! Da zaran ka tura su zasu dawo maka da abinda ka aika dasu,ba abin mamaki
bane wata Rana idan Sidrah ta zama wani abu kafin Ni na moreta kece zaki fara moranta, kinga
kenan kinfi Ni kusa da ita, don Allah a kiyayye gaba konewar da tayi banda a lokacin sanyi ne
da jikin Yarinyar nan ya lalace, kuma nayi imani da Allah, ba zaki so kiji ance kinyi sanadin Yar
kishiya ba, shi hisabi tun daga nan duniya ake yinta idan ka je lahira sai kayi bayani da larabci,
Allah yasa mu dace....
Wannan book din na kuษi ne akan 300โฆ haka ma katin mtn 300โฆ
0472282105 Ramlat Abdulrahman Manga GTBNK, zaku iya tura shaidan ku ga Zahrah
+2347035133148. Yan Nijar su sami Nana Aicha+22784506476
#Mai_Dambu..
[11/13, 8:05 PM] My Zahrah: https://my.w.tt/AHFSeMVsfbb
๐๐๐ ๐๐๐๐
<๐ฒ๐ ๐๐๐๐ ๐ซ๐๐๐ ๐๐ ๐๐๐๐ ๐
๐๐๐ ๐ฒ๐๐๐๐๐>
โ๐ธโค๐ธ๐๐ธ ๐โ๐๐๐ผโ'๐ ๐ธ๐๐๐...
แด๐๐ข_แด
๐๐ฆ๐๐ฎ
Bismillah Rahmani Raheem
1โฃ2โฃ
#Jajantawa
"Yallabai! Ka bari mu maida ka gida, akwai matsala. Wannan rigimar ba sabo bane dole Madam
ta dakatar da Rio! Dole a dakatar da wannan badakalar."
Zafin da yake ji ya sashi fara fita hayacin sa, tare da juya kanshi. Kafin su isa gida motar asibiti
ta iso, sabida kiran su da akayi, can suka nufa. Aka shiga bashi kulawa tare da allurai. Sabida
sun fahimci ciwon shi ne yake son tashi.
*
Hadeja
Tun dawowarta, suka kwashe kayan da tazo dashi, basu bar mata wasu na kirki ba.
Wanda aka bar mata shi ma, wai dan kar a kaita gidan Yan uwan Mamanta babu wani sakakken
kaya ne aka bar mata na fita kala biyu.
Wata Jumma'a, taje gidan Kawunta Yakubu, ranar Lantana ta mata wani irin duka, wanda ya
kwantar mata da jini, a gefen idanunta, shine da tazo Yakubu ya hanata komawa sai Washi gari,
ya saka matar shi Balaraba, tayi mata wanka tare da wanke mata kanta domin kwarkwatan sun
dawo, kuma ga wasu kuraje da suka fito mata su ba Kazuwa ba, kirci dan sun fi kazuwa ma
masifar kaikayi.
Ana gama mata wanka, ya shirya ta suka zo gidan, dake da safe ne.
Ya samu mazan gidan, a kofar gida, suna shirin tafiya kasuwa, ya sauke ta a babur din shi,
sannan ya mika musu hannu suka gaisa. Kafin ya ce musu.
"Zaku yi hakuri da abinda zan fada muku amma iyakar gaskiyar kenan, Mun so kwarai mu rike
Sidrah, amma kuka ce mu bar muku ita, ta zauna da yan uwanta, sai dai bamu ki ba. Amma
kuna daidaita adalci, a tsakanin su kuwa?
.dan girman Allah, ku dubi fuskar Yarinyar nan mana! Ku duba ku gani, dan bata da uwa sai ta
zama mara daraja? Dan bata da uba sai ta zama Allah sarki. Mu dai don Allah idan ba zai zama
damuwa ba ku bamu ita don Allah zamu zauna da ita, don Allah, domin yau an mata wannan
dukar, gobe bamu san wani irin duka za a mata ba. Yarinya sai kace ba jininku ba.
Dube yadda jini ya kwanta a idanunta, haba inda Kamilu da Safiya suka tafi kuma zaku tafi. Dan
duniya ba matabbata bane, dan haka kuyi hakuri ku barmu mu tafi da ita, dan mu muna
kaunarta."
Shiru suka yi, tare da rasa tacewa. Suna kallon fuskar yarinyar da har zuwa lokacin bai sab'e
daga dukar da Lantana tayi mata ba.
"Malam Yakubu, muna baka hakuri Insha Allah ba za a kuma ba, don Allah kuyi hakuri. Mun san
ana cutar da Sidrah, amma Insha Allah, daga yau ya zama tarihi ba zamu kuma aikata haka ba,
kuma zamu riketa domin nan da wasu watani za ayi bikinta, kaga kenan dole mu kula da
al'amarin ta."
Sun jima suna tattaunawa, kafin yayi musu sallama, yana tafiya suka shiga cikin gidan, kaf
mazan gidan sai da suka yiwa matan su tijara, haka ya kuma fusata Lantana, ta kuma cin
alwashin ba zata bar Sidrah ta huta ba, shine ta tsira mata, wani mugun hali, idan aka yi sabon
abinci ba zata ci ba, a lokacin sai kowa yaci ya koshi an jagwalgwala, sai a zuba mata shine
mata, idan kuwa tayi laifi bata da abinci sai dai a dama mata tuwo da dandanon. Shine bakin
rabonta. Gashi gidan akwai wasu masu sayar da rake, da dabino, suna daurawa a tire. Sunan
fita dashi.
Idan dare yayi mazan gidan suka shige cikin iyalan su, toh Kananun yan matan gidan, soron
gidan suke zuwa inda masu sayar da raken suke, suna lalata dasu, domin kuwa. Zasu zo
matasan suna goga musu gaban su, har mazan suyi realizing. Gwanayen abun dama Sahiya
da takiya, sai Zubaina, sauran yaran matan basu sani ba.
Kuma karku ce wani abu ake basu, bai wuce Naira dari biyu zuwa sama bane, sai ko take da
dabinon da ake basu. Sidrah tasha ganin su, amma ita ba irin mutanen nan ne, masu yawan
magana ba, kuma tsoron su take.
....
Idanunta ne cike da kwalla, tana kallon damammen tuwon da aka bata, juya shi tayi tana kallon
yadda kowa yake cikin sabon abinci, shinkafa da miya. Wacce yaji wadataccen kifi, kasancewar
hadeja akwai babban dam, sunkuyar da kai tayi tana had'iye yawunta.
Kafon idanun mutane Saratu tayi, ta raba abincinta rabi, sannan ta zuba a cikin takardan kosai
da suka ci na karyawa, duk da Sidrah ce ta sayo musu, amma haka suka hanata, sai da Saratu
ta ษincina mata, ta ajiye wurga mata. Tura mata takardan shinfaka tayi, da sauri Sidrah ta dauka
ta fara ci, hannu baka hannu ฦwarya.
Suna gama ci, suka nufi bakin rijiya, diban ruwa. Takiyah tana zaune tare da Haule, sai
Sahiyah. Tare da Zubaina. Suna diban ruwa,
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 6 Chapter of 13