Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
yake kamar Kowa, masu zuwa Umrah an daga dai bayan bikin zasu. --- Yau saura kwana uku, bikin abin mamaki sai sako aka Alhaji Ma'aruf ya samu Office din Aamil a rufe yau kwana bakwai baya zuwa aiki. Da aka shiga ciki kuwa aka samu Zungurerren takardan ya bar musu kasar.. _Nasan amarya tana gudu idan bata son aure Amma ango ya gudu 󰣸󰢇󰚥 Muazzam fito ka kare kanka Wallahi ba ayi kome ba a labarin ko sunawa ba ayi ba, amma nasan mun dauki hanyar Chakwakiyya Ango ya gudu_ Wannan book din na kuɗi ne akan 300₦ haka ma katin mtn 300₦ 0472282105 Ramlat Abdulrahman Manga GTBNK, zaku iya tura shaidan ku ga Zahrah +2347035133148. Yan Nijar su sami Nana Aicha+22784506476 [11/13, 8:05 PM] My Zahrah: https://my.w.tt/GbW5hwzNbbb 𝐔𝐖𝐀 𝐁𝐈𝐘𝐔 <𝑲𝒂 𝒔𝒂𝒚𝒊 𝑫𝒂𝒚𝒂 𝒌𝒂 𝒔𝒂𝒎𝒊 𝒅𝒂𝒚𝒂 𝑲𝒚𝒂𝒖𝒕𝒂> ℍ𝔸ℤ𝔸𝕂𝔸 𝕎ℝ𝕀𝕋𝔼ℝ'𝕊 𝔸𝕊𝕊𝕆... ᴍ𝐚𝐢_ᴅ𝐚𝐦𝐛𝐮 Bismillah Rahmani Raheem #Juriya 0⃣9⃣ "Meye abun bakin ciki? Cikin dake jikinki? Toh Allah ya kyauta." Ta bar dakin abinta, dan ta lura baki daya jahilci na damun Hajiya Surayyah. Washi gari da safe bayan an gama abin karyawa aka kira amare, suka shigo da farko zasu yi rawan kai, ganin yadda take musu bayani, wani abubuwan na girki ma basu sani ba, sai jikin su yayi sanyi, musamman yadda take wurga musu turanci, take duk suka sha jinin jikin su, bayan ta gama sannan tayi musu sallama zata tafi aiki. Raba kan su, suka yi wasu suka dauki wani aikin wasu suka dauki wani. Sun nutsu suna aikin kawai, zaka dauka wani abun Arziki zasu aikata, "Sannunku amare aiki ake haka?" Inji Hajiya, d'ago kai suka yi tare da zuba mata ido, kafin aka samu Ummita tace mata. "Eh Hajiya!" Gyada kai tayi sannan tace musu. "Hala bata gaya muku ana kaiwa Kasuwa ba? Wannan matar akwai bakin ciki a ranta, dan haka kuyi abinda yayi muku kawai karku dauki tsarinta." ""Toh Hajiya" suka ce mata. . Hajiya na fita Hindatu na Shigowa, kallon su take kafin tace musu. "Uwani bata gaya muku muna son yaji ba? Toh ku zuba mana gishiri sosai!". "Amma kuma tace mana Abba bai da lafiya bay..." "Ke Ummita! Babu ruwanki da wata mata a gidan nan idan ba zaki iya girkin ba, wacce shashin ki!" Inji Surukata Hajiya Surayyah, "Toh umma." Dan haka taja bakinta ta shiru, sai ya zamana tsakanin Hajiya da Ya Hindatu anawa juna wani irin kallo. Kafin kowacce ta bar kofar. A hankali suka gama aikin aka zuba na shago, tare da zuba na cikin gidan, suka dauki nasu suka watse. Bayan wasu mintuna aka dawo da abincin Alhaji Ma'aruf, da kanshi ya kira Hajiya Uwani, yayi fada sosai. Sannan yasata dole ta dawo gida ta mishi abinci yana jira. Hakuri ta bashi daga haka bata kuma cewa kome ba. A hanzarce ta dawo gida, tare da fara aiki babu shiri. Matar Ali ce ta shigo gidan ta ji kamshi na tashi, kasa hakuri tayi ta leka kitchen ɗin taga Hajiya Uwani da Aashiq da Aseed tare da Abdus Samad, suna aiki su yaran sun mai da hankalin su kan abinda suke mata, itama ta kuma mai da hankalinta kan girkin ta. Wanke namar kaza Aashiq yayi tare da ajiyewa a choping board, ya shiga yankawa yana zuba mata a cikin kwando, Aseed yana barbada mishi garin flour me mix din kayan kamshi dangin curry da thyme, ingredients da sauran su. Abdus Samad yana yanka Albasa, tare da tomatos. Sun mai da hankalin su sosai. Ita kuma tana fama da hada cus-cus, jollop din shi. Dake Yarinyar wayayya ce, shigowa tayi tare da gaisheta tace mata. "Da wanne za a taimaka miki?" D'ago kai tayi tare da sake mata murmushi tace mata. "Huta abinki latifah!" "Ai bazai yiwu ba, kawai ki gaya min abinda zan yi, indai har Mazaje zasu shigo aiki meye amfanin mata irina." "Da kin barshi wallahi!" Ta faɗa mata cikin lumana, "Don Allah." "Shi kenan! Jalil!" Ta kira yan biyu, da gudu ya fito. "Gani Ummi! Kiyi sauri ana spider man." "Lallai zan kashe kallon nan, tunda lokacin islamiyya ya kusa..ka je frig ka dauko min fruit maza ka kawo min, kace Jalal ya tayaka dauko min, kayan salat din nan." Haka yaran suka yi ta kwaso mata duk abinda take buƙata, sannan tana aiki tana duba agogo, tare da turawa Alhaji Ma'aruf sakon hakuri, dauko wani katon bowl tasa Aashiq yayi ya kawowa Latifah, tana gama wanke ya'yan itacen ta shiga yanka su, Hajiya Uwani tana nuna mata yadda zata jera. Shigowa Hasnah tayi tana kallon yadda Hajiya Uwani da Latifah suke aiki, sannan tafita, can suka kuma shigowa ita da Hajiya. "Uwani aiki ake haka!" "Eh hajiya!" Ta bata amsa a takaice. "Toh kar a manta da tsufar mu dai, a tuna da cewa dana ake aure." "Hajiya kiyi hakuri! Amma wannan abincin na baki nayi bana Alhaji bane, gurin aikina zan kai." Wani irin shiru ne ya gifta tsakanin su, Latifah tace. "Ummi duba, haka yayi da ace akwai Strawberries honey ko Apple honey, sai a zuba a kai. Sannan a saka sweetened condensed milk a zuba yummy." Murmushi Hajiya Uwani tayi sannan tace mata. "Bani da honey's din amma ina da condensed milk." "A kawo kiga yadda ake yin shi, i holp Abba bai da diebetis?" Ta tambaya, murmushi Ummi tayi wanda kusan zan iya cewa dabi'arta ce, sannab tace, " Bai da shi!" Ana kawowa ta zuba a kai, sannan ta dauki foil pepa, ta nad'e tiren dashi, sannan ta kalli Hajiya Uwani, tace mata. "A ina zan saka?" "Toh saka a wannan freezer din, kafin mu gama kar yi dumi,!" Ta nuna mata firij din dake kitchen din. Kallon Juna Hasnah suka yi da Hajiya, sannan suka fita da guntun kwadayin su. Amsar kasar da flour din tayi, tare da kallon Ummi tace mata. "Wannan muna kiran shi Orange chicken, amma India suna kiran shi briyami." "Kina da experience Sosai akan girki." Inji Hajiya Uwani ni.. "Eh Ummi, nayi diploma na akan girke girke ne, sannan na kuma yi HND na akan girkin, shi yasa nake da ɗan sani kadan akan girki. Toh da zan tafi University ne, Baban mu yace na bari idan mijina yana bukata na tafi a gidan shi!" "Goodluck! My dear. Kice bani daya bace nake da sani a bangaren girki ba, lallai zamu ci dad'i. Ina koyarwa a jami'ar nan Dutse, amma na shiga class na girki 2002-2003, na sami kwarewa akan sarrafa abinci, Yanzun Muh'd nake so kafin ya shiga SS1 na saka shima ya fara samun horo akan girki, Babana yace zai yi wani aiki ba, mr Chef ne shi, ko Abdus Samad." Dariya suka saka lokacin da Hajiya Surayyah da Amarya suka shigo, juyawa Latifah tayi hannunta kwaɓe da ruwan kwai wanda aka dama da flour za a soya, kazar d'anyen ta. "Mamarmu ina wuni! Yanzun zan shigo ina taya Ummi aiki ne." Ta faɗa kanta a kasa.. "Ya kamata kan dan kin san nice Mahaifiyar Aliyu! Wasu tsabar rashin tsoron Allah, sukan janyo abinda ba nasu ba, su maida nasu. Amma Latifah ba Aliyu yace miki karki na shiga harkan kowa ba, sai d'akina ba?" Wani irin kallo Yarinyar ta bita dashi sannan tace mata. "Inji Aliyu?" Mamaki ne ya kama kowa, jan wayarta da yake samun window tayi tare da kiran layin shi, tace mishi.. "Wai kacewa Mamarka kace kar na shiga cikin hidimar mutane sai na ta, Aliyu kasan a gidan mu, ba a koya min tashin hankali ba, sannan ban iya ba, idan kasan gidan ku akwai damuwa maza zoka mai dani gidan mu, ban sha'awa damu." Kome ya ce mata ta sake tsaki tana fada mishi dalilin da yasa takura shi, cikin murna yace mata tayi ta shigowa tana kuma samun kwarewa akan girki dan Ummi ba karamar gwana bace, karshe suka yi sallama, kallon Hajiya Surayyah tayi sannan tace mata. "Muje Hajiyar mu na baki hakuri." Wanke hannu tayi suka fita, kome ya faru, sai dai yarinyar tafito hankalinta kwancen. Suka ci-gaba da aikin su. Anan Hajiya Uwani take mata fada akan abinda tayiwa surukarta, ta kuma ce bazata kuma ba. Koda suka gama, ta dauko wani babban kula, ta cikawa Latifah abincin sannan ta nufi hanyar gidanta. Koda aka kai abincin kasuwa, mutane ribibin abincin aka yi har da Ali dan yasan matar shi tana cikin aikin abinci. *** Zaune take a gaban murhu, tayi futufutu da ita, sai jan majina take, sabida sanyi da ake na watan Janairu, sake jan hancin tai, a kawo na biyu. Gashi babu wani rigar sanyi a jikinta. "Kwasss!" Aka kafa mata rankwashi, agigice ta d'ago kanta tare da murza hannunra a kan. .dan ji take kamar ta sake fitsari. "Munafuka, wutar abincin har yanzu bata kama ba." "Wallahi bata kama ba," tana sosa kanta, cikin jin zafin rankwashin. Komawa daki Lantana tayi ta kuma kwaso kayan wankin su, ta labta mata, sannan tace? "Maza ki fara aiki ina jiranki!" Cikin rawan jiki. Tana aikin girkin tana kuma wankin, har dumamen ya fara konewa, sannan ta sauke amma sai da ruwan zafi ya zuba mata a kafa. Kara tasaka, tare da yarfe hannun. Tana cikin wannan yanayin ashe bakin zaninta dake roba ce ta kama da wuta, lokacin Sahiyah ta fito daga dakin su. Ganin yadda take tsalle da ihu, tare da wurgi da zanin ta faɗa cikin kwatar da suke zuba wanke wanken. Tana kuka sosai. Sabida ruwan roban da ya koma cinyarta. "Subhanallahi! Me ya faru?" Inji Malam Haliru, tab'e baki Sahiyah tayi tare da cewa. "Wasa da wuta take ya kama zaninta" Cike da mamaki yake kallon Sahiya, sannan yace mata.. "Shine baki kai mata a gaji ba? Sahiyah anya zuciyarki akwai imani a cikin shi? D'an mutum ya kama da wuta ki tsaya kina kallon shi, wannan rashin Imanin har ina?" Fitowa Lantana tayi zata shiga bala'i, amma ganin Yadda Sidrah take cikin kwata, ta tashi tare da dibo ruwa ta fara wanke mata jiki, wani irin tsoro ne ya kamata, sakamakon ganin yadda fatar jikin yarinyar yake salubewa. Jinjina girman rashin Imanin Sahiyah tayi, ta juya tare da ɗaukar tsagun itacce ta shiga maka mata, tana faɗin. "Bani da mutunci! Amma ina da birbidin imani, ba zan tab'a barin dan adam ya kama da wuta, ba ina kallon shi wato gaji nan mara tausayi da jin kai, Ni zaki jawa magana, Dangin Uwarta suna gari su zo, suga abinda ya faru. An bani na iya sukara nasu akai, yar banza mara imani, tabbas zaki iya barin yan uwanki tunda kika kasa jin tausayin ta." "Kyaleta ki shirya yarinyar mu kaita gidan Sarkin makera, a zuba mata magani, dan wallahi ban san me zancewa Binto ba, idan tazo. Tunda Munki basu sannan mun kasa riketa." Haka suka wanke mata jikinta, sannan suka dauke ta zuwa d'akin suka saka mata hijab, sannan suka fito da ita, zuwa gidan Sarkin makera, suna zuwa yasa aka sayo madara ta ruwa, sannan ya kuma sanya aka dama mata da magani aka bata, sannan ya shiga zuba mata maganin. Kafin su dawo har ya kame tsaf. Dama cinyoyinta ne suka sabule, ta gama. Sai samar kafarta, shima ba sauki. Koda mutanen gidan suka sani, kafin kace me! Har an kaiwa dangin Mamanta gulmar, ai kuwa suka zo dayawan su, ana aka shiga rigima karshe suka dauketa aka dawo da ita gurin yan uwan Mamanta. Gatar da bata samu ba, shi aka shiga bata, kulawa na musanman,aka kuwa wanke kan nanda kumfar lux, aka saka wata me kitso ta mata kitso da maganin kwari. Washi gari aka sayo maganin makero aka shiga shafa mata. "Yaya Binto! Ina ga ki tafi da Sidrah Kano mana, dan wallahi ba wani kulawa take samu ba, duba kiga yadda ta koma, jiki duk Kazuwa, ga rashin abincin gina jiki." Inji wacce take bin Maman Sidrah Hakama, "Toh Hakamah idan na dauketa ai zasu ce an dauketa bayan akwai Maganar aurenta a kasa, ni bana son damuwa shi yasa zan na zuwa duk bayan wata uku ina dubata. Kuma kin san ma ai ba bamu zasu yi ba." Tunda taji suna maganar zasu mai data ta fara kuka, domin tasan ba zata tab'a zama a hannun su ba, gashi har kiba tayi .... Dutse. Bayan wata uku.. A cikin wata ukun nan matan su Faruq kowacce ta fidda halinta, idan ka cire matar Ali da kusan halin su daya da Hajiya Uwani. Dan har tafi Hajiya Uwani, tsayar da Iskancin gidan take kuma bata shiga gulmar cikin gidan, da aka ga bata da lokacin su, sai suka shiga ce mata tana da girman kai, halin su daya da Hajiya Uwani. Amma a bayan su, ake fadar haka. A cikin gidan babu wacce aka rena kamar Baria, matar Isah, wulakanci suke mata, idan kuwa tayi musu abu su rufeta da duka, gashi sun mai da ita kamar jaka.duk abinda ake itace zata ci aiki kamar baiwar su... ---- Washington DC. Federal capital state. USA... Destination Yau wata uku kenan da barin shi kasar shi ta gado. Kuma ya fara karatun shi cikin nutsuwa ba tare da wata damuwa ba. Wani abin burgewa, a can unguwar su, akwai masu maida tsohuwar mota sabuwa, dan haka jiya ya cika musu takarda kuma sun dauke shi. Shi yasa yanzun yake tunanin ko zai juya karatun shi zuwa Injiniyar kere kere. Kawai bai gama tunanin shi ba yaji an kai mishi wani bugu a kafad'arshi.. Zafaffe ya tashi zaune tare da juyawa yana kallon su. "Kai dan Ubanka, wato dan munce ka haɗa gwiwa damu, shine bari ka je gurin su Anthony ko! Toh yanzun zamu karya maka kafa." Kallon su yayi tare da jan wani iska, kafin ya nad'e hannun rigarshi. Tare da ɗaukar wani kujeran katako ya shiga rufe su sa mugun duka, sun ɗauka wasa ne sai da Aamil ya raka su har wajen makarantar. Sannan ya dawo yana haki. Sai lokacin dayawan mutane suka ganshi cike da al'ajabi suka zagaye shi suna fadin. "Yallabai me kake bukata? Yallabai ko a kawo maka karin abin motsa baki ne? Yallabai." "Mr rogers ka kyale shi bai cika son hayani ba, dan ko jiya mun hadu nayi mishi magana mr Gorge yace na rabu dashi." Kallon asalin mahaukata yayi musu, ya ciro kudi zai biya coffee da ya sha, suka ce mishi "Yallabai ba zamu amshi kome daga gare ka ba. Dan burin mu ka maye mana gurbin Mr Robert William." Ajiye musu kudin yayi tare da barin guri. Ko minti goma bai yi ba, sai gashi ya kuma dawowa, da sauri mutanen suka zagaye shi suna kuma mishi bayanin da suka yi d'azun nan. Murmushi yayi sannan ya bude baki dakyar kasancewar shi mutum ne da bai cika son dogon zance ba yace musu. "Mr Rogers! Nagode sosai," daga haka bai kuma cewa kome ba, kallon saurayin da yake bawa kowa coffee zai magana ya kawo mishi Green tea. Murmushi yayi sannan yace. " jackson bani coffee, nake so!" B sake yake kallon shi d'azun yace mishi Green tea yake so..... 🤔󰣸 Kuma dai. Wannan book din na kuɗi ne akan 300₦ haka ma katin mtn 300₦ 0472282105 Ramlat Abdulrahman Manga GTBNK, zaku iya tura shaidan ku ga Zahrah +2347035133148. Yan Nijar su sami Nana Aicha+22784506476 #Mai_Dambu.. [11/13, 8:05 PM] My Zahrah: 𝐑𝐔𝐖𝐀 𝐁𝐈𝐘𝐔 <𝑲𝒂 𝒔𝒂𝒚𝒊 𝑫𝒂𝒚𝒂 𝒌𝒂 𝒔𝒂𝒎𝒊 𝒅𝒂𝒚𝒂 𝑲𝒚𝒂𝒖𝒕𝒂> ℍ𝔸ℤ𝔸𝕂𝔸 𝕎ℝ𝕀𝕋𝔼ℝ'𝕊 𝔸𝕊𝕊𝕆... ᴍ𝐚𝐢_ᴅ𝐚𝐦𝐛𝐮 Bismillah Rahmani Raheem. #Alhini 0⃣8⃣ Bude wasikar Alhaji Ma'aruf yayi cike da bakin ciki zai karanta Alhaji Ahmed ya kwace wasikar a hannun shi. "Kayi hakuri!" "Ahmad! Allah Ya Shirya mana Zuri'ar mu, Amma kasan Aamil ya tozartani!" "Ka gama kome! Tunda ka nima mishi shirya, Allah ya tsare shi duk inda yake Allah ya duba Alamarin shi" "Ni ya tozarta! Insha Allah aure babu fashi bazan zarga mata igiyar shi ba, amma tabbas dashi za a daura auren nan duk ranar da ya dawo. Mutumin banza mara kirki." Bai kuma magana ba ya fita, ya d'ago kan tare da cewa. "Ahmad me zancewa Haliru? .me zan gayawa yan uwana, da wani fuska zan fuskance su? Yaron nan ya kunyata ni saura kwana uku bikin ya tsalleke yayi tafiyar shi kaji yadda nake ji kuwa?" "Kayi hakuri! Yayi laifi amma ka bishi da du'a'i, Allah ya shirya mana shi" inji Alhaji Abubakar, gyada kai yayi cikin jin tausayin kan shi, domin duk inda ake niman mara kirki Aamil ya kai. Kallon Garzali yayi driven shi yace mishi. "Kai ni gida!" Cikin tsananin tausayin, Abokan shi suka yi sallama dashi, ya nufi gida. Tun a hanya yake rike da kirjin shi. Kwalla na zuba daga idanun shi. Ba kuka yakewa Aamil ba tausayin Maraicin Sidrah yake, ya kuma san gidan shi ba zai yiwu ya dauko ta ba. Domin Idan Hajiya Uwani bata nan zata zama abin tausayi. Har suka isa gidan shi da yake bayan gidan gwamna, ya fita a hankali, ya shiga cikin gidan. Ya samu mata anata hidimar suyar cincin, kallo daya Hajiya Uwani tayi mishi ta fahimci yana cikin tashin hankali, dan haka yana shiga dakin shi ta bishi. Zama yayi, ta juya tare da dauko ruwa ta zuba mishi a glass cup, yasha sannan ya kalleta da idanun shi da suka cika da kwalla yace. "Aamil ya tafi! Ban san me zanyiwa Yaron nan ba, ya fahimci gatar da na mishi, ya tafi ya bar ni da kunyar mutane, meye na rage shi da shi?" Cikin nutsuwa sannan tace mishi. "Ka dauki haka matsayin kaddarar mu, Allah yana sane dashi da kuma mu, muyi mishi Addu'a a duk inda yake, kar mu watsar da Al'amarin shi. In yaso sai a dakatar da auren shi kafin nan yarinyar ta kuma girma, Yanzun ba zamu daukota ba, sai nan da wani lokaci. Domin idan muka daukota zai zamana zata yi ta walagigi a cikin gidan nan, dan haka ka barta Insha Allah zai dawo kuma zai amshi tayin da ka mishi da hannu bibbiyu. " "Toh ya zanyi? Me zan faɗa musu a fahimce ne, dan kowa zai ga kamar na barwa Aamil daman yayi abinda yake so ne!" Ya faɗa a raunane, "Duk wanda ya zargeka, bai san me ake kira tarbiyya bane, domin ai kayi ƙoƙari, Insha Allah Ubangiji zai dube ka da idanun rahama ya duba Alamarin ka." Sosai take gaya mishi magana masu taushi da dad'i, har ya sata ta kira sauran matan ya gaya musu, auren babu Aamil an d'aga nashi. Sun sha jinin jikin su. Suka yi ta kame kame, ko zasu ji me ya faru amma basu ji ba. Ya kuma je dakin Mahaifiyarshi ya gaya mata an fasa auren Aamil dan haka ta sake guɗa. Tare fadi, "Ga irin ta nan, ka haifi d'an da ya juya maka baya, tirr da ni ne na haife shi sai na tsine mishi albarka" "Hajiya ba zan iya tsine mishi ba, tunda ke da kika haife ni baki tsine min ba, akan me zan tsine mishi.!" Numfasawa yayi cikin damuwa sannan ya cigaba da cewa. "Hajiya lalacewar da Aamil yayi bai kai na wasu yaran ba, amma kuma a haka iyayen su suke jingina kome su rungume su. ... Akan me zan tsine mishi bayan Ni na koya mishi haka,ko sau daya ban tab'a damuwa da halin da yake ciki ba, kai na kawai da abinda kike gaya min nasani, shi yasa zan cigaba da mishi Addu'a har Allah ya dawo min dashi." Daga haka ya mike zai bar dakin, jiri ya nemi yar da shi ya dafe bango. Dakyar ya dawo dakin shi ya zauna tare da dafe kanshi da hannu bibbiyu. Karshe dai zazzaɓi ne ya rufe shi me mugun zafi. ** Hadeja "Wai ni Lantana ban gane ba, ba zaku yi kome na biki bane? Naga ita kanta amaryan baku gyarata ba, balle a mara wani abun Arziki.". "Baraka bana cikin da munafunci. Wani abin biki bayan kin san cewa Alhaji yace kar ayi kome haka zamu kaita daga ita sai kayan auren da suka kawo mata." "Yo ai zaku ja mata abin gori, har tsofarta. Kuyi mata abinda zaki yi mata na uwar goyo idan ba haka ba, wata rana zaku ji kunya shi rayuwar duniya babu kome a cikin shi sai rudu." Banza tayi da ita, bata kuma kulata ba, sabida bata ciki da gulma injita, dauko wata kodaddiyar nera goma tayi ta baddawa Saratu da take taya Sidrah tsifa tace mata. "Toh amara kirjin biki maza, zoki amsowa kawarki kumfar lux, ta bera goma a wanke kwarkwatan kanta, ko zamu huta karta bamu kunya da sosa soshe." Da sauri Saratu ta amshi kudin ta falla a guje kamar wacce aka cillata. Wato Lantana yaran ta biyar ne, Biyu maza uku mata. Atiku shine babba, sai Babangida na biyu, sai Sahiya. Sai Saratu da altine yar autan su, Saratu itace Sa'ar Sidrah, kusan tsayin su daya. . Kuma bata da matsala kamar

Chapter 5 of 13