An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels
11/13, 8:05 PM] My Zahrah: ππππ ππππ
<π²π ππππ π«πππ ππ ππππ π
πππ π²πππππ>
βπΈβ€πΈππΈ πβπππΌβ'π πΈπππ...
Bismillah Rahmani Raheem.
https://my.w.tt/EcTsIaOy2ab
_Allah subhanahu wata'ala ya halicci d'an adam domin ya bauta mishi, kuma bawai zaka kare
shi da kome bane! Sabida babu abinda zaka yi dan ka biya shi wannan kyautar da yayi mana!
Koda miskala zarratin bazamu tab'a karen shi da kome ba! Haka zalika ba zamu rage shi da
kome ba! An karbo hadisi daga d'an Abbas, yace Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama ya
fada mana cewa! Da zamu hadu mutanen farkon mu da mutane karshen mu, mu roki Allah.
Dukkan mu zai amsa bukatar mu! Ba tare da ya manta daya min mu ba! Ashe kuwa dole bawa
ya kasance mai godewa Allah da ni'imar da yayi mishi! A duk cikin halittun da Allah yayi. Babu
wanda Allah ya karrama shi kamar D'an Adam, a cikin Alqur'ani mai tsarki Ubangiji yayi batu da
yawa akan Dan Adam! Ya kuma bashi labarin kanshi a cikin Alqur'ani! Ubangiji yana sane yayi
mu masu banbancin Halitta. Wasu farare! Wasu bakakke! Wasu kuma zabiyoyyi! Kuma yana
sane da banbanta mana ra'ayin mu akan addini! Sannan ya kaddara wasu fararrun alamari
zasu iya shigowa tsakanin mu! Dan haka da wannan nake kuma godewa Allah da ya bamu
ni'imar da bamu isa mu saya ba sai dai mu gode mishi!_ Alhamdulillah!
1989/ July/ 21
Jigawa state
Hadeja General hospital.
0β£1β£
"Dan Ubanki idan kika kuma shigowa rayuwar Ma'aruf sai na saka an yanka min ke. Anyi min
Gunduwa Gunduwa da namarki, bake mayya ba sai na cofin Babanki yar shegiya, tsinaniya. Kai
idan na kuma see you a najeriya, a go cofin kan uwarki bake magret ba toh ko markade kike
babu sassauci a tsakanina da ke, yan banza me manyan idanu, maza take yor culot maki
sakawa ki bar garin nan dan uwarki kar na kuma ganin yor lege, a garin nan yar banza me
manyan idanu." Cikin shashekar kuka matar da bazata wuce shekaru ashirin da hudu ba, ta
durkusa a gaban wata mata wacce idanunta Babu alamun rahama tace cikin bagwaren hausan
da bai gama rike bakin ta ba,
"RiΖo yaro sai Maman shi don Allah ku bani baby na, i swear ba zan kuma came back to
Ma'aruf ba, please baba"
Tauuu suka dauke ta da mari sai da ta dungura, dai dai shigowar Nurse dakin da aka kai
Magret, cikin jin haushi Nurse din tace.
"Amma baku da imani, taya mace daga haihuwar ta ko hutawa bata yi ba, zaku zo ku sakata a
gaba! Kuna cin mutuncin ta, haba ku kuwa!" Kallon jelar gashin Magret a hannun Surayyah tayi.
Cikin mamaki take kallon tsantsar rashin mutunci a idanun su. Takowa ta yi tare da d'ago matar
cikin tausayawa ta ce.
"Mutanen na basu da imani, kuma zasu iya cutar dake, idan kika tsaya sai sun baki yaronki. Kiyi
hakuri kinji." Kallon kayan jikin jikin Hauwa. Riko hannunta tayi suka saka kai zata fita, ta kwace
hannunta, tana kuka tare da fadin.
"Karku rabani da Yarona, ku bani Yarona." Haka Nurse Salamatu taja ta suka fita. Kuka take
kowa ya ganta sai ya tausaya mata, har suka bar ward din, sannan ta kaita wani daki ta bata
kaya ta saka, riga daban zani daban. Sai dan kwali, da ta daura. Hawaye na zuba mata. Ta ce
mata.
"Please ga Yarona a hannun Allah yana kuma hannunki, ki saka ido akan shi, ki kuma bani layin
asibitin nan zan tafi idan na isa, US zan kira ki. Don Allah karki cire idanunki akan shi yaro
karami sun hanani shi." Haka ta riko hannun ta suka fita sai da ta samu wani a koru kura, ta
sakata wanda zai kaita Kano.
***
Bayan tafiyarta Suka dauki yaron suna kara jin haushin Hauwa wacce yar asalin Ζasar Amurika
ce, tafiyar Ma'aruf can karatu ya hadu da ita, inda suka yi aure sannan ya dawo da ita, Magret
William yar wani shahararren attajiri ne a garin newyork, ita kadai ya haifa, uwarta ta mutu ta
barta, shi ne ya dauki son duniya ya daura mata, ya nuna mata wata irin SOYAYYA kamar me,
sai dai zuwan Ma'aruf Adamu Hadeja, ya sata juyawa Soyayyar Mahaifinta baya tace tana son
Ma'aruf, duk yadda Uban yaso karta fada mugun rayuwa, haka taki fir. Sannan aka yi aure
tsakaninta da Ma'aruf, sai da suka shekara biyu. Sannan Ma'aruf ya gama karatu, yace zasu zo
ganin gidan zai dawo da ita. Tunda suka biyo jirgi suka dire a kano, taga yadda kasar Najeriya
yake, take tsoron barinta Ζasar Iyayenta ya kamata, tunda suka shigo hadeja. Ta haΙu da
Muguwar uwar miji, da yan uwan miji, tare da Yayar mijinta, da farko sun dawo da arziki me
mugun yawa, wanda Baban Magret ya basu, kafin su koma, amma suna zuwa Yaya Hindatu ta
kwashe kome hatta kayan sakawar Hauwa sai da suka kwace. Suka wurga mata wasu matattun
kaya, haka ta yi ta rayuwa, watan su biyar aka daura mishi Aure da Surayyah. Yar mijin Yaya
Hindatu, tunda ta shigo gidan suke. Mata cin mutuncin, tare da wulakantata. Sun dake ta, sun
zage ta. Gashi Ma'aruf yana dawowa zasu fadi karya da gaskiya babu bincike zai hauta da
duka, wahala tayi wahala. Tun bata jin Hausa har ta koya dan dole. Abin takaici da ban tausayi,
tana samun ciki zasu zubda mata shi, shi yasa wannan cikin tana samun shi ta boye musu baya
gayawa kowa ba, har ta fara zuwa asibiti a sace. Zuwa lokacin da ta haihu. Sun kwace yaron
ne, wai dan karta tafi dashi dan burin su. Tayi nesa da Ma'aruf karta zauna dashi domin ko sun
hada su, sukan shirya. Kuma sun san idan ta tafi da yaron Ma'aruf zai bita, idan kuma suka
sake ya bita, sunce zata rike musu shi. Da wannan nazarin Yaya Hindatu ta zuga Baba Mero ta
kora keyar Hauwa.
Dan haka lokacin da Ma'aruf ya dawo, Baba ta fashe da kuka tana kallon shi tace mishi.
"Dama sai da muka gaya maka, Ba zata tab'a sonka ba, gashi nan ta gudu ta bar yaron da yake
cike da bukatar soyayyarta, tur da wannan rayuwar, abin tausayi yaron da aka haifa ko dumin
Mahaifiyarshi bai ji ba ta tsallake shi" a zuciye ya amshi yaron, sannan ya zuba mishi ido, kwalla
na zuba mishi, ya sumbaci goshin yaron sannan ya kalli Mahaifiyarshi yace.
"Gashi nan sunan shi Aamil! Zan tafi na nima mishi abinda za a na bashi, yana sha. Ita kuma
Hauwa Ubangiji ya min Sakayya, Ni da Yarona." Ya mike a hankali ya bar dakin. Murmushin
mugunta tayi sannan tace.
"Babu shegiyar da zata mallake min Yarona." Ta cigaba da kula da jinjirin. Har Baban shi ya
kawo madarar da za a cigaba da bashi.
A wahale Aamil ya taso, ga rashin uwa. Yaron haka yayi ta fama da cututtukan, irinta Yara.
Lokacin da ya fara rarrafe, haka zai bata jikin shi da kashi, Baba cikin jin haushin kulawar da
Uban yaΖe mishi zata zage karfin ta ta zabga mishi duka, wani lokaci ya shiΙe. Wani lokaci haka
zai yi shiru, yana sauke ajiyar zuciya. Zai yi wuya ta dake shi bai kwanta ciwo ba.
Duk da gidan da suke family house ne, me cike da sassa masu yawa, shi yasa babu wanda
yake sanin uΖubar da Baba Mero da Hindatu suke bawa Aamil.
A hankali yaron yake girma, sai ya taso baya shiga cikin mutanen gidan nan. Sai ya
zama na ya taso da mugun tsoron mutanen gidan. Kullum yana cikin dakin, yana da shekaru
biyar, Baban shi ya samu aiki a Jigawa. Dan haka da ya tashi komawa da matar shi Surayyah,
sai ya dauki yaron, dakyar Baba ta barshi, ya dauki Yaron, suna komawa can kuwa ya saka
yaron a makarantar boko da islamiyya.
Sai dai idan ya tafi aiki, Surayyah bata taΙa bawa Aamil abincin matukar Ma'aruf yana
gida zata cika mishi kwano har yana zuba, idan kuwa baya nan toh, wallahi azabar duniya sai ta
bashi, ta dake shi ta kona mishi hannu. Ta zuba mishi gishiri, haka zai ta kuka tana dariya. A
hankali ya fara shanye irin azabar da take mishi, idanun shi ba bushewa. Yana wani irin
kangarewa, tare da zama mafadaci. A bayan gidan su yan shaye shaye suna zama, idan ta
daidaici dawowar Baban Shi zata kora shi gurin, yana Shigowa gida zata ce.
"Yaya nifa na fara gajiya da halin Aamil idan zaka zaga gurin yan shaye shayen nan yake zama.
Ka duba ma!" Yana zuwa zai same shi a gurin su, riko Yaron yake zuwa gida yayi ta dukar shi,
kamar wani baba.
Ita kuma haka na mata dad'i, haka zata yi ta murna. Gashi Allah bai bata haihuwa ba, duk
wanan azzabar ta take bawa Yaron.
A hankali yake girma, rashin jin shi yana kara bunkasa, fitinar shi na kara hauhawa. Har
zuwa lokacin da ya cika shekaru talatin cif a duniya..
β€
Wani irin bakin ciki ne ya tokare mishi kirji, kallon Aamil yayi wanda ya fito daga ban daki, ga
budurwa da ta kwana a d'akin shi tana shafa mai, Ganin Alhaji Ma'aruf yasata mik'ewa tana
kare jikinta, dauke kai Aamil yayi tare da kallon yarinyar yace.
"Dan Ubanki ba nace kar na same ki a waje ba, ki fita kafin naci Ubanki!" Ya daka mata tsawa.
Da sauri ta, dauki kayanta, tare da fita zata saka. Abban shi ya matsa mata. Ta fita, tana mita
ganin sai lokacin Aamil zai gabatar da sallar asuba. Karfe bakwai saura Kwata. Wani abin yaji
ya tsaya mishi a rai, kwalla na cika mishi ido. Yana tsaye har ya idar da sallah,kallon shi yayi
sannan yace mishi.
"Ubangiji kana ganin Bawanka, na fita hakkin shi na bashi tarbiyya, na kuma bashi ilimi. Ya
Allah ban san me nayi ka bani shi Zakka ba."
Cikin jin haushin Abban shi yace mishi..
"Idan baka bukata ka kore ni mana kamar yadda kuka raba Ni da Uw..." Tass ya wanke shi da
mari, sai da yaji marin sosai, dan haka ya juya tare da cewa.
"Yau zan bar maka gidanka, na shiga duniya, nasan akwai mutanen da zasu rike ni, kasan aka
kaunata ka samar dani, baku da wani aiki sai aibata Mahaifiyata, toh wallahi zan bar maka
gidanka, tun tasowata ban san soyayyar kowa ba. Ban san dadin Kowa ba, haka na taso cikin
kunci da rayuwa mara amfani, idan nayi abu kace ba tarbiyyar da kayi min ba kenan, ka tsane
ni, bayan baka san meye yake faru da ni ba, taya nima bazan dasa maka bakin ciki ba, zan tafi
na barku ku zauna da mutanen da suka fi maka ni?".
.daga haka ya fice ya bar dakin har ya isa bakin kofar, Baban Yace mishi.
"Kaje kaga Sidrah?" Cikin zafin rai ya juyo yana huci yace mishi..
"Abba kace baka kaunata mana! Wancan yarinyar da babu wanda ya kaita muni itace zan aura!
Yarinyar da bata wuce Jaririyar ba kake cewa naje na ganta! Yar shekaru tara, wallahi ko a yar
wanke wanke gidana bata kai ba balle yar da zan aura, Ni babu ita a cikin rayuwa, duk da ana
gaya min cewa mahaifiya baturiya ce, karshe sai ka Hadani da bakace, meye nayi da zafi da
zaku rasa kyawawan mata, ku bani sai wancan mummunar me kama da kwarangwal, yarinyar
da kafin namiji ya moreta sai bayan nan da shekaru ashirin.
Wallahi idan zaka nimawa Ali ita ba laifi, amma."
"Tabbas da kai za ayi auren! Ko kana so ko baka so! Aamil sai ka auri Sidrah, domin ba zan
lamunci zubda min mutuncina da kake yi ba, kaka dauko yaran mutane kana lalata tarbiyyar su.
Sanan naka hankoron mace kyakyawa, su matan da kake lalata su ba kyawawa bane? Ko
iyayen su basu kaunar su ne? Toh wallahi ka wuce hadeja gurin kaga Sidrah Wallahi ka kuskura
na samu labarin baka je ba, tabbas sai na hukuntaka, dan ba zaka zubda min mutuncina ba,
wanda nayi kai shekaru aru-aru ina tanadin su, sabida kai na da kimata." Daga haka ya mai da
hannun shi baya. Tare da barin d'akin.. wani uban ihu ya Aamil ya buga tare da dukar Kofar
dakin shi.
*Alhamdulillahi gani nan na dawo a wani Lovestory labarin yasha banban da saurar. Ku biyo
Alkalamina......
π€©
. Kuyi hakuri Daula biyu! Insha Allah sai sabon shekara zaku ji ni, Ruwa biyu
kuma Insha Allah! Ko na cigaba a watan da zamu kama ko kuma, A karshen shekara Insha
Allah! Ya danganta da lokacin da na samu ne!* *Nagode
sosai*
#Mai_Dambu
[11/13, 8:05 PM] My Zahrah: ππππ ππππ
<π²π ππππ π«πππ ππ ππππ π
πππ π²πππππ>
https://my.w.tt/U2ZCTqQj4ab
βπΈβ€πΈππΈ πβπππΌβ'π πΈπππ...
Bismillah Rahmani Raheem
0β£2β£
"Taya za a ace min na auri ugly girl. Me zanyi da mace munmuna irin Sidrah yarinyar da bata
wuce Jaririyar ba. Idan na yarda na shiga Lazza a daure." Ya kuma kaiwa kofar duka, tare da
make kanshi. Yana wani haki dan masifa, a fusace ya saka kayan shi ya fito daga dakin.
Tsakar gida ya fito, yana kallon yadda yaran gidan kowa ke shige da fice. Gyara zaman hular
kan shi yayi tare da nufar cikin gidan, duk abinda ya gani a gaba shi ball yake dashi. Ba tare da
ya damu da koma meye ba, yana isa kofar da zata shiga da shi tsakar gidan su, ya ja tunga ya
tsaya. Tare da zabgawa Hasnah wani irin kallon banza, sannan ya kauda kan shi, ya taka a
hankali isowa inda Hajiya Surayyah take soyar kosai. Ya gyara zaman facing cap din shi yadda
zai kafta rashin mutunci a silale ba tare da ya kalli fuskar kowa ba. Gyaran muryan yayi duk yan
kanen shi suka dare, tare da komawa can gefe suna zare ido. Domin sun san shi hukuma ne,
bai da mutunci ko na miskala zarratin, bayi da hakuri kamar rina haka yake, fushinsa yafi na
mayunwacin zaki, idan yana yinka duk duniya babu wanda ya isa yace baka kai ba, haka idan
ba ya yinka babu wanda ya isa yace kayi balle yayi ka, wato Aamil ruwa biyu ne..yana da
sassayar hali, kuma yana da baudaddiyar hali, yana iya zama na tsawon watanni bai yiwa kowa
magana ba, idan kuma aka kuskura yana gida yara suka cika shi da Hayaniya zai kama yaro
yayi ta bashi azaba kamar yadda suka mishi. Mutum ne mai mugun don abu me kyau. Sai gashi
ya kasance gidan su bakake ne! Musamman Familyn su.
Shi kuma ya kasance ruwa biyu, Mahaifiyar shi baturiyar Amurka, mahaifin shi
bahaushen hadeja. Aamil zai iya juya harshen sa ya dai na magana da kowa cikin harshen
Hausa, sai English ba tare da yaji ko dar ba. Sannan yana iya zuwa kofar Church ya zauna, duk
bala'in da Christian zasu mishi ba zai tashi ba sai lokacin da yaji a ranshi ya tashi zai tashi.
A duniya ya tsani mutane uku! Baba Mero wacce suke kiranta da Hajiya. Sai Yaya Hindatu,
wacce suke kiranta da Goggo hinde, sai Hajiya Surayyah wacce suke kiranta da Hajiyar mu.
Dukkan su da sunan su yake kiran su. Sai dai Hajiya Uwani wacce ta kasance matar Alhaji
Ma'aruf ta biyu, sai Amarya shi wacce suke kiranta da Hajiya Amarya.
Alhaji Ma'aruf yana da mata uku cif, Hajiya Surayyah uwargida sai Hajiya Uwani wacce
take Binta, sai Hajiya amarya wacce take karama, A gidan Sun ware Hajiya Uwani basu yi da
ita, gashi itace kusan Alhaji Ma'aruf yake ji da ita, domin itace take jibance da al'amarin Aamil
kasancewar ita tayi karatun boko da na addini, sai ya zama na tana kokarin ganin ta karkato da
hankalinsa kan karatu. Hajiya Surayyah da Hajiya Amarya wacce sunanta Karimah. Basu da
mutunci. Kuma suna tare da Yaya Hindatu da Hajiya. Yanzun haka gidan cike yake da yara
Domin wani irin haihuwa ake kirin na gasa. Idan wannan tana da ciki toh Insha Allah ko
Shayarwa kike sai taje ta kwaso ciki.
Sabida jahilci, idan ka cire Hajiya Uwani wacce take tsarin iyali. Saboda tana koyarwa
a jami'ar jihar Jigawa,kuma tana yawan tafiya course. Dan haka ta cewa Alhaji Ma'aruf.
"Yallabai! Zaka yi hakuri gaskiya, bazan takura kai na da haihuwa akai akai ba, sabida ni
ma'aikaciya ce, kuma ina yawan tafiya karo ilimi, kaga ba zan iya tara yara ina barin su a gida
babu kulawa ba, dan haka zan iya daukar lokaci zuwa lokaci kafin na haihu."
Ajiyar zuciya ya sauke sannan ya riko hannunta, ya ce mata.
"Babu laifi! Nima da ace wadancan zasu bani hadin da mun samu tazarar Haihuwa, domin
Kinga Karimah sai da aka min magana a haihuwar Yusuf, aka ce mahaifar tana bukatar kulawa
da hutu. Da kaina na kaita aka bata maganin da zata na sha na wasu watanin, amma kawai
wata biyar sai naji wai tana da ciki, wallahi abin ya dame ni, kuma ba kome ya kawo haka ba.
Sai kishi tunda taji Surayyah na da ciki shi kenan, magana ya kare."
Murmushi tayi sannan ta ce.
"Manta da batun kowa, ni bana son damuwa, kai ne a gabana!"
Yaran Hajiya Surayyah, goma ga cikin na sha daya,
Ali shine babba.
Ghali ya yake binshi.
Jamila take bin Ghali.
Sadiya, Harira, Mariya,
Dejangala, Haruna, Muttaka, sai Halima.
Hajiya Uwani kuma duk yaranta biyar ne. Muhammad Aashiq, Aseed, Abdus Samad, Jalil
da Jalal, Twins ne. Amma basu kama da juna ko daya.
Hajiya Amarya itace kuma take da yara mata huΙu. Zakiyah, Ihsan, Mufidah, sai Muwaddah.
Sai Yusuf. Da kuma ma cikin jikinta.
Yaya Hindatu, tana da yara biyar. Musa, Sai Dayyabu da Abdullahi, sai Hasnah da
Baria. Gidan Alhaji Ma'aruf, yana da matukar kokari. Domin bayan Kanwar shi akwai matasa
kusan guda bakwai a cikin gidan. Da suke karatu a karkashin kulawar shi. Faruq, Mujaheed,
Sulaiman. Ismail, Mahmoud, Saleh. Bala. Isah. Duk suna zama mishi a shagunan shi da suke
cikin kasuwar Dutse.
Duk yadda zan muku bayani akan gidan Alhaji Ma'aruf, ba zaku fahimta ba. Domin gida ne
wanda baya rabuwa da baki daga kauye. Shi yasa yake noma, yana noma shinkafa, dawa,
gero, masara da kuma wake da wanke suya. Sannan yana noman rani. Inda ake fidda mishi
kayan lambu. Har da ya'yan itace. Sannan tsarin gidan Alhaji Ma'aruf, a bayyane yake. Domin
shi baya bada kudin kome akwai duk abinda ake bukata. Kayan miya idan lokacin shi yayi.
Sawa yake a kawo mishi. A yanka wasu a shanya, wasu kuma a markade su a zuba a babban
deep freeze, maggi kuwa kullum ake kawo laida daya daga kasuwa. Mangyada da Manja, ana
kawo rabin jarka yalo ne. Sai bushashen kifi, da ake kawowa daga numan.
Duk ranar girkin mata, zata jika gero da dawa, a markade shi. Sannan a tacce shi. Washi
gari kuma da sassafe yan matan gidan da masu aiki zasu tashi da gyaran wake, kafin karfe
bakwai matar da take da girki ta fara soya. Masu aiki na tayata, babu batun masu aiki su zasu
miki kome dole ki fito. Sannan kafin ya fita zai tara yaran shi da kuma matan ya tambayi
kowacce abun da take bukata, ya ajiye musu dubu uku uku, yaran kuma dubu daya daya. Sai
ya shiga dakin mahaifiyar shi ya bata dubu biyar, kanwar shi dubu biyu. Yaranta dari biyar biyar..
A kasuwa kuwa, idan ka cire Ghali, wallahi hatta Aamil cutar mahaifin shi yake, domin suna
diban dukiyar shi, bana wasa ba. Sai dai bai da ikon ya kore su, domin yana da yakinin idan bai
mutu ba, Allah zai bashi wanda zai kare mishi dukiyar Hauwa. Dan ba nashi bane, na Hauwa
ne. Gashi Allah ya sanya albarka a cikinta. Duk yadda suka kai da su b'arnan Allah sai ya duba
niyyar dake cikin zuciyar shi ya kuma bunkasa dukiya. Ba zai tab'a mantawa ba, duwatsunta
masu daraja, ta dauka ta bashi lokacin da yake faffutikar niman aiki, bai san dasu ba. Ta cire
tace mishi.
"Ma'aruf! Gashi nan ina ga zasu saya da daraja, ka fara yin kasuwanci mu gani kafin ka sami
aikin gwamnati, dan ko mahaifina da kasuwanci ya fara aikin gwamnati." Guda goma sha biyu,
ta rike sauran sha biyun dan guda ashirin da hudu ne.
Wannan kenan..
Kerere yayiwa Hajiya Surayyah a kai, tana zuba kullu a wuta ya kalli wanda ta kwashe sunyi
kyau murmushi ya sake mata, kafin ta
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 1 Chapter of 13