zai sa Nicolas ya tsane shi ba, dan ya san idan ɗaukaka ce Nicolas ya fi shi, tun da shi ne Captain ɗinsu, a cikin club ɗin ma mutum nawa ne suka fi shi suna? Amma cikinsu babu wanda ya tsokale masa ido sai Wakili. Da farko ya alaƙanta hakan da kasancewarsa sabo a cikinsu, amma daga baya ya sauya tunani, yanzu tunani yake kamar suna samun saɓani saboda shi baƙin fata ne, kuma ɗan Africa, sannan musulmi. Rai ya haɗe sanda Nicolas ɗin ya tsugunna yana miƙa masa hannunsa alamun ya kama zai miƙar da shi. Henri ya kama kafaɗunsa ya miƙar da shi.
“Ba ka ji ciwo ba ko Wakili?”
Ya girgiza kansa yana kallon Coauch ɗinsu dake musu magana.
“Me ya faru ne?”
“Ina gwada kaifin tunanin ɗan wasanmu ne?”
Nicolas ya yi caraf ya amshe yana murmushi.
“To da kyau yara! Maza a ci gaba”
Nicolas ya sake kallon Hammad har yanzu yana wannan murmushin.
“Ba ka da kula Wakili! Yana da kyau ka ƙara kula! Hmm?”
Ya ƙare da tambaya yana miƙa hannunsa zai taɓa kafaɗarsa Hammad ya kauce. Nicolas ya dunƙule hannunsa da ya miƙa yana wani murmushin, sannan ya barsu nan tsaye shi da BB.
“Ba ka ji rauni ba ko Wakili?”
BB ya sake tambaya yana duba hannunsa da ya rike.
“Ban ji rauni ba”
“Sannu”
ZAHRA POV.
Adai-daita sahun da suka hau tun daga Yalwawa ya taka birki a kofar wani gida mai kyau dake cikin unguwar Mobile Base. Ita da kawarta Saddiqa dake cikin napep ɗin suka fito a tare, Saddiqa ce ta sallame shi, sai da mai napep ɗin ya tafi sannan suka fuskanci gidan da aka sauƙesu a gabansa.
“Kamar nan ne gidan ko?”
Saddiqa ta tambayeta tana leƙe-leƙe a ƙofar gidan, wai ko za ta ji hayaniya a ciki.
“Wannan gidan bai yi kama da gidan da ake taron suna ba Saddiqa”
“Haka ne, to ya za mu yi ke nan?”
“Bari na ƙira Zainab ɗin, sai mu ji”
A cikin jakar hannunta ta fito da wayarta ƙirar Tecno Smart5, lambar ƙawarsu Zainab da ta gayyacesu zuwa taron sunan yayarta da ake a yau ta lalubo, sannan ta aika mata kira.
“Har kun zo ne?”
Da ƙyar Zahra ta tsinkayi muryar Zainab ɗin a cikin tarin hayaniyar bikin suna, kuma jin hakan ya ƙara tabbatar mata da cewa gidan da suke tsaye a gabansa yanzu ba shi ne gidan yayar Zainab ɗin ba.
“Eh mun iso unguwar, napep ya sauƙemu a ƙofar wani gida mai farin fenti”
Ta bata amsa da ɗan karfi, dan ita kanta tana jin hayaniyar sosai, ballantana kuma ita Zainab ɗin dake cikin hayaniyar.
“Na gane gidan, ku tsaya a nan bari na sa a muku iso”
“Wa za ki turo?”
“Ku dai ku jira mana, waye zai saceku da girmanku?”
Zahra ta yi murmushi.
“To muna jira”
“Me tace?”
Saddiqa ta yi saurin tambaya sanda ta sauke wayar daga kunnenta.
“Ta ce mu tsaya a nan za ta turo wani ya mana iso zuwa gidan”
“Wallahi da ma kin ce ba ki yarda ba, sarai kin san halin Zee da shiririta, yanzu haka sai ta mance da lamarinmu”
Zahra ta kuma yin murmushi tana girgiza kai, sannan ta samu wani dakali ta zauna.
“In ban yarda ba me kike so na ce mata?... tana cikin hidimar suna dole a mata uziri”
Ita dai Saddiqa abin bai mata ba, dan haka ba ta sake cewa komai ba ta zauna kusa da Zahran, suka shiga hirar form ɗin naiman gurin karatu a poly Dutse da Zahra ta cike. Sai da suka kwashe kusan minti goma suna zaune a wurin, tun Saddiqa na haƙuri har ta fara ƙorafi, tsaki ko ta yi ya fi cikin kwando.
“Dan Allah Zahra sake ƙiranta, wallahi yanzu haka ta manta da lamarinmu”
Cewar Saddiqa da ta ɓata rai.
“To miye abin ɓacin rai? Cool off bari na sake ƙiranta”
Ta ɗauki wayarta da zummar sake aikawa Zee ɗin ƙira dai-dai da fakawar wata mota a inda suke. Sai da suka ƙarewa motar kallo kafin Saddiqa ta kalli Zahra.
“Ko dai su suka zo ɗaukan namu?”
Kafin Zahra ta bata amsar tambayar da ba ta sani ba, aka sauƙe glass ɗin gaba na motar da ya kasance baƙi, wasu samari biyu suka bayyana a cikin motar, ɗaya a mazaunin direba ɗaya kuma a na me zaman banza. Wanda ke mazaunin me zaman banzan tun da suka sauƙe glass ɗin yake jifansu da murmushi…
“Wacece Zahra a cikinku?”
SA’AD POV.
Kasancewar ya ga babu wani sarki sai Allah yasa ya fara shirye-shiryen komawarsa zuwa Abuja. Ranar talata ya yanke shawarar kaiwa abokinsa Mubarak ziyara, abokinsa ne tun na tasowa kuma har kwanan gobe suna nan tare. Tun da ya zo garin sau ɗaya suka haɗu, ga shi nan da kwana biyu yake son komawa Abuja. Motar Aysher ya ara, duk da sharuɗan da aka dinga kafa masa a kan motar bai fasa ɗaukan motar ba, ba wata tafiya mai tsayi ya yi ba sai ga shi a unguwar su Mubarak ɗin.
Yana isa gidansu ya aje motar da ya zo da ita a harabar gidan, sannan ya fito ya nufi part ɗin Mubarak kansa tsaye, tun da gidan ba baƙonsa ba ne. A ɗaki ya samu Mubarak ɗin zaune yana amsa wayar da kana ji za ka san cewa waya ce da ta shafi wurin aikinsa. Ba tare da yace masa komai ba ya nufi gadonsa ya zauna yana cire safar ƙafarsa, zuwansa ya sa Mubarak gajarce wayar da yake domin ya fuskanci abokinsa.
“Ai na ɗauka har ka tafi ba za mu sake haɗuwa ba”
Mubarak ɗin ya fara da wannan bayan ya sauƙa a layi, ba tare da Sa’ad ya kalle shi ba ya miƙa hannu ya buɗe side drawer ya fara laluben shisha.
“Kai ma ka san babu yadda za ai na tafi ba tare da na zo na maka sallama ba”
“Sallama? Ba ka na da sauran sati ɗaya ba?”
“Mts manta kawai, Takawa ne ya rage mini kwanakin hutun”
Mubarak ya yi ‘yar gajerar dariya.
“Dai-dai ke nan, ai Wallahi Sa'ad da ace kai da Hammad ragon uba kuka samu sai abin da hali ya yi, dan duk watsewa za ku yi, to da Allah ya so ku da rahama sai ya haɗaku da jajirtaccen uba, wanda zai yi maganin iskancinku ba tare da rai ya ɓaci ba!”
Sa’ad bai tanka masa ba ya ci gaba da lalube.
“Wai binciken me kake mini ne? ko ka bani ajiya?”
“Shisha nake nema”
“Ina taka?”
“Tawa ba caji ka gaya mini inda take please”
“Babu”
Wani irin kallo Sa’ad ya masa na ka raina mini wayo.
“Babu?”
“To tun da ba ka yarda ba ka ci gaba da dubawa in za ka samu”
A mamakance Sa’ad ya dawo kusa da shi ya zauna yana ƙare masa kallo.
“Me yasa ka daina sha?”
“Budurwata ce ta nuna cewa ba ta so, shi yasa na wastar da ita”
Wata irin dariya ta shaƙiyyanci Sa’ad ya saki.
“Miye abin dariya a ciki? Kai ma wata rana za ka daina”
“Na daina? In your dreams Man!”
Mubarak ya taɓe bakinsa alamun kai ka sani, Shi dai Sa’ad ya kasa yarda da abin da Mubarak ɗin yace masa, dan ya san halin Mubarak sarai idan ya saba da abu duk nacin mutum bai isa ya raba shi da shi ba, to ya za ayi ace wata budurwa ta sauya shi, ai abin ya wuce tunani.
“Taron me ake a cikin gidan ne?”
Ya tambaya ganin warmers da container na abinci a ɗakin.
“Hauwa (yayarsa) ce ta haihu, kuma yau suna”
Sa’ad ya jinjina kai yana buɗe wata container da ya ɗauka, wanda ke ɗauke da cake ya ɗauka me isarsa ya dawo ya zauna ya fara ci.
“So ya aikin naka yake tafiya?”
Mubarak dake latsa wayarsa ya cilla masa tambayar.
“Ba daɗi Mubarak… Wallahi kwata-kwata aikin jarida ba nawa ba ne, ba ƙaddarata ba ce, amma ƙarfi da yaji Takawa ya cuso mini shi cikin tsarikana, kuma babu yanda na iya dole na karɓa… Duk wayewar garin duniya idan ina workout a unguwar da ya kama mini haya sai na wuce ta Kofar Wakili Motors, kullum ganin wurin ƙara saka mini son aiki a wurin yake, kullum zan wuce sai na yi addu’a Allah ya cika mini burina na zama Manager'n kamfanin nan, har na fara tunanin da gan-gan aka kama mini gida a unguwar nan, dan kawai na riƙa kallonsa yana mini ƙwalele”
Mubarak ya yi dariya.
“Sa’ad! Takawa ya yi iya abin da zai iya a kanka, ya baka dama mai kyau wadda idan ka damata za ka mallaki abin da kake buri, kai ne ka sa wasa da shiririta a lamuranka!”
“To wai ni dan Allah me yasa ba za a bani aikin nan ba? Tun da akwai damar hakan, kawai so ake sai na wahala”
Mubarak ya girgiza kansa.
“Manufar Takawa a kanka ba ta shan wahala ba ce, so yake ka san zafin naiman kuɗi da kanka, ka san wahalar dake tattare da samun halal kafin ya baka ragamar wahalarsa ta tsawon shekaru, Wallahi da ace ni ne a matsayinsa zan yi same thing, domin babu yanda za ai na ɗauki ragamar kamfani guda na bawa wanda bai san zafin naiman kuɗi ba”
Sa’ad ya yi shiru, dan ba shi da ta cewa kuma. Wayarsa da ta soma ruri ya kai hannu ya ɗauka, ganin sunan ɗaya daga cikin ‘yan matansa yasa ya aje cake ɗin dake hannunsa ya ɗaga wayar tare da karawa a kunnensa.
“Hello Baby”
Mubarak ya kalle shi, shi kam yana mamakin adadin Babies ɗin da Sa’ad yake da su, ‘yan matan Sa’ad sun fi a ƙirga, ga shi da farin jini kamar aljanna, da wuya yace yana son budurwa ta ƙi amince masa, wata ƙila dan yana da kyau ne, wata ƙila kuma dan yanda yake kashewa ‘yan mata kuɗi ne, amma shi dai Mubarak zai iya rantsewa kan duk cikin tarin ‘yan matan nan babu wadda Sa’ad ke wa son gaskiya.
“Ok nawa ne?”
Ya tambaya kana ya yi shiru yana sauraron bayanin da ake daga ɗayan bangaren.
“Dubu casa’in da biyar ai ba yawa, ki turo mini account details naki, insha Allah yanzu zan saka miki su”
Ya sake yin shiru yana murmushi, kafin ya ce Bye tare da sauƙe wayar, yana ɗagowa suka haɗa ido da Mubarak.
“Ita dubu casa’in da biyar ɗin ta miye?”
“Anko”
Ya ba shi amsa kai tsaye yana latsa wayarsa.
“Naira dubu ɗari ba dubu biyar za ka bawa budurwa saboda anko kawai?”
Ya jinjina masa kai hankali kwance.
“Dubu ɗari ma zan tura mata, wata kila daga wannan ita ma ta ci rabonta”
Jin hakan yasa Mubarak ya yi murmushi yana ɗaukan cup ɗin da ya zuba kunu a ciki.
“Rabuwa za ayi da ita ke nan?”
“Sai ka tambaya ma? Yarinyar ta fiya roƙo, ni kuma ba na son hakan”
Mubarak ya sake sakin wani murmushin.
“Dan Allah Sa’ad yaushe za ka yi wa kanka karatun ta nutsu ka daina wannan albozarancin da kuɗi, ka daina kula ‘yan mata barkatai”
Sai ya aje wayarsa bayan ya yi transfer na kuɗaɗen da ya ambata.
“Wallahi komai lokaci ne Mubarak, ni kaina na san tara waɗannan ‘yan matan ba rayuwata bace, kawai dai har yanzu ban samu wadda zuciyata ta kwanta a kanta ba ne, amma ka san an ce mai naima ba zai rasa ba, wata ƙila mu dace a nan gaba”
Ƙofar ɗakin da aka ƙwanƙwasa ne ya katse hirar tasu, Mubarak ya tashi ya buɗe kofar.
“Mummy?”
Ya faɗa ganin mahaifiyarsu tsaye a bakin kofar.
“Na’am, kai da waye a ciki ne?”
Ƙofar ya wangale mata ta ga Sa’ad dake zaune yana cin cake, shi ma kuma ganinta yasa ya miƙe yana gaisheta.
“lafiya ƙalau Sa’ad, ya wurin Ammin taka?”
“Tana nan lafiya”
“To in ka koma ka ce ina gaisheta”
“Insha Allah za ta ji”
Mummyn Mubarak ta kalli ɗanta.
“An rasa wanda zai kai kajin can, idan babu inda za ka fita ka zo ka kai musu”
“Ah ba inda zan je, bari na kai musu kawai”
“To suna kitchen, bari na saka Taladi ta kawo maka su”
“To Mummy”
Sai da ta juya sannan shi ma ya dawo ɗakin, ya shiga naiman key'n motarsa.
“Ina kuma za ka je?”
“Gidan Hauwa, wai kaji ne ba a kai musu ba”
Mubarak ya amsa masa sanda ya samo key'n.
“To mu je tare”
“OK”…
----------------------
_Me kuke ganin zai faru a wannan tafiyar?_
#SalmaAhmadIsah
#MiniCandy
#Bahadejia
#KawaZuci
~~~~~~~~~~~~~~~~~~
*KAWA ZUCI*
*©SALMA AHMAD ISAH*
*11*
…Tare suka fita, sai da suka jira Ta Ladi mai aikin gidan, ta kawo musu manyan warmers ɗin da kajin ke ciki, sannan suka tafi, ko da suka je gidan sunan suka bada saƙon sai Zainab ƙanwar Mubarak ta same shi da maganar dan Allah ya taimaka ya ɗauko ƙawayenta da suka zo gidan sunan tun da ita abubuwa sun mata yawa.
“Na miki kama da yaronki da za ki aikeni?”
“Ba haka nake nufi ba Ya Mubarak, dan Allah ka taimaka… Ya Sa’ad ka sa baki”
Sa’ad dake gefe yace.
“Ba damuwa za mu daukosu”
“Ta yaya za mu gane su”
“A cikinsu akwai me suna Zahra, suna nan a ƙofar gidan Alhaji Bawa”
Shi dai Mubarak zai je ne dan ta haɗa shi da Allah, amma da ba zai je ba. Haka suka sake shiga mota, inda suka nufi gidan da ta faɗa ɗin, Mubarak ne ke tuƙa motar yayin da Sa’ad ke zaune a mazaunin me zaman banza, kamar yanda tace suna kofar gidan Alhaji Bawa a nan ɗin suka gansu zaune, tun kafin su sauƙe glass Sa’ad ya ƙure wadda ke sanye da Hijabin kallo, hannunta riƙe da waya, kamar me shirin kiran wani, bai ƙara tantance kammanin fuskarta ba sai da ya zuge glass ɗin, sannan ya yi arba da ita, sai motsa bakinta take, kuma hakan da take yake ƙara bawa Dimple ɗinta damar fitowa ta ko wani gefe.
“Wacece Zahra a cikinku?”
.
Tun da suka shiga motar babu wanda ya yi ko tari, sun zauna a gidan baya kamar da aka ajesu, shi kuma Sa’ad ya maida hankali wurin kallon Zahra ta cikin madubin dake sama, da ya ga ba ya samun damar kallonta da kyau sai ya kai hannunsa zai gyara madubin, Mubarak dake ankare da shi ya buge masa hannu yana wurga masa hararar takaici, sannan ya maida madubin yadda yake, Sa’ad ya yi murmushi mai sauti yana furta.
“To ai shikenan”
Su dai su Zahra a zaune suka kamar waɗan da aka takure, dan gaba ɗaya abin sai yay musu wani iri, wai yau su ne a motar wasu samari da ba su sani ba, har gara ma direban dake tuƙi, za su iya cewa sun gane shi domin sun san fuskar a wurin Zee, amma shi dai ɗayan ba su san shi ba. har suka iso gidan babu wanda ya yi magana a cikinsu, fita daga motar ma sai da aka musu lamini.
“Behave your Self Sa’ad Wallahi ba za ka janyo mini raini ba”
Cewar Mubarak da ya lura da take-taken Sa’ad ɗin, murmushi ya saki yana faɗin.
“Miye abin raini a ciki? Ai ba cewa na yi ina sonta ba, kawai ta burgeni ne”
Mubarak ya sake galla masa wata uwar harara.
“Haaa! Me da waƙar ni ba baƙon zafi ba ne”
Ya ƙarashe yana waigawa gidan baya na motar, kuma a nan ya hangi wayar da ya gani ɗazu a hannun yarinyar, aiko da sauri ya miƙa hannunsa ya ɗauka, sannan ya juyo ya kallonsu daf da za su shige gidan, yana so ya ƙirata amma bai riƙe sunanta ba, sai ya samu kansa da faɗin.
“Dimple!”
Aiko cak ta tsaya, ba ita kaɗai ba, hatta Saddiqa da ba sunanta aka ƙira ba sai da ta tsaya, a tare suka juya suna kallon motar dan daga jin kiran daga can ya fito, Sa’ad ya ɗaga musu hannu alamun su tsaya. Yana shirin buɗe motar ya fita Mubarak ya riƙo shi.
“Me za kai?”
“Kai dalla wayarta ta manta”
Ya nuna masa wayar, sai da ya sake banka masa wata hararar sannan ya sake shi, ya buɗe motar ya fita ya nufi inda suke tsaye wayar riƙe a hannunsa.
“Kin manta wayarki”
Zahra ta kalli wayar dake hannunsa, ta zare ido kamar mara gaskiya.
“Oh Allah, na manta ne”
Ta karɓi wayar a hannunsa tana furta.
“Na gode”
Shirin juyawa ta yi ya tsayar da ita ta hanyar faɗin.
“Zan iya samun lambarki?”
Ta kalle shi, wani irin kallo dake nuna masa abin da ya tambaya a wurinta yanzu baƙo ne.
“Ya kike min irin wannan kalon kamar wannan ne karo na farko da wani saurayi ya tambayi lambarki?”
Bai yi ƙarya ba, idan za ta iya tunawa tabbas wannan ne karo na farko da wani saurayi ya taɓa tambayar lamarta, domin ita ko saurayin ma ba ta da shi. A hankali ta girgiza kanta, kafin ta karanto masa lambar bakinta na rawa, ya kwafe sannan ya ɗaga mata hannu ya juya ya nufi motar Mubarak yana hasashen yanda za su kwashe da shi, musamman da ya lura da yanda yake aiko masa da harara tun daga cikin motar.
“Miye kake mini irin wannan kalon kamar na kashe mutum?”
Takaici ya hana Mubarak magana.
“Hey kar ka damu, lamba kawai na karɓa, ni ban ce ina sonta ba, na gaya maka kawai ta burgeni ne”
“Ni dai na gaya maka ba za ka jawo mini raini ba, ba za ka yaudari ƙawar ƙanwata ba ka zubar mini da mutunci a idonsu!”
Haushi bai sake rufeshi ba sai da Sa’ad ya masa banza ya shiga motar ya fara rera waja da bakinsa, shi ma bai sake cewa komai ba ya ja motar suka yi gaba.
*No.23, Rua Visconde de Piraja, Mooca, Sao Paulo, Brazil.*
PEDRO POV.
Da misalin ƙarfe shida dai-dai, alarm ɗin da Juliana ta saita ya karaɗe ɗakinta da ƙara, da ƙyar ta iya buɗe idonta ta miƙa hannunta ta kashe agogon dake side drawer, tana hamma ta tashi zaune a kan gadon, a ƙalla sai da ta shafe mintuna biyu zaune a kan gadon ba ta gama wartsakewa daga baccin ba. haushin Caio ne yasa ta ƙarasa wartsakewa, hannu ta miƙa ta shafa kan karen dake tsaye a gefen gadonta, sannan ta gyara zamanta ta dunƙulewa hannayenta biyu, tare da lumshe idanuwanta domin karanto morning prayers ɗin da ta saba yi a kullum.
“Querido Deus, Obrigado por hoje. Ajuda-me a manter o foco em Ti e enche-me com Tua paz, amor e força. Guia-me ao longo do dia e usa-me para Tua glória. Em nome de Jesus, Amém…”
(Dear God, Thank You for today. Help me to stay focused on You, and fill me with Your peace, love, and strength. Guide me through the day, and use me for Your glory. In Jesus' name, Amen.)
Ta karanto addu’ar a bayyane, kuma cikin harshen portugues. Tana gama karantowa ta yi sign of cross ta hanyar taɓa tsakiyar goshinta, ta taɓa kafaɗarta ta hagu, sannan ta ta taɓa ta dama. Taɓa goshi na nufin ‘Invoking the name of the father’, taɓa kafaɗar hagu na nufin ‘The Son’ ta dama kuma na nufin ‘And the Holy spirit’. Idonta ta buɗe yayin da take sauƙa daga kan gadon, crocs ɗinta ta saka ta fita daga dakin Caio na biye da ita. Kai tsaye ɗakin Pedro ta shiga, dan ko tantama ba ta yi kan bai farka ba.
Iai kuwa, tana buɗe ƙofar ɗakin ta gan shi kwance a kan ɗan ƙaramin gadonsa na kwanciyar mutum ɗaya, yanayin kwanciyar tasa kawai idan ka kalla za ka san cewa baccin sace shi ya yi ba tare da izininsa ba. Domin a karkace yake a kan gadon, kafarsa ɗaya ta sauƙo ƙasa, yayin da system ɗinsa ke aje a gefensa, kuma a kunne take.
Idan aka ɗauke gadon kwanciyarsa dake ɗakin babu komai sai kayan motsa jiki da suka ƙunshi threadmill, barbell, dumbbells sai kuma punching bag dake rataye a sama, ko wardrobe babu, hatta kayan sakawarsa a cikin chest drawer suke. Sai desk da kujera, inda yake aje Laptop da desktop ɗinsa, daga gefen ƙatuwar desktop ɗin dake kan desk kuma rubik’s cube ne zube…
“Hard Rock!”
Juliana ta ƙira tana dukan bayansa, da ƙyar ya motsa yana jan guntun tsaki cikin muryar bacci yace.
“Juliana ki ƙyaleni na yi bacci”
Juliana ta sake dukansa.
“Ka tashi ka yi sallah, ga shi nan har rana ta fito ba ka yi sallah ba, haka ka ga Ibrahim yana yi?”
Bai amsa ba ballanata ya tashi, dan baccin da yake ji ne ya fi ƙarfinsa, jiya bai kwanta ba sai ƙarfe uku na dare, shi ma kuma baccin ne ya sace shi.
“Idan ba ka tashi ba sai na watsa maka ruwa”
Ba shiri ya tashi zaune yana yamutsa sumar kansa da hannayensa da ya saka a cikin sumar tasa.
“Wai ƙarfe nawa ne?”
Ya miƙe yana tambayarta.
“Shida da mintuna”
Idanuwansa dake shaida gajiya tare da baccin dake tattare da shi ya lumshe sannan ya buɗe, da ƙyar ya nufi birthroom yana jin Juliana na masifar yanda ya birkita ɗakin.
“Kai ke nan kullum cikin ɓatawa ka bar ni da aikin gyarawa! Fireball kawai!”
Shi dai bai kulata ba ya shige ya rufe ƙofar, duk kayan dake zube a ƙasa ta bi ta tattare, wanda ta san a wanke suke ta saka masa su a cikin chest drawer'n da yake saka kayansa, na wanki kuma ta fita da su, na zubarwa ta zubar. Ko da ta gama gyara ɗakin nasa falo ta fita ta gyara, sannan ta koma ɗakinta ta shiga bathroom domin yin brush. Tana tsaye jikin sink ta ɗauki toothbrush ta shafa toothpeste a kai, sannan ta saka a bakinta ta fara goge haƙwaranta a hankali, dai-dai da sanda ta ji zubowar wani abu mai ɗumi daga hancinta wanda ta shaida cewa jini ne. Ai ko tana kallon MADUBI ya tabbatar mata da hakan, ta duka ƙofofin hancin nata biyu yake zuba. Da sauri ta aje brush ɗin ta kuna famfo ta tari ruwa ta shiga ƙoƙarin wanke hancinta, duk yadda ta so jinin ya tsaya abin ya ci tura. Dan haka ta yagi audiga ta toshe hancin nata da ita tana jin jiri.
“Juliana!”
Da ƙyar ta iya amsawa, jin Pedro na ƙiranta, a daddafe ta fito daga bayin tana jan ƙafarta da ƙyar, tun da ta buɗe ƙofar ɗakin nata ta gansu tsaye a falo shi da Ibrahim da ya fito cikin shirinsa na tafiya wurin aiki, sautin takunta yasa suka kalleta a tare Pedro na faɗin.
“Kin gama abinci ne?”
Kanta ta girgiza sanda ta ƙarasa sauƙa tana sake noƙe shi ƙasa, dan ba ta so ma su ga audigar dake hancinta.
“Ba damuwa bari kawai na ɗauki bread na tafi dan sauri nake ba zan iya jiran ta girka ba”
Cewar Ibrahim da ya nufi kitchen domin ɗaukan bread ɗin tun da ba zai samu abincin safe ba. duk kwanan duniya a gidan yake cin abincin safe, rana da dare.
“Julia? Lafiya kuwa?”
Ya tambayeta lura da yanayin da ta sauƙo a ciki, tun da ta amsa musu da a’a din nan ba ta sake cewa komai ba, ba cin shi kuma ya san halinta kamar yunwar cikinsa, sam ba ta ɗaya daga cikin mutanen da suke shiru-shiru.
“Lafiya mana”
Ta amsa masa tana juyawa, ya yi saurin riƙo tsintsiyar hannunta dake ɗauke da zanen tattoo na ‘Blassed One’ ya juyo da ita, kuma hakan ya ba shi damar ganin hancinta da ta toshe.
“Baki da lafiya ne? Ko ciwon naki ne ya tashi?”
“A’a lafiyata kalau”
“Julia?”
Ta kalle shi irin kallon nan na rashin gaskiya.
“Faɗa mini gaskiya”
Hannunta ta shiga sosawa tana kame-kame.
“Da ina… wanke bakina ne, hancina ya fara bleeding”
“Je ki shirya mu tafi asibiti”
Kawai yace ya nufi ɗakinsa.
“Ni ba na son zuwa asibiti”
Juyowa ya yi ya kalleta hannayensa rungume a ƙirjinsa, ta sunkuyar da kanta ƙasa.
“Saboda zuwa asibitin nan yau sati biyu ban je Church ba, ina so na je na yi addu’a, in ya so ka bari zuwa gobe sai mu je?”
“Me yake faruwa ne”
Ibrahim da ya fito daga kitchen ya tambaya yana kallonsu, ganin yanda suka yi tsaye a falon.
“Dan Allah Hard Rock”
Ta sake masa magiya.
“Je ki shirya, ni kuma zan yi breakfast”
Nan da nan ta buɗe bakinta cikin kyakkyawan murmushinta mai kama da dariya.
“Yanzu kuwa”
Da gudu ta yi sama duk da jikinta ba ƙwari.
“Me ya faru?”
Ibrahim ya sake masa tambayar da ba su amsa masa ba.
“Ciwon Julia ya fara wuce gona da iri, akwai buƙatar na ɗauki matakin gaggawa”
“Ni dai ba zan taɓa gaji da baka shawarar nan ba, ka yi taka tsan-tsan”
“Kar ka damu da ni Bro… na san yanda zan yi”
Ya ƙarashe maganar da guntun murmushi, sannan ya nufi kitchen yana masa sai an jima, shi dai bai tafi ba sai da ya gama cinye bread ɗin da ya ɗauko, sannan ya fita.
. . .
Zaune yake a kan wan dogon bench dake kan hanya, ya ɗaga kansa sama idonsa a rufe yana sauraron wakar ‘Parado no Bailao’ yayin da Caio ke ɗaure a gefen bench ɗin da yake zaune a kai. A hankali yake gyaɗa kansa ba wai dan yana jin daɗin waƙar
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 9 Chapter of 14