kallonta.
“Idan ni ban miki magana ba ke ba za ki iya mini ba?”
Ita ce tambayar da ya cilla mata, ai ko da sauri ta juya zuciyarta na tsalle a ƙirjinta, Allah ya sani ko muryar Njau ta ji sai zuciyarta ta buga, ballanata ace ita yakewa magana ko yana kallonta.
“Akira”
Ya kira sunan nata yana matsawa kusa da ita, amma ba ta juyo ba, sai zanin hannunta da ta rungume tana jin kamar ta yi fiffike ta tashi.
“Akira”
Ya sake kiran sunanta a karo na biyu, ta kasa amsawa ballantana ta juyo.
“To tun da ba za ki amsa ba koma gida”
Ai ko kamar da take jiran cewarsa ta shige gidan da sauri tana dariya mara sauti, har ta shige yana tsaye yana kallonta, murmushi kwance kan fuskarsa.
“Njau ka taho mana!”
Nikamba da ya gaji da jiransa ya fada a ƙufule.
“Gani nan zuwa”
*Unguwar Yalwawa, Dutse, Jigawa State.*
ZAHRA POV.
“Dan Allah Ruwaida in kin kai musu rubutun nan kar ki zauna, ki dawo da wuri kin ji”
Cewarta sanda ta miƙawa Ruwaida ruwan rubutun da ta cika jarka 5 liter da shi, Ruwaida ta karɓi jarkar Mama na faɗin.
“Ai da baki ɓata bakinki wurin mata wannan maganar ba, dan kamar da ƙasa in ji makaho, in dai Ruwaida ce to sai ta tsaya wasa a hanya…”
“Ai ko Mama ba zan zauna wasa ba, da wuri zan je na dawo”
Mama dake rumfa tana tsintar shinkafa ta taɓe baki tana watsar da ɓuntun da ta tsinto a cikin shinkafar.
“Allah ya sa”
“Amin”
Zahra dake zuba ruwa a buta ta amsa tana dariya. Fitar Ruwaida ba jimawa wani yaro ya shigo da sallama yana faɗin a ba shi attaruhu na ɗari.
“Attaruhu ya ƙare Muhsin, amma insha Allah zuwa gobe za a saro mini”
Mama da ta rage a tsakar gidan ta amsa masa, dan zuwa lokacin Zahra na bayi. Yaron da Mama ta ƙira da Muhsin ya amsa da to yana juyawa.
“Mama ina cazar wayarki?”
Saama dake cikin ɗakin Mama yana kiciniyar saka wayarsa a caji ya tambaya, kamar mai kallonsa Mama ta kalli ƙofar dakinta da yake ciki ta amsa da.
“Ka duba nan kan gado, dazu a nan na ce Ruwaida ta aje mini ita”
“To”
Ya duba kan gadon kamar yanda tace, kuma a nan din ya samu cazar, ya ɗauka yana shirin saka karamar wayarsa a caji aka dauke wuta, wani dogon tsaki ya ja ransa na ɓaci.
“To Gaiwa sarkin iya tsaki, me kuma aka yi?”
Rai a ɓace ya fito daga dakin yana kokuwa da labulen dakin kamar da aka ce shi ya sa aka dauke musu wuta.
“Wutar suka ɗauke”
Mama ta yi murmushi me kama da dariya tana girgiza kai.
“Mts Allah dai ya kyauta, ‘yan Nepa suna abin da ransu yake so a kasar nan”
Shi dai Saama da haushi ya ishe shi hanyar zaure ya kama lokacin da wayarsa ta soma ƙara, wannan ƙiran wayar, dai-dai yake da kiran kaddararsa da kuma silar kaddarar ‘yar uwarsa, dan kaddarar ta soma lokacin da babban ɗan yatsan hannunsa na dama ya latsa maddani mai dauke da koren zane a cikin maddanan wayarsa. Da ace ya san abin da zai biyo bayan hakan, da sai ya zaɓi latsa maddani mai dauke da jan zane sama da koren, sai dai shi kansa bai san gaibu ba, bai san komai ba, bai ga komai daga cikin hukuncin Allah ba sai wanda Allah ya hore masa gani.
“Assalamu alaikum Saama”
Aka yi sallama daga ɗayan ɓangaren dai-dai da wanzuwar kaddarar a doron duniya, wata kaddara da babu wanda ya san ranar tsinkewar zarenta, wata kaddara da za ta bawa kowa mamaki, ciki har da wanda aka zana kaddarar a kansa.
“Eh ina gida”
Saama ya amsa tambayar da abokin nasa ya masa.
“To dan Allah ka zo ƙofar shagon Sadi, ina jiranka”
Muryar abokinsa Sayyid ta fito ta cikin wayar.
“Lafiya?”
Saama ya tambaya jin alamun damuwa kwance cikin muryarsa.
“Kai dai ka zo kawai”
“To gani nan zuwa”
Kiran ya katse a lokacin, ya sauke wayar sanda Mama ke tambayarsa.
“Fita za kai?”
“Eh Sayyid ne yake naimana”
“To me zai hana idan ka fita ka biya kasuwa ka siyo mini kayan miyar nan, babu daɗi sai zuwa naima ake ina cewa babu”
Idonsa a kan wayarsa yake cewa.
“To Mama kawo”
Kuskure na farko ke nan. Mama ta tashi ta shiga ɗakinta, jim kadan ta fito riƙe da kuɗin da a ƙalla zai kai dubu shida, ta nufe shi tana masa lissafin abubuwan da zai siyo mata. Suna cikin haka aka rangaɗa sallama daga soro, suka amsa sanda wanda ya yi sallamar ya bayyana a tsakar gidan.
“Mutan gidan suna nan?”
Matar da ta shigo ta tambaya tana riƙe da bahon kayan kolin dake kanta. Daga ganinta za ta haura shekaru arba’in, sai dai a wanke take fes, domin irin matan nan ce da suka goge da duniya, ta sha wata atamfarta da aka mata ɗinkin riga da zani, ta yafa mayafi a kafaɗarta, fuskarta har da kwalliya.
“Sannu da zuwa Yaatan Dalla”
Cewar Mama baki har kunne.
“Yauwwa Abu sannunmu”
Yaata ta amsa tana ƙarasawa ciki sanda Saama ke gaisheta.
“Lafiya ƙalau Saama Ɗan Samari”
Ta faɗi da murmushinta irin na wayayyun dattijai.
“Mama ni zan wuce”
“To a dawo lafiya”
“Allah yasa”
Ya amsa yana ɗaga wani ƙiran da yake shigo masa daga Sayyid.
“Zauna a nan Yata”
Mama ta shimfiɗa ma Yaata tabarma, Yaata ta zauna, sannan Mama ta kawo mata ruwa ta zauna kusa da ita suka sake gaisawa. A lokacin Zahra ta fito, ta gaida Yata da fara’a, Yata ta amsa mata kamar kowa har da su zolaya, tana shirin shiga ɗaki Mama ta dakatar da ita da faɗin ta zo ta ƙarasa wannan tsintar shinkafar da ta fara, ta ce to sannan ta ɗauki trayn shinkafar ta koma can gefe ta ci gaba.
“Yata kwana biyu kin ƙi mu”
Yata ta yi murmushi.
“Ko ɗaya Abu ban ƙiku ba, kawai dai kwana biyun ne ba na iyowa layin naku”
“Ƙwarai…”
“Yanzu haka daga Fada nake, na je wurin Jakadiya tawa, a nan nake jiyowa wani labari da na daɗe ban ji irinsa ba!”
Yata ta ƙarasa maganar cikin sallalami, alamun lallai labarin dake bakinta mai nauyi ne, Mama ta yi murmushi tana girgiza kai, dan ta san halin Yata Sarai, na iya dakon gulma, duk wani labarin duniya a bakin Yatan Dalla za ta ji shi.
“Wato Abu ana shuka tsiya kala-kala a duniyar nan, ina ‘yar gidan Sarki da aka yi aurenta kwanaki?”
Mama ta jinjina kai, dan kuwa ta tuna sanda aka yi bikin, dan gagarumin biki ne da zai yi wahalar mantawa, domin shi ne biki na biyu da aka yi a fadar garin, bayan bikin Galadima da ya kasance na farko.
“Ita ce wadda ke auren wani sojan ruwa ko?”
“Ƙwarai ita ce”
“To me ya sameta haka?”
“Humph! Abu ba a cewa komai, tun bayan auren yarinyar nan ba ta samu zaman lafiya a gidan nan ba, yau fari gobe tsimma, tun abin na damunta tana iya ɗauka har ta zo ya ci ƙarfinta, yanzu haka yarinyar nan hauka take tibiran, haukan nata ya yi ƙamarin da har mutane take kamawa tana jibga!”
“Wayyoni Allah, wanna abu bai yi daɗi ba!”
Cewar Mama cikin tausayawa, Yata ta jinjina kai tana kama haɓa.
“Dan ba ki ji ba ne, yanda Jakadiya ke bani labarin halin da yarinyar ke ciki abin tausayi, kuma ita tace ma abin nata ganinsa take kamar aikin jinnu ko asiri!”
Sai da Yata ta kawo wannan gabar sannan Zahra ta daga kai ta kalleta, a duk duniya tana jin tausayin mai iska, domin ita ta taɓa ta ji, kasancewar mahaifinta Malami bai sa aljannu sun ƙyaleta ba. Kuma da suka kamata ba su, mata kamun wasa ba, ta sha wahala kamar za ta mutu, da ƙyar da fama Allah ya rabata da su. Wannan dalilin yasa har gobe take tausayin mai iska.
“… Komai zai iya faruwa, kuma kin ga su ‘yan boko ne, ba lallai su yarda da magungunanmu na gargajiya da kuma na addini ba, sai su yi ta jigilar zuwa asibiti”
“Ai kamar da kika sani, sun gwada na asibitin sun gwada amma shiru, ƙarshe ma sai cewa aka yi wai ta haukace!”
“Subahannalahi!... Allah ya bata lafiya da sauran musulmi”
Zahra ta amsa da Amin a zuciyarta, tana jin ina ma ace tana da damar ganin wannan matar, domin haka kawai lamarinta ya yi zaman daɓaro a zuciyarta.
.*.*.*.*.*.*.*.*.
Saamari na fita daga gidan ya nufi shagon Sadi dake can bakin hanya, yana zuwa ya iske abokinsa Sayyid zaune a kan wani mashin ƙirar jincheng blue da baƙi. Da ka kalle shi ba sai an gaya maka cewa yana cikin tashin hankali ba, domin alamunsa sun nuna cewa ba a nutse yake ba.
“Kai ya ne?”
Ya miƙa masa hannu alamun su gaisa. Cikin sanyin jiki Sayyid ya miƙa masa hannu suka gaisa.
“Lafiya ba lau ba?”
“Me ya faru?”
“Magana ce a kan wannan babir ɗin”
Sai a lokacin ma Saama ya yi wani tunani, shi dai bai san abokin nasa da mashin ba.
“Me ya samu mashin ɗin?”
Saama ya tambaya yana duban mashin ɗin.
“Ina sanda muka fita zanga-zangar nan?”
Tun da Saama ya ji haka ya fara fahimtar inda Sayyid ya dosa.
“Ka na ji ko? Yanzu dai Mama ce ta aikeni kasuwa, ka ara mini mashin ɗin na je na dawo, idan na dawo koma wacce ce a yi!”
Kuskure na biyu ke nan.
“Amma ni ba wannan ne ya kawoni ba Saama”
“Idan ba za ka ara mini ba na yi tafiyata, idan na dawo sai mu yi magana”
Kasancewar a halin da Sayyid ke ciki Saama shi ne madafarsa ta ƙarshe yasa bai sake masa musu ba, salin alin ya sauƙa daga kan babur ɗin, ya ba shi key sannan ya zauna a kan wani benci dake kusa da wurin, yana kallon Saama ya tada mashin ɗin ya bar wurin, kuskure na uku, wani irin kuskure da ba zai taɓa iya gyara shi ba.
________
_Humph!_
_Akwai magana, ko wace kaddara ce za ta faɗawa gidan sharifai?_
_Da alama Akira ta samo wani da yake jin ƙanta a KINKIN bayan Nikamba_
_Wata sabuwa, to yanzu dai ga Aminatu nan ita ma ta ɓillo, mu je zuwa, na gaya muku cewar har yanzu ba mu je ko ina ba_
#SalmaAhmadIsah
#MiniCandy
#Bahadejia
#KawaZuci
~~~~~~~~~~~~~~~
*KAWA ZUCI*
*©SALMA AHMAD ISAH.*
*08*
*No.23, Rua Visconde de Piraja, Mooca, Sao Paulo, Brazil.*
Mooca wani ɗan ƙaramin yanki ne da yake cikin babban birnin Sao Paulo, unguwa ce ta masu ƙaramin ƙarfi, mafiya akasirin gidajen dake unguwar na haya ne, mazauna unguwar yawancinsu ma'aikata ne, sai kuma masu zuwa ci rani daga ƙauyuka ko ƙananan garuruwan dake ƙasar ta Brazil.
PEDRO POV.
_"Eu sinto que algo está errado Thiago!"_
_(Ina jin kamar akwai abin da yake shirin faruwa Thiago!)_
Kalaman suka fito tar ta cikin speaker'r ƙaramar plasma'n dake cikin ɗan ƙaramin falon gida mai lamba 23 dake unguwar Rua Visconde. A cikin Film ɗin Medusa, wanda aka haska shi a shekarar 2021 shi ake haskawa a cikin talabijin ɗin.
Zaune yake a kan carpet, yayin da yake operating laptop ɗinsa dake kan ƙaramin center table ɗin cikin ƙaramin falon, Juliana kuma na zaune a kan tilon kujerar dake falon, domin bayan kujerar ta zaman mutum uku babu wata kujera sai Bean Bag chairs guda ɗaya dake gefe.
Ita ce ke kallon ba shi ba, hankalinta na kan tv'n, amma kuma ta saka hannayenta biyu duka ta riƙe gashin kan Pedro tana ɗaure gashin nasa da ƙananun band. Ko ta waje idan ka kalli gidan za ka san cewa ba shi da girma.
Daga entry door falo za ka fara riska, falon ba shi da girma, domin bayan tv da kujerar dake falon babu komai ciki, daga can ɓangaren dama na falon akwai ƙofar kitchen, daga ɓangaren hagu kuma ƙofar ɗakin Pedro, ɗan gaba da ƙofar ɗakin nasa kuma akwai gajeren stairs, wandda yake manne da ƙofar ɗakin Juliana dake sama, kuma bayan ɗan ƙaramin ɗakin nata babu komai a saman.
A ƙalla yanzu sun haura shekaru biyar suna rayuwa a cikin gidan, dan tun bayan fitowar Pedro daga prison ya kama musu hayar gidan suka ci gaba da zama a ciki. Duk da unguwarsu cike take fal da mutane kala-kala, ba su damu da yin mu'amala da kowa ba, idan aka ɗauke Ibrahim maƙocinsu, wanda a yanzu ya zarce maƙoci sai dai su ƙira shi da ɗan uwa. Ba su damu da shiga rayuwar kowa ba, dan haka babu wanda yake shiga tasu. Hatta Juliana a makaranta ba ta da ƙawaye, ba ta kula kowa kamar yanda Pedro ya raineta tun tasowarta.
"Mts wannan Bruno ɗin haushi yake bani, shi bai san dai-dai ba ne?"
Ta tambaya duk da ta san wanda ta tambaya ɗin ba lallai ya iya bata amsa ba, dan tun da ta fara kallon ko sau ɗaya bai ɗaga kansa ya kalli tv'n ba, ita da ta kunna ita kaɗai take abinta.
"Waye Bruno?"
Ya dawo mata da tambaya yana ci gaba da abin da yake, hannunta ta janye daga cikin sumar kansa da ta ƙulle fiye da rabi, musamman ma ta gaban goshinsa, ta ɗora hannun nata a kan kafaɗarsa.
"Bruno! Wannan Bruno ɗin"
Ta nuna masa tvn.
"Oh na gane"
Ya ce ya gane ɗin ba tare da ya gane ba, dan bai kalli tvn ba ballantana ya san wanda take nufi, dukan kafaɗunsa ta yi tana faɗin.
"Hard Rock! Ta ya za ka gane ba tare da ka kalle shi ba?"
"Mm"
Kawai ya sake cewa, dan ba shi da lokacin wannan shirmen nata, abin da yake kan yi yanzu ya fi maganarta sau dubu amfani. Jin bai sake cewa komai ba yasa ta sunkuyar da kanta kusa da kafaɗarsa tana kallon abin da yake.
"Huh? Zuzurutun kuɗi haka? Wannan account ɗin waye?"
"Tsohon minister Mr Lucas?"
Dariya ta yi tana faɗin.
"Wannan matsolon da ko matarsa da 'ya'yansa ba sa iya cin kuɗinsa ne za a biya kuɗin aikin da za a mini da kuɗinsa?"
"Zan buɗe account ɗin duk wanda ya kama domin naima miki lafiya!"
Jin daɗin maganar yasa tasa ta rungume wuyansa ta baya tana lusmhe idonta a lokaci guda kuma tana murmushi.
"Na gode Fireball!"
Sunayen da take ƙiransa da su ke nan, "Fireball" ko "Hard Rock" ba ta cika ƙiransa da Pedro ko Badar ba, dan tace waɗannan biyun sun fi dacewa da shi.
"Ka yi sallah?"
Ta tambaya tana sakin wuyansa.
"Mm"
Ya sake amsa mata a taƙaice tare da gyaɗa kansa sau ɗaya.
"To..."
Kirrrrr! Doorbell tai ƙara alamun wani ya baƙunci gidan.
"Ibrahim ne, bari na je na buɗe!"
Ta miƙe tana ɗaukan karenta Caio, kamar yanda ta yi zato cewar Ibrahim ɗin ne tana buɗe ƙofar wani kyakkyawan farin bafulatani ya bayyana a bayan ƙofar.
"Good day Miomio!"
Ibrahim ɗin ya faɗa yana murmushi, martanin murmushin ta mayar masa tana sakin handle ɗin ƙofar sannan ta ja baya ta ba shi damar shigowa ciki.
"Good day Malam Iro!"
Tare suka yi dariya saboda sun saba gaisuwa irin haka, shi ya ce mata Miomio saboda wai tana kama da mage, ita kuma tace masa Malam Iro saboda ya gaya mata cewar haka ake ƙiransa a can ƙasarsu Nigeria. Takalmansa da ya shigo da su ya cire a nan entry, Juliana ta ɗauko masa slippers ɗin Pedro dake wurin ya saka, sannan suka shiga ciki tare.
"Ibrahim? Yanzu ka dawo?"
Pedro da har yanzu yake zaune a wurin da yake bai tashi ba ya tambaya sanda suka ƙaraso ciki, a gajiye Ibrahim ya zube kan Bean Bag chair ɗin dake falon yana furzar da numfashi.
"Ko gidana ban shiga ba, saboda wata yunwa da na kwaso kamar zan mutu!"
Ibrahim ya amsa.
"Julia ki kawo masa abincinsa"
"Toh"
Ta amsa tana aje karen dake hannunta, sannan ta nufi kitchen ɗin.
"Ki tabbatar kin wanke hannunki kafin ki taɓa abincin fa!"
Ya yi maganar da ɗan ƙarfi, dan zuwa lokacin ta shige kitchen ɗin.
"Ba zan wanke ba"
Ta ba shi amsa da ƙarfi ita ma.
"Me kan katako kawai"
Ya ƙarashe yana dawo da dubansa kan Ibrahim dake murmushin da ya kusa zama dariya.
"Dariyar kuma ta miye?"
Ibrahim ya rufe bakinsa yana nuna masa kansa, bai tuna da abin da ke kan nasa ba sai da ya sa hannunsa ya taɓa gashinsa, ya ji ƙulle-ƙullen da Julia ta masa kamar wata mace. Tsaki ya ja yana ciccire band ɗin.
"Wata rana sai na karya ƙafar yarinyar nan na watsata waje!"
"Ƙafarka ta karye ba ta Julia ba"
Juliana da ta fito daga kitchen ta faɗa tana nufosu hannunta riƙe da plate. Shi dai bai tankata ba har ta ƙaraso ta bawa Ibrahim abincinsa.
"Dare ya yi, ki je ki kwanta da wuri saboda makaranta kar ki makara"
"To Mr Right! Gobe Lahadi, ba Monday ba!"
"Oh haka aka yi ko? Duk da haka na san za ki je church, ki je ki kwanta da wuri kar ki makara!"
Bakinta ta gurmuɗa hagu da dama, sannan ta ɗauki Caio ta nufi stairs ɗin ɗakin nata, har ta kusa isa wurin ta dawo da baya, tana zuwa kusa da shi ta ja gashin kansa da ƙarfi sai da ya yi ƙara, sannan ta fita da gudu ta yi sama tana musu sai da safe shi da Ibrahim.
"Zan zo na sameki a ɗakin nan ne ai!"
Tana tsaye a ƙofar ɗakinta ta juya tai masa gwalo sannan ta banko ƙofar ɗakin.
"Mts ita komai wasa ne a wurinta!"
Ya juyo yana rufe system ɗinsa, kafin ya kalli Ibrahim da shi ma shi yake kallo.
"Pedro?"
Ibrahim dake cin abinci ya ƙira sunansa.
"Mm"
Ya amsa yana ci gaba da cire band ɗin da Juliana ta saka masa su.
"Har kullum ba zan daina gaya maka cewar wannan hanyar da ka zaɓa ma kanka a matsayin sana'a ba dai-dai ba ce, tun a baya sanin cewa wannan ita ce sana'arka bai sa na yada kai da Julia ba, a nan gaba ko da mutum za ka kashe ni mai taimaka maka ka binne gawarsa ne, domin taimakon da ka mini ba zan taɓa mantawa da shi ba a rayuwata...!"
Maimakon yace wani abu kawai sai ya yi murmushi mai sauti.
"Wani aikin ka samo mini?"
Bayan shuɗewar minti guda ya yi tambayar da ya riga ya san amsarta, duk bayan wasu lokuta Ibrahim cikin fafutukar naima masa aiki yake, amma a duk sanda zai kawo masa aikin ba ya kasa rejecting. Ya san niyyar Ibrahim a kansa kyakkyawa ce, amma ba ya jin zai hutar da shi ta hanyar yarda da yin wani aiki da ban da wanda ya saba yi, a ganinsa wannan ita ce hanya mafi sauƙi ta samun kuɗi, kuma hanya mafi sauƙi ta rama abin da aka masa. Abin da yake zaton dai shi ya tabbata, dan bayan wucewar wasu sakkani Ibrahim ɗin ya gyaɗa kansa, sannan ya fito da wata takarda dake aljihun jacket ɗinsa, ya aje a kan center table ɗin dake gaban Pedro.
"Aiki ne da na san za ka iya yinsa, domin aiki ne a ma'aikatar sadarwa, ka laƙanci iya sarrafa computer sosai, dan haka na san aikin ba zai maka wahala ba!"
Hannunsa ya miƙa ya ja takardar, santsin glass na center table ɗin ya taimaka ma takardar ta tafi zuwa gabansa, ɗagata ya yi sannan ya buɗe yana nazarin rubutun ciki.
"Not bad, amma ba zan iya yin aikin ba!"
"Wai sai zuwa yaushe za ka yarda ka daina sata Pedro? Ina jiye maka ranar da za ka sake shiga hannun 'yan sanda! Yau nake samun labarin sabuwar jami'ar da aka kawo sashin binciken laifukan sata na yanar gizo, yanda nake samun labari a kan jami'ar tana da ƙwarewar da za ta iya kama mai laifi duk wayonsa..."
"Luana Carla! Jami'a daga garin Rio de Janeiro, ba ta taɓa aure ba, amma tana da ɗa.... Hmm ta ƙware sosai a kan aikinta, ba ta taɓa faɗuwa a ko wani assignment ba, amma ina da sa ran za ta faɗi a wannan!"
Dalla-dalla yake tsaro jawabai a kan 'yar sandar, kamar mai karanta tsohuwar wasiƙar da ta daɗe da isowa gare shi. Ibrahim ya kasa riƙe mamakinsa, domin sukuti ya yi yana kallon Pedro ɗin.
"Badar?"
Ya kalle shi yana buɗe ƙwayar idonsa gray color a kansa.
"Tun sati biyu kafin a kawota Sao Paulo na san komai a kanta!"
Ibrahim ya kasa magana, domin lamarin ya fara girmar tunaninsa.
"Me Dr Lima ya ce maka game da matakin ciwon Juliana?"
Ya masa wannan tambayar domin ture waccan magana, tun da ya ga magana a kan lamarin ba shi da amfani kwata-kwata. Cak hannayensa dake wasa da takardar aikin da Ibrahim ya ba shi suka tsaya, bayan sakannin da ba su fi uku ba kuma sai ya saki murmushi mai ciwo.
"Dr Lima?... Dr Lima yace daga yau... Zuwa gobe... Zuwa jibi... A ko da yaushe, zan iya rasa Juliana!"
Ƙaran faɗuwar cokalin hannun Ibrahim yasa ya ɗaga idonsa da ya fara sauya kala ya kalle shi, har wani abu mai kama da ƙwalla na taruwa a cikinsa.
"Badar ya aka yi ciwon nan nata ya yi ƙamari har haka ba tare da an ɗauki mataki ba?"
Kansa ya ɗauke yana jinjina shi.
"Rashin kuɗin aikin da za a mata, amma na ɗauki alƙawarin a cikin satin nan za a mata aikin nan, zan samo kuɗi ko da ko za a ɓoyesu a ƙasan tekun Copa Cabana ne..."
A matsayinsa na wanda yake amsa sunan musulmi kamata ya yi ace ya naimi yardar mai kowa mai komai a wannan gaɓar, sai dai bai yi hakan ba, saboda ƙarancin tarbiyyar addini da ya taso da ita.
"Badar! Ni dai shawarar da zan baka ita ce, duk abin da za ka yi ka riƙa duba abin da zai biyo baya, ba na so ka tafka kuskure mafi girma a rayuwarka, wanda za ka zo kana da na sani a kansa!"
Bai ce komai ba, domin tun da ya tuna da batun mutuwar tata zuciyarsa ta fara masa ɗaci. Tunawa yake da irin rashin da ya yi a rayuwarsa, duk wasu wanda yake so kuma suke sonsa a rayuwa mutuwa suke su bar shi, sai dai a wannan karon ya ɗauki alwashin yaƙi da ƙaddara, domin ya faɗawa kansa cewar ba zai taɓa bari Juliana ta mutu ta bar shi ba, ya nisantata daga yunwa, ya nisantata da jahilci, ya nisantata daga duk wani abu da zai cutar da ita, shi ma wannan kamar sauran, haka zai yaƙe shi...
Sai dai duk abin da ƙaddara ta riga ta zana ɗan adam bai isa ya goge shi ba, duk yadda ya kai ga ƙarfin hali kuwa, ko ba ya so ko yana so dole abin da aka rubuta masa sai ya wanzu a kansa.
Har wajen karfe sha ɗaya Ibrahim yana gidan, bai tafi ba sai sha biyu saura. Kuma sai bayan da ya tafi ne ya je ya kulle ƙofar gidan, ya kashe duk wasu kayan wuya na falo da na kitchen. Kana ya zarce zuwa ɗakin Juliana, duk da ya tarar da ta yi bacci bai fasa shiga ɗakin ba. Zama ya yi a bakin gadonta yana kallonta, murmushi ya yi, musamman da ya tuna haɗuwarsa da ita ta biyu, lokacin da ya rasa komai, ita ma kuma ta rasa komai nata.
_"Na tabbata ba za ki tafi ki barni ba!"_
Ya faɗa a zuciyarsa, ya daɗe a ɗakin nata ba dan yana komai ba, sai dan kansa ya miƙe ya gyara mata kwanciya, sannan ya fita daga ɗakin ya shiga ɗakinsa da zummar kwana yana aiki, dan bai ga bacci ba matsawar bai haɗa kuɗaɗen da za ai mata aiki ba.
*Shekarata 2010.*
*Lencois town, Brazil.*
Kamar yanda ya saba attending lessons a duk yammacin ranar juma'a, haka yau ma ya shirya da wuri ya tafi, tun kafin closing time ya yi ya ƙagu ya dawo gida, domin sun yi waya da Papsi ya ce masa yau zai dawo.
Shi ne mutum na farko da ya fara fita daga class bayan an kaɗa ƙararrawar tashi. Tsabar saurin da yake har food-flask ɗinsa ya manta, sai Drake ne ya ɗauko masa ya biyo shi da shi.
"Wai wannan gaggawar da kake ta miye?"
Cewar Drake da ya lura da fara'ar da yake tun zuwansa school ɗin.
"Yau Papsi zai dawo, ya mini alƙawarin idan ya dawo zai kaimu Copa Cabana ni da Sophia!"
Hatta muryarsa ɗauke take da zallar nishaɗi, domin barinsa garin Lencois abu ne da bai cika faruwa ba. Idan zai iya tunawa ma rabonsa da ya bar garin tun shekaru biyar da suka wuce, Papsi ya ɗauke shi suka tafi Sao Paulo, a can suka yi celebrating babbar Sallah a lokacin, bayan wannan kuma ba ya jin ya ƙara barin garin.
"Ni ma zan so na je, amma Dad yace ayyuka sun masa yawa, ba lallai ya kaini ba!"
"Idan ka na so zan iya faɗawa Papsi ya faɗa ma Dad ɗinka cewar za ka tafi da mu!"
"Da gaske?"
Pedro ya jinjina masa kai.
"Eh"
"Ai ko na ji daɗi"
"Kar ka damu zan masa magana"
"Ok"
"Me ake a can?"
Pedro ya yi tambayar yana tsayawa, yayin da yake kallon wasu
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 7 Chapter of 14