sa ambata, Umar ya yi murmushi yana girgiza kansa cikin ta’ajibin wannan lamari.
“Eh ya ce mini nan da wani satin zai shigo ƙasar nan… Me yasa ka tambaya? Ko kun yanke hukuncin shiryawa da juna…?”
“No, no, no... You misunderstood me, i was just asking!”
Sa’ad ya katse shi yana girgiza masa hannu domin tabbatar masa da hakan ba me iyuwa ba ne.
“To me yasa ba za ku shirya ba?”
“Faɗa muka yi da za mu shirya?”
“Sa’ad”
Umar ya kira, bai amsa ba sai kallonsa da ya ci gaba da yi.
“Wai mece ce matsalar ne? Ni na kasa gane kan lamarin nan naku, can you explain to me please”
“There's nothing to explain about, Umar”
“Wel na yarda da hakan, amma ya kamata ace kun shirya da ɗan uwanka, naka ko ya ci ka ba zai karya ƙamshinka ba Sa’ad, na san kai me fahimta ne, domin ka fi Hammad sanyin hali”
Sa’ad ya furzar da huci ta gefen bakinsa yana murmushi as if ya zuƙi sigari ne yake busar da hayaƙinta. Ya tsaida dubansa a kan Umar, kafin ya sake maida hannunsa cikin aljihun ya yi taku biyu zuwa gaban Umar.
“Ni ɗan FC Bayern ne, Hammad kuma tun da can supporter'n FC Barcelona ne, yanzu kuma PSG yake bugawa ƙwallo, ko a ƙwallo ra’ayina da nasa ya bambanta, tun farko a haka muka taso, abin ba zai zama wani iri ba idan muka bar hakan ya ci gaba da faruwa, dan Allah ka fahimta”
Yana kaiwa nan ya juya ya ci gaba da tafiya abinsa, tun farko sashin Ammi ya yi niyyar zuwa, domin yana sa ran barin garin gobe idan Allah ya nufa, dan haka yana fita daga part ɗinsu su biyu da aka ware musu ya nufi can ɗin, yana tafe yana rera waƙa da bakinsa, lokacin da ya ratso ta hanyar da ta raba part ɗin Adda da na Ammi ya ci karo da Sadiq da ya shigo fadar. Tsayawa ya yi suka gaisa, har yace masa shi ma barin garin zai yi shi yasa ya zo duba jikin Maryam kafin ya tafi, ba wata doguwar magana suka yi ba kowa ya kama gabansa, Sadiq ya yi sashen Adda shi kuma ya nufi na Ammi.
A ƙofar falo na farko ya tsaya, ya danna door bell sannan, ya ja baya yana amsa wasu bayi biyu da suka zo wucewa suna gaishe shi. Babu jimawa aka zo aka buɗe ƙofar, har ƙasa hadimar da ta buɗe ƙofar ta durƙusa ta gaishe shi, ya amsa mata yana murmushin da ya saba jifan kowa da shi, sannan ya shiga falo na farko, a nan ya ga wasu hadiman biyu na aikin gyaran falon, su ma gaishe shi suka yi, ya amsa sannan ya nufi ƙofar falo na biyu. Saɓanin falon farko da kayan cikinsa suka kasance milk da yalo falo na biyu kuma kayan dake ciki duka blue da fari ne, tun daga kan curtains, kujeru, carpet da sauransu duka blue da fari ne.
Bai ga kowa a falon ba, bayan sanyin AC da ƙamshin turaren kasko dake tashi babu komai. Kai tsaye stairs ya nufa ƙofar farko dake sama ya buɗe bayan ya haye, nan ma wani falon ne, sanin cewa a lokaci irin wannan Ammi na cikin falon yasa yana buɗe ƙofar ya yi sallama. Muryoyi biyu ne suka amsa masa a bayyane, dan ita Ammi a zuci ta amsa masa. Ƙofar da ya buɗe ya rufe a sannan ya bi falon da kallo, Ammi na zaune na kishingiɗe a kan kujera, yayin da wasu daga cikin masu mata hidima ke zaune a kan carpet, ga wasu kaya zube a gabansu.
“Ammi barka da hutawa”
Ya gaisheta lokacin da ya samu wuri ya zauna a falon.
“Barkan ka dai”
Ammi ta amsa bayan shuɗewar wasu sakanni saboda tsabar niƙa irin ta matan sarakuna masu ji da kansu, tana amsa shi ta maida hankalinta kan hadiman dake jiran umarninta.
“Ba a samu yajin ƙulin ba?”
“Eh ranki ya daɗe har kasuwa na taka na je amma ban samu ba”
“Shikenan, waɗannan ɗin ma sun isa, ku fita da su an jima zan sa a ɗaukesu”
“An gama Allah ya taimakeki”
Suka haɗa baki wurin faɗin hakan. Sannan suka kwashi kayan da suke zube a gabansu suka fita da su.
“Ka gama haɗa kayanka ne?”
Bayan wani lokaci Ammi ta cillo masa tambayar a cikin shirun da falon ya ɗauka, ya ɗaga kai ya kalleta, amma ita ba shi take kallo ba, hankalinta na kan wayarta da take operating, amma ya san tambayar tasa ce.
“Ah a’a ban haɗa ba tukkuna”
Ammi ta ɗaga kai ta kalle shi.
“Miye dalili?”
“Ammi hutun da na ɗauka fa bai ƙare ba, dan Allah ki yi wa Takawa magana ya barni na ƙarasa…”
Kallon da Ammi ta fara jefa masa yana cafewa yasa ya sauƙe kansa ƙasa, tashi ta yi zaune da kyau tana ƙare masa kallo.
“Ka taɓa ganin sanda mahaifinku ya yi magana biyu?”
Ya girgiza kansa, tun da ta fara wannan maganar ya san ba za ta sa bakin ba.
“To ba zai fara a kanka ba, Sa’ad ni kaina na gaji da abubuwan da kake! Ina kauda kai ne kawai saboda mahaifinku bai zuba maka ido ba, idan kana ganin tsananin hukuncin da ya yanke maka idan ka kaini bango ni zan maka hukuncin da ya fi nasa tsauri, dan haka ka shiga taitayinka, ka san abin da kake, ka yi wa kanka karatun ta nutsu kafin duniya ta maka…”
A yanda take masa faɗan ya ta batar masa lallai ranta a ɓace yake da shi, to wai shi Sa’adu bawan Allah me ya yi da za a riƙa masa irin wannan faɗan? Shi in bai so mata ba maza zai so? Kuma duk wannan yawan kula ‘yan matan da yake dan bai dace da dream girl ɗinsa ba ne, once he meet her zai watsar da duka wannan trash ɗin. Kuɗi kuma in ba a kashe shi ba rami za a haƙa a binne? Amfanin kuɗi a kashe! Haka hakankalinsa ya kitsa masa, sanin cewa bai isa ya furta hakan ba yasa ya ƙara sinne kai.
“Allah ya huci zuciyarki ranki ya daɗe! Insha Allah zan gyara”
“Hakan zai fi maka kyau!”
Kafin wani cikinsu ya sake furta komai aka buɗe ƙofar falon kafin sallama ta biyo baya, Kairat da Aysher ne suka shigo, kowacce a cikinsu a gajiye take, duba da yanda suke tafiya, a falon suka zube suna faɗin sun gaji.
“Wallahi Ammi gidan nan da nisa”
“Saboda a ƙafa kuka tafi ko?”
Cewar Ammi tana wurga musu harara daga ita har Kairat ɗin.
“Kun samu matar?”
“Eh mun sameta”
“Wace mata?”
Sa’ad ya sa baki a maganar.
“Wata ce da take yin alkaki na siyarwa, kai muka siyowa”
“Alkaki?”
Ya tambaya muryarsa na fallasa jin daɗin abin da Ammi ta masa, ya kalli Ammi, ita kuma sai ta miƙe tana faɗin Aysher ta biyota, ta fita a falon Aysher na biye da ita, suka bar shi zaune da Kairat dake tambayarsa wai da gaske gobe zai tafi?.
GURU POV.
Zaune yake kan kujerarsa ta gado, idonsa a rufe, ya tokare kansa da ɗan yatsansa ɗaya kamar me bacci. Amma ba baccin yake ba, hasalima a kwanakin nan bacci ya gagare shi, ko da ace yana naiman baccin ba zai samu ba, idan kuma yace zai tilasta kansa yin baccin dole to matsala yake samu. Domin a halin yanzu ba shi da aiki sai tunaninta, a rayuwarsa bai san abu mai kama da wanda yake faruwa da shi a yanzu ba, shi kansa idan aka tambaye shi me yake damunsa? 'Bai sani ba’ ita ce amsar da zai iya badawa.
To kamar yanda ya saba ɗin, yau ma fuskarta ce take shawagi a cikin tunaninsa, har yanzu ya kasa mantawa da haɗuwarsa da ita ta farko, ba zai iya ba, ko da ace ya so hakan kuwa. A gefe guda hirar yaran dake aikin ƙulla farin ƙashi (ƙwayar shaye-shaye) dake kusa da inda yake ce ke damunsa, a fusace ya buɗe idonsa, sannan ya janye hannunsa da ya tokare kansa da ita ya kalli inda suke, a tsawace yace.
“Ko ku yi shiru ko ku tashi daga nan!”
Ɗif! Kake ji, kamar an ɗauke ruwa, gaba daya suka tara yaɗonsu gu ɗaya, dan kowa a cikinsu ya lura da halin da ogan nasu ke ciki, ya sauya sosai, a baya ba shi da saurin fushi, amma yanzu da sun yi ƙanƙanin kuskure zai fusata, har ta kai ga ya hukuntasu, gudun kada su ci gaba da fusata shi yasa suka zaɓarwa kansu abin da ya fi alkairi, wato tattara kayan da suka baje suka bar wurin, ya bisu da kallo yana naiman dalilin fusatar tasa, gaba ɗaya cikinsu babu wanda zai haura shekaru ashirin da biyu, duka matasa ne masu tasowa, sai tarin sheɗanci da aka koya musu.
“Damulo dawo!”
Ya ɗaga hannu yana yafito Damulo da ya bi matasan, jiki na rawa Damulo ya dawo da gudunsa yana risinawa ogansa. Guru ya rintse idonsa yana jan karan hancinsa da yatsunsa biyu.
“Damulo”
“Na’am Oga”
“Ba ka ga wasu sauye-sauye tattare da ni ba akwanakin nan?”
Kamar tambaya, kuma kamar ba tambaya ba, duk da haka Damulo ya zaɓi amsa masa da.
“Kwarai oga, ka sauya sosai…”
Wangale idonsa ya yi yana gyara zama kan kujerar da yake, sannan ya kalli Damulo.
“Kamar me da me kaga ina yi?”
“Ah! A…”
“Kar ka tsaya wani kwane-kwane, ka tafi kanka tsaye”
Ya katse shi ransa na baci haka kurum, a ɗan tsorace Damulo ya sosa hannunsa yana cewa.
“Kana saurin fusata Oga, bayan a da ba haka kake ba, sannan yanzu karfin jinka ya ƙaru, kana alamu na nuna cewa kana cikin damuwa, akwai wani abu da ka ɓoye a ranka wanda ba ka so kowa ya san shi”
Huci ya furzar yana girgiza kansa, sannan ya sake riƙe hancinsa yana tabbatarwa kansa abin da yake zargi.
“A ganinka me yake damuna?”
Ya sake cillawa Damulo wata tambayar bayan wasu sakkani sun wuce.
“Ni dai na san tun daga ranar da ka fara ganin Amina ka sauya Oga, hakan yasa nake tunanin ko ka faɗa eh kogin soyayyar talikar!”
“Inna lilahhi wa inna ilaihi raji’un!”
Ya furta cike da tsantsar damuwar da yake jin kamar za ta fito daga zuciyarsa ta yi magana, ya sake yin shiru yana nazari, kamar an tsikare shi yace.
“Amma ka tabbatar ‘yar Malam ce? Ina nufin rabona da ganinta tun tana ƙarama, hakan yasa na mante da yana da wata ‘ya”
“Ai da yake makarantar kwana take a Taraba shi yasa ba za ka santa ba Oga, amma fa akwai ƙura a wannan tafiyar soyayyar taka Oga, tun yanzu na fara jin ƙaurin gwagwarmayar da za ka sha nan gaba kaɗan”
Wani irin kallo ya watsa masa da ya sa ya yi wa bakinsa linzami.
“Allah ya huci zuciyar me arna! Ba na faɗa da nufin na hassalaka ba ne Oga, tuba nake”
Da hannu ya masa alamar ya tafi, aiko ba musu ya bar wurin. Miƙawa tsaye ya yi ya goya hannunsa a baya, can kuma ya koma ya zauna… Jin gaba ɗaya zaman ba ya masa daɗi sai ya sake tashi sannan ya ƙira Damulo yace ya zo ya rakashi wani wuri.
Tafiya suka fara a gefen gonakin ciyawar shayi na jama’ar ƙauyensu da suke ƙara ƙawata yankin nasu, kafin kuma suka doshi can saman tsauni, tun suna tafiya suna iya hango ƙauyen Yerimaru daga saman tsaunin har ya ɓace musu. Sanda suka iso kusa da wata ƙatuwar bishiya suka tsaya, a nan Guru yace Damulo ya dakata ya jira shi, zai dawo ba da jimawa ba. Ya bar shi a nan ya ci gaba da kutsa kai cikin dajin yana nufar can saman tsaunin.
Ko da ya kai ƙarshen tsaunin ma bai tsaya ba, sai ya fara gangarawa ta ɗayan ɓangaren tsaunin, tafiyar minti ɗaya ya yi ya fara hango wani ɗakin ƙasa da aka gina guda ɗaya tallin tol a dokar dajin. Babu tsoro ko shakkar komai a ransa ya nufi bukkar gadan-gadan, lokacin da yake gaf da cimma ƙofar ɗakin aka harbo wata kibiya daga saman rufin ɗakin, kamar da ya san da tahowar kibiyar ya ɗaga hannunsa ya riƙeta.
Dariya ce ta karaɗe wurin, a hankali kuma wata iska mai sanyi ta fara busawa, cikin ƙasa da sakan biyar wani baƙin mutum ya bayyana tsaye a ƙofar ɗakin, hannunsa rike da kwari, sai dariya yake yana kallon Guru da tun da ya riƙe kibiyar bai yarda ya sake motsi ba.
…
“Lalai wannan karon a ankare kake Guru”
Cewar mutumin nan na ɗazu da ya bayyana a gaban Guru, zaune suke a cikin ɗakin ƙasar shi da Guru, Ɗakin da babu komai ciki sai tarin tarkace da bolar da ba ka tantance ta miye. Guru ya yi murmushi yana juya kibiyar da bai yasar ba har zuwa lokacin.
“Hmm! Yanzu jina ya ninku fiye da da Mangwau, ba na iya bacci da daddare, zuciyata ta matso kusa, ba na iya sarrafa fushina, tunani barkata yana damuna, ban san me yake faruwa da ni ba”
Boka Mangwau ya yi murmushi.
“Tun yaushe ka haɗu da ita?”
“Wa ke nan?”
Ya mayar masa da tambayar. Mangwau ya kalle shi cikin alamun dake nuna ba wasa yake ba.
“Ina nufin ƙaddararka! Tun yaushe ka haɗu da ita?”
Guru ya lumshe idonsa yana tambayar kansa a cikin zuciyarsa ‘Ke nan dai ta tabbata Aminatu ita ce ƙaddarata?’ a zahiri kuma sai yace.
“Kwana uku zuwa huɗu da suka wuce…”
Shiru ya ratsa a ɗakin, Guru ya yi shirun ne kawai dan yana jiran amsar da za ta fito daga bakin Mangwau.
“Amma me yasa Aminatu ta zo a ƙaddarata? Me yasa ba wata yarinyar ce da ban ba? Ka san cewa a baya na cutar da Malam sosai, na raba shi da abubuwa masu muhimmanci a rayuwarsa, me yasa ita ma wannan ni ne silar raba shi da ita?”
Ya zaɓi tambayar abin da ya hana shi sukuni tun da ya fara fuskantar cewa lallai Amina ita ce ƙaddararsa. Mangwau ya juyo ya kalle shi.
“Yanzu tuhumata kake a kan ƙaddarar da ba ni na rubuta maka ita ba ko kuwa? Ka sani cewa ba ni na rubuta ƙaddararka ba, me yasa kake so ka dora mini laifin?”
Guru ya yi shiru.
“Ba wannan ne mai amfani ba, abu mafi muhimmanci shi ne ka tabbatar ka mallaki zuciyarta, sannan ka aureta kafin zuwan guguwar da za ta zama cikas a rayuwarka!”
“Guguwa?”
Ya tambaya cikin alamun rashin fahimta. Mangwau ya miƙe tsaye yana fidda wani sauti daga bakinsa mai kama da tsaki, amma kuma ba tsakin ba ne.
“Ƙwarai guguwa, wadda za ta tarwatsa duk abubuwan da muka daɗe muna shiryawa, wannan guguwar ita ce za ta goge tsoronka a zukatan al’umma, ta ruguje dogon ginin da ka fara ginawa tun da ƙananun shekarunka, ta rabaka da kowa da komai, sannan ta kaika ƙasa!... kamar yanda na gaya maka tun farko kasancewar ƙaddararka a kusa da kai shi ne ƙarfinka, shi zai baka damar ci gaba da kasancewa a raye, ya baka damar girmama ikonka, za ka fi kowa, ka take kowa, ka bi ta kan kowa, ka yi komai a ko ina a kuma sanda ka so, ina mai baka shawarar kada ka tsaya sanya, domin idan ka ce za ka yi wasa to za ai maka sakiyar da ba ruwa!”
AMINA POV.
Tun da safiyar Allah Baffa ya tafi gona ya barta a gidan ita ɗaya kamar kullum. Duk da kaɗaici ya isheta ba ta fita daga gidan ba, dan duk da ƙin jinta a wasu lokutan ba ta cika son shiga cikin mutane ba, ko l dan ta saba da rayuwar kaɗaici ne oho?. Da misalin ƙarfe sha ɗaya ta fito daga wanka, tana shirin shiga ɗaki domin sanya tufafi a jikinta Suwaiba da Lawisa sukai sallama a gidan.
Da mamaki ta aje bokitin hannunta tana kallon yanda suka rangaɗa kwalliya.
"Ku kuma ina za ku je ku kai wannan uwar kwalliyar haka?"
Ta tambaya mamakin kan fuskarta bai gushe ba.
"Kar dai ki ce kin mance da yau ne kamun bikin Hannatu?"
Cewar Suwaiba da mamaki, domin Hannatu ɗaya ce daga cikin ƙawayensu, aurenta da ya gabato yasa aka daina ganinsu da ita.
"La'ila hailallahu, wallahi na manta kuwa"
"Ah to, gara dai ki shirya mu tafi, dan idan kika ƙi zuwa ba ki mata adalci ba"
"Yanzu kuwa zan shirya mu tafi"
Ta yi sauri ta faɗa bukkar da take kwana ciki, su kuma suka zauna a rumfa suna hira. Ba wata kwalliya ta yi ba, dan da ma can ita ba gwanar kwalliya ba ce, ɗaya daga cikin ƙure adakarta ta ɗauko atamfa riga da zani ta saka, ta shafa mai da hoda, bayan kwalli ba ta yarda ta sake saka wani abin a fuskarta ba.
Ganin cewa yau bikin ƙawarsu ake yasa tace bari ta saka mayafi irin na 'yan mata, ita ma ta fito kamar kowa, ta shafa humra ta fito tana ɗaura ɗankwali a kanta, duk da 'yar ƙauye ce ta fita da ban da matan ƙauye, saboda a birni ta taso, cikin mutane daga mabambantan wurare.
Su suwaiba suka sata a gaba suna ta santin kyan da ta musu. Ita ko ranta fess ana cewa ta yi kyau. Da kwaɗo ta kulle ƙofar gidan, saboda ta san babu me zuwa gidan bayan ita da Abboi, ko masu zuwa ɗaukan karatu wurin Abboi ɗin ba sa zuwa sai da yamma bayan ya dawo daga gona.
Hanya suka ɗauka suna tafe suna hirar abubuwan da aka tsara za ai a bikin saboda bikin na masu kuɗin ƙauye ne, ba ƙarya ba kowa ya san uban ƙawar tasu da yawan dukiya, haka shi ma gyatumin angon ba daga nan ba.
"Ni fa saboda na san za a ci mutuncin abinci a wurin bikin nan yasa ban ci abincin safe ba!"
Cewar Lawisa, su kai mata dariya.
"Sannu Lawisa! To Allah sa ba sake reshe kama ganye ki kaiwa kanki ba"
"Ai Wallahi ko da kokawa sai mun ci rabonmu a wurin bikin nan, ai waman saƙara bati siddan fa huwa jahilun!"
Cewar Amina.
"Ni dai ba ruwana, kun san ba na son jisgi, dan yanda 'yan uwan Hannatu suke ji da kansu su ga su 'ya'yan mai kuɗi ba za su bari mu yi kataɓus a wurin bikin nan ba"
"Uhum! Ai Wallahi ba su ba ke ko ub*n..."
Da sauri Suwaiba ta toshe bakin Amina, jin tana shirin yin ashar.
"Ke fa haka kike Amina! Bakinki ba shi da linzami!"
Ta idasa maganar tana janye hannunta baga kan bakin Aminan da ta toshe.
"To miye laifi a cikin wannan maganar? Ba Allah ne ya azurta uban nasu ba? Idan ya so sai ya ƙwace ya bawa wani, kin san ni na tsani baƙin hali Wallahi!"
"To ya isa dai, yanzu maganar ta mutu a nan, mu je kar kallo ya wucemu"
Duk yadda Lawisa ta so maganar ta mutu Amina ba ta yi shiru ba, sai da suka kusa isa gidan sannan ta yi shirun. Kai tsaye suka kutsa cikin gidan su amarya inda ake gabatar da bikin kamun. Wuri suka samu suka zauna cikin 'yan mata 'yan uwansu, ita ko Amina gefe ta koma tana bin kowa da kallo, ba za ta yi gigin shiga cikinsu ta zauna ba, saboda za su iya kawo mata wargi, ita kuma ba za ta raga musu ba, da ma ita tun da can ba ta barin ta kwana.
Duk yadda Suwaiba da Lawisa suka so ta shigo cikinsu ƙi ta yi, ta kame gefe kamar me jiran wani yace mata wani abu. Suna nan zaune 'yan uwan Amarya suka shigo da ɗanyen nono ƙwarya guda, wanda za ai wa amarya feshi da shi a fuska, kamar dai yadda aka saba kamu a al'adar fulani.
Har zuwa lokacin Amina na tsaye a gefe, Suwaiba ta miƙe ta nufi wurin da take tsaye dan ta isar mata da saƙon Hannatu. Sai dai kafin ta ƙarasa Haulatu ɗaya daga cikin yayyen amarya ta biyo ta gefen Amina za ta wuce, har ta wuce ɗin kuma sai ta dawo tana kallonta…
----------------
_Wani abu zai faru a wurin bikin nan🤣, kar ku ce ban faɗa muku ba._
_Free pages sun kusa karewa, ku hanzarta ku fara biyan naku domin kasancewa ɗaya daga cikin wanda za ayi wanna tafiyar dasu_
_Ku tura ₦400 ta 5487270431 Salma Isah Monie Point, sai ku tura shaidar biyanku ta 08130172702_
#SalmaAhmadIsah
#MiniCandy
#Bahadejia
#KawaZuci
~~~~~~~~~~~~~~~~~~
*KAWA ZUCI*
*©SALMA AHMAD ISAH*
*14*
"Ke! Me kike a nan?"
"Sata na zo"
Amina ta bata amsa dai-dai da sigar da ta mata tambayar.
"Kar ki naimi yi mini rashin kunya, dan Wallahi yanzu zan yi ƙasa-ƙasa da ke!"
"A cikin ƙasar za ki binneni ba ƙasa za ki yi da ni ba idan kin isa!"
"Ke Hannatu uban waye ya gayyaci wannan yarinyar?"
Haulatu ta tambaya da ƙarfi, maganarta ta ja hankulan matan dake wurin gaba ɗaya zuwa kansu, har waɗan da ba su lura da Amina nan ba ma suka lura da ita. Hannatu amarya da ta sha lulluɓi kanta a ƙasa babu damar magana, ko kanta ba ta isa ta ɗaga ba saboda kar ace ta yi rashin kunya.
"Haba Haulatu? Yau kika fara sanin alaƙar Hannatu da Amina? Ai duk wannan tambayar ma ba ta taso ba!"
Faɗin wata datijjuwa.
"Duk da haka bai kamata ace mara asali kamarta ta zo gidan bikinmu ba, dan haka ƙafarta a likafa ta bar gidan nan kafin zuwan dangin ango!"
Hayaniya ta kacame a wurin, kowa na faɗin albarkacin bakinsa. Amina ta yunƙura za ta mayarwa Haulatu martani Suwaiba ta riƙeta, sannan ta jata zuwa wurin da ta ƙi zuwa wato cikin 'yan matan amarya kusa da inda take zaune.
"Amina"
Hannatu ta ƙira sunanta tana kama hannunta.
"Dan Allah ki yi haƙuri ki tafi, ba na so a samu matsala a wurin nan, kin san halin Haulatu da masifa, idan masifarta ta ciwota sai ta kai maganar nan har gaban Baffa, ba korarki na yi ba, amma dan Allah ki tafi! Na gode da zuwanki!"
Har ta gama maganar kanta a ƙasa kuma a lulluɓe da mayafi, da yake Amina ta san wacece Hannatu sai ba ta ji haushi ba, ta miƙe kawai ta kama hanya za ta fita, su Harira suka bi bayanta ta juya tace musu su zauna abinsu ita za ta koma gida.
Ba ta jira cewarsu ba ta bar gidan bikin, yo da ma in banda tsautsayi me zai kawota gidan bikin nan, sai dai alwashin da ta ɗauka na cin abincin gidan bikin nan fa ba ta bar shi ya tafi a iska ba, dan tana fita daga ɓangaren da ake gudanar da kamun ta wuce madafa, inda ta san a nan ake aikin raba abinci, domin ba wannan ne aure na farko da aka yi a gidan ba, ta sha zuwa bukukuwan gidan.
Tun daga nesa ta hangi irin kokawar da mata ke yi a kan tuwon biki, wata ma ta ƙi yin girkin ranar saboda za su je su ci na banza, abincin gwana goman da ba dan jaraba irin ta mutane ba ba wani daɗi gare shi ba. Ba ta damu da kokawar da ake ba ta ɗauki kwano hankali kwance ta nufi kulolin da aka cika da abinci ta buɗe ta shaƙe kwanon da ta ɗauka dam, da yake hayaniyar raba faɗan da ake ta ɗauke hankalin kowa har ta gama ɗiban abincin ba wanda ya lura da ita.
"Suna ta faɗa a kan abinci sai ka ce 'yan gudun yunwa! Allah ya sawaƙe"
Ta ƙarshe da jan tsaki ta bar wurin, ta fita daga gidan baki ɗaya, ta ɗauki hanyar komawa gida tana riƙe da kwanon da ta shaƙe da shinkafa da miya har da naman kaza, ga fanke, ƙosai da finkaso da ta zuba duka a ciki.
"Allah ya bani ikon barin ƙauyen nan, dan Wallahi idan na samu dama babu abin da zai sa na ci gaba da zama a ƙauyen nan, yo a kan me?"
Ita kaɗai take tafe tana maganar, saboda yanzu abin nan ya fara isarta. Can da ta yi nisa a tafiyar ta tsaya ta huta, kafin kuma ta tashi ta ci gaba da ta fiya, lokacin da ta gifta ta jikin wani gida aka ƙira sunanta.
"Aminatu?"
Cak ta tsaida ƙafafunta, ba ta juya ba, dan ba ta san mai muryar ba, kawai dai ta tsaya ne dan ganin waye, in ya matsu da son magana da ita ko waye zai riske inda take. Ba tai ƙarya ba kuma, dan wanda ya ƙira sunan nata a matse yake ya yi magana da ita, domin tun daga gidan bikin yake biye da ita har ta kawo nan, a hankali yake taku har ya zagaya gabanta, idonta ta ɗaga tana ƙare masa kallo, duk zamanta a ƙauyen ba ta san shi ba.
"Waye kai?"
Ta masa tambayar da ta zo ranta kai
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 11 Chapter of 14