da yake saurare ba, ba kuma wai dan yana fahimtar waƙar ba, sai dan wasu amsoshi da yake samu yayin da ya kutsa cikin nazari, ba wai kunna wakar ya yi dan nishaɗi ba, ya kunnata ne kawai dan ya toshe kunnuwansa da headphones da ita, domin ta nisanta shi daga hayaniyar jama’a da ta duniya, ta yanda zai samu damar yin tunani a kan halin da suke ciki.
Waƙar da yake ji ba ta hana shi jin sanda aka kaɗa ƙarrarawar dake saman Church ɗin unguwarsu da ya saba kawo Juliana ba, dan kamar yanda ya saba rakata a duk ranakun Lahadi, yau ma shi ya rakota bayan sun yi breakfast. Duk da ba ya shiga ciki, in suka zo ita za ta yi ciki shi kuma ya zauna a kan bencin dake tsallaken Church ɗin. Idonsa ya buɗe tare da cire headphones ɗin dake kansa, ya gyara zamansa yana kallon sanda aka buɗe ƙofar church ɗin.
Mutanen dake ciki suka soma fitowa ɗaya bayan ɗaya, yana kallon fuskokin ko wanne a cikinsu har ya tsinto tata a cikin tarin mutanen, tun daga sanda ta fito har sanda ita ma idonta ya kai kansa, sanye take da farar strapless shirt, ƙafafunta cikin fararen Basic sneakers, baƙin gashin kanta nannaɗe cikin messy bun, hannunta na dama riƙe da Bible, a kan Bible ɗin kuma akwai wata farar takarda kamar katin gayyata. Tun kafin ta tsallako ya miƙe tsaye, tana tsallakawa inda yake ta miƙa masa katin gayyatar da take riƙe da shi, yana karɓa ta tsugunna ta shiga kunce chain ɗin da ya ɗaure Caio a jikin bench ɗin da ya zauna.
“Wannan fa?”
Pedro ya tambayeta yana jujjuya katin cike da naiman ƙarin bayani.
“Katin gayyatar ɗaurin auren Matilda ne”
Ta faɗa masa da-dai da yanda ya karanta a jikin katin.
“Matilda? Aure za ta yi?”
Juliana ta miƙe tsaye bayan ta kunce Caio tana kallonsa.
“Da sai ta zauna ta yi ta jiranka bayan kai kuma ba aurenta za ka yi ba?”
“Da ma ni na taɓa cewa ina sonta ne?”
“Ba ka taɓa ba, amma ka san tana sonka ai”
Murmushi ya yi mai sauti yana jujjuya katin a hyannunsa.
“A ganinki zan yarda na tafka kuskure irin na mahaifina?...”
Ya yi fasali yana girgiza kansa.
“Har abada!”
Juliana ta gane nufinsa, abin da yake nufi shi ne ba zai yi kuskuren bin hanyar da ta zama silar tarwatsewar rayuwarsa a yau ba, ba zai aikata irin abin da mahafinsa ya aikata ba, kuma ta nan ɓangaren yana da gaskiya, domin ruwan da ya dakeka shi ne ruwa. Kafin ta dawo daga tunanin da ta tafi har ya yi gaba ya barta a nan tsaye, Caio ta ɗauka sannan ta bi bayansa.
“Ranar litinin ne auren, za mu zo?”
“In har kina son zuwa ba zan hanaki ba”
Ya amsa ba tare da ya kalleta ba.
“Tare da kai nake son zuwa ai”
Sai yanzu ya kalleta.
“So kike mutane su zageni? Su ce na ƙi aurenta kuma na zo shagalin bikinta?”
“...‘Ki rabu da mutane, ra’ayinsu ba ra’ayi ba ne, duk yadda za ki kai ga gujewa maganar mutane sai kin risketa a gaba, dan haka duk abin da kike son yi kawai ki yi, matsawar hankalinki ya kwanta da abin…’ idan ban manta ba waɗannan kalamanka ne?”
Ta zayyano masa maganar daki-daki, kuma a yadda ya saba faɗa mata, ya girgiza kansa alamun shi fa ba zai je ba.
“To idan har ba za ka je ba ni ma gobe ba zan je asbiti ba”
Cak ya tsaya yana kallonta, ta wani haɗe rai kamar gaske.
“Kar ki manta ranar litinin akwai school, kawai zan barki ki yi skipping saboda kina son zuwa bikin, amma shi ne har kika samu bakin ƙalubalantata?”
“Koma dai miye, in ba ka yarda ba ba zan je asibiti ba, faƙat!”
Goshinsa ya dafe yana kallonta.
“Daga zuwa bikin Matilda sai me?”
Ya ci gaba da tafiya ya barta tana dariya ƙasa-ƙasa, ta bi shi tana faɗin zai kaita siyayya, kuma zai kaita a gyara mata kai, sannan shi ma sai ya sai sabon kaya saboda duk nasa tsofi ne.
“Kayan nawa ne tsofi?”
“Eh mana, yaushe rabon da ka sai sabbin kaya?”
Ya yi shiru, dan ya manta.
“To dan haka dole ka sai abbin kaya, dan ba za ka je wurin bikin nan da tsohon kaya ba”
Idonsa ya juya cike da gajiyawa a kan wannan maganar auren Matildan da ake son tada masa zaune tsaye a kanta.
```````````````````
_Free pages sun kusa ƙarewa fa! Ya kamata a hanzarta a fara biyan kuɗin book ɗin nan!_
_Naira 400 ne ga mai buƙata, za ku tura kuɗin ta wannan account details ɗin: 5487270431 Salma Isah Monie Point_
_Sai kuma ku tura shaidar biyanku ta 08130172702_
_Kada dai ku manta, na gaya muku har yanzu ba mu yi komai ba_
#SalmaAhmadIsah
#MiniCandy
#Bahadejia
#KawaZuci
~~~~~~~~~~~~~~~~~~
*KAWA ZUCI*
*©SALMA AHMAD ISAH*
*12*
AKIRA POV.
Zaune take a kan reshen bishiya, yayin da take kallon ruwan kogin dake kusa da bishiyar, ƙafarta take lilawa tana jin daɗin yanayin ranar ta yau, wata ƙila don ba ta shiga cikin gari ba ballanatana har ta haɗu da wani abu da zai ɓata mata rai ya sa take jin hakan. Amma ko ma dai mene ne, yau tana cikin farin ciki. Tun daga nesa ta fara jiyowa alamun takun sawayen mutum cikin gudu, aiko da sauri ta juyo dai-dai da sanda Njau ya kama trunk ɗin bishiyar da take kai da nufin girgizawa, aiko kafin ya kai ga girgizawar ta yi sauri ta ƙanƙame trunk ɗin daga sama. Ganin ta tsorata tun kafin ma ya kai ga jijjiga bishiyar yasa Njau yin dariya, har da riƙe ciki. Akira ta kumbura baki tana kallonsa da alamun jin haushi.
“Ban san cewa tsoron naki ya kai haka ba ai”
Cewar Njau bayan ya gama sheƙa mata dariyar muguntar da yake, bakinta ta sake kumburawa tana sakin trunk ɗin da ta kama tare da ɗauke kai.
“Akira!”
Njau ya ƙira sunanta, amma ba ta kalle shi ba ballantana ta amsa, kama bishiyar ya yi ya hau sama, sannan ya zauna kusa da ita.
“Kin ga abin da na kawo miki”
Ya daɗi yana miƙa mata ɗan itaciyar da ya ɗauko cikin jakar dake rataye a wuyansa, sai ta kalle shi, sannan ta kalli ɗan itaciyar.
“Kina so?”
Ta gyaɗa kai tana dariya, dan gaba ɗaya rayuwarta ta ginu ne a kan cin ‘ya’yan itatuwa, tun da ba ta da wurin zama da ya wuce daji. Sake miƙa mata ya yi ta, ta miƙo nata hannun za ta karɓa sai ya janye, ta kalle shi da mamaki.
“Ka bani mana”
“Sai kin ce kin daina fushi da ni”
“Na daina fushi da kai”
Ya ƙi ya bata, ya tsaya yana mata kallon ban yarda ba.
“Kin tabbata?”
“Na tabbata, yanzu dai ka bani”
Ta miƙa hannu za ta karɓa sai ya ɓoye a bayansa.
“Kin tabbatar kin daina fushi da ni?”
“Aiyyah! Na ce na daina”
Ta ƙarashe tana ƙwacewa ɗan itaciyar daga hannunsa, babu tunanin wanke shi ko gogewa kawai ta saka dauɗaɗan haƙwaranta ta fara ci.
“Yau ina Nikamba? Tun da ya zo ya kawo mini nama da safe bai sake dawowa ba”
Ta cilla masa tambayar bayan sun kwashe sama da minti uku zaune a wurin, ita tana cin abin da ya bata, yayin da shi kuma yake aikin kallonta.
“Ah! Nikamba? Sun tafi dajin Mwati”
Ta jinjina kanta lokacin da amsar tasa ba ta shiga cikin ƙwaƙwalwarta ta zauna ba, sau biyu kawai ta gyaɗa kan nata, a na ukun kuma ta tsayar da shi cak a iska… Me? Dajin Mwati? A saninta mutanen garinsu ba sa shig dajin Mwati in har ba gasar farautar da aka saba sakawa shekara-shekara ce ta zo ba, suna shiga dajin ne domin su sabunta kayan farautarsu, dalilin gwabzawa a gasar farautar da sarkin kauyen KINKIN ya saba sakawa a tsakin matasan ƙauyen duk shekara.
Gasar da har zuwa yanzu ba a taɓa samun mutum ɗaya da ya yi nasara ba, domin duk wanda ya tafi ba ya dawowa, shi kansa dajin da suke shiga farautar ba shi da maraba da sunan mutuwa. Kuma duk da haka har gobe ba su daina zuwa farautar ba. Da sauri ta juya kanta ta kalli Njau da ya kula da suɓutar bakin da ya yi.
“Dajin Mwati? Me za su yi a dajin Mwati?”
Da sauri ya girgiza kansa, dan ba ya so Akira ta san cewa Nikamba ya shiga gasar ta wannan shekarar, tun da Nikamba ya buƙaci ya ɓoye hakan.
“Ba dajin Mwati nake nufi ba, Djin Kwazi nake nufi”
Shiru ta yi tana kallonsa, kallon tuhuma.
“Njau”
“Mm”
Ya amsa yana ɗauke kansa, dan ba ya son kallon da take masa.
“Ka faɗa mini gaskiya”
“Ya za ayi na miki ƙarya Akira? Ko da ma can kallon maƙaryaci kike mini?”
Ta girgiza kanta.
“Ko daya, kawai dai zuciyata ce ba ta gamsu ba”
“To gaskiya na faɗa”
Ta sake jinjina kanta.
“To”
Ta faɗi kawai, dan kuwa ba ta yarda ɗin ba, ita za ta bawa wani labarin yanda Nikamba yake matuƙar son shiga gasar farautar nan, amma duk shekara sai ta hana shi, ba abin mamaki ba ne in aka ce ya shiga gasar ba tare da saninta ba.
ZAHRA POV.
Ba su suka dawo gida ba sai sanda ake daf da kiran sallahr magrib, dalilin da ya sa hankalinta ta shi ke nan, sanda za ta fito sai da Mama ta ja mata kunne kan kada ta bari magariba ta mata a can, kuma kasancewar ta saba mata faɗa irin wannan yasa ta kasa sukuni har napep ɗin da ta ɗaukosu tun daga gidan sunan ta sauƙe su a gefen hanya. Ita ta fara fita daga napep ɗin, ko yanayin tsayuwarta ka kalla za ka san cewa hankalinta ba a kwance yake ba.
“To wai ke Dimple duk wanna gaggawar da kike ta miye? Ba ga shi mun iso kafin a ƙira sallah ba?”
Cewar Saddiqa lokacin da take bawa mai napep ɗin kuɗinsa.
“Mts ba za ki gane ba Saddiqa, sarai kin san halin Mama, yanzu sai ki ga ta yi fushi saboda na karya dokar da ta kafa mana, ba ma ita kaɗai ba, ko su Ya Adali idan suka dawo gidan suka ga ba na nan dole raina ya baci”
“Hump! Ke dai mu je kawai”
Ta zagayo sanda me Napep ɗin ya ja abarsa ya yi gaba, jerawa suka yi zuwa wani layi, amma duk da haka Zahra ta fi Saddiqa sauri, sai ta yi gaba take tsayawa jiran Saddiqa.
“Dan Allah Dimple ki sauƙaƙawa kanki, kin ga fa har yanzu ko sallar ba a ƙira ba ballantana a shiga”
“Kuma ba ki ga duhu ya fara shiga ba? ni fa duk abin da zai jawo mini matsala gudunsa nake”
Saddiqa ta taɓe bakinta.
“Ni batun wananan saurayin ma nake so na miki”
Duk saurin da take sai da ta tsaya. Ita ma Saddiqan dakatawa ta yi suna kallon juna.
“Na tambayi Zee waye shi, kuma Wallahi idan kika san waye shi sai kin yi mamaki”
Zahra ta ɗauke kai ta ci gaba da tafiya.
“Miye wani abu na musamman a tattare da sanin waye shi ɗin?”
“Akwai mana, Zee tace min ɗan Sarkin garin nan ne”
“Me?”
Tambayar ta fito daga bakinta ba tare da izininta ba. Saddiqa ta yi murmushi.
“Eh kamar yadda kika ji na faɗa ne”
“To sai me kuma? Ai dai ba cewa ya yi yana sona ba, bance ina sonsa ba either, to miye wani abu a ciki?”
“Ke nan idan yace yana sonki za ki amince?”
Tambayar ta girmi tunaninta, domin guje mata sai ta juyo ta kalli Saddiqa a cikin duhun magaribar da ya fara shiga.
“Ni zan wuce gida, sai mun haɗu gobe”
Tana kaiwa nan ta juya da sauri tana tafiya kamar za ta kifa, ko juyawa ba ta yi ba har ta kai ƙofar gidansu. A kusa da guntun gargarin da ya rage a ƙofar gidansu ta ci birki tana haki kamar wadda ta yi gudu daga Ringim zuwa Dutse. To wai ma miye na ɗorawa kai? Miye na tashin hankali a cikin wannan lamarin? Yace yana sonta ne? Ko ita tana jin sonsa a ranta? Babu ɗaya! Ok Fine, me zai hana ta tattara wannan trash ɗin dake son kawo mata matsala a rayuwa ta watsasu gefe ta fuskanci abin da yake gabanta?. Numfashi mai nauyi ta furzar tana girgiza kanta, ta damƙe wayarta dake hannunta da ƙarfi tana kallon ƙofar gidansu da a baya idan ka zo a lokaci irin wannan za ka samu almajiran mahaifinta zaune suna karatu, yanzu kuwa wurin ba kowa, sai gargarin da suke zama a da, da kuma rumfar dake ƙofar gidan inda Almajiran ke zama da asuba ko da yamma. Ƙafafunta ta ja ta ci gaba da tafiya, bakinta ɗauke da sallama ta shiga gidan, tsakanin amsa sallamar da Mama ta yi, da kuma fitowar muryar limamin unguwarsu cikin rangaɗa ƙiran sallahr magaribar ba ace ga wanda ya riga wani ba.
“Kin dawo a dai-dai”
Cewar Mama tana dubanta, murmushi ta yi tana kallon Yata dake zaune a tabarma ɗaya ita da Mama. Ta gaidashe da Yata, wadda ta baje wasu labule (curtains) a gaban Mama, alamun dai cikinsu ake, kuma ta san ba kowa za a siyawa ba face ita, tun tana high school Mama ta fara tara mata kayan kitchen da ɗan abin da ba a rasa ba na kayan aure, lokacin har dariya take idan Maman ta ce ga shi ta siya mata abu kaza saboda lokacin aurenta. Idan ta yi dariyar Mama kan ce.
“Zahra ke nan! Ki daina dariya, aure da mutuwa lokaci ne, yayyenki suna iyaka bakin ƙoƙarinsu a kanki, ni tayasu kawai nake, kuma ina rage musu nauyin da zai hau kansu lokacin aurenki”
Har yanzu tana iya tuna hakan.
“Anti Dimple Barira ta zo ba kya nan”
Cewar Ruwaida dake cin tuwon dare, a lokacin har ta shiga ɗaki ta sauya kaya ta fito domin ɗaura alwala.
“La haula fi sha,atillahi! Kin ga ni na manta ma”
In ji Mama da ta mance da zuwan Barirar, saboda sanda ta zo Zahran ba ta nan Maman tace idan ta dawo za a gaya mata ta zo ba ta sameta ba.
“To bari na yi sallah sai na je gidansu, na san ba zai wuce a kan maganar hular da tace zan saro mata ba ne”
“To ai da ma zaman banzan ba shi da amfani, ke ma da za ki ji tawa da kin riƙi sana’ar nan… Ke! Kin yi sallah ne?”
Mama ta ƙarashe tana taɓa auta dake zaune kusa da ita.
“Mama na yi fa, kin manta sanda zan yi sallahr kika ce na zubawa Yaata ruwa a buta”
“Kwarai an yi haka, na manta ne”
“Mantuwar tsufa ce”
“Ka ga ja’irar yarinya, ni ce na tsufa?”
Da sauri Rauda ta mike riƙe da kwanon tuwonta tana dariya, ganin Mama na laluben carbinta a kan tabarma, ta san kuma ana samun carbin nan babu abin da zai hana shi sauƙa a kan fatar jikinta. Zahra dake alwala ta musu dariya, dan lamarin na Mama da auta sai kallo kawai.
“Ai da gaskiyarta, mantuwar taki ta fara yawa Abu”
Faɗin Yata da ta idar da sallah, Mama ta yi murmushi kawai tana shafa gwiwar ƙafarta.
“Auta ɗauko mana fitilar nan!”
Ruwaida ta amsa, sannan ta fito riƙe da fitila ta kuna ta aje musu a tsakar gidan saboda su yi maganin duhu.
“Umm yauwwa Yata! Wace magana kika ce za ki mini?”
Mama ta tunawa Yata batun maganar da tace za ta mata tun zuwanta gidan, abinka da aku sarkin zance, ai tuni Yata ta gyara zama.
“Ina yarinyar can da nake gaya miki ta gamu da abu kamar ciwon ƙwaƙwalwa?”
Mama ta gyaɗa kai, dan kuwa ba ta mance ba.
“To yanzu dai suna naiman wadda za ta riƙa kula da ita kuma tana tayata kwana, kar ki so ki ji irin kuɗaɗen da suka ce za su biya duk wacce ta yarda za ta kula da ita!”
Cike da alhini Mama ta girgiza kanta.
“Ai ko zai yi wuya su samu wadda za ta kula da ita, duk da yanzu mutane naiman kuɗi suke kamar su yi sata, amma idan Allah yasa suka dace za su iya samu”
Yata ta yi wani murmushi.
“Yo ai ni har na samo musu ita”
“Wace yarinya ce wanna mai zuciyar ƙarfen yarda ta kwana ɗaki ɗaya da mai aljannu?”
Mama ta tambaya tana kama baki.
“Eh to, ni dai tun sanda suka bani aikin naimo yarinyar ban hango kowa a face Zahra!”
Kwaf! Sautin faɗuwar wayar dake riƙe a hannun Zhara ya fito daga ɗaki.
~*~*~*~*~
Hular da Bahijja ta miƙa masa ya karɓa ya sanya a kansa, ya gyara zaman hular da ta hau kansa ta zauna ɗas yana kallon Madubi, Bahijja da tai tsaye a gefe rungume da hannayenta ta ci gaba da kalllon mijinta da ta yi wa kanta alƙawarin ba zai taɓa zama na wata ba bayan ita. Wannan hukunci ne da ta yanke musu shi tun kafin su yi aure, har ta kai ga sun yi auren, matsalar rashin haihuwa da take fama da ita ne ya kawo musu cikas. Domin sai da suka kwashe shekaru biyar da aure ba su samu rabo ba, dan haka suka je aka gwadasu, a nan aka tabbatar musu da cewa ai ita ce mai matsalar ba shi ba. To fa a nan ne aka samu matsala, dan kowa ya shaidi Sadiq da son yara, tun farkon aurensu ya fara siyan kayan jariran da za su haifa, kai hatta sunan da za a sakawa yaran ya zaɓa, yanzu kuma da aka sanar musu da wannan batu sai komai ya ruguje.
Allah shaida ne, a lokacin tabbas ya cire rai da haihuwar, tun da shi dai yana son matarsa, ba zai iya rabuwa da ita domin matsalar rashin haihuwa ba. Kuma ba zai iya ƙara aure ba, domin bai ga wadda zai aura a lokacin ba, to ana cikin haka Allah ya haɗa shi da Maryam, abu kamar wasa, tun yana ɗaukansa a wasan har ya kusa zama gaskiya, domin ba su jima da fara soyayya ba suka yi aure. Wani lamari da ya tashi shaiɗaniyar dake bacci a cikin zuciyar Bahijja, domin tun da aka fara batun auren ta ɗauki huɗubar ƙawaye na fara bin bokaye da Malaman banza.
Duk yadda ta kai ga ƙoƙarin ta hana Maryam shigowa gidan ta kasa, ƙarshe ma sai aka gaya mata cewar idan ba ta yi wasa ba ƙarshe rabo ne zai yi ajalinta, maimakon jin hakan yasa ta saduda ai sai ta ƙara kaucewa, dan ba ta hango zamanta da wata ba a matsayin kishiya, mijinta nata ne ita kaɗai, kuma ba zai zama na wata ba. Duk abin da ta yi ba ta ci nasara ba sai da Maryam ta shigo cikin gidan, duk da haka ba ta zubar da makamanta ba ta ci gaba da naiman duk wata hanya da za ta yi amfani da ita wurin fitar da Maryam daga gidan. Allah bai bata dama ba sai sanda Maryam ta cika wata takwas a gidan, kuma a lokacin Allah ya azurtata da samun juna biyu.
Lokacin da Bahijja ta gano hakan hauka ne kaɗai ba ta yi ba, ko da ta ƙira ƙawarta abokiyar shaiɗancinta Fa’iza sai ta ƙara rura mata wutar, sannan ta ce mata ta zo akwai wani wuri da za su je, to ko da ta nutsu sai ta gane cewa daga Maryam har Sadiq ɗin babu wanda ya san da batun cikin, da wannan damar ta yi amfani ta…
Ƙyasss! Sautin yatsun Sadiq da ta ji a kusa da idonta ne ya dawo da ita zahiri, ta kalle shi da sauri tana wadata fuskarta da murmushi.
“Ka gama shiryawa?”
Ta sa hannunta tana gyara masa wuyan rigar dake jikinsa.
“Eh na gama zan fita”
“Ina za ka je wai?”
Ya kalleta bayan ya gama ɗaura agogo a tsintsinyar hannunsa.
“Zan je na duba Maryam, saboda ina sa ran komawa wurin aiki nan da Monday, ba na so na tafi ba tare da mun haɗu ba”
Wani abu me kama da ƙuli-ƙuli da ya tsaya a maƙoshinta tun daga ranar da aka fara batun auren Maryam har zuwa yau shi ne ta ji ya motsa a wuyanta, shi bai faɗa cikinta ba kuma ta kasa amayoshi ta baki, amma da yake makira ce sai ta yi murmushi, domin duk wannan abin da take a ɓoye take yinsa, ko cacar baki ba su taɓa yi da Maryam ba, domin ko da ace ita za ta so su yi Maryam ba za ta biye mata ba, saboda kowa ya shaideta da hakuri da kawaici.
“Wai haka jikin nata ya yi tsanani?”
Har da su marairaice fuska kamar da gaske.
“Mts! Abin nata fa sai addu’a Bahijja”
“To Allah ya bata lafiya”
Laɓɓanta na furta hakan zuciyarta na amsawa “Ba Amin ba!” yo ita da take sanadin ciwon dan me za ta yi addu’ar zuwan sauƙinsa? Sauƙin da ta san idan ya zo kuma abin kanta zai dawo?.
“Amin, na tafi, sai na dawo”
Da ido ta bi shi har ya ɗauki takalmansa ya fita, yau ko rakiyar da ta saba masa ma ba ta yi ba, zama ta yi a kan gado tana jin nishaɗi har cikin zuciyarta, lallai boka ya cancanci ta ba shi kyauta, sannan dole ta ƙira Fa’iza ta bata labari.
“Ai ke da dawowa gidan nan kuma sai a lahira idan ana zuwa Maryam! Kuma ki jira takardar sakinki na nan tafe”
Ta faɗa kamar tana magana da Maryam ɗin kai tsaye, yayin da take naiman lambar Fa’iza dan ta fesa mata wannan batu…
``````````````
_Ta shin hankali ba a sa maka rana!_
_To fa!_
_Ashe haka aka yi? A gaskiya wannan mata akwai makira! Allah dai ya shiga tsakanin na gari da mugu_
_Shin a ganinku Yata za ta samu abin da take so? Kuna ganin cewa Mama, Zahra, Adali da Saamari za su karɓi wannan tayin na Yata?_
_Ku dai ku ci gaba da bina a sannu, insha Allah yanzu muka fara warwarar, domin ba mu yi komai ba_
_Free pages huɗu ne suka rage, ku hanzarta ku fara biyan kuɗin book a kan naira 400 kacal, domin morewa wannan tafiya, kada ku bari a yi babu ku_
_Za ku iya tura kuɗin ta 5487270431 Salma Isah monie point, sannan ku tura shaidar biyanku ta 08130172702_
#SalmaAhmadIsah
#MiniCandy
#Bahadejia
#KawaZuci
~~~~~~~~~~~~~~~~~~
*KAWA ZUCI*
*©SALMA AHMAD ISAH*
*13*
SA’AD POV.
Takalmansa dake aje kusa da ƙofar fita daga dakinsa ya saka, sannan ya kama handle ya buɗe ƙofar ya fita, yana rufe ƙofar dakinsa ya kula da ƙofar ɗakin Hammad dake buɗe, mamaki ya kama shi, shi dai ya san ko da yaushe ɗakin a kule yake in har ba Hammad ɗin ne a ƙasar ba, ko yana ƙasar ma wani lokacin a gidansa yake kwana. Taku huɗu ne kawai ya kaishi ƙofar ɗakin, domin ɗakunan nasu suna kallon juna ne, amma duk da haka masu ɗakunan ba sa ga maciji.
Hannayensa ya zuba cikin aljihu yana leƙen ɗakin, bai leƙa kansa ba ya ji alamar tafiyar mutum zai fito daga ɗakin, taku biyu ya yi baya still yana kallon ƙofar ɗakin domin ganin wanda zai fito.
“Umar?”
Ya faɗa da murmushi haɗe da mamaki yana kallon saurayin da ya fito daga ɗakin kunnensa kare da waya alamun zai amsa ƙira ko kuma yana kan amsawar. Shi ma Umar ɗin sai ya mayar masa da martanin murmushin yana sauƙe wayar da ya kara a kunnensa, alamun dai kiran da yake son yi bai kai ga shiga ba.
“Na’am Sa’ad!”
Ya miƙa masa hannu suka gaisa.
“Ashe kana ciki?”
“Eh ina ciki, yaushe ka shigo? Sam ban ji sanda ka buɗe ƙofar ba”
“Ban jima da shiga ba, Wani file Hammad ya sa na ɗauka masa, kuma na gama bincike ɗakin gaba ɗaya ban ganshi ba”
Sa’ad ya taɓe bakinsa kaɗan yana jinjina kai, duk da kasancewar Umar shi ne babban abokin Hammad suna shiri sosai da Sa’ad, ba ma shi kaɗai ba, Sa’ad mutum ne me sauƙin kai ga kowa da kuma saurin sabo, ba ya ɗaukan kansa a matsayin kowa, domin ya san shi ba kowa ba ne. Me waɗannan halayen Hammad ne, shi ne ya ɗauko ji da kai irin na sarauta, ba shi da fara’a ga wuyar sha’ani. Wato akwai wani abu mai ban mamaki a cikin lamarin ‘yan uwan biyu, in har za ka samu ɗaya daga cikinsu da ɗabi’a guda, to ba za ka samu ɗayan tattare da ita ba, ta ko ina ba su yi haɗin hallaya ba.
“Ni bari na wuce”
Cewar Sa’ad, ya sake fidda hannunsa daga cikin aljihu a karo na biyu ya miƙawa Umar suka gaisa Umar na faɗin to sai an jima, har ya juya sai kuma ya sake dawowa.
“Dawowa zai yi ne?”
Ya cillawa Umar tambayar, sarai Umar ya gane a kan wa yake magana, dan a cikin su biyun idan za su yi magana a kan junansu ko sunan juna ba
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 10 Chapter of 14