Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
da ke faruwa, sai dai kafin ta amsa masa ya samu amsar tambayar a maganar mahaifiyarsa da take cikin Daga murya. “...Nunca vou acreditar, Abdallah, por que você pegou sua casa em São Paulo e deu para o Pedro? Ele é seu único filho? Então agora que você colocou o nome dele de volta em tudo na casa de Sophia e eu, o que sobrou para nós?!” (… Ba zan taɓa yarda ba Abdallah, a kan me za ka dauki gidanka dake Sao Paulo ka bawa Pedro? Shi kaɗai ne ɗanka? To yanzu da ka mayar da sunansa kan komai na gidan ni da Sophia me ka bar mana?!) Da sauri ya kalli Sophia da ta dafa kafaɗarsa, sai kuma ya kalli hanyar da ɗakunan gidan suke jin takun Ma alamun falon take dosowa, shi kuma Papsi na binta yana mata magana, tsayawa ta yi sanda ta iso falon ta iske Pedro Tsaye shi da Sophia, take ta ƙanƙance idonta tana jifansa da wani irin kallo da ta saba masa na tsana da takaici, kafin muryarta ta fito cikin ɗacin ɓacin rai da baƙin ciki, kaurin dake cikin muryar tata shi zai tabbatar maka da zallar gaskiyar maganar da ta fito tun daga ƙasan zuciyarta. “Não importa o que você faça eu nunca vou te amar Pedro!” (Ko me za ka yi ba zan taɓa sonka ba Pedro!) _____________________ _Har yanzu fa sharar fage ne, ba mu tsunduma cikin labarin ba tukkuna, kafin nan dai ina ƙara tuna muku cewar wannan littafin na kuɗi ne a kan naira 400, maza ku hanzarta ku fara biya tun yanzu, domin kada ku bari ayi wannan tafiyar babu ku_ #SalmaAhmadIsah #Candy #Bahadejia #KawaZuci ~~~~~~~~~~~~~~~ *KAWA ZUCI* *©SALMA AHMAD ISAH* *04* *Unguwar Yalwawa, Dutse, Jigawa state, Nigeria.* ZAHRA POV. “Ruwaida wai har yanzu Zahra ba ta tashi ba?” Cewar Mama sanda ta fito daga ɗakinta ta duba tsakar gidan ba ta ga Zahran ba, bayan Adali da dake cin abinci, da Saama dake wanki sai Ruwaida da ita ma ke cin nata abincin safen, ta san dai a lokaci irin wannan Zahra ba ta zaman ɗaki, dole ka sameta zaune a tsakar gida tana wani aiki. “Mama ba ta daɗe da kwantawa ba ai… Jiya ba ta kwanta da wuri ba” Ruwaida ta bawa Mama amsar. “Ai na san ba za ta hutar da kanta ba har sai ta gama wannan azababben rubutun nata” Cewar Mama tana taɓe baki, ta ja kujera ‘yar tsugunno ta zauna kusa da Ruwaida, yayin da take kallon Saama da Adali dake hirar satar da aka yi lokacin zanga-zanga. “… Shi fa Abba Jaalo ya saci buhun taki ya fi goma, ya je ya taresu a ɗakinsa, yana jiran lafawar ƙura ya je ya siyarsu” “To ai shi tasa satar ƙarama ya yi, ka san Habibu na gidan Malam Adamu? Allah ne kaɗai ya san adadin abin da ya kwasa na ganima, shi kuma Khabiru shi ne ya cinnawa wannan motar wuta ta sakateriya!” “Hmm! Ai yanzu gwamna ya bada umarnin ayi bincike a kamo duk wanda aka kama da kayan gwamnati, ko waɗan da suka lalata kayan gwamnati” Mama ta basu ɗan kaɗan daga abin da ta saurara a labarai. “Ai Wallahi Mama duk abin da za su yi ba su isa sun kama kowa ba, domin wasu ma sun yi hijara sun koma Haɗejia, wasu kuma Kano” Faɗin Saama. “Yo a Haɗejian ma tsira suka yi? Can ɗin ma kamen ake… Shi yasa ranar da aka yi tashin hankalin nan na ce ku kula, kar ku taɓa kayan wani ballantana na gwamnati” “Ai Mama wannan zanga-zangar ba ta kawo ci gaban komai ba face ci baya, har yanzu wasu masu shagunan ba su kai ga fara buɗewa ba, an tafka asarar rai da ta dukiya, ga yanda abincin nan ke hawa, abin dai sai dai kawai mu ce Allah ya mana magani” Cewar Adali da ya gama cin abincinsa, Mama da Saama da a lokacin ya miƙe tsaye yana shanya kayan da wanke a igiya suka amsa da amin. “Wai da ma har yanzu Zahra ba ta gama rubutun nan ba” “Ina fa? Ta dai kusa gamawar, ina jin bai fi izu ɗaya ya rage mata ba” “To ya kamata ta maida hankali dai” “Ruwaida wai ba za ki hanzarta ki gama cin abincin nan ki tafi makaranta ba? Ko yau ɗin ma ba ki da niyyar zuwa?” Adali ya tambayi Ruwaida da tun d'azu ta kasa gama cin abincin dake gabanta saboda kawai yau ma ba ta son zuwa makaranta, shi yasa ta ƙi ta gama da wuri, ta yanda za ta makara sai tace ba za ta je ba saboda kar a mata dukan makara, ta san Saama zai goyi bayanta a kan hakan, shi yasa ma ta yanke wannan shawarar, amma dai yanzu tun da Zazzaɓi sarkin duka ya yi magana ta san cewa shirin nata ya wargaje, dan in ba ta yi wasa ba sai ya sakata kuka kafin ya tisa ƙeyarta a gaba zuwa makarantar. “Ai gara ka tambayeta, dan jiya ma haka yarinyar nan ta yi ƙirmisisi ta ƙi zuwa makaranta saboda iskanci” Kamar Ruwaida za ta yi kuka haka ta kalli Mama, cikin sigar Mama ki rufa mini asiri, abin da take gudun ya faru dai sai da ya faru, Adali ya sakata a gaba yana mata faɗa, faɗan da da kanta take cewa da ace Malam na raye ba su isa sun mata ba. Ta san Mama ba ta mata gatan autanci, mahaifinsu Malam shi ne ke shagwaɓata, tun bayan mutuwarsa kuma ta rasa mai shagwaɓata, sai Saamari, shi ma ba kullum, dan ko yanzu da ake mata faɗan bai saka baki ba, tunowa da mahaifinsu da ta yi yasa ta fara hawayen kewarsa. Ba ta tanka ba har Adali ya gama banbamin faɗan nasa, sannan ta tashi ta bar sauran abincin nata da take jin ya fita ranta. Ta kai sauran ta aje a rumfar da suke girki a gidan, ta dawo ta saka hijabinta ta tafi makarantar duk jikinta a sanyaye. “Allah sarki Ruwaida, Adali ka riƙa binta a hankali, Malam ne ya sangartata haka dole ba za ta dawo yanda muke so tashi ɗaya ba sai a hankali” Cewar Saama cikin tausayawa halin da ƙanwar tasu ke ciki. “A’a fa Saama, rashin jin Ruwaida ya fara yawa, dole a rija taka mata birki” Mama ta ba shi amsa. Kafin wani cikinsu kuma ya sake cewa komai aka rangaɗa sallama a soron gidan, suka amsa su duka dai-dai da lokacin da wata farar mata ta shigo gidan, riƙe take da wata yarinya wadda kammninsu suka nuna cewa yarinyar ‘yarta ce. Yanda yarinyar da aka shigo da ita take rusa kuka yasa dukansu suke binsu da kallo ɗauke da tambaya ɗaya a ransu ta me yake faruwa. “Laraba lafiya?” Mama ta tambaya sanda ta nufi matar tana bin ‘yar tata da kallo. “Ina fa Lafiya Abu? Ruwan zafi ne ya ƙona Mannira!” Ta faɗa tana yaye hannun rigar yarinyar, gurin da ruwan zafin ya zubo mata ya yi jawur, abinka da farin mutum, kuma wurin ya fara alamun tashi. “Subhannalahi… Adali zo ka zuba mata ruwa a wurin” Faɗin Mama da ta kama hannun yarinyar tana dubawa, Adali da Mama ta umarce shi ya nufi randar dake tsakar gidan, ya saka kofi ya ɗebo ruwa a ciki, sannan ya dawo wurin da suke tsaye ya kama hannun yarinyar ya zuba mata a wajen. “Sannu Mannira” Ya mata sannu bayan ya zuba mata ruwan, Mannira ta jinjina kai tana sharar hawaye, Saama ya shimfiɗa musu tabarma, Mama ta zaunar da Mannira Laraba ta zauna kusa da ita suna ta jera mata sannu, a lokacin kuma Zahra da kukan Mannira ya tasheta ta fito daga ɗakinsu tana hamma, dan ba laifi yau tana jin bacci sosai. “Insha Allah ba zai tashi ba tun da har an zuba miki ruwan nan, Saama ka ɗauko roba ka zuba musu ruwan su tafi da shi ana zuba mata a kan ƙunan insha Allah ba zai tashi ba” “To Abu, mun gode sosai” Laraba ta godewa Mama. “Ah haba ai ba komai Laraba, wannan abu ne da Malam ya bar musu gadonsa, kuma ya zama dole garesu su taimakawa al’ummar annabi da baiwar da Allah ya wadatasu da ita domin gode masa” “Haka ne” “Ina kwana Maman Mannira” Zahra ta gaisheta tana zama kusa da su, murmushi kwance kan fuskar Laraba ta amsa, kamar ba ita ce ta shigo hankali tashe ba. “Mama ni zan fita” Cewar Adali yana saka takalmansa. “To a dawo lafiya, Allah ya tsare ya bada sa’a” “Amin… Zahra zo” Ya ƙarashe da ƙiran Zahra tare da nufar hanyar soro, Zahra ta bi shi a baya, a soron gidan nasu inda ɗakinsu yake shi da Saamari ya tsaya, ita ma tsayawar ta yi domin jin abin da zai ce mata. “Kina da indigene ko?” Ita ce tambayar da ya fara cilla mata, ta yi saurin gyaɗa masa kai. “Zamanki hakan nan ba ya min daɗi, dan haka zan naima miki gurin karatu a Poly Dutse...” Cikin wani abu da ya ɗara murna Zahra ta ɗago kai ta kalli yayan nata, bakinta kawai take motsawa tana son cewa wani abu, amma ta kasa, sai dimples ɗinta na ko wani ɓangare dake motsawa tare da motsin bakin nata, domin duk yadda za ta motsa bakinta to sai sun loɓa. “Na-na gode sosai Ya Adali, Allah ya ƙara buɗi” Wani gajeren murmushi ya mata, dan shi ba mutum ne me fara’a ba. “Ba komai Zahra, ki je ki haɗo min indigene ɗin naki da certificate ɗinki na makaranta da kuma result na WAEC ɗinki” Ta jinjina masa kai, ya nufi ƙofar fita tana masa addu’ar Allah ya dawo da shi lafiya, ta dawo gida tana jin kamar ta tashi sama dan farin ciki. Za ta iya cewa bayan rasuwar mahaifinsu ba ta taɓa samun wani giɓi a rayuwarta ba, kuma duk da Allah ya ɗauki ran mahaifinsu lokacin tana kan tasowa ya bar mata ‘yan uwa guda biyu da suke kula da ita tamkar mahaifin nata. Rayuwarta na tafiya a kan dogon miƙaƙƙen layin da bai karkace ba tun daga farkonsa har zuwa inda take a yau, ba ta san ƙarshen layi ba, domin komai zai iya faruwa da ɗan adam a lokacin da bai yi tsammani ba, ita dai har zuwa yanzu da take numfashi a duniya bata taɓa haɗuwa da wani abu da ya girmi ta ɗauke shi ba, kullum cikin fatan kasancewarta a hakan take… ba tare da sanin tarin abubuwan da suke tunkaro rayuwar tata ba, domin taƙi kaɗan ne ya rage tsakaninta da ƙaddarar rayuwarta. Asalin mahaifinsu Malam Rabi’u Sharif mutumin wani ƙauye ne da yake Yobe, wai shi Tulotulo, babban malamin addini ne kuma sharifi wanda ya yi gado tun daga kakkaninsa, yawon kasuwanci ne ya kawo shi Jigawa, har ya haɗu da matarsa Abu, ‘yar asalin garin Haɗejia. Bayan sun yi aure suka koma garin Dutse da zama, inda ya kafa makarantar gargari. Malam Rabi’u ya tara almajirai bila adadin, domin a unguwar da ya zauna babu wanda bai san makarantar Malam Rabi’u Sharifi ba. Ana kawo masa almajirai daga jahohi da-ban-da-ban na sassan Nigeria, Adali shi ne ɗansu na farko, me biye masa kuma Saamari, sai Zahra da auta Ruwaida. Duka cikin yaran Malam Rabi’u babu wanda bai taso da baiwa irin ta mahaifinsu ba, wuta ba ta ƙonasu, kuma sukan bada maganin ƙunan wuta, ko ruwan randar gidansu suka ɗiba suka zubawa mutumin da ya ƙone to da yardar Allah wurin ba zai tashi ba. Hatta Ruwaida ƙarama dake da shekaru goma sha uku ta sauƙe al’kur’ani mai girma, ballantana kuma manyan, shi Adali sau biyu yana rubuta al-kur’ani da ka. Allah ya musu ilimi kamar zuban ruwan sama, abin da ya kawo wargajewar makarantar Malam Rabi’u ita ce rasuwarsa, bayan rasuwarsa gaba ɗaya almajiran makarantar suka kama gabansu. Sannan ‘ya’yansa suka ci gaba da kula da gidan, duk da ba wani kuɗi suke samu ba ba su yarda ƙannensu su yi rashin wani abu da bai fi ƙarfinsu ba. Shi Adali shago ne da shi a kasuwa na siyar da yadika, yayin da Saamari yake aiki a wani gidan shinkafa, duk da sun rasa mahaifinsu ba su daina bada taimakon maganin ƙuna da addu’o’I ba idan mutane sun zo da buƙata, hakan yasa ma ake ƙiran gidan nasu da gidan Sharifai. *Masarautar Dutse* SA’AD POV. Gyaran muryar Galadima Khabir, babban ɗan Takawa kuma ɗan fari a wurin Adda ne ta fara musu iso a falo na biyu dake turakar Adda. Shi ya fara wucewa, sanda bayi da hadiman sashin Adda da suka zube a ƙasa suke ta kwasar gaisuwa suna ta ƙirari. Sa’ad na biye da shi a baya har zuwa cikin falon, Galadima ya zauna a kan sofa, yayin da Sa’ad ya zauna a saman carfet kusa da ƙafafunsa. Jim kaɗan Adda ta shigo falon da suke, cikin girmamawa kowannensu ya gaisheta, ta zauna tana binsu da kallo, domin ta san da batun da suka zo da shi, saboda tun da Sa’ad da Maryam suka dawo daga asibitin da ya kaita bai zo ya ce musu ga takamemen abin da ya faru ba, ita kanta Maryam ɗin da Adda ta tambayeta cewa ta yi ba ta san me likitan ya gayawa Sa’ad ba. “Adda! Sa’ad ya gaya mini komai game da abin da likitan da ya duba Maryam ya gaya masa, ba ni kaɗai ba, hatta Takawa ya san da batun, domin a gabansa Sa’ad ya faɗi komai… Nauyin maganar yasa Sa’ad ya kasa furta miki ita kai tsaye, ya fara sanar da mu domin mu mu sanar da ke” Adda ta kalli Sa’ad da yake kallon wasu vase da aka jera kan kykkyawan center table da aka aje a tsakiyar falon, don shi ba ma su yake kallo ba, amma kuma a jikinsa yake jin kallon da Adda ke binsa da shi, sanin halin da za ta iya shiga yasa ya kasa gaya mata da kansa, duk rashin hankalinsa ya kan iya fahimtar halin da za ta shiga idan har ta ji batun cewa ‘yarta ta kamu da ciwon hauka, shi yasa ya zage ya fara faɗawa Takawa da Galadima, in ya so a cikin su biyun a samu wani ya tunkari Adda da ita kanta Maryam da wannan batun. “Me likitan yace yana damunta?” Adda ta tambaya cikin ƙarfin halin son danne abin da zuciyarta ke raya mata, yo me ma zai kasance yana damun ‘yar tata? Bayan ta san wurin irin likitan da aka kaita ya dubata, ai da ace lafiya ƙalau take tashin farko kawai za a gaya musu cewar ƙwaƙwalwarta lafiya take, amma tun da aka fara mata wannan kewaye-kewayen ta san cewa abin da ake zargi ne ya tabbata. Galadima ya yi gyaran murya tare da zamowa daga kan kujerar da yake kaɗan yana tattara hankalinsa gaba ɗaya kan kalaman da suke hanƙoron fitowa daga bakinsa. “Abin da likitan da ya duba Maryam jiya yace shi ne… akwai alamu na ƙwaƙwalwar Maryam ta taɓu, duk da bai ba da tabbacin hakan ba, yace zai iya kasancewa aikin jinnu ko asiri, amma a nasu ɓangaren za a iya danganta ciwon na Maryam da hauka!” Maraym da Muhibba dake tsaye a can cikin corridor ta inda Galadima, Sa’ad ko Adda ba za su iya ganinsu ba ta yi baya-baya tana jin hajijiya na naiman kayar da ita, Muhibba ta miƙa hannunta za ta riƙota ta kauce hawaye na zubo mata, sannan ta fara ja da baya tana yin hanyar da ɗakinta yake, cike da tausayawa Muhibba ta ƙira sunanta ita ma nata hawayen na zubowa na tausayin ‘yar uwarta. “Ya Maryam!” Ba ta amsa ba ballantana ta tsaya, tana shiga ɗakinta ta kulle ƙofar, sannan ta ɗauki wayarta ta naimo lambar Sadiq mijinta ta aika masa ƙira, sai da ta jera masa ƙira uku ba a ɗauka ba. Zama ta yi a bakin gadonta tana fashewa da kuka. “Dan Allah ka ɗaga wayana Sadiq” Ta faɗa hawaye na zubo mata kamar da aka tanadesu dan wannan ranar kawai, sai a karo na biyar ta ci sa’a ya ɗaga wayar, ba su ko gaisa ba ya birkice yana tambayar abin da yake damunta, jin tana kuka. “Maryam me ya faru? Ko jikin naki ne? Hammad ba ya nan ballantana na ce shi ya ɓata miki rai… me aka miki?” Kanta ta girgiza tana jan numfashi kamar za ta shiɗe dan kuka, akwai matuƙar tashin hankali a cikin lamari irin nata, a ganinta wannan ƙaddarar ta mata nauyin da ba za ta iya ɗauka ba, ta manta da Allah ba ya taɓa ɗorawa rai abin da ba za ta iya ba, kuma abin da ba ta sani ba shi ne, ƙaddararta na ɗaya daga cikin ƙaddarori mafiya sauƙin cinyewa a duniya, domin akwai waɗan da suka fi nata wahala da nauyin ɗauka. “Sadiq! Sadiq me ya sa ba ɗaga ƙirana ba” Ta daure ta faɗa da ƙyar tana shafa wuyanta. “Sanda kika ƙira wayar tana hannun Bahijja (Abokiyar zamanta) ban san me ya sa da ta ga ƙiran naki ta ƙi ɗagawa ba, faɗa mini abin da yake damunki” Silalewa ƙasa ta yi tana riƙe kanta da hannunta ɗaya, ɗayan hannun nata kuma riƙe da wayarta tana kuka sosai. “Jiya mun je asibiti ni da Ya Sa’ad, mun… Mun je wurin likitan ƙwaƙwalwa, ya zaunar da ni ya min tambayoyi game da cutar da take damuna, bayan ya gama yace… wai yace…” “Me yace? Kar ki tabbatar min da abin da nake hasashe yanzu haka?” Cikin ƙunar rai ta jinjin kai tana toshe bakinta. “Sadiq wai yace akwai alamun taɓin hankali a tattare da ni!” ---------------- #SalmaAhmadIsah #Candy #Bahadejia #KawaZuci ~~~~~~~~~~~~~~~ *KAWA ZUCI* *©SALMA AHMAD ISAH* *05* *No. 32 Rue de I’Abreuvoir, 278, Paris, France.* *09:01 na safiya.* HAMMAD POV. Gida ne da ya ƙunshi ɗakunan bacci guda biyar, uku daga ciki na ɗauke da bathrooms, sannan akwai living rooms guda biyu, a cikin ko wanni living room akwai fire place, saboda yanda weather'r sanyi ta zama jiki a garin na Paris. Akwai private garden a gidan wanda yake da outdoor a dining area. Akwai kitchen dai-dai misali, wadda yake haɗe da living room ɗin dake ƙasa, sannan akwai wani sitting area da yake saman gidan, wadda idan kana wurin kai tsaye za ka iya ganin Eiffel Tower. Daga ƙasa kuma akwai babban compound da ya ƙunshi parking lot. A cikin babban bedroom ɗinsa yake kwance saman wani gado mai kyau, yanda ya nutse cikin ɗumi da laushin gadon yasa a kallon farko ba za ka ce akwai mutum a kan gadon ba, kukan dokin da yake ji ne ya yi nasarar farkar da shi daga bacci, maimakon ya tashi sai ya miƙa hannunsa ya ɗauki wani pillow ya toshe kunnuwansa da shi, kuma hakan bai sa ya daina jin kukan dokinn ba, ya san gardamar dokin nasa, yanzu haka masu kula da shi sun kasa control ɗinsa, shi yasa yake ta jin hayaniyarsu a waje. Ba dan baccin ya isheshi ba haka ya tashi zaune yana shafa gajerun twist ɗin dake tsakiyar kansa, dan bayan gashin da akayi wa twist ɗin wanda yake a tsakiya ƙasa da kuma gefe da gefen kan nasa babu gashi an aske. Ƙafafunsa ya sauƙe ƙasa, saitin inda night slippers ɗinsa ke aje, sai da ya yi miƙa sannan ya tashi tsaye yana jan wani siririn tsaki, sanye yake da wasu sport wears masu kauri, saboda sanyin da ake a gari, bai fita daga ɗakin haka ba sai da ya ɗauki jacket ya ƙara a kai, sannan ya fito daga ɗakin. Sai da ya ratsa ta cikin ɗan ƙaramin corridor sannan ya shiga ƙaramin living room ɗin dake sama, wanda ya ƙunshi kofofin ɗakuna uku daga cikin biyar da suke gidan. Daga falon ya buɗe wata ƙofa wadda take manne da stairs, ya sauƙa ƙasa inda babban living room ɗin gidan yake, shi kuma ƙofofi huɗu ne a cikinsa, ɗaya ɗakin Sarah ne, wato maid ɗin dake masa girki da kuma kula da gyaran gida, ɗaya ƙofar ta store ce, ɗayar kuma ta gym, kitchen kuma babu ƙofa, domin marabarsa da falon wata ‘yar gajerar katanga ce, sai kuma ɗaya ɓangaren da galss yake a tsakaninsu. Kai tsaye ya wuce kitchen, inda Sarah ke aikin haɗa abin kari, tana jin shigowarsa ta tsayar da abin da take ta juyo tana risinawa, cikin girmamawa ta masa barka da safiya. “Me yake faruwa a waje ne?” Ya cilla mata tambayar bayan ya amsa mata da ƙyar, fuskar nan kuwa a haɗe kamar hadarin dake gaf da sakin ruwa. “Mik ne ya ƙwace Sir” Kansa ya girgiza dan ya san hakan ne ke faruwa a wajen, a karo na biyu ya sake jan tsaki, sannan ya nufi outdoor dake cikin kitchen ya fita garden ta ƙofar. Tun daga inda yake ya hango mutum ukun da suke da alhakin kula da Mik ɗin wato dokinsa, suna ta famar ƙoƙarin riƙe dokin amma sun kasa, dan gardama ce da shi kamar uban gidansa, in ba shi ya masa magana ba a irin wannan yanayin da yake ciki ba ya jin maganar kowa. “Me yake faruwa ne?” Ya tambaya sanda ya isa wurin, sai da gaba ɗaya suka gaishe shi kafin ɗayan cikinsu ya amsa tambayar tasa. “Tun jiya da likita ya zo duba shi ya ƙi cin abinci, yanzu kuma da na yi ƙoƙarin masa loma (A cusawa doki abinci a bakinsa ta karfi) sai ya birkice ya fara ƙoƙarin guduwa...” Suna ba shi ba’asin yana nufar dokin dake ta huci yana buga kofatonsa a ƙasa, babu ko tsoron illar da farin ingarman dokin zai iya masa ya nufe shi. “Hey! Hey! Kwantar da hankali Mik…” Ya ƙarasa maganar tare da ɗora hannunsa a gefen wuyan dokin, a hankali ya soma shafa wuyan nasa yana kallonsa da ƙananun idanuwansa. Tun dokin na huci har ya dawo dai-dai, a hankali ya kama wuyan dokin ya haye kansa. “Bravo good boy” Ya fada yana shafa kansa. “Ku je ku ci gaba da aiki Machelle” Cewarsa ga masu aikin, suka amsa masa sannan suka bar wurin, Ya daɗe zaune kan dokin yana zagayawa a cikin wadataccen garden ɗin dake kewaye da gidan, har sai da ya gaji dan kansa ya sauƙa, sannan ya ƙira mai kula da shi yace ya maida shi wurin da ake killace shi. Shi kuma ya koma cikin gidan, tsakanin shigarsa ɗakinsa da fara ringing ɗin wayarsa ba ace ga wanda ya riga wani ba. Ko kallon wayar bai yi ba ya nufi jikin wani stand yana cire jacket ɗin da ya saka a saman sport wear'n dake jikinsa, ya rataye jacket ɗin a jiki, sannan ya dawo ya zauna bakin gadonsa, sai a lokacin ya kalli fuskar wayarsa dake ruri a karo na biyu. Hannu ya miƙa ya ɗauki wayar, duk da ya ga cewa Muhibba ce ke inviting ɗinsa voice call through WhatsApp hakan bai sa ya ɗaga kai tsaye ba. Kawai yana riƙe da wayar yana kallon sunan nata kamar mai ƙirga adadin harufan. A wannan karon bayan ƙiran ya katse ba ta sake ƙira ba sai ta tura masa da saƙo, ganin shigowar saƙon yasa ya shiga inbox ɗinta. 'Ya Hammad ka ɗaga wayata, wani abu zan faɗa maka game da ciwon Ya Maryam..' shi ne abin da ta rubuto masa, fuskarsa ya haɗe yana tunani kan me take so ta gaya masa game da Maryam? Tunowa da cewar Maryam ɗin ba ta da lafiya ya ba shi damar ɗaga ƙiran nata da ya sake shigowa wayar tasa. Ya kara wayar a kunnensa bayan ya ɗaga, amma sai ya yi shiru ba tare da yace komai ba. "Ya Hammad ka san me ya faru yau?" Muhibba ta fara faɗi, domin ta san in ba ita ta yi magana ba sarkin jin kan da wuya ya fara magantuwa. Hanmad ya tsinkayi tashin hankali a cikin muryarta, dan haka kai tsaye yace. "Cut the carp! Ta fi zuwa ga gundarin magana" Muryar nan a dake, babu sautin nishaɗi cikinta ko wani abu mai kama da walwala. "Jiya Ya Sa'ad ya kai Ya Maryam asibiti wurin likitan ƙwaƙwalwa..." "What the hell? Uban waye ya ba shi wannan damar?" Ya katseta tun kafin ta ƙarasa, tuni wani baƙin abu ya soma tasowa daga ƙirjinsa zuwa maƙogwaronsa na ɓacin rai. "Ubanmu mana? Ka san dai ba zai yi hakan ba tare da izinin Takawa ba..." "Me likitan yace?" "Ya ce akwai alamun taɓin hankali tattare da ita, Wallahi ba ka ga halin da ta shiga ba sanda ta ji wannan batun..." "Shi kansa Sa'ad ɗin ai ba hankali ne da shi ba, da dan har ya ɗauketa ya kaita wurin wani mahaukacin da shi ma bai san kansa ba, ya shatci magana ya gaya muku za ku yarda! Babu gwaji babu komai? Saboda su suka fi kowa hauka?" Ita dai Muhibba shiru

Chapter 4 of 14