Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
a tare da ni” Ta ƙarashe muryarta a raunane, hawaye kuma na bin kuncinta, Dr ya zari tissue ya miƙa mata, ta karɓa ta share hawayenta da suka ƙi tsayawa. “Ina ji a jikina kamar mutuwa ma zan yi, hatta mijina ya kasa zama da ni saboda wannan damuwar tawa, nan gaba kaɗan kowa zai gudu ya barni ni kaɗai!” “Ki yi haƙuri Maryam… Insha Allah za ki warke” Cewar Dr yana ɗaukan pen ɗin da ya aje. “Za ki iya tafiya, idan kin fita ki turo min ɗan uwanki” “Na gode Dr” Ta miƙe tsaye tana riƙe da wayarta, ta fita daga office ɗin. Sanda ta rufe ƙofar office ɗin bayan ta fita ta hangi Sa’ad tsaye da wata nurse wayarsa a hannunta, yayin da yake mata magana fuskarsa ɗauke da murmushi. Duk da tana cikin wani yanayi lamarin Sa’ad ɗin bai kasa bata dariya ba, shi dai har ya mutu ba zai daina kula ‘yan mata barkatai ba. Shi ne ya kula wanna ya kula waccan, idan aka ce za a zauna lissafa adadin ‘yan matan Sa’ad za a jima ba a gama ba. “Ga shi… sai na jika” Ta miƙa masa wayar tana jifansa da murmushi, Sa’ad ya karɓi wayar yana jifanta da murmushi yace. “Sai an jima” Tana barin wurin Maryam na tsayawa a gabansa. “Wata sabuwar ka yi ne?” Maryam ta tambaya tana kallonsa da murmushi, nan da nan ya sha mur, shi a dole kar ta raina shi. “Har kun gama ne?” Ya cila mata tambayar a maimakon amsa mata tambayar da ta masa, idonta da take jin kwanciyar damshin hawaye ciki ta sake gogewa tana gyaɗa masa kai. “Eh… Yace ka je yana son ganinka” Sa’ad yay shiru yana kallonta. Kafin ya kamo hannunta ya zaunar da ita kan wata kujera dake kusa da office ɗin, yace ta jira shi yanzu zai dawo, ta amsa masa da to. Ya tashi ya shiga office ɗin. “Sa’ad! Ba zan ɓoye maka ba… A zahirin gaskiya alamu sun nuna cewa Maryam na fama da cutar ciwon kwakwalwa, ta wani wurin kuma abin nata ba ya kama da ciwon asibiti… Duk da ni likita ne ba zan kasa ba ku shawara kan ku dage da addu’o’I da kuma naiman taimako ba… Sannan zan ɗorata a kan wasu magunguna, ta riƙa amfani da su mu gani, ba a san a inda za a dace ba…” Sa’ad ya jinjina kansa bayan da Dr ya gama koro masa jawabin, ya rubuta musu wasu magunguna, sannan ya ba shi, ya masa godiya ya fita. Yana fitowa Maryam ta miƙe tana kallonsa. “Me likitan yace?” Saurin girgiza mata kai ya yi. “Mu je gida, daga baya zan miki bayani” Ya karashe yana ɗaukar mata jakarta, sannan ya turata suka yi waje. *Parque do park, Henrique Chamma Avanue 420, Pinheiros, Sao Paulo, Brazil.* Park ɗin na ɗaya daga cikin parks ɗin da ba su cika girma ba a garin Sao Paulo, duk da kasancewarsa a gefen titi hayaniyar ababen hawa da ta mutane ba ta sauya daddaɗan yanayinsa me sanya nutsuwa ba. Zaune yake kan ɗaya daga cikin dogayen bench ɗin da suke a park ɗin, sanye yake cikin dark brown khaki trouser, da hoodie baƙa, babu komai a kansa, hakan yasa kai tsayi za ka iya ganin gashin kansa da yake dark brown color, wanda ya sha askin curly fring. Kalar fatarsa na wani abu tsakanin fari da baƙi, shi bai kai turawa fari ba, kuma ya fi baƙaƙen fata haske, sannan ba irin farin ‘yan Asia ne da shi ba, a taƙaice za a iya kiran kalar fatarsa da light skin. Idanuwansa ba su cika girma ba, kuma ba ƙanana ba ne, abun da ya fi jan hankali a kansu shi ne ƙwayar cikinsu da ta kasance gray color, me ɗison baƙi a tsakiya. Akwai zanen tattoo na rubisk’s cube a gefen wuyansa. Sai kuma wanda yake kan yatsun hannunsa biyar na ɓangaren hagu. A ko wani dan yatsansa akwai harrufan sunansa, a kan babban ɗan yatsansa akwai harafin ‘P’ a ɗan yatsansa manuniya akwai harafin ‘E’ na kusa da shi kuma harafin ‘D’ sai kuma ‘R’ ɗan ƙaramin yatsansa kuma na ɗauke da harafin ‘o’ wato ‘PEDRO’ a jumulce. Gaba ɗaya hankalinsa na kan laptop ɗin dake gabansa, cikin wani irin sauri yatsunsa ke danna ko wani key da zuciyarsa ta basu umarnin dannawa, kuma idonsa na kan screen din, ko kaɗan ba keybord ɗin yake kalla ba, kai ba ka ce ya san keys ɗin da yake dannawa ba. Wani guntun gajeren murmushin gefen baki ya saki, sanda ya ga abinda ya zauna a wurin yana aikin yi na gaf da kammaluwa, hannayensa dake kan keybord ɗin ya sauke tare da ɗagasu sama yana kallon ɗan siririn layin da yake ja a hankali a kan screen ɗin, tare da rubutun ‘loading…’ a ƙasan layin. Sanda layin ya gama kaiwa ƙarshe ya sake sakin wani murmushin mai tarin ma’anonin da bayan mahallicinsa da shi kansa babu wanda ya sani. Sannan ya ɗaga yatsun hannunsa huɗu, ya saka a cikin sumar kansa data kwanto har kan goshinsa, ya jawota gaba sannan ya ciro hannun nasa. Cikin nishaɗin da ya bayyana kan allon fuskarsa ya rufe system ɗin, ya sakata cikin jakar dake aje a gefensa, ya gyara zamansa lokacin da wani abu dake faruwa kusa da shi ya ɗauki hankalinsa. “Beatriz dan Allah ki kaini na yi wasa…’ Faɗin wani yaro da ba zai haura shekaru goma ba yana jan hannun wata budurwa da suke tare da ita, wadda ya kira da Beatriz ɗin ta fizge hannunta da ya riƙe tana faɗin. “Ni yanzu ba ni da lokacin kaika wurin wasa, dan haka ka samu wuri ka zauna a can!” Cikin alamun dake nuna rashin jin daɗin abinda mai kula da shi ke masa yaron ya sunkuyar kansa ƙasa, sannan ya zauna kan bencin da Pedro ke zaune, yayin da ita kuma Beatriz ta nufi wani sashin da ban dake cikin park ɗin, dan ta je ta gana da saurayinta. Pedro da ya bi bayan Beatriz da kallo ya dawo da dubansa kan yaron da har yanzu kansa yake a ƙasa, ya harɗe hannayensa ya kuma kumbura bakinsa alamun dai ya yi fishi. Haka kawai Abin da yaron ya yi sai ya tuna masa da yarintarsa, shi bai cika hulɗa da mutane barkatai ba, babu ruwansa da rayuwar wani, hakan yasa ba kowa ya damu da rayuwasa ba. Amma haka kawai sai ya samu kansa da son kula yaron, matsawa kusa da shi ya yi yana leƙen fuskarsa. “Ola!” (Barka!) Ya daɗi cikin harshen Portugese da shi ne official language da ake magana da shi a ƙasar Brazil. A hankali yaron ya juyo ya kalle shi, sai kuma ya ɗauke kai. Jakarsa ya buɗe ya ɗauki rubik’s cube guda biyu, sannan ya miƙawa yaron guda ɗaya. “Voce pode conectar o cubo de Budki?” (Ka iya haɗa rubki’s cube?) Yaron ya sake kallonsa tare da gyaɗa masa kai. “Voce vai brincar comigo?” (Za ka yi wasa da ni?) “Simh” (Eh) Yaron ya amsa yana karɓar Rubik’s cube ɗin da ya miƙa masa, sannan ya juyo suna fuskantar juna. “Qual e condicao do jogo?” (menene sharaɗin wasan?) “Quem vencer entre nos vai se apresentar primeiro… concorda?” (Duk wanda ya yi nasara a cikinmu shi zai fara gabatar da kansa… ka yarda?) A wannan karon har da murmushinsa yayin da yake gyaɗa masa kai, shi ma Pedro ɗin martanin murmushin ya mayar masa, kafin kuma suka soma wasan, shi kam tsayawa ma ya yi yana kallon yanda ya dage yana son sai ya yi nasara, har abin ya so ba shi dariya, domin da ya so a cikin sakkani zai iya jera duka six faces na Rubik’s cube ɗin, amma saboda yana son yaron ya samu nishaɗi daga wasan sai bai yi hakan ba, ya tsaya jujjuya puzzle ɗin kawai, sai da ya ga ya kusa gama haɗawa tukkuna ya maida hankali ba wai dan ya yi nasara ba, kuma kafin ya gama haɗa nasa yaron ya gama, sannan ya aje shi a tsakiyarsu. “Yehhhh!... Eu ganhei” (Ni ne na yi nasara) “Ahh! Nao consigo me conectar” (Ahh ni kam na kasa haɗawa) Faɗin Pedro fuskarsa na nuna alamun bai ji daɗin rashin nasarar tasa ba. Hakan yasa yaron ya ƙyalƙyale da dariya. “Tun da ka yi nasara ka gabatar min da kanka” “Sunana Luiz…” Ya miƙawa Pedro hannu alamun su gaisa, sai murmushi yake, saboda a cikin ƙasa da mintuna biyar Pedro ya sauya yanayin damuwa da yake ciki zuwa nishaɗi, shi ma hannunsa ya miƙa masa. “Ni kuma BADAR PEDRO ABDALLAH SANTOS” “Kai kam ka ji daɗi kana da surname…” “Kai ba ka da shi ne?” Pedro ya tambaye shi cikin kokwanto. “Ban san babana ba, Mum kawai na sani…” Pedro ya yi shiru kawai yana ƙiyasta shekarun yaron, can kuma ya gyara zamansa yana nuna hanyar da Beatriz ta bi d'azu. “Waccan da kuka zo da ita, ita ce Mum ɗin taka?” Luiz ya girgiza kai. “Ita ce me kula da ni, saboda kullum Mum tana tafiya wurin aiki, sai a bar ni daga ni sai Beatriz a gida, kuma Beatriz ba ta kula da ni sosai, idan nace ta mini abu ba ta mini, ita kuma Mum kullum ba ta nan, ko makaranta Beatriz ce ke kaini, shi yasa bokaina na makaranta ke tsokanata kan ni bani da Baba” Maganarsa ta ƙarshe ta haskowa Pedro wani abu da ya shuɗe a rayuwarsa tsawon shekaru, wani lokaci can baya. _“Mamar Pedro ba ta sonsa, shi yasa ba ta siya masa sabuwar sweater ba…”_ Dariyar da wani abokinsa na makaranta ya yi a lokacin har yanzu ba ta goge a cikin tunaninsa ba. “Za mu iya zama abokai?” Maganar da Luiz ya yi ta jayo shi daga wannan tunanin, sai ya dube shi kamar ma bai san me yace ba, kuma shi ma Luiz ɗin kamar da aka gaya masa cewa bai gane abin da yace ɗin ba sai ya maimata masa. “Na ce za mu iya zama abokai?” Ƙoƙarin ture abinda ke son taso masa ya yi, ya danne shi da murmushin yaƙe yana jinjina kansa. “ƙwarai… manya manyan abokai ma kuwa” Suka sake gaisawa, lokacin kuma wayarsa dake cikin aljihun wandonsa ta soma ruri alamun shigowar ƙira, hannun Luiz ya saki sannan ya ɗauki wayar ya ɗaga ƙiran ya kara wayar a kunnensa. “Pedro ka na ina ne, tun ɗazu nake so na tafi amma Juliana ta hani tafiya saboda ba ka dawo ba, ka yi sauri ka dawo ina so na koma wurin aiki ni ma” “Oh Ibrahim ka yi haƙuri na manta kana jirana, ka tafi kawai dan zan iya ɗaukan lokaci kafin na dawo” Daga cikin wayar muryar da ta yi magana a farko ta sake fitowa cikin harshen hausa. “To sai ka zo” Wayar ya sauƙe ya kalli Luiz da shi ma tun ɗazu yake kallonsa. “Abokina ni zan tafi, fatan za mu sake haɗuwa wata rana” Ya ɗauki jakarsa tare da goyata a bayansa, suka miƙe a tare. “Rubik’s cube ɗinka” Cewar Luiz yana miƙa masa rubik’s cube ɗin. Sai ya kalli Abin sannan ya kalli yaron, ya ɗora hannunsa a kansa. “Ina da su da yawa, dan haka na bar maka wannan, ka ɗauke shi a matsayin kyauta daga sabon abokinka” “Na gode Peter” (wato Pedro a turance) Wani murmushin ya sake sakar masa, kafin ya juya yana ɗaga masa hannu, har ya kusa fita daga park ɗin tunanin rayuwarsa ta baya ne ke farautar nutsuwarsa, duk yadda ya so dannewa ya kasa, musamman da ya ga wani yaro yana wasa da babansa a kusa da hanyar fita, a wannan karon ba zai iya ba, ko ya so ya danne ba zai iya ba… *Shekara ta 2010* *Lencois town, Brazil.* “Badar Pedro Abdallah Santos!” Malamar dake kula da ajinsu ta ƙira sunan lokacin da ta zo kan takardarsa a test ɗin daliban ajin suka yi a safiyar ranar, jin shiru yasa ta sake ƙiran sunan a karo na biyu tana bin fuskokin ɗaliban nata da kallo domin zaƙulo Badar ɗin a cikinsu. Can ta hange shi zaune kan kujerarsa, yayi tagumi da duka hannayensa biyu, idanuwansa a kan wani littafi dake aje kan desk ɗinsa, amma kuma ba nazarin littaffin yake ba, tunani ne cunkushe fal a cikin kansa, tunani yake kan rayuwar da yake gudanarwa tsakanin rayuwa da mutawa, tun da… Dukan desk ɗinsa da aka yi ne ya tsamo shi daga kogin tunanin da ya afka, kansa ya ɗaga ya zubawa Malamar dake tsaye a kansa fararen idanuwansa masu ɗauke da gray ƙwaya, kafin a hankali kuma ya miƙe yana sauƙe kansa ƙasa. “Badar?” Malamar ta ambaci sunan nasa tana ƙare masa kallo, dududu a lokacin bai fi shekaru goma sha takwas ba, amma damuwar da yake ɗawainiya da ita mai shekaru ashirin ma ta masa nauyi. “Maa” Ya amsa da sanyin muryarsa. “Tunanin me kake?” Sai a lokacin ya ɗago kansa ya shiga bin class mate ɗinsa da kallo, waɗan da su ma shi suke kallo, saurin girgiza mata kai ya yi tare da faɗin. “Babu komai Maa” “Idan ba ka son ka faɗa a gaban abokanka za mu iya zuwa office ɗina ka faɗa mini a can…” Bai bari ta gama maganar ba ya karɓe takardar test ɗinsa dake hannunta ya zauna yana ƙara faɗin ba komai. Ganin ba ya son gaya mata yasa ita ma bata takura ba, domin za ta iya cewa ta san wani sashi na damuwar tasa, ba ma ita kaɗai ba, kusan kowa ya san hakan. Matsalar tasa kuma daga gida ta samo asali, Mahaifiyarsa Racquelita ita ce matsalar Pedro a duniya, domin kowa ya shaida cewa Racquelita ba ta son Pedro, ita da bakinta ma ta sha sanar da shi hakan. Mahaifin Pedro Abdallah Santos musulmi ne, duk da kasancewar ƙasarsu ba ta ɗaya daga cikin ƙasashen duniya da musuluncin ya yawaita a cikinsu an shaida tun asali iyayen Abdallah da duka danginsa musulmai ne, lokacin da yana matashi ya haɗu da ƙaddararsa ta soyayya da Recquelita Tylor, wadda ta kasance ‘yar gani kasheni wurin riƙe addininta na Christianity. Tun farkon fara soyayyar tasu aka samu tangarɗa, domin tun kafin su kai ga batun yin aure iyayen Abdallah suka ce ya rabu da Racquelita, don su ba za su bari ya aureta ba, a nata ɓangaren kuwa babu irin wannan matsalar, domin ita bata da kowa sai kakarta Laala, wadda take matuƙar sonta ta yanda za ta iya barinta ta yi duk abin da take so. Duk da iyayen Abdallah sun so datse alaƙarsa da Racquelita tun kafin ta yi girma Abdallah bai bi abin da suka ce ba, ya ci gaba da soyayya da Racquelita a ɓoye, har ta kai ga sun fara shirin yin aure, a nan ne Abdallah ya dawo da maganar sabuwa zuwa ga iyayensa, su ko suka ce har yanzu suna kan bakarsu na ƙin amincewa da Auren Racquelita, duk yadda suka kai ga nuna masa illar abin da yake shirin yi ya kasa gani, soyayya ta masa baƙin fenti a ido har ta kai ga ya kasa zaɓawa kansa abin da ya dace da rayuwarsa. Ganin ya kafe kai da fata yasa iyayensa suka ce matsawar zai auri Racquelita to su za su cire hannunsu a kansa,in har zai auri Racquelita to tabbas zai fita cikin jerin ‘ya’yansu, abinka da wanda ya yi nisan da ba zai ji kira ba, haka yasa ƙafa ya tsallake gidansu da iyayensa da kuma ‘yan uwansa. Ya tafi kai tsaye ga cikar burinsa wato auren Racquelita. An ɗaura auren soyayya na masoyan, yayin da suka ci gaba da zama a garin Lencois, duk da shi Abdallah na tafiya zuwa Sao Paulo, domin a can ne yake aiki a wani banki. Yakan tafi can ya yi kwana hudu a sati ya dawo Lencois ya yi sauran kwanakin. Kamar dai auren ko wasu masoya a farkon auren babu wata matsala da ta ɓullo, har zuwa lokacin da Racquelita ta yi haihuwar farko, ta haifi ‘ya mace, wadda aka yi wa laƙabi da Sophia, shi kuma Abdallah na ƙiranta da Safiyya. Ta inda matsalar ta fara bayyana kanta ke nan, lokacin da Sophia ta fara tasawa sai Racquelita ta ɗauketa su tafi coci tare, sannan ko addu’o’i za ta koya mata sai dai ka ji tana koya mata na addininta. To a nan ne fa Abdallah ya fara damuwa, domin shi yana so ‘ya’yansa su rabauta, dan haka yake burin su taso da addinin gaskiya, ko da ya yi wa Racquelita maganar sai ta nuna ɓacin ranta a kan hakan, ta kuma ƙara da faɗin. “Antes do nosso casamento, não prometemos que os filhos que teremos seguiriam a sua religião” (… Ai kafin aurenmu ba mu yi da kai cewa ‘ya’yan da za mu haifa za su bi addininka ba) Tun da ta yi wannan furucin bai sake mata magana game da wani abu makamancin wannan ba. Ya koma gefe ya zubawa sarautar Allah ido, amma shi dai ya san abin na damunsa a cikin zuciyarsa. Sai da Sophia ta cika shekara huɗu sannan Racquelita ta sake haihuwa, a sa’ilin nan ne ta haifo namiji, mai kamar ubansa, amma kuma kalar fatarsa da kuma kalar idonsa duka na Racquelita ne. domin shi Abdallah fari ne sosai, farin fatarsa irin na turawa ne, haka ma Sophia ta gado farin fatar tasa, shi dai jaririn da ya tashi sai ya ɗauko irin fatar mahaifiyarsa da take wani abu tsakanin fari da baƙi, shi ba za a ƙira shi da farin turawa ba, baƙinsa bai kai na Africans ba, sannan kuma fatarsa ba ja ba ce irin ta ‘yan Asia, kawai dai yana da light skin. Duk soyayyar duniya Racquelita ta ɗauka ta dorawa yaron da ya ci sunan BADAR, Amma ita da Pedro take ƙiransa, hakan yasa yaron ya mallaki sunaye biyu mabanbanta. A wannan karon Abdallah ya ɗauki ɗamarar ɗora Badar a kan hanya mai ɓullewa, idan har ya bari Sophia ta bi hanyar uwarta to ba zai bari Pedro ya kauce hanya ba. Hakan tasa tun ba shi da wayo yake ɗaukansa ya tafi masallaci da shi, ita ma kuma Racquelita a nata ɓangaren in za ta tafi coci to da shi za ta tafi. Duk wani abu da ya shafi addinin Musulunci shi ne abin da Abdallah ya dage kan koyawa yaron, ita ma haka Racquelita ke yi. Shi yasa har zuwa yanzu da ya girma ya san abubuwa mabanbanta dangane da addinan guda biyu. Ta wani ɓangaren ma ya fi sanin Christianity, domin a ƙasar da ya taso mabiya addinin sun fi masu bin Addinin musuluncin yawa, kuma a saninsa bayan mahaifinsa babu wanda ya taɓa zama ya koyar da shi wani abu da ya shafi musulunci, shi yasa a yanzu yake da ƙarancin sani game da addinin. Abin da iyayen nasa ke yi sai ya zama kamar gasa, kowa ta team ɗin da yake, shekarun Pedro na ƙaruwa yana girma dai-dai da girman matsalolinsa. Sai sanda ya fara yin hankali ya tsayar da addini ɗaya wanda zai bi, kuma shi ne addinin musulunci. To ai fa tun daga nan ya shiga jahannamarsa ta duniya, domin tun daga lokacin da ya zaɓi bin hanyar da Abdallah ya dora shi ita kuma Racquelita tace za ka gani, tun daga sannan ya daina jin daɗin zama da mahaifiyar tasa, kyara tsangwama da tsana babu wanda ba ta nuna masa, to da yake yana da mahaifinsa a kusa sai ya aje lamarinta a gefe, tun da mahaifinsa na sonsa matuƙar so. Sai dai yana girma yana ƙara wayo, tun kyarar da mahaifiyarsa ke masa ba ta damunsa har ta zo ta fara damunsa, amma ko da yaushe mahaifinsa cikin nuna masa yake wasu daga cikin sahabbai ma sun fuskanci ƙalubale daga wurin mahaifansu lokacin da suka zaɓi bin turba madaidaiciya, amma daga baya komai ya sauya, to shi ma ya yi haƙuri, komai zai sauya da yardar Allah, amma har kawo yanzu bai ga sauyin ba, kullum cikin tambayar kansa yake shin yaushe sauyin zai zo? “Pedro ka ga sabuwar sweatern da Mamata ta siyo mini jiya” Abokinsa Drake ya faɗa yayin da suke hanyar komawa gida bayan sun dawo daga makaranta, backpack ɗin bayansa ya gyarawa ruƙo yana kallon sweatern da Drake ɗin ke nuna masa. “Ta yi kyau” Kawai yace yana maida hankalinsa kan doguwar hanyar da suke bi, domin gaba ɗaya garin nasu tudu da kwari ne, amma kuma garin na da matuƙar kyau, Lencois ba wani babban gari ba ne, amma irin gine-ginen dake cikinsa suka sa ya zama gari mafi kyawu a yankinsu. Irin fentin da sukewa gine-ginensu shi ke ƙawata garin, domin idan ka yi wa gidanka fenti pink color, makocinka kuma blue zai yi, na gaba da kai kuma yalo, sannan kuma suna da teku, wani abu da ya kara jawowa garin ƙima ke nan. “Kai ina taka sweater'n? Ya kamata a ce an siya maka a gida, saboda ka ga sanyi ya kusa zuwa” Drake ya sake faɗi, kafin Pedro ya kai ga amsa masa ɗaya abokin tafiyar tasu ya yi caraf yace. "Mamar Pedro ba ta sonsa, shi yasa ba ta siya masa sabuwar sweater ba…” Cak ya tsayar da ƙafafunsa, ya juyo ya kalli yaron dake dariya, take wani abu kamar hawaye ya soma kwanciya a saman idonsa, wanda ya sa ƙwayar idonsa ta soma ƙyalli a cikin hasken ranar da suke tsaye, yunƙurawa ya yi zai daki yaron Drake ya riƙe shi, hakan ya bawa wancan ɗin damar guduwa. “Ba ka faɗa Badar, kar ka kula shi” Cewar Drake dake riƙe da shi, fisge riƙon da Drake ɗin ya masa ya yi, sannan ya juya ya soma tafiya da sauri, kira biyu Drake ya masa amma bai amsa ba ballantana ya tsaya, hakan yasa Drake ya girgiza kansa, dan ya san halin abokin nasa idan ransa ya ɓaci, ba zai saurari kowa ba, ciki kuwa har da kansa. Kawai tafiya yake yana jin wani abu na masa ɗaci a wuyansa, ji yake kamar ya cire wuyan nasa gaba daya ya huta, tsabar baƙin cikin abin da yake tunowa, a lokacin kuma wata mata da ta taho da gudu ta bangaje shi ya yi gefe, binta ya yi da kallo lokacin da ta ƙira wani suna, wani suna da har gobe yake da tasiri a rayuwarsa. “JULIANA!” Dubansa ya zarce zuwa kan wata yarinya da ba ta fi shekaru biyar zuwa shida ba a lokacin, tana bin ball ɗin da ta gangara zuwa bakin titi kuma ga ababen hawa sai kai komo suke a kan titin, ganin haka yasa shi ma ya bi matar da gudu, da yake mace da namiji ba ɗaya ba, kuma jikin ma ba ɗaya ba, har sai ya wuceta, yarinyar na gaf da hawa kan titin da wata mota ta taho a ɗari ya samu nasarar janyota. “Juliana?!” Cewar matar da ya lura ita ce mahaifiyar yarinyar tana fisgeta a hannunsa, ta rungume abarta tana haki saboda gudun da ta yi, ga kuma bugun zuciyarta da ya ƙaru saboda tashin hankali, haka kawai uwar da ‘yar suka burge shi, ya riƙe jakarsa dake bayansa yana kallon yanda tashin hankali ya bayyana ƙarara a kan fuskar mahaifiyar dake tunanin rasa ‘yarta, har yana jin ina ma ace wannan ita ce mahaifiyarsa, juyawa ya yi yana shirin tafiya mahaifiyar yarinyar ta gode masa. “Muito obrigado meu filho, você realmente salvou minha vida hoje” (Na gode sosai yaro, hakika yau ka ceci rayuwata) Fasa tafiyar ya yi ya juyo ya kalli uwar dake faɗin ‘yarta ita ce rayuwarta, me ya fi wannan daɗi a duniya? Ya tambayi kansa, wata ƙila wasu na ganin cewa akwai abin da ya fi soyayyar uwa ga ɗanta daɗi, amma shi kam a halin yanzu ya fi buƙatar soyayyar uwa sama da komai. Murmushi kawai ya sakar mata, sannan ya juya ya ci gaba da tafiya, wannan abin da ya gani yanzu ya wanke kaso sittin na damuwarsa. Tun kafin ya ƙarasa ƙofar gidansu ya hangi motar mahaifinsa, daɗi kamar ya kashe shi, domin ya san cewa yau Papsi ɗinsa yana gari, Ma ba ta isa ta masa wani abin ba. Sai dai yana buɗe ‘yar ƙaramar ƙofar shiga gidan murnarsa ta fara komawa ciki, domin tun daga nan yake jiyowa masifar Ma. Ba shi kaɗai ba, hatta Papsi ɗin nasu yanzu ba ya zaman lafiya da ita, duk wani abu da ya shafe shi Ma ba ta sonsa. Jiki a sanyaye ya buɗe ainahin ƙofar shiga gidan, wadda daga zarar ya buɗe za ta sada shi da falon gidan da yake a farkon shigowa, bakinsa ɗauke da sallama ya shiga, yana shiga suka haɗa ido da Sophia dake tsaye a falon, inda take ya nufa yana tambayarta abin

Chapter 3 of 14