tsaye, dan Amina irin mutanen nan ne da ko za a kashesu to sai sun faɗi abin da ya zo ransu. Murmushi ya yi yana zaro hannayensa dake cikin aljihu, sannan ya furta sunan da ya ƙunshi harufa huɗu.
"Guru!"
*CG Police Headquarter, Tobias Histórico Street, São Paulo, São Paulo, Brazil.*
"Ni fa ba zan lamunci wani uzirinku ba, dole ne ku ɗauki mataki a kan wannan lamarin, ba zai iyu ace a matsayinku na jami'an tsaro kun kasa kama mai laifin nan ba!"
Cewar Mr Lucas Maoura, minister'n yankin Lossi dake ƙarƙashin jahar Sao Paulo. A tsawace yake maganar yana buga tebirin dake gabansa, alamun dake nuna ƙwarai Mr Lucas a fusace yake. Ms Luana dake tsallaken tebirin da yake zaune ta kwantar da murya tana kallonsa.
"Ka kwantar da hankali Mr Lucas..."
"Maganar kwantar da hankali ma ba ta taso ba, na baku nan da sati guda ku kamosu a duk inda suke, in ba haka ba duk sai na sa an sauƙeku!"
Yana gama faɗin hakan ya miƙe tsaye a fusace ya fuce fuuu mataimakinsa ya bi shi a baya. Luana ta miƙa hannu ta ɗauki file ɗin binciken satar da aka basu, ta matse takardar a hannunta ƙarfi, kafin ta yi wurgi da file ɗin.
"Damn it!"
Ƙofar ofishin aka ƙwanƙwasa sau biyu, kafin ƙofar ta iyo ciki alamun wanda ya ƙwanƙwasa kofar na shirin shigowa. Rodrigo abokin aikinta ne ya shigo yana kallonta.
"Me yake faruwa?"
"Dole mu gaggauta kama ɓeran nan kafin ya ja mana sanadiyayyar barin mu aiki, Mr Lucas ya fusata sosai, zai iya ɗaukan ko wani mataki a kanmu matsawar ba mu kama shi ba!"
"Kama mutum kamar wannan abu ne mai wahala Luana! A ganina zai fi kyau mu tsame hannunmu daga cikin wannan case ɗin..."
Luana ta juya ta kalle shi.
"Rodrigo da ma kai ba ɗan sanda ba ne?"
"Pardon?"
"Ya za ai saboda wani ƙaramin ɓarawo za ka saduda nan take..."
Ta ɗan yi fasali tana girgiza kanta.
"Ba zan saduda ba sai na kama shi, ko da zai binne kansa a cikin ƙasa sai na haƙo gawarsa"
"Luana?"
Dakatar da shi ta yi ta hanyar ɗaga masa hannu.
"Idan ka san ba za ka taimakeni da wani abin ba kai ka cire hannunka, and I'll handle it myself, I'm not the kind of person who will surrender on the battlefield"
Wayarta dake riƙe a hannunta ta shiga gurzawa a cikin hannunta alamun shigowar ƙira cikin vibration mood. Kallon screen ɗin wayar ta yi, ganin sunan "HotHead" yasa ta furzar da huci dan ta san complain ya ƙira zai mata.
"Za ka iya tafiya Rodrigo"
Ta faɗa ba tare da ta sake kallon wurin da yake ba ta ja kujera, ta zauna sannan ta ɗaga ƙiran, kukansa ne ya fara mata sallama, kafin kuma ƙorafi ya biyo baya.
"Mum! Mum! Beatriz Ta hanani fita waje!"
Muryar ɗanta Luiz ta fito daga cikin wayar da sautin dake nuna cewa kuka yake. Goshinta ta dafe tana girgiza kai.
"Ina Beatriz?"
"Tana kitchen"
"Kai mata wayar zan yi magana da ita"
Ta jira har sanda ta ji ya fara tafiya, a ranta take ƙiyasta tafiyar da yake daga ɗakinsa zuwa kitchen inda yace Beatriz tana ciki. Tana jin sanda ya buɗe ƙofar kitchen ɗin, sannan ya shiga ya bawa Beatriz wayar.
"Beatriz me yasa kika hana shi fita?"
"Sorry Ma! Yau akwai sanyi, shi yasa na ce ya zauna a gida kada ya fita"
Beatriz ta fara da bada haƙuri sannan ta bada uzirinta domin kare kanta.
"Yanzu haka wata biyu ne tsakaninmu da zuwan lokacin sanyi, rabon da ayi sanyi a Sao Paulo tun wattani biyar da suka wuce, a hakan za ki ce ana sanyi?"
"Sorry Ma!"
"Ki bar shi ya fita, sannan dan Allah na roƙeki kada ki bari ya ƙara kawo mini ƙararki! Ku bar ni na ji da ayyukan da suke gabana"
"Sorry Ma!"
Beatriz ba ta gama bada haƙurin ba Luiz ya ƙwace wayar daga hannunta.
"Mum kin min alƙawarin dawowa da wuri yau kafin na yi bacci ko?"
"Eh! Eh na ɗauka, kuma zan cika"
"Na gode Mum bye!"
"B..."
Ƙit! Ya katse ƙiran, ta sauƙe wayar daga kunnenta tana murmushi.
"Bye"
Ta ƙarasa faɗin Bye ɗin da ta yi niyyar faɗa ba ta ƙarasa ba. Wayar ta aje a gefen keyboard ɗin desktop ɗinta, sannan ta gyara zaman keyboard ɗin ta ci gaba da aiki, domin ta riga ta ɗauki alƙawarin sai ta kama wannan ɓarawon kuɗin Mr Lucas ɗin da ya hansu sakat. A zuciyarta ta furta tambayar da ba ta da amsarta 'Ko yana ina a halin yanzu?'
PEDRO POV.
Zaune suke a cikin cocin da za a ɗaura auren Matilda, kamar waɗan da suka ci bashin wani, sassafe Julia ta tashe shi wai sai ya shirya sun tafi cocin saboda kar a barsu a baya. Kamar yadda tace sai ya sai sabbin kaya sai da ta tilasta masa ya siya ɗin, amma gaba ɗaya tun da ya saka kayan yake jinsa a takure, domin ba zai iya cewa ga rana ɗaya da ya taɓa saka suit ba.
A ko da yaushe kayansa masu sauƙin nauyi ne, amma yau an saka shi saka suit, babu abin da ya fi damunsa ma sama da tie ɗin nan da ya ɗaure masa wuya, jinsa yake kamar karen da aka sakawa chain. Ya ja tsaki ya fi cikin kwando, sai kaiwa hannu yake yana son sassauta ɗaurin tie ɗin amma ya kasa, saboda da ma bai iya ɗaurawa ba, hamshaƙiya Juliana ce ta ɗaura masa.
"Julia!"
Ya ambaci sunanta, Julia dake zaune kusa da shi tana shafa kan Coai ta ci uwar kwalliya kamar flower girl ta jiyo ta kalle shi.
"Ki sassauta mini wannan abin, ya takura mini"
Ya faɗa yana kokawa da tie ɗin.
"Wai sai yaushe za ka waye ne?"
Ta aje Caio a gefenta, sannan ta cire hannunsa a kan tie ɗin ta kama za ta sassauta masa. Tsaki ya sake ja yana kallon mutanen da suke shigowa cocin duk domin halartar bikin, ko ina na cocin an ƙawata shi da furrani da kayan ado.
"An zo an aje mutane kamar kayan wanki..."
Rufe bakinsa ke da wuya Juliana ta matse tie ɗin dake wuyansa, zarowa idonsa ya yi yana kallonta tare da riƙe hannunta.
"Julia? Kasheni za ki yi?"
"Waye ya tilasta maka zama a nan? Idan ba ka so ka tashi ka tafi mana"
"Au? Na tashi na tafi?"
"Eh ɗin wa ya damu da kai"
Miƙewa ya yi zai tafi kamar yanda ta ce ta yi saurin riƙo shi tana dariya.
"Wasa nake maka Hard Rock zauna na sassauta maka tie ɗin"
Ya galla mata harara yana komawa ya zauna, ta sassauta masa tie ɗin sannan ta gyara kwalar farar dress shirt ɗin dake ciki, har da su jan gashinsa.
"Yau ka yi kyau"
Ya yi murmushi yana kallonta. Sun shafe sama da minti talatin kafin amarya ta iso, da ma ango da danginsa tuni suka iso cocin. Shigowar amarya da mahaifinta da ya rakota zuwa cikin cocin yasa kowa ya miƙe ana ta musu tafi. Kowa sai kallonsu yake cike da burgewa, shi dai Pedro hankalinsa na kan Juliana da yanayinta ya sauya, kafaɗarsa ya saka ya bigi tata, ta kalle shi, sai a lokacin ma ya lura har da hawaye a kan fuskarta, gira ya ɗage mata tare da ware idonsa alamun me nene?
"Ji nake ina ma ace ni ma zan ga wannan ranar! Ranar aurena, da ace ranar za ta zo da kai ne wanda za ka rakoni tun da kai ne mahaifina a yanzu!"
Ta kai aya wasu hawayen na ɓallo mata.
"Waye yace ba za ki ga ranar aurenki ba?"
Ta ɗaga kai ta kalle shi.
"Ko ba a faɗa ba jikina na bani cewar na kusa mutuwa! Ko yau, ko gobe, yanzu ko an jima da ko wani lokaci mutuwa nake!"
Nan da nan shi ma yanayinsa ya sauya, ya soma kallonta da wani yanayi da ya fi kama da ɓacin rai haɗe da mamaki, a iyaka saninsa bai faɗa mata cewar an ƙayyade mata kwanakin da za ta yi a duniya ba, hatta ciwon da ace yana da halin ɓoye mata zai ɓoye ɗin, sai dai ba shi da ikon hakan, tun da ciwon a jikinta yake.
"Nurse ɗin dake kula da ke ce ta gaya miki hakan?"
Ta girgiza kanta tana goge ƙwalla da bayan hannunta.
"A'a! Ba ita ba ce, a cikin sakamakon gwajin da aka mini na karanta, tun a waccan ranar na san na kusa mutuwa, shi yasa ba na so ka ci gaba da ɓata lokacinka a kaina, ka yi rayuwarka kawai!"
"Julia!"
Ya katseta yana kama kafaɗunta.
"Na taɓa miki alƙawari na kasa cika shi?"
Ta girgiza kai.
"Na miki alƙawarin zan ceci rayuwarki a wannan karon kamar yanda na ceci rayuwarki a baya, zan cika sannan alƙawarin ko da kuwa hakan zai zama dalilin komawata gidan yari a karo na biyu! Mu biyu muka faro rayuwarmu, kuma mu biyu za mu ƙareta! Ba zan bari ki tafi ki bar ni ba"
Kuka ta fashe da shi sannan ta rungume mutumin da ba ta da kamarshi a kaf faɗin duniya, wanda ya zame mata uba, uwa, ɗan uwa, ƙawa kuma abokin rayuwa, komai zai iya yi domin ita, zai saka kansa a haɗari saboda ita, hatta rayuwarsa zai bada saboda ita, kuma duk da hakan ba su haɗa jini ba, babu abin da ya haɗata da shi face tsautsayi, wani tsausayi da ya tarwatsa rayuwarta da tasa a lokaci guda.
"Lokaci ya ƙure Badar"
Ta furta cikin kuka.
"Har yanzu muna da sauran lokaci..."
Ya bata amsa yana rarrashinta, a lokaci guda kuma yana tuna lokaci na farko da ƙaddara ta haɗasu, sai kuma haɗuwarsu ta biyu, wadda bayan ita kuma ba su sake rabuwa ba, kuma ya na ganin kamar ita ce haɗuwarsu ta ƙarshe wadda ba rabuwa, ita kaɗai ce danginsa, shi kaɗai ne ahalinta, rayuwar kowanne a cikinsu ta dogara da ɗaya.
ZAHRA POV.
“Dimple miƙo mini takalmina”
Faɗin Saama da ya shirya cikin kayan da ya saba sakawa idan zai je ball, Zahra dake wanke-wanke ta miƙa hannunta ta dauƙo masa takalman nasa da ya shanya a wurin bayan ya wankesu da rana.
“Ga su”
“Yauwwa Dimple, za ki yi albarka”
Ta yi murmushi mai kama da dariya saboda yanda ya yi maganar cikin raha.
“Idan Mama ta fito ki ce mata na fita, kuma yau muna da wasa, ba lallai na dawo da wuri ba”
“To Ya Saama, a dawo lafiya”
“Allah yasa”
Ya amsa sanda ya nufi zaure. Tana nan tsugunne tana wanke kwanuka Ruwaida ta shigo tana bata labarin tuwon ƙunshin da za su yi ita da ƙawayenta, suna haka kuma Mama ta fito daga ɗakinta, sanye da hijabi hannunta riƙe da carbi alamun dai sallah ta idar.
“Wai har Saama ya tafi?”
“Eh ya fita, yace na faɗa miki yau zai je kallon wasa ba lallai ya dawo da wuri ba”
“To Allah ya tsare”
Mama ta faɗi tana jan wani niƙab da ta gani rataye a jikin igiyar shanya.
“Zahra wannan naki ne?”
Ta ɗaga shi tana tambayar Zahra, Zahra ta kalli niƙab ɗin tana girgiza kai.
“A’a ba nawa ba ne, jiya na bawa Saddiqa aron nawa”
“Ikon Allah, to na waye?”
“Mama mu ga”
Ruwaida ta karɓa tana juya niƙab ɗin.
“Laaa ai na Yatan Dalla ne”
“An yi haka, to wallahi kin ga ni na mance shaf!”
Batun Yata da aka yi ya tunowa Zahra abin da ya wakana tsakanin Mama da Yata a waccan ranar. A waccan ranar tana ƙoƙarin saka hijabinta da ta naɗe a cikin loka wayarta da take amfani da fitilarta ta wurin haska lokar ta suɓuce ta faɗi ƙasa, dai-dai da sanda Mama ke bawa Yata amsa da.
“A’a Yata, a halin yanzu Zahra ƙoƙarin ci gaba da karatunta take, kuma ko ba wannan ba na san yayyenta ba za su lamunci wannan batu ba, dan haka mu bar wannan zancen”
Da ace za a tambayi ra’ayinta a kan maganar da Yata ta zo da ita da za ta ce a’a, domin kuwa duk yadda take tausayin matar ta fi tausayin kanta sama da ita, a ganinta wannan ita kaɗai ce damar da take da ita wadda za ta ciyar da rayuwarta gaba, ba za ta yi fatali da ita ba domin wani kuɗi da za a bata wanda zai ƙare nan ba da jimawa ba. sai dai da dukkan zuciyarta take mata fatan Allah ya bata lafiya, Allah ya bata kafaɗun ɗaukan ƙaddararta.
*Da misalin karfe 10:53 na dare*
"Mama har yanzu Saama bai dawo ba ne?"
Adali da shigowarsa gidan ke nan ya tambayi Mama da ya iske zaune a tsakar gida tana wa Ruwaida firfita, wadda ta yi bacci tun wajejan ƙarfe takwas. Mama ta ɗaga kai ta kalle shi tana amsawa da.
"Bai dawo ba Adali, ni kaina rashin dawowar tasa da wuri ta so ta dameni, amma da yake yau yace wai suna da wasa, shi yasa ma ban damu sosai ba, wata ƙila ya tafi kallon wasan ne!"
Adali dake tsaye ya girgiza kansa.
"A'a, tun ƙarfe goma aka gama wasan, sai dai in akwai inda ya tsaya..."
"Ko yana wurin su Audu ba?"
Cewar Zahra da ta fito daga ɗaki, sanye da hijabi, alamun fita za tai.
"To, Allah masani, amma tun da fita za ki yi sai ki tsaya wurin zaman su Audun ki ga ko yana nan, in ba ya nan kuma sai ki tambayi su Audun"
"To Mama"
Zahra ta amsa sanda ta nufi soro.
"Ina za ta je?"
Adali ya tambaya, Zahra da ta kusa ficewa ta dakata tana amsashi da.
"Siyan siga zan je shagon Ɗan Ƙani"
Kuma ba ta jira ya amsa ba ta sa kai ta fita, sai da ta je ta siyo sigan, kafin ta biya ta ƙofar wani shagon drinks, inda ta san yayan nata na zama tare da abokansa a kan bencina idan yamma ta yi ko da daddare. Amma da ta je sai ta iske iyaka abokansa biyu ne kawai a wurin babu shi, kuma cikin abokan nasa har da Audu, su ma suna ganinta suka miƙe a tare, kamar masu jiran zuwanta. Duk da yake yanzu haka shawara suke na yanda za a yi su tunkari gidansu Saamari da batun cewa 'yan sanda sun kama shi, cikin girmamawa Zahra ta gaishesu, suka amsa ba yabo ba fallasa.
"Ya Audu ka san inda Ya Saama yake?"
Ta jefa musu tambayar bayan sun gaisa, juna suka kalla, kafin Audu ya sake kallonta.
"Umm da ma yanzu muke shirin zuwa gidan naku..."
Idonta ta ƙifta a kansu su biyu tana gyara tsayuwarta, alamun tana sauraronsu.
"Ɗazu da rana 'yan sanda suka kama Saama, a bisa zargin satar mashin lokacin zanga-zanga!"
Zuciyar Zahra ta harba dai-dai da faɗuwar ledar sigan dake hannunta.
---------------------
_Free pages sun kusa ƙarewa, ku hanzarta ku fara biyan naku domin kasancewa ɗaya daga cikin wanda za ayi wanna tafiyar dasu_
_Ku tura ₦400 ta 5487270441 Salma Isah Monie Point, sai ku tura shaidar biyanku ta 08130172702_
#SalmaAhmadIsah
#MiniCandy
#Bahadejia
#KawaZuci
~~~~~~~~~~~~~~~~~~
*KAWA ZUCI*
*©SALMA AHMAD ISAH*
*15*
*Kauyen Kinkin, gabashin Tanzaniya, Afrika.*
AKIRA POV.
Bisa al’ada, yanda ta saba kwana a wajen ƙauyen a duk ranar Asabar hakan ce ta kasance a yau, tun safe ta tashi tana dakun zuwan Nikamba amma shiru, tun tana sa ran zai zo ya kawo mata abincin safe har ta cire rai.
“Ai da ma kwana biyu ya manta da ni, shi yasa ba ya iya kawo mini abinci da wuri”
A fili ta yi maganar, yayin a take laluben ƙashi a cikin ƙasa, tana jin yatsanta ya taɓo wani sisirin ƙashi mai kaifi da ta saba zane da shi ta dauko, sanna ta matsa jikin wata bishiya ta fara zane a jiki, ta cije lebenta na ƙasa kamar yanda ta saba yi a duk sanda ranta ya ɓaci. Zane take a jikin bishiyar amma ba ta san me ta zana ba saboda tsabar yunwar dake nuƙurƙusarta. Da ta ga zaman ba zai kaita ba sai ta tashi tana ta hamma kamar za ta ci babu.
Tafiya ta fara tana ƙara shiga cikin dajin ba tare da sanin inda ta nufa ba, a kan hanya ta ci karo da wani ɗan garinsu yana kiwo, hakan yasa ta tsaya dan ta tambaye shi ko ya ga Nikamba? Duk da ta san ba lallai ya amsa mata ba ko da ya sani.
“Nujjara! Aji ko hin” (Nujjara sannu da aiki)
Kallon arziƙi mutumin bai mata ba ballanata ya bata damar sanin cewa akwai wata hallita mai kamarta a wurin, ba ta saduda ba ta sake faɗin.
“Ka ga Nikamba kuwa?”
Kallon da ya mata a wannan karon ya bata mamaki, dan kallo ya soma binta da shi na mamakin shi ma.
“Ba ki san abin da yake faruwa a ciki gari ba?”
Ya tambaya yana kallonta, kanta ta grigiza, yo ya ma za ai ta sani ɗin? Ita da rabonta da garin yau kwana biyu.
“Nikamba na ɗaya daga cikin matasan da suka shiga gasar farautar bana, kuma yanzu haka ana can a fadar sarki an taru domin yau za su tafi!”
~*~*~*~*~*~*~
"Ya ku jaruman wannan ƙabila ta HADZA! Ku sani cewa wannan daji da za ku shiga farauta cikinsa daji ne da ya gagari iyaye da kakaninku! Domin akwai muggan namin daji masu cutarwa da dama a ciki, idan har ku ka yi nasarar farauto dabbar da sarki ya umarceku, rayuwarku za ta sauya, sauyi irin na har abada, idan har kuma mutum ya yi saken bari mutuwa ta riske shi a can!..."
Cikin dandazon jama'ar ƙauyen, ɗaya daga cikin amintattun sarkin ƙauyen KINKIN yake shelar da babbar murya, yayin da gaba ɗaya jama'ar ƙauyen da ba su fi a ƙirga ba suka taru a fadar sarki, kusan duk shiga iri ɗaya ce a jikinsu, domin kowa ka kalla a cikinsu fatar jikinsa ta rine da jan taɓon da suka saba shafawa a jikkunansu da kuma gashin kansu. Hakan yasa hatta da tufafin da suke sakawa wanda UNICEF da sauran ƙungiyoyin tallafi ke raba musu sun dauɗaɗe a cikin jan taɓon.
Kuma duk da zamani ya sa sun sauya tufafin da suka saba sakawa tun a zamaninsu na baya bai sa sun daina amfani da sauran kayansu na al'ada ba, domin al'adu su ne jigon kafuwar ƙauyen na Kinkin.
Tun da ta fello da gudu daga cikin daji ba ta dakata ba sai da ta fara dosar fadar sarki, kuma tun daga nesa take jiyowa shelar da ake kan farautar da za a tura samarin garin. Tun kafin ta ƙarasa ta hango Nikamba cikin samarin da aka zaɓa, hakan yasa ta ƙara gudun da take.
Lokacin da ta ƙaraso har sarki ya bawa matasan damar tafiya, shewa da iface-ifacen jama'ar ƙauyen ta karu, domin a bisa al'ada wannan ihun nasu alama ce ta nuna murna ko kuka ƙwararawa matasan gwiwa. Tana isa wurin ta nufi Nikamba dake kan gaba, ta riƙo hannunsa ta juyo da shi, hawaye ko tuni suka ɓallo mata.
“Nikamba akwa oonta?” (Nikamba ina za ka je?)
Ta tambaye shi cikin harshen Hadzane.
Nikamba ya yi murmushi yana kallonta, a lokaci guda kuma yana mamakin yanda akai ta san cewa har da shi za a tafi farautar, duk da ya yi ƙoƙarin ɓoye mata hakan, domin ya san ba za ta so tafiyarsa ba.
"Ti sho kaka Akira!" (Farauta zan je Akira!)"
Ya bata amsa a taƙaice, Akira ta girgiza kanta tana ƙara riƙe hannunsa, hawayen dake zubo mata suka ƙara gudun da suke.
"Zalikma Nikamba! Bania shir'ala" (Ban yarda ba Nikamba! Ba zan barka ka tafi ba).
"Akira! Ninahitaji kiwenda!" (Akira! Dole na tafi)
Ya yi maganar yana cire hannunta a kan nasa da ta riƙe, kuka ta saki mai sauti tana zubewa a ƙasa, lokacin da ya juya mata baya ya bi sauran abokan tafiyarsa da suka fara yin nisa, duk da shi ma ransa bai so ya tafi ya bar ƙanwar tasa ba. Sai dai abij da alƙalamin ƙaddara ya zana ya fi ƙarfin ruwan hawaye ya wanke shi.
*Abuja…*
*06:22 na safe.*
SA’AD POV.
_🎶 I realy wanna make things right_
_Cause without you in my my life girl…_
_I’m so lonely, I’m Mr. Lonely_
_I have nobody for my own...🎶_
Waƙar Lonely wadda Akon ya rera yake saurare ta cikin eardots ɗin dake maƙale a kunnensa, gudu yake a hankali yayin da yake kan workout ɗin da ya saba fita a duk safiyar duniya. Jiya ya iso garin Abuja, kuma a yau zai koma bakin aiki, a gabansa Takawa ya kira ogansa ya sanar masa da a jiya zai dawo, kuma zai kama bakin aiki a yau. Ba dan Takawa ya masa haka ba da babu dalilin da zai sa ya koma aiki yau ɗin nan.
Kamar yanda ya saba cin birki a duk sanda ya zo wucewa ta gaban Wakili Motors haka yau ma ya ci birki a wurin, duk da a tsallaken titi yake yana iya kallon masu aikin sharar safe dake share harabar wurin. Waƙar da yake ji ya dakatar ya tsaya a wurin na wasu ‘yan mintuna yana kallon wurin saboda tsabar ƙauna. Can kuma ya girgiza kansa, sannan ya ɗaga shi sama, a fili yace.
“Allah Amin”
Ya juya ya ci gaba da gudun da yake, daga nan inda yake yana iya hango Estate ɗin da Takawa ya sa aka maka masa hayar gida a ciki, domin da kamfanin da gidan babu wata tazara mai tsayi a tsakaninsu, domin duk fitar da zai yi sai ya wuce ta kofar kamfanin, shi yasa yake tunanin wata ƙila da gayya takawa ya masa haka, dan kawai yana ganin kamfanin yana masa ƙwale-le. Amma ba komai, wannan karon ya ɗauki ɗamarar gyarawa, zai ti tuban muzuru, zai gyara halinsa kamar yanda suke so, in yaso in aka ba shi abin da yake so kuma sai abin da suka gani.
Yana daf da isa babban gate na estate ɗin nasu da a ƙalla ya ƙunshi gidaje hamsin ya ji wakar da yake saurare ta tsaya, sannan wayarsa dake cikin aljihun jogger troser ɗinsa ta fara gurzawa, alamun dai ƙira ne ya shigo. Ɗan yatsansa yasa ya taɓa eardots ɗin.
“Dan Allah ka ce mini ba ka dawo ba”
Shi ne abin da aka fara daɗi daga ɗayan ɓangaren bayan ya ɗaga ƙiran, Sa’ad na jin hakan ya san waye, domin ko daga bacci ya tashi ya ji muryar Salis ba zai kasa ganeta ba. Salis abokinsa ne da suke aiki tare a gidan Tvnsu. Ba tare da ya dakata da gudun da yake ba yace.
“Idan na ce maka jiya a Abuja na kwana me za ka yi?”
Yana iya jin dariyar da Salis ya bushe da ita ta cikin wayar.
“Duk yadda aka yi na san Takawa ne da wannan aikin”
“Kai da ka sani”
Ya amsa dai-dai lokacin da ya iso babban gate, ɗaya daga cikin masu gadi biyun dake zaune ya tashi ya buɗe masa yana masa barka da safiya, dan sanda ya fita ɗayan ne kawai a wurin.
“Ba ni labarin yanda aka yi”
“Ka bari sai na shigo office tukkuna”
“Lallai Takawa ba da wasa yake ba wannan karon… Sa’ad? Wai kai ne za ka shigo station daga dawowarka? Da alama yau za ayi ruwa har da ƙanƙara”
“Jeez!”
Ya furta yana murmushi lokacin da ya nufi wata ƙofa ya buɗe yana amsawa da.
“Sai anjima Salis, idan na shigo sai mu ci gaba da magana”
“See you then”
“Bye”
Daga haka wayar tasu ta ƙare. Stairs ya nufa ya fara takawa, a hawa na biyu ya tsaya, inda gidansa yake. Ya sa key ya buɗe ƙofar gidan ya shiga. Gidan ba wani babba ba ne, ginin ɗakuna biyu da falo da kuma kitchen ne, a cikin ko wani ɗaki akwai barthroom, falon gidan babu wani tarkace, haka kitchen ɗin gidan da za ka iya ganinsa daga falon, domin a hade suke, wanu dan dogon table ne kawai ya rabasu, wanda ya kasance shi ne dining table. Duba da kujeru huɗun da yake zagaye da su, biyu daga cikin falon biyu daga cikin kitchen.
A falo ya zauna ya cire sneakers ɗin dake ƙafarsa. Kafin ya miƙe ya shiga ɗakin da yake kwana a ciki, kamar dai falon, shi ma dakin babu wasu tarkace, bayan gado, wardrobe, mirror babu komai, sai bookshelf ɗinsa cike da litattafai, kasancewarsa mutum me yawan son karance-karance.
A kan gado ya aje wayarsa, eardots da kuma I watch ɗin da ya cire a hannunsa, kai tsaye bayi ya shiga ya yo wanka, ya fito ya sauya tufafi zuwa wani yadi brown color, kasancewar ya mallaki farar fata sai kalar fatar jikinsa da ta yadin suka haɗu suka bada wata kala mai kyau. Babu aikin komai a jikin rigar kayan, amma duk da haka kayan sun masa kyau, da ma can shi yana son sanya tufafin gargajiyar Malam Bahaushe sama da ƙananan kaya. Hammad ne bai damu da ruƙo da al’adu ba, domin idan ka gan shi ma ba za ka ce bahaushe ba ne.
Sumarsa ya taje sannan ya fesa turare, ya saka hula a kansa kana ya dawo wurin da ya aje kayansa ya
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 12 Chapter of 14