dauki wayarsa da agogon kaɗai, ya bar eardots din a wurin domin ba ya buƙatarsu a ayanzu.
A falo ya saka wasu takalman, sannan ya cire system ɗinsa dake chaji a falon, ya sakata a cikin jaka ya kashe duk wani kayan wuta na gidan, ya soma shirin fita ba tare da ya karya ba. Shi zai iya cewa ma tun da ya tare a gidan bai taɓa girka ko da pasta a kitchen ɗin gidan ba. Hana ƙarya dai ya san yakan dafa tea ko ruwan zafi, duka ci ukun nan da dan adam ke yi a rana abincin waje yake ci, ba kuma dan bai iya girkin ba, sai dan ba shi da niyyar yin girkin.
“Sa’adu ashe an dawo?”
Ya ji muryar maƙocinsa a bayansa lokacin da yake kulle kofar gidan, da murmushi ya juyo ya kalli Malam, kamilin magidancin da kowa yake girmamawa a estate ɗin. Domin Malam mutumin arziki ne, ga shi kuma malami, domin shi ne ke jansu salla a masallacin dake cikin estate ɗin nasu. Hannu ya miƙawa Malam Adamu suka gaisa.
“Na dawo jiya Malam, da yake shigowar dare na yi, ɗazu da asuba ma kuma na je masallaci, ba ka lura da ni ba ne”
“Masha Allah! Aikin za a tafi?”
“Eh Malam”
“To Allah ya yi jagora, Allah ya taimaka”
Ya amsa da Amin yana kallon Malam da ya juya ya nufi ƙofar gidansa dake kusa da nasa gidan. A gurguje ya sauka ƙasa, zuwa lokacin gari ya gama wayewa, mutanen estate ɗin duka sun fara fitowa kowa na ƙoƙarin tafiya wurin naiman abincinsa, wasu kuma na shirin tafiya makaranta, tsayuwar da yake domin gaisawa da mutane yasa bai isa parking space inda motarsa take da wuri ba. Yana isa wurin ya buɗe motarsa da ya sa aka kaita aka wanketa a jiya, ya shiga ciki tare da aje jakar system ɗinsa a kan kujerar me zaman banza.
*KG News TV station, Abuja.*
*08:29 na safe.*
Sai ƙarfe takwas da rabi saura ya samu ƙarasawa wurin aikinsa, a wurin aje motoci ya aje tasa motar, ya fito yana riƙe da ledar take-away ɗin da ya yi a hanyarsa ta zuwa, yayin da jakar system ɗinsa ke rataye a kafaɗarsa. Fitowarsa daga motar ta yi dai-dai da sanda motar Salis ta iso wurin, hakan yasa ya fasa wucewa ya tsaya yana jiran ya dai-daita parking ya fito. Ai ko yana fitowa ya gan shi ya fara sheƙa dariya.
“Ikon Allah! Sa’ad?”
Cewar Salis cike da zolaya yana binsa da kallo kamar ya ga sabon mutum, Sa’ad ya sha mur yana faɗin.
“Ya aka yi?”
“Wallahi yau na kasa cinye mamakina, wai kai ne ka zo office ƙarfe takwas da rabi? Mutumin da ba ya zuwa office sai goma saura? It’s Really unlike you”
Sa’ad ya girgiza kansa yana naima musu shiriya shi da Salis ɗin, sannan ya nufi main ginin station ɗin, suna hira da Salis. Kowa ya ga Sa’ad ya zo office a lokaci irin wannan sai ya yi mamaki, sannan su dai sun san hutun da ya ɗauka bai ƙare ba, abin sai ya musu wani iri. Suna isa inda tables ɗinsu suke a cikin na sauran ma’aikata kowa ya zauna a kan nasa table ɗin, duk da tables ɗin nasu na kusa da juna. Sai da Sa’ad ya gama gaisawa da sauran abokan aikinsu sannan ya fito da abincin da ya yi zo da shi wanda dake cikin leda yana ma Salis tayi.
“Wa? An gaya maka kowa irinka ne da zai fito daga gida ba tare da ya ci abinci ba”
Salis ya ba shi amsar, kafaɗunsa ya ɗaga yana faɗin kanka ake ji, ya buɗe robar da nufin zai fara ci telephone ɗin dake kan tebirinsa ta fara ringi. Ba ya buƙatar a gaya masa waye me kiran, dan haka ya aje murfin robar da ya buɗe ya ɗaga wayar tare da karawa a kunnensa.
“Sa’ad ka zo office ina son ganinka”
Ana gama faɗin hakan daga ɗayan ɓangaren aka katse ƙiran, maida telephone ɗin yay ya aje yana jin kamar ya yi me dan takaici, shike nan kuma jin daɗinsa ya ƙare tun da ya saka ƙafarsa a office ɗin, ya san ogansa ba zai taɓa raga masa ba, tun da ya samu goyon baya daga wurin Takawa.
Ba yadda ya iya haka ya miƙe ya nufi office ɗin shugaban nasu dake wata kusurwa, sai da ya ƙwanƙwasa aka ba shi izini kafin ya buɗe ƙofar ya shiga, ya nufi kujera da nufin zama ogan ya katse shi da faɗin.
“Na ba ka izinin zama ne?”
Sai ya koma gefe ya tsaya yana girgiza kansa, Shugaban nasu ya ƙare masa kallo sama da ƙasa sanda yake gaida shi.
“Ina staff ID ɗinka?”
Sai ya taɓa kirjinsa ya ji wayam, sai a lokacin ya tuna da ya manta shi a gida.
“Na manta shi a gida Sir”
Oga ya girgiza kansa yana kallonsa.
“To gobe ka tabbatar ka zo da shi”
“In sha Allah”
“A cikin takardunka na aiki na ga cewar kana jin yaren Swahili ko?”
Sa’ad ya ɗaga kansa ya kalle shi yana jinjina shi a hankali.
“Eh sir, ina jin Swahili, saboda a South Africa na yi degree'na na farko”
“Shi kuma na biyun fa?”
Tambayar ta taho masa kai tsaye.
“A Canada”
Ya amsa tashi ɗaya.
“Mm dole ka ce ka fi ƙarfin aiki a gidan TV kamar wannan”
Sa’ad ya yi shiru, domin ya san da ya yi maganar ne da manufa biyu. Oga ya gyara zama bisa kan kujerarsa, sannan ya furta asalin mafarin ƙaddarar mutane biyu lokaci guda, ba tare da sanin girman ƙaddarar ba, kalaman ba su da tsayi sosai, amma kuma tasirinsu a cikin rayuwar mutanen biyu kan iya sauya duhu ya koma haske.
“Any way, sabon aikin ɗaukan rahoto ne da za mu turaku Tanzania kai da Salis!”
“Cikin Tanzania Sir?”
Ya dawo masa da tambayar ba tare da sanin irin amsar da za ta biyo baya ba, amsar da za ta shafi gobansa da ta wasu.
“A’a, ƙauyen Kin-kin dake gabashin Tanzania za ku tafi, domin haɗa mana rahoto a kan ƙabilar Hadzabe dake rayuwa a cikin ƙauyen”
Tsabar shock Sa’ad bai san sanda bakinsa ya suɓuce ba har ya furta.
“What the hell?!”
--------
_ƙaƙaƙara ƙaƙa!_
_Wannan fa shi ake ƙira da ana dara ga dare ya yi_
_SALMANIANS! Shin kun hango abin da na hango?_
_To kada ku manta dai page ɗaya ya rage mu kammala free pages, domin kasancewa ɗaya daga cikin Wanda za ayi tafiyar dasu za ku biya naira 400 kacal, ku tura kuɗin ta 5487270431 Salma Isah Monie Point, sannan ku tura shaidar biyanku zuwa ga 08130172702_
~~~~~~~~~~~~
#SalmaAhmadIsah
#MiniCandy
#Bahadejia
#KawaZuci
~~~~~~~~~~~~~~~~~~
*KAWA ZUCI*
*©SALMA AHMAD ISAH*
*Last free chapter*
*16*
*Dutse Divisional Police Headquater.*
“Ka ce kai ne yayan Saamari Rabi’u ko?”
Wani siririn baƙin dan sanda ya faɗi yana duban Adali dake tsaye a jikin kantar ‘yansandan, haƙiƙa jiya sun ga tashin hankalin da ba shi da kama. Idan ka ɗauke Ruwaida babu wanda ya rintsa a gidan, hakan yasa da sanyin safiya ya taho police station ɗin da suka samu labarin an tsare Saama da Sayyid.
“Eh Yallaɓai, Adali Rabi’u”
“To jiya muka damƙe ƙaninka sakamakon kama shi da laifin satar mashin lokacin da aka yi zanga-zanga a garin nan”
Adali ya girgiza kansa.
“Tabbas mun fita zanga-zanga tare da shi, amma Wallahil azim Yallaɓai zan iya rantse maka da Allah kan Saama bai saci mashin ɗin kowa ba”
“Ƙarya za mu yi masa ke nan?”
Ya sake girgiza kansa.
“A’a Yallaɓai, ba haka nake nufi ba, ni dai yanzu ku mini alfarma ɗaya, ina so ku bani damar ganinsa, ina so na yi magana da shi”
Da farko kamar ba za su yarda ba, sai da ya yi ta musu magiya kafin wanda yake shugaba a wurin yasa aka fito da Saama daga cell. Kwanansa ɗaya kawai a wurin, amma gaba ɗaya an sauya masa hallita, kamar ba shi ba. Dama suka ba shi ya shiga bayan kantar suka zauna tare da ɗan uwansa yana kallon yanda ya zama kamar ba shi ba, shi kuma Saama ya ƙi yarda su haɗa ido.
“Saama? Me ya faru wannan abin ya ritsa da kai?”
Saama ya yi shiru kansa a ƙasa.
“Ba za ka amsa mini ba?”
Ya girgiza kansa.
“Ina so ka gaya mini abin da ya faru dalla-dalla, idan ka ɓoye mini wani abin ka sani cewa babu yanda za ai na iya kuɓutar da kai daga nan”
Saama ya kuma yin shiru, can ya ɗaga kansa ya kalli Adali da idanuwansa da suka ɗashe, suka zurma ciki kaɗan alamun yunwa ta ci ta cinye.
“Rannan ina gida Sayyid ya kirani yace na zo yana son ganina, da na je sai na gan shi da mashin, yana ƙoƙarin yi mini bayani game da yanda ya samu mashin ɗin na ƙi saurararsa, na karɓi mashin ɗin na tafi kasuwa da shi domin siyowa Mama kayan miya, da na dawo na naime shi na ba shi mashin ɗin, a lokacin yake gaya mini cewar mashin ɗin ya same shi ne a matsayin ganimar zanga-zanga. Ga shi yanzu kuma ana kamen wanda suka yi ɓarna lokacin zanga-zangar, shi ne yake naiman shawarata ya za ai da mashin ɗin? A lokacin na ce masa ni ba ruwana, ya san yanda zai yi da mashin ɗin tun da ba ni na aike shi ya ɗauko kayan satar ba, har ga Allah lokacin da na hau mashin ɗin ma na san na sata ne, kawai na karɓa na hau ne saboda ba na son zuwa kasuwa a ƙafa lokacin… Tun daga ranar ba mu sake haɗuwa da shi ba, jiya kuma bayan na dawo daga gidan shinkafa ina tafe a hanya motar ‘yan sanda ta tsaya a gabana, ‘yan sanda biyu suka fito daga ciki suka kamani, sai da suka kawoni nan suka faɗa mini abin da ake zargina da shi na satar mashin ɗin mai gadin sakateriya da aka ƙona a waccan ranar da aka yi zanga-zanga. Da na ƙaryata zargin da ake mini sai suka rufeni da duka, daga bisani kuma suka kira mai mashin ɗin ya zo, ya nuna yace da idonsa ya ganni a kan mashin ɗin a ranar da na je kasuwa… Haka suka ci gaba da dukana kan sai na faɗi ina mashin ɗin yake, daga ƙarshe na faɗa musu ainahin abin da na sani, sannan na gaya musu inda za su iya samun Sayyid, shi ma a jiyan suka kamo shi, kuma da aka tambaye shi buɗar bakinsa sai yace tare da shi muka siyar mashin ɗin, kuma tare muka raba kuɗin ni da shi, bayan rabona da shi tun ranar da na bashi mashin ɗin! Wallahi Adali ban san komai ba, ko nera biyar ban ci a kuɗin mashin ɗin nan ba, na san kuskurena ɗaya shi ne hawa mashin ɗin da na san na sata ne, kuma na yi nadamar hakan!”
Adali ya rasa me zai ce, domin bai san me zai ce ɗin ba, a yanda abin ya faru dole a ɗora laifin satar a kan Saama, tun da shi aka gani a kan mashin ba Sayyid ba, dan haka babu mai fitar da shi idan har ba Sayyid ne ya buɗi baki ya faɗi gaskiya ba, ajiyar zuciya ya yi sannan yace.
“Na ji daɗi da ka gane kuskurenka, kuma insha Allah zan san yanda zan yi case ɗin nan ya mutu kafin ya kai State CID”
Saama bai sake cewa komai ba har Adali ya ce zai tafi, bai bar cikin division ɗin ba sai da suka tsaida magana kan zai dawo idan aka ƙira mai mashin ɗin. Ya fita gaba ɗaya ransa ba daɗi, domin bai san me zai je ya faɗawa Mama dake cikin tashin hankali ba.
“Adali!”
Ya ji an ambaci sunansa, da sauri ya juya duk da yana cikin yanayi mara daɗi bai kasa murmushin ganin abokinsa Musa ba, hannu ya miƙa masa suka gaisa.
“Gaba ɗaya ka ɓuya ba a ganinka ko a gari”
“Kasuwa ta ɓoyemu dole mu yi wuyar gani”
“Masha Allah, ya batun naiman aikin Civil Defence da kake? Fatan an dace?”
Adali ya girgiza kansa.
“Har yanzu dai, amma muna sa ran dacewa a wannan ɗaukan da za ayi”
“To Allah ya bada sa’a, lafiya na ganka a nan?”
Sai ya ɗaga kai ya kalli ginin division ɗin yana furta.
“A’a, ƙanina Saama aka kama da laifin satar mashin”
“Subhannallahi, ko su ne wanda aka kama jiya?”
Ya gyaɗa kansa.
“A zahiri ma dai ba shi ne ya saci mashin ɗin ba, kuskurensa ɗaya shi ne hawa mashin ɗin da ya yi ya shiga gari bayan ya san mashin ɗin na sata ne, kuma hakan ya. sa abin ya shafe shi, domin abokinsa da ya saci mashin ɗin yace tare suka saci mashin ɗin kuma tare suka siyar da shi!”
“Abu bai yi daɗi ba…”
Musa ya ɗan yi fasali yana kallon harabar division ɗin, sannan ya ƙara matsawa kusa da Adali ya yi ƙasa da murya kamar munafiki.
“Na baka wata shawara Adali?”
Adali ya gyaɗa kai da sauri, shi ko yake naiman shawara, duk shawarar da za ta fitar da ƙaninsa daga cikin wannan zargin sharrin naimanta yake.
“Duk abin da ka san za ka yi ka yi domin a kashe case ɗin nan a cikin division ɗin nan, domin idan har kuka bari aka sauƙesu aka kaisu state CID wallahi abin ba zai yi kyau ba, saboda ba za a tuhumesu da laifin satar mashin kawai ba, sunansu za a kai a matsayin wanda suka yi ƙone-ƙone lokacin zanga-zanga, idan suka tafi kuma ba lallai ku sake ganinsu ba… Ni ɗaya daga cikinsu ne, na san abin da za su iya yi!”..
*~*~*~*
*Lencois town, Brazil.*
Tun bayan rasuwar Abdallah Badar ya fara haɗuwa da ƙalubale fiye da wanda ya saba samu a baya daga wurin Recquelita, ashe ma a baya ba wahala yake sha ba! tun da lokacin Abdallah yana raye yana tare masa wasu abubuwan, kuma albarkacin ganin idonsa Recquelita ba ta iya masa wani abin. Amma yanzu da Abdallah ya kau duk wata shara da za ta kwaso a kansa take zubawa, azaba babu kalar wadda ba ta masa, kuma tun lokacin ta haramta masa cin abincin gidanta.
A kullum ƙara tsanarsa take, yayin da shi ma yake jin tsanarta na gina kanta a cikin zuciyarsa, duk kuwa da yanda yake yaƙi da hakan, lamarin da ya ƙara cusa tsanar Recquelita a zuciyar Badar shi ne fara bin wasu samarin da ta yi bayan rasuwar Abdallah. Har bayan wata ɗaya da rasuwar Abdallah Pedro ya kasa yarda da cewa mahaifinsa ya tafi ya barsu, ya kasa karɓar hakan, a duk sanda zai dawo daga makaranta a ranakun Juma’a gani yake idan ya dawo zai iske shi a gida, ya kasa mantawa, ya kasa karɓar mutuwar mahaifin nasa. A gefe guda kuma tsana me karfi ce take ƙulluwa a tsakaninsa da Recquelita.
Abubuwan da take masa yasa ya fanɗare, ya daina tsoronta har ta kai ga yana iya maida mata martani a duk sanda za ta ce ta tsane shi, a ranar farko da ta fara cewa ta tsane shi ya maida mata martani da same thing da ta faɗa yi ta yi kamar za ta raba shi da ransa, dan duka ta masa ba na wasa ba, da ƙyar Sophia ta ƙwace shi a hannunta, kuma duk dukan da ta masa bakinsa bai mutu ba, ya ci gaba da faɗa mata cewar ya tsaneta. Ranar a gidan ba su yi bacci ba, saboda mumunan dukan da ta masa har kwantar da shi ya yi, ya samu raunika a jikinsa sosai, wanda har kwanan gobe akwai sauran tabon wasu a jikinsa, musanmman shatin bulalar da ta shimfiɗa masa a bayansa.
Sai da aka shafe sama da wata ana shari’a a kan case ɗin bai mutu ba, domin Marcel ne ya maka Recquelita a kotu a bisa zargin cin zarafin ɗan adam. Bayan case ɗin ya mutu ma yaƙin bai ƙare ba, haka rayuwarsu ta ci gaba da tafiya a gurɓace, uwa ta tsani ɗanta shi ma kuma ɗan ya tsani uwarsa. Ikon Allah ne kawai ya ci gaba da rayar da Pedro bai mutu ba, domin duk azabar da Recquelita ke ba shi ba ta sa ya mutu ba. Idan ta hana shi abinci sai ya tafi wurin Laala ta ba shi, idan ta dake shi sai ya je ya haɗata da Marcel.
Rayuwa ta ci gaba da garawa, kwanaki suna ta gudu yayin da a gefe guda kuma aka ci gaba da sanarwa a kan tsammanin girgizar ƙasa a garin Lencois a ko wani lokaci, tsammanin hakan bai sa jama’ar garin sun dakatar da al’amuransu na yau da kullum ba, domin gwamnati tace za ta san yanda za ta yi wurin ganin an dakatar da girgizar ƙasar. Sai dai duk wayon ɗan Adam, duk dabararsa bai isa tsalleke ƙaddararsa ba… domin jama’ar garin ba su taɓa hasaso ranar 12 ga watan Janairu a cikin tarihin rayuwarsu ba, har sai da ranar ta zo musu da abubuwa masu girman da ba za su taɓa gogewa a tarihin jama’ar garin ba.
Ranar 12 ga watan Janairu…
*Present Day.*
*Sao Paulo, Brazil.*
PEDRO POV.
Ƙararrawar ƙofar shagon da ya fito bayan ya siyo grapes ta kaɗa dai-dai da sanda ya rufe kofar, grapes ɗin dake cikin wata container mai kyau ya juya a hannunsa yana hasaso farin cikin da Juliana za ta yi idan ya kai mata su, dan ita ya siya, saboda ya san yanda take sonsu sosai. Jakar dake goye a bayansa ya gyara lokacin da ya nufi Parque do park, domin da ma can ya nufa, ganin shagon saida kayan marmarin dake bakin hanya yasa ya tsaya ya sai mata grapes.
Tun shigarsa park ɗin ya lura yau da akwai cikowar jama’a a wurin, dan haka ya nufi can gefe inda ya lura da rangwamen mutane, bai kai ga zama ba ya hangi abokinsa Luiz tsaye da wata mata dake sanye da suit, duk da ta ba shi ba ya ya lura da ita ce mahaifiyar Luiz ɗin, duba da yanda yake ta zuba mata kukan sangarta yana jan hannunta. Abin sai ya burge shi, ya yi murmushi yana naɗe hannunsa tare da ci gaba da kallonsu, domin shi a tasa yarintar bai samu irin wannan gatan ba.
“Mum please”
Luana ta girgiza kai yayin da Luiz ke mata magiya.
“Ba za ka sha ice-cream ba Luiz, period!”
Fuska ya kwaɓe yana shirin yin kuka kamar da aka ce ya kalli bayan mahaifiyarsa ya hangi Pedro tsaye a wurin yana murmushi, take kukan da yake son yi a koma murmushi.
“Peter? Mum kin ga abokina Peter”
Luana ta juya domin ganin Pedro ɗin da babu ranar banza da za ta fito ta faɗi ba tare da Luiz ya bata labarinsa ba, abokinsa da suka haɗu a Parque do park, wanda ya ba shi kyautar Rubik’s cube. Kyakkyawan brasilian ɗin matashi ta gani tsaye a bayanta, sanye da men’s cargo troser indigo color, da farar shirt, daga nan inda take za ta iya cewa dogo ne, kuma ba fari ba ne domin bai kai su fari ba, duk da a ƙasarsu akwai banbancin launin fata da suke da su, hatta masu baƙi irin na Africans za ka iya samu a Brazil. Ta ga tattoo a yatsun hannunsa na hagu, sannan ta ga na gefen wuyansa, hatta kalar ƙwayar idonsa ta hango. Ba ta san sanda Liuz ya ruga wurinsa da gudu ba, sai ganinsa ta yi tsaye kusa da wanda ya ƙira da Peter, wato Pedro.
Luana na yi wa Pedro kallon nazari shi kuma da na mamaki ya shiga jifanta, kafin ta juyo nishaɗin ganin wani abu ne a fuskarsa, amma yana kallonta mamaki ya fito ɓaro-ɓaro a kan fuskarsa, Luiz dake masa magana ya kalla, sannan ya sake kallon Luana, wata ƙatuwar murya ta ambato masa sunanta a cikin kansa Luana Carla! Ke nan ita ce mahaifiyar Luiz? Ya tambayi kansa yana kallon yaron.
“Pedro? Ashe za mu sake haduwa?”
Ƙoƙari ya yi ya shanye duk wani mamakinsa, saboda kada ya zama abin zargi tun a tashin farko, murmushi ya yi yana taɓa sumar yaron.
“Ba ga shi mun sake haɗuwa ba”
“Pedro wannan ce Mum ɗina, ‘yar sanda ce”
Cewar Luiz lokacin da Luana ta ƙaraso wurin da suke tsaye, ta rungume hannayenta har zuwa lokacin ba ta gama nazarinsa ba.
“Barka”
Ya furta yana kallonta shi ma.
“Pedroo!?”
Ta furta sunan kamar wadda ba ta yarda da cewa shi ya mallaki sunan ba, kansa ya gyaɗa domin tabbatar da cewa sunan nasa ne. Luana ta taɓe bakinta sannan ta miƙa masa hannunta na dama.
“Luana Carla”
Ya kalli hannun nata, kafin ya sake kallon fuskarta.
“Badar Pedro”
Ya furta mata sunan ba tare da ya miƙa nasa hannun ba, alamun dai ba zai gaisa da ita ba, kuma sai da ya ambaci sunansa ta fahimci cewa shi musulmi ne. Hannunta ta janye tana kallon Luiz da ya ƙanƙame shi kamar zai koma cikinsa.
“Mu tafi ko?”
Ya girgiza kai.
“A’a Mum, ki bari sai mun yi wasa da abokina”
“Ka san cewa ba ni da lokacin ɓatawa ko?”
Ta ƙarasa tana kallon Pedro.
“Mum pleace”
Ya mata magiyar yana riƙe hannunta.
“Luiz babu wani uziri yau, dole ka koma gida a kan lokaci saboda lessons ɗinka”
Zai sake mata musu Pedro ya taɓa kansa, ya kalle shi.
“Be a good boy, listen to Maama and don't ever argue with her.”
Ya ɓata fuska kamar zai sa kuka.
“Maza ka je ka yi karatu, za mu sake haɗuwa”
Ba da son ransa ya yarda ya bi Luana ba sai dan bai samu goyon baya a wurin Pedro ba. Suna masa sallama suka tafi, ya bi bayansu da kallo yana tambayar kansa, ‘Me ke shirin faruwa ne?’… Babu wanda ya ba shi amsa wayarsa ta soma ƙara, da sauri ya ɗaukota cikin aljihun cargo ɗin jikinsa, ganin baƙuwar lamba yasa da farko ya yi kamar ba zai ɗaga ba, bai kai ga gama yanke shawara ba ƙiran ya katse, sai kuma ya sake shigowa a karo na biyu. Ba tare da tunanin komai ba ya ɗaga wayar ya sadata da kunnensa.
“Hello! Shin ina magana da Badar Pedro Abdallah ne?”
Yana duba agogon hannunsa ya amsa da.
“Eh, how may I help?”
“Ina magana da kai ne daga ST. Paul’s School!”
Da wani irin sauri murfin idonsa da ya sauƙa ƙasa saboda agogon da ya kalla ya ɗaga sama, jin an ambaci ƙiran daga makarantar su Juliana ne.
“Me yake faruwa?”
“Yanzu haka ɗaya daga cikin ɗalibanmu Juliana Costa Badar ‘yarka na sashen kula da marasa lafiya na makarantar nan!”
*St. Paul’s International school, Juquia street, Paulistino, Sao Paulo, Brazil.*
A ruɗe ya buɗe ƙofar ɗakin, kuma ba tare da an masa izini ba ya sa kai ciki, tsaye ya yi a bakin kofar yana kallon Juliana dake zaune kan gadon marasa lafiya, an toshe mata hanci da audiga, bayan ita kuma sai wata malamarsu dake tare da ita, kamar yanda yake kallonsu haka su ma suke kallonsa.
“FireBall?”
Juliana ta ambaci sunan cikin karyayyen amonta da ya fallasa kukan da ta yi, sauƙa ta yi daga kan gadon dai-dai da sanda ya ƙaraso inda take ya riƙeta yana tambayar abin da ya sameta.
“Babu wani abin tada hankali, kawai muna wasa a playing ground na yanke jiki na faɗi, amma yanzu ba komai, na warke…”
Bai ce komai ba, sai kallonta yake kamar bai yarda da abin da tace ba, daga yanda take ma tana iya jin fat!fat! fat! Na bugun zuciyarsa dake nuna lalllai a tsorace yake, har wani gumi ne ke keto masa, hannunta ta sa ta shiga goge masa gumin dake gefen fuskarsa.
“Duk ka tada hankalinka, kuma ni ba abin da ya sameni”
Yanzun ma bai ce komai, ganinta a raye shi ne kwanciyar hankalinsa.
“Komai ya wuce”
Ta sake faɗa tana riƙo hannunsa, Malamarsu dake tsaye a gefe ya kalla sannan yace.
“Na gode sosai, amma zan ɗauketa mu je asibiti domin a dubata”
Malamar na murmushi tace.
“Ba damuwa za ka iya tafiya da ita… Juliana, have a good rest”
Ta ƙarshe maganar tana kallon Juliana, shi ya ɗaukar mata jakarta tare da jacket ɗinta suka fita, suna tsaye a ƙofar makarantar Juliana ta dube shi yanda har yanzu babu alamun kwanciyar hankali tattare da shi.
“HardRock”
Ya kalleta yana bincika jakarta.
“Ba sai mun je asibiti ba, na warke fa”
“Da ma ko hakan ba ta faru ba dole mu je asibiti yau, jiya na gama biyan kuɗaɗen aikinki, dan haka yau za a miki gwaji na ƙarshe, zuwa gobe kuma za a fara shirye-shiryen yi miki aiki!”
Julia ta yi shiru tana kallonsa, lokaci guda kuma sai wata ƙwalla ta zubo mata, ta matsa kusa da Hard Rock ɗinta ta rungume shi.
“Yanzu kuma miye?”
Ya leƙa fuskarta da ta kifa a kan ƙirjinsa.
“Ki daina kuka kin ji?”
Ta sake shi tana gyaɗa kai, Grapes ɗin da ya mata guziri su ya bata,
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 13 Chapter of 14