kan wata kujera da aka aje a falon tare da table ke satar kallonsa tana ƙunƙuni. Bayan shi da ita akwai Kairat da yayanta Mujahid a falon, wanda suke zaune kusa da Sa'ad, ita Kairat na zane-zane a cikin littafinta na makaranta yayin da yayanta Mujahid ke buga game a Tab ɗin Aysher.
Kairat da Mujahid dai yaran matar Mai matarba ta uku ne, wadda Allah ya yi wa rasuwa shekaru biyu da suka wuce, ta mutu ta bar yaran nata guda biyu da suke da ƙarancin shekaru, domin du-du-du shi kansa Mujahid bai wuce shekaru goma sha biyar ba, ita kuma Kairat ba ta haura shekaru goma ba. Zamansu ya dawo hannun Fulani Amrya ne bayan rasuwar mahaifiyarsu, kuma Fulani Amrya ta riƙesu kamar ita ta haifesu.
"Tun yaushe ka yi sabuwar budurwa?"
Maganar ta fito daga bakin Aysher ba tare da ta kalle shi ba, kuma ya san da shi take, dan haka ya ɗauke idonsa daga kan wayar ya kalleta.
"Bai shafeki ba 'yar sa ido"
"Hump! Bai shafeni ba kam, Playboy!"
Ta faɗa tana ɗage kafaɗunta alamun ba ta damu ɗin ba.
"Lallai yarinyar nan kin rainani da yawa, amma zan yi maganinki"
"Ya Sa'ad ai da Ya Hammad ne ba ta isa ta masa haka ba"
Mujahid ya sa baki.
"Ƙyaleta Mujahid, ni ɗin ma dan ta ga ina mata wasa shi yasa ta maidani karkatacciyar katanga mai daɗin ƙetara, ai shi dodon nata ko ido ba ta isa ta haɗa da shi ba..."
Kairat ta yi dariya.
"Na ɗauka ni kaɗai nake yi wa Ya Hammad kallon dodo"
"Ni fa ban taɓa ganin Ya Hammad ya yi murmushi ba..."
"Ku gama gulmar tasa, ni kuma na ƙira shi na gaya masa"
Aysher da ta taso ta faɗa tana tsayawa a kansu.
"To ki gaya masa mana, tsoronsa ake ji?"
Cewar Sa'ad, Aysher ta yi murmushi kawai tana zama a kan kujera.
"Mujahid ka ƙira Haula ta zo ta ɗauke kayan abincin nan"
Mujahid ya amsa mata da to, sannan ya miƙe ya fita falo na biyu, a nan ya ƙira Haula ɗaya daga cikin hadiman sashin Fulani amarya, suka dawo tare da ita, ta shigo falon tana musu sannu da hutawa, sannan ta kwashe kayan abincin kamar yadda aka sakata.
"Ya Sa'ad za ka zana mini kifi, tun ɗazu nake gwadawa amma na kasa zana mai kyau"
Cewar Kairat tana nuna masa takardar littafinta, inda alamun zanen pencil ya fito, duk kuwa da an saka eraser an goge shi bai kasa fitowa ba.
"Miƙo na gani"
Ta tashi ta miƙa masa littafin.
"Kairat sau nawa zan gaya miki cewar in ana zane ba a sakawa pencil ƙarfi, kar ki zana shi sosai yanda zai yi baƙi da yawa, dan wannan eraser ɗin taku ba za ta iya goge shi ya fita dika ba!"
Ya faɗi yana duba yanda takardar ta ɓaci.
"Wannan ta ɓaci gaba ɗaya, dole mu yageta"
Ya kama takardar littafin ya yage, sannan ya karɓi pencil ɗin dake hannunta, yana shirin fara zana mata Aysher dake kallonsu tace.
"Wai zana mata za ka yi?"
"To kar na zana mata?"
Ya maido mata tambayar yana kallonta bakinsa a buɗe cikin mamaki.
"Yanda ka ƙware a zane idan aka gani dole zanenka da nata ya bambanta, sai ka sa ta faɗi a homework ɗin"
"Aikin banza, su ma malaman nasu ai sun san cewa wasu a cikinsu ba za su iya zanawa da kansu ba"
Ya bata amsa yana ɗora pencil ɗin a kan paper'r littafin, sannan ya fara tsara mata zanen kifin cikin salo mai jan hankali da birgewa.
"Wai yaushe za ka koma Abuja ne?"
Aysher ta sake jefo masa tambayar, murmushi kawai ya yi ba tare da ya kalleta ba.
"Nan da sati ɗaya"
"Sati ɗaya? Ba ka ce sati huɗu za ka yi ba? Kuma na ga ba ka fi sati biyu da zuwa ba"
Ya jinjina kansa a hankali.
"Takawa ne yace kada na haursa sati ɗaya a garin nan... Da ace na yi magana a lokacin kuma da na bar garin nan tun a ranar"
Aysher ta sauƙe numfashi.
"Me zai hana ka faɗawa Ammi, Wata ƙila idan ta sa baki ya barka ka ƙarasa hutun da ka ɗauka"
Ba shiri ya ɗaga kansa ya kalleta.
"Karo na farko da kika yi magana ta hankali a rayuwarki ke nan, kin kawo shawara mai ma'ana yarinya"
Ta juya idonta alamun kai ka sani tana buɗe wayarta. Kamar daga sama haka aka banko ƙofar falon da suke ciki, abin da ya furgitasu ke nan, gaba ɗayansu suka miƙe dan ganin wanda ya zo da wannan gadarar, dan hatta bayi da hadiman fadar ba kasafai suka cika shiga falon ba.
"Innalillahi wa inna ilaihirraji'un Ya Sa'ad ka zo"
Cewar Muhibba da ta shigo hankalinta gaba ɗaya a tashe, Sa'ad ya nufeta yana tambayar.
"Me yake faruwa?"
Ta kasa magana, sai hawaye take tana yarfe hannu tana maimaita ta shiga uku.
"Muhibba me ya faru ne?"
Aysher ma ta tambaya tana ƙarasawa wurin da take tsaye.
"Ya Maryam! Ya Maryam ce..."
Sa'ad bai tsaya ya gama jin abin da take son faɗa ba ya raɓata ya fita daga falon da sauri, ita da Aysher kuma suka take masa baya. Kafin su ƙarasa sashin Adda har sun ƙagu, barin ma Sa'ad da yake ganin nisan tafiyar fiye da ko yaushe.
Tun da suka ƙarasa sashin suke jiyo ihunta, hakan ya bashi damar ƙara sauri kai tsaye ya nufi sashin da ɗakinta yake, tun a hanya yake cin karo da hadiman sashin sun yi tsilli-tsilli da su halan ya ƙara tabbatar masa da lallai yau abin na Maryam ba ƙarami ba ne.
Yana isa ya iske Adda da jakadiya tsaye a ƙofar ɗakin Maryam ɗin, yayin da suke jiyowa ihunta ita da wata da bai ma san wacece ba, ba tare da ya ce komai ba ya nufi ƙofar, yana zuwa ya kama handle ya murɗa da ƙarfi, ƙofar na buɗewa ya yi arba da Maryam ta shaƙe wuyan wata daga cikin masu musu hidima.
Ai da gudu ya faɗa cikin ɗakin, ya shiga ƙoƙarin ɓanɓare hannunta a kan wuyan matar, amma da yake ƙarfin ba nata ba ne sai ya kasa, ita tana ihu, haka ita ma wadda aka shaƙe ɗin ihun naiman taimako take. Sa'ad bai haƙura ba ya ci gaba da ƙoƙarin ƙwatar matar, da ƙyar ya yi nasarar cire hannunta a wuyanta, ai ko tana jin iska ta fara isa huhunta yadda ya kamata ta miƙe ta yi waje a ɗari uku da sittin tana kuka.
A hankali Maryam ta miƙe tsaye kanta a ƙasa, ba ta ɗago ba ballantana ta kalli fuskarsa.
"Maryam!"
Ya ambaci sunanta a hankali yana leƙa fuskarta, amma har yanzu kanta a ƙasa, sai ta soma ja da baya da baya, tana kaiwa bango ta juya ta fara buga kanta da bango tana kuka faɗi take.
"Maryam me yasa ba kya kyautawa? Me yasa ba kya jin magana? Maryam ki yi wa kanki faɗa, Maryam ke fa abar tausayi ce, Maryam!..."
Ganin tana shirin illata kanta yasa Sa'ad ya riƙota ta fara kiciniyar ƙwacewa.
"Ka ƙyaleni! Ka ƙyaleni na mutu! Mutuwa zan yi! Gara ma na mutu!"
"Ba za ki mutu ba Maryam"
Ya faɗa yana kallon jajayen idanuwanta da kallo ɗaya za ka musu ka san cewa me su ba ta cikin hayyacinta, tun tana ƙoƙarin ƙwacewa yana riƙeta har ta saduda, jikinta ya saki, a hankali ya ɗauketa ya ɗorata saman gadonta, sannan ya zauna yana tofa mata addu'o'i. Ya jima a ɗakin bai fita ba, dan gani yake kamar idan ya fita za ta iya farkawa ta ci gaba da wannan abin ne.
Bamm! Aka banko ƙofar ɗakin, ya ɗaga kansa ya kalli Sadiq mijin Maryam ɗin, gaba ɗaya yanda ya shigo zai sa ka gane a birkice yake, duk alamun tashin hankali sun bayyana ƙarara a tare da shi.
"Sa'ad me yake faruwa?"
Ya tambayi Sa'ad da ya miƙe yana kallonsa.
"Abin nata ne ya tashi, har ta shaƙe wadda ke kwana tare da ita, amma ba komai, ta samu bacci..."
Sadiq da idonsa ke kanta ya furzar da numfashi yana jin zufa na ci gaba da tsattsafowa a goshinsa.
"Waye ya gaya maka abin da yake faruwa?"
Sa'ad ya tambaya, dan ya san dole wani ne ya gaya masa, domin babu yadda za ayi Sadiq ɗin ya ɗauko ƙafa ya zo fada da wannan daren.
"Muna cikin waya da ita abin nata ya tashi, shi yasa na taho hankalina gaba ɗaya a tashe..."
Sa'ad ya sake kallonta jin ta yi motsi.
"Ruwa! Ruwa"
Ta furta ba tare da ta buɗe idonta ba, Sa'ad na ƙoƙarin tashinta zaune Sadiq ya riga shi, ya zauna bakin gadon yana kallonta.
"Baby ruwa kike so?"
Ta jinjina kanta tana dafe shi, saboda ɗan banzan ciwon da yake mata. Shi dai Sa'ad juyawa ya yi ya fita daga ɗakin, a falo ya samu Adda, Muhibba da Aysher zaune, kowa a cikinsu hankalinsa a tashe yake.
"Ku je ku kwanta tun da ta wartsake"
Ya faɗa yana kallon Muhibba da Aysher.
"Ya Sa'ad..."
Wani kallo da ya yi wa Aysher yasa ta yi shiru, duk da yana sakar musu fuska su yi wasa idan ya zama serious su kansu tsoransa suke ji, dan halin Hammad ne ya fito fili, shi ma Sa'ad ɗin sai dai in ba a taɓa shi ba. Babu wadda ta sake musawa a cikinsu suka ta shi suka fita Muhibba na faɗin za ta tafi sashin Fulani Amarya wato Ammi ta kwana a can tare da Aysher.
Adda ta gane dalilin hakan, tsoro ne cike fal a zuciyar 'yar tata, ba ta so ta kwana a sashin saboda halin da Maryam ke ciki. Kuma ita ba za ta hanata tafiya can ɗin ba, dan tsakaninta da kishiyarta ne kawai suke kishinsu, shi ma ba wani sosai ba, amma tsakanin yaransu kansu a haɗe yake, Takawa ya yi iyaka bakin ƙoƙarinsa wajen ganin ya haɗa kansu duka. Kuma ya cimma nasarar hakan, ta wuri ɗaya ne kawai aka samu tangarɗa, wato tsakanin Hammad da Sa'ad duk da su ma har gobe yana so su shirya amma abin ya ci tura.
A hankali ya zauna a kan sofa yana shafa kansa, Adda kuma na kallon wani ɓangare na falon, Allah ne kaɗai ya san irin abin da take tunani a cikin zuciyarta a halin yanzu. Dole ta damu sosai, domin jinyar Maryam kullum gaba take ba ta baya, kullum da sabbin abubuwan da take zuwa da su, a baya sai dai ta yi ƙoƙarin guduwa ko ta faɗi tana koke-koke, amma yanzu abin ya yi ƙamari ta yanda har ta fara kaiwa duka, suna zaune a falon babu wanda ya yi magana har Galadima ya shigo, ya samu wuri ya zauna Adda na tambayarsa wa ya gaya masa abin da ke faruwa.
"Ni na ƙira shi ranki ya daɗe"
Cewar Sadiq da ya shigo kansa a ƙasa, Adda da Sa'ad suka bi shi da kallo har ya zo ya zauna a falon.
"... Bai jima da ƙirana ba yace zai zo gidana mu yi magana, sai na ce masa ya bari ni da kaina zan zo fada"
Cewar Galadima. Jin cewa magana za su yi yasa Adda ta tashi faga falon suna mata sai da safe.
"Ranka ya daɗe magana ce a kan ciwon nan na Maryam, a gaskiya na fara tunanin cewa wannan matsalar tata ba ta asibiti ba ce, abin ya fi kama da shafin aljannu ko kuma sihiri... Yanzu da kanta take gaya mini cewar tun da ta fara shan magungunan nan da aka rubuta mata su a asibiti jikinta ya ƙara rikicewa, dan haka a ganin zai fi kyau mu aje magungunan nan na asibiti, mu dage mata da addu'a da kuma naiman maganin gargajiya, wata ƙila Allah yasa a dace!"
"Ni kaina a yau na tabbatar da ba ciwon hauka Maryam ke fama da shi ba, sanda na kalli idanuwanta na ga wani abu kamar bijirewa, kamar duk abubuwan da take ba yin kanta ba ne, kamar kawai ana controling ɗinta ne ba tare da ikonta ba"
Cewar Sa'ad yana tuno abin da ya gani a cikin idanuwanta a ɗazu.
"To kafin dai mu kai ga yin komai dole sai mun sanar da Takawa, duk abin da yace shi za ayi kawai"
Faɗin Galadima.
"Na san insha Allah takawa ba zai ce a'a ba..."
Sadiq ya amsa.
"To Allah yasa" Duka suka amsa da Amin.
_____________
_Me?_
_To wai ni wannan Julianar ba ita ce yarinyar da Pedro ya ceceta shekarun da suka wuce ba?_
_To yanzu ya aka yi suke tare da Pedro a Sao Paulo ba a Lencois town ba?_
_Me ya faru da su har ya kaisu ga zuwa gidan marayu?_
_Ina iyayensu suke?_
#SalmaAhmadIsah
#MiniCandy
#Bahaɗejia
#ƘawaZuci
~~~~~~~~~~~~
*ƘAWA ZUCI*
*©SALMA AHMAD ISAH.*
*07*
AKIRA POV.
*Ƙauyen Yarimaru, Gembu, Mambilla, Taraba state.*
A nutse kuma cikin taka tsan-tsan ya jingine kekensa da hannunsa ɗaya da ubangiji ya bar masa, domin yanda iska ke kaɗa hannun rigar jikinsa na ɗaya ɓangaren ya isa ya ankarar da mai kallo cewar hannu ɗaya ke ga bawan Allahn.
Da wannan hannu ɗayan ya kunce ciyawar da ya ɗaura a bayan keken nasa, ya ɗaukota da hannun nasa ɗaya ya nufi cikin gidansa ginin ƙasa ya yi sallama. Daga can cikin ƙwalli ɗayar bukkar dake gidan aka amsa sallamar, sannan wata farar matashiya ta fito daga cikin bukkar da sauri, tana ɗora idonta a kan mahaifinta ta washe baki.
"Sannu da zuwa Abboi"
Ta nufe shi ta karɓi ciyawar da ya riƙo, ta aje a gefe, sannan ta dawo ta shimfiɗa masa tabarma ya zauna tana ta jera masa sannu, ta je ta ɗebo ruwa ta kawo masa, ya karɓa ya sha, ta ɗauki ciyawar da ta aje a gefe ta yi rumfar da suke kiwon akuyoyinsu da ita.
"AMINATU ɗazu na ce da su Walidi su zo su baki hadda, fatan sun zo?"
Malam Yakubu ya cillawa ɗiyar tasa tambayar wadda ke turken dabbobin dake gidan.
"Eh Abboi sun zo, kuma sun bada haddar!"
“Masha Allah"
"Abboi na kawo maka abinci yanzu ko sai anjima?"
Ta tambaya sa'ilin da ta fito daga tirken dabbobin tana karkaɗe hannunta. Malam Yakubu da ake ƙira da Malam ya aje ƙwaryar da ya sha ruwa a ciki ya rufeta da fai-fai yana bata amsa da.
"A'a AMINATU, bar abincin nan ba yanzu ba..."
"Assalamu alaikum!"
Sallamar da aka rangaɗa daga can bakin ƙofa ta katse maganar tasu, kusan a tare suka kalli bakin ƙofar da tambayar waye yake sallama haka a zuciyar kowannensu.
"Wa alaikummusallam!"
Malam ya amsa yana miƙewa, ya saka takalmansa ya fita don ganin mai sallamar.
"Barka da rana Usama! An yini lafiya"
Ya amsa gaisuwar mutumin da ya iske tsaye a ƙofar gidan nasa.
"Lafiya amma ba lau ba!"
Naman goshin Malam na tattarewa ya furta.
"Me yake faruwa haka da rana tsaka?"
"Mai gari da kansa yace a gaya maka ka je ka tsawatarwa wancan almajirin naka Suma'ila Guru, a kan abubuwan da yake, yanzu haka Malam Halliru da Malam Tijjani suna hannunsa ya riƙesu, yau tsawon kwana uku ke nan, hatta mai garin da kansa ya tura a ƙira shi amma ya ƙi zuwa!"
Nan da nan yanayin Malam ya canza, a duniya idan yana da wata damuwa bayan wadda ta same shi a baya to ba ta wuce damuwar tsohon almajirinsa ba wato Guru, wanda a yanzu ya gagare shi, sannan ya gagari kowa dake ƙauyen, da ace ya san abin da marayan Allahn zai zama nan gaba ke nan da bai riƙe shi a matsayin ɗalibinsa har ya girma ya kawo haka ba, sai dai an ce ƙaddara ta riga fata. Sai dai duk da har yanzu Guru ya zama kangararre ko duk duniya za su taru a kansa kan ya daina wani abu guda ba zai daina ba matsawar ba Malam Yakubu ne ya saka baki ba, duk rashin mutuncin da zai yi daga zarar Malam ya masa magana a kai zai bari, domin har gobe yana darajanta shi.
"Shike nan Usama, insha Allah yanzu zan je na same shi na masa magana a kan ya sakesu"
"To Malam, ni na yi nan sai anjima"
Ya miƙa masa hannu suka sake gaisawa bayan wadda suka yi ta farko, sannan Usama ya juya ya kama hanyarsa. Malam ya juya ya dawo cikin gidan gaba ɗaya damuwa na maye gurun farin cikin da yake ciki.
"Abboi waye?"
Aminatu dake tsaye a tsakar gida har zuwa lokacin ta tambaye shi, Malam ya kalleta.
"Babu komai Aminatu, bari zan ɗan je wani wuri yanzu zan dawo"
Ta bi shi da kallo har ya shiga ɗakinsa, sannan ya fito ya bar gidan, ta san dalilin fitar tasa ba zai wuce a kan wancan Guru ɗin ba. Ita dai har yanzu ba ta taɓa ganinsa ba, duk yadda ake labarinsa a ƙauyen kuwa... To wai ma ina ruwanta da wani Guru ne? Ta tambayi kanta sanda ta tuna da fitar da take son yi kafin zuwan Abboi, zuwansa ne ya dakatar da ita, yanzu kuwa da ya sake fita ita ma fitar za ta yi ta tafi can bakin kogi, inda Popular ke zaunar da su yana musu Lecture a kan rayuwar Lagos. Duk da Abboi ya hanata zuwa ba ta hanuwa, ko ba saninsa sai ta saci ƙafa ta tafi, duk kuwa da idan ta je wurin ba ta dawowa cikin daɗin rai, dan abu ne mai wuya ta je ta dawo ba tare da ta samu wani ya goranta mata rashin sanin asalinta ba
Asalinta? Wannan asalin nata har gobe shi ne ƙalubale ɗaya da yake dawo da ita baya, har yanzu ba ta san wace ce ita ba, ko mahaifiyarta ba ta sani ba, ita dai kawai ta taso ta ganta tare da Abboi ne, amma ko sunan mahaifiyarta ba ta sani ba, a baya tana jin haushi sosai idan aka mata gorin asali, amma yanzu har ta fara sabawa da abin, ya zame mata jiki, kuma ta kauda kai daga tambayar Abboi asalinta, tun da a duk sanda za ta tambaya ba ya amsa mata, sai dai ya yi shiru, ko yace "Sanin hakan ba shi da amfani gareki Aminatu, ki yi rayuwarki kawai" Sai dai har zuwa yanzu da take numfashi a doron duniya ta kasa yarda da cewa sanin asalinta ba shi da amfani gareta, domin ita ma tana so ta san 'yan uwanta, ta san danginta kamar kowa, amma Abboi ya ƙi bata damar hakan.
AKIRA POV.
Tun da garin Allah ya waye ta tafi daji da sunan za ta je farauta, duk yadda Nikamba ya so hanata ƙi ta yi ta kama hanya ta tafi abinta. Ba ita ta dawo cikin ƙauyen ba sai da la’asar ta kawo kai, ba ta samo komai a farautar da ta je ba, amma ta dawo da tarin ‘ya’yan itaciyar da ta samo a cikin daji. Haka ta shigo cikin ƙauyen rungume da zanin da ta saka ‘ya’yan itaciyar da ta samo a ciki.
Tun da ta shigo garin jikinta ya bata cewar akwai wani abu da ya faru ko yake kan faruwa a cikin ɗan ƙaramin ƙauyen, domin duk inda ta bi sai ta ga mutane tsaye suna ƙus-ƙus, ta dai san koma miye yake faruwa to tabbas ba a kanta ba ne, da ace a kanta ne yanda ta shigo haka kowa zai yi ta binta da kallo, kuma duk inda za ta ratsa sai ka ga ana darewa, amma ta lura yau kowa da abinda yake, hakan ya sa ta a cikin mamakin abin da ya faru har ya girmi lamarinta garesu, ga shi babu wanda yake mata magana a cikin ƙauyen ballantana ta tsaya ta tambayi wani a cikinsu.
Da wannan saƙe-saƙen ta nufi gidan kawunsu, inda a yanzu nan ne kaɗai madafarta, bayan rasuwar iyayensu zamanta da Nikamba ya koma gidan, tun tana jaririya a gidan ta taso, duk da a halin yanzu shi ma kawun nasu ya mutu, sai matarsa da kuma yaranta. Zaman da suke a gidan na ba yanda suka iya ne, dan kwata-kwata matar kawun nasu ba ta sonsu daga ita har Nikamba.
A rakuɓe ta fara zaga bayan bukkar gidan gabanta na faɗuwa, dan ba ta san me za ta shiga ta tadda ba, kasancewar duka gidagen ƙauyen ba kewaye ne da su ba yasa kai tsaye take iya ganin matar kawunta Nasi, zaune a tsakar gidan tana dafa wani abu a cikin tukunyar ƙasar dake kan wuta, yaranta guda biyar sun baibayeta, wasu na kuka biyu daga cikinsu na faɗa a kan wani jan nama. Ta fi minti biyar tsaye a wurin tana shawarar da za ta fisheta, shin ta shiga gidan ko kada ta shiga ta tsaya ta jira zuwan Nikamba sai su shiga tare? Dan duk tsiya Nasi ba ta iya hantararta ko dukanta a gaban Nikamba, dan ba zai bar hakan ta faru ba.
“Ke!”
Ta ji an faɗa a bayanta, ai ko a razane ta juyo, dan tsabar razana sai da zanin dake riƙe a hannunta ya faɗi ƙasa. Ganin Nikamba tsaye a bayanta yana dariya yasa ta kumbura bakinta, sannan ta tsugunna ta shiga tattara kayan da tsoro yasa ta zubar, shi ma tsugunnawa ya yi ya tayata tsincewa.
“Me kike a nan?”
Ya tambayeta yana miƙa mata wanda ya dauko, ta karɓe abinta ta shiga goge shi a jikinta.
“Ba komai”
“Ko jirana kike?”
Sai ta jinjina masa kai, a tare suka miƙe tana kallonsa.
“Ina ka je?”
Kansa ya girgiza mata yana faɗin.
“Ukkali ce aka ganta da Jaruto a bayan tsauni, shi ne Mai gari ya sa a yanke mata hukunci irin wanda aka saba yankewa sauran mata masu hali iri nata kamar yadda al’ada ta tanadar, ba a jima da kaita Juju kukali ba…”
Magana ya bata a rufe, duk da ba ta shiga duk wata harka ta garin ta san dokoki da kuma ka’idojin kauyen nasu, hukuncin da aka saba yankewa ‘yan matan da aka gansu da wasu mazan da ba mazan aurensu ba shi ma ta sani. Hukunci ne da a yarensu suke kira da Rukil, a turance kuma (Female Genital Multilation FGM) da hausa kuma ana ce masa kaciyar mata. Wannan hukunci ne da ya samo asali tun daga zamanin magabantasu, kuma har kawo yau ba su daina ba, a zahiri ne suka daina saka tufafinsu na da, amma al’adunsu kam ko me za ai ba zasu watsar da su ba.
Duk da wayar da kan da jami’an gwamnati da kuma kungiyoyin tallafi ke musu bai sa sun ajiye ba, kowa ya san kabilar ta Hadzabe da matukar ruko da al’adu. Da ace a iyaka nan ma hukuncin ya tsaya to da an ce da sauki, domin bayan an danne mace an mata Rukil ta karfin tsiya haka za a ɗauketa akai ta wani kogo dake farkon garin wanda ake ƙira da Juju Kukali, sai ta shafe sati daya a cikin wurin tana jinyar jikinta, sannan ba a yarda an bata abinci ba, shi kansa ruwa ba dan sun san cewa sai da shi mutum zai rayu ba da ba za a bawa mutum ba.
Akwai tarin illoli da kuma matsaloli da kan biyo bayan wannan Female Genital Multilation ɗin, domin wasu ma shi ke sanadin rayuwarsu, wasu kuma daga lokacin ba sa sake amfanuwa, wasu su gamu da ciwon yoyon fitsari, abubuwa dai da dama. Akira ba ta haɗa komai da Ukkali ba, hasali ma ko magana ba ta taɓa haɗasu ba, amma har cikin zuciyarta take jin tausayinta, domin ta san wata kila wannan shi ne sanadin rayuwarta.
“Yau da kika je farautar me kika samu?”
Tambayar da Nikamba ya mata ta dawo da ita duniyar zahiri, hakan yasa ta dube shi.
“Ban samo komai ba sai wadannan”
Ta nuna masa kayan da take rike da su.
“Ai da ma sai…”
“Nikamba!”
Kiran da aka ƙwala masa tun daga nesa yasa bai karasa maganar da yake son yi ba, juyawa ya yi don ganin wanda ke kiran nasa, yayin da Akira ta dora idonta a kan Njau abokin Nikamba da yake dososu.
“Njau argi?” (Gukuli ya aka yi?)
Nikamba ya tambaye shi sanda ya ƙaraso wurin.
“Sarki ne zai yi sanarwa”
Nikamba ya juya ya kalli Akira dake kallonsu.
“Ki je ki jirani ba zan jima ba”
Ta gyaɗa kai tana kallon Njau domin sun saba a duk sanda zai ganta sai ya mata magana, hakan wani abu ne da ba ta saba da shi ba a wurin mutan ƙauyensu, bayan Nikamba ba ta jin tana da wani wanda yake mata magana, in ka ji wani ya mata magana to lalle baƙar magan ce zai gaya mata ko kuma tsine mata za su yi. Har ta juya bai ƙirata ba kamar yanda ta yi fata, maimakon ta yi sauri ta shige gidan sai ta fara tafiya a hankali tana son ta ji ya ƙirata, amma shiru, sai ta juyo domin ganin ko dai Nikamba ya ja shi sun tafi, kuma tana juyowa idonta ya faɗa cikin nasa, Nikamba ya bar wurin amma shi yana tsaye yana
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 6 Chapter of 14