Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
sannan ya bata riƙon jakarsa da tata yace zai je ya dawo ta jira shi a wurin. Ba za ta iya jira sai ta zauna a wani wurin ba, dan haka ta buɗe container da grapes ɗin ke ciki ta fara ci. Ta yi nisa a enjoying grapes ɗinta ba ta zata ba ta ji an bangajeta an wuce, aiko ta dago da sauri tana duban wanda ya bigeta, wucewa ya yi abinsa kamar bai san da ya buge mutum ba, da ma Juliana ba haƙuri ba, jakukkunan hannunta ta saki a ƙasa sannan ta nufe shi a zafafe ta janyo rigarsa ta baya. Hakan yasa ya juyo tare da wanda suke tafiya, kana ganinsa ba sai an gaya maka cewar tantiri ba ne, domin gaba ɗaya busashen jikinsa me kama da sillan kara a zane yake da tattoo, saboda tsabar ya shara ma daga shi dai singlet yake yawo, ba kunnensa ne kaɗai a ɓule ba har hancinsa da saman girarsa duka an ɓula. “Kai makaho ne da za ka bangajeni kuma ka wuce ba tare da ka bani haƙuri ba?” Babu tsoro ko shakkarsa a idonta take faɗar hakan, yo tsoron me za ta ji, wannan busasshen abin da bai fi ta hure shi da iskar bakinta ba, wani kallo ya mata kafin ya ƙwace kafaɗar rigarsa da ta riƙo, ya sa hannunsa ya sake tura kafaɗarta baya. “An bigeki ki ɗauki mataki” Zuciya ta ciyota har ta raya mata abin da zai kawo ƙarshen rayuwarta a duniya, hannunta na hagu ta ɗaga ta sharara masa mari, ba wanda aka mara ba kaɗai, hatta wanda ke tare da wanda aka mara ɗin mamakin marin ya shigesu. “Ke!? Kin san waye Felipe a garin Sao Paulo?” Kai tsaye kuma cike da tsiwa tace. “Waye shi a cikin kayan miya? Na ce waye shi a cikin kayan miya?” Har wani tsalle-tsalle take tana zare musu ido. Shi ma nasa hannun ya ɗaga zai mareta Pedro ya shiga tsakaninsu tare da riƙe hannun nasa, cike da kashedi ya girgiza kansa. “Kul! Kar ka kuskura” Felipe ya ƙwace hannunsa yana kallonsu, sai kuma ya soma ja da baya yaransa na binsa, babban ɗan yatsansa ya ɗaga ya saita a wuyansa sannan ya ja layi alamun yanka, kashedi ne buɗaɗɗe yake mata cewar zai kasheta. Wani gundumemen ashar ta masa tana nuna shi da hannu, Pedro ya kalleta. “Kin san waye shi?” “Ni ina ruwana da waye shi” “Shi ne Felipe, ƙanin Andirigo Antony!” Ƙululu! Ta ji cikinta ya bada ƙarar tsoro, take container'r dake hannunta wadda duk wannan gumurzun da aka sha da ita tana riƙe a hannunta ta suɓuce ta faɗi, ta kalli Pedro da manyan idanuwanta da tsoro yasa suka ƙara girma, har ga Allah da farko ta ɗauka cewa irin ƙananun ‘yan dabar nan ne na lungu da gefen hanya, ba ta san ƙanin riƙaƙƙen ɗan daba ta taɓo ba, ba ta san hawaye na zubo mata ba sai da ta ji Pedro na share mata su yana dariya. “Nan gaba idan za ki yi abu ki fara tunani kafin ki aikata shi” “For Pete's sake ban san waye shi ba” “Na sani” “Yanzu me zai faru da ni?” Kafaɗarta ya dafa yana faɗin. “Ba gani ba? ba zan bari wani abu ya sameki ba” “Jesus, give me peace that surpasses understanding!... ” Ta kalle shi. “Na manta ina da kai ai!” Ya yi dariya. “Ba ri na tsaida taxi mu tafi asibiti” Ta gyaɗa masa kai tana tsugunnawa, dan ta ɗauki graphes ɗinta. Tun da suka je asibitin ake ta mata gwaje-gwaje, ba su suka gama da asibitin ba sai ƙarfe tara na dare, zuwa lokacin duk Juliana ta gaji, dan tun suna taxi ta fara bacci, sanda suka isa Mooca me taxi ya tsaya a farkon unguwar ya sanar da su an riga an rufe hanya babu damar da zai shiga ciki, su sauƙa su ƙarasa da ƙafa. Hakan kuwa aka yi, Pedro ya sallame shi suka taka da ƙafa. kasancewar zuwa lokacin dare ya yi sosai yasa layin nasu babu kai kawon mutane, saɓanin cikin garin Sao Paulo da yake cike da kaikawon jama'a kamar safiya ba dare ba. "Pedro" Juliana ta ƙira tana dubansa, shi ma ya kalleta yana ɗage mata gira alamun Miye?. "Har yanzu hankalina bai kwanta ba game da abin da Felipe yace, ina jin labarin irin muggan abubuwan da suke aikatawa shi da ɗan uwansa, kar ya mini wani abin!" Pedro ya yi murmushi yana girgiza kansa, ya kalleta yayin da ita ma take jiran abin da zai ce. "Felipe ko yayansa Andrigo ba su isa su miki komai ba matsawar Pedro yana raye! Ba zan taɓa bari su cutar da ke ba, alƙawari" Juliana ta yi murmushi, kafin ta haɗe tazarar dake tsakaninsu, ta saƙala hannunta a nasa dake cikin aljihu, suka ci gaba da tafi suna hira. Suna daf da shiga wata kwana aka dallesu da hasken fitilar mota ta baya, hakan yasa suka dakata. Suka dubi juna shi da Juliana, wadda alamun tsoro suka gama bayyana tattare da ita. "Kar ki juya" Ya umarceta ganin tana shirin juya kanta domin ganin motar da me ita. A hankali Pedro ya zaro hannunsa daga cikin aljihunsa, sannan ya kamo hannunta ɗaya, ya ci gaba da janta suna tafiya, kuma ita ma motar dake bayansu sai ta ci gaba da binsu kaɗan-da-kaɗan. "A ganinka su waye?" Cewar Juliana da take a tsorace, cikin dakiya Pedro yace. "Wannan ba shi ne mai muhimmanci ba" Ta haɗiyi miyau tana yawo da idonta a layin da suka shiga, wai ko za ta ga wani. Jin saurin tafiyar motar dake binsu ya ƙaru yasa Pedro ya fara janta suka soma gudu, ita ma kuma motar sai ta shiga binsu da gudu. "Ki yi gudu Julia!" Ya faɗa da ƙarfi yana janta, ita ma gudun take tun ƙarfinta, amma duk da haka shi ya wuceta. Suka soma daren gudu da motar har suka kai ƙarshen kwanar da suka shiga babu giftawar ko da kare ballantana ɗan adam. Har suka isa daf da layin da suna shiga za su iske gidansu, kuma suna daf da shiga layin ƙaran fitar bullet daga bindigar da aka harba shi ya karaɗe layin. Cak ƙafafun Juliana suka tsaya a galaɓaice, Pedro dake kan gaba ya ja hannunta jin ta tsaya, mai makon ta taka ƙafafunta sai ya ji gaba ɗaya jikinta ya saki. Hakan yasa wani abu ya shiga birkita ƙwaƙwalwarsa, musamman da ya yi tunanin cewa ko ita aka harba, tunanin hakan yasa ya ji wani zafi na ratsa zuciyarsa, kuma hakan yasa ya yi kokwanton ko dai shi aka harba ba ita ba. Lokacin da ya juya bai rabe ɗayan biyu ba, motar dake ƙoƙarin guduwa kawai ya kalla, Felipe ya gani ya leƙo ta tagar motar, ta ɓangaren mai zaman banza, hannunsa riƙe da bindiga, yana waving masa ita, lokaci guda kuma yana haɗa masa da gwalo. A lokacin kuma ya ji hannunsa dake riƙe da na Juliana ya ƙara nauyi, dan haka dubansa ya zarce zuwa kanta, tsaye take tana numfashi da sauri-sauri, yayin da idanuwanta ke ƙoƙarin yin sama gaba ɗaya, bakinta a buɗe, yayin da idanuwanta ke fitar da ƙwallar azaba. Da sauri ya saka hannayensa biyu ya taro bayanta, lokacin da ta yi baya za ta faɗi. "Julia!" Laɓɓansa suka furta sunan ba tare da sauti ya fito ba. A hankali ya zame da ita zuwa ƙasa, ya riƙeta da kyau yana jijjigata. "Julia!" A lokacin kuma hannunsa dake bayanta ya taɓo wani abu mai damshi, wani abu mai ɗumi, wani wuri daf da ramin da bullet ɗin da aka harbeta ya huda a jikinta, wani abu ja. Hannunsa na hagu na rawa ya janye daga jikinta, sannan ya kalli hannun nasa da ya ɓaci da jininta. Sai a lokacin ya tabbatar da cewa ba shi aka harba ba, Juliana aka harba. Tunin hakan kaɗai ya kusa sawa shi ya rigata tafiya kafin tata ta zo, da ƙyar ya janyo numfashinsa dake shirin yin sama gaba ɗaya, sannan ya kalli fuskarta, lokacin da jini ya fara bin bakinta, kuma tana kallonsa da idanuwanta da yake yawan cewa tun na yarinta har yanzu ba su sauya ba, waɗannan idanuwan da suka ba shi sabon fata a rayuwarsa, idanuwan da suka cike masa wurare da dama da suka yi zurfi a rayuwarsa. Hannunsa na hagu mai jinin ya ɗora a kanta yana shafa gashinta, lokaci guda wani ruwa ya ƙwace daga idonsa, sannan ya biyo hancinsa, ya ɗisa a kan kumatunta. Sanda jikinta ya kama rawa, maganarta gare shi ranar auren Matilda kawai yake tunawa. _"Ko ba a faɗa ba jikina na bani cewar na kusa mutuwa! Ko yau, ko gobe, yanzu ko an jima da ko wani lokaci mutuwa nake!”_ "Juliana!" Ya ƙira sunan muryarsa tana rawa, lokaci guda kuma yana taɓa fuskarta, a lokacin ita kuma tata ta ƙare, ruhinta ya fice daga gangar jikinta, sannan idanuwanta suka rufe gaba ɗaya, rufewar da ba za su sake buɗewa ba har yaummu takkunu, jikinta ya saki tare da hannunta dake kan wuyan rigarsa. Alamun rai ya yi halinsa… -------------------- _Jama’a ga tambaya!_ _Shin a ganinku wani hali Akira za ta shiga a ƙauyensu idan har Nikamba bai dawo ba?_ _Kuna tunanin Sa’ad zai yarda ya tafi Tanzania?_ _Mecece makomar Maryam? Tun da yanzu dai alamu sun nuna mana ɓaro-ɓaro wannan ciwon nata shiryayye ne_ _Mene asalin abin da Guru ke shiryawa?_ _Wasu abubuwa ne wanda ya raba Malam Yakubu da su?_ _Ya tabbata cewa Aminatu ita ce ƙaddararsa, shin kuna ganin wannan ƙaddarar tasa za ta kammala kuwa?_ _Wace guguwa ce wadda Mangwau ya yi magana a kai?_ _Yaya za a ƙarƙe a tsakanin Aminatu da mutumin da yace mata shi ne Guru_ _Mecece makomar Saama a hannun ‘yan sanda?_ _Tayaya halin da yake ciki zai zama silar ƙaddarar Zahra_ _Menene ainahin labarin Pedro da Juliana, wata irin gwagwarmaya suka sha a rayuwa kafin su kai ga wannan matakin?_ _Wace ƙaddara ce ta haɗasu? Sannan wace ƙaddara ce ta rabasu?_ _Yanzu da Julia ta mutu, kuna ganin zai naɗe hannayensa ya koma gefe yana kallon Felipe da ɗan uwansa suna yawo a gari?_ _Yanzu aka soma wasan, yanzu aka fara labarin, sai a yanzu ne aka buɗe shafin ƙaddarar kowa a cikinsu, ga shi kuma a nan free pages suka dakata._ _Domin kasancewa cikin wanda za su mori wannan tafiya za ku biya naira 400 kacal_ _A tura kuɗin ta 5487270431 Salma Isah Monie point, sai a turo shaidar biya ta 08130172702_ *Kada ku manta da na ce muku ba mu yi komai ba har yanzu, ba zan gajiya da gode muku ba masoyana, ababen alfaharina, abin tinƙahona a ko da yaushe, godiya cikin cokali, Allah ya saka muku da alkairinsa, I love you like WUJIGA-WUJIGA❤️, sai mun haɗe a paid group_ Best Regards Salma Ahmad Isah a.k.a Candy 🦋 a.k.a Bhadejia 🐎 2024… An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels

Chapter 14 of 14