mutane tsaye a kan wani tudu, alamun mutanen ya nuna cewa ma'aikatan gwamnati ne, wasu na bincike a kan wasu takardu, wasu kuma na ta dube-duben garin nasu daga sama, dan a inda suke tsaye za su iya hango ko ina na garin, duk da garin a kwari da tudu yake.
"Oh waɗancan? Dad yace mini malaman kimiyya da fasaha ne, a kwanakin nan an yi hasashen za a iya samun girgizar ƙasa a Lencois, shi ne gwamnati ta turosu domin su bincika abin da zai iya janyo matsalar!"
Pedro ya taɓe bakinsa, dan bai ɗauki maganar serious ba, hasali ma shi ba wannan ne a gabansa ba, haɗuwarsa da Papsi a yau ta fi komai faranta masa. Dan haka ya watsar da batun girgizar ƙasa suka ci gaba da tafiya da Drake suna tattaunawa a kan abubuwan da za su yi idan sun je Copa Cabana, hatta irin wassanin da za su yi a bakin tekun sai da suka yi magana a kansu. Ba tare da sanin cewa su da zuwa Copa Cabana za a samu wani lokaci mai tsayi ba, wata tazara da za ta iya saka shu ya mance wannan farin cikin da yake ciki, domin abin da zai je ya tarar a gida shi ne silar tarwatsewar rayuwarsa gaba ɗaya, tun daga farko har zuwa tsaki.
A kan wata hanya da ta rabu gida uku suka yi sallama da Drake, ya wuce gida yana ta farin ciki abinsa, sai dai me? Tun daga nesa ya fara hangen kofar gidan, wai ko zai ga kotar Papsi ɗinsa, amma saɓanin motarsa sai ya ga Ambulance. Mamaki ya kama shi, to me Ambulance take a ƙofar gidansu? Me ya faru? Me aka yi? Me ake kan yi?.
Gaba ɗaya ma sai ya naimi farin cikin nasa ya rasa, son sanin abin da yake faruwa yasa ya nufi gidan da ɗan gudunsa, kafin ya ƙarasa mutum biyu sanye cikin kayan nurses na asibitin gwamnati suka fito daga gidan, a kan idonsa suka shiga Ambulance ɗin suka bar ƙofar gidan. Tun kafin ya shiga gida yake jiyowa wasu surutai a cikin gidan, saɓanin a baya da idan ya dawo da masifar Racquelita yake fara cin karo, yau bai ji ko bakinta ba.
To fa a nan ne jikinsa ya fara sanyi, domin wani zargi da ya fara ɗarsuwa a zuciyarsa. Sai yake ji kamar kar ya shiga gidan, juyawa ya yi, sai dai taku biyu kawai ya yi, ya ji an ƙira sunansa.
"Badar!"
Ko bai juya ba ya san wa ya ƙira shi, abokin aikin babansa ne, wanda suka saba zuwa gidan tare da shi, a hankali ya juyo yana riƙe da hannun jakar dake goye a bayansa, irin kallon da Marcel ke masa kawai yasa gabansa faɗuwa. Amma bai bari hakan ya yi tasiri a kansa ba, hannunsa yasa ya ture gashin kansa dake ƙokarin rufe masa ido.
"Kawu Marcel! Barka da yamma"
Marcel da ya yi tsaye yana kallonsa cike da tausayawa ya daure yace.
"Barka da yamma Badar, har kun taso ke nan?"
Ya gyaɗa kansa yana kallon ƙasa, dan gaba ɗaya ƙafafunsa rawa suke.
"Ka shigo ciki!"
Marcel ya kuma faɗi yana daga tsaye a ƙofar gidan, Pedro ya kasa amsawa, ya kasa motsawa, ya kasa komai.
"Badar!"
Ya ɗaga kansa ya kalli Marcel....
________________
_A ganinku me yake faruwa a cikin gidan Abdallah?_
_Wai me ya faru a rayuwar bayin Allahn nan guda biyu?_
# SalmaAhmadIsah
#MiniCandy
#Bahaɗejia
#ƘawaZuci
~~~~~~~~~~~~
*ƘAWA ZUCI*
*©SALMA AHMAD ISAH.*
*09*
..."Ka shigo ciki nace"
"Mm"
Ya amsa yana haɗiyar yawun da bai san ta ina ya taho ba, kamar wanda aka tirke a wurin, da ƙyar ya iya ɗaga kafarsa, ya soma takawa a hankali yana nufar gidan, ta gaban Marcel ya wuce. Kuma yana shiga falon kukan Sophia ya masa sallama, abu na farko da ya fara gani a falon shi ne, wani abu mai kama da mutum kwance a ƙasa, an lulluɓe shi da farin ƙyalle, wanda ya ɓaci da jini.
Sai kuma Racquelita zaune a can kan steps, ta ginjina kanta da banister ɗin Stairs tana kallon gawar dake kwance a ƙasa, hawaye kuma kwance a kan fuskarta. Daga kanta kuma dubansa ya zarce kan Sophia dake rungume a jikin Laala tana kuka, Laala na rarrashinta, bayan su kuma sai abokan babansu guda biyu da ya sani, akwai kuma wani mutum ɗaya da bai ma san daga wace duniya yake ba.
Abin sai ya zama kamar mafarki, dan ko ji ya yi kamar ana juya kansa daga hagu zuwa dama, a hankali ya ja ƙafarsa da ya ji ta yi nauyi, kamar wanda ya shekara bai motsata ba, wurin da Sophia ke tsaye ita da Laala ya nufa, yana zuwa ya riƙo hannunta yana kallon fuskarta da ta yi gaje-gaje da hawaye, fuskar nan jajir, kamar da aka mata kwalliya da strawberry.
"Sophia? Sophia ina Papsi?"
Bai san lokacin da wasu hawaye suka ƙwace masa ba, dan bai shirya zuwansu yanzu ba, ya fi so ya tabbatar tukkuna, in ya so sai ya yi mai dalili, a halin da yake ciki yanzu ya kasa gaskata abin da yake ji kamar raɗa masa ake a kunnensa, hankalinsa ya gaza ɗaukar batun. Sophia dake masa kallon tausayawa ta ɗaga kanta daga jikin Lala tana kallon ƙaninta.
"Papsi! Papsi ya samu haɗari a hanyarsa ta dawowa daga Sao Paulo... Dan... Dan!"
Ta kasa ƙarasawa, lokacin da ya fisge hannunsa da take shirin riƙewa, hawayensa suka ƙara gudu yana girgiza mata kai.
"Papsi! Papsi?"
"Ƙwarai kuwa Pedro, Allah ya karɓi abinsa, Abdullah ya rasu Badar! Ya rasu!"
Marcel ya maimata masa kalmar har sau biyu, shi dai ta farkon kawai ya ji, dan bayan ita bai sake jin komai ba, gaba ɗaya ma hoton ne ya masa sama, sai kuma wani hazo-hazo da ya baibaye ganinsa, bai ji komai ba sai Sophia dake ƙiransa da ƙarfi, a bayan muryarta akwai ta Marcel, akwai kuma ta Lala, amma babu ta Racquelita!...
*Present Day...*
*Masarautar Dutse.*
"Dan girman Allah ranki ya daɗe ki min rai, ki yi haƙuri da abin da zan faɗa, amma Wallahi ba zan iya kwana da ita ba, jiya ma da ƙyar na sha!"
Cewar baiwar dake kwana tare da Maryam, saboda a halin da take ciki ba a barinta ta kwana ita kaɗai, durƙushe take a gaban Adda, kanta a ƙasa jikinta na ɓari. Adda ta yi ajiyar zuciya tana jin kamar an saka zare an ɗaure zuciyarta.
"Ba zan tuhumeki ba Kamila, na san kin yi iya bakin ƙoƙarinki, ki je ki ci gaba da aikinki!"
Kamila ta yi kamar ta dungura tana godewa Adda, kafin ta tashi ta fita. Tana fita Adda ta dafe kanta dake sara mata, ta rasa ina za ta sa ranta saboda damuwa, a kullum ciwon Maryam gaba yake ba ya baya, babu abin da yake raguwa sai ma ƙaruwar da yake.
"Allah ya huci zuciyarki gwanata!"
Cewar Jakadiya dake zaune a gefe, kuma maganar da ta yi ta tunawa Adda cewar akwai wanzuwarta a falon, sai ta ɗago tana kame kanta.
"Jakadiya yanzu ciwon Maryam har ya yi ƙamarin da jama'a za su fara gudunta?"
Jakadiya ta sunkuyar da kanta.
"Da yardar ubangiji uwar ɗakina za ta samu lafiya! Wannan ɗaya daga cikin jarabawoyinta ne, kuma da izinin ubangiji za ta cinyesu!."
"Mts!"
Adda ta ja guntun tsaki tana ambaton 'inna lillahi wa inna ilaihirraji'un'
"Yanzu me kike ganin ya kamata ayi Jakadiya?"
"Allah ya taimakeki, ina da shawara"
"Umhum! Ina jinki"
"Me zai hana ba za a je wurin malamai masu bada magungunan aljannu da na sihiri ba, a kai musu bayani game da ciwon uwar ɗakina, tun da kin ga har yanzu magungunan asibitin da ake gwadawa ba su yi komai ba, a ganina idan hagu ta ƙi sai a koma dama, amma abin da kika ce shi za a yi ranki ya daɗe!"
Adda ta yi shiru tana juya maganar.
"Kafin mu kai nan, abun da ya fi muhimmanci yanzu shi ne a samu wanda zai tayata kwana ya kuma riƙa kula da ita, ba na jin wani cikin bayin gidan nan zai iya hakan, saboda haka dole a naimo wadda za ta riƙa kula da ita daga waje, kafin a je ga batun masu magani"
"Haka ne ranki ya daɗe, insha Allahu za mu binciko wadda ta dace, domin ba za mu yi wasa da lamarin da ya shafi uwar ɗakina ba, wadda za ta kula da ita dole sai an samo mai ladabi mai hankali mai tarbiyya!"
Adda ta jinjina kanta.
"Na baki wuƙa da nama, sannan idan an samo yarinyar kar a ɓoye mata komai game da ciwon Maryam, idan ta ce za ta iya to, in ko ta ce ba ta amince ba kar a tursasata, sannan za mu riƙa biyanta duk sati"
"An gama ranki ya daɗe, Wannan karamci ne daga gareki Shugabata, Allah ya taimakeki!"
"Za ki iya tafiya"
"Godiya nake Ranki ya daɗe..."
Jakadiya ta miƙe ta fita, sai d ta fice daga sashin Adda baki ɗaya, sannan ta ɗauko wayarta ta aikawa Yatan Dallah ƙira.
"Dan girman Allah Jakadiya kar ki takurawa rayuwata, ni tsiyata da ke ke nan, kar ki naimi ɗaga mini hankali dan kin ara mini dubu biyar ɗinki"
Yata ta fara da faɗar hakan ba tare da ta amsa sallamar da Jakadiya ta mata ba.
"Ke tafi can, ni ba wannan yasa na ƙiraki ba"
"To ya aka yi kika ƙirani da wannan la'asariyyar?"
"Ina 'yar gidan uwar gijiyata da na baki labarin tana jinya?"
Shiru Yata ta yi, kafin tace.
"Wadda kika ce hauka ya fara kamata ko?"
"Eh ita, yanzu Uwar gijiyata ta bani umarinin tana so a naimo mata yarinyar da za ta riƙa kula da ita, na san ku ne idon gari, shi yasa na ce bari na baki aikin naimo yarinya mai hankali mai tarbiyya da nustuwa!"
Yata ta yi 'yar gajeriyar dariya.
"Ai ki ɗauka an gama Jakadiya, insha Allah za ki ji ni da zarar na samota"
"Shi yasa na yarda da ke Yata... Sai na jiki"
*Ƙauyen Yarimaru, Gembu, Mambilla, Taraba state, Nigeria.*
AMINATU POV.
Su uku ne ke tafe, kowacce a cikinsu na riƙe da bokitin fenti. Tuƙa-tuƙa suka nufa domin ɗiban ruwa, kasancewar inda aka kafa tuƙa-tuƙan yana can saman tsauni ne yasa dole sai sun bi ta cikin daji kafin su kai wurin.
“Kun ga gara ku yi sauri, dan ba mu san irin layin da za mu je mu tarar a tuƙan nan ba!”
Wadda ta yi furucin a cikinsu ta ƙara saurin tafiyarta tana cilla bokitin hannunta sama, sannan ta cafe.
“Haka ne, Amina mu yi sauri”
Cewar ɗayar tana jan hannun Amina.
“Da ma kun daina ɓata lokacinku, dan Wallahi ko sama za mu ta shi dan sauri sai mun tarar da layi a wurin nan”
Cewar Amina.
“Da ma ai ke bakinki ba ya faɗar abin arziki, sai ki zauna kina kallon ruwa kwaɗo ya miki ƙafa, mu kin ga tafiyarmu…”
Da ido ta bi su har suka yi gaba, tun tan tana hangosu har suka mata nisa. Wani guntun tsaki ta ja ta ci gaba da tafiyarta a nutse, tunanin makarantar gaba da sakandire da take mafarkin yi ya faɗo mata. Da wuya ace Baffanta ya amince, ba ta jin zai taɓa bari ta tafi Taraba domin ci gaba da karatu, ga shi kuma tana son ci gaba da karatun, tun bayan da ta gama high school ba ta da aikin yi sai zaman gida, ba kamar tana makaranta ba, dan boarding school ta yi, in dai ta koma makaranta bata dawowa gida sai term ya ƙare. Wani lokacin ko mararin dawowa gidan ba ta yi dan idan ta dawo ɗin ba wata tsiya take tsinanawa ba, ga kaɗaici da yake damunta. Duk safiyar Allah idan Malam ya sa ƙafa ya fita ba ta sake ganinsa sai da yamma, ita kaɗai take yini a gidan, sai wani lokacin in zaman kaɗaicin ya isheta sai ta tafi gidan su ƙawayenta Lawisa.
Tun kafin ta ƙarasa wurin da bohole ɗin yake ta hangi tarin mutanen da suke wurin, a gefe ta hangi Lawisa da Suwaiba ƙawayenta, tsaye suke suna kallon wasu dake kokuwa a kan satar layi da aka yi a wurin. Dariya suka bata, yanda suka rakuɓe a gefe alamun dai ba su da wata mafita face su jira zuwan layi kansu.
“Muguwa, fito ki yi dariyarki a fili”
Cewar Suwaiba tana hararta ƙasa-ƙasa, Amina ta yi gyaran murya tana son tsaida murmushin da take da yake son komawa dariya.
“Ba dariya nake ba ai”
Suna kallonta ta giftasu ta je ta saka bokitinta a layi, zuwa lokacin an samu wasu sun raba faɗan da ake. Wurin da suke tsaye ta koma, suka shiga bata labarin farkon faɗan da ta yi missing. Sun jima a wurin suna jiran zuwan layinsu, Lawisa da Suwaiba ne suka fara cika nasu, tun da sun riga Amina zuwa, amma duk da haka bayan sun cika sai suka tsaya jiran zuwan layi kanta, sai da wasu mutum biyu suka cika kafin layi ya zo kanta, ita ba ma ta lura ba saboda hirar da suke ita da su Lawisa.
“Ke layinki ya zo”
Suwaiba ta ankarar da ita, ai ko da sauri ta miƙe ta nufi bokitin nata domin saka shi a bakin tuƙan, amma kafin ta isa wata ta zo ta saka nata a wurin. Baki sake kuma cikin mamaki ta ƙarasa wurin.
“Baiwar Allah, wannan layina ne fa”
Wani irin kallo budurwar ta wurga mata na ke kin isa.
“Da uban wa ye yace ki tafi yawo? Kin san layin ya zo kanki kika ƙi zuwa ki saka!”
Amina ta yi sukuti tana kallon ƙarfin hali, wai ɓarawo da sallama.
“Kin ga dan Allah, ni ba faɗa nake naima ba, ki janye bahonki ki bari idan na cika nawa sai ki cika naki…”
“Ke har kin isa ki sa na janye bahon nan? Ai ko ubanki ne zai zo da kansa bai isa…”
“Malama ya isheki, idan ke ba ki san darajar iyayenki ba ni na san darajar nawa, kuma kina sake furta wata magana mara daɗi a kansu ba zan saurareki ba”
Wata dariyar renin hankali budurwar ta sheƙe da ita tana tafa hannu, a lokacin kuma su Lawisa su ma suka ƙaraso, ganin abin na shirin zama babba.
“Ni ko na san darajar iyayena, wanda bai san asalinsa ba ma ya san darajarsu ballantana ni da na san asalina”
Magana ta goga mata a fakaici, gori ta mata mai ciwo, irin gorin da aka saba mata irinsa, wannan gorin asali da ake mata na ɗaya daga cikin dalilin da suka sa ba ta son zuwa Yerimaru, domin a idon kowa ita ba komai ba ce face mara asali.
“Kin yi gaskiya cewa ban san asalina ba, amma ba zan bari wannan ya zama raunina ba, wanda kowa zai yi amfani da shi a kaina wurin cin nasarata… Ni ce a layi ba ke ba, dan haka ko za mu tashi wurin nan ba ki isa na bar ki kin ɗebi ruwa kafin ni ba!”
Ta faɗa a hassale, ƙoƙari take ta danne famun ciwon da aka mata, dan har ga Allah a duk sanda za a goranta mata abu irin wannan tana jin haushi, sai dai kawai ta danne dan ya zama dole. A ƙufule ta sa ƙafa ta ture bahon da budurwar ta saka a bakin tuƙan, sannan ta saka bokitinta. Ita ma budurwar ba ta yi sanya ba wurin yunƙurawa za ta janye bokitin da Amina ta saka. Hannu biyu ta sa ta cakwamo budurwar, sannan ta tureta.
“Wallahi! Wallahi! Wallahi! Idan har kika kuskura kika taɓa bokitin nan sai na miki duka a wurin nan!”
Magana take a fusace, yanda ta haɗe rai kaɗai ya isa ya tabbatar maka da gaskiyar maganarta har zuwa zuciyarta. Ganin faɗan Amina abu ne da ba a saba gani ba, ita dai ba ta da haƙuri, in ka ce mata cas sai ta ce kule, ba ta taɓa bari a ci riba a kanta wurin fadan baka kokaaa ce dai ba ta taba ba, yanzu ma tura ce ta kai bango. Abin da ta yi yasa budurwar ba ta sake tankawa ba, har Amina ta buga tukan ta cika bokitinta, sannan ta ɗauka tana cewa da su Suwaina su zo su tafi.
GURU POV.
“… Oga! Kayan da muka tura Taraba sun isa lafiya”
Cewar Damulo, babban yaronsa, kuma na hannun damansa. Hakimce yake kan kujera a tsakiyar daji, kusa da wurin da ya kafa dabarsa, wani littafi ne dake ɗauke da izifin al’kur,ani wanda aka rubuta shi da ajami ne riƙe a hannunsa yana karantawa, kamar yanda ya saba zama, kafarsa ɗaya kan ɗaya yana jijjigata, a hankali ya jinjina kansa alamun ya ji. Hakan ya bawa Damulo damar ci gaba da koro jawabi a kan kasuwancinsu na kayan maye kamar haka.
“Sai kuma wanda muka tura Kano, sai dai su… sun… sun..”
Ya kasa ƙarasawa, hakan yasa Guru ya kalle shi.
“Mi ye na in-inar? Ka ƙarasa mana”
“An kama kayan a hanya”
Damulo ya ƙarasa yana sinne kansa ƙasa, dan ya ɗauka bayanin nasa zai ɓata ran ogan nasa. Sautin tsaki da ya ji yasa ya ɗaga idonsa ya kalli Guru da ya maida hankalinsa kan karatun da yake hankali kwance, shi ya ɗauka ma wata babbar matsala ce.
“Ni na ɗauka ma wata tsiyar ce… A wani gari aka kama kayan?”
“Tsakanin Gombe zuwa Kano”
Guru ya ja hanci kamar me mura.
“Wani ɗan siyasa muka taɓa yi wa aiki a Gombe?”
Damulo ya yi shiru alamar yana tunani.
“Ina ga!”
“Bana buƙatar ƙila wa ƙala, duk abin da za ka faɗa matsawar ba ka da tabbaci a kansa to ka ce ba ka sani ba zai fi”
Ya katse wa Damulo tunani.
“Yi haƙuri Oga, ina da tabbaci a kan abin da zan fada, ina ga…”
Kallon da ya watsa masa yasa ya gwaɓi bakinsa, sannan ya gyara maganar.
“Alhaji Sidi Guduma, ɗan takarar sanata”
Lokaci guda Guru ya saki murmushi.
“Na kwana biyu ban taɓo shi ba kuwa, maza latso mini shi”
“To Oga”
Sai dai kafin a latso masa lambar Alhaji Sidi, Sidiyar ƙaddararsa ta ƙwanƙwasa masa ƙofa, ƙaddarar da wayonsa, dabararsa, tunaninsa da kuma ƙarfin da yake tunanin yana da shi, ba su isa sun tsallakar da shi ba. farkon ƙaddarar da abu ta fara masa kamar ɓacin rai, ƙwarai ya ji ransa na shirin ɓaci lokacin da yake jin hayaniya sama-sama daga wurin da ya san cewa tuƙa-tuƙa ne a wurin, yana da tabbacin masu ɗiban ruwa ne suke faɗa. Ba shi da saurin fishi, duk da ƙeta da mugunta da ya iya bai cika fusata da wuri ba, amma yau kam ya ji ransa na shirin baci da hayaniyar da bai san me ya haddasata ba. Ko dan ƙaddararsa ce za ta ja shi zuwa wurin? Oho. Tsaki ya ja a ƙasan numfashinsa. Sannan ya kalli Damulo dake riƙe da waya yana laluben lambar Alhaji Sidi.
“Ka je ka raba faɗan can, hayaniyarsu za ta tashi kaina”
Ya umarci Damulo da bai san hawa ba bare sauƙa.
“To Oga”
Ya amsa yana nufar wurin da tuƙan yake.
“Damulo!”
Ya ƙira, Damulo ya dakata sannan ya juyo yana amsawa.
“Ka kori kowa daga wurin, duk wanda ya yi gardama ka caka masa wuƙa, sauran faɗan kuma ka bar mini shi”
Ya ƙarasa maganar cikin ƙarfin hali yana miƙewa tsaye, dan ji yake kamar wani abu ne ke jansa zuwa wurin da ake tada wannan hayaniyar.
“To Oga”
Damulo ya sake amsawa sannan ya juya. Yayin da shi kuma ya miƙe, sannan ya koma ya zauna, sake miƙewa ya yi yana jan tsaki. Sai kuma ya yanke shawarar zuwa da kansa, dan haka ya nufi wurin da sauri, har ya tadda Damulo a hanya bai ƙarasa ba, dan akwai ‘yar tazara tsakaninsu da wurin, shi yasa yake mamakin yanda aka yi hayaniyar take zuwa wurin da suke. A dai-dai lokacin da suka haura saman wani dutse shi da Damulo abin ya faru, domin yana tsayar da ƙafarsa a kan ƙasa yayi tozali da ita, dai-dai lokacin da ta ruƙo wata, sanna ta jata baya ta tureta har sai da ta faɗi, tar iska take ɗauko masa kalaman da ta yi a lokacin, wahid warra sani (ɗaya bayan ɗaya) take ɗura masa su a kunnensa.
“Wallahi! Wallahi! Wallahi! Idan har kika kuskura kika taɓa bokitin nan sai na miki duka a wurin nan!”
Yanayin fuskarta ya nuna cewa a fusace take, sannan yanda laɓɓanta ke furta kalaman ma kaɗai ya isa yasa ka gane cewa ta fusata da gaske. Abu na farko da ya fara kalla bayan wannan shi ne wasu ‘yan ƙananun gashi da suka fito daga ƙasan ɗankwalin kanta, suka yi wa kansu masauki a saman goshinta, sai kuma gashin girarta da bai cika sosai ba, amma kuma har sun kusa haɗewa da juna. Sai kuma idanuwanta, a fusace take, jan da suka yi na ƙara bayyanar da alamun ɓacin ran da take ciki, gashin da suka kewaye mabuɗar idon nata na sama da na ƙasa dogaye ne, musamman ma na saman, sannan ƙwayar idonta da take juyawa a cikin idon nata. Sai kuma hancinta, dogo ba wai can-can ba, a ƙasan hancin kuma akwai ɗan ƙaramin bakinta da aka tsaga mata shi dai-dai da dacewar tsayin haɓarta, a cikin haƙwaranta na sama akwai siririyar ushirya da take nan kamar an tsaga mata ita.
A karo na farko wani abu ya motsa a zuciyar Guru, wannan ne karo na farko da ganin ‘ya mace ya jijjiga nutsuwarsa da kuma tunaninsa, wacece? Wace aljana ce a cikin jinsin aljannu da ta isa ta gigita nutsuwarsa, har ta kai ga ya fasa aiwatar da wani abu da yake da niyya a kai, duk duniya bayan Tsohon Malaminsa Malam Yakubu babu wanda ya isa ya hana shi yin abu kuma ya hanu ɗin, amma a yau, a yanzu, waccan farar hallitar da hasken rana ya haska masa ita ta hana shi yin wani abu ba tare da ta furta ko da kalma ɗaya ba, wannan wani irin sihiri gareta da ya yi aiki a kansa? Tambaya mafi a’ala wacece ita?
“Wacece ita?”
Tambayar ta tsaga laɓɓansa biyu ta fito, sautin ma kamar ba nasa ba, kamar wanda aka yi wa dolen furta maganar.
“Wai ba ka santa ba Oga? Aminatu ce fa!”
Amsar da Damulo ya ba shi ta sa ya fahimci a fili ya yi tambayar.
“Aminatu? Wace Aminatu?”
Ya dawo masa da tambayar sunan na haddace kansa a cikin kansa.
“ ‘yar gidan Malaminka, Malam Yakubu!”
-----------------
_Ni dai ba ruwana, ƙafar Guru ta kai shi wurin da alamu suke nuna zai sha wahala kafin ya fita_
_Akwai matsala fa jama’a! ‘yar Malam da Ɗan daba? Wannan gamin ganbiza ya yi yawa_
_Shin a ganinku wace yarinya ce za ta yarda ta zo ta kula da Maryam da alamu suka nuna cewa ta haukace, haukan ma mai duka_
_Bayan mutuwar Abdallah me ya biyo baya?_
_Ku dai ku ci gaba da bina sannu a hankali za mu kai inda kuke son a je_
#SalmaAhmadIsah
#MiniCandy
#Bahadejia
#KawaZuci
~~~~~~~~~~~~~~~~~~
*KAWA ZUCI*
*©SALMA AHMAD ISAH*
*10*
*PSG (Paris Saint-Germain) Training Center, Camp des Loges, Paris.*
HAMMAD POV.
Gaba daya ‘yan wasan club ɗin ne ke training a cikin ƙaton training ground ɗin dake centern, duk sun bazu a ko ina suna atisaye bisa jagorancin Coauch ɗinsu. Tsaye yake a cikin filin, sanye cikin baƙin jogger trouser da farar jersy irin wadda ke jikin sauran abokan wasan nasa. Sai woollen hat dake kansa ya naɗa scarf a wuyansa, saboda sanyin da ake a gari, shi da abokinsa Henri BB suke nasu training ɗin.
Da ƙarfi Henri ya buga ƙwallon da suke passing da ita, tana isowa inda yake ya tareta da ƙafarsa ta hagu, ya ɗora ƙafarsa ta dama a kan ball ɗin, ya yi knee block ya sakata a tsakiyar kafafunsa biyu, sannan ya yi slap ya haɗa da Rocket launch ta hanyar ɗagota da ƙafarsa ya cafeta da hannunsa ya cilla sama, kafin ta faɗo ƙasa ya sa ƙafarsa ta hagu ya bugata da ƙarfi, bisa tsammanin za ta isa ga BB, sanya hakan a cikin tunaninsa yasa dawowar ball ɗin ya zo masa a bazata, dan bai ankara ba sai da ta dawo ta daki ƙirjinsa da mugun ƙarfin da saida ya faɗi ƙasa. Faruwar lamarin tasa hankalin kowa ya dawo kansu, Hammad bai damu da ya kalli waye ke da wannan aikin ba, dan ya san duk cikin club ɗinsu mutum ɗaya ne zai aikata hakan.
Nicolas Wande! Kuma yana ɗaga kansa suka yi ido huɗu da shi, tsaye yake a kansa yana murmushi, shi dai a duniya ya rasa abin da ya tarewa bawan Allahn nan, amma haka kawai ba ya sonsa, tun sanda ya fara bugawa PSG ƙwallo har zuwa yanzu da ya shafe shekaru uku a Paris ba su taɓa dai-daitawa da Nicolas ba, tun abin na iya tsakaninsu har ta kai ga kowa ya fara fahimtar hakan. Shi dai Hammad bai ga dalilin da
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 8 Chapter of 14