sosai da wanda muke Sch d'aya da kuma wanda suke cikin Family
d'in mu , amman bantab'a jin soyayyar su araina ba kamar yadda lokaci d'aya naji soyayyarki ,
tun had'uwar mu naji kin shiga raina sosai tamkar wacce muka fito ciki d'aya , dan Allah Aysha
inaso kibani shawara akan Soyayyata da Khalid , tunsan da mukazo gidan nan naku nida shi
har yau ban kuma samun kan sa ba , kullum da irin uzirin da yake bani kwata kwata ko kirana
bayayi a waya , gashi in nakirashi nan ma sai ya katse yace aikine yayi masa yawa , kuma yau
d'in nan da safe Daddy ya tabba tar min da rashin zaman sa sosai a kasuwa , narasa me ke
damun Khalid kwata kwata da ya canza lokaci d'aya , hawaye ne suka taru a idanun Ruma ta
rik'e hannun Aysha tam taci gaba da magana " wallahi Aysha ina mutuk'ar k'aunar Khalid
shiyasa na damu , Aysha tausayin Ruma ne ya rufe ta cikin ranta tace " tabbas na tausayawa
Zuciyarki data kamu da Soyayyar wanda yake Gaibu , a fili kuma ta zame hannun Ruma daga
nata tana mik'ewa tsaye , juyawa tayi tana kallon mirrow wanda take hango Rumar ta ciki tana
share hawayen ta , a hankali Aysha tace " shawara 'Daya zan iya baki a yanzu itace ki hak'ura
da Khalid , kallo ta Ruma tayi sannan tace " meyasa zakice narabu dashi ? Aysha cikin ranta
tace " saboda baku dace dashi ba , shi mugune azzalumi ke kuma salaha ce me mutunci wacce
tafito daga gidan mutunci , a fili kuma tace " Abinda yasa nace kirabu dashi bawai ina nufin
kirabu dashi kidaina kulashi ba a'a inaso kibashi nan da kwana biyu muga yadda za'ayi , indai
har cikin kwana biyun nan bai zo wajen ki ba to tabbas Khalid ya canza budurwa sai mu shirya
d'amarar k'wato shi , Ruma tayi shuru tana nazarin maganganun Aysha , tabbas Aysha
gaskiya tafad'a mata dan Mumyn ta ma sai da tace mata hakan , dan haka cike da gamsuwa ta
yarda da shawarar Ayshar ta shirya yin hakan , Aysha ganin ta amince yasa tace " gaskiya
Ruma inaso ki rage damuwa dan kin rame sosai , dubi yadda kika fige tamkar wacce tayi jinya ,
Ruma tayi murmushi sannan tace " wallahi wanda inyi jinya akan yadda zuciyata ke gasuwa ,
Aysha tayi tsaki sannan tace " wallahi soyayya batayi ba , shiyasa bana d'orawa kaina wannan
tension d'in dan bazan iya ba , iya kacina da maza kawai in anshi 'yan canji na inbar su , dan
nasan wallahi soyayya b'ata lokaci ne kawai , Ruma ta kalli Aysha tana mamakin kalmar da ta
fad'a , a hankali tace " Aysha wai kina nufin kice baki tab'a Soyayya ba ? kuma wanne canji
kike karb'a a wajen maza har kika fi fifitashi akan Soyayya ? Aysha tayi murmushi tace " amsar
tambayar ki nanan tafe nan bada jimawa ba , dai dai lokacin aka kira sallar Magriba , toilet
Aysha ta fad'a tayo arwala tare da shimfid'a sallah ya dan gabatar da sallah , Ruma da yake
fashin sallah take shisa bata mik'e ba har Aysha ta idar , duban ta Aysha tayi sannan tace "
kizo muje muci abinci dan yunwa nakeji ni , Ruma tace " sai da naci abinci nataho kawai muje
kici kirakani hanya zan tafi , Aysha tace " malama muje kawai muci abinci tare , nasan bawani
abinci kika ci ba kina wannan damuwar , haka suka fito palor suka samu Gogal ta tashi , kan
Dinning Aysha ta kallah aikuwa Gogal gar tagama girki , Ruma tace " gaskiya Aysha bakida
murunci nasan girkin nan Mama ce tayi , zama sukayi kan Dinning Aysha na bud'e kular abincin
, dambun shinkafa tagani wanda yaji kayan lambu wada tattu sai k'amshi yake , tuni Aysha taja
filet ta zuba musu suka fara ci............
[11/08, 3:43 pm] Maman Islam: *'YAR HANNU*
🤒🤒
_NA_
*Zee* *MD*
*WOMEN WRITERS ASSOCIATION* 📚
(Domin Marubuta Mata )
✨ (W.W.A) ✨
https://www.facebook.com/106752595253176/posts/107924965135939/
*Bisimillahir Rahamanir Rahim*
_Page._ 26
Shurun da Aysha tayi ba k'aramin tayar da hankalin Hameed yayi ba , duban ta
yayi cike da sallama wa aran sa baza ta soshi ba ko kuma wani ya riga sa , a hankali ya furta "
kinyi shuru Aysha plss dan Allah kidaure kice min wani abu wallahi zuciya ta gab take da
bugawa , k'wayar idanun sa ta kallah nan ta hango zallar soyayyar ta da k'auna , tabbas
dagaske yake yana son ta amman baza tayi saurin yadda dashi ba , dan lokaci da Farouq yazo
mata kusan shima da irin wannan salon yazo mata , dan haka haryan zu tarasa yadda ake
gano soyayyar gaskiya , duk da idanun Hameed sosai ya fallasa abinda ke cikin zuciyar sa ,
jikin ta a sanyaye tace masa " inaso kabani lokaci plss komai na yanke zakaji ni , Hameed ya
dubi Aysha kamar zaisa kuka yace " inajin kafin lokacin d zaki d'ibar min kibani amsa ta to zaki
iyajin zuciya ta ta buga na mutu , dan Allah Aysha ki tausaya min zuciya ta bak'uwa ce a
soyayya , akan ki tafara so kuma akan ki zata k'are shi ki tausaya min , Aysha tace " kabani ko
zuwa gobe ne sai muyi magana , komai na yanke zakaji kuma kadaina damuwa sosai kar ka
rauna ta zuciyar ka , sosai Hameed yaji dad'in kalmar k'arshe da Aysha ta furta masa , bayan
sun tab'a hira yayi mata sallama tare da ansar phone number ta......
Hameed na tafiya Khalid yazo ko gida bata shiga ba , yana k'araso wa ya janyo ta jikin sa
yana shin shinar ta kamar wani bunsuru , ture sa tayi da k'arfin ta sannan ta shiga magana "
haba Khalid a cikin gidan mu fa kake meyasa kake min irin hakan ? yanzu in wani yagan mufa
shikenan ka janyo min magana , Murmushi yayi sannan yace " Sorry Babyna kinsan in kina tare
dani ji nake kamar ko da yaushe in kasan ce cikin lallausan jikin naki , tab'e baki Aysha tayi
sannan tace " ina kayana suke ? Khalid yace " Muje daga motar sai muyi hira daga nan ki
d'auko abinki , Aysha samun kanta tayi da jin tsoro batason meyasa bataso Hameed ya ganta
tana irin wannan rayuwar ba , a gaskiya baza ta fita tashiga motar Khalid ba gudun kar
Hameed yaganta , tunda bai b'oye mata komai ba ya sheda mata a cikin unguwar gidan su yake
shima , kallon Khalid tayi sannan tace " bazan iya zance ba yau saboda kaina yana min ciwo ,
kasan dai yau tunda rana muke tare don haka kayi hak'uri zuwa gobe , Khalid bai so haka ba
kwata kwata dan so yayi su shiga motar ko k'irjin ta yasamu yasha zai rage ruwan marar sa da
yataru , amman sanin halin Aysha in batason abu to bazatayi ba yasa ya k'yaleta , juyawa yayi
ya nufi cikin motar ya d'auko mata ledojin kayan ta , yana kawo mata ta ansa tana fad'in "
yakama ta fa kaje wajen Ruma dan tadamu dayawa , Khalid yaja tsaki sannan yace " k'yaleta
dan Allah wallahi saboda takurar ta nakashe wayata , Daddyn tama ya kirani nayi masa k'aryar
banajin dad'i kwana biyu , Murmushi Aysha tayi sannan tace " yakamata dai ka duba ta ko sau
d'ayane , tsaki yaja sannan yace " mezan samu a tare da ita in ba kayan haushi ba , kwata
kwata bata wani waye ba kullum kanta a duhu yake , kawai ki share ta zan d'aga wayar ta in ta
kira ince mata banjin dadi , Da haka sukayi sallama Aysha ta shige cikin gida abinta , shikuwa
Khalid yana tsaye ya k'urawa Mazaunan ta idanu har tashige abinta Sannan yatafi......
Tunda Aysha ta shiga gida tayi sallah sannan ta kwanta , sai dai ko alamar bacci bataji
saboda daman ba baccin takeji ba , tunanin Hameed ne ya dami zuciyar ta dan dagaske ta
gano zallar k'aunar ta a k'wayar idanun sa , itama tun sanda ya taimake ta taji acikin zuciyar ta
ya kwanta mata , Abinda yasa take share sa sabida tana jin tsoron maza , duba da yadda ko
wanne namiji in suka had'u dashi bashi da buri sai ya kusan ce ta da iskan ci , amman zata
fallasa masa kanta ta sanar dashi ko wacece ita , in har yaga zai amince mata to in kuma jin
hakan zai nisan tasu dama ita bata saka akai ba , da haka tagama tunanin ta tare da d'auko
wayar ta ta kunna data , tana hawa Whaspp taga tarin sak'onni daga maza kala kala , haka
tashiga duba na dubawa tana share wad'an da basu da amfani ......
Ruma tana komawa gida bayan tayi wanka ko abinci bata kallah ba , dan dambun dataci a
gidan su Aysha ya k'osar da ita , Mumyn tace t dube ta tace " wai Ruma ko kun samu sab'ani da
Khalid ne naga kwana biyu baya zuwa ? Murmushin takaici Ruma tayi sannan tace " ko d'aya
Mumy kawai dai bansan me yake damun sa ba kwana biyun nan , Daddy ma yace ko kasuwa
yanzu baya zuwa sosai kuma inna kira sa a waya baya d'agawa , Mumy tayi shuru tana nazari
kafin tace " tabbas to akwai wani abun amman kiyi masa test ko zaki samu kiji meke damun sa ,
Ruma tace to Mumy zanyi masa insha Allah , daga haka ta mik'e tayiwa Mumyn sai da safe ta
nufi d'akin ta .....
Tana zuwa ta bud'e data ta hau Whaspp , sak'onni ne suka shiga shigowa saboda
dad'ewar datayi bata hau ba , duk wad'an da suka mata magana k'awayen tane sai wata
Number guda d'aya wacce bta san taba taga kamar anturo mata pic , kamar zata wuce sai
kuma ta fasa ta dawo tashi ga , tana shiga cikin pic d'in k'irjin ta sai da ya buga ganin wanda
yake jikin pic d'in , Khalid tagani yana shan Nonon wata budurwa wacce bataga fuskar ta ba ,
zoom d'in hoton tayi ta k'ara tabbatar da ba gizo ida nun ta keyi mata ba , a hankali ta furta "
Khalid dama haka kake ? shiyasa ya guje ta saboda tak'i yarda su kauce hanya , kullum burin
Khalid yatab'a jikin ta , takan ce masa yayi hak'uri suzama Mallakin juna har gajiya sai yayi da
ita , wato bazai iya hak'ura har lokacin da zasuyi aure ba sai da yaje yana neman mata ,
hawayen dake gangaro wa a fuskar ta tayi saurin gogewa , tabbas Khalid ba mijin aure bane
tunda ya kasance fasik'i , tamkar zata kira Aysha sai kuma ta fasa gudun kar ko tayi barci ta
dameta , number da aka turo mata sak'on tashiga kira , sai dai akashe ake ce mata haka tai ta
gwadawa amman ana sheda mata tana kashe , number Khalid tashiga kira tana ring amman fir
yak'i d'agawa , tabbas ta hak'ura da Khalid koda shine autan maza , kuka sosai Ruma take
tanajin tsanar Khalid na ratsa jikin ta , ta yanke wa ranta ba wanda zata sanar wa da abinda
tagani , kawai dai baza ta k'ara kula Khalid ba itama ta hak'ura da sonshi koda zai kashe ta , da
wannan tunanin Bacci b'arawo yayi gaba da Ruma......
Washe gari Aysha na tashi ta d'auki layin da ta turawa Ruma hoto tasa akan waya , tana
shiga whaspp taga alamar Ruma taga sak'on da ta tura mata , murmushi Aysha tayi sannan ta
d'auki layin datake amfani dashi tashiga kiran Ruma , dai dai kokacin Ruma na zaune a cikin
d'akin ta na tunani , koda kiran AYSHA yashigo da sauri ta d'aga tana jin wasu zafafan hawaye
na zubo mata , murya a sanyaye tace " Yar uwa dafatan kin tashi lafiya ? Aysha tanajin
muryar Ruma tasan kuka tasha kuma tasan wannan pic d'in data gani ne zai sa ta kukan ,
Aysha tace " lafiya lau natashi 'Yar uwa sai dai kuma tunda naji muryar ki nasan 'Yar uwa ta
tana cikin damuwa , ina fatan ba akan wannan Guy d'in kike damuwa , plss 'Yar uwa banason
kidunga saka damuwa aranki , haka kawai ya saka miku ciwon zuciya yazo ya gudu ya barki ,
aikuwa Ruma me jiran k'iris tuni tashiga rera kuka tamkar 'yar goye , kukan da Ruma keyi har
cikin zuciyar Aysha , dan har ga Allah itama tana k'aunar Ruma , dan haka takeso tayi ta rabata
da Khalid ko hankalin ta ya kwanta itama , nan Aysha ta shiga kwantar wa da Ruma hankali har
tasamu tayi shuru , duk da Ruma bata shedawa Aysha abinda yasa ta kuka ba , itama kuma
bata tambaye ta ba tunda tagane sak'on ta datakeso ta isar ya isa , nan sukayi sallama tare da
yi mata alk'awarin itama zatazo gidan nasu gobe , ......
Bayan sungama waya da Aysha Ruma tasake gwada number da aka turo nata pic , ga
mamakin ta sai taji number ta shiga ba bata lokaci , sai da ta kusa katsewa sannan aka d'aga
tamkar ba'ason magana , Ruma tace "naga sak'on da aka turomin da wannan Number , sai dai
inaso in sanar miki ko kad'an ban damu ba , shida ma namiji ai inyayi abu ado ne agaresa
kuma hakan bazai tab'a mana soyayyar mu ba , inaso kisani in so kike ki rabamu to ina me
tabbatar miki da kinyi kad'an , yanzu nafara son Khalid har sai yazamo mijina , Murmushi taji
anyi mata cike da gadara da isa sannan aka furta " haba 'yan mata ki kama bakin ki , ai Khalid
ya ruga da yayi miki nisa sai dai ki hangesa , kuma wannan pic din ba komai bane akan abinda
muke yi da Khalid , inhar kina so ki tabbatar da waye Khalid to gobe da misalin k'arfe biyar na
yamma kizo Taheer gate place hotel zaki abinda zai baki mamaki , kitt aka kashe wayar batare
da ta yi magana ba , Ruma sake bin wayar tayi amman sai jitayi har ankashe , badan tanason
Khalid tace haka ba kawai tanaso tagane ko shiri ne ko kuma gaske ne , amman lallai gobe sai
taje Taheer Hotel taga abinda akeson tagani , dan itama tanaso takama Khalid da hujja wacce
zata tabbatar masa da tasan waye shi , .........
*Comment* plss
*'Yar Mutan Kanawa* _Ce_ 🌹💞💔
[11/08, 3:43 pm] Maman Islam: *'YAR HANNU*
🤒🤒
_NA_
*Zee MD*
*WOMEN WRITERS ASSOCIATION* 📚
( Domin Marubuta Mata )
✨ (W.W.A) ✨
https://www.facebook.com/106752595253176/posts/107924965135939/
*Bisimillahir Rahamanir Rahim*
_Page._ 29
Tabbas Jabir ya wuce duk tunaninta , Mamakin yadda yasan sirrikan ta tashiga yi ,
koda yake bazatayi mamaki ba duba da tun farko dama tasan shu'umine sosai , shiyasa tun
farko taji jinin ta bai had'u dashi ba amman duk da haka sai bibiyar ta yake , yanzu gashi yana
neman janyo mata Gogal tayi fushi da ita , kuma hakan ba k'aramin tashin hankalin ta bane dan
ko kad'an batason Gogal tayi fushi da ita , duk duniya bata da kowa sai Gogal itace gatan ta
itace duk wani farin cikin ta , da ita tabud'i ido tun tasowar ta dan haka dole ta guji duk wani
abunda zai b'ata ranta , gashi Dr. Yace mata tana gab da kamuwa da matsala a kwakwalwar ta
, duk da Aysha ta k'udur ta aran ta bazata k'ara aikata zina ba tunda har shirinta na k'arshe
yau takeson kammala shi , Amman tuni taci Alwashin tabbas saita koyawa Jabir Hankali dan
haka itama zata bibiyesa batare da yasani ba , ......
Wayar tace tashiga ruri ta duba dan ganin me kiran nata , Khalid ne haka ta katse batare
da ta d'aga ba , wata tsanar sa ce ke nunkuwa a zuciyar ta duk sakon na duniya , zama tayi a
bakin gadon ta tashiga tunanin yadda zata samu wacce zata tura Hotel anjima , tabbas tasan
Ruma zataje Hotel d'in dan ko iya wayar da sukayi ya tabbatar mata da hakan , whaspp d'in ta
ta bud'e tashiga wani group datake ciki , duk wad'an da suke group d'in *'Yan Hannu ne* dan
daga masu yin lez sai masu neman maza , duk da bata magana a group d'in amman sukan
biyota Prvt tallata Hajar su , duba Contact d'in su tashiga yi d'aya bayan d'aya , tsayawa tayi a
Contact d'in wata tsaleliyar budurwa me suna Leeemah , take Aysha ta kunna data tare da
shiga direct Message tace mata Hy , aikuwa taci sa'a Leeemah na kan online tuni ta dawo mata
da Reply na Hy My dear you'r welcome , Aysha tace " kozan iya magana dake in babu damuwa
? Leeemah tace " bawata damuwa Uwar ruwa ina jinki , sunan da Aysha ke amfani dashi shine
Uwar ruwa , Aysha tace wani aiki nakeso zakimin yaud'in nan inba damuwa ? Leeemah tace "
fad'i komai kikeso kan ki tsaye zanyi miki shi , Aysha tace yanzu dai kina wane gari dan inji ,
Leemah tace "Ina garin Kano unguwar Gadon k'aya , Aysha tace " gud inaso kimin wani aiki
anjima a Hotel d'in Taheer gate palace , Leemah tace angama Uwar Ruwa fad'i yadda aikin zai
kasance , Nan Aysha ta sheda mata tana so su had'u a Hotel d'in k'arfe hud'u da rabi dai dai ,
daga nan zatayi mata bayanin yadda zata yi aikin , take Leemah tayi Na'am nan suka gama
magana , Aysha kafin ta kashe datar ta ta kuma nemo Number Ruma ta tura mata voice d'in
muryar Khalid , wanda yake fad'in bason ta yake ba kawai saboda kud'in Mahaifin ta yake
kulata , amman da zarar ya aure ta yasamu kud'i to zai auri kalar matar da yakeso , harda
yadda yake cutar Mahaifin Rumar a kasuwa batare da yasani ba , duk voice d'in da sukayi sai
da Aysha ta turawa Ruma sannan a k'asa ta rubuta " ko zaki iya sheda wannan muryar waye ?
daga haka ta kashe datar ta ta sauka gaba d'aya daga kan Whaspp d'in ......
Wajen k'arfe Uku Aysha ta shirya cikin shigar ta ta kamala tafito , d'akin Gogal tashiga
tasa meta a zaune tana jan cazbi , durk'usawa Aysha tayi sannan tace " barka da wannan
lokacin Gogal ya jikin naki ? ba yabo ba fallasa Gogal tace jiki da sauk'i , Aysha tace "Allah
yak'ara miki lafiya da nisan kwana me amfani , Gogal bata amsa da Ameen d'in data saba ba
tayi shuru , Aysha takuma risinawa tace " ga Abinci can a kan Dinning nadafa miki ni zan wuce
makaranta , Gogal batare da ta dube ta ba tace " Allah ya kiyaye Aysha ta mik'e ta fita......
Koda ta fito sai da tagama dube duben ta bataga kowa ba sannan ta kama hanyar fita
bakin titi , wayar ta ta ciro tashiga kiran number Leeemah , tana d'agawa tace mata gatanan
tana shirin fitowa itama , nan Aysha ta kashe wayar sanan ta kira number Khalid , yana d'agawa
yace " Sweet yau kwata kwata kin ki bari naji muryarki dayawa , muna fara waya kike katsewa
kodai nayi laifine ? murmushi Aysha tayi sannan tace " babu laifin dakayi yau nayi busy ne sosai
, to Babyna ina fatan baki gaji da yawa ba dan kinsan yau zan danneki dayawa , Aysha wani
takaici taji ya kamata amman sai ta dake tace " bangaji ba My Baby kasan akan ka zan jure
komai , Khalid cike da murna yace " dama zakiyiwa Uncle d'inki dabara da munkwana tare
mufaran ta ran juna sosai , Aysha tace " karka damu zan gwada nagani ko zai barni , Khalid
har wani shauk'i yake yana ce mata shifa tun yanzu zai shirya dan ya matsu da yawa , itama
tace masa yanzu zata shirya taje takama musu d'akin tunda ya turo mata kud'in , nan sukayi
sallama Aysha tana duban wayar tana murmushin mugunta.....
Ruma wajen k'arfe uku ta d'auki wayar ta tana shiga Whaspp , sak'onni ne suka shiga
shigowa cikin wayar a ciki ta kuma ganin number da aka turo mata pic d'in Khalid , hannun ta
har rawa yake wajen bud'e sak'on taga me suka sake turo mata , tana bud'ewa taga Voice
guda uku ajere , tuni ta bud'e bayan ta karanta rubutun k'asa , Muryar Khalid tashiga ji yana bai
yana yadda yake shirya komai , jikin ta har tsuma yake tanajin wata iriyar tsanar Khalid , bayan
duk tagama ji ta mik'e da saurin ta ta nufi d'akin Mumyn ta , tana zuwa ta kunna mata Voice d'in
Muryar Khalid itama tashiga ji , bayan tagama ji ta kamo mata hotunan da aka turk mata tare
da sheda mata ance k'arfe Biyar taje Hotel d'in Taheer taganewa idon ta komai , nan Mumyn ta
tashiga salati tare da cewa bari takira Daddy ta sanar masa dan suma suje Hotel d'in dan
tabbatar wa , aikuwa koda suka sanar masa cewa yayi sutaho Hotel d'in su had'u acan dan
shima dama yagaji da abinda Khalid d'in keyi masa na rashin zuwa kasuwa , ashe ashe akwai
abinda ya taka shiyasa yake haka , .....
Tuni Ruma da Leeemah sun Bayyana a Hotel d'in Taheer , tana gama kama d'aki ta nemi
Number Ruma ta tura mata Room number d'akin , ciki suka shiga nan ta tsarawa Leeemah
komai yadda zata tafiyar dashi , basu dad'e da zuwa ba saiga Khalid ya iso sai faman zabga
k'amshi yake , akan idanun Ruma da iyayen ta ya fito daga motar batare da yagan suba ya nufi
Reception.........
*kumin Comment kuga ruwan Typing*✍🏻😜😝😝
[11/08, 3:43 pm] Maman Islam: *'YAR HANNU*
🤒🤒
*NA*
*Zee* *MD*
*WOMEN WRITERS ASSOCIATION* 📚
( Domin Marubuta Mata )
✨ (W.W.A) ✨
https://www.facebook.com/106752595253176/posts/107924965135939/
*Bisimillahir Rahamanir Rahim*
_Page._ 27
Washe gari tunda safe Aysha take shirya yadda Khalid zai shiga hannu , tunowa
tayi da jiya yace mata 2m .A account d'in sa kuma sunje shopping ta cinye masa 1m da dubu
d'ari uku , ya siya mata gold sark'a da kuma zobuna , yanzu in ta auna cikin Account d'in
Khalid saura dubu d'ari Bakwai , dole yanzu zata shirya cinye sauran canjin daya rage masa ,
dan bataso ko canji ta bar masa bare yaji dad'in cutar wasu agaba , tanaso ta maida shi talakan
k'arfi da yaji tunda dama motar dayake hawa ta gidan su Ruman ce Yake d'auka , wata dabara
ce ta fad'o mata da sauri ta d'auki waya zata kira Khalid , wata Number tagani ana kiranta da ita
, da kamar bazata d'aga ba sai kuma wata zuciyar tace d'aga kiji ko waye , d'agawa tayi tare da
yin shiru batayi magana ba , daga cikin wayar taji muryar Hameed yana fad'in Assalamu
Alaikum , muryar tasa tuni ta ratsa duk wani sassa na jikin ta , idanuwan ta ta lumshe sannan
tace " wa'alaikas salam , Hameed wata ajiyar zuciya yaja dan duk a tunaninsa baza ta d'aga
wayarsa ba amman sai gashi ta d'aga , My Angel dafatan kin tashi lafiya kuma ina fatan dai ba
bacci kike na tashe ki ba ? Murmushi Aysha tayi karo na farko a rayuwar ta dataji 'Da namiji ya
burgeta , kuma wannan shine karo na farko da aka tab'a kiran ta tare da tambayar ta tashi lafiya
, duk Namijin da zai kira ta sai dai yace mata A inah zasu had'u ko kuma yana Hotel kaza tazo
tasa mesa , baruwan su da tambayar lafiyar ta su dai kawai burunsu tazo su aikata Fasik'an ci
, karo na biyu dataji ta tsani zina dan bata da wata riba sai dai k'arshe ma ka had'u da tarin
dana sani , a hankali ta furta masa " natashi lafiya kaima ina fatan hakan daga gareka ,
Murmushi Hameed yayi har Aysha najiyo sautin yace " lafiya lau nima natashi sai dai zuciya ta
datake d'auke da farga da tarin k'alubale , Aysha ta d'an fito da ido a tsorace tamkar yana
gaban ta tace " wanne irin Fargaba da k'alu bale kuma ? murmushi yayi sannan yace " Zuciya
ta tana jiran amsar da zata samu daga gareki kinga kuwa dole na kasance cikin fargaba ,
Murmushi tayi sannan tace " kar kadamu komai zai zo da sauki kawai dai kajira lokacin yayi ,
Hameed yace " lokaci ya kusa tunda zuwa anjima zanji komai dan haka yau kisa aranki kina da
mara lafiya mai buk'atar tallafin ki , murmushi ta kuma yi tace " sai najika ta kashe wayar
batare da tajira yace mata wani abun ba , kallon wayar tayi tamkar me gano Hameed d'in aciki
tace " in na biye masa sai yaja zancen da hira har nazo na furta abinda zuciya ta bata yanke ba
, .......
Number Khalid ta nemo sannan ta shiga kiran sa , sai dai har ta katse bai d'auka ba ko
baya kusa da wayar ko kuma yana bacci , ajiye wayar tayi sannan tafito palor dan ganin ko
Gogal ta fito , bata gan ta ba hakan yasa ta shiga kitchen ta hau girka musu abinda zasuyi kari
dashi , Kunun gyad'a ta dama tare da soya musu dankalin turawa , tana gamawa ta d'auko ta
ajiye akan dinning sanna ta d'auki na Habu ta mik'a masa , koda ta shigo cikin d'akin ta ta koma
sannan ta fad'a wanka toilet
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 9 Chapter of 13