Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ya duk'a yana bawa Aysha hak'uri tare da yin alk'awarin bazai k'ara yi mata makamancin abinda yayi ba , sannan yayi mata alk'awarin fita daga dukkan al'amuran ta , Aysha ta dubesa tace " shikenan sai a kiyaye , ra juya zata shiga cikinngida , da sauri ya mik'a mata mukullin motar ta yace ' gashi kiyi hak'uri karki turawa budurwar tawa videon plss , murmushi tayi sannan tace bazan tura ba amman gaba in ka kuma hakan wallahi itace zata fara kallon episode 2 kafin kai kagani , kumq mukullin mota ka koma da ita gobe in ka kaita car wash sai ka kawomin abata sai da safe , batajira cewar saba ta komar da gate d'in gidan ta rufe abinta......... *Nagode Sosai masu bibiyar book d'ina , masu min magana ta prvt ina k'ara godiya sosai da sosai , Masoyana ina Alfahari daku a duk inda kuke*😍😘😍😘🤝🏻🌹 _Masoyana kune ni inbaku nima babu ni_🌹 *Taku a koda yaushe* _'Yar Mutan Kanawa_ 🤝🏻🌹 [11/08, 3:43 pm] Maman Islam: *'YAR HANNU* 🤒🤒 _NA_ *Zee* *MD* *WOMEN* *WRITERS* *ASSOCIATION* 📚 ( Domin Marubuta Mata ) ✨ (W.W.A) ✨ https://www.facebook.com/106752595253176/posts/107924965135939/ *Bisimillahir Rahamanir Rahim* _Page._ 20 Kamal yashiga bin bayan Motar Aysha tamkar zasu tashi sama , Aysha naganin haka tasamu wani waje ta faka motar sannan ta fito a fusace , dai dai lokacin suma su Jabir suka k'araso wajen sai maida numfashi yake , saukowa yayi da sauri yana nufo wajen ta ya shiga fad'in " Aysha meyasa kike guduna ? meyasa bakyaso muhad'u dake ? Aysha ta dubesa a wulak'an ce tace " meye had'ina dakai ? taya zaka shiga rayuwata duk inda nayi kadunga bina ko kana bina bashi ne ? Jabir ya gyara tsayuwa yana duban Aysha yace " Aysha ina sonki sosai kuma son danake miki shine dalilin dayasa nake bibiyar Al'amarinki , inaso kisani wallahi duk abubuwan danake fad'i akanki da kuma tona miki asirin danace zanyi a gun kakarki ina fad'a miki haka ne dan ki shiryu , tun farkon had'uwa ta dake zuciya ta takamu da soyayyarki , dan Allah Aysha ko sau d'aya ne kibani dama na nuna miki soyayyar dana ke miki plss , Yadda Jabir ke magana da kuma irin kalaman da yayi ba k'aramin tasiri yayi a zuciyar Aysha ba , duk wani haushin sa datakeji sai gashi tasamu kanta da sakkowa , ganin yanayin ta ya canza hakan yabawa Jabir daman k'ara shigar da kansa... Aysha k'ofar gidan ku nan ne yazamo wajen zamana a koda yaushe , kullum sai na dunga ganin kamar zanganku kundawo zaku bud'e gidan , Kullum cikin yawo nake a gari ko Allah zai had'ani dake , sai yau Allah ya cikamin burina na ganinki , dan Allah Aysha ki fahimceni wallahi da gaske nake inasonki sosai , Aysha ta dubesa ido cikin ido dan ganin ko zata hango aibun Jabir , Jabir bashi da makusa dan kyakkyawa ne ajin k'arshe , gashi cikakken Namiji dashi komai ya had'a matsalar sa kawai rashin kud'i , dan kana ganin sa kasan bashi da abun yi ko ayanayin sittirar sa , sunfi minty 3 a haka sannan Aysha tace " naji duk maganganun ka kuma zan duba nagani sai muyi magana , Jabir yace " to yanzu kifad'a min inda kuka koma plss inaso inzo sai muyi maganar , Aysha cikin ranta tace " nan fa d'aya dan bazan aminta dakai da wuri ba har sai na gwada ka , a fili kuma tace " ni babu inda muka koma kawai Gogal tana garin mu nikuma ina Hotel da zama , kawai kabani number ka sai muyi magana , Jabir batare da yakawo komai ba ya karantawa Aysha Number sa , bayan tasa Number tayi masa sallama ta shiga motar ta tayi gaba abinta...... Kamal ya dubi Jabir yace " Abokina gaskiya wannan yarinyar me zafi ce , a inah kasamo ta haka dan ko yadda ka rud'e kad'ai yasa na tabbatar da tana da muhimman ci a gunka , murmushi Jabir yayi sannan yacewa Kamal " Aysha ta daban ce a cikin mata Abokina , tuntuni zuciya ta tayo farautar ta , duk da nasan tafi k'arfina amman ko soyayya mukayi ai nasan nayi nasara , Kamal ya dubi Jabir yace " Kasan irin wannan matan wallahi ba matan yara bane , koda sun auri yaran to sai dai in yakasan ce yaro da kud'i abokin Manya , Jabir yace " nima kasan me zan zama agaban ko zanyi kud'in da sai na auri balarabiya ma , Kamal yasa dariya yana fad'in " kana zaman lungun Abokina ? sai katashi kafara nema dan irin wannan matan ko siyan turare suka had'a ka dashi wallahi aikine , nan suka hau lifan d'in su suna hira wacce dukan ta akan Aysha ne........ Wajen shopping Aysha taje nan tashiga d'ibar abubuwan da zatayi amfani dasu , tana dube duben ta taji muryar da bazata tab'a mantawa da ita ba wato muryar *Khalid* , jiyowa tayi a hankali tana kallon inda taji maganar ai kuwa Khalid ne shida wata budurwa wacce ta juya baya bata ga fuskar ta ba , da sauri ta kauda kanta tare da yin gaba tashiga wani b'angaren , lek'en su tashiga yi dan tana son ganin fuskar budurwar dasu tare da Khalid d'in , duk yadda taso taga budurwar abun ya faskara dan kwata kwata ba wajen take kallo ba , ita kuma gashi batason Khalid d'in yaganta da sai taje taduba fuskar budurwar tagani , tana tsaye har suka gama siyayyar suka juya zasu bar gun , koda budurwar ta jiyo sai Aysha taga face mark ne a fuskar ta tare da wani siririn glass , dafe kai Aysha tayi na rashin ganin cikakkiyar fuskar yarinyar , haka suka fice daga Shopping d'in batare da ta ga fuskar taba , bayan fitar su itama zuwa tayi ta biya kud'in kayan ta sannan ta fito...... Koda Aysha ta dawo gida duk ranta a mutuk'ar jagule yake , dan duk abinda zai tuna mata da Khalid bata k'aunar sa a cikin rayuwar ta , Khalid shine sanadin lalacewar ta , yadda ta tsani Khalid haka ta tsani mutuwar ta , Khalid ya cuceta yakuma yaudare ta ya lalata mata rayuwa , hawaye ne yashiga zubowa daga idon ta tashiga tuno yadda yake mata dad'in baki lokacin suna tare , kwanciya tayi dan jin yadda kanta ke sarawa bacci ne yayi gaba da ita batare da ta shirya ba ....... Hameed waya yake da Asibitin sa nacan k'asar London , neman sa suke sosai saboda tarin marasa lafiya da sukayi yawa , nan ya shiga basu uziri tare da sheda musu k'arshen wata yana tafe , yana kashe wayar Hajiyar sa ta dube sa tace " Yakamata ace ka koma aikin ka Hameed , ni haryan zu bansan abinda yadawo dakai k'asar nan ba alhalin lokacin zuwanka baiyi ba , Habeeb ya dubi Hajiyar sa yace " nafad'a miki akwai aikin da nazo yi Hajiya amman nakusa kamma lawa , Hajiya tace " Allah ya taimaka kuma inaso kafin katafi kaje gidan Kawun ka ku gana da Abida , kaga wata da wowar da zakayi kawai sai dai ayi maganar aure tunda itama nasan lokacin ta kammala karatun ta , Hameed nan da nan fuskar sa ta canza dan kwata kwata bayason anayi masa zancen wata Abida , to kawai yacewa Hajiyar tare dayin hanyar fita daga falor , da ido Hajiya ta bishi cikin ranta tana fad'in " yanzu kamar kai Hameed sai anta yi maka maganar aure , Allah ya kyauta yaku saka kagane......... Ruma bayan sun dawo daga Shopping ita da Khalid suka zauna hira a babban palor gidan , Ruma ta dubi Khalid tace " My one amman kana ganin in nakaiwa k'awata wannan shopping d'in zataji dad'i ? Khalid yayi murmushi yana duban Ruma sannan yace " taya bazata ji dad'i ba kuwa , ni wallahi Baby har tsoron wannan k'awar taki nake , daga had'uwar ku duk tabi ta shiga ranki ko kulawa kindaina bani , daga munfara zance kin ringa zancen had'uwar k'awarki da cewa kaza kaza , kin manta kema me kyau ce kuma kema gwana ce wajen sace zuciyoyin mutane , Murmushi Ruma tayi sannan tace " bazaka gane irin yadda ta shiga raina bane , kuma ai kasan matsayinka daban yake a guna babu abinda ya canza , kawai dai nasan K'awata ta had'u kuma ta shiga raina dayawa , har sauri nake k'arfe hud'u tayi muje gidan su sai kagan ta ka tabbatar da nayi had'add'iyar k'awa , Murmushi Khalid yayi sannan yace " ai k'arfe hud'u da ita ake magana dan haka sai ki fara shiryawa ,...... Aysha baccin ta take sosai hankali kwance abinta , Gogal sau biyu tana lek'owa cikin d'akin tana ganin bata tashi ba , ana fara kiran sallar la'asar Aysha ta farka d'auke da salati a bakin ta , toilet kawai ta fad'a don yin wanka tare da d'auro arwala , bayan ta fito tazo gaban mirror tashiga shiryawa , kwalliya tayi bamai yawa ba sannan tasaka kayan ta , atamfa tasa riga da siket wacce ta anshi jikinta , Aysha akwai k'ira shiyasa maza dayawa suke susucewa indai suka kalli k'ugunta , bata d'aura d'an kwali ba kawai wani k'aramin gyale ta yafa ta nufo palor.... Samun Gogal tayi tana kallon tashar Arewa sun sako wani film , zama tayi a d'aya daga cikin kujerun Palor tana fad'in Sannu da hutawa Gogal , Gogal ta dubeta tace " ke zanyiwa sannu da hutawa Sayyada , yau naga kinsha bacci sosai tunda zuwana d'akin ki sau biyu kina bacci , Aysha tace " kaina ne yakemin ciwo shine nasha magani na kwanta , Gogal tace " ayya Allah ya sauwak'e amman ya daina ko ? Aysha tace ea yadaina tunda nayi bacci , Gogal tace " kitashi kije kitchen ki d'auko abinci sai kici watak'il harda yunwa ma , Aysha tace " me kika dafa mana ? Gogal tace " shinkafa da wake sai kuma na yanka kayan lambu da k'wai dafaffe , Aysha tanason wake da shinkafa shiyasa ta mik'e da sauri ta nufi hanyar kitchen , sallamar Ruma itace ta tsayar da Aysha tare da juyawa tana kallon inda akayi sallamar , Ruma tagani a tsaye tana murmushi , itama Ayshar Murmushi tayi tana nufo wajen Rumar tana fad'in " oyoyo K'awata sannu da zuwa , Shigowa ciki sukayi Ruma ta zauna tana fad'in " kinganni da zumud'i ko bari banyi kin kirani kince kindawo ba nataho , cike da jin kunya Aysha tace bandad'e da shigowa ba nayi wanka zan kiraki sai gaki , a zuciya kuwa Aysha ta manta da wata Ruma ma musamman da ranta ya b'aci akan had'uwa da Khalid , gaisawa sukayi sannan Ruma ta durk'usa ta gaida Gogal , da fara'a Gogal ta amsa gaisuwar Ruma tare da yi mata sannu da zuwa , Aysha taje cikin kitchen ta d'ebowa Ruma ruwa da lemuka ta kawo mata , Gogal tashi tayi tabar musu waje , Ruma ta dubi Ayshs tace " nida wanda zan aura mukazo fa , yana waje cikin motar kizo muje ku gaisa , Aysha tace " Masha Allah kice da Mijin namu kike tafe bari na d'auko Hijab d'ina sai muje mu gaisa , Ruma tace " haba k'awata wanne irin hijab kuma nida nakeso yaga k'awata yasan babu k'arya ta had'u , badan Aysha taso ba tacewa Ruma to muje amman sai dai na tsaya daga ciki kishigo dashi harabar gidan , Ruma tace " na yadda nan suka fito harabar gidan , Ruma ta fita waje dan shigo da Khalid ita kuma Aysha ta zagaya dan d'auko kujerun da zasu zauna , lokacin data d'auko kujerun guda biyu a lokacin suma suka shigo cikin gidan , tunda ga nesa Aysha ta hango Khalid jere da kafad'ar Ruma suna hira cike da so da k'auna , kujerun ne suka fad'i daga hannun ta da sauri ta dafe k'irji , wato Khalid shine wanda Ruma zata aura ? ashe dama Ruma ce tagani d'azu a wajen Shopping ita dashi ? to yanzu yazatayi yadda Khalid bazai gane taba ? wata zuciyar tace mata ai yanzu da da ba d'aya bane , lokacin da Khalid yasanki kina salaharki koda yaushe cikin Hijab da Nik'af , yanzu kuma kin canza tunda kin k'ara girma komai na jikin ki ya fito sannan kin k'ara haske da gogewar fata , da wannan shawarar Aysha ta nutsu ta saita kanta tare da nufo wajen da suke tsaye , murmushi tashiga yi dan kar su fahimci komai , kuma tanason ta nunawa Khalid ba ita bace yadda zaifi sakin jiki , tana k'arasowa shima Khalid ji yayi gaban sa ya fad'i , cikin ransa yashiga fad'in " wannan tamkar Aysha duk da a yanzu baisan inda suke ba , Aysha cike da saita murya tace " barka da zuwa Mijin K'awata , wani Murmushi Khalid ya k'ak'alo yana fad'in " Barka kadai K'awar mu dafatan munsame ku lafiya , ajiye masa kujera tayi tana fad'in " bisimillah kazauna sannan ta ajiyewa ruma itama , juyawa tayi tace ina zuwa bari na d'auko tawa nima sai musha hira , tana juyawa Khalid yabi mazaunan ta da kallo yana had'iyar wani mugun yawu , tabbas wannan ta cika mace irin wannan k'ugu haka , inama itace zai aura da yakwashi gara , har Aysha ta k'ure idon Khalid na hanyar da tabi , Ruma sai magana takeyi amman baisan tanayi ba , duban sa tayi taga inda yake kallah take taji wani kishi ya soketa , a tsawace tace " wai me kake kallo ne haka ina magana kamin shuru ? firgigit yayi yana fad'in " wallahi yanayin gidan yayimin kyau shine nake kallon ko inyi irin wad'an can bukkokin anamu gidan , Ruma taja ajiyar zuciya tace " nima gidan ya burgeni sosai yakamata kayi mana irin bukkar , Khalid yayi murmushi yana fad'in " angama gimbiya ta yadda kikeso haka za'ayi , dai dai lokacin Ayshs ta taho rik'e da kujera a hannun ta , ido Khalid ya kuma zuba mata inda ya hanyo dukiyar fulanin ta sun cika riga a tsaye k'yam suna kallon sa , Ayshs dataga yadda yake kallon ta tuni tafara karkad'a ko inah ns jikin nata , take Khalid yafara jin wani Abu na yawo a jikin sa...... [11/08, 3:43 pm] Maman Islam: *'YAR HANNU* 🤒🤒 _NA_ *Zee* *MD* *WOMEN WRITERS ASSOCIATION* 📚 ( Domin Marubuta Mata ) ✨ (W.W.A) ✨ https://www.facebook.com/106752595253176/posts/107924965135939/ *Bisimillahir Rahamanir Rahim* _Page._ 22 Khalid yana kai Ruma gida ya dube ta yace " My luv ni zanje gida zuwa Bayan isha'i insha Allah zanzo ko , Ruma ta langab'ar da kai sannan tace " Haba My Baby naga ai magariba tayi kawai kashigo kaci abinci kayi sallah kaga basai ka koma gida ba , Khalid cike da k'aguwa dason yatafi dan yakoma gidan su Aysha yace " sorry My Wifey yanzu zandawo kedai kawai ki shirya min abinci me dad'i , yana fad'in haka ya shige motar da sauri dan bayason ta tsareshi da surutun ta , yana jan motar Ruma na d'aga masa hannu har yafice daga cikin gidan ,..... Aysha na zaune suna hira da Gogal , rabin hirar duk akan Ruma ne Aysha kebawa Gogal labarin Ruman , Sai hirar su suke cike da nishad'i suna dariya , Habu ne ya katse su d'auke da Sallama abakin sa , amsawa sukai yadubi Aysha yace " kinada bako a k'ofar gate yana jiranki , Aysha ta maimaita kalmar Bak'o kuma ni yake nema ? Habu yace " ke yake nema dan har na shigo dashi nabashi kujera yana harabar gidan , Gogal da saurin ta tace " kaje kace masa gatanan zuwa , Habu ya amsa da to sannan ya fice daga Palor , Aysha tadubi Gogal tana turo baki tace " nifa bani da wani bak'o dazai zo gashi kince ace ina zuwa haka mukayi dake ? Gogal ta mik'awa Aysha dak'uwa tana fad'in " ungo naki Aysha wai meyasa bakyason kiyi aure ne ? to wallahi ahir d'inki nagaji da ganinki a gabana , dagani sai kefa muka ragewa junan mu , tun kina yarinya nake kewar dangi wasu sun mutu wasu kuma ban san ina suke ba , yanzu Aysha in kikayi aure Allah yabaki yara ai zanji dad'i , inaso kafin nabar duniya nabarki a hannun wanda zai zamo komai naki Aysha , Aysha sosai jikin ta yayi sanyi tadubi Gogal tace " kimin addu'a Allah yabani miji nagari shine kawai burina , nan tq mik'e ta nufi d'aki dan d'akko gyale taje taga waye yazo kuma da me yazo...... Khalid yana zaune sai latsa wayar sa yake hankali kwance Aysha tafito , tunda ga nesa tagane waye dan haka taja ta tsaya tana duban sa , murmushi tayi cikin ranta tana fad'in " tabbas me hali baya canza hali koda ya shekarw d'ari baka gansa ba to halin sa nanan ... Ganin duk tsayuwar ta bai san ta fito ba yasa ta nufi wajen sa cikr da yanga , d'agowa yayi yana kallon ta tare da zubawa k'ugun ta kallo , ganin yadda ya zubawa k'ugun nata idanu yasa ta kuma jujjuyashi har ta k'araso , sallama tayi cikin kissa da kashe murya sannan tace " ina fatan dai lafiya ? Khalid ji yayi tamkar ya rungumota dan muryar ta tama abin sauraro ce , a kasalance ya amsa " lafiya lau Aysha dama wani muhimmin abune yakawoni wajen ki , Aysha taja kujerar dake kusa dashi ta zauna tana fad'in " Bisimillah inajinka , Khalid yace " dan Allah anan garin kike tun asali ko kuma zuwa kikai ? Murmushi Aysha tayi sannan ta gyara zama tace " gaskiya ni banfi wata biyu da zuwa garin kano ba , amman asalina ni 'yar garin yobe ce acan iyayena suke nan nazo gidan uncle d'ina ne , Khalid wata ajiyar zuciya yayi jin ba Aysha bace kawai sunan ne yazo d'aya dakuma kamar su , amman wannan ai tafi Aysha kyau gogewa tare da cikar jiki , murmushi yayi mata sannan yace " dan Allah kuma baku da wasu dangi anan garin dan kina min kama da wata dana sani ? Aysha cikin zuciyar ta wata irin tsanar Khalid takeji , haka ta daure tabashi amsa da cewa " gaskiya banda Uncle d'ina bamu da kowa agarin nan kuma matar sa har yanzu bata haihu ba , wata ajiyar zuciya yaja sannan yace " tabbas kama ce kawai dan waccen ma a wajen Kakar ta take , kuma sana'ar k'osai sukeyi talakawa ne sosai , basu da wasu dangi masu kud'i ma bare ince kun had'a dan ganta ka , Aysha sosai takejin zafin maganganun Khalid tare da wata tsanar sa a ranta , murmushi tayi sannan tace " shikenan dama abinda yadawo da kai kenan ? Khalid yayi murmushi yace " ea kuma a'a dan gaskiya inaso mu k'ullah abota kibani phone number ki , amman dan Allah karki fad'awa Ruma kinsan bazataji dadi ba , cikin zuciyar Aysha tace " anzo wajen yanzu wasan zai fara , a fili kuma tace " taya zan gaya mata dama ina neman wanda zai dunga fita dani ina ganin gari dan bansan ko inah ba , Khalid jiyayi kamar yatshi yafara taka rawa , cikin ransa yake fad'in " dole na kore k'ishirwata a wannan lafiyayyan jikin , a fili kuma yayi wa Aysha godiya tare da ansar contact d'in ta , yana gama saka number kiran Ruma na shigowa cikin wayar sa , wani guntun tsaki yaja cikin ransa yana fad'in " mace babu aji sai nacin bala'i , shifa kawai ya yarda zai auri Ruma ne saboda kud'in Mahaifin ta dan yasan tunda ba d'a namiji garesa ba kuma itace babba a gidan komai wajen sa zai dawo , shiyasa yake ta kwantar musu da kai yana kuma sanin komai nasu .... Nan ya d'aga yana cewa tayi hak'uri tabashi minty 30 gashinan , bai jira tabashi amsa ba ya katse wayar tare da duban Aysha , murmushi tasakar mai tana fad'in " k'awata ce takira kenan ? kai ya d'aga alamun ea sannan ya mik'e yana fad'in " ni zan zo na tafi sai ki shirya gobe mufara fita ko , Aysha ta mik'e tana turo k'irji tare da yin wata mik'a wacce indai namiji lafiyayye ne sai sandar sa ta mik'e , aikuwa tuni Khalid yayi mutuwar tsaye yana kallon k'irjin Aysha , jiyayi tamkar ya kai musu cafka ganin yadda suke tsaye k'yam suna kallon sa , lura da Aysha tayi ya fita a hayyacin sa yasa ta matso gab dashi tana fad'in " mezan sa a number taka ? sosai jikin ta yake gugar nasa jikin take ya duburbur ce yana fad'in " kisaka Kha lid , sunan ma ya kasa had'eshi saboda yanayin daya shiga , nan Aysha tayi masa sai da safe ta juya tana kad'a d'uwawu tayi cikin gida....... Binta yayi da ido yana kuma kallon girman mazaunan ta har ta k'urewa ganin sa, da k'yar ya iya saita kansa yasamu yabar cikin gidan nasu....... *Bayan kwana biyu* Tuni Aysha da Khalid sun d'inke ko yaushe suna tare , kullum yana hanyar zuwa gidan su tare da d'aukar ta sufice wajen shan ice cream da sauran su , duk zuwan dayake bata bari ya shigo saboda kar tsautsayi yasa yaga Gogal shirin ta ya lalace , kuma duk fitar dasuke kullum cikin cewa Gogal tafita koyan motar dan haka bata samun wata matsala ,... Ruma sosai tashiga damuwar canzawar da Khalid yayi , dan kullum bata samun wata kulawa daga garesa , ko waya suke basa minty 5 sai yace mata yana zuwa shikenan bazai k'ara kiran ta ba sai dai ko ita takirashi , haka zaita shimfid'a mata k'aryar wai kwana biyu aiki yamasa yawa shiyasa amman tayi hak'uri yakusa dawo wa dai dai , Ruma ta yadda da k'aryar da yayi mata shiyasa bata kawo komai ba ta amince masa ,.... Ranar da sukayi wata fita sosai Khalid yasamu had'in kan Aysha ta yadda ya tab'a jikin ta , murna sosai ya shiga yi a zuciyar sa yana fad'in " da sannu zan kai wajen da nakeso , itama Aysha a zuciyar ta tace " ka kusa zuwa inda nakeso kazo , lokacin da Khalid yake tab'a kirjin Aysha a cikin motar yana kai bakin sa a lokacin ta faki idon sa ta shiga yi masa Vedio , bayan sun rabu dashi tasamu layin ta wanda yake a k'asa ta d'ora ta nemo number Ruma ta whaspp ta tura mata wannan videon , yana shiga ta cire layin tare da ajiyeshi tana murmushin mugunta ,.... Ruma tuntana yadda da uzirin da Khalid ke bata har tadaina , gashi Daddyn ta yace mata kwana biyu Khalid baya zama sosai a kasuwa , kullum da wuri yake ficewa daga kasuwar , zama tayi tana nazarin can zawar sa da yayi lokaci d'aya , tamkar wacce aka zabura ta mik'e ta nufi d'akin ta dan d'auko wayar ta , kiran Aysha zatayi dan taje gidan su tabata shawara akan Khalid dan gaskiya tunanin sa na [11/08, 3:43 pm] Maman Islam: *'YAR HANNU* 🤒🤒 _NA_ *Zee* *MD* *WOMEN* *WRITERS* *ASSOCIATION* 📚 ( Domin Marubuta Mata ) ✨ (W.W.A) ✨ https://www.facebook.com/106752595253176/posts/107924965135939/ *Bisimillahir Rahamanir Rahim* _Page._ 21 Ruma sai magana takeyi takuma jin shuru , d'agowa tayi a hankali ta tana duban sa nan taga hankalin sa gaba d'aya baya gunta , duban inda yake kallo tayi taga Aysha rik'e da tire a hannun ta ta nufo wajen nasu , wani kishi Ruma taji ya rufe ta ta yadda Khalid yake kallon Aysha , da k'afa ta zunguri Khalid firgigit yadawo hankalinsa , dai dai lokacin Aysha ta k'araso d'auke da murmushi tana fad'in " kuyi hak'uri na barku shuru ko , duk da nasan kuna nan kuna hirar ku irin ta masoya , Murmushin yak'e Ruma tayi dan kwata kwata Khalid ya b'ata mata rai , zama Aysha tayi tana ajiye lemukan data kawo musu , duban Khalid tayi tace " bisimillah Angon Ruma ga abin sanyi kasha , Khalid jin maganar Yasake tabbatar wa da kan sa lallai wannan Aysha ce , dan babu abinda ya ragu a muryar ta sai dai kawai yadda ta goge sosai tamkar wata 'yar bariki , duban ta yayi yana murmushi yace " muna godiya sosai k'awar mu , Ruma dai bata tanka ba dan har yanzu tanajin zafin abinda Khalid d'in yayi , sai yanzu taga haukar ta na tahowa da saurayin ta gidan su Kawa , duba da irin yadda Ayshar ta had'u komai yaji ajikin ta babu Namijin da zai ganta batare da yakuma duban ta ba , ganin tayi shuru Aysha tace " Kawata lafiya kuwa naga kinyi shuru ? Ruma tayi murmushin yak'e tace " kaina ne yake sarawa yana ciwo , Aysha tace " Ayya sannu bari nashiga na samo miki magani sai kisha , Ruma tace " kibarshi ma ai yanzu zamu tafi inyaso naje gida sai nasha , Aysha tace " habadai tun yanzu zaku tafi kuma gashi ko lemon dana kawo muku baku sha ba , Ruma tace " kiyi hak'uri zanzo miki zuwa na musamman sai muyi hira amman yanzu kinga kaina ciwo yake , Aysha dayake ta fahimci abinda yasa Ruma canzawa lokaci d'aya kawai murmushi tayi tace " to shikenan Allah yabaki lafiya sai munyi waya , Khalid kwata kwata baiso su tafi yanzu ba dan gaskiya yanaso yaita kallon Aysha ko zai ga abinda yakeso yagani , haka ya mik'e jiki a sab'ule suka tafi....... Murmushi Aysha tayi bayan fitar su sannan tace " yarinya tabbas zaki wahalar da kanki akan wannan

Chapter 7 of 13