Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
fasik'in , har yanzu Khalid bai canza hali ba duba da yadda yayi ta kallona , amman lokacin canzawar sa yayi dan yanzu wasan nata kanshi zai juyo....... Tunda Ruma suka baro gidan su Aysha ba wanda yace da wani kanzil , ita tanajin haushin sa na irin yadda yadunga kallon Aysha shikuma yanajin haushin ta na yadda tak'i bari su dad'e , ganin shurun yayi yawa yasa Ruma yin magana "Khalid meyasa muna tare dakai amman idanunka na wajen da ba muhallinka ba ? Cikin zuciyar sa ya furta indai zanga mace irin wannan a gabana ai bazan iya duban ki ba Ruma , a fili kuma yace " haba My luv amman sanake ko labari zaki iya rubutawa akaina ki shedar halina , kinfi kowa sanin waye ni sannan kinfi kowa sanin irin k'aunar dana ke miki , ko sch d'inku kinsha min k'orafi akan bana sakarwa k'awayen ki fuska , meyasa yanzu zakimin wani kallo daban ? karki manta abinda yasa nasaki jiki a gurin wannan k'awartaki saboda yadda naga kin d'aukaketa , amman insha Allah ko hanyar gidan su bazan k'ara ba tunda har hakan zai fara shiga tsakanin mu , tuni Jikin Ruma yayi sanyi tafara dana sanin zargin Khalid d'in datayi , cikin siririyar murya tace " kayi hak'uri Dear idanuwa na sun rufe a kan ka shiyasa , ganin yadda Ruma ta sauko yasa Khalid cigaba da shigar da ita " bakomai my luv ai nasan kishine akan abinda kike so kikayi amman ki sa aranki ke kad'ai ce mace tafarko kuma ta k'arshe data samu gurbin zama a zuciya ta , daga ke kuma bana buk'atar kowacce mace duk kyanta , wani dad'ine ya rufe Ruma tuni tasaki jiki tashiga zubawa Khalid kalaman soyayya tare da alk'awarur ruka da dama in sunyi aure , Shima haka yashiga tsara ta da nuna mata bayan ita baya buk'atar kowacce mace a rayuwar sa , cikin zuciyar sa kuwa Allah Allah yake yakai ta gida yadawo wajen wannan me kama da Ayshar dan yanaso ya tabbatar da wacece ita , ... Hameed yau ma ya fito da k'udirin sake duba Aysha , dan kiran da ake masa a k'asar London yayi yawa so yake yakoma , gashi abun yana neman kaishi ga kwanciya ciwo , dan kusan kullum baya bacci sai tunanin Aysha wanda yazamar masa jiki , yana k'ok'arin fita daga get d'in gidan su ita kuma Abida tana k'ok'arin shigowa , karo sukayi kowanne yaja da baya yana duban d'an uwan sa , Abida cike da so da k'auna ta dubi Hameed tace " Yaya Hameed ina yini , Hameed batare da ya dube ta ba yace " lafiya sannan yasa kai ya fice batare da yakuma bi takan ta ba , da idanuwa ta bishi tanajin wani sonshi na k'ara shiga ranta , tabbas Yaya Hameed ya had'u sosai ga kyau ga kud'i ta ko inah yayi , a hankali ta furta " duk yadda zanyi nasameka sai nayi Yaya Hameed , dan kaine irin mijin da nakeson kasancewa dashi miji na nunawa sa'a wanda ko wacce mace zata so samun irinsa....... Hameed na fita yashiga tsaki yana fad'in " mace ayita kwata kwata bata da aji , samun waje yayi nesa da gidan su ya zauna yana dube dube tamkar me hango wani abu , gani yake kamar zaiga Aysha ta b'illo ta wani gidan ... Koda Aysha ta shiga cikin gida tuni tafara karatun yadda zata fara yak'ara Khalid , tabbas duk duniya babu wanda ta tsana sama da Khalid , duk wani shirin ta na rayuwa shine ya rusa mata shi , tabbas zai gane Aysha da da ta yanzu ba d'aya bace , sai ta nuna masa yanzu ita cikakkiyar *'Yar Hannu* _Ce_ .......... Kuyi maneji plss🤝🏻 [11/08, 3:43 pm] Maman Islam: *'YAR HANNU* 🤒🤒 _NA_ *Zee MD* *WOMEN WRITERS ASSOCIATION* 📚 ( Domin Marubuta Mata ) ✨ (W.W.A) ✨ https://www.facebook.com/106752595253176/posts/107924965135939/ *Bisimillahir Rahamanir Rahim* _Page_. 25 Bayan sun kammala cin abincin Aysha ta dubi Ruma tace " 'yar uwa ta inaso in kuma baki shawara akan ki rage saka damuwa aranki , kici gaba da addu'a komai zaizo da sauk'i in sha Allah , nan Aysha tashiga bawa Ruma shawar wari tare da nasiha me saka nutsuwa , sosai Ruma tasamu nutsuwa har tasaki jiki suka shiga hira , sai Bayan sallar Isha'i sannan Ruma tamik'e tare da yiwa Gogal sallama zata wuce gida , Aysha ta yafo gyale zata rakata titi suka jero suna hira har suka fito daga gate d'in gidan , suna fitowa waje suka ci karo da Hameed yana fitowa daga motar sa , kwata kwata Aysha bata ganeshi ba shiyasa ta d'auke kanta tana bawa Ruma labari , da sauri Hameed ya k'araso yasha gabansu yana fad'in " Barkan ku da wannan lokacin , tsayawa sukayi turus Aysha tana duban sa , jitayi k'irjin ta ya buga saboda ganin fuskar Hameed , tabbas bayan Jabir anaci to lallai wannan Hameed d'in shine na biyu a shugaban 'yan naci , Ruma ce ta amsa masa da fad'in " Barka kadai bawan Allah , ya kalli Aysha yana murmushi yace " haba Aysha kin wahalar dani sosai kinsa nafara fita hayyacina , babu irin neman da banyi miki ba amman sai yanzu Allah yasa zan ganki , Aysha itama dai murmushin ta d'anyi tana fad'in " kayi hak'uri ina zuwa zan takawa 'yar uwata zuwa bakin titi , Hameed yayi murmushi yace " muje mana mu taka mata baki d'aya ai nima 'yar uwata ce , nan ya jera da su yana kusa da Aysha wacce yake jin bayaso tayi masa nisa ko kad'an , a haka suka k'arasa bakin titin unguwar da babu nisa me napep suka tarar mata Hameed yabiya kud'in Ruma tamusu sallama ta tafi , .... Juyowa sukayi tare Hameed sai jan Aysha yake da hira amman tak'i sakin jiki , wayar hannun tace tashiga ruru kiran Khalid yashigo , har ta yanke bata d'aga ba sake kira yayi akaro na biyu , Hameed yadube ta yace " wayarki fa ake kira yakamata ki d'aga kiji ko kiran nada muhimmanci , murmushin yak'e Aysha tayi sannan tace " nasan Gogal ce ke kirana tunda taji shuru , Hameed bai wani damu da jin hakan ba duk dayasan ba lallai Gogal d'in ce me kiran nata ba , suna k'arasowa k'ofar gidan Aysha ta kallesa suka had'a idanu dan shima idanun sa akanta yake , wani abu taji ya ratso ta kanta har jikin ta , batasan meyasa batason had'a idanuwa da Hameed ba , yana da kwarjini da cikar haiba gashi ingarman namiji , a Hankali ta furta " ni zan shiga gida dan akwai abinda zanyi , Hameed yadube ta sannan yace " Aysha wajen ki nazo yakamata ki tsaya ko sau d'aya ne kibani lokacin ki maganar da nazao da ita tana buk'atar zama , ji tayi bazata iya yi masa gaddama ba samun bakin ta tayi da cewa to kashigo daga ciki sai muyi maganar , aikuwa Hameed ji yayi tamkar ya taka rawa jin Aysha ta yadda su shiga daga ciki suyi magana , ada in yazo gidan su tana lek'owa tagansa zata juya abinta , amman gashi yau yasamu matsayin da har tace yashigo , suna shiga gidan sai da ya yaba tsaruwar gidan , amman yana mamakin taya Aysha suka dawo wannan gidan kodama Alhaji Na Lamma d'an uwan sune ? dan shidai yasan asalin gidan na Alhaji Na Lamma ne tunda suna gaisawa sosai , dan akwai wata jinya da Alhajin yayi lokacin yana gari shine yake dubashi sosai har yasamu lafiya , maganar Aysha ce ta katse masa tunani tace " bisimillah ka zauna ina zuwa , Hameed yaja kujera ya zauna fuskar sa d'auke da murmushi , juyawa Aysha tayi ta nufi cikin gidan Hameed ya raka ta da lumsassun idanun sa , cikin zuciyar sa yana tasbihi ga ubangijin da ya halicci kyakkyawar surar Aysha , dan ko ta inah Aysha ta had'u musamman idanuwan ta da dirin jikin ta , har ta shige ciki idanunsa na kan hanyar data bi tamkar ita yake kuma gani , bayan kamar minty 5 saiga Aysha ta fito sanye da hijab d'in ta har k'asa tayi ainahin shigar ta , hannun ta rik'e da tire wanda yake d'auke da lemo da ruwa a kai , tana k'arasowa tayi masa sallama sannan ta ajiye tiren hannun ta kan d'an madai daicin table dake gaban sa , itama kujerar ta janyo ta zauna sannan ta dube sa tace " Bisimillah ga ruwa kasha , Hameed yayi murmushi sannnan ya d'auki ruwan yana cewa " nagode sosai da wannan karramawar taki , ruwan yasha sannan ya ajiye yana duban ta a hankali ya furta " Aysha inso kibani aron minty 10 in gabatar miki da kaina , tun daga lokacin dana had'u dake zuciyata takamu da sonki sosai kullum innazo gareki bakya bani lokaci , a haka har na tattara nakaoma k'asar danake aiki wato London , koda nakoma mai makon in rage tunaninki sai ma k'aruwa da yayi dan kullum dake nake kwana araina , kwata kwata nadaina samun nutsuwa indai bansamu na keb'e nayi tunanin ki ba , ahaka har nafara gazawa game da aikina ina samun matsalaloli sosai , kinsan anaso koda yaushe yakasance likitoci suna samun nutsuwa dan su samu damar kulawa da mara lafiyar su , tunda na fahimci nima me jinya ne yasani na tattaro nadawo gida nageria , sai dai wacce nadawo domin ta bata san inayi ba dan ina durowa k'asar nan na nufi gidan ku amman ina zuwa nasamu gidan a kulle , Aysha naje gidan ku yafi a k'irga amman kullum a rufe yake , na tambayi 'yan unguwar ko sun san inda kukaje sai suce suma basu sani ba , nasha zaga gari Aysha akan nemanki amman Allah bai had'a ni dake ba sai yau d'in nan , duk naganki kwanaki amman kika nuna bake ceba haka yasa na k'yaleki naci gaba da bibiya har Allah yasa na samu nasara , zamowa yayi daga kan kujera yad'an matso kusa da ita yana magana a hankali " dan Allah Aysha ki taimaka ki anshi soyayyata ko zan samu sauk'i daga rad'ad'in da zuciya ta kemin , ina sonki da gaske kuma inaso kizama matata uwar yayana , Aysha tunda Hameed yafara magana taji duk kalaman sa suna ratsa jikinta , tabbas tasha ganin maza da yawa kuma tayi rayuwa dasu amman meyasa shi dayake mata magana takejin ta har cikin jikinta ? kodai shidin masoyin tane na gaskiya shiyasa takejin hakan ? tabbas badan tayi alkawarin bazatayi aure a rayuwar taba da babu abinda zai hana ta ansar soyayyar Hameed , sai dai kash bazata tab'a aure a duniya ba dan har yanzu bata yadda da soyayyar maza ba kawai tana kallon sune mayaudara wadan da basa son mace dan Allah sai dan wani abu nata , ........ *Kumin hakuri wlh nafita unguwa bansamu yin typing dayawa ba*✍🏻 [11/08, 3:43 pm] Maman Islam: *'YAR HANNU* 🤒🤒 _NA_ *Zee* *MD* *WOMEN WRITERS ASSOCIATION* 📚 ( Domin Marubuta Mata ) ✨ (W.W.A) ✨ https://www.facebook.com/106752595253176/posts/107924965135939/ *Bisimillahir Rahamanir Rahim* _Page._ 23 Aysha ta dubi Khalid tace " kasan da wa mukayi waya ? Khalid ya girgiza kai yana fad'in " taya zan san da wa kikayi nasan dai mace ce , Murmushi Aysha tayi sannan tace " Mutuniyar ka wai zatazo yau in ina gida , Khalid ya tab'e baki sannan yace " nasan indai tazo to sai tayi zan cena , kinsan Allah Baby ni nafison inyi rayuwa da wa yayyiyar mace irin ki , inason inga budurwa ta tana bani kulawa kamar yadda kike bani , Ruma babu abinda ta iya sai k'auyan ci itafa ko romance bata bari muyi , kullum sai ta runga cewa in k'ara hak'uri in mukayi aure tazama tawa komai sai yadda nayi dashi , ... Aysha tuni taji wani ciwo a zuciyar ta yataso , tabbas ko wacce mace me mutunci babban burin ta shine ta tsare mutuncin kanta , amman ita ta k'arfi da yaji aka b'ata mata mutuncin ta , ta sanadin haka yanzu gashi ta lalace ,hawaye ne suka cika mata idanun ta tayi saurin maidasu , dan bata so ko da wasa Khalid yasan damuwar ta , Khalid yaci gaba da magana " kin san wani Abu Baby ? Aysha ta girgiza kai alamun a'a , yace ko sau d'aya bantab'a son Ruma ba , saboda bata d'aya daga cikin Matan da nake da burin aura , kawai ina kulata ne dan kud'in Baban ta , kuma sannan ina son dukiyar kaf tazama tawa nan gaba bayan babu shi , Aysha ji tayi wata tsanar Khalid ta nunku a cikin ranta , tabbas Khalid azzalumine kuma sai takawo k'arshen zaluncin sa nan ba da jimawa ba , Murmushi tayi nasu na asalin 'Yan duniya ta dubesa tace " to meyasa ka yadda zaka aure ta bayan kuma bata d'aya daga cikin matan da kakeso ka aura ? Murmushi Khalid yayi sannan yace " Baby ai kinsan a k'ark'ashin Mahaifinta nake kinga da kunya 'yar sa ta nuna tana sona nak'i amincewa , da zarar komai yadawo hannu na zan iya rabuwa da Ruma ko kuma na auri wacce rai na keso , Aysha tace " gaskiya kai d'in ka iya buga game amman karkaje fa ayi maka Babban bugun da ya wuce naka , Dariya yasa yana fad'in " waye zai bugani alhalin ba wanda yasan meye a zuciya ta indai bake ba dana fad'a miki , kuma ni nasan ina da tabbacin bazaki fad'awa Ruma komai ba , Aysha tayi murmushi tace " haba Dear taya zan tona maka asiri , ai in nayi haka tamkar na tonawa kaina asiri ne nima , kadaina ma fad'in haka dan kasan ni taka ce kai nawa ba ta yadda za'ayi inga wani abu da zai zo ya kawo maka matsala batare da na kaudashi ba , haka Aysha ta karkace tashiga yiwa Khalid dad'in baki sosai , nan yayi mata alk'wari komai takeso tafad'a zai siya mata , ... Aysha tanajin haka ta kashe masa ido tace " account d'inka da zurgi kenan My Dear ? Khalid cike da shauk'in so yace "2 milloine acikin account d'ina yanzu , sai kinsan dayake ban dad'e dafara zuwa kasuwar ba , kuma ahakan ma ina had'awa da cuwa cuwa batare da me wajen ya lura ba , nan Aysha taji sirrin Kud'in da Khalid yake dashi , Murmushi tayi cikin ranta tace " yanzu zaka fara rabuwa da 1 Million kafin nan da kwana biyu ka rabu da sauran ma , cike da kissa Aysha tace " ni yanzu abinda nakeso kawai shine muje kasiyamin zobunan gold da sark'a dan ina son du sosai , Khalid ganin irin yadda Aysha ta kwanto jikin ta ajikin sa ga Na shanun ta rabin su duk sun fito yasa shi rud'ewa tare da cewa " muje Baby angama ,...... Jabir tunda suka rabu da Aysha yake ta dakon kiran ta amman shuru , gashi ya gwada layin ta amman baya tafiya kwata kwata , damuwa ya shiga sosai tare da fad'in " wato wayo Aysha tayimin batare da nagane ba , meyasa na yadda nabar ta ta tafi batate da nabi bayan ta ba ? tabbas indai yakuma ido biyu da Aysha bazai barta takuma raina masa hankali ba , kuma ai yagane number motar ta dakuma kalar motar tabbas zai ci gaba da neman ta tamkar yadda yayi kwanaki , ....... Yau saura kwana biyu Hameed yabar k'asar Nageria , hankalinsa sosai yatashi ganin har yakusa tafiya bai samu Aysha ba , yaje sau biyu unguwar su Aysha yana ganin ko Allah zai sa yayi sa'a sundawo , sai dai ko kad'an basu dawo ba kullum gidan arufe yake , yauma yana zaune a k'ofar gate d'in gidan su yana chat da wani abokin sa a can k'asar London , kwana biyu zaman cikin gidan baya masa dad'i saboda Hajiyar sa ta damesa da Maganar Abida , shikuma har ga Allah bason maganar yake ba , shifa indai ba Aysha ba haryanzu baiga macen data yi masa ba , dan acan ma London akwai mata wad'an da suke son sa sosai amman duk yak'i basu fuska........ Koda su Aysha sukaje wajen saida sark'ok'i , sai da Khalid ya siya mata na Million d'aya da dubu Hamsin , dan zab'a tayi sai dataji masu kud'i dayawa tace su takeso , Khalid sosai yaji fitar kud'in amman gudun kar ta gane ya dake tamkar wani Alhajin Birni , da suka taho hanya tasa shi ya biya da ita wani Shopping Mall tayi siyayyar dubu d'ari nan ma ya biya , Khalid suna fitowa ya nuna shima yanaso tabashi jikin ta dan haka su biya Hotel yakama musu waje , ko kad'an Aysha bata damuba dan dama jiran wannan ranar take , dan tasan daga wannan ranar bazai k'ara ganin Nonon ta bama bare jikin ta , haka sukaje Hotel Khalid ya kwashi gara sosai ,kusan sumewa yayi saboda sambatu dan iya jin dad'i yajishi a tare da Aysha , sai yake ganin ko nawa ya kashe mata bai fad'i ba ganin yadda ta rud'ashi shima , sosai yayi mamakin yadda Aysha ta k'ware wajen iya wasanni ,ko dayake bazai mamaki ba ganin ta wayayyiyar Yariya wacce tagaji da had'uwa, haka suka gama d'ebewar su sannan sukayi wanka suka nufo gida...... Aysha tun a farkon layin su tasa Khalid ya sauke ta , koda zata fita daga motar sai da Khalid yace " Babyna yaushe zamu kuma had'uwa ne ? dan gaskiya kinjiyar dani wani dad'in da ban tab'a ji ba sai sau d'aya , Murmushi tayi sannan tace " sau d'aya Dear ashe katab'a yin sex ? Khalid yace " natab'a kwanciya da wata yarinya duk ba'ason ranta ba mukayi kuma shine farkon yina nima bana cikin nutsuwa amman haryanzu abin na raina , Aysha wani abune yataho mata ya tokare k'ahon zuciyar ta , kallon sa tayi cike da tsana tace " Saboda me ya tsaya maka arai kuma alhalin kace ba'ason ranta kayi ba ? jin yadda tayi maganar yasa ya dube ta , sai sannan Aysha tayi saurin ankarewa ta sassauta muryar ta tace " sorry Dear tausayin yarinyar naji ,amman meyasa kayi mata haka Alhalin bataso ? Murmushi yayi sannan yace " gaskiya sha'awarta tadameni kullum in muna tare to sai kinga abata a mik'e saboda yadda nake shaawar ta , ban daina jin hakan ba har sai randa na kusan ce ta , tana kuka tana magiya amman haka idona ya rufe na keta mata mutuncin ta , Aysha jitayi kamar a lokacin Khalid yake keta mata mutunci , hawaye ne ya cika idon ta wanda ta kasa iya maidasu , tabbas Khalid ya zalince ta dan shine sanadin komawar ta wannan rayuwar , yanzu waye zai aure ta a irin wannan rayuwar tata ? Meza tacewa Yaranta dazata haifa nan gaba ? taso ace Mijinta wanda zai aure ta shine zaifara sanin ta a duniya , amman Khalid ya rusa mata duk wani shirin ta ya lalata mata rayuwar ta , yasa taci gaba da sab'on mahaliccin ta , duk da tashiryu bayan zubar da cikin da tayi wanda yayi mata , Farouq shine ya maida ta ruwa shima yasa ta koma *'Yar Hannu* , tabbas Khalid azzalumine ya cuceta a rayuwar ta , jin tayi shuru yasa Khalid yin magana yace " meye naji kinyi shuru My Baby ? wani guntun Murmushi tayi sannan tace " wallahi danaji abunda kayiwa Yarinyar nan sai na tuno da wani Malamina a makaranta nima da yayimin fyad'e , Khalid yace " ayya sorry Baby kice mugun malami shine yafara yi mana hanya , nima kinsan Allah nine nafara yiwa yarinyar nan hanya , daga baya tasamu ciki nikuwa nayi mata korar kare , dan a ganina taya za'ace daga kwanciya sau d'aya wai ciki yashiga ai tazo da iskanci , sotake na aure ta ganin bata da wani asali gasu talakawa ba k'aruwa yasa na yi mata fata fata muka rabu , Aysha jitayi in bata yi saurin fita daga motar Khalid ba to tana gab da had'a masa jini da majina , shiyasa tayi saurin d'aukar kayan ta tace "muyi waya My dear , bata jira cewar saba ta fice da sauri abinta , Khalid ko ajikin sa bai kawo komai ba sai ma bin Mazaunan ta dayayi da kallo yana kuma wassafo dad'in daya sha ajikinta....... Hameed yana zaune kamar ance masa ya kalli hanya ya hango Aysha ta nufo ta wajen dayake , da sauri ya mik'e yana murza idanun sa itace dai ba gizo take masa ba , kwata kwata Aysha bata kula da Hameed ba har tazo ta gifta ta gaban sa , haka yashiga binta batare da yayi magana ba , sai datazo k'ofar gidan su lokacin Habu na zaune yanajin radio ta wuce shi yana mata sannu da zuwa , da yauwa ta amsa ta shige ciki abinta shikuma Hameed yaja ya tsaya gana yiwa Habu sallama......... *Ina mutukar Son Comment d'inku Masoyana* _Yin Comment shine ke k'ara mana k'aimin yin Typing_✍🏻✍🏻 *Saina jiku* *'Yar Mutan Kanawa* _Ce_ 🌹😘🥰 [11/08, 3:43 pm] Maman Islam: *'YAR HANNU* 🤒🤒 _NA_ *Zee* *MD* *WOMEN WRITERS ASSOCIATION* 📚 ( Domin Marubuta Mata ) ✨ (W.W.A) ✨ https://www.facebook.com/106752595253176/posts/107924965135939/ *Bisimillahir Rahamanir Rahim* _Page._ 24 Habu ya amsa sallamar Hameed yana duban sa , Hameed yace " Abokina dan Allah inaso kamin magana da wacce ta shiga gidan nan , Habu ya dubi Hameed tabbas yaso gane fuskar sa saboda yana yawan zuwa gun Aysha da dad'ewa lokacin suna wancan gidan , Habu ya nisa sannan yace " gaskiya yanzu ta dawo daga Makaranta nasan ba lallai ta fito yanzu ba , sai dai ko kabari zuwa anjima in ta huta sai nayi mata magana , Hameed ya dubi Habu sannan yace " nan ne gidan su kenan ? Habu yace ea. Hameed yayi wata ajiyar zuciya kafin yace " nagode abokina xuwa anjima zan dawo nasan lokacin ta huta , nan yayi wa Habu sallama ya juya cike da murna ya nufi gida , tabbas yau yasan zai kwana cikin farin ciki na ganin wacce ya dawo Nageria domin ta , duk da yaso ace bai baro k'ofar gidan ba har sai yaganta , amman gudan Habu yace masa bazata fito yanzu ba yasa ya hak'ura , dan haka yanzu in anyi sallar Magriba zai shirya yaje gareta ya bayyana mata abinda ke zuciyar sa..... Aysha tana shiga tasamu Gogal na zaune tana kallo , bayan tayi mata sannu da gida ta shige d'akin ta dan ta watsa ruwa , tunowa tayi da siyayyar da tayi a motar Khalid tayi sauri d'aukar waya tashiga kiran sa , yana d'agawa yace mata " Babyna me kayan ruwa ya akayi kin barni da tunaninki tunda kika tafi , wani murmushin takaici Aysha tayi jin sunan da yaki rata dashi , cike da kasalalliyar Murya tace " My D nayi mantuwa a cikin motar ka , murmushi yayi sannan yace " nima sai yanzu nagani dan haka ni mantuwar nan tamin dad'i dan ko bakomi na sake dawowa na kalli kyakkyawar fuskar Mata ta , Wani abu Aysha taji ya tsirga mata a kwanyar kanta , ada lokacin datake Ayshar ta sanda takeson Khalid indai yace mata matar sa har wani dad'i takeji , amman a yanzu tamkar yasa mata dalmar wuta , dan ji tayi takuma tsanar sa a ranta , shurun da yaji tayi shine yasa yace " naji kinyi shuru Aysha ko nayi laifi dan naki raki da sunan Mata ta ? Da sauri Aysha tace " taya zanyi fushi naji ka kirani da kalmar da nadad'e ina jiran ta daga bakin ka , duk a tunani na kawai muna abota ne amman bazaka iya auren mace irina ba , Khalid ya zaro ido tamkar yana gaban Aysha yace " ni asuwa da zan k'i mace kyakkyawa irinki , ina kallon kaina ne kawai a wanda basu isa ki aura ba saboda yanayin ki da kuma irin gidan da kika fito , Murmushin mugunta Aysha tayi sannan tace " kadaina cewa haka My D kasan shi so baruwan sa da haka , sai dai ina ganin in mukayi haka tamkar zamuci amanar Ruma ne , Khalid yace " dan Allah kidaina saka wannan bagidajiyar a lissafi nifa nafad'a miki ko sau d'aya ban tab'a son taba , kinsan manufa ta akan ta ki kwantar da hankalin ki kawai kibani had'in kai , Aysha tace " karka damu Nawan nabaka , wani tsalle Khalid ya buga kafin yace " ina nan hanya in anyi sallar isha'i nasan lokacin Ruma tazo ta tafi , Aysha tace " shikenan sai kazo ta katse wayar sannan ta shiga wanka...... Tana fitowa takira Ruma a waya ta sheda mata ta dawo , bayan ta shirya cikin doguwar riga ta nufo palor wajen Gogal.... Tana zama suka shiga hira take shedawa Gogal takusa daina koyarwa a Makaran ta , Gogal ta dube ta tace " kin sami mijin aure ne Aysha da zaki daina koyar wa ? Murmushi Aysha tayi sannan tace " ina dai kan hanyar Samu sai ki kuma tayani da addu'a , Sallamar Ruma itace ta katse su daha hirar su , shigowa tayi tasamu guri ta zauna tana gaida Gogal , ta amsa tare da tambayar ta iyayen ta suna lafiya , Ruma tace "lafiya lau suke suna gaidake , hannun Ruma Aysha taja suka tashi suka nufi cikin d'akin Ayshar...... Koda shigar su Ruma ta dubi Aysha tace " zakiyi mamaki jin cewar inason muyi magana dake , Aysha ina da k'awaye

Chapter 8 of 13