da kika siyar ? Aysha a
zafafe tace masa " Ya isheni haka malam , inaso kafita daga cikin sha'anina tunda bansaka ka a
ciki ba , Jabir ya tab'e baki sannan yace " ai dama bance kisakani ba , kuma inaso kitanadi
wata k'aryar da zaki kuma yiwa Kakarki dan wannan lokacin kamar baki da mafita , yana kaiwa
nan ya juya yayi tafiyar sa .......
Da ido Aysha ta bi bayan Jabir tana mai maita kalmomin sa na k'arshe , me Jabir yake nufi
? kodai yakuma zuwa ya had'ata da Gogal ne ? indai hakane tabbas Jabir zai girbi hukuncin ta
nan bada jimawa ba , komawa tayi cikin motar ta zauna tana sak'e sak'en tare da tunanin inda
su Gogal sukaje , a haka har aka kira sallar Magriba bataga wasu masu kama sa Gogal ko
Habu ba , tuni gabanta ya shiga fad'uwa take ta tuna ai bata kira Habu taji ina suke ba , nan
tayi saurin d'aukar waya tare da kiran Habu aikuwa bugu d'aya ya d'aga , da sauri Aysha tace "
wai ina kukaje ne Habu nadawo naga gidan a rufe da kwad'o ? jin Muryar sa tayi a sanyaye
yana cewa " Muna tsohon gida , a zabure Aysha ta mai maita Tsohon gida kuma ? Habu yace
" Ea tun bayar fitarki ba dad'ewa Gogal ta fito tace mun inzo in raka ta Unguwa , Makarantar da
kike zuwa mukaje da ita nan tagana da Babban Malamin makaran tar taku , to nan san me yace
mata ba tunda muka taho hanya take zubda hawaye har muka iso gida , muna zuwa tasani na
nemo me napep ta d'ibi kayan sawar ta tare da cemin nima in d'ebo nawa zamu koma tsohon
gida , na tambaye ta meyasa amman haryanzu bata gayamin ba har muka dawo gida , tuni
Aysha tayi mutuwar tsaye ko motsi takasayi , tanajin Habu nata faman cewa Hello hello amman
takasa janyo maganar ma tayi , kashe wayar tayi baki d'aya tanajin wata zufa na karyo mata ,
taya zata tunkari Gogal ? mezata ce mata intaje gurin ta ? kodai guduwa zatayi tabar garin baki
d'aya ? kuma inta gudu ina zataje batasan ina zata nufa ba , sannan kuma indai tayi haka to
tabbas Hak'k'in Kakar ta bazai tab'a barin ta tasamu kwanciyar Hankali ba , dole ta shirya
tunkarar duk irin hukuncin da Gogal zata yanke mata , haka ta zauna cikin motar tana ta
tunane tunane , kafin daga baya taja motar ta nufi hanyar tsohon gidan su........
Khalid tunda su Aysha suka fita ya zauna bakin gadon yana furzar da wata irin iska ,
tabbas Aysha tagama cutar sa meyasa zatabi ta wannan hanyar danyin ramuwa akan abinda ya
mata ? dan kawai yayi kwanta da ita shine zatace yayi mata fyad'e ? ai koma Fyad'en yayi
mata itace ta janyo tunda ta bayyana surarta yaganta , yanzu gashi tayi masa buk'ulu kasuwar
dayake zuwa an koresa , duk kud'ad'en daya samu tayi masa gaba dasu , Mahaifin sa babu irin
gargad'in da bai masa ba akan ya rik'e amana a kasuwan cinsa , sannan ya kyauta ta
mu'amalar sa da uban gidan sa , haka yasa k'afa ya ture dan son zuciyar sa , gashi yanzu yayi
biyu babu ai ba Ruma kuma ankorwsa daga kasuwa , yana zaune yaji ana buga k'ofar d'akin ,
a hankali yabada umarnin ashigo d'aya daga cikin Ma'aikatan Hotel d'in ne yashigo , duban
Khalid yayi yace " Oga lokaci ya cika zaka fita zamu gyara d'akin wasu zasu shigo , duban sa
Khalid yayi sannan yace " kamarya in fita alhalin kud'in kwana d'aya na kama , Ma'aikacin ya
dubi Khalid yace " gaskiya ba kwana bane a list d'in da muke dashi , yarinyar da takama kud'in
Awa Uku ta bada kuma lokaci yayi , Khalid runtse idanun sa yayi yana jin wata iriyar tsanar
Aysha na shigar sa , tabbas dole ya d'au mataki akanta , haka ya mik'e ya fice daga cikin d'akin
yana jin wani irin d'aci aransa .......
Tunda su Ruma suja fito daga cikin Hotel ita da iyayen ta take sharar hawaye , Mummyn
tace ta janyota jikinta ta shiga rarrashin ta tare da bata baki , Ruma tace " Mummy ba ina kukan
rabuwa da Khalid bane kawai inajin muguwar tsanar sane akan abinda yayi mana , ashe
bashida hali me kyau yana ta zalintar Daddy duk bamu gane ba sai yanzu , Mummy tace "
kansa ya zalinta ai tunda gashinan Allah ya toni asirin sa tun ba'aje ko inah ba , Daddy yace " ai
wannan yaron ba k'aramin azzalumi bane , tunda yazo shagona nake ganin yanayin kamar ana
min d'auke d'auke , amman ganin yadda yake nunamin shi na Allah ne kuma yana nunamin zai
iya tsaremin komai na dukiya ta , sannan ya nunamin yana da k'wazo sosai wajen nema hakan
yasa nasaki jiki nadaina kawo zargin sa araina , ashe lullub'eni yake da mugun k'ullin sa arai ,
lallai Allah ya dubemu da bamu aurar dake gashi ba da yanzu sai kin shiga zaifara nuna halin
sa , haka suka ci gaba da zancen Khalid har suka k'araso gida......
Aysha tunda ta tunkari tsohon gidan su gaban ta yake fad'uwa , haka ta daure har ta
k'araso k'ofar gidan ta nemi guri tayi parking , zama tayi cikin motar ta had'a kanta da sitiyarin
d'in motar tana tunanin ta inda zata fara...........
_Inayiwa 'Daukacin Masoyana Albishir na Sabon Book d'ina Me Suna_ *NI KO ITA*
_wannan littafi ya k'unshi abubuwa da dama,kudai kuyi saurin Mallakar naku akan farashi
K'alilan_ βπ»
*Sai najiku Masoyana*π₯°π
_Ina mutuk'ar K'aunar ku Masoyana kamar yadda kuke sonaβ€οΈ_ _saboda Son danake
muku kamar nazo na janyoku muyi rayuwa tareπΉπΉππ»ππ»ππ»β€οΈπ₯°_π€π»
[11/08, 3:43 pm] Maman Islam: *'YAR HANNU*
π€π€
_NA_
*Zee MD*
*WOMEN WRITERS ASSOCIATION*π
( Domin Marubuta Mata )
β¨ (W.W.A) β¨
https://www.facebook.com/106752595253176/posts/107924965135939/
*Bisimillahir Rahamanir Rahim*
_Assalamu Alaikum Masoyana ina yi muku fatan Alkairi a duk inda kuke , ina Barar
addu'arku daga bakunan ku masu Albarka , Allah yabiya mana Buk'atun mu na Alkairi_ππ»ππ»π€π»
*Taku Har Kullum*
_Zee MD_ π₯°β€οΈπ
_Page._ 33
Banda Hawaye babu abinda idanun Aysha ke zubar wa , addu'ar ta d'aya shine
Allah yasa kar Gogal ta mutu dan tasan itama rayuwar ta tazo k'arshe , suna k'arasowa Asibitin
da yake mallakine ga Hameed tuni likitoci sukayo caa kansu , tuni aka nufi Emergency da ita
akan gadon marasa lafiya ,...
Suna zuwa k'ofar shiga aka dakatar da Aysha ita da Habu aka shige da ita , Aysha
hawaye sai zuba yake akan kuncin ta tana zagaye k'ofar d'akin , Habu ya dube ta yace " kiyi
hak'uri Aysha kisamu waje ki zauna insha Allah zata samu sauk'i , Aysha ta kalli Habu tace "
bazan tab'a yafewa kaina ba mutuk'ar Gogal ta rasa ranta , a yau nayi dana sanin zuwa na
duniya Allah na tuba Allah kayafemin , nan kuka yaci k'arfin ta tashiga rerasa tamkar k'aramar
yarinya , Bayan kusan Minty 10 sai ga Hameed ya fito daga d'akin , da gudu Aysha ta nufoshi
tana fad'in " Dr dan Allah kar kacemin tarasu , wallahi itace kad'ai farin cikina itace duk wani
gatana a duniya , Hameed ya kalleta cike da tausayin ta tare da tsan tsar K'auna yace " Am
sorry My Dear mun shawo kan Matsalar yanzu haka tasamu bacci , kuma insha Allah inta farka
to komai zaiyi dai dai , tasamu Bugawar Zuciya ne na wani lokacin amman munyi nasarar saita
komai , Aysha ta lumshe ido hawayen da suka cika idanuwan ta suka gangaro a hankali ta furta
" Alhamdulillah Allah kabata lafiya , Hameed da Habu suka amsa da Ameen....
Hameed ya dubi Habu yabashi wata takadda yace " kaje Reception kace a nuna maka Dr
Kamal , kabashi takaddar nan kace ya duba sai yabaka abubuwan da suke a rubuce , Habu
yasa hannu biyu ya karb'a sannan ya nufi Reception ,....
Sauran likitocin da suka shiga da Gogal d'akine duk suka fito , nan suka cewa Hameed
tasamu bacci nan da awa biyu zata iya farkawa , suna gama masa bayani suka bar gurin cike
da bashi girma , Aysha tayi sauri zata shiga cikin d'akin Hameed ya tsayar da ita , duk Abinda
kikasan zai kuma d'aga mata hankali in ta farka to lallai a nisan tar mata dashi , cak Aysha ta
tsaya sannan ta jiyo tana duban Hameed shima ita yake kallo idanuwan su suka sark'e waje
d'aya , take kowannen su yaji wani Abu ya soki zuciyar sa , Aysha tayi saurin kau da kai
sannan tace " yanzu kana nufin sai dai abar ta ita kad'ai kenan ? Hameed yace " indai kinsan
ganin ki zaisa takuma samun matsala to tabbas ki nisanci gurin ta har zuwa wani d'an lokacin
da komai zaiyi saiti , Aysha jiki a sanyaye ta dawo ta zauna kan wata kujera , Hameed ya
tsaya yana kallon ta tare da nazarin yanayin ta cikin ransa yace " wato wannan matsalar da
Kakar ta tashiga tasamu asali ne daga gare ta , lallai yana son jin meyasa Kakar ta tasamu
wannan bugun zuciya haka , a hankali yacewa Aysha " in babu damuwa inaso ki biyoni office
zamuyi magana me muhimman ci , batare da musu ba Aysha tacw masa to tare da mik'ewa tabi
bayansa ......
Suna shiga office d'in wani k'amshine ke tashi tare da sanyin ac , wani hoton Hameed ne
k'ato tamkar zaiyi magana kana shiga shine yake kallon ka , samun waje tayi ta zauna shima
Hameed d'in ya zauna yana duban ta , sai da ya nisa sannan yace mata " idan babu takura
inaso kibani labarin da kikace zaki bani yau , sannan inaso insan dalilin cutar kaka , dan bai
kamata ace ta had'u da wannan cutar me saurin salwan ta ran mutum ba , tabbas inaso inji
damuwar da ta haifar mata da hakan , Aysha ta yanke gayawa Hameed gaskiya , haka kawai
takejin bazata iya b'oye masa komai ba , watak'ila ko ta sanadin sa tasamu ta shirya da Gogal
dan yaga yana da halayen k'warai , ....
Gyaran Murya Aysha tayi tare da fara bawa Hameed labarin su tunda farko har izuwa
lokacin da suka kawo Gogal Asibiti.... Duk irin rayuwar da Aysha tayi babu abinda bata gayawa
Hameed ba , har cikin datayi ta zubar tare da gaya masa lokacin da suka had'u da ita shima
wato lolacin da Farouq da Abokan sa suka mata fyade.......
Hameed tuni ya jik'e da gumi saboda rud'anin da yashiga , Ayshar sa wacce yake
tsananin so yake mafarkin mallakar ta wacce yake wa kallon Ustaziya kamammiya me rik'o da
addini ashe *'YAR HANNU* CE ? shuru yayi tare da yin k'asa da kai , tabbas Gogal tayi sakaci
da yawa da har Ayshar tazama haka batare da ta lura ba , amman dole zaiyi mata uziri saboda
yadda Ayshar takasan ce me nuna Fuska Biyu , Muryar Aysha ce tadawo dashi daga tunanin
daya tafi tace " kaji Labarina kaji irin yadda nayi rayuwata wannan yana d'aya daga cikin Abinda
yakesa nake nisan ta kaina da kai , kai Mutum ne kamili wanda yake da tsoron Allah dan sai
dana bibiyeka nasan yadda halin ka yake , kana da taimako tare da tausayi da kuma
kyautatawa Al'umma , nikuma rayuwata babu wani Abu wanda yake na Alkairi a cikin ta , ba
kowa bace ni face *'Yar Hannu* mai bin Maza wacce tagama saida jikin ta , Hawayen dake
idanun ta ta share sannan ta mik'e tana fad'in " ina fatan daga yau zaka nisan ceni nagode da
taimakon da kayi mana , bata jira cewar saba tasa kai ta fice daga cikin office d'in .... Shima
Hameed baiyi yunk'urin dakatar da itaba dan bashi da abin da zai ce mata a yanzu......
Ruma tunda suka dawo gida take kiran wayar Aysha , sai dai tana ta ring. Amman
ba'adagawa , tunani ta shigayi ina Ayshar taje tabar wayar haka ? haka ta hak'ura da kira ta
tura mata test akan yadda sukayi da Khalid da kuma irin amanar ta dayaci , ......
Aysha tana fitowa daga Office d'in Hameed ta samu guri ta zauna dai dai d'akin da Gogal
take , duk bayan minty 5 tana lek'awa ta windo dan ganin ta , a haka Habu yazo yasa meta a
wajen yashiga tambayar ta ina Dr ? nan ta nuna masa hanyar office d'in Hameed batare da tayi
magana , Habu ya nufi office d'in rik'e da Magungunan da aka bashi , Bayan kusan minty 3
saiga Hameed da Habu sun nufo wajen Ayshar , Suna zuwa Hameed ya shiga cikin d'akin tare
da cewa Habu kaima ka jira anan , bayan wasu minty na shima ya fito tare da cewa " zan turo
wata nurse d'in sai ta kwana da ita , zaku iya tafiya gida saboda gudun damuwar ta kuma kunga
dare yayi , Habu bai fahimci inda zancen Hameed ya nufa ba shiya sa yace " ai anan zamu
kwana nida Aysha basai ka turo nurse ba , Hameed yace " kai zaka iya kwana amman ita zaya
iya tafiya yana fad'in haka yayi gaba abinsa , Aysha wani abu taji ya soketa arai taya zaice ita
ta tafi abinta ? meyake nufi da hakan da zai fad'i ? ai koda bazata je wajen Gogal ba to tqbbas
bazata bar asibitin nan ba dole ta zauna dan kulawa da Gogal d'in ta , ....
Nan ta dubi Habu tace " Habu kazo ka komq gida , kaga ko rufe gidan ba muyi ba kar azo
asamu matsala , kuma kaga jinyar mace ai sai mace kai inyaso ko gobe ne sai kadawo , Habu
yace " to shikenan babu abinda kuke buk'ata ? Aysha tace " babu komai sai da safe kawai ,
Habu yayi mata sallama ya shige yatafi abinsa ,.......
Hameed yana komawa Office ya d'auki wayar sa ya kira Hajiyar sa akan bazai dawo gida
ba , yana da mara sa lafiya anan asibitin sa kuma suna buk'atar kulawar sa , Hajiya tasan halin
Hameed da son bawa marasa lafiya kulawa , shiyasa tayi masa addu'a tare da yi masa sai da
safe ,......
Yana zaune cikin Office haryanzu zuciyar sa takasa fad'a masa matsayin da Aysha take ,
sosai yashiga tunani ga shi ko kad'an Son Aysha da K'aunar ta basu ragu a zuciyar saba , wani
sabon son tane ma yake kuma ratsa duk wata gab'a ta jikin sa , a hankali ya runtse idanu yana
tuno labarin nata , tabbas so masifa ne dan badan so ba a gaskiya da bazai iya k'ara saurarar
Aysha ba , amman ina a yanzu ma ji yake tamkar ya tashi yaje yagan ta ko zai samu sauk'in
zuciyar sa , a hankali yabi shawarar zuciyar sa me cewa yaje ya duba ta Allah yasa bata tafi
gida ba , yana fitowa daga office yanufo hanyar d'akin da aka kwantar da Gogal , tunda ga nesa
ya hango ta ta takure a jikin Bango , daga gani kasan sanyi takeji duba da yanayin garin ana
zabga sanyi sosai , wani tausayin tane ya kama Hameed har ya k'araso wajen da take batare
da ta sani ba , rigar dake saman tashi ya cire ya d'ora mata ajikinta ganin yadda take rawar
sanyi...........
[11/08, 3:43 pm] Maman Islam: *K'arashen 'YAR HANNU*π€π€
Gogal tace " nidai na ruga na yaba da hankalin sa amman kisamu 'Yar uwarki kuyi
magana , tana fad'in haka ta mik'e tabar wajen .......
*Bayan kwana biyu*
Kwata kwata Aysha ta daina sukuni , Ruma tayi tambayar duniya akan meke damun ta
amman tayi shuru , sai Gogal ce take fad'awa Ruma abinda yasa Aysha tarage wal wala ,
Ruma murna tayi sosai tashiga tsokanar Aysha Amaryar Hameed , Aysha dai bata tankaba
dan batason ayi mata zancen Hameed , suna cikin hirar sai ga Hameed d'in yayi sallama , nan
Ruma ta amsa masa tare da yi masa sannu da zuwa , ya amsa cike da sakin fuska dan jin sa
yake cikin farin ciki tun baiji amsar da zai samu ba......
Bayan sun gaisa da Gogal yasamu waje ya zauna suka shiga magana , nan Gogal ta
sheda masa ya jira dawowar Mahaifin Ruma dan shine zai amshi kud'in auren Aysha , murna
sosai Hameed yashiga tare da yiwa Gogal godiya , itama godiya ta masa dan shine masoyin
gaskiya wanda ko wacce mace zata yi Alfahari da samun sa , duk da irin abubuwan da yaji na
Aysha amman ya amince da auren ta tabbas shine ya can can ci ayi masa godiya .....
Hameed bai tab'a zuwa gurin Aysha zance ba sai dai kullum cikin yi musu hidima yake ,
ko waya basayi amman kusan kullum sai yazo gidan dan yaganta ,..
A b'angaren Hajiyar Hameed baisamu matsala da ita ba , dan tana son abinda d'an ta
yakeso take tashiga hidimar had'awa 'Dan ta kayan lefe , duk da bata tab'a ganin yarinyar ba
amman Hameed ya gaya mata yadda take , Unguwar su Aysha babu magul mata shiyasa
bawanda yakai sukar auren ta......
Alhaji Ashir suna da wowa bayan ya huta Gogal tasame sa da maganar zai anshi sadakin
Aysha , yayi farin ciki da jin hakan kuma ya amince dan dama Gogal ta sheda musu basu da
kowa , Dan haka shine yazama Uba ga Aysha ,....
Iyayen Hameed sunje nemawa Hameed auren Aysha gidan Alhaji Ashir , sosai aka
karramasu bayan nan suka bada kud'in aure aka tsaida wata d'aya za'a had'a dana Ruma
.....
Hameed baiso aka saka wata d'aya ba duk da yayi farin ciki da yadda aka karb'esu hannu
biyu suka gaya masa , nan aka fara shirye shirye ta kowanne b'angare.....
Mummyn Ruma tuni ta tura Amare gida Mrs MD dan ayi musu gyara tare da tsumasu da
magun guna , Aysha kwata kwata bata murna da auran nan dan ita a ganin ta Hameed b son
ta yake ba , kawai dai zai aure tane dan wata manufar tashi daban , ko sau d'aya bai tab'a
zuwa gunta zance ba sannan ace a hakan zasu zauna zaman aure , ba yadda zatayi haka take
zuwa gyaran jiki ita da Ruma , yadda Ahmad ke nan nan da Ruma abin na birgeta amman ita ko
sau d'aya Hameed yaki bata kulawa , bata b'oye wa me gyaran jiki ba aka itafa fa ba cikakkiyar
budurwa bace , nan aka shiga had'a ta da magun gunan matsi masu kyan gaske batare da
Ruma ta gane ba ,.....
Yau saura sati d'aya bikin Aysha da Hameed Ruma da Ahmad , suna hanyar su ta
dawowa daga gidan gyaran jiki sukayi karo da Farouq nan yake gaya mata rasuwar Alhajin sa
da kuma auren da yayi , sosai Aysha taji mutuwar Alhaji Na Lamma tayi masa Addu'ar samun
Rahamar ubangiji , tayiwa Farouq gaisuwa tare da yi masa fatan Al kairi akan auren sa ......
Suna zuwa gidan sukaga ankawo lefen su baki d'aya , Alhaji Ashir gidan Gogal yasa aka
kawo kayan lefe dan shima jin ta yake tamkar Mahaifiya a gurin sa , Ruma ankawo mata
akwatuna takwas ita kuma Aysha Akwatina 12 kaya iya kaya abin ba'a magana , Ruma tafara
yiwa Aysha maganar yadda zasu tsara dinner da party amman Aysha tace bazatayi ko d'aya ba
kawai walima zatayi ,....
A daren ranar Hameed yazo wajen Aysha da maganar tayo masa list d'in duk abinda take
buk'ata , Aysha ta sheda masa bata buk'atar komai duk da haka ya d'auki dubu dari yabata
sannan yatafi ,...
Ana gobe kamu sukaje akayi musu kunshi da gyaran kai , nan ne Aysha taga Jabir yake
sheda mata bayan yazo wajen ta ya tafi yan zuwa gida ya tadda Mahaifin sa ya nema masa
auren wata yarinyar Abokin sa , yanzu haka saura sati bikin sa kuma Baban sa yace mudun ya
bijirewa maganar sa sai ya tsine masa , Aysha tace Allah yasanya Al kairi Ruma tace " itamq
jibi d'aurin auren ta Allah yabata miji na kere sa'a , duk da Jabir yaji rashin dad'i amman yataya
Aysha murna yasan ko ba komai aure shine rufin asirinta ......
Walima kawai sukayi basuyi wata bidi'a ba , Washe gari aka d'aura auren Aysha da
Hameed Ruma da Ahmad , sai muce Allah yabasu zaman lafiya.....
Komai iri d'aya Alhaji Ashir yayi musu babu wani bambanci , Gogal ta had'a musu gyara
sosai itama wacce komai itama kai d'aya tayi musu , dare nayi kowacce aka mik'ata gidan
mijin ta tare da tarin nasihohi daga wajen iyayen su ......
Fad'in had'uwar gidan Aysha b'ata bakine dan gidane na alfarma , kuma Alhaji Ashir ya
zuba musu dukiya sosai kowacce sai san barka , tunda aka kawo Aysha take kuka dan batasan
wace irin rayuwa zatayi da Hameed ba , shigowar sa ce tasa tayi k'asa da murya dan karyaji
sautin kukan nata , ledojin hannun sa ya ajiye tare da shiga toilet yayi wanka , bayan ya fito ya
umarce ta itama akan ta je tayi wanka ta d'auro arwala dan suyi sallah nuna godiy ga
mahaliccin su , Bayan tayi tafito sukayi sallah nan ya yi mata addu'oi tare da addu'ar Allah
yabasu zaman lafiya , .....
Wannan Daren haka Hameed ya rayashi tare da nunawa Aysha zallar k'auna , kwata
kwata sai ya susuce mata tamkar qani k'aramin yaro , ita kanta sai da ta ji ajikin ta dan tabbas
ta yadda da gyara da kayi mata tamkar wata sabuwar budurwa , shi ya taimaka mata ta gyara
jikin ta yana ayyana anya wannan Aysha *'Yar Hannu* ce kuwa ? dan ji yayi tamkar shine yafara
bud'e ya aleda, haka yai tasa mata Albarka ya zage ya rungumi matar sa yana nuna mata zallar
k'auna.......
Satin su biyu sukayi sallama da iyayen su da Abokan Arziki suka d'aga England.......
Acan Aysha taci gaba da karatun ta tana karanta irin aikin mijin ta wato Likita , tare suke
fita kullum suna tare da juna tamkar su cinye junan su sabo da kulawa ....
*Bayan shekara biyu*
Tuni Aysha ta haifi d'iyar ta mace wacce suka saka mata sunan Gogal , wato Aysha kuma
sunan uwara ta suke kiran ta Eesha , lokacin Aysha ta gama karatun ta suka shirya zuwa
Nageria , kafin suzo tuni angyara musu gidan su suna zuwa suka sauka a nan , sai da suka
huta sannan suka je gidan su Hameed , sosai Hajiyar Hameed tayi farin cikin da ganin su tare
da jikar ta , anan suka wuni sai dare suka nufi gidan Gogal , sai dai Aysha tasha mamakin ganin
yadda aka maida gidan Gogal har da saka masa gate , tana shiga taga irin had'uwar da yayi
sosai tasamu Gogal zaune da wata yar matashiyar budurwa suna hira , suna ganin su Gogal
tace " ai bayi fushi wato sai yanzu zaazomin ko , nan Aysha tasa dariya tana fad'in " ko kinyi
fushi dani ai bakyayi da Esha ba , nan Gogal ta anshe ta tanajin k'aunar yarinyar har cikin ranta
, ashe da rabon zataga 'yar gidan Aysha lallai duniya komai mai wucewa ne , Anan suka
kwana sunsha hira sosai anan take gaya mata wannan gyaran gidan Hameed ne yaturo da
kud'i akai musu , sannan ya kaita aikin hajji ita da su Mummyn Ruma da Alhaji , sosai Aysha
tashiga mamaki dan ko sau d'aya Hameed bai nuna mata ba , lallai Hameed gwarzon namiji
ne wanda takewa Allah godiya da samun sa ....
Wannan budurwa da tagani Gogal ta sheda mata ai Matar Habu ce daya auro daga garin
su , shine tace su zauna tare da ita dan batason zaman kad'ai ci , sosai Aysha taji dad'i gashi
ta yaba da hankalin Rabi'a matar Habun , washe gari Hameed yazo ya d'auke ta suka nufi
gidan su Ruma , saida suka jima da Mummy suna hira sannan suka nufi gidan Ruma , murna
sosai Ruma tayi da ganin 'yar uwar tata tare da Esha ita lokacin har tana shirin yaye Abul kairi ,
dayake ta ruga Aysha haihuwa , anan Ruma take bata labarin Khalid ya haikewa 'yar gidan
yayan sa anka masa yanzu haka yana can virson sai ya shekara goma sannan zai fito , Aysha
tace " Allah ya kyauta wato me hali baya canzawa Allah yasa mudace , dare nayi Hameed yazo
ya kwashe su suka nufo gida .....
Aysha tana jikin Hameed a kwance tace " bani da bakin da zanyi maka godiya mijina
akan Alkairan ka gareni , sai dai a koda yaushe ina maka addu'a akan Allah yabiyaka da
mafificin Alkairi , rungumeta yayi sannan yace " Ameen My Baby Esha one inaso kibani had'in
kai a yau musamowa Esha baby k'ani ko k'anwa , dariya tasa tana tura fuskar ta cikin jikinsa ,
anan nafito na barsu dan kar nasa musu ido ......
*Bayan shekara uku*
Tuni Aysha tazama cikakkiyar Dr. Itama tafara aiki a asibitin da Hameed keyin aiki acan k'asar
England , lokacin yaran ta biyu ga Esha ga Daddy wanda yaci sunan Mahaifin Hameed , In
sun samu hutu suna zuwa Nageria dan Gogal ma Aysha tuni ta d'auko ta ta dawo da ita wajen
su , Arzik'i sai Abinda yai gaba , dan yanzu Aysha tazama Babbar Hajiya tare da Mijin ta Alhaji
Dr Hameed , Rayuwa ta sauya musu sai dai suce Alhamdulillah ........ Hameed yazama na
Aysha Aysha tazama ta Hameed , kullum inta tuna irin abubuwan da tayi sai taji tana tarin
nadama tare da kuma yin istigifari dan neman
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 12 Chapter of 13