nadaina komai ,
rumgumo Gogal tayi ajikin ta wacce taji kamar bata motsi , da gudu ta ajiyeta ta fito tana neman
ruwa ta yayyafa mata , dayake a rud'e take kawai waje ta nufa tana kuka tare da neman
taimako , dai dai nan Hameed ya iso a motar sa yana ganin Aysha ta fito ko mayafi yasan ba
lafiya ba , ko tsayawa baiyi kashe motar ba ya fito da gudu ya nufota yana cewa " lafiya Aysha
meyafaru ? da sauri ta rik'o hannun sa tana fad'in " kataimaka min dan Allah kar Gogal ta Mutu
bazan iya zama a duniya ba indai babu ita , haka suka shiga cikin gidan a rud'e dan shima
ganin ta haka ba k'aramar rud'ewa yayi ba , ...
Koda yaga Gogal a shimfid'e tuni ya sab'eta a kafad'a yana cewa Aysha zo muje asibiti ,
tuni suka fito ta janyo hijab d'in ta suka fito tare , karo sukaci da Habu shima ya rufa musu baya
akasa Gogal a motar Hameed suka nufi Asibiti.......
[11/08, 3:43 pm] Maman Islam: *'YAR HANNU*
🤒🤒
_NA_
*Zee MD*
*WOMEN WRITERS ASSOCIATION*📚
( Domin Marubuta Mata )
✨ (W.W.A) ✨
https://www.facebook.com/106752595253176/posts/107924965135939/
*Bisimillahir Rahamanir Rahim*
*Alhamdulillah !*
*Alhamdulillah !!*
*Alhamdulillah !!!*
_Page._ 35
Jikin Gogal itama sanyi yayi tare da jin tausayin Aysha , ba komai ne yayi tasiri a
zuciyar Gogal ba yasa har tayi nadama sai Sakacin datake gani tayi akan kula da Ayshar ,
itakuma Aysha ba komai ne ya janyo mata haka ba face Rashin yadda da kaddara , da tunfarko
ta yi hak'uri da Abinda Khalid yayi mata da bata zama haka ba , duk da bayan Khalid ya yi mata
hakan kuma taso wannan yazama farko yazama k'arshe amman sai ga Farouq ya billo mata
shima , a haka zuciyar ta tashiga zugata akan cewar duk Namiji inyazo gunta to tabbas ba
soyayyar Allah yake mata ba sai dan surar jikin ta , tunda ganan tashiga bin zuciyar ta meyi
mata wannan hud'ubar , Allah yarabamu da sharrin Zuciya Ameen......
Gari nayi haske saiga Habu da kaya a hannun sa ya shigo d'akin d'auke da sallama ,
samun Gogal da yayi a zaune ba k'aramin dad'i yaji ba , dan yanajin tamkar Mahaifiyar sa
saboda gatan da ta nuna masa , nan suka gaisa tare da yi mata fatan samun lafiya me d'orewa
, ....
Kunu ya taho mata dashi tare da k'osai sai kuma kayan sawa kala biyu , sosai Gogal taji
dad'in ganin kunun tayi masa godiya tare da sanya masa albarka , Aysha tayi murmushi tace "
shine ni baka tahomin da waina me k'uli ba kawai ta Kakar ka kake ko ? inda sabo Aysha da
Habu sun saba tsokanar juna shiyasa Gogal tayi murmushi kawai batare da tace komai ba......
Dr. Hameed ne ya shigo cikin d'akin d'auke da sallama , amsawa Habu yayi tare da yi
masa sannu da shigowa , ganin yadda Aysha ke zaune tana bawa Gogal kunu tana sha cike da
kulawa , wani dad'i Hameed yaji ya ratsa shi dan da alama Gogal tadaina fushi da Ayshar , cike
da girma mawa yagaida Gogal tare da tambayar jikin ta , amsawa tayi cike da sakin fuska
sannan tashiga masa godiyar kulawar da yake bata , Hameed murmushi yayi yana satar kallon
Aysha wacce ta kauda kanta gefe tamkar bata gansa ba ......
Gogal ce tace " Sayyada baki gaida Dr ta ba kiyi masa godiya yana da mutunci , Aysha ta
jiyo ta gaida Hameed amsawa yayi shima yana me d'aure fuska tamkar bashi ba , Aysha bata
damu ba dan tasan dama dole Hameed zai tsaneta dan irin rayuwar datayi , Habu ne ya mik'e
tare da cewa bari yaje yadawo .....
Yana fita Hameed yace " Mama inaso dan Allah kidaina saka damuwa aranki , zuciyar ki
zata iya samun matsala a zo ana wani zancen ba wannan ba , Gogal tace " insha Allah zan
kiyaye daga yau nadaina saka komai arai , Cikin zuciyar Gogal kuwa tace " bazan daina
damuwa ba mutuk'ar ba Aysha tayi aure ba , amman indai tana gaba na to zan kasan ce cikin
damuwa , a fili kuma tashiga cewa Hameed " yau zaku bani sallama ko ? Hameed yayi
murmushi sannan yace " kibari sai nan da kwana biyu jikin naki ya kumayin kyau , Gogal tace "
banason zaman asibiti indai ba dole ba kuma jaga ai jikina yayi sauk'i sosai , Hameed yace
k'a'idar asibitin sa baya sallama akwana d'aya , dan haka tayi hak'uri zuwa gobe , badan taso
ba tace shikenan da yau da goben duk d'ayane , Aysha ita kanta so take a sallamesu dan
kawai ji tayi batason zama a inda Hameed d'in yake , wata kunyar sa takeji tare da nauyin sa
sannan yadda yake had'e mata rai sai take ganin tamkar tsanar ta yayi , ......
Wata Nurse ce tayi sallama cikin d'akin d'auke da Basket food a hannu , rissinawa tayi
tagaida Gogal tare da mik'awa Habeeb kwandon tace " gashi inji direban gidan ku yace abaka ,
ansa yayi batare da yace mata komai ba ita kuma ta fice....
Hameed ya dubi Aysha yace " ungo wannan ki d'ibar muku kuci sannan ki zubomin nawa ki
kawomin office , yana fad'in haka ya mik'e ya fita tare da cewa Gogal anjima zaidawo suyi
hira.....
Aysha bata tab'a kayan Abincin ba ta share tamkar bataji abinda yace mata ba kafin ya fita
, itama Gogal ba yunwa takeji ba sai dai kawai saboda Dr d'in , duban Aysha tayi tace " kiziba
masa abincin ki kai masa mana , Aysha ba musu tashiga bud'e kulolin Abincin , farfesun kaji ne
sai kuma farfesun kayan ciki daban , sai Shinkafa da miyar ganye wacce taji kifi wadatacce ,
sai kuma kunun gyada a cikin wani karamin flast , d'aukar filet tayi sannan ta dubi Gogal tace "
nifah bansan wanda zan zuba masa ba , Gogal tace "kawai ki d'auki kwandon Abincin kije
office d'in nasa sai kitambaye shi abinda yakeso aciki , Aysha badan taso ba ta mik'e ta d'auki
kwandon tafita ta nufi office d'in Hameed......
Tana shiga tayi sallama a hankali ta tsaya , Hameed yaji sallamar amman sai yayi kamar
baiji ba , ta dad'e a tsaye kafin yace " waye a tsaye ne in bazai shigoba ya koma , Aysha ta
shiga ciki sannan ta ajiye kwandon kayan abincin tashiga bud'ewa , bayan tagama bud'ewa
tace " mezan zuba maka daga ciki ? duban Abincin yayi sannan yace ki zubamin kunun gyad'a
sai ki zubamin farfesun kayan ciki , hakan tayi masa ta ajiye sannan ta juya zafa fita , Aysha
ya kira sunan ta cak ta tsaya zonan , a hankali ta tako tazo gurin dayake ta tsaya batare da
tace uffan ba , Hameed yace " meyafaru da Mama ta tashi taganki ? shuru Aysha tayi kamar
bazatayi magana ba sai kuma tashiga fad'a masa duk yadda sukayi da Gogal , Hameed ya saki
ajiyar zuciya sannan yace " ki godewa Allah da kika samu batayi dogon fushi dake ba , kuma
Allah yasa kinyi tuban gaske bazaki k'ara komawa ruwa ba , Aysha sosai taji rashin dad'i akan
kalmar sa na cewa wai Allah yasa tayi tuban gaske , Ameen tace masa ta juya tabar office d'in
nasa da sauri......
Haka suka yini a asibiti wannan abincin da aka kawo daga gidan su Hameed shi sukaci
har Habu ,.....
Hameed gida ya koma sai bayan Magriba yadawo asibitin , da kayan abinci yataho musu
sosai Gogal take godiya dan irin kulawar da yake basu har tayi yawa , wannan karon tun da
yashigo Aysha ta tsiri lazimi dan batason magana ta had'asu , tanajin sa shida Gogal sai hira
suke tamkar sun dad'e da sanin juna , nan take masa godiya akan nauyin ta da ya d'auka a
asibitin batare da an anshi ficikar suba , murmushi Hameed yayi sannan yace " Mama ai
asibitina ne kuma kinga ke Mama tace taya d'a dan yayi hidima da Mahaifiyar sa ace kuma sai
ta biya , Hawaye ne suka shiga zubowa a kuncin Gogal nan tashiga sama sa Albarka .......
*Bayan kwana biyu*
Tuni an sallami su sundawo gida , sosai Aysha take kulawa da Gogal tare da gujewa duk
wani b'acin ranta , Anan Aysha ta yanke maidawa da Alhaji Na Lamma mukullin gidan sa da
kuma motar sa , Gogal sosai tayi na'am da maganar Ayshar , ranar wata laraba da safe ta
shirya ita da Habu suka hau motar tare da tafiya da mukullin gidan dan maidawa Alhaji Na
Lamma , sai da suka fara zuwa gidan duk wasu kaya datasan natane a cikin gidan ta kwashe
ta fito dasu , Bayan ta gama kwashewa gida ta dawo dasu ta ajiye sannan suka nufi gidan Alhaji
Na Lamma.....
Gidan sa ba b'oyayye bane shiyasa basu sha wuya ba suka gano , suna zuwa Megadi ya
lek'o ya tambaye su su waye kuma wajen wa sukazo ? nan Aysha tace masa wajen Alhaji
sukazo suna son ganin sa , nan Megadi yace musu " Alhaji bashi da lafiya bazai iya fitowa ba
amman bari yayiwa yaron sa magana , nan yashiga cikin gida yayiwa Farouq magana akan
suna da bak'i , Farouq yace masa ya shigo dasu kawai , koda Aysha suka shigo Farouq yana
ganin ta ya mik'e dan mamakine ya kamasa , cikin zuciyar sa yake tambayar me Aysha tazo yi
gidan su kuma yanzu ? Aysha ta gaida Hajiyar Farouq sannan tace mata " dan Allah ko zan iya
ganin me gidan ? Hajiya tace " wacece ke baiwar Allah da kikeson ganin sa , Farouq yayi saurin
cewa " zaki iya ganin sa Aysha muje in muna miki d'akin sa , Aysha tabi bayan Farouq itama
Hajiyar mik'ewa tayi tabi bayan su....
Alhaji yana kwance gefen jikin sa baya motsi , sai dai fess jikin sa da alamar ana bashi
kulawa sosai , Suna zuwa Ya kafe Aysha da idanuwa bakin sa kuma yayi nauyi dan baya iya
magana sosai , take Aysha tasake jin tsoron duniya da dukkan abinda ke cikinta , tabbas me rai
baigama ganin halittar sa ba mutuk'ar ba mutuwa yayi ba , nan tashiga neman yafiyar Alhajin
akan barazanar da tayi masa san kawai ta mallaki gidan sa , ta kuma bashi mukullin gidan nasa
tare da na motar Farouq , kuma ta sheda musu tuntuni ta goge komai dayake wayar ta na
Abinda ta d'auka , Alhaji Na Lamma shima rok'on ta yayi tayafe masa duk da batajin wani abun
dayake fad'a , Farouq dama tuni ya tuba ya canza hali yanzu duk yadaina yawace yawacen
banza ya koma kula da dukiyar Mahaifin nasa , nan Shima Farouq yakuma rok'on yafiyar
Aysha sannan ta fito tabar musu gidan , Alhaji Na Lamma ya yagawa Farouq ya maidawa
Aysha komai ya bar mata halak malak , ......
Hameed yazo yayiwa Gogal sallama akan zai koma England sai nan da shekara zai
dawo , Gogal tanuna rashin jin dad'i na tafiyar sa , dan zuwa yanzu sosai sun shak'u da
Hameed kuma sosai yake bata kulawa , haka tayi masa fatan Alkairi tare da addu'ar kariya
daga sharrin duk kan abin k'i , Hameed sai dube dube yake kozaiga Aysha amman bai ganta
ba , gashi yakasa tambayar Gogal inda Ayshar taje , haka ya ajiyewa Gogal kud'i me yawa
sannan ya mik'e yana mata sallama , har k'ofar soro ta rakosa tana masa fatan ya sauka lafiya
, yana k'arasowa jikin motar sa ya fito da kayayyakin abinci da yasiya musu akaita shigar musu
dashi , yana shiga cikin motar zai tashe ta ya hango Aysha da Habu sun sauka a Napep , har
sukazo suka gitfa ta gaban sa bai tafi ba sai dayaga shigar su cikin gida ,.......
Koda Aysha tashiga gida da wannan kayan suka fara karo , daman tunda taga motar tasan
Hameed ne yazo amman ko kallon wajen da motar take batayi ba , duk wannan abun tanayine
dan ta nisan ta kanta da Hameed , tasan koda wasa ba aurar ta zaiyi ba tunda ta fad'a masa
asalin wace ce ita....
*Bayan kwana biyu*
Ruma sunyi waya da Aysha ta sheda mata sun tashi , nan tazo gidan da suka dawo kuma anan
Ruma take bawa Aysha labarin rabuwar ta da Khalid , sai sannan Aysha itama tashiga bawa
Ruma labarin waye Khalid da kuma irin abinda yayi mata , sai dai ko kad'an bata gaya mata
itace ta turo mata komai da Khalid yakeyi ba , nan suka jimantawa juna sannan suka shiga hirar
su , Ruma tacewa Aysha " sister yakamata ki shiga Makaranta dan zaman haka bazai yuwuba
,.. Aysha tayi na'am da shawarar Ruma tasamu Gogal sukayi magana , da k'yar Gogal ta
amince mata da taimakon Ruma da Mahaifin ta Aysha tafara karatu a B.U.K ......
*Bayan wata shida*
Rayuwar Aysha sosai ta canza ta koma kamar da , duk wani abu da zai tuno mata da rayuwar
datayi ada ta banza sai ta kaudashi , kullum suna tare da Ruma har kwana Ruma na zuwa
gidan su Aysha tayi , Mahaifin Ruma ya d'auki Aysha tamkar shi ya haifeta sosai yake taimaka
musu , Gogal lafiya tasamu tuni ta koma sana'ar ta ta saida k'osai dan tace bazata zauna haka
ba koya sana'a tana da dad'i , ...
Farouq yadawo wa da Aysha mukullin gida da motar kamar yadda Alhaji Na Lamma ya
umarceshi , sai dai fir Gogal tace bazasu ansa ba ta gode , haka ya koma jiki a sab'ule duk
babu dad'i ,.....
Khalid kuwa tun wani lokaci da yazo wajen Aysha yayi mata rashin mutunci , sannan yace
duk kud'in da yakashe mata sai ta biyashi ko kuma yayi mata abinda bazata manta dashi ba ,
lokacin suka kaishi k'ara akayi musu tsakani , Aysha ta tattara duk kud'in da tasamu a yawon ta
takai gidan marayu sadaka.......
*BAYAN SHEKARA DAYA*
Aysha da Ruma suna tafe sai hirar su suke abinsu , dayake su Mummyn Ruma suntafi Hajji
shiyasa Ruma tadawo gidan su Aysha da zama , ganin wata mota sukayi tana binsu cikin
lungun da zasu shiga gida , Ruma tace " Sister wai bakya ganin wata motar ana bin mu ne ?
Aysha tace nagani koma waye shi yajiyo , suna zuwa k'ofar gida suka shige abinsu batare da
sun wai waya ba , Motar tayi parking a k'ofar gidan sannan ma mallakin ta ya fito daga ciki ,
ba kowa bane face Jabir Abokin fad'an Aysha , tsayawa yayi jikin motar yana neman yaron da
zai aika ayi masa kiran Aysha , aikuwa wani yaro yazo zai wuce Jabir ya kirasa tare da turasa
cikin gidan yace yakira masa Aysha , koda yaron ya shiga ya sheda mata Aysha cewa tayi ace
bata nan , har yaron zai fita Gogal tace " kai yaro kace gatanan zuwa kaji , Aysha ta dubi Gogal
itafa a yanzu babu shirin soyayya a tare da ita bare kuma aure , amman gudun b'acin ran
Gogal yasa batace komai ba ta maida Hijab d'in ta ta fita.....
wa zata gani Jabir tauraruwa me wutsiya ganin sa ba Alkairi ba , d'aure fuska tayi ta samu
waje ta tsaya tsam , k'arasowa yayi wajen ta yana murmushi sannan yace " Hajiya Aysha ko
kuma nace Malama Aysha , Aysha tayi masa wani kallo sannan tace " duk wanda yayi maka
kirani dashi , Jabir yace " me yai zafi haka nifa yanzu bak'one a gareki me niyar zama miji a
gunki , wani kallo Aysha tayi masa sannan tace " Kanemi wacce zata zama matarka tun lokaci
bai k'ure maka ba , wai menayi maka ne kake shiga rayuwata ? Jabir yace " sonake ki shiryu ki
nutsu ki canza ki zama ba mai 2 face ba , tun sanda nafara ganinki nakamu da sonki saboda
kamalar ki , amman dana bibiyeki sai nasamu ashe ba haka zuciyar ki take ba , tunda ga nan
na kud'iri niyar gyaraki koda zanyi bak'in jini a gurin ki , to Alhmd kin gyaru yadda nakeso kuma
nayi bak'in jini a wajen ki amman bandamu ba tunda kin shiryu , Aysha inasonki ina kuma son
aurar ki inhar zaki amince , karki damu da komai kikai a baya ni naji kuma na amince zanyi
rayuwa dake , a yanzu ina da sana'ar yi dan haka zan iya rik'e ki batare da kin buk'aci komai
daga wajen wani ba , Shuru Aysha tayi tana nazarin magan ganun Jabir , tabbas sai yanzu
tagane Jabir yafita gaskiya tunda gashi ta shiryu kuma ta dalilin nasa , amman a gaskiya ita a
yanzu bazata iya aure ba dan bata shirya hakan ba , ta d'ago ta sheda masa bazata iya aure
yanzu ba kawai taga wata had'add'iyar motar ta tsaya a kusa dasu , andad'e ba'a bud'e motar
ba hankalin ta gaba d'aya yatafi wajen motar , Jabir ya kalleta yaga tana kallon wajen da motar
tayi parking , wani kishi yaji ya kamasa a d'an tsawa ce yace mata " me kike kallo Aysha
magana fa muke , jiyowa tayi sannan tace " naji duk batunka sai dai kayi hak'uri ni a yanzu ban
shirya yin aure ba.......
Tana gama ce masa haka ta shige cikin gida dan bata da wani abun da zata kuma gaya
masa , Jabir wata iska ya furzar a bakin sa yana me fad'in " bazai yuwuba Aysha wallahi sai
kin aureni dan nine nafi dacewa dake , yana gama fad'in haka ya juya yashige motar sa yabar
k'ofar gidan ......
Aysha na shiga cikin gida tasamu Ruma tana cin d'an wake ita da Gogal suna hira ,
band'aki tashiga dan yin wanka dan zafi ya dame ta sosai.....
Hameed yana ganin tafiyar Jabir ya fito daga motar ransa a d'an b'ace , wato Aysha bazata
daina kula mazan nan yan iska ba , amman tunda yadawo kuma dama da maganar auren ta
yazo komai yazo k'arshe , cikin gidan yashiga d'auke da sallama a bakinsa , Gogal tanajin
muryar sa tace " wanake ji kamar Yarona Hameed ? Hameed yana murmushi yace " nine
Gogal lale marhabun da yarona saukar yaushe ? Hameed yace " jiya da daddare Mama , tuni
ta shimfid'a masa tabarma saboda ana zafi shiyasa batace ya shiga d'aki ba , Ruma ta gaidashi
cike da girmamawa sannan ta tashi ta basu waje....
... Aysha kuwa tana toilet tana jinsu samun kanta tayi dajin wani farin ciki , Hameed yadawo
kenan lallai Gogal dole tayi murna da dawowar Hameed , .....
Nan suka gaisa ta tambaye sa ya iyayen nasa tare da tambayar sa ya aiki , Hameed duk ya
sheda mata komai lafiya itama yashiga tambayar ta ya ya barsu , lafiya lau Muke Yarona ai
kullum cikin zuba ido nake tunda shrkara ta cika , Ruwa Ruma ta kawo masa tare da zubo
masa d'an wake , Dai dai lokacin Aysha ta fito daga toilet tagama wanka , Hameed sai da
k'irjin sa ya buga ganin surar Aysha a yanayi da bai tab'a gani ba , duk da tasa hijab amman iya
gwuiwa ne ana hango k'asan k'afarta , da sauri ya saita kansa dan gudun Gogal ta fahimceshi ,
nan Aysha ta shige d'akin ta da sauri , Hameed ruwa ya d'auka yasha sannan ya faracin d'an
waken , dama shi ma'abocin son abincin gargajiya .....
Bayan ya kammala suka ci gaba da hira da Gogal , nan su Aysha suka fito dan zasuje
gidan su ruma d'ebo mata wasu kayan , Aysha ta gaisar da shi ya amsa ba yabo ba fallasa.
Suka gayawa Gogal tace musu sai sundawo sai dai kar su zauna , .....
Suna fita Hameed yacewa Gogal " Mama nazo muyi magana dake dafatan zaki amince ,
Gogal tace inajinka Yarona fad'i duk abinda kakeson fad'a , gyara zama yayi sannan yace "
Mama inason Auran Aysha da fatan zan samu , Gogal tayi shuru na wasu lokuta sannan ta
nisa tace " a gaskiya Yarona Aysha bata dace dakai ba , Aysha takasance a baya batajin
magana duk ta gama yawace yawacen ta , duk da a yanzu Aysha ta tuba tadaina komai amman
bazan iya b'oye maka wannan halin nata ba , kaima yarona ne kuma na yaba da hankalin ka
dan haka bazan so in rufeka da komai ba , Hameed yayi murmushi yace " nasan komai game
da Aysha dan tafad'a min komai lokacin da kika kwanta a asibiti , inhar Aysha ta shiryu wallahi
a shirye nake na aure ta kuma banaso bikin ya wuce sati biyu , Gogal tace " sati biyu Yarona ai
yayi sauri kabari ku fahimci juna Mana , Hameed yace " ba dad'ewa zanyi ba Mama daman
maganar ce tadawo dani kuma nagama magana da iyayena , sun amince min akan auren dan
haka zasu zo nema min auren ta cikin satin nan , Gogal shuru tayi na wasu lokutan sannan
tace " Babu komai za muyi magana duk yadda muka yanke zangaya maka , Hameed yace "
karki damu Mama kece me aurar da Aysha dan haka kece zaki yanke komai , murmushi tayi
sannan tace " nasan da hakan Yarona amman komai yanason nutsuwa da kuma shawara , da
wannan suka gama magana Hameed ya tashi ya fita , kayan tsarabar da yayi musu ya shigo
musu da shi sannan yayi musu sallama ya tafi......
Sai Bayan sallar Magriba su Aysha suka dawo , Bayan sunci abinci sunyi sallah suka
zube suna hira har Gogal d'in , nan aka turo kiran Ruma saurayin ta me suna Ahmad wanda
shine zata aura , dan tun rabuwar ta da Khalid bata sake kula kowa ba , Ahmad d'in ma dan
tayaba da hankalin sa kuma ta gwadashi ta hanyoyi da dama batasame sa da wani mugun halin
ba , shiyasa yana zuwa basu d'auki wani lokaci ba aka samu su rana , ....
yarage daga Aysha sai Gogal suke hirar tasu , a cikin hirar da suke Gogal ta sako maganar
Hameed akan zuwan da yayi , Gogal tace " Aysha yaron nan da gaske yana sonki kuma yace
cikin satin nan zai turo iyayensa , Aysha tayi shuru batace komai ba , meyasa Hameed bazai
tambaye ta ba zai ce zai turo iyayen sa ?
[11/08, 3:43 pm] Maman Islam: *'YAR HANNU*
🤒🤒
_NA_
*Zee MD*
*WOMEN WRITERS ASSOCIATION*📚
( Domin Marubuta Mata )
✨ (W.W.A) ✨
https://www.facebook.com/106752595253176/posts/107924965135939/
*Bisimillahir Rahamanir Rahim*
_Page._ 31
Aysha ta kalli Leeemah tace " K'awata tashi mutafi kingama aikin ki , dama tuni
Leeemah tasa kayan ta dan haka mik'ewa tayi kawai suka nufi hanyar fita , Muryar Khalid a
fusace yace " Aysha inaso duk kud'ad'en da nakashe miki kidawomin da abuna , dan ashirye
nake in k'waci kud'ina ko taya ya tunda bake na nemawa ba , cak Aysha ta tsaya tare da jiyowa
tana duban Khalid , tabbas tasan me hali baya tab'a canzawa amman batayi tunanin Khalid zai
sake magana ba dayaji ko wace ce ita , wani murmushi tayi me ciwo sannan tace " inaso
kasani duk sanda ka shirya karb'ar kud'in ka ko tayaya d'in nima na shirya , tunda har hakan
bazai gyara maka rayuwa ba sai ma wani sabon furuci da kake bina dashi , to tabbas kota yaya
ka shirya nima a shirye nake sai najika , tana fad'in hakan tasa kai ta fice daga d'akin batare da
ta kuma bi ta kansa ba , Leeemah na biye da ita har suka k'araso wajen motar ta suka shige
tare da ficewa daga cikin Hotel d'in , ....
Tunda suka taho ba wanda yayi magana har sai da suka kusa zuwa hanyar da zata kaisu
gidan su Aysha, Sai a lokacin Aysha ta dubi Leemah tace " inane unguwar ku inason inkai ki ?
Leeemah tace " kawai ki saukeni anan na hau Napep ya k'arasar dani , nan Aysha ta bata
dubu Ashirin sukayi sallama ta sauke ta ......
Aysha na k'arasowa cikin gida tafara Hon. Alamar azo a bud'e mata , ganin shiru Habu
bai zoba yasa ta sauko da kanta ta nufo k'ofar gidan dan ta bud'e , sai dai tana zuwa taga
kwad'o alamar gidan a rufe yake , wani irin fad'uwar gaba Aysha taji ta kamata Ina Gogal ta tafi
haka alhalin bata da lafiya ? tsayawa tayi tana nazari can ta hango Jabir ya nufota yana wani
murmushi , gaban tane ya fad'i dan yanzu ganin Jabir yazame mata annoba , aikuwa yana
k'arasowa yace " Hajjaju Aysha 'Yar Hannu yana ganki a tsaye ? had'e fuska tayi sannan tace "
to dan kaganni a tsaye wani abun ne ? wai me nayi maka haka kake shiga rayuwata ? Jabir
yayi murmushi yace " babu abinda kikamin kawai inasonki ne kuma inaso inga kin shiryu ,
Aysha ta galla masa harara sannan tace " dana shiryu da kar na shiryu meye matsalar ka ?
inaso kafita daga cikin rayuwa ta tunkafin nayi maka abinda bakayi tunani ba , wannan lokacin
dariya sosai Jabir yasa har da tafawa kafin yace " to nikuma wanne abu zakiyi min zakiyimin
yadda kikawa Khalid ne shima , sosai Aysha taji bugawar k'irji amman sai ta daure ta saita
kanta tace " zanyi maka mutuk'ar kaima kashiga hurumina , Jabir yace " sud'in wanne Hurumin
naki suka shiga ? kawai dan kin kasa hajarki sun siya shine zaki dunga binsu kina musu
barazana ? runtse idon ta tayi dajin Abinda yace , katseta yayi da cewa " kece kikayi tallah
kuma aka siya to dan me zaki dunga binsu kina anshe musu kayan
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 11 Chapter of 13