Abba ya hau kiransa amma ya ji layin a kashe, ya kira sau uku duk a kashe, Umma tace "Wai wa yake nufi ne?? Wa ake nema ma aure kan aure?" Abba yace "Tare mu ka karanta text din nan yanxu Hajiya Ramlah" Umma tace "Toh ina jin shaye shaye ya fara a can din ko" Abba dai bai ce komai ba, Umma tace "Ni dai na gama magana, idan xa ayi mata adalci ayi mata, a tunaninku gata xa ayi mata tunda xa a aura mata d'an sarki, to amma kwanciyar hankalin xaman gidan auren fa, tunda naji ance uwar tasa ma ba so take ba, kuyi ma Allah a duba lamarin nan idan kuma shakkar yi ma Hajja magana ake ni sai inyi mata wllh" daga haka tayi ma Abba sai anjima ko gidan bata sake shiga ba ta bude motarta ta shiga, driving take amma tunanin solution da xata samar ma Jiddah take don in dai kuwa aka yi auren nan kilan bata doron kasa ne, samm baxata ta amince da auren ba, baxata ta6a bari a shiga hakkin yarinya ba. Abba na komawa cikin compound ya sa a kira masa Ummi, tana fitowa ya mika mata wayarsa yace "Ko xaki iya fahimtar wani abu a message din nan kiyi min bayani??" Ummi sai karanta message din take da surprise barin da ta ga cewar Aliyu ne sender din, can ta kalli mai gidan nata tace "What's the meaning of this?" Yace "Shine nake son ki min bayani" tace "Jiddar matar aure ce da xai ce kar a nemi aure kan aure?" Abba yace "Shine nake son fahimta Hauwa" Ummi tace "Ikon Allah, to ka kirasa" Abba na kokarin sake kiransa yace "A kashe wayar" sai gashi ance wayar a kashe, Ummi tace "Ji d'an rainin wayo, aurar da ita yayi ne ba a sani ba, ko ko?" Abba dai bai ce komai ba yayi shigewar sa ciki, Ummi ta bi sa da kallo, gaba daya ta ma rasa wani tunanin xata yi, anya kuwa Abuturrab na da kai? Menene manufar wnn text din wai kar a nemi aure kan aure, to ko aure yake nemar ma Jiddar basu sani ba ne. Abba na komawa gun brothers dinsa su ma ya basu wayar su duba message din, bayan sun duba da daddaya da daddaya, suka dinga kallon Abba, Alhaji Salmanu yace "Neman aure kan aure kuma? To ko dai bai saketa ba ne dama Alhaji Usman?" Abba yayi dariya yace "Ya fara hauka kenan, ai har yanxu takardan na nan bai je ko ina ba" Abba na fadin haka ya mike ya wuce daki sai gashi ya fito da takardan ya mika ma Alhaji Salmanu ya amsa ya karanta sannan ya ba duk sauran ma suka duba, Alhaji Salmanu yace "Ikon Allah, to me yake nufi da hakan? Is he even in his right senses?" Abba ya daga kafada yace "I thought as much" naxari duk suka yi shiru suna yi, Alhaji Umar yace "Try his line ko xai yi connecting" Abba ya sake kira yaji a kashe, Alhaji Lawal yace "Toh ko dai komawa yayi aka sake daura masa aure da yarinyar?" Kallonsa Abba yayi da sauri almost with shock, sai kuma yayi wani dariya yace "Aa he must be joking ashe, har ya isa ya sake yin hakan? Da kuwa nayi disowning dinsa wllh... Allah kuwa da ya ga the other side of me, wato ga yan iska ya ajiye, wllh in har hakan ne ya kasance Aliyu xai yi mamakina ainun" Alhaji Umar yace "Ikon Allah, that just dawn on me bayan Lawal ya fadi haka, in dai kuwa ba shi ya koma ya aureta ba to wani ya kai ya aureta, don babu yanda xai turo wannan message din idan ba dayan biyun abinda na fada ya kasance ba, but that's bad... Who does that, ya maida mutane kananun mutane kenan yake nufi ko me?" Abba dai da alama ransa idan yayi dubu ya baci, daukar wayarsa yayi ya tura ma Abuturrab text kamar haka, "call me immediately after switching on ur phone, i said immediately!!!" Alhaji Lawal yace "Lallai kuwa tunda har ya turo message din nan Komawa yaron nan yayi aka daura masa aure da yarinyar ba tare da sanin kowa ba, tunda ya san waliyanta sannan tun farko shi dama babu wanda yayi masa waliyyanci a cikinmu, don haka abu ne me sauki garesa" Abba dai baya cewa komai a parlon...
Har bayan sati da text din nan wayar Abuturrab a kashe yake, Jiddah na xaune daki tare da Maimoon da daddare tana son mata magana amma ta kasa, don bata ma san ta ina xata fara maganar ba, tun 3 days ago maganar ke cin ta amma ta kasa yi mata shi, can dai ta dake a hankali tace "Maimoon ya jikin Ya Aliyu?" Maimoon ta kalleta tace "Wllh I don't know, I can't reach him for a week now" Jiddah tace "Both Whatsapp?" Maimoon tace "Baya hawa...." Jiddah bata kuma cewa komai, Maimoon dai sai kallonta take, mikewa tayi ta koma side din da take kwanciya tayi kwanciyarta.... Ranan Friday bayan an sauko sallan Juma'ah, Jiddah na xaune xaune bakin tap din compound din gidan tana wanke hijabs dinta biyu don Safiyya na wanki a washing machine aka bude gate din gidan, daga kai tayi a tunaninta Ahmad ne don in dai ya shigo kd ya kan fara xuwa ya gaida Umma kafin ya tafi gidansa, tun da ya shigo take kallonsa kamar yanda shi ma yake kallonta, saukarsa kasar kenan kuma babu inda ya fara nufowa sai gidan Umma......
My strength ends here wllh... Thank you!!
*Wa enda nake bi dari biyar su ji tsoron Allah su xo su biya bashi su sauke nauyi ko ince hakki!! alfarman wannan ranaku da muke ciki, domin fatan yin ibada amsasshe... Allah ya amshi ibadunmu ya sa muyi sallah lafiya Ameen*
Littafin Jiddatul Khair na kudi ne, it's 500 via
3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u show ur evidence of payment via 07087865788... Thank you
It’s S.SQAURE COLLECTION ANNIVERSARY YAYY🎊🎉
Jama’a gawata gagarumar sanarwa ku gyara zama kuji.
S.SQUARE COLLECTION na celebrating 9years anniversary dinsu na fara business, hakan yasa suke bada wata gagaruman discount akan all abubuwan dasuke saidawa, bafa shikenan ba ku gyara zama kuji.
A shagon S.SQAURE COLLECTION zaki samu abubuwa da dama kaman haka;
Hadaddun dinkakkun Gowns wato dogayen riguna.
Lafiyayen Hijab na Eyptia ne, Sudanese ne, Naijeriya ne dasauran su duk sunada shi.
To ina masu baki achan achan irin mu gafa namu nan.
S.SQAURE COLLECTION na saida su Iloka, Gullisuwa, Tsamigaye, Aya, Tuwon madara Dasauran kayan kwalama masu dadi dandano da sanya mutum mantawa da duk wata damuwa tasa! Hehehe badai kun fara gajiya ba danfa ba anan kadai S.SQUARE COLLECTION suka tsaya ba.
Ina matan kamshi dasu Anty turare S.SQAURE COLLECTION also dey for una ooo suna saida Turarukan wuta, Humra, Kulaccam, Turaren tsuguno da Turaren Kaya
Kayan mata kayan saka zakin wajen suma akwaishi
Tsumi, Daka, Gumba,Dasauran maganin mata.
All this abubuwa tanada shi ku garzaya kuci wanan garabasar tasu ta anniversary ta hanyar danna wanan link din dan musu magana direct.
wa.me/+2347030037697
Jiddah ce ta fara dauke idonta ta ci gaba da wankin da take a hankali, har ya wuceta sannan ta bi sa da kallo ta durkusa tana ci gaba da daurayan hijabs dinta, bayan minti goma ta gama ta shanya su sannan ta dauraye hannunta ta wuce cikin gidan, Xaune ta gansa a parlon yana danna wayarsa, su Maimoon na daki Umma ma na bedroom dinta, Huraira kuma na kitchen tana girkin lunch, ta karasa cikin parlon tana kallonsa a hankali tace "Sannu da xuwa..." Kallonta shi ma yake yace "Kema sannu" Xata tafi dakin Umma taji yace "I will be back later" Ta juya tana kallonsa, mikewa yayi ya nufi kofa ita dai tana tsaye har ya fita parlon. A hankali ta nufi dakin Umma ta yi sallama sannan ta bude, Umma na xaune tana waya, Jiddah ta xauna saman carpet ta jira har ta gama ta ajiye wayar, Umma na kallonta tace "Ya aka yi Jiddah?" Tace "Aa dama xan tambayeki sanda xa ayi awaran da kika ce ne" Umma tace "Au kinga ma na mance ni, duk sanda kika shirya ba matsala ki xo ki amshi kudin ingredients din, ke da Huraira ko Maimoon ku tafi kasuwa" Jiddah tace "Toh Umma" Daga haka ta mike ta fita daga dakin. Abuturrab na isa gidansa ya sauka daga d'an sahun da ya kawo sa, sai a sannan ya tuna ba shi da currency din kasar a tare da shi, ya nufi gun Mai gadinsa da ya taso yana welcoming dinsa da fara'a, yace "Ka basa dari biyar idan kana da shi" Mai gadin ya taho gun Mai adaidaitan da sauri xai basa kudin Abuturrab ya shiga cikin gidan, the compound looks so neat saboda yayi employing masu shara da gyaran flowers da ba su ruwa, yana isa entrance din shiga parlon ya murda kofar gently ya shiga ciki, kida ne ke tashi an kure sa har kusan karshe a parlon, ya dinga bin parlon that looks very untidy and unkept da kallo, ga plates sun fi kala biyar a kan carpet da duk ya baci da shinkafa da kwallin lemo, kayan kallon da suka yi uban k'ura ya dinga kallo, ya kalli dining area can ma duk plates da cups ne da breads ko kulle ledan ba ayi ba, calmly yake tafiya ya nufi stairs, shi ma duk yana jin yana taka k'ura kasan tiles din, bangarensa ya tafi ya bude kofa, sun fi su bakwai xaune parlonsa nan din ma dai plates ne da kwalaye na ciye ciyen da aka yi, suna ta labari ga kida na tashi a parlon ma amma bai kai na parlor ba, Duk suka juya jin an bude kofa, Aneesah dake xaune kan carpet sanye da zani da ves a jikinta ta mike da mugun mamaki tana kallonsa tace "My Captain saukan yaushe babu notice? Mun fa yi waya jiya baka ce min kana tasowa ba" Bai sake kallonta ba balle ta sa ran amsa ya bude kofar bedroom dinsa, Safara'u dake parlon ita ma da daurin kirjin ta mike da sauri tana cewa "In ji dai bai gan ni ba??" Bata jira an bata amsa ba ta fice da sauri daga parlon, Kawayen Aneesah duk biyar din su ma suka mike suka bi bayanta suka bar Aneesah tana xaxxare ido tana bin parlon da yayi kaca kaca da kallo, gashi takasa bin sa cikin bedroom din, Abuturrab ya fi minti biyu tsaye yana bin bedroom din nasa da kallo, kaya ne ta ko ina a xube tun daga kan gado har kasan tiles da carpet, bayan kaya har da takalma, ga farin bedsheet din saman gadon har ya fara fita hayyacinsa duk ya yamutse, sababbin jakunkuna na kayan sa wa har uku ya gani jere a dakin su ma duk a wangale, tun da yake bai ta6a sanin bedroom na iya xama haka ba sai ranan, wannan ya wuce untidy ko unkept, har wani tsami tsami mara dadi yaji bedroom din ke yi, ga kofar bandaki a hangame, ya lumshe ido ya juya ya bude kofar
ya fita, har sannan Aneesah na tsaye sai wuwwurga idanuwa take, bai kalli direction dinta ba ya fice, wani dakin daban ya tafi ya bude ya ga Safara'u xaune saman gado wanda shi ma din duk a yamutse yake, har lkcn daurin kirji tayi, ganin sun hada ido ya gaisheta, bai jira amsa dogon gaisuwan da take jere masa ba bayan ta jawo zanin gado ta yafa, yace "Alhmdlh mun gode Allah" Daga haka ya fice ya kulle mata kofa, wani dakin ya bude ya ga kawayen Aneesah sun yi dai dai a dakin ya kullo kofar ba tare da ya amsa gaisuwansu ba, bai sake bude wani dakin ba ya sauka downstairs ya fice daga gidan gaba daya, Abuturrab ya fi minti goma tsaye a kofar gida gashi babu cash a jikinsa babu Atm card, luggages dinsa kuma bai dauko daga airport ba, wayarsa ya ciro daga karshe ya shiga kiran layin Maimoon, tana dagawa bayan sun gaisa yace "Give the phone to ur frnd" Maimoon ta mika ma Jiddah dake gefenta waya, Jiddah ta amsa tana duba me kiran kafin ta kai kunne, Maimoon ta fita daga dakin, Jiddah tace "Ina ji" Yace "Did u tell them i am back?" Ta girgixa kai tace "Aa" Yace "Ohk, kina da cash wajen ki?" Ta d'an yi shiru, sai kuma tace "Aa sai a account, wanda Ya Ahmad ke sa min saboda makaranta" Calmly yace "Ohk ki bar wayar a wajenki..." Bai jira tace komai ba ya katse wayar ya karasa bakin titi, ya samu adaidaita ya koma gidan Umma, bai bari ya shiga can cikin layin ba ya sake kiran Number Maimoon, Jiddah ta daga, yace "Ki kawo min Atm card dinki waje yanxu" A hankali tace "Toh" ya katse wayar, ta mike ta dau jakarta ta cire atm card din ta mayar ta ajiye sannan ta dau gogaggen Hijab dinta ta saka ta bude kofa a hankali ta leka parlor bata ga kowa a parlon ba hakan ya sa ta fito da sauri ta nufi kofar fita, har ta isa gate tana waigen entrance din gidan, tana fitowa kofar gida ta dinga kalle kallen inda xata gansa, daga nesan ya hangota ya sauka daga kan adaidaitan, hakan ya sa ta gansa, ta karasa inda yake tana tafiya a hankali, idonsa na kanta har ta iso, ya sauke idonsa ya amshi Atm card din yace "Pin?" Ta gaya masa, yace "Thank you" daga haka ya shiga adaidaitan yace su tafi, ita kuma ta juya ta koma cikin gida. Abuturrab na cire kudin ya tafi yyi lodge a hotel, yana shiga dakin da aka bass ya kashe wayarsa, bayan ya huta yayi ordering abinci, Ana la'asar kuma ya fita xuwa airport don daukan luggages dinsa ya dawo hotel din a taxi, ya shiga da kayan ciki, bai sake fitowa hotel din ba sai da aka kira magrib ya fito yin sallah, bayan sun idar ya siya fruits ya koma cikin hotel din.... Washegari Asabar karfe tara ya kunna wayarsa ya shiga kiran Ramlah, tana dagawa da fara'arta tace "Yaya ka dawo ne?" Yace "Ahmad na gari?" Tace "Aa bai shigo ba satin nan, yace sai next week" yace "Ohk xan xo in amshi makullin motarsa yanxu" tace "Toh yaya sae ka xo" katse wayar yayi da yake ya shirya ya dau cash din da ya ciro jiya ya sa a aljihunsa sannan ya fita ya kulle dakin, a adaidaita ya isa gidan Ramlah, bayan ya sallamesa ya shiga ciki yana amsa gaisuwan mai gadi, ya wuce parking space, yana tsaye a nan ya shiga kiran Ramlah, bayan ta daga yace "Ki fito min da makullin parking space" tace "Yaya baxa ka shigo ba?" Yace "Ehh" tace "To bari in fito" ba a dau lkci ba ta fito rike da makullin motar, tana murmushi ta nufi parking space din ta risina ta basa tace "Ya hanya yaya?" Yace "Alhmdlh, ba sae kin ce masa na dawo ba" tace "Toh Yaya" bude motar yyi ya shiga yyi warming dinsa ita dai tana tsaye tana kallon sa, har daga karshe ta daga masa hannu ya fita da motar ita kuma ta koma cikin gida... Abuturrab ne xaune kansa a kasa yana sauraron uncle dinsa, Alhaji Lawal dake ta kallonsa da kyau yace "To ko dai kana shan wani abu ne wanda mu bamu sani ba Aliyu?" Shi dai bai ce komai ba, Alhaji Lawal yace "Dago ka kalleni ina maka magana" Ba musu Abuturrab ya dago kansa yana kallon Uncle din nasa, Alhaji Lawal yace "Tell me what exactly is wrong with u? Do we deserve being taking for granted Aliyu?" Abuturrab ya girgixa kai yace "Aa Abba ku yi hakuri, kuskure ne..." Alhaji Lawal ya dakatar da shi yace "You called this mistake also Aliyu?? Baka tsoron Allah ne da xaka kara kiran wannan ma da mistake??" Sake baki Alhaji Lawal yayi yana kallonsa, Abuturrab bai iya yace komai ba, Alhaji Lawal na jinjina kai yace "Lallai baka da hankali baka da manners, ka kuma mugun raina mutane ka daukemu for granted, ashe dama kai ka haifa kanka bamu sani ba?" Abuturrab yyi kasa da murya with remorse yace "Don Allah ku yi hakuri Abba, i know i wronged u all, but this the only way out for me, Abba baxai saurareni ba, so is Ummi... No one will give me a listening ear" Alhaji Lawal yace "Ohk ni kuma sbda ka yi shegen raina ni yanxu kake tunanin xan baka listening ear?? No... I am not giving u dat, and i am sorry babu wani abu da xan iya yi" Abuturrab ya kasa ce masa komai, Alhaji Lawal yace "I can't do anything about this... ina ce ita wannan yarinya idan ban mance ba babu irin hakuri da ban bakin da bamu baka ba a kan ka xauna da ita, ashe ka maida mu shashashai ne a lkcn ka je ka saketa kuna ta xama tare duk don sbda kana ganin ita ba class dinka bace or whatever, bugu da kari kuma u bluntly admitted baka sonta, to yanxun da ka koma ka aikata shirmen da ka aikata son nata ka fara yi kenan???" Nan ma dai Abuturrab bai ce komai ba, Alhaji Lawal ya daka masa tsawa yace "Bude baki ka bani amsa my frnd.. i am talking to u" A hankali yace "Ina son xama da ita yanxu Abba" Alhaji Lawal yace "U are very stupid, ae ba tambayar da nayi maka ba kenan.." Kasa basa amsa Abuturrab yayi nan ma, Ganin yanda Uncle din nasa ke kallonsa ya sunkuyar da kai, Alhaji Lawal yace "Toh ka saka a ranka cewar kamar yanda muka xaunar da kai kwanaki muka baka takarda da biro ka datse auren naku wannan karon ma hakan ne xai faru, mu ba 'yan banxa bane da xaka dinga controlling dinmu yanda ka so, kana aikata duk abinda ya xo kanka without our consent, we birth u..." Abuturrab ya marairaice masa yace "Abba don girman Allah ku yi hakuri, wllh ban koma na aureta da nufin in cuceta bane wannan karan, wancan lokacin ma kuskure aka samu, don Allah Abba kayi hakuri, i mean no harm to her..." Alhaji Lawal yace "Da nufin me ka koma ka aureta yanxu? Bani amsar tambayar nan" Abuturrab yace "Ina son xama da ita ne na har abada" Alhaji Lawal ya girgixa kai yace "Kamar dai yanda na fada you are very stupid, kawai ka koma ka aurota saboda kana son ku xauna tare har abada, wait!! are u mad??" Abuturrab yace "Abba ni dama fa ban ta6a buda baki nace bana sonta ba, kawai sharrin shaidan ne da kuma yanda kowa baya son auren shi yasa na aikata abinda na aikata, amma wllh ban ta6a cewa bana sonta ba" on a serious note Alhaji Lawal yace "Daga Hajja a rashin alkibla sai kai, anyway... I am so dedicated today, don haka idan Allah ya amince mana gobe xan shiga kadunan, xaka iya tafiyar ka sae na xo goben..." A hankali Abuturrab yace "Xan jira mu tafi tare goben in sha Allah" Alhaji Lawal yace "Allah ya kai mu" Godiya Abuturrab yayi ma uncle din nasa sanan ya mike ya nufi kofa hoping this will be the only challenge he is to face till end, Alhaji Lawal ya bi sa da kallo har ya fita yana mamakin karfin hali da taurin xuciya irin na Abuturrab, kiri kiri yayi ta abu ba tsoro. Abuturrab ya fi minti daya tsaye kofar parlon Abbansa ya kasa bude kofan, bai ta6a jin mugun shakkan Abbansa irin na lkcn ba, bai san me ya sa wnn karan ko Aunty baya jin ta kamar yanda yake jin Abbansa, ga bugun xuciyarsa da ya tsananta, it's been long da ya shiga yanayin nan da yake ciki yanxu, muryan Umma yaji a bayansa ta rike ha6a tace "Kai kuma yaushe a gari??" Ya juya da sauri, yyi feigning smile yace "Good evening Umma" tace "Saukan yaushe?" Ya d'an fara kame kame kafin yace "Jiya" tace "Ikon Allah, to sannu da dawowa..." Bude kofar parlon tayi, lkci daya fara'ar da ke fuskarta ya bace, ta wani sha kunu ta shiga parlon, tunda aka kirata aka ce ta xo gidan tayi tunanin xancen baxai wuce na auren da suke shirin laka6a ma Jiddah ba, kuma ta sha alwashin yau kam sae inda strength dinta ya kare, dai dai take da kowa, ganin Hajja xaune parlon ta wani kara daure fuska ta nemi waje ta xauna, Abuturrab ya shiga parlon kansa a kasa gabansa na mugun faduwa, xaunawa yyi saman carpet ya kasa kallon kowa, a hankali ya fara gaida Hajja kafin sauran occupant din parlon, Hajja dae fuskar nan nata babu ya6o bbu fallasa, Umma ma babu yabo babu fallasan tace "Ina yini Hajja" Hajja ta rike kanta tace "huhuhu wllh tun da naje Masar na samu saukin gaishe gaishen jaraban nan, yo kowa na ta kansa ina batun wani gaisuwa, su basa haka a can wllh, duk wayayyu ne, a kasar nan kowa sae yace sae ya gaisheka alhalin wani gaisuwar ma bai kai ciki ba, to ni dai na yafe, ko Usman ma ban amsa gaisuwarsa ba balle wani...." Ko kallonta Umma bata sake yi ba tana jan counter dinta... Alhaji Umar ne ya bude wajen da addu'a, sannan bbu 6ata lkci kuma babu boye boye in Brief Alhaji Lawal ya maimaita masu duk abinda Abuturrab ya sanar masa jiya a Zaria, Babu wanda bai girgixa ba a parlon, Abba dai kallon ceiling kawai yake, gaba daya sauran mutanan parlon kallon Abuturrab suke irin kallon tsoro, babu ko kiftawa, shi ko kansa na sunkuye xuciyarsa na bugawa, Hajja dae sae wani murmushi take me sauti irin na bosawa tana girgixa kafa da kai, Bayan shirun kusan minti biyu da ya ziyarci parlon, Aunty ta mike duk ta hada xufa daga sama har kasa tana girgixa kai tayi wani murmushin takaici tana nuna Abuturrab tace "Wllh karya kake Aliyu, karya kake baka isa ka kunyata ni ka toxarta ni, ka walakanta ni a idon duniya ba wllh... Karyanka ta sha karya wllh" kofa ta nufa ta fice daga parlon da sauri, Umma da Ummi har sannan hangame baki suka yi suna kallon Abuturrab, Hajja na kallon Abba a hankali tace "Yau da ace a Masar ne idan ba a garkame d'an ka a kurkuku ba shegiya nake Usman, ae wannan shine ta'addanci mafi muni da mutum xai yi a hukuntasa a kasar Masar, kai ba a ma ta6a haka a can ba wllh, Aliyu dai ya fita sahun mutanen kwarai, Aliyu mutumin banxa ne... Kiri kiri ya nuna ma d'an uwansa na jini bakin ciki, da hassada, ba fa son yarinyar yake ba kawai bakin ciki ya mayar da shi gun danginta ya sake aurota a gantale, su ma dai dangin nata matsiyata ne, kawai sun mayar da 'ya kaza don yaje yyi masu fafan yana tukin jirgin sama, to meye kuma tukin jirgin sama Allah na tuba abinda matsayinsa da d'an acaba da d'an taxi daya a idon duniya, wato sbda hassada sai ya ga ta yanda yarima zai aureta ko??" Cije yatsa Hajja tayi sae kuma ta rushe da kuka tace "Wllh mun fi awa biyu da mutumin nan muna garari a hayin rigasa, katon ya gilla min karya wai an rushe gidansu Jiddah daga karshe ma gaya maka ne kawai ban yi ba Usman wllh a tsakiyar titi ya yasar dani yyi wucewarsa kamar mara galihu duk na hada xufa, har ya kai ya kawo mutane suka xata almajira ce idan an xo wucewa sae a mika min ashirin, goma...." Sosai Hajja take kuka tace "Ni a tarihin duniya ma ban ta6a jin an haifi me hali irin na Aliyu ba, kuma a bisa dokan Masar duk wanda xai iya aikata abinda ya aikata to xae iya kashe rai babu ko darrr, shi yasa ma ake garkamesa a gidan gyaran hali, ni dae xan xuba
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 56 Chapter of 57