da Jiddah ke ciki tace "Kaya kala nawa kika taho da?" jiddah tace "Na yau ne da gobe kawai" Umma tace "Ohk, xaku fita da driver xai kai ki gidan kawata yanxu, tunda naga ke ba son taro kike ba ai" Jiddah ta d'an yi shiru, sai kuma a hankali tace "Umma ai yace xai dawo anjima ya daukeni" Umma tace "Ehh kafin ya dawo din, sai yaje can gidan ka ya daukeki, ki tafi da jakar kayanki kawai" Jiddah tace "Toh" Bayan mota Umma ta sa ta shiga ta ajiye mata jakarta a gefenta, sannan driver ya bar gidan bayan ta sanar masa inda xai kai ta, tafiyar kusan minti ashirin da wani abu suka yi suka isa gidan Hajiya Rukayya, Drivern yayi ma mai gadi maganan cewar yayi leading dinta har entrance din gidan, tana shiga cikin compound din mai gadin ya nuna mata direction da xata bi, ta makale jikin kofar ta kwankwasa a hankali, ta fi minti biyar tsaye sannan aka bude kofa, wata mata ce ta bude kofar ganinta tace "Ke ce bakuwar da Hajiya ta sanar kina xuwa?" Jiddah ta gyada mata kai kawai, Badiya ta amshi jakar hannunta tace "Toh sannu da xuwa, Bismillah" Bin bayanta Jiddah tayi, ta xauna parlor, Badiya ta shiga dakin yan matan Hajiya Rukayya ta ajiye mata jakarta. Karfe biyar saura Abuturrab ya isa gidan Umma, ya fi minti biyar cikin mota sanin da mutane gidan shi kuma ba iya shiga xai yi ba, daga karshe kawai Maman Abdallah da ya gani a compound ya aika ta kira masa Jiddah, ba a dau lkci ba sai ga ta, tace "Wllh yallabai Umma tace suna can gidansu amarya" Da mamaki ya dinga kallonta, can yace "Toh nagode" Tada motar yayi ya bar layin ya dau hanyar gidansu, bayan yayi parking a waje ya dau waya ya kira Siyama tana dagawa yace "Ki ce Jiddah ta fito" Tace "Yaya mu muna wajen make up fa, kuma har muka bar gidan bamu ga ta xo ba" ya d'an yi shiru, kafin ya katse wayar. Tunanin wanda xai kira ya dinga yi a ciki amma ya ga ba kowa kuma don ko hauka yake ya san baxai kira Ummi ba, d'an tsaki yyi ya tada motarsa ya bar wajen. Tun da Abuturrab suka isa wajen da ake dinner tare da Ahmad da sauran abokansu yake xuba ido yaga inda xai hango Jiddah a wajen amma bai ga alama ba, hakan bai wani damesa ba don dama xuwa dinner din ne baya son ta xo ya kaita can gidan Umma, tun sanda Aneesah ta kyallara ido ta gansa take masa zarya a wajen, barin yanda taga yayi wani kyau cikin fararen shaddan da duk abokan Ahmad suka saka, ita a dole sai ta ankarar da jama'a cewar saurayinta ne, Ko mayafi bata daura kan damammen doguwar rigar jikinta ba shi dai sai bin ta yake da kallo, wani abokin Ahmad dake side din Ahmad din Abuturrab ke ta kallo yana son tuna inda ya ta6a ganinsa, he looks familiar amma dai bai ce masa komai ba, karfe goma saura Aneesah ta xo ta samesa tana yauki tace "My captain wai xaka xo ka maida su Mummy gida yanxu" Ya d'an kalleta yace "Toh ai bani na taho da motata ba, ban ma san inda yake yanxu ba, nima abun hawa na samu ya kawo ni nan" Tace "Haba Captain, ko wajen daya daga abokanku baxa ka amshi mota ka maida su gida ba...." Ko rufe baki bata yi ba sai ga aunty ita ma ta sha wani ubansun lace tana goge xufan goshinta da handkicin hannunta tace "Aliyu ka tashi ka maida su Hajiya Safiyya gida" Bai ce mata komai ba, tace "Ko baka ji na ne?" Yace "Toh bari in nemi wanda makullin motata ke wajensa" Juyawa tayi ta bar wajen, ya kalli Aneesah da ta hade rai tana kallonsa, d'an murmushi yyi yace "Kema dai kinsan wasa nake, dole in nemo mota ko na waye in maida su" Yana fadin haka yayi patting shoulder din Umar dake side dinsa yace "Bani makullin motarka pls" Umar ya mika masa sannan ya mike yace "Kice su fito" Daga haka ya nufi hanyar fita daga hall din.... Karfe daya Abuturrab ya koma gidansa bayan sun maida duk bak'in da suka je dinner masaukinsu, ya fi minti goma xaune a parlornsa thinking of where Jiddah might be, daxu da ya maida Mum din Aneesah har gida ya shiga bai ga alamar tana nan ba, shi kuma ya kasa tambayar Ummi, akwai wasu bakin da still ya mayar can gidan Umma, can ma ya shiga bai ganta ba, bayan kuma ya tambayi Maimoon tace ai tana gidan Umma, mikewa yayi daga karshe ya wuce sama xuwa dakinsa don ya gaji sosai. Da asuba kiran sallah ya farkar da jiddah, ta mike xaune daga kan gadon da take tana kallon yarinyar dake kwance saman gado gefenta, tun xuwanta gidan jiya banda ita da Badiya bbu kowa a gidan har tayi bacci wajajen karfe goma saura, bandaki ta tafi ta dauro alwala ta fito sannan ta tada yarinyar da baxata wuceta ba, yarinyar ta mike xaune, ita kuma ta shimfida darduma ta fara sllh.... Karfe tara saura yarinyar da tayi wanka ta shirya cikin atamfa ta kalli Jiddah tana murmushi tace "Ya sunanki?" Jiddah tace "Jiddah" Yarinyar tace "Ni sunana Amina, mu je parlor mu gaida su Mama sun fito" Jiddah ta saka Hijab dinta ta bi bayan yarinyar suka fita parlor, yan mata biyu ne xaune parlon sai Hajiya Rukayya, wanda Jiddah na ganinta ta gane mahaifiyarsu ce don sun yi kama, Jiddah bata yarda ta xauna kan kujera ba ta gaida matar, ta amsa da fara'a tana tambayarta ta tashi lafiya, Jiddah ta sunkuyar da kanta, sauran yan matan ma sai kallon Jiddah suke, Wani ne ya shigo parlon daga waje waya kare kunnensa, ganin mahaifiyarsa a parlon ya katse wayar ya zauna yace "Ina kwana" Tace "Lafiya lau... Jiya kuma sai kayi wucewarka ka bar mu a event center" Yace "Mama ciwon kai wajen ke sa min, it's been long da na tsaya waje that's so noisy haka" Hajiya Rukayya tace "Toh Allah ya kyauta" Tun da ya shigo Jiddah ke kallonsa kamar taga wani mugun abu, Ganin xai kalli direction din da take ta dauke kanta da sauri gabanta na faduwa, Yace "Mama bakuwa ku ka yi?" Hajiya Rukayya tace "Ehh, ga breakfast dinka can a dining" Yace "Ohk" sannan ya mike ya tafi dining din, Mikewa Amina tayi ta tafi dauko ma ita da Jiddah breakfast don taga alamar yayyinta duk sun yi, kuma da ba don Jiddar ba tare xata je ta xauna su yi breakfast din da yayanta, gaba daya Jiddah ta kasa sakin jiki a parlon, lkci lkci take satan kallon hanyar dinning din, daga karshe dai ta mike xata wuce daki, Hajiya Rukayya tace "A daki xaki yi kumallon?" Ta d'an yi murmushi ta gyada kai ta wuce daki da sauri, dole dakin Amina ta kai masu Breakfast din. A ranan bayan an sauko juma'ah aka daura auren Ramlah da Ahmad... Abuturrab na tsaye daga bakin kofa a bedroom din Umma bayan sun gaisa yace "Tana gidan nan ne Umma?" Umma ta kallesa tace "Wa?" Jin bai ce komai ba tace "Wai Jiddah?" Yace "Eh" Tace "Ba a jima ba suka tafi can gidanku da Maman Abdallah" Bai kuma cewa komai ba, tace "Hajja kuka tace tun da ta xo baka je ka gaisheta ba" Yace "Ai ban je can gidan ba Umma, anjima da daddare xan shiga in gaisheta" Tace "Yauwa gwara kaje din da daddare dama ya fi, an kai maku abincin kuwa?" Yace "Ehh an kai" daga haka ya juya ya fita. Da yamma su Amina duk suka tafi gidan yinin Biki, Hajiya Rukayya kuma tun karfe goma dama ta bar gidan, gidan ya rage daga Jiddah sai Badiya, tana kitchen tare da Badiya tana tayata girkin dinner, wayar Badiya dake parlor ya fara ring, Badiya tace "Dauko min wayar Jiddah..." juyawa tayi ta fita xuwa parlor, dai dai nan kuma aka bude kofar parlon suka hada ido, sanye yake da farar shadda idonsa sanye da glasses, sosai gabanta ya fadi, ta sunkuyar da kanta tana kalle kallen inda xata ga wayar Badiya, kasa karasowa cikin parlon yyi, sbda rudewa ta ma rasa inda wayar yake ta juya xata koma kitchen din taji yace "Jiddah" juyowa tayi suka sake hada ido, tayi murmushin karfin hali tace "Ina yini?" Ya karaso cikin parlon yana ci gaba da kallonta da mamaki, bata jira me xai ce ba ta juya da sauri ta koma kitchen din. Har Hajiya Rukayya ta dawo wajajen magrib Jiddah bata sake yarda sun hadu da Yousuf ba, can daki ta shige taki fitowa through out, Hajiya Rukayya na shigowa gidan ta kira Yousuf a waya don baya nan, yana shigowa tace "Don Allah bakuwar nan xaka ajiye min gidansu Ahmad yanxu, Hajiya Ramlah tace ka kaita" Yousuf yace "Ohkk" Har mota su Amina suka raka Jiddah, shi da Yousuf na xaune cikin motar tasa, Jikin Jiddah yyi sanyi ganin shi xai maidata, hannu kawai ta daga ma kanninsa har suka fita compound, sai da suka d'an yi nisa taji yace "Dama ke yar uwar Ahmad ce?" Kai ta gyada masa kawai, ya d'an kalleta yyi murmushi yace "Har yanxu sai kice min baki da waya ko?" Ta gyada masa kai, yace "What if na baki tawa wayar?" Ta xaro ido tace "Sai in ce wa ya bani?" Yace "Ni" ta girgixa kai tace "Aa bana so" yace "Jiddahh" ta d'an kallesa suka hada ido, yace "Kin san wani abu?" Ta girgixa masa kai, yace "Tun da muka hadu dake a jirgi kullum nake addu'an Allah ya sa in sake arba da ke, sae gashi kin xo har cikin gidanmu, kinsan me yasa hakan ya faru?" Nan ma ta girgixa masa kai, yace "It is because i have good intention toward u..." Jiddah dai tayi shiru kamar ta gane me yace. And the rest of the ride was silent, yayi parking dai dai kofar gidansu Ahmad ya juya yana kallonta, yace "Tunda baxa ki amshi wayata ba, xan kiraki ta wayar Maimoon" Ita dai bata ce komai ba, ta bude motar ta sauka, ta bude baya ta dau jakan kayanta, Yousuf na kallonta yace "Sai na kira" Tace "Toh" sannan ta nufi gate, shi kuma yayi reverse.... Dama Umma Jiddah kawai take jira don har ta saka Hijab dinta tana parlor a xaune, Jiddah na shigowa kuwa ta saka driver ya kai su can gidansu Abuturrab, har sannan da akwai sauran yan biki a gidan duk da tun wajen shidda saura aka kai amarya, direct parlon Abban Abuturrab Umma ta nufa tare da Jiddah suka shiga da sallama, Abban Abuturrab da brothers dinsa ne a parlon sai Hajja dake xaune kan carpet, bayan ta xauna suka gaggaisa, ta gaida Hajja ma, Hajja tace "Ni dai tun jiya nake ta kallon ki Ramlah, ya aka yi kika amince kika narka uban kiba haka, to ai ba kyau, mu a masar da tuni an kai ki asibiti duk hankali a tashe, mu ba ma haka a can" Umma dai bata ce mata komai ba, Can ta kalli Jiddah da ta sunkuyar da kanta tun bayan gaida su Abba tace "Ita kuma wannan sadaka yallar fa?" Nan ma babu wanda ya ce mata komai, Abba ya dau waya ya kira Ummi ya sanar mata Umma ta iso, su xo tare da Aunty, Hajja tace "Ai masar tayi wallahi, ba ruwanmu da abinda bai shafemu ba, kowa ta kansa yake, shi yasa xuwa jibi nake son idan Allah ya kai mu in koma, nafi wayo a can..." Ummi ce ta shigo parlon tare da Aunty, tunda Jiddah taga Aunty gabanta ke faduwa, Brother din Abba dake gefensa yace "Ka kira Aliyun ne?" Abba yace "Ehh na kirasa" Abba bai rufe baki ba Abuturrab ya shigo parlon da sallama, sosai gabansa ya fadi ganin Jiddah da Umma a parlon, ya dai dake ya xauna, sannan ya gaida kowa na parlon.... Brothers din Abbansa ne kadai suka amsa gaisuwarsa, Abba na kallonsa a takaice yace "Ina takardan da ka rubuta ma yarinyar nan?" Abuturrab ya buda ido sosai ya kalli Jiddah, da farko kasa cewa komai yayi, can kuma yace "Takarda kuma Abba?" Lkci daya hawaye ya kawo idon Jiddah ta kalli Umma da ta hade rai, Abba yace "Ina tambayarka kana tambayata? Are u stupid?" Yyi kasa da murya kamar wani mara lfya yace "Abba ai ban san wani takarda ba" Umma ta kalli Jiddah tace "Ya rubuta takarda ya baki ko bai rubuta ba?" Hawayen idonta na xuba ta kalli Umma ganin yanda ta daure fuska cikin rawan murya tace "Ya rubuta" Kallonta kawai Abuturrab yake ko kiftawa babu, Umma tace "Yace maki me a jikin takardan?" Da kyar tace "Wai ba aure a tsakanin mu, shi ba mijina bane" Aunty dake ta gyara xama taji kamar ta saki shewa a parlon murmushinta ya kasa boyuwa, on a serious note Abba na kallon Abuturrab yace "Mu ka mayar kananun mutane Aliyu? Ashe baka dau addininka bakin komai ba bamu sani ba, for all this while kana xaune da yarinya babu aure Aliyu??" Da kyar Abuturrab yace "Abba wllh wllh ba saki na rubuta a takardan ba..." Hajja dai ta hangame baki tana bin kowa da kallo a parlon, Caraf Aunty ta amshe tace "Toh ai aikin banxa kenan, tunda duk ka bi ka sanar ka saketa aure kuma ai ya lalace, ko ka mance addininka ne? Ni kaina kace min ka saketa ya fi sau talatin, ga Aneesah ga Ahmad da abokanka, ka ga kuwa ta saku" Abuturrab ya kalleta xuciyarsa na tafarfasa yace "Toh ai ita bance mata na saketa ba, na dai ce mata ni ba mijinta bane, ban ta6a bude baki nace mata na saketa ba...." Mikewa Abba yayi ya tafi daki sai gashi ya fito.... Abuturrab ya dinga kallonsa xuciyarsa na bugawa.
I just have to update today not to keep pple waiting, but I'm not feeling well....
Littafin Jiddatul Khair na kudi ne, it's 500 via
3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u show ur evidence of payment via 07087865788... Thank you
Fareeskinglow is a last bus stop do u wanna have a fairer skin or u wanna glow up ur skin here is the last bus stop where u can get ur desired results, a dream of having auniform complexion, glowing skin nd getting rid of any skin problems
Fareeskinglow karshe ne Ina kuke masu son farar fata ko masu son jikin yayi glowing kawai ga dama ta samu fareeskinglow taso muku da kayan gyara jiki fatarki yayi fari tayi sheki duk Wani tabo irin su konewar rana masu zagayen Baki a ido,masu pimples masu fama da combination skin Nan Baki Nan fari Ina mata masu ciki da masu jego wayanda wuyansu ke Baki duk fareeskinglow tazo muku da kayan gyara Wanda zaisa fatarki tayi sulbi da sheki ki komai kamar tarwada
Instagram -fareeskinglow_89
TikTok-fareeskinglow
Facebook page-fareeskinglow
WhatsApp -08031898240
Abba ya ajiye masa takarda da biro din hannunsa ya koma ya xauna yace "Tunda kana kokwanton auren da ake ce maka babu tsakaninku upon sanarwa da ka dinga yi ka saketa, to ni yanxu na umarce ka da ka kara wanda baxa kayi kokwanto ba a ranka" Kallonsa kawai Abuturrab ke yi kamar bai gane me yake nufi ba, Abba ya daka masa tsawa yace "C'mon my frnd ina sauraronka" Ya sauke idonsa a hankali yace "Toh ai Abba ni bance baxan xauna da ita ba, ban ta6a maku musun xama da ita ba, tuni na riga da na hakura...." Da karfi Aunty tace "Wllh karya kake munafuki... har ce min kayi kawai sbda Abbanka kake xaune da ita bayan ka saketa don kar ya samu labari yayi fushi da kai, kuma mu baxa mu xuba maka ido kuna xaman haram da yarinya ba, banda ma dai ni da na damu da lamarinka, ina ce ranan da na gano irin xaman da ku ke na xo na sanar gwaleni Abbanka yayi, to Alhmdlh ai yanxu tunda Hajiya Ramlah ce ta xo da batun da kanta" a kufule Hajja tace "Waye wannan dallah... Ya xa ki cika ma mutane kunne haka, ita uwar yaro ma ta ja bakinta tayi gumm kamar sabuwar kurma sae ke xaki dinga daga jijiyoyin wuya kina hak'i uwa dai kin hada wani abu da Aliyun, iyakarki fa matar ubansa, waye bai san auren cin amana ku ka yi da Usman din ba, daga dai ke da uwarki kuna fama da bakar talauci kuna tuyan masa da miyar taushe a daya daga gidajen hayana dake Tudun wada, shi kuma Usman na aikesa yaje ya fatattaki wani kato da yaki biyana haya kusan sati uku da karewar kudinsa, shkkn fa mata kika makale ma d'a na har da kullo masa yar wainar shinkafa a leda, to mu muka san abinda aka barbada a kai sai ga Usman ya birkice shi xai kara aure bayan ko shekara biyu da auren wannan Bafillatanar Hauwan bai yi ba, a takaice dai wllh tsallake maganata yayi ya aureki don na hanasa yaki ji ya bada toka a ido xai xageni, to ba dole in yafe masa ba tunda kowa dai yasan ku 'yan Benue ne, Mu dai babu abinda muka sani da ya wuce wannan, to yaushe ma xa a ga haka a Masar? Aa wllh basa haka...." Alhaji Umar yayi kasa da murya yace "Hajja ai ina ga ba wannan xancen muke yi a nan ba, duk ba shine ya kawo mu nan ba" a fusace Hajja tace "Toh don ba xancen ake ba sae in yarda ta gigita min jik'a, ni dai har gobe ina danasanin basu gidan hayata, daki daya ma fa suka kama suke rayuwa a ciki, kafin ma in basu dakin cewa suka yi gidan da suka baro watsi aka yi da kayansu bakin titi a unguwar mu'axu, gashi suka dinga ban wahala da kyar suke biyan kudin hayan a lkcn ma wllh.. to ni duk na wannan ba don Allah ma bai ce ayi tone tone ba, wanda kuma ya rufa ma d'an uwansa asiri Allah ma xai rufa masa asiri, amma ai an cuci Usman, to kuma ni ance min Aliyu ya auri yar hayi lkcn ina Masar, tsoro ya kamani na fita hayyacina na gigice da naji wannan xance sbda ni nasan ina ne hayi, kuma ni nasan mutanen cikinta, to sae gashi kabiru yace min ae suna xaune lafiya lau da matarsa, hakan yasa na saki raina duk da ban samu xuwa bikin ba, toh ynxu abinda ban gane ba wannan yar farar dake xaune ce yar hayin koko?" Umma tace "Ita ce" Hajja tace "Ikon Allah... toh kai Usman ya kake son kashe masu aure kamar kai ka halicci auren?" Alhaji Umar yace "Hajja babu wannan auren fa yanxu musulinci, don ya riga da ya saketa da bakinsa, sannan kuma ya saketa a rubuce, ni ba mijinki bane ae dai dai yake da na sake ki...." Hajja ta rike ha6a tace "Naga jaraba, a gabanka aka yi sakin kake wnn ciccijewan ko kawai karere, Sannan kana min gatsal gatsal idan shafa'atu ce xaka mata haka yau?" Abba yace "Don Allah Hajjaju kiyi shiru muyi abinda ya kawo mu nan, baki san komai a kan maganar nan da ake a nan ba, yaushe rabonki da kasar??" Hajja ta rungume hannu hade da ta6e baki tace "Nayi shiru, amma mu a masar wa xai yi haka? Wllh ba a haka, ayi aure kuma a dawo ana cewa ya mutu bai mutu ba" Ta gefen ido Abuturrab ya kalli Jiddah da ta kasa dago kanta, Aunty dai ta wani sha kunu a parlon tun bayan xancen Hajja a kanta, ita dai Ummi kallonsu kawai take ba um ba um um, a fusace Abba yace "U are wasting our time Aliyu, saki me hujja nake so kayi ynxu tunda duk wanda kayi a baya baka aminta da su ba..." Ya dago kansa yana kallon Abbansa yace "Abba ni nasan na aureta sannan ina xaune tare da ita saboda inyi biyayya gareka, bayan hakan babu wani abu kuma...." Abba ya katse sa yace "Toh an dauke maka wannan biyayyan, write d divorce now, sai ka tashi ka tafi Allah ya baka ladan taimako, ae kayi me wuyan tunda ka rabota da tsananin da take ciki" Abuturrab bai kuma cewa komai ba, bayan few seconds yace "Yanxu sakin xan rubuta mata?" Abba yace "Ehh, baxa ka mayar da mu kananun yara ba mu xuba maka ido, har yau mun rasa gane xaman me ku ke da yarinya" Abuturrab ya sunkuyar da kansa ya fara rubutu a takardan, d'aga kai Jiddah tayi tana kallonsa, ya gama rubutun ya mike da ladabi ya mika ma Abba, Abba ya amsa yana duba content din takardan, Abba yace "Good, Allah ya maka albarka, ya baka ladan taimako, daga yanxu kuma babu ruwanka da duk wani harka da ya shafeta, xa mu yi mata komai in sha Allah, kai ma kuma kayi iya naka kokarin don ta dalilinka duk muka santa, Allah ya maka albarka...." Abuturrab ya amsa da "Ameen" Sannan ya juya ya fita daga parlon jiddah ta bi sa da kallo, Abba ya nuna ma brothers dinsa biyu takardan, Alhaji Umar yace "To maa sha Allah, kaga yanxu babu wanda xai ci gaba da kokwanton xaman da suke, Allah ya sa hakan shine mafi alkhairi, shi kuma Allah ya saka masa ya basa ladan taimakonsa, ku kuma Allah ya baku ikon riketa da gaskiya" Aunty da taji jikinta na wani tsumma don farin ciki gaba daya ta mance abinda Hajja tayi mata sae jiran takardan take ya xo garesu, ai ko ana miko mata bayan ta karanta tayi wani murmushi ta mika ma Umma, Umma ma ta mika ma Ummi bayan ta karanta, Hajja tace "Amma na tsorata da lamarin Aliyu, Kunga da yana sonta da gaske ai kuka xai sakar mana a nan yace shi baxai saketa ba, amma almurin kamar jira yake gashi ya cike takarda da rubutu, aa gaskiya ba sonta yake ba, ku duba fa babu wani gardaman a xo a gani ya rubuta takardan, Lahh wanne mutum a masar, to amma ai shkkn sae a bani ita mu tafi Bauchi don kwana biyar xanyi a can kafin in koma Masar, idan ma kunga xaku iya biya mata jirgi kawai sai mu tafi tare, ai d'a na kowa ne bawa sai mai shi..." Umma ta kalleta da sauri tace "Hajja karatu xa a sata ai" Wani kallo Hajja ta watsa mata tace "Shi kuma masar din duk jahilae ne ba a karatu.... Banda neman magana ina ruwanki Ramlah, ni fa da d'a na nake kika tsomo baki, ko Ahmad ne ya tsintota a hayi?" Ta gefen ido Ummi ke kallon Hajja, Abba yace "Dama haka ake tafiya Masar din Hajja, ina laifin ma kice idan kin tafi a turo ta?" Hajja tace "Kai ba ruwana ni ku rabu dani, xa a Wani min caaa, dangin uwa ko na uba, meye hadina da ita banda Aliyu da ya aurota a gantale ya saketa kuma a gantale, kuma ma wasa nake, haka kawai inje in daura masu nauyi nima da ya ake bani yar gurasar da ake ban balle na tafi da wata?" Mikewa tayi tace "Banda Najeriya ina ake aure a gantale ayi saki a gantale, Hauwa taho ki bani sakon da na baki" Tana kai wa nan ta fita, Ummi ta mike ta bi bayanta, Aunty ta bi ta da harara, Umma ta sauke ajiyar xuciya tace "Alhaji xan tafi da Jiddah ta koma gidana ta fara karatu" Caraf Aunty ta amshe tace "Me xai hana tayi a nan din, ga dai sa'aninta su Aisha" Abba yace "Da nan din da can ai duk daya ne, Allah dai ya bata ilimi mai amfani" Ko kadan Aunty bata ji dadin haka da Abba yace ba, Umma tace "Toh nagode Alhaji, Allah ya tayani riko" Duk suka amsa mata da "Ameen" amma banda Aunty da ranta ya
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 29 Chapter of 57