parlon Umminsa yace "Umma muje in ajiye ku gida yanxu tunda driver din bai dawo ba" Umma ta ki tashi, Sanin at anytime Umma na iya tanka Aunty yasa Ummi tace "Ramlah dare nayi ku tafi a ajiye ku a gida" Umma ta mike ta dau wayarta tace "Sai mun yi waya yaya" daga haka ta fita Abuturrab na biye da ita bayan ya ciro makullin motarsa a aljihu, Umma bata ko kalli Aunty ba tana kai xuciyarta nesa tace ma su Jiddah su taso su tafi, daga haka ta fita parlon, Mikewa Jiddah tayi ta xaga xata wuce ta bayan Aunty dake tsaye tsakar parlon dab da ita tana kumfar baki, Aunty na ganin haka ta fixgota a fusace ta sauke mata lafiyayyen mari tace "Don uwarki ta bayana xaki bi ki wuce duk ga hanya a gidan sbda ni sa'ar uwarki ce fitsararriya?? An aiko ki wajena ne xaki bi ta bayana, to koma wa ya aikoki ki koma kice masa na fi karfin sa, baki gan ni ba, kaji min dai yarinya xaki xaga ta bayana duk ga hanya a parlo??" Bude baki Abuturrab yyi ya tsaya yana kallon Aunty, Jiddah ta kasa motsawa tana dafe da kuncinta ta rufe ido, hakan ya kara tunxura Aunty ta fincikota tana jan kunnenta tace "Ooo rashin kunya xaki min?" Karasowa Abuturrab yyi parlon cikin annoyance yace "This is mean of u Aunty, me ta maki xaki mareta haka? Who does that? Akan me xaki mareta a fuska, what offense did she commit?" Sake baki Aunty tayi tana kallonsa, can tace "Ni kake tambaya me yasa na mareta Aliyu?" Ko kallonta bai yi ba ya kalli Jiddah dake shessheka yace "Fita...." Taki motsawa hawaye na xuba idonta ya Fixgo hannunta ya nufi kofa, Aunty ta bi sa da kallo baki bude, sae bayan da suka fito balcony ya sake hannunta ta nufi gate tana goge idonta, Umma na tsaye jikin motar Abuturrab dake waje tana jiransa, har suka isa gidan Umma babu wanda yace komai a motar, Abuturrab yyi parking kofar gida Umma ta bude motar ta sauka, ta nufi gate Abuturrab ya bi ta da kallo, Safiyya dake gaban motar ta sauka, Maimoon ce karshen sauka a motar, yana kallon Jiddah kafin ta wuce yace "Dawo ki rufe min motata da kyau" Dawowa tayi ta bude motar ta sake rufewa sannan tayi wucewarta ciki. Washegari lahadi da yamma Jiddah na xaune balcony tare da Yousuf hannunta rike da Literature da ya sa ta karanta masa, mota ce ta shigo compound din, tunda ta kalli motar sau daya ta ci gaba da karatun da take Yousuf na kallonta, Ummi ta fara saukowa motar sannan Abuturrab ya sauka, suka nufo entrance din gidan a tare, tun basu kai balcony din ba Abuturrab ke kallonsu, Da ladabi Yousuf ya gaida Ummi ta tsaya Balcony din ta amsa da fara'arta, Abuturrab bai ko kallesa ba ya shige parlon, Jiddah ta gaida Ummi sannan ta mike ta amshi ledan hannunta, Ummi tace "Ki xauna kiyi karatun ki Jiddah... Don't worry my dear" Jiddah tace "Bari in kai ciki Ummi" Daga haka ta amshi ledan ta shiga parlon Ummi ta bi bayanta, dakin Umma ta nufa tare da Ummi, bayan ta ajiye ledan ta fito parlor, satan kallon Abuturrab tayi taga idonsa na kan TV, sai ta kasa wucewa bata gaishesa ba, hakan yasa ta d'an tsaya tace "Ina yini" Bai ko kalli direction dinta ba balle ya amsa fuskarsa daure, tayi wucewarta waje, tana dawowa balcony din ta dau literature din da ta ajiye sannan ta xauna Yousuf na kallonta, murmushi tayi tana duba page din da take, sai ga Abuturrab ya fito, ya nufi motarsa ya shiga yayi horn mai gadi na bude masa gate ya fice daga gidan, Yousuf ya kalli Jiddah yace "Is he alright?" D'an murmushi tayi tace "Nima ban dai sani ba" Yousuf yace "Naga baki gaishesa ba" Tace "Aa na gaishesa a parlor" Yousuf yace "Go on with ur reading" ba musu ta ci gaba da karatun yana kallonta. Aunty ce kwance kan gadon sister dinta godiya, Aunty ta mike xaune tace "Ni fa duk abubuwan da aka yi a gidan nan bai dameni ba don Alhaji ya tsaya min kuma ya dawo yayi ta bani hakuri wllh, ita ma Hauwan taga bacin ransa wllh kuma komai ya xo da sauki tunda uwarsa ba gidan ta kwana ba, abinda ya dameni shine yanda har yanxu Aliyu ya ki ce min komai a kan lamarin, tun da ya shigo sau daya ina waya da Abban nasa a daren har yau da nake maki magana bai sake ce min komai ba, ko a waya kuwa, abinda bai ta6a min ba, bayan xuwa ya bani hakuri sai ya sake kirana ya ban hakuri sannan ya tura min text kuma to wannan karan wllh duk babu" Godiya tace "Kuma yana gidan?" Aunty tace "Jiya Monday dai ya koma bakin aiki da safe, kuma ko baya gidan ma ai yana kirana a waya, to ni duk ba wannan ba, abinda ya bani shock shine yanda yake querying dina a kan dalilin marin talakan nan da ya je ya kwaso mana a hayi...." Godiya tace "Wai ba kince an gama case dinta ba har ma ya saketa? To me kuma ya hadasa da ita" Aunty tace "Toh ai har yanxu tana gun kanwar uwarsa, ta amsheta wai xata riketa har sun sa ta a karatu" Godiya tace "Toh sai ya maki magana don kin mareta ko ko?" Aunty tace "Wllh kuwa Kyauta, cikin bacin rai ya gaggaya min magana wai a kan me xan mareta sannan ya kada keyarsa ya fita, ni tsabar shock ma ban samu bakin ce masa komai ba" Godiya tace "Aa to da akwai lauje cikin nadi a wannan batun naki, me yasa xai ji haushi har yyi magana don kin mareta" Aunty dai bata ce komai ba ta ta6e baki abun na sake dawo mata ranta na k'una, Godiya tace "Toh ko dai bai saketa din bane dai Hafsah" Aunty tace "Haba dai ga takarda ubansa ya sa ya rubuta kowa ya gani, kowa ya shaida babu wani aure tsakaninsu, kawai toxarta ni yake da niyyar yi dama, amma ba komai in dai ni ce ya xuba ido" Godiya tace "Gaskiya kam, to yanxu ranan juma'ahn da munafukar kanwar Hauwan xa ku je kai kayan??" Aunty tace "Aa Alhaji yace in bar masu kawai suje su kai kayan ba sai naje ba, kuma ina ga da wannan takadiriyar tsohuwar xa a, kinga gwara ai inyi xamana, abu dai namu, ta wani bangaren fa uwa nake a gun amaryar, iyaka kawai ki shirya ki bi su don ki kwaso min rahotu" Godiya tace "Aa gwara kam kiyi xamanki ni inje, don na lura da take takensu so suke wani abu ya billo daga bangarenki a sa yaron ya fasa auren Aneesar tunda ai an san uwar Aneesar aminiyarki ce" Aunty tace "Yauwaaa ashe kin gano godiya, haka suke so ni kuma ba shashasha bace duk xan bi su a nutse ayi auren, shi sa kika ga na fara ja baya, ayi komai a gama su ga ko xasu sake iko da Aliyu kuma a rayuwar nan, ba uwarsa ba, wllh har ubansa sai ya nuna baya yinsa, balle wata kanwar uwarsa can, don tun farko ma shi bai dauketa mutum ba, su da Aliyu kuma sai dai hange daga nisa al-qur'an" Godiya tace "Shkkn kuwa Hafsah" Aunty ta d'an yi dariya tace "Allah dai ya kai mu lokacin lafiya, ai ni yanxu ido xan xuba ma kowa in ta binsu a samu a daura auren cikin aminci Aneesah ta tare" Godiya tace "Amma fa hankalina bai kwanta da xaman wannan yar hayin ba tsakaninku, tunda kinga dole dai Ramlah xata dinga xuwa da ita wajen yayarta..." Aunty tace "Toh sai me idan tana tahowa da ita, shi fa Aliyu bayan auren nan ko gidan ba xuwa xai dinga yi ba, tsaf xan masa iyaka da gidan wllh, kawai dai idan ina bukatar wani abu in shirya in tafi gidansa amma shi da gidan nan sai hange daga nesa.." Godiya tace "To da kyau hakan, Allah ya nuna mana auren nan lafiya" Aunty tace "Ameen, satu biyu kamar gobe ne ai in sha Allah" Godiya tace "Haka ne, bari in dubo mana girkin ko ya nuna" Daga haka ta mike ta fita dakin. Ranan Juma'ah Umma da frnds din Ummi biyu sai wasu yan uwan Abba da Godiya suka tafi kai lefen Aneesah garin Abuja, Hajja ta so xuwa amma Abba ya hanata don kar ya kullaceta ya sa ta hakura kawai suka tafi, sai ta 6ige da cewa su Jiddah ai ita ba yarinya bace dama da xa aje kai lefe da ita, banda ma an rainata ai bai kamata ayi mata xancen kai lefe ba tunda dai ita ba yarinya bace, iyayen Aneesah sun amshi su Umma da mutunci ganin uban kaya na gani na fada da aka yo ma yar su, ga zobunan gwal manya har biyu a ciki, Godiya dai na ta kwashe rahotun kai ma Aunty, aka yi komai cikin mutunci da girmama juna sannan su Umma suka juyo xuwa Kaduna..... Abuturrab na kwance dakin hotel dake cikin garin Lagos idonsa a lumshe kafin lkcn da xa su yi piloting jirgi xuwa kano yayi wayarsa dake gefensa ya fara ring, ya bude idanuwansa ya dau wayar ganin Aneesah ce ya daga ya kai kunne yayi shiru, cikin wani salo tace "Mijinaaa" Calmly yace "Ya aka yi?" Ta lumshe ido tace "I love you my Captain... Ina sonka fiye da yanda kake xato a ranka, I can't wait in ga na mallakeka a matsayin mijina" Shi dai sauraronta kawai yake, ta kanainaiye murya tace "I can't wait a daura in 2 weeks time, I can't wait to be ur wife officially My captain" Yace "Amma kin san wajen aiki nake Aneesah, i tot it's something serious u want to say" Tace "Ban gane something serious ba, wannan da nake gaya maka ba something serious bane?" Yace "Amma ba da rana ina wajen aiki ba" Tace "Ohk haka xaka ce min captain?" Yace "Ohk, i love you, idan na sauka kano xan kiraki..." Katse wayar yayi ya sa flight mode yayi rub da ciki ya lumshe ido.
Littafin Jiddatul Khair na kudi ne, it's 500 via
3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u show ur evidence of payment via 07087865788... Thank you
Duk wacce batayi anfani da sabulunnan ba anbarta abaya acan karshen bayama kuwa duk Mai tantama akan sabulai nagyaranjiki cewa basa Aiki toh yacire mg's domin kankat ne insha Allah babu Wanda yayi anfani dasabulunmu yace baiyi ba koyaushe mg's sai sanbarka amare da uwargidaye hardama yanmata kuhanzarta kusamu naku ba karya domin bama cika Baki kugwada kubada labari da bakunanku sabulu daya tamkar dubu wadandama basasan using cream sabulun mg's herbal whitening black soap yawadacemuku jikinku zaiyi kyau koyaushe kukasance clean cikin kamshi Kuna glowing koda bakusa turare ba🤗
Kayanmu bana bleaching bn organic ne sunagyarajiki fiye da tsammaninku zaifiddomuku da ainihin natural beauty dinkine Wanda yagwada shi zaitabbar amare kuyi kokari kumallaki mg's domin baruwanku da zuwa adirjemuku jiki zakuga yanda fatarku zata dinga walwali
Ina masu pimples
Tabo(spot)
Sunburn dama dukwani matsalar fata kuyi kokari kunemi soap dinnan before 2weeks zaisharemuku hawaye kuzama abun kwatance
Sister's masu nankarwa kuma kunemi soap dinnan Yana rage nankarwa sosai🧖🏻♀️duk me shakku tayi kokari tagwada mg's insha Allah bazakiso rabuwa dashi ba
Akwai maisa haske Amma kayanmu nafada bana bleaching bn zaifiddomiki d ainihin halittarkine yagoge dukkan dattin jiki
Akwai Kuma Wanda zaimiki maintaining skin dinki yasaki fresh fatanki tazama kalar hutu
Pls bamacika Baki you HV to try it and see for yourself
100%tested nd trusted
Soap price:3k
Location:kaduna buh munaturawa ko Ina Amma delivery is not free
Maiso kindly message 08062991549
07046881166
Call 08064532391
Note:Babu inda zakusami mg's herbal whitening black soap sai a number dinnan bairiga yakai market b inyakai we will let you know buh as for now wnn numbern ne kawai🙏
Maiso yahanzarta before yaji sold out akwaisu available now insunkare you HV to wait akawo so maiso yahanzarta🙏adade anayi sai gsky🤭🤝
Mg's skincare
Shirye shirye kawai ake babu kama kafar yaro a gidansu Abuturrab kasancewar kwana uku kacal ya rage daurin aurensa da Aneesah, kai kana ganin wannan shirin da ake kasan ba karamin biki xa ayi ba na first child of the family, tuni Umma ta dawo gidan da yan matan ta har da Huraira mai aikinta, yan uwa da abokan arxiki kuwa duk sun fara tahowa daga garurruka daban daban, Kamar yanda Aunty ta sanar ma yar uwarta godiya haka tayi a wannan period din, don sosai ta kwantar da kanta komai sai dai taje ta samu Umma taji yanda xa ayi, duk kuma yanda aka ce bata musu, har hakan ya ba Umma mamaki hatta idan wani shawara tayi da Abba sai taje ta tattago Umma ta xo taji ko shawaran yayi, ganin haka Umma ta sake gaba daya don da farko ko sakar mata fuska ta ki yi, ashe hakan ba karamin kona ma Hajja dake ta lura da su rai yake ba, ranan laraba wanda ya rage saura kwana biyu daurin aure Umma ta shigo dakin Hajja rike da babban cooler din soyayyan nama xata ajiye Hajja tace "Meye haka?? Aa ba ruwana da tarkace Ramlah, fita da shi gaskiya ki kai dakin Hafsah tunda naga dai ku ke aurar da yaro ke da ita" Umma ta tsaya tana kallonta, Hajja ta ci gaba da kakka6e gadonta fuska daure tace "Haka kawai kya shigo min da wani katon rubabben cooler daki kamar wata rubabbiyar tsohuwa, a ina xan sa shi? Kinga da ruwana da sha'anin bikin ku ne, ba dai kawai nasan ni na haifi uban Aliyun ba" Umma ta juya ta fita da naman, Hajja ta bi ta da wani shegen kallo tace "Idan ba gulma ba sai ki kama Hafsah ki rike hannu bibbiyu kuna abu gaban kanku bakwa sako kowa, in dai Hafsah ce ni nasan tana da wani mugun kudurin a ranta ne... Ahaf mu je dai xuwa, ni dai ba Allah ya so 'ya ta na hanya gobe ba, duk ita xan sa kan komai na bikin nan ai tafi ku kusanci da Aliyun tunda kanwar ubansa ce ita, sannan matan Kabiru duk suna hanya su ma gobe kwa sha mamaki ke da Hafsar, idan ma barbadensu na yan garin Benue tayi ta baki mu dai mun fi karfinta sai dai ke din da yayarki tunda naga ba a tsaye kuke ba" Tun da Jiddah suka xo gidan ko kallon inda take Aunty bata yi balle har tayi abinda xai sa ta 6ata likimon da tayi ma kowa, Jiddah ma bata yarda hanya ta hadasu, da ta ga Aunty a waje take barin wajen, duk Aunty na lura da hakan, sai dai tayi kwafa a hankali tayi murmushi, ita dai babban damuwarta yanxu a daura auren nan ran friday Aneesah ta xama mallakin Abuturrab tukun, yawanci Jiddah na gun Hajja tun xuwansu, don Hajja bata sa kowa aiki sai ita, a dakinta ma take kwana, da taga bata ji motsinta ba xa ta sa a kira mata ita ko a nemota, sauran yan matan kuma dama ta ce babu abinda ya hadata da su sun ma rainata. Washegari Thursday da safe Jiddah da Nafisa kanwar Abuturrab da ke boarding suna sharan parlor kamar yanda Umma ta saka su, Maimoon kuma na goge goge aka bude kofar parlon, duk suka daga kai El-Basheer ne ya fara shigowa sannan Abuturrab dake biye da shi a baya, Jiddah dai ta ci gaba da sharan da take, Nafisa ta gaida El-Basheer cike da murnan ganinsa yace "Ashe kin girma da yawa Feenah" Rungume Abuturrab tayi tace "Yaya sannunku da xuwa" Ya ja hancinta yace "Yaushe kika dawo" Tace "Tun ran Tuesday fa yaya" yace "To ya karatu?" Tace "Alhmdlh" Maimoon ta gaida El-Basheer ya amsa mata with smile, sannan ta gaida Abuturrab ya amsa a takaice, Jiddah ta dago tana kallonsu tace "Ina kwanan ku" El-Basheer yace "Lafiya lau, ya kike?" Tace "Lafiya lau" Dama Abuturrab bai amsa ba banda wayarsa da ya hau dannawa, Jiddah ta ci gaba da sharanta, kallon El-Basheer Abuturrab yayi ganin yanda yake kallon Jiddar, ya maida wayarsa aljihu ya nufi dakin Hajja, El-Basheer ya kallesa sannan ya maida dubansa gun Jiddah yace "Are you Asthmatic?" Ta daga kai ta kallesa amma bata ce komai ba, Maimoon tace "Aa bata da Asthma" yace "Ohk" daga haka ya bi bayan Abuturrab xuwa dakin Hajja. Hajja na ganin El-Basheer tace "Kai ma kaje kayi ma kanka fada Bashir, ba wai ka dinga yawo kana bin sabbin angwaye xalo xalo a baya ba, da ka san ciwon kanka yanxu ba cewa xaka yi a hadaku da wannan mutumi Aliyu ba, balle duka duka da watanni nawa ya girmeka? Amma ka tsaya shashanci kai a dole d'an sarki, to ko ni da nake uwar sarki bana abinda kake yi wllh" El-Basheer yace "Toh kin samar min matar ne nace maki bana so Hajja? Ni na xata Masar da kika je xaki samo min mata daga can fa" Ta marairaice tace "Wllh nayi niyya Bashir, Nafisah ce ta hanani wai su ba a haka a can, toh kaga kuwa ai sai inyi shiru in koma gefe tunda idan na botsare masu suka maido ni Najeriya sai inyi yaya, amma yanxu tunda har ka bani wuka da nama idan Allah ya yarda baxan baka kunya ba, yanxun ma na fara maka sha'awar wata yarinya wllh, baka ganta ba kyakkyawa doguwa jazur da ita kamar balarabiya, da ta bude min gashinta kuwa sai da na gigice, ga ladabi da biyayya sannan bata da kiwiya, komai aka sata yi take cikin dadin rai ga shegen hakuri, ai ni tuni na fara maka sha'awarta sai gashi ashe kai ma ni kake jira" El-Basheer yace "Toh fah, a ina kika samo min ita Hajja" Hajja tace "Sakin wawa ce..." Abuturrab dake danna wayarsa ya daga kai ya kalli Hajja, El-Basheer yayi dariya yace "Sakin wawa kuma Hajja, bazawara kika samo min kenan?" Hajja tace "ka ji ka da wani xance Bashir, wllh babu wanda xai ce ta ta6a aure, yarinya ce fa yar karama bata wuce Nafisah kanwar mutumin nan dake xaune ba, kuma ai ni na samu labarin wannan auren da tayi ba aure bane don babu abinda ya ta6a shiga tsakaninta da mijin, a gantale aka yi auren kuma a gantale aka yi sakin, yar yarinya ce karama fa nake gaya maka wllh, sannan kakan Aliyu nima ai a bazawarar ya aureni tunda sai da na auri kakanka aka haifi Kabiru da Aisha sannan kishiyoyi suka fiddani, Allah ya hadani da kakan Aliyu ya aureni sannan na haifi su Usman da Nafisah" Shi dai El-Basheer murmushi kawai yake yace "Toh shkkn ai ni nasan baxa ki min xabin da xai cutar da ni ba Hajjaju" Hajja tace "Haba haba ai na cuci kaina kenan idan na cuceka, in sha Allahu xabi ne har xabi na maka, kar ka ji komai a ranka, bari dai mu gama da bikin wannan mutumin tukun" Abuturrab dai bai daina kallon Hajja ba, El-Basheer yace "Toh baxa mu samu ko d'an ruwan shayi ba, ni yunwa nake ji fa" Hajja tace "Kaji ka, ai magana xaka yi, har abincin ma akwai naga sun dafa idan kuna so a xubo maku" El-Basheer yace "Aa shayin dai, bamu yi breakfast ba" Hajja ta mike tace "Toh bari in sa a kawo maku" Fita tayi dakin xuwa parlor, har sannan su Jiddah na parlor, Hajja tace "Yar nan ajiye masu sharan su ki xo in sa ki aiki kinji" Jiddah ta ajiye broom din hannunta ta karaso gun Hajja, Hajja tace "Xuwa xaki yi kitchen ki wanke hannu da kyau, don baya son kazanta Bashir, bayan kin wanke hannunki ki dau babban faranti da naga suke fafa da shi a gidan nan ki daura masa flask da cokali da kopi daya sannan ki ajiye kayan shayi a gefe, to shi kuma dayan mutumin ban san ko xai sha ba don ko gaisheni ma bai yi ba, amma dai baxa a biye ta halinsa ba, shi ma ki dora masa kofi da cokali daya mu mayar masa da aniyarsa, ki tabbatar duk ki dauraye kofunan don kinsan sarakan tsafta ne su, kuma duk a wajena suka gado, bayan nan idan akwai burodi ki daura kan tray din duk ki kawo masu" Jiddah tace "Toh" sannan ta juya ta wuce kitchen, Hajja ta koma daki tace "Toh ba shikenan ba bakina alekum, da wannan gantalallun 'ya yan na saka sai in samu me xagina ma tunda ba isasshen tarbiya garesu ba" Jiddah tayi duk yanda Hajja ta ce mata, tray biyu tayi ta daura kayan shayin da bread din a daya, dayan kuma ta daura cups da spoon sai flask din a kai, na flask din da cup ta fara dauka ta fito kitchen din suka kusa cin karo da Aunty ta koma gefe da sauri, Aunty ta hade rai ta ja gefe, Jiddah ta sunkuyar da kai ta bi gefe ta fita don tun sassafe ta gaisheta bata amsa mata ba, Jiddah na shiga dakin Hajja, Hajja ta mike ta shimfida rug da sauri tana cewa "Yauwa yar albarka, sannu kin ji, taho ki ajiye" Jiddah ta sunkuya ta ajiye tray din tace xanje in dauko dayan, Hajja tace "Toh yi maxa" Shi dai El-Basheer kallonta kawai yake, ta juya ta fita, Hajja tace "Wllh ba sawa ba hanawa, tunda uwata ta haifeni ban ta6a ganin nutsattsiya me tarbiya irin wannan yarinyar ba, gashi bata fushi ko kadan yanda ka san ni ce ina karama" El-Basheer yyi murmushi yana shafa kansa yace "Toh ko dai canje xaki min da sakin wawan da kika ce" Hajja tace "Aa kai dai kayi shiru kawai ka kyaleni yanda ka gan ni, ban fiye son surutu ba gaira ba dalili ba...." Abuturrab kallon wayar hannunsa kawai yake amma babu abinda yake da wayar, Jiddah ta dawo da tray din kayan shayin ta ajiye, Hajja tace "Yauwa er albarka, sannu" Sai kuma ta kalli El-Basheer tace "Ko ta soya maka kwai, naga ta iya, jiya da uwar rikonta ta sa ta soya mata naga tayi sa da kyau snn bbu karni ga albasa ta yankasa rimi rimi a kai abun zar sha'awa, ni dai har Ramlah ta gama cin kwan nan banji karni ba" El-Basheer yace "Aa ba sai na bata wahala ba ta bari kawai" Hajja tace "O'o Allah ina ruwanka da wannan batun, kai dai ba a soya maka kwai ba ka hada da burodi ka ci, da tana da son jikinta ai baxan ma fara sa ta ba, kaga na bi ta kan yaran gidan nan" Jiddah ta kalli El-Basheer tace "Xan iya" Yace "Toh je ki soya" kofa ta nufa ta fita, Hajja ta kalli El-Basheer murya can kasa tace "Ga tsafta kamar tsatsonmu wllh, ko kai baka gani ba?" Shafa kansa kawai yake yana murmushi, tace "To ni dai ba ruwana, kawai a barni yanda aka gan ni ba banxa nake ba" Bayan kusan minti goma jiddah ta dawo da kwai rufe a plate da fork biyu a kai ta dora, ta sunkuya ta ajiye plate din kan carpet, Hajja tace "Allah yayi maki albarka kinji" Jiddah tayi murmushi ta mike suka hada ido da Abuturrab da ya dago kansa, sunkuyar da kai tayi ta nufi kofa ta fita, El-Basheer ya sauko ya fara hada shayin yana kallon Abuturrab yace "Hey dude come let breakfast" Abuturrab ya mike yace "Alhmdlh" Daga haka ya nufi kofa ya fice. Da yamma Jiddah na dakin Hajja ita da Nafeesah, El-Basheer ya shigo da sallama yace "Hajja xa mu je dauko su Maman Farida" Hajja ta washe baki tace "Ehh wllh yanxu mijin ya kirani wai sun sauka ashe" yace "Toh dama xance maki sai gobe ne, don ni daga can baxan dawo ba" Hajja ta xare ido tace "Saboda mene?" Yace "Aliyu xai karaso da su ni xan sauka gida in huta ne" Hajja tace "Aa ba ruwana ba haka Kabiru yace
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 35 Chapter of 57