captain Musa ya daga, ya sauke wani boyayyen ajiyar xuciya yace "Captain baku tashi har yanxu ba?" Captain din yace "About to... in few minutes time, ya gajiya?" Abuturrab yace "I think i will have to follow you to kaduna now" Da mamaki pilot din yace "Baxa kayi piloting jirgi gobe da safe ba, and hope all is well?" Abuturrab yace "Sure alhmdlh, jirgin gobe na sha daya ne, i don't have early morning duty" Musa yace "Toh shkkn, ka taho yanxun nan kasan basu fiye son jira ba, in some minute time xamu yi take off" Abuturrab yace "In sha Allah" Cikin few minutes ya shirya cikin kananun kaya Hoping not to miss the private flight going to kaduna, cikin ikon Allah ya isa, kuma suka daga sama, within some minutes suka sauka a garin kaduna, a motar Musa dake airport din kaduna suka shigo cikin gari, Musa ya kawo Abuturrab har layinsa ya sauka yana masa godiya, Musa yace "Sai mun hadu Wednesday in sha Allah" Abuturrab yace "Sure in sha Allah, thank you" daga haka suka yi sallama ya karasa cikin layin da kafa, makullin gidan ya fiddo a aljihunsa ya bude sannan ya shiga, har ya isa main entrance nan ma ya bude sannan ya shiga parlor, wutan parlon a kunne yake parlon sai kamshin turaren wuta yake, ko ina na nan ynda ya barsa jiya, kuma babu alamar ana xama cikin parlon ma, karasawa yyi sama yana kallon kofar dakinta ya murda a hankali ya shiga, babu kowa cikin dakin ya bude ido sosai sai dai lkci daya yayi calming kansa jin kamshin sabulu a dakin, coz he is a very sharp percipient, bin dakin ya dinga yi da kallo yana duba inda xai ga wayar amma bai ga alamarsa ba, can kusa da window ya nufa ya tsaya hade da rungume hannunsa ya daure fuska, bayan few seconds ta bude kofar bandakin, ta fito daure da towel, bata ko kalli direction din da yake ba ta nufi gaban mirror, sai a sannan ta ga mutum ta madubi wani ihu ta fasa da karfi ta nufi bandakin a guje ruwan kafarta ya sa tsantsin tiles ya kwasheta ta fadi nan bakin kofar bandakin, da sauri Abuturrab ya nufeta ya durkusa kusa da ita ya dagota yace "Ke nine fahh" wani kuka ta fashe da bayan ta kare masa kallo ta tabbatar shi din ne, tana rike da towel din jikinta gam tace "Wayyo kafata, wllh kila nayi targade, wayyo Baabarmu" Komawa baya yyi yana kallon kafar, ya mike yace "Tashi tsaye" Tana girgixa kai hawaye na sauka idonta tace "Ni baxan iya ba wllh" Ya kamata ya dagata, lkci daya ya hade rai yace "Wani kafar ne kika yi targade" Ta nuna masa right leg dinta, gefen gado ya xaunar da ita ya duka yana kallon kafar, ita dai hawaye kawai take tana hade laps dinta tana kallonsa, wani kallo ya mata ta sunkuyar da kai da sauri, mikewa yayi ya nufi gaban madubi don yasan ya siya mata man xafi ranan da suka yi shopping incase she will need it, a hankali tace "Don Allah ka yi hakuri ka miko min hijabi na" Ya dau man ya juyo ya dawo kamar bai ji ta ba, ta marairaice tace "Hijabina nace" Yace "Ki bari in duba maki kafar in ga babu targade, yau duk kukan karyar nan da kike ma mutane sai ya dawo na gaskiya, kuma xaki gaya min inda kika jefar da wayar da na baki" Shiru tayi bata ce komai ba, ya duka ya bude man ya diba sannan ya kama kafar da tace, wani ihu tayi ya ja kafar da karfi, har kasa sai da ta sauko tana kokarin kwace kafarta sbda axaban da take ji, ganin da gaske ta ji ciwon yasa yace "A hankali fa nake maki amma wllh idan kika sake ta6a ni xan yi da karfi" hawaye na sauka idonta tace "Wllh xafi yake min sosai, don Allah ka rufa min asiri kayi hakuri" Ya daure fuska ganin xata sake kai hannunta kan nasa yace "Kin xata wasa nake maki" Da sauri ta dauke hannun, duk da yanda yake mata a hankali haka ta dinga kuka tana neman birgima a wajen, shi dai kallonta kawai yake, don a fuska bata yi kama da warce xata yi shagwaba ba, ko warce baxata iya jure xafi ba ko yaya ne, dauke idonsa yyi ganin tawul din na neman sauka a kirjinta, ya sake mata kafar ya mike, sai a snn ta ankare, tana shessheka ta kankame abarta, ya ajiye man xafin hannunsa ya nufi kofa ya fita.
*Pls i am bringing this to the notice of people coming to disturb me with... ina karanta littafin ki kuma bani da kudin biya ki yafe min!!! For what?? Na aikeki karanta littafi baki da kudi? Ga dai free books kaca kaca a gari, Toh a gaskiya baxan iya lalacewa da gantalewa ba kije can ki nemi wanda xaki ce ya yafe maki ba dai khaleesat Haiydar ba, ba ruwanaa tunda ban aike ki karanta littafi ba, ki sani you owe me har sai ranan da kika mula kika mulmule kika ga daman biya*🤷
Littafin Jiddatul Khair na kudi ne, it's 500 via
3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u show ur evidence of payment via 07087865788... Thank you
Kamar wanda ya tuna abu ya sake juyowa, rarrafawa yaga tayi xuwa gun da hijab dinta yake xata dauka, ya hade rai sosai yace "Ina wayar da na baki?" Ta juya ta kalli gadon dakin, a hankali tace "Ya fada karkashin gadon na kasa daukowa" Da mamaki ya dinga kallonta, ta sunkuyar da kanta, can yace "Wa ya jefar karkashin gadon?" Ta sake kallonsa tace "Xamewa yayi ya shige ban sani ba" cikin tsawa yace "Saboda ke yar yarinya ce ko?" Shiru tayi bata ce komai ba ya juya ya fice daga dakin ya kulle kofar, da kyar ta lallaba tayi shafe shafen mayukanta da turarruka sannan ta dauki wani rigar bacci ta saka tana dingishi ta hau saman gado ta kwanta, mamaki ta dinga yi na yaushe ya shigo gidan bata ji karan shigowar mota ba, ko dai bai dawo da motar bane, kuma ai ce mata yyi sae karshen sati, da wannan tunane tunanen bacci yyi awon gaba da ita. kasa bacci Abuturrab yyi sbda shayi da bai sha ba, don ya fara shan shayin kenan ya bari ya taho, shi kuma idan da abinda ke takurasa rashin shan shayin dare, ji yake yunwa na damunsa indai bai sha shayi ba, and he detest making tea himself, da dai yayi da kansa gwara kar ya sha, rub da ciki yyi ya lumshe ido hoping to force sleep, wajen karfe daya da rabi ya mike ya fito daga bangarensa, downstairs ya sauka ya shiga kitchen ya bude fridge, kallon fridge din ya dinga yi don bai ga alamar ta ta6a komai na ciki ba tun jiya, ya dau Chivita daya ya bude ya dau glass cup bayan ya dauraye ya xuba a ciki, sau biyu ya cika ya shanye sannan ya mayar fridge, da ya hada shayi gwara yyi hakan, fitowa yyi daga kitchen din ya xauna saman kujera a parlon cikin duhu, yana ta xaune har karfe biyu sannan ya mike ya haura sama, har ya nufi part dinsa ya dawo ya bude kofar dakinta, cikin duvet ya ganta ta takure waje daya tana bacci, ya karasa cikin dakin ya janye duvet din, dukawa yyi yana kallon kafarta sannan ya d'an danna kafar, da sauri ta janye ta juya masa baya, sake kai hannu yayi ya kamo kafar, da sauri ta bude ido, ya hade rai amma bai ce komai ba ya mike ya sake dauko man xafin, a hankali ya shafa mata sannan ya mike ya kashe wutan dakin ya fita. Da asuba bayan ya dawo masallaci ya fara tunanin ta yanda xai koma kano babu mota, gashi bai fiye son shiga commercial vehicles ba, karfe bakwai ya gama shiri ya fito daga bangarensa, dakinta ya murda a hankali ya shiga, a kwance ya ganta amma idonta biyu, ganinsa ta mike xaune da sauri... yace "Kafin in dawo ran juma'ah ki tabbatar kin fito da wayata da kika jefar karkashin gado" shiru tayi bata ce komai ba, yace "Sannan kayan marmarin da na xuba a fridge ki tabbatar kar in dawo in sami ko daya" Daga haka ya juya, da sauri tace "Tafiya xaka yi?" Yace "Aa xama xan yi" sai bayan da ya fita ya fara tunanin wayar da xai sake bata, he just need to hand a phone over to her, shi kuma bashi da strength din daga kayan gado da sassafen nan, can dai yyi deciding ya koma dakin ya ga inda ta jefar da wayar tukun, Yana shiga bai ko kalleta ba ya nufi gadon ya fiddo wayarsa ya kunna fitila ya duka yana haskawa karkashin gadon, cikin few minutes ya ciro wayar da hannunsa, ita dai tana tsaye ta rakube gefe da hijab dinta har kasa, ya dago yana kallonta fuskarsa a tamke, ta sunkuyar da kanta, ajiyewa yyi kan gado ya nufi kofa ya fita ta bi sa da kallo, dole commercial car din ya tafi ya hau a park xuwa kano... Jiddah na xaune kasan carpet a parlon hannunta rike da apple biyu, ta kasa ci sbda rashin sabo da shi, tunda take a rayuwarta bata ta6a shiga matsatsi da takura irin wannan ba, duk da ba jin dadin xama take da Hansai ba amma ai xaman bakin titi ma da take ya kan debe mata kewa tana ganin mutane da motoci, amma tun shigowarsu gidan nan yau kwananta nawa bata ga kowa ba banda shi kadai, tunanin hakan ya sa hawaye ya kawo idonta, kallon ma sbda rashin sabo da shi da ta fara xata soma gyangyadi, Mikewa tayi a sanyaye tana goge idonta ta nufi wani window dake parlon ta makale jiki ta bude labulen a hankali tana lekan tsakar gidan, babba ne tsakar gidan da flowers masu kyau xagaye, ta dade tsaye wajen tana ta kallon tsuntsayen dake tashi da sauka a tsakar gidan, kiran sallan azahar yasa ta juya a hankali ta bar wajen tana kallon apples din hannunta kitchen ta koma ta mayar, marairaice fuska tayi tana kallon fruits din fridge din banda ayaba babu abinda ta iya ci a ciki ita dai, tana tafiya a hankali ta fita kitchen din. Hansai ce xaune gaban mai anguwa da Zulai da ta rakota, bayan sun gaisa, ta kunce ha6ar xaninta ta sakar masa kuka tana matsar kwalla da zanin tace "Wllh Mai Anguwa shiru shiru har yau babu yarinyar nan tawa babu labarinta fa, abun nan ya fara damuna duk inda taje ai ya ci ace ta dawo yanxu, yau fa sati daya cur ba ita ba labarinta, na rasa inda xan sa kaina, ga komai nawa ya tsaya kamar ta tafi da shi" Sae kuma ta rushe da kuka, Mai Anguwa dake ta kallonta da mamaki yace "Ikon Allah, ni ai na xata da naji shiru Allah ya sa ta dawo gida, toh ke duk kwanakin nan me yasa kika yi shiru kinsan bata dawo gida ba, sai yanxu xaki taho kice bata dawo ba" Hansai ta marairaice cikin rawan murya tace "Wallahi na danni xuciyata ce don ban debe tsammani ba, ina ta baxa ido amma naga shirun yayi yawa" Mai Anguwa yace "Cabb, amma kina da ganganci Hansatu, anya ke kika haifi yar nan kuwa kamar yanda kika ce?" Hansai ta kara marairaice masa cikin kuka tace "Nice mana Mai Anguwa, ina da kauda kai dai xaka ce kawai" Mai Anguwa yace "Toh, ranan dai na amshi lambar shi mutumin da ya aureta, wato shi matukin jirgin saman, kuma bayan wannan aure da kwana uku ya xo min har nan da mahaifinsa da kawunsa, mahaifin nasa sanannen mutum ne dattako kuwa a garin nan..." Hansai ta hadiye abu da kyar tace "Toh kira mana shi xaka yi yanxu kenan don Allah? Don dai gaskiya na fara xargin kilan ma ya ganta ya tafi da ita ne kawai bamu sani ba, banda haka me yasa xai yi shiru haka babu labarinsa, bayan gashi kace har ya xo da mahaifinsa, to idan haka ne ba sai sanda na ga damar basa matar xai tafi da ita ba, to wllh ni na canxa ra'ayi kan auren ma, ya dawo ya fadi nawa ya kashe ko gidan da muke ciki ne sai in sayar in biyasa, ba ruwana wllh" Mai Anguwa dake ta kallonta, ya d'an yi murmushi yana kara jinjina hali irin nata, ya fiddo wayarsa bayan kusan minti biyar yace "Alhmdlh, na samo lambar" Yana fadin haka yayi dialing number Abuturrab ya sa handsfree, kallon Hansai yayi bayan an sanar wayar baxai je ba, Hansai ta rushe da wani matsanancin kuka tace "To ko dai lambar karya ya baka, ni sai yanxa nake jin ma ban yarda da mutumin nan ba wllh, wa ya sani ma ko d'an yankan kai ne yace mana matukin jirgi ne shi, jirgi abar wasa ce da xai iya tukata bayan an sanar mana turawa ne kadai suka iya daga jirgi sama su tuka, sannan idan ba d'an yankan kai ba mutumi babu dangin iya balle na baba kayi ta kashe mana kudi haka daga jin an mana mutuwa, daga haduwar mu xuwa fa ranan da ya bada sadakinta wllh mutumin nan ya kashe mana yayi kusan rabin miliyan, to akan me? Aa wllh ya xo in biyasa ya maido min da 'ya ta" Mai Anguwa dai tabe baki kawai yake bai bata amsa ba, Hansai ta fara kokarin mikewa tace "Ai dai wayar baxata dauwama a mace ba, don haka ko gobe ma xan dawo sai ka sake gwada kiran lambar don ni bani da waya, haka kawai yarinya ta bace batt kamar yar kaza" Mai Anguwa yace "Allah ya kai mu goben" daga haka ta bar wajen tare da kawarta, Zulai tace "Anya wannan mai anguwan na da gaskiya kuwa Hansai?" Hansai ta kalleta da sauri tace "Atoh, nima shi na gani, baki ji har ya fara cewa Uban yaron sananne ne a garin nan ba, kawai dai sun danna masa uban kudi shi ma shine yayi mukus, to wllh a maido min da 'ya ta babu wani xancen auren karya" Zulai tace "Kuma fa da gaskiyan ki, ko dai wannan yaron d'an yankan kai ne, idan ba haka ba a wnn xamanin ina xai samo rabin miliyan ya kashe maku" Hansai ta tsaya tana kallon Zulai, can ta marairaice tace "Toh kuwa in har haka ne ya kassara ni, wa gareni da muke sana'a tare banda jiddar, ke baki ga ko me nasa Bibalo kin yi take ba sai ta nemi ta xageni, ai jiddah ita ce rufin asiri na a duniyar nan, gashi duk jarin na fatattakar, kuma sana'ar ba wani ciniki nake yi ba yanxu, uwa dai an juya min baya a anguwan" tana fadin haka ta fara matsar kwalla, Zulai tace "Toh da da kike shirin aurar da ita Jiddar ga Iliya fa?" Hansai ta ci gaba da tafiya tace "Toh ai ko daga gidan mijin sana'ar xan dinga bata tana min nufi na" Zulai ta ta6e baki tace "In ko ba d'an yankan kai bane to tana gunsa Wlh, abinda kowa dai ya shaida matarsa ce" Hansai ta share xufar goshinta tace "Toh uban me xai yi da ita wai Zulai, sai kiyi ta wani cewa matarsa, wllh babban mutum ne ko da kudi aka hadasa da jiddah banjin xai amsa balle bbu ko sisi, don baki gansa bane shi yasa kike wannan xancen banxan, lafiyayyen namiji ne fa wanda da kyar ya amince ya auri yar kaduna sai dai yar Abuja" Zulai tace "Toh wai ke kinga tun bayan da aka daura masa aure da ita ya sake dawo maki kofar gida, ai da wllh bata wajensa da tuni ya dawo an kai xance gidan yan sanda, duk inda ta shiga kuma sai an nemota, ke dai kawai kin cuci kanki, kina ji kina gani sbda shegen son kudi kin ba babban mutum irinsa auren Jiddah ga Bibalo yashe a gida" Hansai ta fashe da kukan takaici tace "Ni anjima da daddare ma wllh xan dawo gun mai anguwa ya sake kiran lambar, don bani da waya ne da na amsa lambar ai, kuma wllh in har da gaske jiddah na wajensa to ni ba da amincewata ya aure min 'ya ba, wllh sai ya sakar min ita, ina jiddah ina babban mutum kamar shi idan ba yana da wata manufa na yanka min ita ya bunkasa arxikinsa a ransa ba" Zulai ta sauke wani ajiyar xuciya tace "Ohh!!! wa yasan irin daulan da Jiddah ke ciki yanxu" Turata Hansai tayi a mugun fusace tace "Don Allah idan baxa ki dinga fadan alkhairi ba kiyi shiru, jiddah ita har tana da wani daula a duniya, wllh ko tana da shi kinji rantsuwar musulmi ko? To sai na rushe daulan nan, muna nan da ke kuma xa ki ga jiddah sai ta dawo gidan nan, ai ba mijin aurenta bane shi din sai in kasheta yake da niyyar yi ya kara arxikinsa, ba kuma sa'an aurenta bane ko da kuwa ita ma yar me kudi ce, sai dai in ban haifu cikin shafa ba wllh" Daga haka tayi gaba a mugun fusace tana jin xuciyarta na tafarfasa.... Washegari alhamis Jiddah ta tashi taji tana jin yunwa sosai sbda daren jiyan babu abinda ta ci ta kwanta, sai kusan karfe takwas na safe ta shiga kitchen bayan tayi wanka, rasa abinda xata dafa tayi a kitchen din, jingina tayi da bango ta 6ata fuska xata yi kuka tana kallon tulin kayan abincin, tuwo ne kawai a ranta, lkci daya hawayen ya kawo idonta ta juya ta fice daga kitchen din, dakinta ta koma ta fada kan gado tana shessheka a hankali, bayan wani d'an lkci ta daga kai a hankali tana kallon wayar dake gaban madubi yana vibrate, mikewa tayi tana share idonta cikin sanyin jiki ta nufi wayar ta dauka tana kallon screen din, throughout jiya basu yi magana da Abuturrab ba banda yanxu da yake kira, ta daga ta kai kunne, Abuturrab na driving xuwa airport kasancewar karfe sha daya yake da duty, Shiru Jiddah tayi kamar yanda shi ma yayi shirun, bayan few seconds yace "Ni kike jira inyi maki magana?" Ta sauke idonta kasa a hankali tace "Aa" yace "Ohk in gaishe ki?" Tace "Ina kwana" Yace "Me kika ci yanxu?" Ji tayi kamar ta fashe masa da kuka, yace "Ina jin ki" cikin rawar murya tace "Ban ci komai ba" Yace "Me kike jira?" Tace "Ni bana son taliyar" ya d'an yi shiru kafin yace "Me kike so?" A hankali tace "Tuwo nake son ci" Yace "Toh sai ki ci inda kika gansa, ga abinci kusan kala nawa a gida kice duk baki ga abinda kike so a ciki ba, Shinkafa, doya, macaroni, spaghetti, irish, wake, indomie, cous cous.... Wait.. Are you even okay?? Dama tuwo abinci ne?" Ita dai bata ce komai ba, lkci daya hawaye ya kawo idonta, yace "Samun waje kika yi" daga haka ya katse wayar, hawayen dake makale idonta ya silalo, ta ajiye wayar ta koma kan gado ta kwanta tayi lamo tana shessheka. Har kusan karfe sha daya na safe tana kwance, jin yunwa ya dameta sosai ta mike a hankali ta fita dakin, kitchen din ta koma, indomien kawai ta dafa daga karshe sai dai gwara na yanxu a kan wanda tayi shekaranjiya. Da yamma Jiddah ta ji kamar an bude gate ta mike da sauri ta isa window ta bude labulen tana lekan waje, shi ta gani ya shigo gidan ta xaro ido ta sake labulen ta koma can karshen gado ta xauna kamar mara gaskiya, bayan kusan minti goma sha biyar ya bude kofar dakin nata, sunkuyar da kai tayi, yana tsaye bakin kofar yace "Baki iya dafa shinkafa bane ko wani abincin?" Tace "Aa na iya" Yace "Toh me yasa baki dafawa?" Tayi shiru, yace "Ohk, daga yanxu... daga ranan lahadi xuwa asabar xan sanar maki abinda xaki dinga girkawa tunda baki da hankali ke" Ajiye ledan hannunsa yayi ya juya ya fita, ba a dau lkci ba taji alamar ya fita gidan gaba daya, mikewa tayi ta isa gaban ledan da ya ajiye ta leka ciki taga take away ne, fiddowa tayi ta bude taga tuwon shinkafa that looks so palatable, ta bude inda miyan ke ciki taga miyar kubewa danye lafiyayye da ya ji nama da kayan ciki da ganda, kallon miyan da tuwon ta dinga yi, bata san lkcn da tayi murmushi ba ta mike ta wuce bandaki da sauri ta wanke hannu sannan ta dawo ta xauna ta fara cin tuwon, she was eating happily, mulmula hudu ne tuwon, ta rage wanda xata ci da daddare, har bacci barawo ya saceta sbda tsoron dake damunta a rai bata ji alamar ya dawo gidan ba. Washegari Friday ana saukowa masallaci Abuturrab ya shigo gida daga garin kano, babu kowa parlon, yana tafiya a hankali ya nufi bangaren Aunty, da sallama ya shiga parlonta, daga uwar daka ta fito ya xauna saman kujera murya can kasa yace "Ina yini Aunty" tana kallonsa daga sama har kasa tace "Kiran nawa bashi da amfani a gareka sbda kasan abinda ka kullala shi yasa ka daina dauka ko??" Ya shafa kansa cikin sanyin murya yace "Aunty ae na maki text nace xan dawo weekend in sha Allah" ta nemi waje ta xauna fuska daure bbu yabo bbu fallasa tace "Toh gashi ka dawo weekend din yau ai, ya ake ciki kenan?" Ya daga kai ya kalleta a hankali yace "Aunty ni fa ba matata ce ita yanxu ba kuma, kawai gaya maku ne ban yi ba" Da mamaki Aunty tace "Ban gane ba" Ya gyada kai yace "Haka ne, babu aure tsakanina da ita tun ranan da muka tafi can gidan nawa, so nake sai na dawo ne in sanar maku" Aunty ta daga hannu biyu sama tace "To Alhamdulillah ya Allah, tun faruwan lamarin nan sae ynxu naji dama dama" cikin sanyin murya yace "Amma don Allah wannan ya xama sirri tsakaninmu Aunty, Abba won't take it likely with me if he finds out" Aunty ta hade rai tace "Haba dai wa xan gaya ma kamar wata yar yarinya, wllh baka ji sanyin da xuciyata tayi ba yanxu, to ina ka bar ta yanxu? Ka maida ta kauyen nasu ne?" Yace "Tana can gidana Aunty" Aunty ta hade girar sama da ta kasa tace "Wani gidan naka?" Yayi kasa da murya yace "Aunty ina sane da abinda nake wllh, ba lkci daya xan yi komai ba ai sbda kada a xargeni" Aunty tace "Amma xamanta gidan nan naka ai bai yi ba" yace "Na sani Aunty, give me few days to think of another solution" yana fadin haka ya mike yace "I will be coming back" daga haka ya fita, ta sauke wani ajiyar xuciya tana jin kamar an biya mata wani bukatarta na musamman. Part din Ummi ya nufa, ya xauna ya gaisheta da ladabi, ta amsa tana kallonsa tace "Ya ku ke?" Yace "Alhmdlh" Tace "Toh madallah" kallon Tv dake aiki a parlonta kawai yake, can ya kalleta yace "Abba xai dawo yau ne?" Ta girgixa masa kai tace "Sai gobe in sha Allah" Yace "Allah ya kai mu lfya" Ta amsa da "Ameen... Ina Amaryar taka take?" Lkci daya ya d'an 6ata rai, ita dai tunda ta fada haka bata kalli fuskarsa ba, ya dago yace "Ni daga wajen aiki nake yau" Da sauri ta kallesa tace "Wajen aiki kuma, dama ka koma ne?" Yace "Tun lahadi" Tace "Toh ita sai ka bar ta a ina, ko tare da ita ka koma" Yace "Aa, gida take" Ummi tace "Ita kadai?" Ya gyada kai, Ummi tace "Toh kada ka sake barin ta gida ita kadai, idan baxa ka tafi da ita ba ka kawo ta nan" Yace "Toh" Shiru ne ya biyo baya, bayan few minutes ya mike yace "Sai na
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 17 Chapter of 57