whatever u wish" Ta dinga kallon kudin memories din lkcn da Abuturrab ke xuwa wajenta a hayi ya hau dawo mata, shi kadai ne ya ta6a bata kudi da yawa haka ta ba Baabarsu, wajensa ta fara ganin kudi da yawa, Yousuf dai kallonta kawai yake ganin yanda take kallon kudin, can tayi murmushi tana girgixa masa kai tace "Aa nagode" Yace "Ni na baki ki amsa Jiddah" Daga kai tayi suka hada ido da Abuturrab dake tsaye jikin motarsa a bit far from them, ta sauke idonta tace "Ni bana bukatan komai don haka ba abinda xanyi da kudi, nagode Allah ya saka da alkhairi" Yousuf ya dinga kallonta, sai kuma yace "Ni nace kina bukatar wani abun ne!" Ita dai bata ce komai ba, yace "Toh shkkn sai da safe" Yana fadin haka ya xaga ya shiga motarsa ta juya ta koma cikin gidan, dakinsu ta shiga direct ta kulle kofar tayi kwanciyarta, Maimoon da ke danna laptop tace "Sai ga yaya Aliyu ya xo yau ma" Jiddah ta kalleta tace "What about that?" Maimoon tace "Atoh ni naga kwanan nan sai yayi ta xuwa gidan nan bayan mu sai mu shafe wata da watanni bamu gansa ba in dai ba Ya Ahmad na nan ba, to shine abun ke bani sleepless night..." Tagumi tayi bayan ta fada hakan, Murmushi Jiddah tayi tace "Za ki ga Sleepless night" Maimoon ta fashe da wani dariya tace "But on a serious note me ke kawo Ya Aliyu gidan nan don Allah?" Jiddah tace "Toh ki tambayesa mana" Maimoon tace "Ni kaza??? Bari dai kawai in sa a raina saboda yana son su yi sulhu da Umma ne yake sintirin xuwa, kinsan fa Umma haushinsa take ji tun lokacin bikinsa da wnn ajebo din, amma bari dai in ci gaba da xuba ido ko xan gano wani abun daban" Jiddah ta juya mata baya bata ce komai ba, abinda ya faru daxu a hospital ne ya fado mata, ta turo baki sai kuma ta kulle idonta da sauri. Kwana uku Jiddah tayi tana period kafin ya dauke har a lkcn kuma Umma bata san tayi ba, amma throughout period din babu wani ciwo da ta ji, sai dai bata iya cin abinci ne kawai. Ranan talata ta koma gidan Ramlah ta ci gaba da karatun ta.... As usual ranan friday da yamma Abuturrab ya shigo gidansa from Kano state, Aneesah ta fito daga kitchen tana sanye da kananun kaya ta karaso da sauri ta rungumesa warmly tace "Welcome back my captain" Ya d'an kalleta yace "Thank you" Ta durkusa ta fara cire masa cover shoe din kafarsa, da kansa ya karasa cirewa yayi wucewarsa sama, ta bi sa tana rike da jakar laptop dinsa da ya ajiye... Har ya fito wanka tana dakin ta shigo masa da abinci ta baxa kan carpet da zobo drink, ya gama shiryawansa cikin kananun kaya, cike da shagwaba tace "In xuba maka abincin yanxu ne My Captain?" Yace "Na ci abinci tun after juma'at prayer" Lkci daya ta hade rai tace "What did u mean then??" yace "I mean xan ci anjima in sha Allah, yanxu Abba na kirana ne" bata fuska tayi ya gama abinda yake ya dau car key yace "Sae na dawo" daga haka ya nufi kofa ya fita, da sauri ta mike ta bi bayansa tace "Captain nima yau nake son xuwa gaida su Ummi fa" Ya girgixa kai yace "Ni kin ga sauri nake yanxu, sai dai gobe" Tabe baki tayi har ya fita parlorn. Abuturrab na isa gida a waje yayi parking ya shiga ciki, parlon Abbansa ya nufa yayi sallama bakin kofa har aka amsa masa sannan ya shiga, Abba ne xaune parlon da uncle dinsa Alhaji Umar, ya xauna kasa duk ya gaishesu, bayan few minutes Abba yace "I wanted asking you about that girl with Umma" Abuturrab ya daga kai ya kalli Abba, Abba yace "A wani anguwa suke a can hayin rigasa?" Abuturrab ya d'an yi shiru, sai kuma yace "Me ya faru Abba?" Abba yace "Babu abinda ya faru, sani muke son yi..." Ya sauke idonsa sai kuma yace "Ni ban san sunan anguwan ba" Abba yace "Amma kasan anguwan ai ko?" Da kyar yace "Na sani" Abba yace "Toh madallah" Alhaji Umar yace "Ko kuma kawai ka dangana mu da gun mai anguwan tunda ka san sa" Abuturrab yace "Abba wani abu ya faru ne?" Abba yace "Not at all, gobe asabar tunda kana nan sai mu tafi gaba daya" Abuturrab bai kuma cewa komai ba, Abba yace "I think that's all" Mikewa Abuturrab yyi yace "Xan je in gaida su Ummi" Abba yace "Alright" fita yayi daga parlon, ya tafi dakin Hajja, Hajja tayi masa kallo daya ta karasa dage labulayen dakin da take yi, yace "Ina yini" sai da ta fara kallonsa don tabbatar da cewar da ita yake sannan tace "lafiya lau" Tsintsiya ta dauka tace "Yanxun nan muka gama waya da Kabiru, kaga da nayi masu bori ai gashi an dau maganata da muhimmanci, da fa gantalar da xancena aka so yi, basu san ni er banxa bace idan tsiyata ta tashi, amma duk Safinah ce munafukar.. tun farko naga yanda ta dau maganar tawa ai" Abuturrab dai kallonta kawai yake, Hajja tace "Shi ma El-Basheer din mun yi waya da shi daxu ai..." Abuturrab yace "Me ke faruwa?" Hajja ta kallesa tace "Aa wannan kuma sirrinmu ne, babu ruwanka, kai wa kake gaya ma sirrinka balle mu bude maka cikinmu?? Kaji min mutumi dai, ko a Masar wanda ke yi da kai da shi kake yi ko da kuwa jininka ne..." Mikewa Abuturrab yyi ya nufi kofa ya fice daga dakin, Hajja tace "Da dai ya fi maka, nan nan nan ka auro dangin xabiya har aka gama bikin nan babu karen da yayi shawara da ni balle in tofa Albarkacin bakina, mu dai duk yanda aka ce mana haka muka dinga yi kamar shashashai, daga karshe ma ashe er iska kazama ka auro.. to ka dai yi ma kanka wllh" Abuturrab na fita bangaren Ummi ya tafi, Bayan sun gaisa, Ummi da ta lura da mood dinsa tace "Is there anything?" Ya girgixa kai yace "Nothing" Ummi ta ci gaba da aikin da take, bayan few minutes Abuturrab yace "Daxu kafin mu taho daga Abuja Abba ya kirani yana nemana, and na xo yanxu sai yake tambayata unguwar su Jiddah" Ummi ta kallesa tace "Wacece Jiddah?" Abuturrab yyi shiru yana kallonta, Ummi tace "Ohh... sure ni ma ya tambayeni nace masa sai dai a kiraka..." yace "Toh me ke faruwa Ummi?" Ummi tace "Baka tambayesa ba kafin ka fito?" Shiru yyi, Ummi tace "Toh nima ban sani ba kam" Mikewa yayi yace "Xan koma gida sai anjima" Ummi tace "Toh Allah ya kiyaye" ya nufi kofa ya fita, kallo daya yayi ma bangaren Aunty ya fice daga gidan gaba daya. Ahmad ne xaune dakin Umma yana kallonta yace "Me yasa Hajja take haka ne wai Umma?" Umma ta ta6e baki tace "Ni kuma idan ka tambayeni in tambayi wa? Abun dai gashi nan gashi nan kamar wasan yara, amma laifin su Alhaji Usman din ne dake biyeta ai" Ahmad yace "How will that even be possible? Shi El-Basheer din ne yace masu haka?" Umma tace "Kaga wannan xancen bacin rai yake sa min Ahmad" Ahmad ya mike yace "Xan kira Bashir din yanxu" daga haka ya fita dakin, nasa dakin ya koma ya xauna gefen gado sannan yyi dialing number El-Basheer yana fara ring ya daga, suka gaisa sannan Ahmad yace "Kana Bauchi ne?" El-Basheer yace "Yeahh..." Ahmad yace "Wani labari nake ji wajen Hajja shine na kira so i can confirm from u" El-Basheer yace "Labarin me kenan fa?" Ahmad yace "Auren da kake nema" El-Basheer ya d'an yi dariya yace "Ohh really? Nima nake neman ma kaina kenan" Ahmad yace "Haka nake tunani" El-Basheer ya girgixa kai yace "Aa su dai suke nema min, ni ba ruwana" Ahmad yace "Ban gane ba ruwanka ba, dama xa ayi abu without ur consent ne?" El-Basheer yace "You heard me right Ahmad, su suke nema min aure ba ni ke nema ba" Ahmad yace "Toh Allah ya sa hakan shine mafi alkhairi" El-Basheer yace "Ameen" Ahmad yayi masa sai anjima sannan ya katse wayar... Abuturrab na xaune main parlor din gidansa tare da Ahmad, Ahmad yace "Magana xaka min ba shiru ba Captain" Abuturrab yace "Ni ban gane tambayar nan taka ba" Ahmad yace "Ohk haka kace?" Abuturrab ya gyara xama yace "But me yasa wnn thinking din ma ya xo maka at the first place Ahmad, u can see i am happily married with my wife, menene xai sa kayi tunanin i have anything to do with that girl? Da ina da ra'ayinta ai kome xai faru ni baxan amince in saketa ba lkcn da su Abba suka min umarnin yin hakan" Ahmad yace "Is that so?" Abuturrab yace "Yes" Ahmad yace "Ohk then, i was mistaken kenan, cause ni a nawa tunanin if u have nothing to do with something baxa ka dinga bibiyan abun blindly ba..." Abuturrab ya dakatar da shi yace "They are some kind of talks dake 6ata min rai.. what are u insinuating now?" Ahmad yace "Nothing!!" Abuturrab ya ja tsaki yace "Da ina da intention din xama da ita babu wanda ya isa ya sa in saketa.... Balle ma duk su gama haukansu" Ahmad yace "I am glad i cleared this now" Mikewa yyi yace "Sae mun yi magana" daga haka ya nufi kofa, Abuturrab ya jinginar da kansa jikin kujera ya bi sa da ido. Da daddare Jiddah ta fito wanka kenan tana shiryawa Maimoon ta shigo dakin rike da wayarta tana xaro ido ta mika ma Jiddah wayar murya can kasa tace "Ya Aliyu" Da mamaki Jiddah ke kallon wayar, can ta amsa ta kai kunne jin shiru tayi sallama murya can kasa, daga daya bangaren taji yace "Kina jina?" Tace "Eh" yace "Duk wanda xai ce ki kai sa can gidanku a hayi kice baki san hanyar gidan ba" Tayi shiru tana sauraronsa, calmly yace "Kin ji abinda nace maki" Tace "To saboda me?" A takaice yace "Saboda haka nace maki" kasa ce masa komai tayi, taji ya katse wayar, tana kallon Maimoon ta mika mata wayarta, Maimoon ta amsa tace "Me yace maki?" Girgixa kai tayi tace "Abu yayi misplacing a hospital yake tambayata ko na gani" Maimoon dau ta juya ta fita bayan ta ta6e baki. Xaunawa Jiddah tayi gefen gado ta kasa ci gaba da abinda take tana tunanin to wa xai tambayeta gidansu a hayi. Washegari Asabar tun safe Abba ke kiran Abuturrab wayarsa a kashe, Hajja sai cewa take "Yau naga bala'i.. to wai baku san gidansa bane Usman, ko kuma mu tafi a dau yarinyar ai baxata rasa sanin hanyar gidansu ba tunda ba kwakwalwar kaza ce ita ba da xata mance gidansu, amma kun tsaya kuna ta kiran mutumi dake can yana bacci tare da matarsa, ranan ma fa da muka je gidan da Jiddah suna can suna ta bacci da rana tsaka har da garkame kofa" Abba yace "Toh sae a je da yarinyar ta nuna unguwar nasu" Aunty ce tsaye dakinta tana waya duk abun duniya ya isheta, Godiya tace "To ai duk laifinki ne Hafcy, da tun farko kin fito min da haka ai ni da tuni naje anyi abinda xa ayi an gama" Aunty tace "Ni kinga abinda yasa ban ce maki komai ba naga suna yawan waya har ma da chatting sai na fara tunanin ko abinda nake so ya kasance ne ke son kasancewa a raina, ashe ba haka bane" Godiya tace "Yanxu shi yariman da bakinsa yace yana son shegiyar yarinyar?" Aunty tace "Ji wata magana, da bai ce yana sonta ba neman auren me xa aje yi kuma, bbu wanda xai masa dole, da yardansa shi sa kika ga abun ke son yi nisa, wai yau fa xa aje can gidansu yarinyar" Godiya tace "Toh bari dai xan kira ki xuwa anjima" Daga haka ta katse wayar, Aunty ta xauna gefen gado tayi tagumi, Yarima da take ma Aisha sha'awa ne xa a nemi a makala ma wata can mara asali da dangi da kaf duniya bbu wanda take jin tsana irin ita, sake kiran Number mum din El-Basheer tayi amma har ya katse ba'a dauka ba, ta ja tsaki tace "Ko ina ta jefar da waya haka nake ta kira tun daxu" Kusan a guje Aneesah ta nufo Abuturrab ganin ya dau wayarta ta kwace tace "Wayana ne ai captain, naka na parlor" Ya dinga kallonta, sai kuma yace "Kira xan yi" tace "Naka fa?" Yace "A kashe yake" Tace "A kashe kuma, to me yasa baka sa a caji ba" Yace "I switched it off ba wai bani da caji ba" Tace "Toh bari in baka karamin wayana wnn ba credit" Bai ce mata komai ba ta karasa ta dau karamar wayar sai da tayi deleting duk out going da incoming sms snn ta kai masa wayar, amsa yayi ya fita parlor, ta sauke wani boyayyen ajiyar xuciya, downstairs Abuturrab ya sauka yayi dialing number El-Basheer dake kansa, yana fara ring ya daga, Abuturrab yace "How are you doing?" El-Basheer yace "Alhmdlh, ya aka yi wayarka a kashe?" Abuturrab yace "Na shiga bathroom da shi ya fada cikin ruwa" El-Basheer yace "Hard luck, grandma tace ana ta kiranka ka kashe waya" Abuturrab yace "Saboda me xan kashe waya" El-Basheer yace "Ai ban sani ba" Abuturrab ya shafa beard dinsa yace "Jiya na samu labarin matar da aka samar maka" El-Basheer yace "Ashe baka samu labarin da wuri ba kenan" Abuturrab yace "Amma nayi mamaki" El-Basheer yace "Mamakin me" Abuturrab yace "Warce Prince ke da niyyar aure" El-Basheer yyi murmushi yace "Sai dai kuma kasan ba prince din yayi ma kansa xabin ba" Abuturrab yace "A seventeen year old girl? Sai kace ka auri me kenan?" El-Basheer yace "Hajja xa mu yi ma wannan tambayar" Abuturrab yace "Kuma ka bani mamaki" El-Basheer yace "Na me fa?" Abuturrab yace "Ban yi tunanin xan rabu da abu ka dawo ka nuna kana son abun ba, in saki mata kace xaka aura" El-Basheer yace "Saboda hakan haramun ne?" Abuturrab yace "Whatever, amma it's more a less of abun kunya hakan da kayi, Allah ka bani mamaki" El-Basheer yace "From the beginning i was never serious with Hajja saboda ina ga kamar abinda baxai ta6a faruwa bane, amma wannan words din da ka fada min yanxu ya sa naji dole ma sai na auri Jiddah, kuma ka xuba ido ka gani... Till then" daga haka ya Katse wayar, Abuturrab ya dinga kallon screen din.... Ummi da wata frnd dinta tare da Aunty suka tafi can gidan Umma don nufin tafiya gidansu Jiddah tare da Jiddar, bayan Umma da Ummi sun kebe a daki Umma tace "Yanxu yaya menene amfanin wannan abun da Hajja ke shirin yi, duka duka shekarun yarinyar nan nawa, ko secondary din ma baxa a bari ta gama ba, yaushe ta samu yancin kanta har xa a fito da wani xancen aure a kanta? Don Allah ni dai a san yanda xa ayi a janye maganan nan wllh banyi farin ciki da shi ba, ina ita ina family dinsu El-Basheer? Yarinyar da har yanxu bata samu karatun kirki ba, takaicin da ta sha a gidan Aliyu ai kadan ne da wanda xata je gidan sarautan nan ta fuskanta... " Ummi tace "Kar ki yarda Hajja ta ji wannan abinda kike gaya min, nima na fara kawo mata hakan tace bakin ciki nake ma yarinyar saboda Bashir bai ce yana son Nafisah ba... Tun daga sannan na ja bakina nayi shiru, mu dai namu kawai fatan alkhairi" Umma tace "Aa wllh idan tsoron gaya mata gaskiya kuke sai ni in buda baki in gaya mata abinda ke raina, ya muna xaune lafiya xata dawo daga Masar duk ta bi ta daga mana hankali haka, ba fa Bashir din yace yana so da kansa ba, duk hade hadenta ne da rikicin tsufa irin nata, ni baxan amince da hakan ba gaskiya, yarinyar da nake so har university sai ta fara kafin aure... Sannan ni akwai d'an aminiyata ma a kasa" Ummi ta juya ta fita daga dakin kawai, Umma dai sai tafarfasa xuciyarta ke yi, Aunty kuwa na xaune parlor bakin ciki na ta cinta ita ma, Jiddah ta fito dag dakinsu ta durkusa ta gaida Ummi, sannan ta gaida frnd din Ummi da Aunty, Ummi tace "Xa ki gane anguwar ku Jiddah?" Jiddah tayi shiru tana kallonta, Can ta girgixa kai a hankali tace "Aa" Ummi tace "Baxa ki gane ba??" Jiddah ta gyada mata kai, Umma dake tsaye parlon taji dadi har ranta da Jiddah tace baxata gane gidansu ba...
Littafin Jiddatul Khair na kudi ne, it's 500 via
3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u show ur evidence of payment via 07087865788... Thank you
Fareeskinglow is a last bus stop do u wanna have a fairer skin or u wanna glow up ur skin here is the last bus stop where u can get ur desired results, a dream of having auniform complexion, glowing skin nd getting rid of any skin problems
Fareeskinglow karshe ne Ina kuke masu son farar fata ko masu son jikin yayi glowing kawai ga dama ta samu fareeskinglow taso muku da kayan gyara jiki fatarki yayi fari tayi sheki duk Wani tabo irin su konewar rana masu zagayen Baki a ido,masu pimples masu fama da combination skin Nan Baki Nan fari Ina mata masu ciki da masu jego wayanda wuyansu ke Baki duk fareeskinglow tazo muku da kayan gyara Wanda zaisa fatarki tayi sulbi da sheki ki komai kamar tarwada
Instagram -fareeskinglow_89
TikTok-fareeskinglow
Facebook page-fareeskinglow
WhatsApp -08031898240
Ummi ta kalli Umma tace "Ahmad ai xai gane gidan shi ko?" Umma tace "Anya kuwa? Amma dai bari in kirasa in tambayesa" Daukar wayarta tayi ta wuce daki, bayan few minutes ta fito tace "Ai kam bai sani ba wai shi ma" Ummi dai kallonta kawai take, Aunty tace "Tunda duk basu sani ba ai sai mu wuce gida kawai a nemi wani solution din, don baxa mu kama hanyar xuwa inda bamu sani ba gaskiya," Umma tace "Ai ko dai" Haka nan su Ummi suka koma gida, Aunty farin ciki fal xuciyarta, ai ko ita kadai ta isa ta hana xuwa gidansu Jiddah.... Hajja ce xaune parlon Abba ta dafe kai, cike da bakin ciki tace "Huhuhu... mutane dai yanxu tsoron Allah wuya yake masu ni Dije, da kyar al'ummar yanxu ke tsoron Allah wllh, yo banda rashin tsoron Allah ba a san gidan Aliyun bane da baxa a je a tisa keyarsa ya kai mu gun dangin yarinyar ba? Ko kuna da wata manufa da kuke boyewa a ranku ne ban sani ba, ni dai wllh ban ta6a sanin Masar rahama bace sai da na baro can, wllh da can ne duk haka baxai dinga faruwa ba, yo ina hakan xai faru kowa ya tashi ya girma da tsoron Allahnsa" Abba yace "Yanxu ya kike so ayi Hajja, ba fa sauri ake wannan lamarin ba..." Hajja ta dakatar da shi a fusace tace "Aa wllh sauri nake, kune dai baku sani ba, yanda xa ayi yanxu kuma shine a tashi a tafi gidan wancan mutumi Aliyu, idan kuma duk baxa ku ba, ni da kai na sai in dau gyale in je in dau yarinyar mu tafi gidan Aliyun in sa shi gaba ya kai ni unguwar tunda shi ya san asalinta" Abba yace "To gaskiya idan haka xaki dinga axalxalan lamarin nan ni Hajja xan cire hannuna, sai shi Mai martaban ya taho da kansa..." Hajja ta runtse ido tace "Qul Usman, kar ka sake fadin haka wani sai yace bakin ciki kake wllh, nima don na kai xuciya nesa ne da haka xance wllh, ba fa wani yasa gantalallan d'an ka ya saketa ba Usman, bakin ciki kake ma d'an yayan naka ne? Aa to gaskiya har ka ban tsoro, da kaina xan tashi yanxu in shirya in tafi gidan Aliyun, ai ba bakona bane gidan, irin wannan lamarin ance maka ana bin sa da sanyi sanyi ne" Tana fadin haka ta mike ta fice daga parlon, sai da ta fara sa aka kai ta gidan Umma wai xa ta tafi gidan Aliyun tare da Jiddah, daga can shi kuma sai ya kai su hayin, Umma dake tsaye bayan kujera tace "Toh ai bata nan Hajja sun tafi Islamiyya, kuma ba ma gidan nan take ba yanxu tana gidan Ahmad ne" Hajja na kallonta daga sama har kasa tace "Waye kuma Ahmad, ana magana sai ki dinga wani sako Ahmad... Ita kuma ba sai ki kira makarantar kice a turota gida ba, ko su basu san uxuri bane" Umma tace "Hajja idan kin je can gidan Aliyun kuma Allah ya sa kin samesa..." Da sauri Hajja ta katse tace "Yana nan ba inda xai je ana hutun karshen mako, ke dai kiyi ta kanki ki fada abinda xaki fada in tashi..." Umma tace "Shkkn, sai ya kai ki har gidan tunda nasan baxai rasa sani ba, amma xancen a kirawo makaranta ace yarinya ta dawo a katse mata karatu bai taso ba balle ma ni bani da number shuwagabannin makarantar" Mikewa Hajja tayi ta nufi kofa murya can kasa tace "Aniyarki ta baki, mata kin narka kiba kina ta xuba ma mutane iko, yaushe xa a ga haka a Masar, 'ya yan bakin ciki kawai... Daga ke har Uban Aliyun" sannan ta fita.... Daga sama har kasa Aneesah ke kallo Hajja bayan ta bude kofar, can ta ja gefe ta kauda kai tace "Sannu da xuwa" Banxa da ita Hajja tayi ta shige parlon kai tsaye ta tafi kan kujera ta xauna, Aneesah ta bi ta da wani shegen hararan tsana, ita dai kaf kaduna bayan Jiddah bata da wanda ta tsana kuma kamar Hajja, Hajja tace "Zo ki kira min mijinki ni wajensa na xo ba wajen wani ba, kuma sauri nake yi" Babu yabo babu Fallasa Aneesah tace "To ai baya nan Hajja, da kin kirasa kafin ki xo...." Ko rufe baki bata yi ba sai ga Abuturrab yana sakkowa, tsaye shi ma yyi a stairs din karshe ganin Hajja, Hajja ta kalli Aneesah tace "Kika ce baya nan?" Aneesah tace "Ohh ban ma san ya shigo ba, ni ina kitchen ne" Hajja ta ja tsaki ta mike tace "Mu je Aliyu, ba xama na xo yi ba..." Bai yi musu ba saboda Aneesah ya bi bayanta suka nufi kofa, Aneesah ta kirkiro murmushi tace "Toh baki sha ko ruwa ba Hajja, ga girki ma ya kusa nuna yanxu" Hajja tace "Aa wllh Alhmdlh, ai daga gida nake, kuma ni wajen jikana Aliyu na xo ba xama na xo yi ba dama" Daga haka ta fice Abuturrab ya bi bayanta, Da sauri Aneesah tace "My captain abincin fa?" Yyi mata alama da hannu yana xuwa, yana fita tayi wani murmushi ta xauna saman kujera ta dau chips dinta ta ci gaba da ci. Suna fita parking space Hajja tace "Kaga da kyau ai da muka fito tunda maganar sirri ne, baxan bar wata 6are can taji cikinmu ba, wai don rashin kunya tayin ruwa take min saboda in sha in tsuge da gudawa, kai hancinka baya jin karnin da parlon nan ke yi ne kamar an fasa danyen kwai, ko iyayenta basu mata irin turarurrukan wutan xamanin nan da naga ana yi ne, wllh fa kazama ce, da a Masar ne dole a raba wannan auren naku don guje maka wata cutar, toh dai ba ruwana da abinda bai shafeni ba, yanxu so nake mu hau mota ka kai ni gidansu yarinyar nan Jiddah, naji ance a hayin rigasa take koh?" Ya dinga kallon Hajja kafin yace "Ehh, me xaki je kiyi a can?" Tace "Aa wannan sirri na ne, yanxu muje ka kai ni, ni kadai ma na ishi inje gun iyayen nata... Waye kuma Usman ko Umaru" Abuturrab yace "Toh bari in dauko makullin motar" Tace "Toh yi maxa" tana tsaye har ya shiga ya fito
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 50 Chapter of 57