Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
baci, can dai tace "Amma ai xata dinga xuwa nan din ko" Umma tace "Aa me xai hana kuwa" Umma na fadin haka ta mike tana kallon Jiddah tace "Mu je Jiddah" Jiddah ta mike a hankali ta bi bayanta, Aunty ta bi ta da kallon tsana, shi kam Abba tausayinta kawai yake ji, banda rashin gata ya xa ayi hakan ya faru gareta ma. Bangaren Ummi Umma ta kai ta, Ummi na xaune parlonta da Hajja dake mata magana kasa kasa, amma ganin Umma sai tayi shiru, Umma tace "Toh yaya mun tafi sai da safe" Ummi tace "Baxa ku yi isha ba?" Umma tace "Eh to bari inyi" Daga haka ta karasa bedroom din yayarta, Jiddaj dai na rakube jikin kujera, Ummi ta kalleta tace "Kije kiyi sallan ke ma" Mikewa Jiddah tayi ta fita, Hajja ta tabe baki tace "Toh ai gwara ma da aka kashe wannan auren don ai Aliyu d'an usuli ne, ita kuma bamu san yaya ba" Ummi tace "Ai babu wanda bashi da usuli Hajja" Hajja tace "Aa Hafsat dai bata da shi, an rasa gane ko kwatakwali ce har yau, duk da tace uwarta yar Benue ce" Ummi dai bata ce komai ba, Hajja tace "Shi yasa gashi duk ta amshe gida tayi bake bake, komai sai inji Usman yace Hafsa, to wacece kuma Hafsa, dama Hadiza ta bani labarin irin xaman da ku ke yarda ce kawai ban yi ba, gashi duk ta rufe maki baki ta amshe gida, wa ya sani ko ma har da ya yanki? Tunda na xo naga take takenta komai sai ace sai ita, to a kan me?" Ummi tace "Aa Hajja kowa ai da matsayinsa a gidan" Hajja tace "Toh kunga lalacewa ko? Wani matsayi matar da ta kwace maki miji ta karfi, me yasa kike abu sakwa sakwa kamar warce aka ce ma je ki kya gani Hauwa, komai fa na bikin nan naga sai dai ace Hafsat to wacece kuma Hafsat, gashi ana maganan tabargaxan da yaro yayi mata tayi bake bake a kan xancen kamar d'an ta, to ni tunda na xo ma ba sau daya Salem ya shigo gaisheni ba, duk sun tsotsa a nono wllh, dubi fa Aisha kamar yar karuwai Allah na tuba, to ba dai komai tunda duk jikokina ne, amma idan xaki tashi tsaye ki amshi gidanki ki tashi" Fitowar Umma yasa Hajja tayi shiru, Umma tace "Toh sai da safe Hajja, yaya sai mun yi waya" Hajja tace "Toh Allah ya ba yara xaman lafiya ya kauda fitina amma ki dai je asibiti kiga kibar ta mecece kika narka haka kinji" Umma bata tankata ba har ta fita, Hajja tace "Toh sai da safe" Sai da Jiddah ta sake shigowa tayi ma Ummi da Hajja sai da safe sannan suka bar gidan tare da Umma, har driver ya maida su gida Jiddah bata cewa komai, duk tayi sanyi sosai, ta rasa ko farin ciki take ko bakin ciki, Wajen karfe tara Umma ta xaunar da ita a dakinsu Maimoon tace "Kina ji na Jiddah?" Jiddah ta daga kai ta kalleta, Umma tace "Kin dai ga yanda abubuwa suka kasance, ni nasan Abuturrab bai da niyyar cutar dake a ransa, kuma har abada ina son ki daukesa da girma da mutunci don ya maki abinda ba kowa xai iya maki ba a rayuwa, duk abinda xaki xama a rayuwa nan gaba Allah ne ya tabbatar da hakan amma Abuturrab ne sanadi, ina son kuma ki maida hankalinki kiyi karatunki, kin san wacece ke kinsan daga inda kika fito" Hawaye ne ya shiga xarya idon Jiddah tana kallon Umma, Umma tace "Ni kuma ina fatan Allah ya bani ikon yi maki duk abinda ya kamata a rayuwarki Jiddah" Cikin rawar murya tace "Toh Umma baxan sake ganinsa ba kenan?" Da mamaki Umma tace "Don me baxa ki gansa ba, in dai Allah ya kawosa gidan nan ai xaki gansa, sannan xaki dinga yawan xuwa gida Ummi, idan baku hadu a nan ba xaku hadu a can, balle ma nace tsakaninki da shi kawai girmamawa ki daukesa kawai a matsayin babban wan ki, nasan shi ma a matsayin kanwarsa xai daukeki" Jiddah ta share hawayen idonta a hankali tace "Toh Umma nagode" Umma ta sakar mata murmushi, har ranta taji tana son Jiddah tana kuma son inganta rayuwarta, Umma tace "Gobe da safe sai mu je can gidan a kwaso duk wani abu naki" Jiddah ta gyada mata kai kawai, Umma ta mike tace "Toh sai da safe" Daga haka ta nufi kofa Jiddah ta bi ta da kallo wasu hawayen na kawowa idonta, Umma na fita Maimoon ta shigo dakin. Washegari misalin karfe Goma Umma ta kira Abuturrab, miss calls tayi masa kusan uku kafin ya daga, bata amsa gaisuwan da yake mata ba tace "Kana gidanka ne?" Yace "Ina nan" Umma tace "Ohk i am coming now" Bai ce komai ba ta katse wayar, tare driver ya kai su gidan Abuturrab da Jiddah da Maimoon da safiyya, mai gadi ya bude masu gate driver ya shiga da motar cikin compound, Umma ta sauka motar sannan su Jiddah, Hijab ne har kasa jikinta, suka bi bayan Umma xuwa entrance din parlon, a bude suka tarda parlon, yana kwance saman doguwar kujera da jallabiya, suna hada ido Jiddah tayi saurin sunkuyar da kanta gabanta na bugawa da karfi, sanye yake da jallabiya ya mike xaune a hankali yace "Ina kwana Umma?" Tace "Lafiya lau, ya gajiyan jiya?" Yace "Alhmdlh" Maimoon ta gaishesa ya amsa, Jiddah ma tace "Ina kwana?" Sai dai taki yarda ta kallesa, bai amsa ba ita dai ta xauna kasa kusa da kujeran da Umma ta xauna, Umma tace "Jiddah xata debi kayanta na nan ne" Ba tare da ya kalli Umma ba yace "Ohk" Umma ta mike tana kallon Jiddah tace "Mu je" Mikewa Jiddah tayi ta nufi stairs Umma na biye da ita Maimoon ma ta bi bayansu, da ido Abuturrab ya bi su har suka haura sama, Kaf sai da Umma ta kwashe duk abubuwan Jiddah dake dakin, Maimoon ce ke kai wa booth din mota, Ita dai Jiddah na tsaye jikin kofa sai kallonta take, ta rasa dalilin da yasa taji tana son tayi kuka, Umma ta mika mata babban ledan da ta hada duk abubuwan gaban madubi a ciki tace "Ki kai wannan" Jiddah ta karasa ta amsa ta nufi kofa ta fita, a stairs suka hadu da Maimoon, Maimoon tace "Kawo in kai toh" Jiddah ta kirkiri murmushi tace "Xan kai" Maimoon ta shiga dakin ita kuma fita, satan kallon parlon ta dinga yi taga baya nan, ta fita balcony, sosai gabanta ya fadi da ta gansa a xaune kan kujera yana danna wayarsa. Xata sauka stairs din balcony din taji yace "Toh ni dake wa yyi lose?" Ta juya tana kallonsa don bata gane me yace ba, yayi wani murmushi ya mike, speaking calmly yace "Kema kinsan wllh idan ba kaddara ba babu abinda xai hadani dake a rayuwa balle har in aureki bisa kuskure, aurenki da ni babban kuskure ne wanda nayi sbda in taimaki rayuwarki.. banda haka ai ni nafi karfin ki, komai da ya faru ya faru ne sbda haka Allah ubangiji ya tsara, duk da fin ki komai da nayi haka na hakura na xauna same roof dake sbda biyayya da kuma xuciyar musulinci, amma wai har ke xaki je ki sanar ma iyayena na sakeki? Toh yanxu da na maki sakin me hujja akwai wani abu da xai ragu a rayuwata ko kuma wani asara xan yi?" Ita dai kallonsa kawai take ko kiftawa babu, yayi wani murmushin kuma yace "Toh na maki duk abinda na maki saboda Allah ba don ki nuna kin san ni wataran ba, kai ni ko a hanya kika gan ni kar ki ta6a nuna kin ma san ni don kunya hakan xai bani, kiyi wucewarki inyi wucewata, na kuma fi kowa farin ciki da murnan xuwa karshen wannan al'amarin, i am now free like every other...." Jiddah dai kallonsa kawai take bbu ko kiftawa, ganin ya koma ya xauna cikin sanyin murya tace "Toh nagode" Daga haka ta juya ta kai ledan mota... Tare suka fito gidan da Umma bayan duk an kai komai mota, Har sannan yana xaune balcony, Umma tace "Toh sai anjima, yaushe xaka koma aikin" Yace "Anjima in sha Allah" Tace "Toh Allah ya tsare" Daga haka ta nufi mota, Maimoon tace "Sai anjima yaya" Yace "Ohk" Sai da Jiddah ta sauka balcony ta d'an kallesa tace "Sai anjima...." *Rumor Creators how market? A masar dai ba a haka idan xaku gyara ku gyara, ku kuma masu karanta na bati da kuka fi kowa xakalkalewa a xo a biya bashi dai ko xa a samu nutsuwa, my fans dat wished me speed recovery ina godiya Allah ya saka da alkhairi sbda ku nace let me manage and give this little update na karfin hali, nagode sosai, snn abinda ke ci mun tuwo a kwarya shine yanda masu karantawa a free suka fi kowa bada hakuri, wllh duk sun cika min inbox, don Allah bakwa jin kunya ne, baka biya abu ba ka dage sai an ci gaba, tsaf ina da saved number din duk wanda yayi subscription din littafin nan ku ji in gaya maku* 🙄 Littafin Jiddatul Khair na kudi ne, it's 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u show ur evidence of payment via 07087865788... Thank you *Mîkyããj_Sããdy Beauty Soap* *Hy my beautiful people ina gaisuwa🙋🏻‍♀️ku karka'de kunnuwanku da kyau ku ji💃🏻ina mai sanar muku da cewa akwai gara6asa me kyau ta musamman ga wanda suka saba sayen sabulunmu da ma wanda zasu fara saya🥰, akwai ragin kaso 20% bisa dari 100% ga wanda suka saba saye, sannan akwai ragin 10% bisa ga masu sha'awar fara saye🥰, akwai farashi mai sauki ga 'yan sari, me yapi wannan dadi kam🤔ki sayi guda 4 kanana a baki kyautar daya, ki sayi guda uku manya a baki kyautar karami daya, ki sayi bucket biyu a baki kyautar babban rubber daya😍 kema da kike da burin saya ku'dinki bai kai ba😰to ga naki, ki kawo customers uku ki karbi naki kyautar Sabulun😍😍* *Kawata 'yar 'kwalisa me kike jira,ita mace fa kullum cikim yin ado da 'kãwa take😍 ya kamata ki yunkuro wajen ganin kin rabu da wannan kurajen da tabo tabon fuskan nan haka🥺, kinga kema sai a saka ki a layin masu 'kwalisa da bajakolin ado💃🏻😍uwar gida a daure ayi gyaran jiki, sbd karbar goron a wajen me gida🥰,, ina amaren bayan sallah ku pito ku sayi naku Sabulun kuje kuyi ta wanaka hmmm 😍kamshi kawai zaku yi tayi kaca kaca😍😍, laushin fata Baja baja😃😂😂a yunkuro azo a karbi kayan gyaran jiki tare da sabulun gyaran fata a wurin _Mîkyããj_Sããdy_🥰* *Duk wanda suka gwada Sabulun mu sun san babu 'karanta a ciki🥰in dai fannin gyaran jiki ne to sabulunmu shine amsarku,, shi ke mai da fata ta zama babu Pimples, Acne, Spot, Stretch Mark, da Duk wata matsala da ta shafi fata,, akwai lightening, nd glowing😍* _*In kina son jikinki yai su6ul da shi, fata tai santsi da sul6i, ki yi haske me aji, 'kamshi kaca kaca ko ta Ina, ki ta fresh abunki hankali kwance ki zama Wankan madara yauqin zuma😍💃🏻Anty madam😃To ki mallaki 3d (Extra Whitening Soap, Ko da kudinki sai da rabonki hajiyata)💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻*_ *Akwai hadin:* *Mai da tsohuwa yarinya* *Uwargida ta koma amarya* *Amarya ta koma tamkar 'yanmata* *'Yan mata su koma 'yan dagwai²* _Ga masu bu'kata sai su tuntu6emu ta kafar sadarwa kamar haka;_ _Call/WhatsApp:08061570778_ _IG@mik_yaaj_saady_ Bayan sati biyu Jiddah na xaune dinning area ita kadai bayan magrib, Hijab ne har kasa jikinta, Huraira kuma na kitchen tana wanke wanke, gaba daya hankalinta na kan takardan gabanta taji an danna bell, mikewa tayi ta nufi kofar ta bude, ta koma baya tana kallonsa tace "Ina yini" Da murmushi yace "Lafiya lau Jiddah" ta juya ta koma parlon ya karaso ya xauna, tace "Ya Aunty Ramlah?" Yace "Tana gaisheku, Umma na daki ne?" Tace "Ehh" yace "Tou xauna mana" d'an murmushi tayi ta xauna edge din kujera yace "Kin fara karatu koh?" Tace "Eh" yace "Amma ki fada min gaskiya, kina ganewa?" Ta gyada masa kai, yace "Aa bude baki ki min magana" Sunkuyar da kai tayi har sannan tana murmushi tace "Ina ganewa" Yace "Toh wani rana da wani rana ku ke karatun?" Tace "Ranan litinin xuwa juma'ah" Yace "Asabar da lahadi fa?" Tace "Islamiyya muke xuwa tare da su Maimuna" Yace "Toh me da me ake koya maki litinin xuwa Juma'ahn?" Tace "Karfe tara na safiya take xuwa mu yi boko xuwa karfe biyu, sai kuma Islamiyya karfe uku xuwa shidda" Yace "Duk ita ke maki bokon da Islamiyya?" Ta girgixa kai tace "Aa wata ce daban take xuwa karfe uku" Yace "Maa sha Allah, kawo takardun naki in ga" Mikewa tayi ta nufi dining ya bi ta da kallo ta dauko jakar da duk litattafanta ke ciki ta dau har da na kan dining table sannan ta kai masa, ya amsa yana dubu abubuwan da suka yi na sati biyu, ita dai tana xaune tana wasa da fingers dinta, ya daga kai ya kalleta yace "Anya ke da kanki kike aikin nan da malama ke baki?" Tayi murmushi tace "Ni ce nake yi ka tambayi Maimuna" Yace "Maa sha Allah, ki dinga maida hankali haka kinji?" Tace "Toh" Ya dau wayarsa dake ring, ta jira har ya gama wayar ya ajiye sannan tace "Aliyu fa?" Daga kai yayi ya kalleta, ta sauke idonta yace "Waye Aliyu?" Jin bata ce komai ba yace "Ohh captain wai?" Still bata ce komai ba, yace "Yana kano, mun yi sati biyu bamu hadu ba, kuma bana jin ya xo weekend" Tace "Toh" Umma ce ta shigo parlon ganin Ahmad tace "Yaushe ka shigo?" Yace "Not too long" Ta karaso ta xauna yace "Ina yini Umma" Tace "Lafiya lau, yau ma baka xo da Ramlan ba?" Yace "Ehh na barta da su Aisha ne sun je can gidan" Umma tace "Ohk" kallon Jiddah tayi tace "Har kin gama karatun?" Tace "Aa ina kan yi" Tana fadin haka ta mike ta isa gun Ahmad ta kwashi duk takardunta ta wuce daki, Ahmad yace "Cewa nayi ta kawo in ga performance dinta and naga she is really trying" Umma tace "Gaskiya kam, she isn't dull kawai dai karatun ne bata samu ba, amma in sha Allah nan da few months a yanda naga take da hazaka she might catch up with her mate, tana da kwakwalwa kam maa sha Allah" Ahmad yace "Toh Allah ya sa hakan, sai ayi enrolling dinta jss3 ko?" Umma tace "Ehh" Ya shafa kansa yace "Umma daxu Yousuf ya kirani..." Umma tace "Ya aka yi?" Ahmad ya d'an yi shiru, sai kuma yace "Wai a kan Jiddah..." Murmushi Umma tayi tace "Ni dai nasan ba haka nan yake xuwa gidan nan frequently ba da dalili, toh maa sha Allah..." Ahmad yace "But Umma ai bata bukatar wannan yanxu, she need to concentrate fully on her studies" Umma tace "Toh ai sai ka jira in gama magana ko... ni baxan hanasa alaka da ita ba, sai dai shigo da batun soyayya gareta yanxu isn't necessary, he should wait a little...." Ahmad dai bai ce komai ba. Aunty ce xaune gefen gadonta waya kare kunnenta tayi shiru fuskar nan nata a daure, can ta mike tace "Haka yace maki?" Daga daya bangaren Aneesah tace "Wlh Aunty" Aunty tace "Toh kyaleni da d'an iskan, nasan maganinsa...." Aneesah tace "Ni fa wllh Aunty yau kusan wata daya kenan na ma kasa gane kan relationship din nan namu" Aunty tace "Daina kiranki yayi?" Tace "Toh ai dama tun farko ba kira yake ba sai in ni na kira ya bi miss call, yanxu kuma ko na kira din ma sai sanda ya ga dama yake kira, sai yace aiki yayi yawa..." Aunty tayi shiru tana sauraronta, sai kuma ta sauke wani ajiyar xuciya tace "Amma kuna dai maganan still koh?" Tace "Aa muna magana, kawai sabon miskilanci da jiji da kai ya karo... Sai yayi ta cewa shi baya son damuwa, shi baya jin dadi, shi he want to sort somethings bothering him, shi yana son break, shi he wants to be alone for sometimes, haka dai wllh... Kamar baya son magana da ni" Aunty dake ta jin ta, tace "Amma ya siya maki abinda nace kice ya siya maki ko bai siya ba?" Tace "Aa ya tura min kudin har da kari ma" Aunty tace "Toh shkkn, xan kiraki xuwa anjima, ki kwantar da hankalinki" Tana kai wa nan ta katse wayar tayi dialing number Abuturrab, sai da ya kusa yankewa ya daga, yace "Ina kwana Aunty?" Tace "Wani laifin muka maka Aliyu yau kusan sati uku babu kai babu labarin ka?" Yace "Aa aiki ne yayi yawa yanxu..." tace "An sake employing dinka a wani airline din ne bayan wanda kake aiki?" D'an murmushi kawai yyi bai bata amsa ba, tace "Atoh gwara ai in ji, kuma ai kana shigowa kadunan, xuwa gida ne kawai baka yi" yace "Aa bana shigowa, amma xan shigo friday din nan in sha Allah" Tace "Toh ina saurarenka" Daga haka ta katse wayar. Hijab Jiddah ta dauka xata saka bayan ta gama shiryawa Maimoon ta hade rai tace "Meye hka kuma, ba ga mayafi na ajiye maki ba" Jiddah ta xaro ido tace "To ae an hanani" Maimoon tace "Wa ya hanaki?" Ta sake xaro ido sae kuma tace "Tou bari in sa" daukan mayafin tayi ta yafa, Maimoon ta washe baki tace "Waoww kinga yanda kika yi kyau kuwa" Murmushi kawai Jiddah tayi, suka fita xuwa dakin Umma, Umma tace "Kuna kai sakon ku dawo, ba sai na gaya maku kuna da Islamiyya karfe biyu ba" Maimoon ta marairaice tace "Yau dai kawai Umma, Sis Ramlah fa na can gidan" Umma tace "Toh ku bani xan ba Driver ya kai idan ya dawo" Maimoon ta xaro ido tace "Aa wllh ynxu xa mu dawo Umma" Kudin mota ta basu suka fita gidan, Jiddah na rike da ledan sakon da Umma ta bada su kai ma Hajja, karfe sha daya da rabi suka isa gidan, Maimoon tayi sallama bakin kofa tayi knocking sannan ta tura, Jiddah ta bi bayanta, babu kowa a parlon suka nufi part din Ummi, Ummi ta fito daga bedroom dinta jin sallama, ganinsu tace "Aa sannunku da xuwa" duk suka xauna suka gaisheta ta amsa da fara'a tace "Ku kadai?" Maimoon tace "Eh Umma ce ta aiko mu gun Hajja" Ummi tace "Ohk, ya karatu Jiddah" Jiddah ta kalleta ta d'an yi murmushi tace "Alhamdulillah" Ummi tace "Toh maa sha Allah, Allah ya taimaka" Maimoon tace "Ramlah ta koma ne Ummi?" Ummi tace "Aa tana ciki tana bacci" Maimoon tace "Toh bari mu kai ma Hajja mu dawo" Ummi tace "Ohk" mikewa tayi jiddah ma ta tashi suka fita daga parlon, dakin da Hajja ke sauka idan tana garin Maimoon ta nufa Jiddah na biye da ita, Maimoon tayi sallama bakin kofar sannan ta bude, Hajja ta daga kai tana amsa sallaman, karasawa ciki Maimoon tayi ta duka tace "Ina kwana Hajja" bata jira ta amsa ba ta kalli Abuturrab dake xaune dakin yana kallonsu daga sama har kasa ta cikin glass din idonsa, ta sunkuyar da kanta tace "Ina kwana yaya?" Yace "Me yasa baki ajiye mayafin a gida kin fito haka ba?" Maimoon ta hau gyara mayafin jikinta tana murmushi, Jiddah dai kanta na kasa ta durkusa ita ma ta gaida Hajja, sannan ta d'an kallesa taga wayarsa yake dannawa tace "Ina kwana" Ya kara wayar a kunne ya mike ya nufi kofa, Hajja ta saki baki tana kallonsa har ya fita, can ta kalli Jiddah tace "Ji ruba66e, toh ke idan ba dai neman wajen xama kike ba meye na gaishesa bayan iyayensa sun sa ya sakeki babu ko dar ya cike takarda ya mika maki, ai babu abinda kika hada da shi kuma yanxu, toh ga dai shi ya gwaleki, tun jiya fa na samu labarin dawowar almurin amma kun ga sai yanxu ya shigo gaidani yana shan kamshi ya wani sha uban gilashi kamar sabon makaho, Aa bak'in halinsa ya fi karfinsa gaskiya, alhalin sbda shi nake xaune har yau a gidan nan ban koma masar ba, to Hafsah ta ce min sati me xuwa xa a kai kudi gidan yarinyar da yake so da aure amma in ja bakina inyi shiru tunda ba a gaya min ba tukun, shine yasa nake ta xaune nan Allah" Maimoon dai sai murmushi take, Hajja tace "Toh aiko ku Ramlan tayi?" Maimoon ta ajiye mata ledan kusa da ita tace "Ehh tace mu kawo maki wannan" Hajja ta leka cikin ledan tace "Ahh da kyau, baiwar Allah nace mata gobe xan tafi shine ta bada tsaraba a kawo min, to tafiya ai ta lalace tunda auren Aliyu ya tunkaro, yanxu shigowarsa nake tambayarsa shi ma ya tabbatar min da haka ne" Jiddah dai sai kallon Hajja take, Maimoon tace "Toh Allah ya kai mu lafiya" Hajja tace "Ameen, ita ma Ramlah gata can ta xo tun shekaranjiya, kilan mijin baya nan, amma da kyar idan ba ciki ne da ita ba, kai cikin ne ma wllh, sai wani salalo salalo take" Maimoon ta kalli wayarta dake ring ta mike tace "Xa mu koma Hajja, sbda muna da Islamiyya karfe biyu" Hajja tace "Toh ai shkkn, anjima xan sa Aliyu ya kawoni in mata godiya idan ya ga dama kenan, kabu kabu fa yake amma jin kansa yake kamar me wani sana'ar arxiki baya ganin kowa da gashi, ga d'an banxan girman kai, ba ga masu kabu kabun ba muna ganinsu a tashar mota, ga yan acaba suma ai duk kabu kabun ce, to kuma waye shi Allah na tuba" Su dai basu ce mata komai ba suka fita dakin, sai a snn Maimoon ta mika ma Jiddah wayar tace "Yousuf" Jiddah ta amsa ta daga sannan ta kai kunne, murya kasa kasa Maimoon tace "Don Allah kice ya xo ya daukemu basu da nisa sosai daga nan" Tana fadin haka ta wuce bangaren Ummi, Jiddah ta nufi parlor, cikin sanyin muryarta tace "Ina kwana" Yace "Lafiya lau, me Maimoon take rada maki?" Murmushi tayi ta xauna saman kujera tace "Aa babu komai, ya ciwon kan yayi sauki?" Yace "Alhmdlh, ya su Umma?" Tace "Umma tana gida" Yace "Ku kuna ina?" Tace "Umma ta aiko mu gidansu Aunty Ramlah" Yace "Ohk, yaushe xaku koma gida?" Tace "Karfe biyu xa mu tafi Islamiyya" Yace "Baxa ku dade ba kenan?" Tace "Eh" yace "Toh in xo in maidaku gida?" Ta d'an yi shiru, yace "Kin fa ce kin daina taurin kai" D'an murmushin tayi ta kwantar da kanta jikin kujera dai dai nan suka yi ido hudu da Abuturrab dake xaune dinning area din parlon da laptop gabansa, wani faduwa taji gabanta yayi, Yousuf yace "Kinyi shiru" Ta dago kanta tace "Toh sai ka xo" Yace "Good, in few minutes time xan iso yanxu in sha Allah" Cikin sanyin murya tace "Toh" Katse wayar yayi, ta dinga kallon screen din, can ta saci kallon Abuturrab taga laptop dinsa yake dannawa, ta mike ta wuce part din Ummi, ya bi ta da ido. Karfe daya saura Yousuf ya iso kofar gidansu Abuturrab, ganin xa a tada sallah ya sauka ya shiga masallacin kofar gidan, bayan an idar ya kira number Maimoon, Maimoon ta mika ma Jiddah, Jiddah na kai wa kunne yace "Ina waje ku fito" Jiddah tace "Toh" Katse wayar yayi, suka yi ma Ummi sallama a bedroom dinta sannan suka fita, gaban Maimoon ya fadi ganin Abuturrab da ya fito daga masallaci, amma taki yarda su hada ido, Jiddah kam bata ma gansa ba ta kalli Maimoon tace "Ke da kike son ya xo ya daukemu ai ke xaki yi jagora" Maimoon tace "Don Allah ke dai mu je" Jiddah ta fara tafiya Maimoon na biye da ita, ta bude front seat ta shiga, Maimoon ta shiga baya, sai a sannan Jiddah ta ga Abuturrab da ya tsaya yana kallonsu, Yousuf da ya gansa shi ma yace "Ba yayan nan naku bane wancan" Maimoon ta kirki murmushin

Chapter 30 of 57