rike da makullin motarsa, ya bude mata back seat ta shiga sannan ya shiga maxaunin driver ya tada motar, yayi horn aka bude masa gate ya fita, Hajja tace "Ina gamawa da Bashir kai ma xan samar maka xukekiya mai tsafta kamar Jiddah, ko don saboda ka tsira da lafiyarka" Ta madubi yake kallonta, tace "Kar fa a ga ina ta koda tsaftar wannan yarinya Jiddah wllh tana da shi ne, ni fa na sha gwada in ga ko tsaftar ganin ido take amma wllh ashe ba haka bane, kaga ko shara ka sa ta duk sai ta bi ta dage ko mai ta gani ta share fess, sannan idan ta gyara maka gado sumul sumul kamar kar ka bar kowa ya hau... Sannan naga ta san muhimmancin turaren wutan nan na xamani, tana gama gyaran daki take sakawa, bandaki kuwa da na sa ta ta wanke sai da nayi xaton 6atan hanya nayi da na shiga, wllh har wani talli yake gwanin ban sha'awa, abinda kanninka su Aisha da Nafisah basu da shi, Allah bai basu ba... Toh amma dai ban sani ba ko ganin ido take, idan ma shi din ne dai ai ta iya aikin duk da haka, wasu ma na ganin idon basu iya ba" Abuturrab dai bai ce mata komai ba, har suka shigo Hayi Hajja bata yi shiru ba surutu kawai take a motar, tafiya kawai yake har ya kusa karshen kwalta, ya ga wani d'an gida da aka rushe kusan rabinsa kasancewar a bakin titi yake, har sannan kuma ba a gyara gidan ba don kamar ma anyi abandoning din gidan ne, waje ya nema yayi parking yana kallon wajen rusasshen karamin gidan, can ya kalli Hajja ya nuna mata yace "Ga gidan can Hajja, naga kamar kuma ba kowa yanxu" Hajja ta sauko da sauri tace "Ba kowa kamar yaya? Wannan kuturum gidan ne gidansu Jiddar?" Yace "Ehh" karasawa tayi tana kallon wasu da suka kasa kayan siyarwansu a kasa tace "Ke yarinya ina masu rubabben gidan nan?" Yarinyar tace "Sun tashi tun da aka yi rusau" Hajja ta gwalo ido tace "Suka tashi suka je gidan uban wa?" Yarinyar ta buda hannu alamar bata sani ba, Hajja ta kalli Abuturrab da ya jingina da motarsa ya rungume hannu yana kallonta, tace "Kai kaji wai sun tashi ba a san inda suka je ba" Ya daga kafada shi dai bai ce komai ba, Hajja tace "Yau naga abinda ya isheni, yanxu babu wanda xa mu tambaya me d'an wayo a nan ko an san inda suka koma, ai dole baxa su wuce cikin hayin ba dai tunda dai naga alamar talaucin nasu ba na wasa bane..." Abuturrab yace "An ba ma wani gadinsu ne da xa su fadi inda suke? kinga kawai mu tafi Hajja, ranan nan ya fara damuna..." cike da masifa Hajja tace "In tafi ina banyi abinda ya kawo ni ba, ko wiwi kake sha ne?? kai da xaka tayani mu baxama neman inda iyayen nata suka koma tunda hayin ba wani girman a xo a gani yake da shi ba xaka wani ce mu tafi, wannan wace irin wiwi ka sha" Yace "Toh Allah ya baki sa'an ganinsu, kin xata hayi iyakarsa girman dakin ki ne ko gidan Alhaji Usman" Hajja tace "Atoh ni dama wani xagin naka ne ban saba da shi ba, har ubana dake kabari ka sha xagi kuma in hakura inyi shiru tun kan ma in tafi Masar.... Amma dai ni ba mahaukaciya bace baxan kulaka ba, kuma in sha Allahu ina nan har sai na hadu da iyayen nata sannan in tafi..." Hannu ya sa a aljihu ya ciro dubu daya ya sakala mata a katon jakarta yace "Duk ranan da Allah ya sa kika gansu sai ki dawo gida, ni dai na tafi, kin xata nan Masar din ki ne" Daga haka yayi shigewarsa mota ya wuce, Hajja ta gyara tsayuwa ta bi sa da kallo har yayi nisa. Da sallama Abuturrab ya shigo parlon Abbansa daren ranan, bai yarda ya kalli kowa a parlon ba ya nemi waje ya xauna a kasa sannan yayi gaisuwa, Abba yace "Why did u switch off ur phone?" Ya daga kai a karo na farko ya kalli Abba yace "Wayar ce ta samu matsala" Abba yace "But i told u xa ka raka mu Hayin Rigasa?" Yace "Abba ni ai ban san gidansu ba..." Abba yace "Sai ina ka sani?" Shiru Abuturrab yyi, Abba yace "Wajen mai anguwa?" Abuturrab ya sunkuyar da kansa yace "Eh" Abba yace "Toh gobe lahadi ka taho da safe ka kai mu wajensa" a hankali yace "Toh Abba, Allah ya kai mu" Abba yace "Ameen" D'aga kai yyi ya bi mutanen dake xaune parlon da kallo, sai kuma ya mike yayi sallama ya fita. Bangaren Ummi ya tafi, Ramlah ce kwance kan kujera a parlon Jiddah na xaune daga gefenta hannunta rike da wayar Ramlah tana game, duk suka daga kai suka kallesa, kallo daya ya ma Ramlah sannan ya xauna kan kujera, Jiddah dai bata sake kallonsa ba ta ci gaba da game dinta, Ramlah ta mike xaune da murmushi fuskarta tace "Sannu da xuwa Yaya" Yace "Yauwa" Tace "Ina yini?" Yace "Lafiya" Ta koma ta kwanta tace "Ya Aunty Aneesah?" Yace "Lafiya" Jiddah dai taki yarda ta dago, Yana kallon Ramlah yace "Idan akwai abinci a kitchen ki debo min" Ta kara tashi xaune tace "Toh" sannan ta mike tsaye ta nufi kofa, tunda Jiddah taga haka gabanta ya fara faduwa, tana ganin Ramlah ta bude kofa ta fita ita ma ta mike da sauri, amma tuni ya riga ta mikewa shi ma, tsaye tayi ta marairaice xuciyarta na bugawa tana kallonsa ya karasa gun kofar ya kulle, tana ganin haka ta shige bedroom din Ummi, saboda rudewa ta ma kasa sa makullin ya tura kofar ya shiga, durkushewa tayi kasa har hawaye ya kawo idonta tace "Don girman Allah kayi hakuri ka kyaleni, don Allah nace maka kar su Ummi su shigo...." Dukawa yayi yanda tayi ita ma ta rufe fuskarta da sauri jikinta na rawa tace "Wllh su Ummi xa su iya shigowa yanxu" Ta kusa minti daya a hakan ganin bata ji yace komai ba kuma bai ta6ata ba ta dago a hankali ta kallesa har sannan xuciyarta na bugawa, kallonta taga yana yi ganin yanda kirjinsa yake bugawa ta fara ja baya a hankali tace "Wllh su Ummi xa su iya shigowa" Ya fixgota yace "Aure kike so??" Ta xaro ido jikinta na 6ari tace "Ni bance haka ba" kana ganinta kasan a rude take, yace "Toh me yasa baki ce masu baki so ba?" Ta marairaice masa tace "Don Allah ka bar ni in fita kar su Ummi su shigo su ganmu mu kadai a nan?" Yace "Sai aka yi yaya idan sun ganmu?" Buda baki tayi tana kallonsa ta girgixa masa kai tace "Ai bai kamata ba..." Runtse ido tayi bayan ya kara fixgota har tana jiyo saukan breathing dinsa yace "A wajensu da wajenki ne bai kamata ba...." Rungumeta taji yayi, ita dai har sannan bata bude idonta ba, yanda kirjinsa ke bugawa haka ma nata, taji yayi kasa da murya yace "Tell them u are not interested, tell them...." Sai kuma yayi shiru, haka kawai taji jikinta yayi sanyi ta buda ido a hankali... babu abinda ta gani a lkcn sai ranan farko da ta fito daga cikin gidansu a hayi ta gansa tsaye kofar gidansu ya xo bata hakuri, a hankali ta daga kai ta ga idonsa a rufe suke, hannunta taji ya kamo cikin nasa, ta kalli hannun nasu sannan ta kara daga kai ta kallesa taga har sannan idonsa a rufe suke, lamo tayi jikinsa tana kara jin bugun xuciyarsa, bata san dalilin da ya sa taji hawaye ya taho mata ba, Saukan hawayen nata da ya ji a jikinsa ya sa ya bude idonsa ya kalli fuskarta suka hada ido, ganin hawayen da take yi ya hade goshinsa da nata murya can kasa yace "A ganin ki ina takura ki ko?" Ita dai bata ce komai ba har sannan hawaye na sauka idonta, a hankali yace "I want nothing but the best for u, ban shiga rayuwarki da wata manufa na daban da ya wuce taimakonki da inganta maki rayuwa ba, may be i was mistaken... a lot happened and are still happening..." Shiru yayi sai kuma ya rufe idonsa holding her more closer to him, calmly yace "I don't know.. i was mistaken at many thoughts then... Things turn out the way they weren't suppose to" Xaro ido Jiddah tayi jin an bude kofar parlor ta turasa da karfi, a tare suka mike tsaye, yana kallonta kafin yace komai ta bude kofa ta fice da sauri, Ramlah ce ta shigo parlon da abinci, Ramlah dai sae kallonta take ganinta a bedroom din Ummi, Jiddah ta nufi kofa ta fita don ta ki yarda su hada ido, Ramlah ta xauna kan kujera amma gaba daya kanta ya daure, sae kallon kofar dakin Ummi take, bayan few minutes dai ta mike ta nufi kofar ta bude a hankali, tsaye ta gansa kusa da window staring into space, Ramlah ta yi yake bayan sun hada ido tace "Dama na kawo maka abincin ne Yaya ashe kana ciki" Yace "Ohk" juyawa tayi ta fita, ta koma saman kujera ta xauna a hankali with different thought in her mind. Ummi ce ta shigo dakin tare da Aunty Nafisah, Ummi na kallonta tace "Ikon Allah baku tafi ba, Ahmad din bai xo ba kenan" Ramlah tace "Bae xo ba Ummi" Ummi tace "Abuturrab ya shigo nan ne halan" Ramlah ta nuna mata bedroom alamar yana ciki, Ummi tace "Naji kamshin turarensa ne" Aunty Nafisah tace "Nima magana xan yi kenan kika rigani wllh, idan xan koma tsaraban irin turaren kawai nake so a wajensa" Ummi tayi dariya tace "Lallai kam" a nan parlon duk suka xauna, bayan kusan minti goma Abuturrab ya fito daga dakin, Ummi dai bin sa kawai tayi da kallo, ya xauna saman kujera ya kara gaida Aunty Nafisah, ta amsa tana murmushi tace "Ina Aneesah?" Yace "Tana Lafiya Alhmdlh" Kallon agogon wrist dinsa dake nuna karfe tara saura yayi, ya mike yace "Sai da safe" Ramlah tace "Abincin fa yaya?" Ya kalli abincin da ta ajiye masa yace "Ohk, dare yyi I can't take heavy food now" Ummi tace "Toh tunda hanya ce ya ajiye ku a gida mana, ko lallai sae Ahmad din ya xo" Ramlah tace "Toh shkkn bari mu bi sa" Abuturrab yyi ma Umminsa da Aunty Nafisah sae da safe ya nufi kofa ya fita, Aunty Nafisah tace "Na gansa wani iri, what does that mean?" Ummi ta ta6e baki tace "Ae a haka yake kullum" Aunty Nafisah tace "Haka kuma?" Ummi tace "Dama shi bai da fara'a ae, sannan ba a sanin cikinsa balle kasan me ya damesa" Aunty Nafisah tace "Toh Allah ya kyauta" Ramlah ta dau jakarta da na jiddah tayi ma su Ummi sai da safe, Ummi tace "Jiddar fa?" Ramlah tace "Kilan tana dakin Hajja, can xan je in duba..." Daga haka ta fita, Jiddah na xaune tayi jigum tana ta kallon Hajja dake ta surutanta, amma kusan duk bata ma san abinda Hajja ke cewa ba, Ramlah ta shigo tana kallonta tace "Taso mu tafi Jiddah" Hajja tace "Toh xa ku tafi, Ahmad din ya xo ne?" Ramlah tace "Ehh" Hajja ta tabe baki tace "Shi dai baya ba mutane komai, bakar rowa kamar uwarsa wllh" Ramlah dai ta juya ta fita, Jiddah na kallon Hajja a hankali tace "Sai da safe" Hajja tace "To Allah ya kai mu, ai ni ban san gidan Ramlah kike ba da na dinga kai maku xiyara a kai a kai tunda babu wani babba a gidan, Shi kuma Bashir idan ya aiko wayar xan amsa in ajiye maki, kuma babu shegen da ya isa yace baxa kiyi amfani da shi ba da rai na dai" Murmushi Jiddah ta kirkira ta mike ta fita, sai da ta fara xuwa tayi ma su Ummi sallama sannan ta fito, parlor ta tarda Ramlah na jiranta, ta amshi jakarta a hannun Ramlah sannan suka fita, har suka fita kofar gida babu wanda yace komai cikinsu, Jiddah ta dinga kallon motar da Ramlah ta nufa, lkci daya jikinta yyi sanyi sosai ta bi bayanta walking slowly, back seat Ramlah ta bude ta shiga, a hankali ta kai hannu gaban motar ta bude ta shiga sannan ta kulle, Abuturrab na kallon Ramlah yace "Ke gidanki xa a ajiye ki ai?" Ramlah ta kalli Jiddah da d'an confusion, sai kuma tace "Ohk to shkkn" Jiddah ta xaro ido tana kallonsa sai kuma ta kalli Ramlah, ya tada motar suka bar layin.
*fear Allah and pay for Jiddatul Khair before reading*
Littafin Jiddatul Khair na kudi ne, it's 500 via
3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u show ur evidence of payment via 07087865788... Thank you
It’s S.SQAURE COLLECTION ANNIVERSARY YAYY🎊🎉
Jama’a gawata gagarumar sanarwa ku gyara zama kuji.
S.SQUARE COLLECTION na celebrating 9years anniversary dinsu na fara business, hakan yasa suke bada wata gagaruman discount akan all abubuwan dasuke saidawa, bafa shikenan ba ku gyara zama kuji.
A shagon S.SQAURE COLLECTION zaki samu abubuwa da dama kaman haka;
Hadaddun dinkakkun Gowns wato dogayen riguna.
Lafiyayen Hijab na Eyptia ne, Sudanese ne, Naijeriya ne dasauran su duk sunada shi.
To ina masu baki achan achan irin mu gafa namu nan.
S.SQAURE COLLECTION na saida su Iloka, Gullisuwa, Tsamigaye, Aya, Tuwon madara Dasauran kayan kwalama masu dadi dandano da sanya mutum mantawa da duk wata damuwa tasa! Hehehe badai kun fara gajiya ba danfa ba anan kadai S.SQUARE COLLECTION suka tsaya ba.
Ina matan kamshi dasu Anty turare S.SQAURE COLLECTION also dey for una ooo suna saida Turarukan wuta, Humra, Kulaccam, Turaren tsuguno da Turaren Kaya
Kayan mata kayan saka zakin wajen suma akwaishi
Tsumi, Daka, Gumba,Dasauran maganin mata.
All this abubuwa tanada shi ku garzaya kuci wanan garabasar tasu ta anniversary ta hanyar danna wanan link din dan musu magana direct.
wa.me/+2347030037697
Parking Abuturrab yyi a kofar gidan Ramlah, Ramlah ta bude motar xata sauka, Jiddah ma ta bude xata sauka, Hijab dinta taji ya rike gam daga kasa, ta kallesa da mamaki amma ta ma rasa abinda xata ce, Ramlah ta kulle motar bayan ta sauka tana jiran ganin ko saukowa Jiddah xata yi, Jiddah ta marairaice tana rike da handle din kofar motar murya can kasa tace "Meye haka wai, ka sakeni in sauka mana" Abuturrab ya hada ido da kanwarsa dake tsaye still waiting for Jiddah to come down, a hankali ya sake Hijab din Jiddah ta bude motar ta sauka da sauri, Ramlah ta masa murmushi tace "Sai da safe yaya" Nodding kawai yayi, tuni Jiddah har ta shige cikin gidan, Ramlah ta bi bayanta... Karfe sha daya da wani abu Ramlah na kwance kusa da Ahmad dake operating laptop dinsa, tace "Doctor" ya kalleta yace "Yess dear" Tace "Ina son in maka tambaya ne dama" Ya bar danna laptop din da yake yace "Ina jin ki" Tace "Nasan yaya baya boye maka komai da ya shafi rayuwarsa da dai sauransu..." Murmushi Ahmad yayi yana kallonta, tace "Ka gaya min gaskiya ko da akwai wani alaka tsakanin sa da Jiddah" Yace "Me yasa kika min wannan tambayar?" Ta d'an yi shiru sai kuma tace "Naga wasu abubuwa ne da suka yi confusing dina" Yace "Kamar me?" Ta gyara kwanciya tace "Daxu a can gida muna xaune tare da Jiddah ya shigo yace in je in debo masa abinci, bayan na dawo da abincin sai ban gansu a parlor ba, i dropped the food sai ga Jiddah ta fito daga bedroom din Ummi, she didn't say a word ta fita, i was so surprise bayan few minutes na karasa dakin na gansa shi ma a ciki, sai kuma still daxu ya ajiye mu a gida, xata sauka mota naga ya rike hijab dinta but duk basu san na gani ba" Kallonta kawai Ahmad yake babu ko kiftawa yana sake assimilating din abinda tace, can yace "Sai aka yi yaya?" Tace "I don't know what she told him kuma daga baya naga ya saketa ta sauka motar" Ahmad dae yyi shiru, Ramlah tace "Tun daxu abun ya tsaya min, cause I am confused" Ahmad ya jawo laptop dinsa ya ci gaba da abinda yake, Ramlah tace "Ko akwai wani abu da ake boye mana ne Doctor?" Ahmad yace "I am confused just as u now Ramlah" Ramlah bata kuma cewa komai ba, Bayan few minutes ta mike ta fita dakin, dakin da Jiddah take ta nufa ta bude a hankali tana kallon cikin dakin, kwance ta ganta idonta a lumshe ta lullube da hijab dinta maimakon blanket da ke ajiye gefe, ta fi minti biyu a tsaye har xata juya Jiddah ta bude ido, mikewa xaune Jiddah tayi tace "Kina son wani abu ne?" Ramlah ta sakar mata murmushi tace "Nothing naga baki kashe wuta bane" daga haka ta kashe fitilar dakin ta juya ta fita ta kulle kofar, Jiddah ta lullube har kanta da Hijab din jikinta ta lumshe ido... Karfe daya da rabi na dare Abuturrab na kwance Aneesah na gefensa kamar xata shige jikinsa tana bacci, lumshe ido yyi ya bude, ya mike xaune a hankali being very careful not to wake Aneesah ya sauka kan gadon ya nufi kofa ya fita parlor ya xauna saman kujera ya rike kansa, ya fi minti talatin a nan sai kuma ya mike ya tafi bandaki ya dauro alwala ya fito... Washegari da ciwon kai sosai Abuturrab ya tashi, hakan bai hanasa ya shirya ya fita gida karfe goma ba ya tafi can gidansu, sai da ya jira na kusan minti talatin sannan suka dau hanyar Hayin rigasa da Abbansa, Alhaji Umar, da wani aminin Abban nasa, shi yake driving so absentminded, har suka iso hayi yayi parking dai dai layin Mai anguwa, kasa ce masu komai yayi, shi dai Abba kallonsa kawai yake ganin yayi parking babu wata magana, ya saci kallon Abban nasa, suna hada ido ya bude motar yace "Abba xa mu karasa ciki da kafa babu nisa" Daga haka ya sauka sauran ma duk suka sauka, Xaunawa Abuturrab yyi saman tabarman dake kofar gidan Mai anguwa suka gaisa da mutane biyu dake nan, Abuturrab ya d'an shafa kansa yace "Gun Mai anguwa muka xo" wani matashi yace "Ayya ai bashi da lafiya yau kwanansa uku a shika" Kallonsa Abuturrab ya dinga yi babu ko kiftawa, sai kuma yace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un... Allah ubangiji ya tashi kafadunsa" Suka amsa da Ameen, mikewa yayi yana kallonsu Abba dake tsaye suna jin duk abinda Abuturrab yyi da matasan, Abba da Alhaji Umar da abokinsa suka ma Mai anguwan fatan samun lafiya sannan suka koma gun mota, Abba yace "Allah ya sa hakan shine mafi alkhairi, idan ya samu laifi sai a dawo ayi magana" Shi dai Abuturrab bai ce komai ba ya tada mota tunani iri iri a ransa, gida ya maida su Abba sannan ya karasa bangaren Ummi ya gaisheta, Ko minti uku bai yi a parlon Ummi ba aka bude kofar, Aunty ta shigo tana kallonsa tace "Wato da ni kake gaba a gidan nan ko Aliyu, sai dai ka shigo ka yo bangaren uwarka idan ka gama abinda ya kawoka ka fice kayi tafiyarka, to kayi ta banxa in dai nice wllh, dama uban me kake tsinana ni da shi banda ma ni da nayi tsaye kan lamarinka tun baka kai haka ba, in dan ta ita uwar taka ce ka xata xaka kai matsayin da kake yau?? To wllh kayi da ni Aliyu, kuma ni nasan tsinanniyar da ta shiga tsakanina da kai, nasan musabbabin duk wannan abinda kake min, xa kuma tasan ni er halaq ce...." Tana gama fadin haka ta fita tana huci, Shi dai danna wayarsa kawai yake, Ummi dake dakinta duk tana jiyo Aunty ta ta6e baki ta gama abinda take ta fito, gaisheta yayi bayan ta xauna, ta amsa tace "Akwai wani abun da tayi maka ne wanda ban sani ba take maka gori yanxu?" Yana danna wayarsa yace "Ko daya Ummi, ni babu wani abu da ta ta6a min" Ummi tace "Ohk, to me ya hadaka da ita yanxu baka shiga ka gaisheta?" Yace "Ra'ayi" Tace "Kamar yanda for years kayi ra'ayin dena shigowa gaisheni sai ka ga dama" D'an murmushi yayi yace "Aa Ummi" Tace "Toh Allah ya kyauta" Shi dai bai ce komai ba, tace "Har yanxu kuna samun matsala da Aneesar ne?" Ya kalli Ummi yace "Me kika gani Ummi?" Ummi tace "Sai naga abu xan tambayeka?" Ya girgixa kai yace "Aa Ummi, tana gyarawa yanxu" Ummi tace "Toh gaya min meye damuwarka Aliyu" Ya daga kai yana kallon Umminsa, Ummi tace "Tell me" Yyi kasa da idonsa, sai kuma ya mike ya koma gefenta ya xauna yyi kasa da murya yace "Ummi addu'a kawai nake son ki taya ni da shi" Tace "Baxan yi ba sai ka gaya min me ke faruwa" Yyi shiru ya rasa abinda xai ce, bayan few seconds cikin sanyin murya yace "Ummi , I don't know how everyone is going to take this, but..." sai kuma yayi shiru yana jin xuciyarsa na bugawa, Ummi tace "Bother not... Go ahead tell me what's happening, i might take it softly" ya marairaice mata yace "Might kuma Ummi, you just have to take it softly" tana kallonsa tace "Ina sauraronka" Ya d'an kalli kofa, Ummi na ganin haka ta mike tace "Mu je daki to" Mikewa yayi ya bi bayanta xuwa dakin. Driving Abuturrab yake a hankali har ya isa gida, bayan yayi parking ya sauka motar, baka ta6a fadin wani kalan expression ne a fuskarsa a lkcn, yana shiga parlor Aneesah ta leko daga kitchen tace "Welcome back my Captain" Yace "Thank you" tace "Na gama hada maka kayan, kaje ka duba ko sun yi" yace "Sai nayi sallah" Bandaki dake parlon ya shiga ya dauro alwala ya tafi masallaci don lokaci yayi, Aneesah ta karasa ta dau wayarta dake ringing bayan ya fita, ganin Aunty ke kiranta ta daga ta kai kunne, daga daya bangaren Aunty tace "Kar ki kuskura yayi tafiyar nan baki amshi abin nan ba Aneesah" Aneesah na ci gaba da taunar cingam din bakinta tace "Sai kace ina hauka Aunty, na fa gaya maki yanxu lafiya muke xaune babu komai wllh, duk abinda nace yana yi, girki kuwa kan ya dawo weekend chef salmah ta xo ta min varieties in xuba a deep freezer, sai dai in ciro inyi warming, kuma wllh yana ci yanxu, gida kuma kafin ya dawo nake sa almajirai su shigo har sama da dakinsa su share tsaff, in basu batattun kwanuka ta can bayan gidan su wanke, iyaka in kunna burner in cika turaren wuta... " Aunty tace "Toh kun kara hada shimfida kuwa?" Aneesah tayi wani dariya tace "Na fa ce maki Aunty Safara'u ma ta yo min sako me yawa last week bayan wanda kika kawo min, lafiya lau komai ke tafiya yanxu" Aunty tace "Toh madallah haka nake son ji, ni kuwa kinsan har yau ko xuwa gaisheni a bangarena baya yi, to amma ni nasan tun bayan da ya rabu da tsinanniyar yarinyar nan da naji ana ce ma Jiddah hakan ya faru, duk gaba daya ya canxa min ke kyace ni makiyarsa ce" Aneesah tace "Ikon Allah, to ita Jiddar haka xaki xuba mata ido Aunty??" Aunty tace "Ahaf ashe wasa da ni kike... Anjima dai ina nan shigowa in amshi kudin nan na ranan..." Aneesah tace "Aa Aunty ki bari ko jibi don nasan kafin ya tafi dole xai ban kudi me yawa" Aunty tace "Toh shkkn Allah ya kai mu, xan je anguwa ne dama da yamma, so duk da haka xan biyo din dai" Aunty tace "To sai kin xo" Daga haka ta katse wayar.... Ramlah na kwance parlor da yamma taji sallaman Hajja, mikewa xaune tayi don kofar ma a bude yake tun bayan da Jiddah ta tafi Islamiyya, Hajja ta shigo tace "Sannu, a nan ana ta fama ko, ai uwarki ma lokacin da take da cikin Aliyu haka
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 51 Chapter of 57