min ba, bai ce min xaka sauka a wani waje ba nan ba, nan din ba gidanku bane, sannan ba ga dakin Aliyu ba idan ma bak'in hali Aliyun ke maka ba ga dakin wancan yaron da ya gantale ba Salem yake kowa, ni tunda na xo har yau ban dora ido a kansa ba idan anyi magana sai uwar tace yana benue, tsafin suke koya masa a can din oho mu dai ga mu ga Allah, bikin d'an uwansa guda ma gashi babu alamar xai xo, ni dama a tsorace nake da yaron tun asali" El-Basheer yace "Toh xan dawo" Nafisah tace "Yaya don Allah in bi ka?" Yace "Airport din?" Hajja tace "Ehh mana ku tafi da ita ai yar makaranta ce" El-Basheer yace "Toh idan da mijin Nafisan xamu dauko fa" Hajja tace "Toh ai mijin tun da muka dawo da shi bai koma ba, Nafisar ce kadai ta taho ko yaro daya bata xo da shi ba ta bar ma wata makociyarta balarabiya me kirki, mijinta kuma na Habuja" El-Basheer yace "Ohk" Nafisah na jin dadi ta dau mayafinta, Hajja tace "Toh gaskiya ni bana son kai, idan har xa aje dake sai dai a tafi da wannan yarinya Jiddah itama tunda tare kuke, ita ma kuma ba 6are bace" El-Basheer yace "Toh ta dau mayafinta mu je" Nafisah tace "Amma Hajja kar ya Abuturrab ya koro mu fa" Hajja tace "Xai ko aika, ku mu je gun motar gaba daya" A tare suka fita, suka tadda Aliyu xaune cikin mota yana jiran El-Basheer, ganinsu gaba daya ya daure fuska, Hajja ta bude ma su Nafisah bayan mota, Ita dai Jiddah gabanta sai faduwa yake don mayafi ne ita ma jikinta, kallon mamaki Abuturrab ke masu gaba daya, can yace "Ina xa a kai wa ennnan?" Hajja tace "Usman ne yace a tafi da Nafisah su hadu da takwararta a Iyapot, ni kuma nace a tafi da Jiddah tunda a kan kunnenta aka yi xancen kuma mu bama nuna banbanci a xuri'armu" Abuturrab yace "Aa ni baxanje da kowa ba sai dai El-Basheer yaje ya dauko Aunty Nafisar a Airport" Hajja tace "Amma kasan ina lura da yanda ka raina ubanka, shi fa ya fada bani ba, albarkacin daga bakinsa hakan ya fito ai sai kayi masa biyayya ko ba ta dadin rai ba kayi abinda yace, ba fa goyasu xaka yi ba balle kace aiki aka hadaka da, ko wacce xaunawa xata yi a bayan mota har kuje ku dawo, gaskiya ka sake hali Aliyu, wllh Bashir ba haka yake ba kai dai bar shi da tsokana da mugunta, amma kai wllh kana da bakin hali" Abuturrab yace "Duk naji su sauka kawai" Hajja tace "Allah ya tsine min idan sun sauka, a kira min Usman" El-Basheer dake dariya kasa kasa bayan ya shiga front seat ya kalli Abuturrab yace "Plss let them, it's Abba's instruction" Dama Hajja ko sake kallon Abuturrab bata yi ba tana kallonsu Nafisah tace "Ku shiga kawai" Nafisah ta turo baki ta shiga motar tana kallon yayanta, Jiddah tace "Hajja ni ai kince xan wanke maki bandaki ko?" Hajja tace "Aa wancan me fuskar uwar tata xata wanke min, wato Aisha" Jiddah ta girgixa kai tace "Hajja ni xan wanke kawai su tafi" A fusace Hajja tace "Oo Allah ya ana yabonki sallah sai ki kasa alwala, bayan nabi duk na barbada ma duniya cewar baki da musu kuma yanxu ki nemi karyatani gaban yaran nan??" Jiddah ta sunkuyar da kanta tace "Toh kiyi hakuri" Daga haka ta shiga motar, Hajja tace "Yauwa, ku je Allah ya tsare, idan kinga yalo a hanya ki tuna masu idan sun ga dama sun siya min to" Daga nan ta kulle motar tayi wucewarta ciki tana cewa "Da ban masa haka ba koran min 'ya yan xai yi, gwara ma yayi aure kowa ya huta wllh yaje can su ci kansu da matar ni dai xan dinga kai masu ziyara kawai da d'an rakiya" Tada motar Abuturrab yyi fuska daure ya danna horn mai gadi na bude motar ya fita compound din ya dau hanyar titi, ta madubi El-Basheer ke kallon Jiddah da ya lura she is uncomfortable yace "How is ur studies going Jiddah?" Nafisah ta kalli Jiddah dake gefenta, Tana wasa da gyalenta tace "Alhmdlh" Ya dinga kallonta kafin yace "Hope u are assimilating what u are being taught?" Ta d'an yi murmushi tace "Ehh" ya langwabar da kai yace "Ni ai ba da Hausa na maki ba ko" sake kallonsa tayi suka hada ido, sai kuma tayi murmushi, yace "Do you have any idea of where we are heading to now?" Ta kalli Nafisah dake ta kallonta tana murmushi, Nafisah ta gyada mata kai alamar tayi magana, Shi dai El-Basheer na ta jiran respond dinta, ta d'an kallesa tace "Ka sake fadan abinda kace" Yace "Ohk.. Did u have any idea of where we are heading to now?" Ta d'an kalli Abuturrab da fuskarsa babu yabo bbu fallasa yana kallon titi yana driving, cikin sanyin murya tace "Yes i have" El-Basheer yace "So where are we going to now?" Tace "Hajja said we are going to take Aunty at the...." Sai kuma tayi shiru, ya gyada kai yace "Yess good, ci gaba" Tace "Airport?" Murmushi El-Basheer yayi sosai yace "Ohh yes, Hajja said we are going to pick Aunty Nafisa from the Airport" Ta sunkuyar da kai ita ma tana murmushi, Nafisah dai sai kallonta take, El-Basheer yace "So can you brief me about ur self?" Ta d'an yi shiru sai kuma ta kallesa yace "I am all ears" Tace "My name is Hauwa Jiddah yusuf, i was born and brought up in kaduna hayin rigasa, i lived with my step mum not until..." Da sauri Abuturrab ya kauce ma mai mashin da ya kusa bugewa, Nafisah da taga yanda abun ya faru tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Da mamaki El-Basheer yace "How manage?" Abuturrab ya sauke glass ya ba ma mai mashin din hakuri ya ja motarsa ya kara gaba ba tare da ya tanka kowa ba, El-Basheer yace "Are u sure hankalinka na kan tukin nan Aliyu?" Abuturrab bai tanka sa ba still yana driving din, El-Basheer yace "Toh Allah ya tsare" Maida dubansa yayi kan Jiddah ta madubin gaba yace "Go on Jiddah" tace "I am currently living with Umma at Unguwar Dosa..." Sai kuma tayi shiru, kallonta kawai El-Basheer yake, tayi murmushi tace "Shikenan" Yace "Yea, kinyi kokari sosai Jiddatul Khair, maa sha Allah" Ita ma murmushin tayi tana daga kai suka yi ido hudu da Abuturrab dake kallonta ta madubi, ta sunkuyar da kanta, Nafisah ma duk tana lura da kallon da yake ma Jiddah ta dinga fatan Allah ya sa kada yaje ya sake buge wani kuma. Aunty Nafisah ta rungume takwararta cike da murnan ganinta tace "Haka kika girma Nafisah" Nafisah dake ta washe baki tace "Aunty me yasa baki taho da su Farida ba?" Aunty Nafisah tace "Suna makaranta ne amma in sha Allah xa su xo wani lokacin" Sai a sannan ta kalli Jiddah, Jiddah ta gaisheta da ladabi, Aunty Nafisa ta amsa da fara'a tana kallonsu El-Basheer tace "Wacece?" El-Basheer yace "Yarinyar Umma ce" Aunty Nafisa tace "To madallah" Tuni Abuturrab ya wuce da trolley dinta, duk suka bi bayansa xuwa mota, bayan ya saka jakan a booth ya shiga driver seat, Su ma suka shiga motar sannan ya bar airport din, hira kawai El-Basheer ke yi tare da Aunty Nafisah da ta fita harkan Abuturrab ganin yanda ya tarbeta a airport, shi dai driving dinsa kawai yake, suna fara shigowa gari, Jiddah na kallonsa tunda ita ce setin kujeransa ta d'an matsa, El-Basheer ya kalleta ta gefen ido, a hankali tace "Yaya... Hajja tace a taho mata da Yalo wai" Abuturrab da ya ji ta sarai don setin ears dinsa tayi maganan yyi shiru yana driving dinsa, El-Basheer yace "Kina son wani abu ne Jiddah?" Ta kallesa tace "Aa Hajja ce tace a siyo mata yalo" El-Basheer yace "Ohk idan an gani sai a siya mata" Luckily suka samu yalon El-Basheer yace "Oga ka samu waje kayi parking a siya ma Hajja yalo" Abuturrab yace "Wa ennan rubabbun abubuwan" Daga haka ya ja motarsa ya ki tsayawa, Aunty Nafisah dai bata ce masu komai ba, El-Basheer yayi wani murmushi shi ma bai ce komai ba, sai da suka kusa gida Abuturrab yace "Aunty ya baki taho da zee ba?" Tace "Ban sani ba" Murmushi kawai yayi ya shiga layinsu, a kofar gida yayi parking, El-Basheer ne ya fara sauka, Aunty Nafisah ta sauka, snn Nafisah, Jiddah xata sauka Abuturrab yace "Tsaya" kallonsa tayi, ya hade rai yace "Ke har wani nishadi kike kiyi ta hira da kattin maza kina washe baki don baki da kamun kai koh? To daga yau na sake jin kin wani bude baki kina ma wani turanci xan baki mamaki, sannan ki ci gaba da yawo da kananun gyale" Ita dai kallonsa kawai take, yace "Saukar min a mota" bude motar tayi ta sauka ta wuce cikin gida ya bi ta da kallo.....
Littafin Jiddatul Khair na kudi ne, it's 500 via
3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u show ur evidence of payment via 07087865788... Thank you
Fareeskinglow is a last bus stop do u wanna have a fairer skin or u wanna glow up ur skin here is the last bus stop where u can get ur desired results, a dream of having auniform complexion, glowing skin nd getting rid of any skin problems
Fareeskinglow karshe ne Ina kuke masu son farar fata ko masu son jikin yayi glowing kawai ga dama ta samu fareeskinglow taso muku da kayan gyara jiki fatarki yayi fari tayi sheki duk Wani tabo irin su konewar rana masu zagayen Baki a ido,masu pimples masu fama da combination skin Nan Baki Nan fari Ina mata masu ciki da masu jego wayanda wuyansu ke Baki duk fareeskinglow tazo muku da kayan gyara Wanda zaisa fatarki tayi sulbi da sheki ki komai kamar tarwada
Instagram -fareeskinglow_89
TikTok-fareeskinglow
Facebook page-fareeskinglow
WhatsApp -08031898240
Washegari har karfe goma na safe Abuturrab na dakinsa kwance, babu wanda ya san yana cikin gidan banda Aunty da ta shigo tun karfe takwas wai ya tura ma Aneesah kudin make up, wanda ya tura da farko yayi kadan, babu yanda ya iya haka ya tura kudin, bayan nan kuma bata sake shigowa ba. Goma saura yan mintuna El-Basheer ya shigo gidan tare da Ahmad, don ba gidan ya kwana ba, El-Basheer ya dinga kallon Abuturrab yana 'yar dariya yace "Wannan ai ko kaine amaryar sai haka, ka wani makale a daki tun jiya kamar wanda xa ayi ma auren dole, kamar dai ba Aneesah bace matar" Ahmad yyi murmushi shima yana kallon Abuturrab yace "Captain duk xullumin auren ne ya ramar da kai haka..." Abuturrab yace "Saboda ita ce xata aureni ba nine xan aureta ba ko?" Ahmad yace "Toh wa ya sani, ita dai tana can tana ta sabgar gabanta da kawayenta, kai kuma kana nan ka makale a daki" El-Basheer ya nufi kofa ya fita xuwa dakin Hajja, Hajja na ganinsa tace "Ina Aliyun?" El-Basheer yace "Yana dakinsa" Hajja tace "Dama yana gidan nan?" El-Basheer yace "Yana nan" Ta mike tace "Ni ba ruwana, gida duk jama'a sun cika kilan babu wanda ya bi ta kan ko ya ci abinci ko bai ci ba, ita Ramlah naga sai masu kudi kawai take ma marhaba tayi ta nan nan da su duk ina lura da ita, kaga ai ko shigowa ta tambayeni ko an kawo min kumallo bata yi ba wllh, gwara ma Hauwan ta kawo ma Nafisah da kanta...." El-Basheer ya bi ta da kallo yana murmushi har ta fita sannan ya xauna yana kallon Aunty Nafisah yace "Ina kwana Aunty?" Tace "Lafiya lau Bashir, ashe baka kwana gidan ba" Yace "Ehh yanxu na shigo, ya gajiyan ku" Tace "Gajiya ta bi lafiya, karfe nawa ne daurin auren?" Yace "Sai an sauko Juma'ah in sha Allah" tace "To maa sha Allah" Ahmad ne ya shigo dakin da sallama, Aunty Nafisah tace "Bokan turai ina ta xuba idon ganinka tun jiya ban ganka ba" Yana murmushi yace "Sannu da isowa Aunty, ya hanya" tace "Alhmdlh Ahmad" Hajja na shiga dakin Abuturrab ta tsaya daga bakin kofa tace "Kunga abinda nake gudu ko? Yanxu tun safe babu wanda ya kawo maka kumallo kenan?" Ya d'an kalleta amma bai ce komai ba, tace "Toh ni ba ruwana wllh, wannan ai ba yi bane" Tana fadin haka ta fita, dakin da yan matan gidan suke ta tafi ta bude, bak'i ne kawai a dakin ta gama kare masu kallo tace "Tirrr" sannan ta fita tana girgixa kai tace "Abin dai ba tsari, wa xai yarda da wnn gayyar a Masar, wasu ma rabonka da su ya fi shekara talatin amma suna jin biki xa su taho riiii, ko yar shinkafar suke ma oho" Safiyya ta gani tace "Ke ina Jiddah?" Safiyya tace "Umma ta aikesu da Maimoon can gida" Hajja tace "Toh kije duk yanda xaki yi a kitchen ban sani ba, amma ki samu ruwan xafi da kofi me kyau ki dau kayan tea ki kai ma Aliyu, idan babu burodi ki xo in baki kudi kije ki samo masa, kowa fa ya karya a gidan banda shi don walakanci" Safiyya tace "Toh" daga haka ta wuce kitchen, Hajja to kama dakinta tana mita, Safiyya tayi duk yanda Hajja tace sannan ta kai masa daki, bayan ta gaishesa ta ajiye tray din, yana kallonta yace "Ina su Maimoon?" Tace "Umma ta aikesu" Yace "Ita da wa?" Tace "Jiddah da Nafisah" yace "Xuwa ina?" Tace "Can gida" tsayawa tayi jin bai sake cewa komai ba xata fita yace "Xo ki bani number Maimoon din" Safiyya ta dawo ta amshi wayarsa ta sa masa number Maimoon sannan ta mika masa, ta juya ta fita, dialing number yayi, Maimoon dake compound sun fito tare da Jiddah da Nafisa xasu wuce wajen kwalliya ta xaro ido tana kallon wayarta tace "Dama Ya Aliyu yana da number na, kuma me xai ce min yake kirana..." Dagawa tayi ta kai kunne a hankali tace "Assalamu alaikum" Daga daya bangaren ya amsa yace "Kuna ina?" Tace "Umma ta aiko mu gida" yace "Ke da wa?" Tace "Jiddah da Nafisah" Yace "Yaushe xa ku baro gidan?" Tace "Aa yanxu dai wajen tailor xa mu je amsan kayan da xa mu saka na dinner...." Ta d'an kalli su Jiddah, jin yyi shiru tace "Hello" yace "Ina jin ki, minti nawa xa kuyi wajen tailor din" Ta d'an turo baki tace "Yanxu xa mu dawo dai Yaya, amso kayan kawai xa mu yi" Yace "Toh ku sameni a daki idan kun dawo, gaba dayan ku" Tace "Toh" daga haka ta katse wayar ta ta6e baki tace "Toh me xa mu yi masa xa mu wani samesa a daki, ni ba da ni ba wllh, ko a ina ma ya samu Digit dina" Nafisah tace "Da kince masa ma daga wajen tailor din xamu je gun make up, ni bana son komai da xai hada mu da shi fahh" Maimoon tace "Kyalesa kawai, ba sai ya ganmu ba" Ita dai Jiddah bata ce komai ba har suka fita gate din gidan. Har karfe sha biyu da rabi su Maimoon basu koma gida ba, Abuturrab ya kira numberta sau uku ya ji a kashe, ya kira Nafisah ita ma numberta a kashe, yana xaune dakin Hajja da Ahmad da El-Basheer, dukkansu fararen shadda ne jikinsu xasu tafi masallaci, Ahmad ya kalli Abuturrab bayan ya kalli agogon wrist dinsa yace "Wai da wanda kake jira ne Captain, dubi fa lokaci..." El-Basheer yace "I'm still wondering also, yace mu jira ban san wanda muke jira ba" Hajja tace "Aa gaskiya ku bi sa a hankali, ku baku san duk fargaban aure bane, yanxu fa ana saukowa sallah sai daurin auren..." Abuturrab ya kalleta ta gefen ido ya mike ya fita daga dakin, Hajja tace "Toh Allah ya tsare Aliyu, Allah ubangiji ya sa a daura a sa'a ni dai" Sai bayan da suka shiga mota Abuturrab ya sake kiran Maimoon yaji wayar a kashe still.... Bayan an sauko Juma'ah aka daura aurensa da Aneesah a kan sadaki dubu dari biyu, abokan aikinsa sun masa solidarity sosai don sun samu halartar daurin auren, Ahmad don't want to believe yak'e kawai Captain yake, gaba daya he doesn't look someone happy but he is still smiling as if all is well, suna cikin mota Aneesah ta dinga kiransa yayi silencing wayar ya jefa cikin aljihu, El-Basheer yace "Ya dai da wannan shirun Capt, isn't today ur happy day, u are wedded to the love of ur life..." Captain ya gyara xama a motar yace "Okay saman motar ka so in hau don farin ciki?" Dariya El-Basheer yayi yace "Gaskiya that's what i was expecting, yau dai Aneesah da ka ishemu ta xama matarka" Ahmad dai driving kawai yake bai ce komai ba, El-Basheer yace "Nima Allah ya nuna min ranan da xa a daura min aure da xabin nan na Hajja duk da ban santa ba amma naji har ta kwanta min" Abuturrab ya kara gyara xama bai dai ce komai ba, Ahmad yace "Hajja ta maka wani xabi ne?" El-Basheer yace "Wllh fah, tace ta samar min mata so i will be next in sha Allah" Ahmad yace "A masar?" Dariya El-Basheer yayi yace "Aa nan kasar idan mun je yanxu xan sake tada mata xancen gaskiya don na zaku, yanxu fa ni kadai ne tuxuru cikin ku ko?" Ahmad yace "Atoh, ba dai ka tsaya wasa ba" Abuturrab ya jinginar da kansa da kujera still bai ce masu komai ba yana kallon wajen window. Suna isa gida Abuturrab ya bude motar ya sauka ya wuce ciki yana sake dialing number Maimoon still a kashe, ya wuce bangarensa kawai, Aisha ya kira bayan ya xauna gefen gado, yana fara ring ta daga yace "Maimuna sun dawo?" Tace "Aa suna wajen make up" Yace "A ina ake make up din?" Tace "Ni ban san wanda suka je ba, kasan ba waje daya muka tafi ba" Ya d'an yi shiru sai kuma ya katse wayar, Karfe hudu saura Jiddah suka shigo gida daga wajen make up, da farko taki yarda a mata make up amma sai da su Nafisah suka yi forcing dinta, idan ba sake kallonta kayi ba ma baxa ka ganeta ba, wato tayi kyau ne ba kadan ba duk da ba heavy make up aka mata ba, basu yarda sun sa ankon Dinner din daga can ba, suna shigowa compound suka hadu da Safiyya, Safiyya tace "Ke ina kika sa wayarki ya Aliyu na ta kiranki a kashe" Maimoon ta turo baki tace "Toh wai ma a ina ya samu numberta kuma me yake nemana xan masa?" Daga haka ta kara gaba su Jiddah na ta biye da ita, gud'a da ake ta yi a ciki ne ya tabbatar masu Amarya ta iso, don bayan daurin aure da awa uku aka kawota via flight tunda a kaduna xa ayi dinner din, Mutane ne cike gidan ba masaka tsinke, Maimoon tace "Mu tafi dakin Hajja kawai, kar ma a wani ya aikeni bayan nayi make up" a kulle suka ji kofar an sa makulli, wai ashe amarya na ciki, ga mutane cike bakin kofar dakin, Hajja ta bude kofar duk ta hada xufa cikin ubansun lace din jikinta ga dankunnenta na gwal dake ta sheki a kunnenta, cike da masifa take cewa "Wallahi ba a haka a Masar, mu bama haka a masar, bamu san haka ba a Masar, ita fa wannan amaryar ba ta gwal bace kowa xai ganta idan lokaci yayi, an wani xo an cika min kofar daki kamar ina bada sadaka, ni wllh idan xuciya ta debeni sai in mayar da amaryar tsakar gida yanxun nan, wannan fitina har ina" Maimoon ta dinga rabawa ta gefenta xata shige dakin Hajja ta fincikota tace "Kun ga bala'i ko, wacece wannan kuma" Maimoon tace "Hajja nice fa da su Jiddah don Allah ki bar mu mu shiga yanxu muka dawo" Hajja ta kankance ido tana kare ma Jiddah da Nafisah kallo tace "Shampoo aka ma fuskar ko me?" Maimoon ta shige ciki ta fixgo hannun Jiddah Nafisah ma ta shige dakin sai a sannan Hajja ta kulle kofar da makulli, Aneesah na can karshen dakin saman lallausan rug duk jikinta a lullube har fuskarta, daga gefenta kawayenta hudu ne, Hajja tace "Haba mutanen kasar nan kamar mayu ni Dijee, wllh har na yi adadin shekaruna a Masar ban taba ganin kwatankwancin haka ba, komai a nutse cikin tsari ake yin sa, duk fa rubabbu yan kauye ne suka cika bakin kofar, wani me kudin ne xai wani xo ya tsaya bakin kofa ya tsaya yace sai ya ga amarya kamar wata amaryar gwal, ba gata can na ganta ba sai hasken fata kawai malam, kawayen nata kuma duk bakake ne, kwalliya su ma ni ban gane kanta ba, Ai da sun sani su bari idan sun xo nan sai ku kai su inda aka maku kwalliyan Maimuna, naku yayi kyau sosai har ma ba na jiddah ba, wani ba sai yace ita ce amaryar ba" Maimoon ta dinga kunshe dariyarta, Aunty Nafisah tayi tagumi tana salati a xuciyarta, Ta cikin mayafi Aneesah da ta hade rai take leko Hajja, kawayenta kuwa sai danna waya suke ko wacce fuska a murtuke, Caraf idon Aneesah ya sauka kan Jiddah da ta durkusa jikin kujera, ita bata ma san ita ce jiddar da Hajja ke fadi ba don bata san sunanta ba, amma lkci daya ta gane ta, sosai gabanta ya fadi ta dinga kallonta, Aunty Nafisah ta dau wayarta dake ring ganin Aliyu ke kiranta ta daga, yayi kasa da murya yace "Aunty su Maimunan sun dawo?" Aunty tace "Ehh yanxu suka shigo" Yace "Toh ki turo min su gaba daya yanxu ina mota a kofar gida" Aunty tace "Toh" katse wayar tayi tana kallonsu Maimoon da cikinta ya kada jin ance eh sun dawo, Aunty tace "Wai ku je Aliyu na kiranku kofar gida" Aneesah dai sai binsu take da kallo ta cikin mayafinta, Maimoon ta mike kamar xata yi kuka, Nafisah ma ta tashi suka nufi kofa, ganin Jiddah bata taso ba Maimoon tace "Aunty banda Jiddah yace ne?" Tace "Aa ya dai ce ku je ban san da wa da wa ba" Hajja dake ta fifita duk da fankan dake aiki a dakin tace "Toh me xa su masa har su uku haka, su dai su je, ina ruwansa da wata Jiddah da bata kula kowa a gidan, kilan wani laifin suka masa... Ita dai nasan ba ruwanta tayi xamanta su suje, bata shiga sabgar kowa" Maimoon tace "Laifi kuma Hajja, mu ba abinda muka masa wllh, ko ganinsa ma ban yi ba yau gaba daya" Daga haka ta fice daga dakin tare da Nafisah, ta cikin mutane suka dinga kutsawa har suka fita kofar gida, can suka hango motarsa nesa da gidan, suka nufi motar, ya sauke glass yana kallonsu, suna isa motar Maimoon tace "Yaya ga mu, daxu wayana ya mutu ne sai da na dawo yanxu na jona a dakin Hajja" Yace "Ku nawa ku ka je make up din?" Maimoon tace "Ni da Nafisah da Jiddah" Yace "Ita tafi karfin ta fito ne?" Maimoon tace "Hajja ce ta hanata ta fito wllh" yace "To koma ki kira min ita kuma kar ki fada mata gaban Hajjan" Maimoon tace "Toh" daga haka ta juya da Nafisah suka bar wajen tana sauke ajiyar xuciyar relieve, suna komawa dakin Hajja, Hajja tace "Kiran me yake maku?" Maimoon tace "Aa kawai dai tambaya yayi min" Tana fadin haka ta xauna kusa da Jiddah murya can kasa tace "Yaya Aliyu yace kije" Jidda ta xaro ido tace "Ni kuma?" Maimoon ta cunkuleta tace "Don't allow this old woman to know" Jiddah tayi kasa da murya tace "Tare xa mu je da ku?" Maimoon tace "Aa ni kaya xan sa yanxu, ya gama magana da mu, ke kadai xa ki je" Lkci daya jikin Jiddah yayi sanyi, bata
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 36 Chapter of 57