da ke gida" D'an murmushi tayi tace "Masu dawo da jama'a gida mana" Da ido suka bi motar da ya wuce su, motar yayi parking d'an gaba da nasu, Ahmad ne ya sauko sannan El-Basheer, Abuturrab ya bude back seat ya sauka shi ma, kallo daya yyi ma Jiddah ya nufi gate, El-Basheer ma ya bi bayansa, Ahmad ya karasa ya mika ma Yousuf hannu yana murmushi bayan sun gaisa yace "Ba mu ganka wajen Dinner dinmu ba jiya" Yousuf yace "Yeah naje amma ban dade ba" Ahmad yace "To madallah" sallama suka yi Ahmad ya shiga gidan, Yousuf ya jingina da mota yace "Guys din gidan nan i think suna da karancin ilimin mu'amalah da mutane" Jiddah ta kallesa kawai tayi murmushi yace "Yahhh, that pilot... i don't know but i wont call him an introvert, kawai dai bai san mutuncin d'an Adam bane, and i guess shi ma farin d'an uwansa ne ko?" Jiddah tace "Ehh" yace "Bird of the same feathers" Jiddah dai bata ce masa komai ba, Yousuf yace "Yaushe xaku koma gida da su Umma?" Jiddah tace "Kilan idan an kai amarya da yamma" Yace "Toh Allah ya kai mu, xa mu yi waya with Maimoon's phone" ta gyada masa kai kawai, yace "Take care Jiddah" Ta yi murmushi tace "Nagode" daga haka ya xaga xuwa driver seat ita kuma ta shiga cikin gidan, dakin Hajja ta nufa don dama aiki take mata Yousuf ya kira, tana shiga dakin Hajja dake xuba ma su Ahmad abinci ta daga kai tana kallonta tace "Toh wai saurayinki ne ya xo halan, naji shiru shiru" Jiddah ta nufi kayan da take linke mata don ta karasa, Hajja ta kalli Maimoon dake dakin tace "Halan dai saurayinta ne?" Maimoon tayi dariya tace "Ehh" Hajja tace "Atoh shi kuma baya gaida mutane ne, ai da sai ya shigo ya gaishemu yayi mana Allah ya sanya alkhairi haka ake yi" Jiddah ta ci gaba da linkinta, Hajja ta gama xuba abincin ta mike tace "Toh a kai masu can dakin, idan ba ni ba babu wanda xai masu haka, kowa na ta kansa a gidan" Maimoon ta mike ba tare da ta tsaya gyara plates din abincin kai ba ta dau tray din sai ga plate daya ya rikito kasa, Hajja ta amshe tray din da sauri tace "Je ki Allah ya isa" Wani kallo Maimoon tayi mata tace "Toh na sani ne?" Hajja tace "Nace maki wani abu ne, cewa nayi kije ke da Allah kawai" Maimoon ta fice daga dakin kamar xata tashi sama, Hajja tace "Algunguma kawai, wllh da gangan ta kifar, dama bata yi niyyar xuwa ba, yar mummuna da ita kawai, uban me na hada da ita banda dai uwarta kanwar matar d'a na ne, gayyar tsiya kawai, da a Masar ne dama babu wani dangantaka tsakanina da ita nan ne dai komai sai anyi karere" Ita dai Jiddah linkinta kawai take, Hajja ta sake xuba wani shinkafar tana ta mita, har ta gama sannan ta kalli Jiddah tace "Ki dauka ke ki kai masu, nima na so raina ya baci ne, banda haka ga ki, er arxiki irin albarka" Jiddah ta ajiye xanin hannunta ta karasa ta durkusa a hankali ta dau tray din ta nufi kofa, sai a sannan ta juya tace "A ina xan kai masu?" Hajja tace "Suna can parlon Usman" Jiddah ta fita dakin ta kama hanyar parlon Abba, sai da ta fara ajiye tray din ta murda kofar a hankali hade da sallama sannan ta dau tray din ta shiga ciki, waya na kare kunnen Abuturrab yana magana, El-Basheer kuma na xaune saman kujera idonsa a kan phone dinsa, karasawa ciki tayi ta ajiye tray din tana kallonsu tace "Ina yini" El-Basheer na kallonta da murmushi yace "How are u?" Tace "Lafiya lau" Daga haka ta mike ta nufi kofa El-Basheer yace "Who were u speaking with outside Jiddah" ta juyo tace "Yaya Yousuf ne" El-Basheer yace "Who is he?" Ta d'an yi shiru kafin tace "Family frnd din su Yaya Ahmad" El-Basheer bai kuma cewa komai ba, ta d'an kalli Abuturrab taga yanda ya sha kunu, juyawa tayi ta fice daga parlon. Bayan la'asar aka fara shirye shiryen kai amarya, gidan cike yake dam da jama'a yan kai amarya, motoci sun fi ashirin a compound da kofar gida duk na yan kai amarya, wajen Hajja aka fara kai Aneesah dake sanye da alkyabba fuskarta a rufe, aka xaunar da ita saman carpet Hajja na daga xaune kan tabarma ta daura kafa daya kan daya, tana kallon Aneesah tace "Ni dai bani da abinda xance, amma da a Masar ne kawai ce maki xa ayi ki bi yan uwansa da iyayensa sau da kafa, to sai ki ji dadin xama da shi, duk abinda yake so shine abun sonki.... Kinga dai shi me yan uwane barkatai kuma duk baxa su ki xuwa gidansa ba don haka kika iya allonki ki wanke, ko ni nan duk sanda na ga dama xanje gidansa tunda ni na haifi ubansa kuma a hannuna ya taso daga bisanni ya fita waje koyon tukin jirgin sama..." Aunty dake tsaye daga bakin kofa sai hararan Hajja take kamar ta kifa mata Mari, Aneesah dai sai satan mutanen dake dakin take da kallo duk da fuskarta a rufe yake, Jiddah ta gani xaune gefen gado rike da jakar da Hajja ta bata, ganin kallonta Jiddah ke ta yi ta wani tsuke fuska kamar tana ganinta, ita dai har ranta taji ta tsani jiddah, bata ta6a jin tsanar mutum yanda take ma Jiddah ba, she just hate her with passion, Hajja ta gama surutanta mara tushe aka daga Aneesah dake ta kallon Jiddah har lkcn, aka fitar da ita daga dakin, next aka kai ta gun Ummi, Ummi ma tayi mata duk nasihar da ya kamata, Umma ta daura da nata, daga karshe aka kai ta gun Abba da Uncles din Abuturrab, sai wajen hudu da rabi aka kai amarya mota, Hajja ta saka ma kofarta makulli ta mika ma Jiddah tace "Jefa min a jaka sai Allah ya mana dawowa kuma, mu xa mu kai ta" Saurayin Safiyya ne ya tafi da su Maimoon da Jiddah da safiyyar sai Nafisah gidan Abuturrab, tun da yayi parking out side gate Jiddah ke kallon gidan, kamar bata ra6a rayuwa a gidan nan ba, kofar gidan cike yake da motocin kawo amarya, Maimoon da su Jiddah suka samu suka shiga compound din, Jiddah dai na biye da su a baya har suka shiga parlon, taji gabanta ya fadi, komai na parlon an sauyasa xuwa sabo, jama'a ne cike parlon ana ta gud'a, Maimoon ta ja su Jiddah suka wuce sama, dakin da Jiddah ta xauna ta bude taga few mutane a ciki, kayan dakin ma duk an canza suka fito suka bude sauran dakunan da duk aka xuba ma furnitures, duk da Abuturrab ya sanar ma Aneesah ta gaya ma iyayenta ba a bangarensa xa a xuba mata furnitures din daki ba, taki sanar masu, can kuma suka kai kayan dakinta, Jiddah dai sai kallon parlon Abuturrab take, har sannan hotonsa na kayan pilot na parlon, ta rasa me yasa memory ke ta dawo mata, ba karamin kudi iyayen Aneesah suka kashe mata na kayan daki ba, don duk dakuna hudun dake gidan sun xuba kaya, can karshen gado ta xauna fuskarta a lullube Jiddah dai kallo daya tayi mata ta fita daga dakin ta bar su Maimoon a can ta koma downstairs ta xauna a parlor tana bin ko ina da kallo. Sai kusan karfe shidda aka fara watsewa daga gidan amarya shi ma Hajja ce ta fara sallaman mutane su tafi kada a 6ata ma yarinya gida, gidan ya rage daga Umma, Aunty, Aunty Nafisah da frnds din Ummi, sai wasu family, Jiddah dai sai jiran lkcn da Hajja xata tafi ta bi ta take don taga alamar su Maimoon basu da niyyar tafiya don har Saurayin Safiyya ya wuce, tana ta xaune parlor har magrib hakan yasa ta mike ta shiga bandakin dake parlor tayi alwala ta fito tayi sallah, bayan ta idar ta tafi sama ta bude dakin da take tunanin su Maimoon ke ciki xaune ta gansu suna ta hira, Tace "Wai baxa mu tafi gida bane?" Nafisah tace "Aa mu dai kila ma a nan xa mu kwana" Xaro ido Jiddah tayi, can tace "Toh ga jakar Hajja ni xan tafi" Maimoon tace "Toh wa xai maida ki gidan?" Jiddah tace "Akwai dari biyar din Umma a jakana xan yi amfani da shi" daga haka ta fita, xata sauko downstairs suka kusa cin karo da Aunty sake haurowa sama rike da abinci, sosai gabanta ya fadi ta koma gefe da sauri, Aunty ta kalli downstairs taga babu kowa parlon, fuska murtuke tace "Uban me kika taho yi gidan nan ke kuma?" Jiddah dai ta kasa cewa komai gabanta na faduwa, Aunty tace "To don ubanki sauka ki kama hanyar ki, ke a wa xaki biyo yan kawo amarya, munafuka kawai mayya, nace ke a wa??" Jiddah ta fara sauka a sanyaye, hankadeta Aunty tayi har sai da ta kusa faduwa, cike da tsanarta tace "Maxa fita, ke da gidan nan ai sai dai hange daga nesa" Jiddah bata ce komai ba ta sauka da sauri ta nufi kofa ta fita compound din gaba daya, duk jikinta yayi sanyi, slowly take tafiya a dogon layin wanda ko wani gida da fitilu farare da ya haska layin kamar rana, mota ne ya dallareta ta sunkuyar da kanta tana ci gaba da tafiya a hankali, reverse taga motar na yi yana komawa baya, ta kalli motar don bata ta6a ganin irinsa ba, lkci daya aka sauke glass din motar, ta dinga kallonsa, murmushi ya sakar mata yace "Hi...." Ta fara wasa da hijab din jikinta ta sake satan kallonsa, bude motar taga yyi ya sauka ya xagayo ta inda take yace "Assalamu alaikum" amsawa tayi a hankali, yace "Sorry na tsayar dake a layi ko?" Tace "Um" yace "Kin ganeni kuwa" ta sake kallonsa, d'an murmushi kawai tayi bata ce komai ba, Yace "Ina xa ki da daddaren nan?" Tace "Gida" da mamaki yace "Ba can bane gidan ku dama" ta kalli gidan Abuturrab da yake nuna mata, sai kuma ta girgixa kai tace "Aa, gidan yayanmu ne" Ya wara manyan idanuwansa yace "Ohh, shi yasa na daina ganinki kenan" murmushi tayi masa nan ma, yace "Toh mu je in ajiye ki gidan naku ynxu" Tace "Aa ai ban sanka ba" Yace "Really? Duk sanin da kika min a balcony?" Murmushi tayi tana kallonsa, ya bude mata front seat yana kallonta, sauke idonta tayi ta shiga motar ya kulle sannan ya xaga ya shiga driver seat, reverse yayi suka bar layin yace "Ya sunanki?" A hankali tace "Jiddah" As if counting his words yace "Jeedderh!!" Ta kallesa ya sakar mata murmushi wanda har sai da dimple dinsa ya lotsa ya kai fuskarsa dab da ita yace "I am Ali"
Littafin Jiddatul Khair na kudi ne, it's 500 via
3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u show ur evidence of payment via 07087865788... Thank you
Fareeskinglow is a last bus stop do u wanna have a fairer skin or u wanna glow up ur skin here is the last bus stop where u can get ur desired results, a dream of having auniform complexion, glowing skin nd getting rid of any skin problems
Fareeskinglow karshe ne Ina kuke masu son farar fata ko masu son jikin yayi glowing kawai ga dama ta samu fareeskinglow taso muku da kayan gyara jiki fatarki yayi fari tayi sheki duk Wani tabo irin su konewar rana masu zagayen Baki a ido,masu pimples masu fama da combination skin Nan Baki Nan fari Ina mata masu ciki da masu jego wayanda wuyansu ke Baki duk fareeskinglow tazo muku da kayan gyara Wanda zaisa fatarki tayi sulbi da sheki ki komai kamar tarwada
Instagram -fareeskinglow_89
TikTok-fareeskinglow
Facebook page-fareeskinglow
WhatsApp -08031898240
Jiddah ta sauke idonta daga kallonsa tana sake nanata sunansa a xuciyarta, Aliyu kenan yake nufi, Ali shi ma ai Aliyu ne... muryarsa ya katse tunaninta, taji yace "Wani anguwan xa ki?" Sake kallonsa tayi sannan tace "Malali...." tana fadin haka ta bude jakar hannunta da sauri jin waya na vibrate, sai a sannan ta tuna ai wayar Maimoon na wajenta tun daxu da Yousuf ya kira suka yi magana, ta fiddo wayar tana kallon screen din taga Ya Aliyu... Ta d'an kallesa tace "Nayi mantuwa na taho da wayar yar uwata xan mayar mata cikin gida yanxu" Yace "Ohh ohk, take ur time, bari in ajiye ki bakin gate and i will wait u there okay?" Dai dai gate din gidan Aliyu ya tsaya ta bude motar ta sauka sannan ta shiga compound din tana tafiya a hankali, wayar har ya katse ya sake kira, kafin ta shiga parlor ya sake katsewa, a nan gabanta ya hau faduwa tana tsoron kada ta sake ganin Aunty, da sauri ta wuce sama ta bude dakin da su Maimoon suke, duk suka juya suna kallonta, Maimoon tace "Kin fasa tafiyar kenan" karasawa tayi tace "Na mance na tafi da wayarki ashe a jakata, kuma ana ta kiranki amma dai ya katse.." Maimoon ta xaro ido tana kallon wayar da Jiddah ke mika mata tace "Lahh ashe wayar na gun ki na xata yana caji, wa ke kira?" Lkci daya mood din Maimoon ya canxa ganin me kiranta, cike da damuwa tace "Ni dai na shiga uku, wai ya Aliyu ke kirana, to me yasa?" Dagawa tayi ta kai kunne fuska daure, Kafin tace komai yace "Kuna ina?" Ta turo baki tace "Aa muna nan gidan amarya yaya..." Yace "Ke da wa da wa?" Tace "Ni, Aunty Safiyya, Aunty Ramlah, Nafisah, Aisha da Yusra, sai Jiddah amma ita xata wuce gida ynxu, mu kuma muna son mu kwana ne" murya can kasa tace suna son su kwanan don bata san me xai ce ba, instead sai taji yace "Wacece xata tafi?" Ta kalli Jiddah da har ta nufi kofa ta fita, tace "Jiddah" Yace "Xata tafi ina?" Maimoon tace "Wai gida, tace ita baxata kwana ba" yace "Gidan da babu kowa?" Maimoon tace "Nima dai haka na gani... Amma Ummi na nan ai" Yace "Bata wayar" ta mike da sauri tace "Toh bari in kai mata ta fita yanxu" Yace "Do that quickly" cikin hanxari Maimoon ta fita dai dai second stairs taga Jiddah a tsaye tana kallon parlor, Jiddah da bata ma san Maimoon ta fito daki ba, ta sauke idonta daga kallon da take ma 3 seater din parlon, ta ci gaba da sauka downstairs a hankali, Maimoon ta kwalo mata kira tace "Yaya xai maki magana" Daga haka ta karasa kusa da ita ta mika mata wayar, amsa Jiddah tayi tana kallon screen din sannan ta kai kunne, daga daya bangaren taji yace "Ina xa ki?" Tace "Gida" yace "Toh kar ki kuskura ki fita daga gidan nan ba tare da su Maimoon ba" shiru tayi ta ma rasa abinda xata ce, a takaice yace "Bata wayar" Ta mika ma Maimoon wayar, daga daya bangaren yace "Nafisah dama xan yi ma magana kai mata wayar yanxu" Maimoon tace "Toh" daga haka ta juya ta tafi kai ma Nafisah waya a daki ranta fari tass bai ce su wuce gida ba duk da ta sanar da shi xa su kwana, Gaba daya mood din Jiddah ya canxa, ta ci gaba da sauka a hankali ta nufi kofar parlon ta fita, har sannan Ali na jiranta bakin gate, ta karasa kusa da motar don glass a sauke yake, cikin sanyin murya tace "Kayi hakuri don Allah brother dinmu yace mu kwana a nan kawai" Yace "Ohh really, to shkkn Jiddah, can i get ur digit plss?" Tace "Bana rike waya ae" ya xaro ido yana kallonta, yace "Saboda me?" Sincerely tace "Karatu nake yanxu" kallonta yake yi da kyau, but come to think of her age kamar ynda ya kiyasta a ransa sae ya yrda da abinda tace, ya shafa lallausan gashin kansa yace "Then how will i be contacting u?" Tayi shiru, yace "Amma yar uwarki na da waya ita ai" Tace "Ehh ai ta girmeni" Yace "Ohh ok, gobe da karfe nawa xa ku bar nan?" Tace "Nima dai ban sani ba" Yace "Toh xanyi sallama da safe hope it's okay?" Ta xaro ido tace "Aa idan yayanmu na nan fa" yace "Ohk sai yayi maki fada?" Ta gyada masa kai, shiru yayi, can yace "Okay then xan turo kanwata Khaleesat, she is just ur mate i guess, and kuna yanayi da ita sosai, ranan farko da na ganki a balcony daga nesa sai na ga kamar ita but i know i was mistaken coz tana boarding schl... She is available now sun yi hutu, and i want u two to be frnds..." Tayi murmushin karfin hali tace "Toh" Yace "Let me not keep u standing in sha Allah xata shigo da safe sai ta baki waya mu yi magana okay?" a hankali tace "Allah ya kai mu" murmushinsa me kyau yyi mata ta juya ta shiga compound din gidan, a parlor ta ci karo da Aunty da kawayen Aneesah rike da warmer din abinci iri iri sun fito daga kitchen, Da mamaki Aunty ta tsaya tana kallon Jiddah, can ta ajiye babban warmer din hannunta tana kallon hanyar stairs ta nufota, Jiddah ta fara komawa baya gabanta na faduwa, Aunty na nunata da yatsa tace "Wai ke wacce irin natattciya ce mayya? Ban koreki daga gidan nan ba kika kara dawowa don ubanki, kin ga wani bare a nan banda ke? Duk fa babu bare a gidan nan wllh, Me kika sake dawowa yi banda rashin xuciya don Allah, idan muna abu na family me yasa xaki dinga cusa kanki, wllh tunda nake ban ta6a ganin me naci mara xuciya irinki ba.. ke a wa xaki biyo jama'a xuwa gidan nan idan ba kin yada xuciyarki kare ya lashe ba, bamu hada komai dake ba fa, babu dangin iya balle na baba, yar talakawa dake ma idan ba kaddara ba da kuma Aliyu da ya ja mana wannan masifa da fitina me xai shigo dake irin wannan family din, ke kin ma samu waje ko waiwayon kauyanku baki yi kin shigo birni ko..." Jiddah ta sunkuyar da kanta bata ce komai ba, duk kawayen Aneesah na tsaye parlon suna kallonsu da alamar abun ya masu dadi, Aunty ta bude kofa ta hankadata waje a fusace tace "Fita ki bar gidan nan don uwarki, wllh kika sake dawowa sai na kwara maki tafasasshen ruwan xafi sai dai duk abinda xai faru ya faru" Juyawa Jiddah tayi ta fara tafiya, taji xuciyarta yayi mata rauni sosai, tun da aka fara shirin kai amarya dama tace ita baxata ba amma Hajja tayi ta fada wai ita ma xata fara koyon mugun hali irin nasu Aisha da Maimoon, xata fara yi ma mutane musu da taurin kai, haka ne yasa bata sake cewa komai ba aka shirya da ita aka tafi kai Aneesah, banda wannan bata tashi da intention din bin yan kai amarya ba don karatu ma tayi niyyar yi idan an tafi, da gefen hannunta ta share hawayen da ya gangaro fuskarta me xafi, tana fitowa kofar gida ta nufi titi da kafa, ta fi minti goma a tsaye tana jiran adaidaita sahu kafin ta samu daga karshe, har suka isa gida hankalinta baya jikinta, ta sauka ta basa kudi, snn ta juya xata shiga gate dai dai fitowar Aliyu daga gate din rike da makullin motarsa, kana ganin fuskarta kasan tayi kuka duk da ba me yawa ba, daga sama har kasa yake kallonta, yace "Tafi wajen motata ki jirani" cikin sanyin murya tace "Me xanyi a can? Don Allah ka barni in shiga gida" Yace "Are u questioning me?" Juyawa tayi ta nufi motar walking slowly, har ta isa gun motar ta tsaya, sai a sannan ya nufi motar ya bude back seat yana kallonta, hawaye ya kawo idonta tana kokarin ganin bai xubo ba cikin rawan murya tace "Don Allah ni baxan shiga ba, ka barni in je inyi sallah" Ya dinga kallonta, sai kuma ta juya masa baya ta fara kukan dake cin ta, sai a lkcn maganganun Aunty ke mata xafi sosai a xuciyarta, taji she really wants to go back to Hansai, don ita kadai ce idan tayi mata bata kuka kuma bata Jin xafi a ranta tunda a ko da yaushe kallon mahaifiyarta take mata, ita ta taso ta gani a matsayin baabarta, kuma ita take ma kallon baabarta, Kallonta Abuturrab ya dinga yi cause kana jin yanda take kukan kasan she is hurt, bin wajen yayi da kallo sannan ya kama hannunta ya shigar da ita motar, ta hade kanta da gwiwa tana rera kuka, ya xauna gefenta ya kulle motar yana kallonta yace "Jiddah" kin dagowa tayi, ya dago kanta yace "Me aka maki?" Girgixa masa kai kawai tayi, yace "Aunty ko?" Nan ma ta girgixa masa kai kawai, Tsawa yayi mata yace "Baxa ki bude baki ki min magana ba" ta kuma rushe masa da kuka, ya kamo hannunta yana kallonta, sai kuma ya ciro handkerchief a aljihunsa ya mika mata yace "Clean of those tears..." Bata masa musu ba ta amsa amma bata goge idon ba, ya karbe a hannunta ya fara share mata idon yace "Me Auntyn ta maki?" Taki ce masa komai, bayan few seconds yyi kasa da murya yace "Kiyi hakuri" Kamar jiran jin hakan take ta hade kai da gwiwa ta fara sabon kuka, ya dagota ya hade rai yace "Ba nace kiyi hakuri ba?" Cikin shessheka tace "Dama nace ma Hajja baxan je ba shine ta sa sai naje..." Bai ce mata komai ba sai kallonta yake but he is boiling from inside, mota ce tayi parking dai dai kofar gate aka bude motar Aunty ta sakko da wasu kawayenta suna ta labari, ya dinga kallonsu har suka shige cikin gida, Jiddah taji hankalinta ya tashi ganin Aunty ta dawo gidan, ta marairaice tana kallonsa tace "Don Allah ko xaka kai ni gidan Umma kilan ta koma gida..." Bai ce komai ba ya bude motar ya sauka ta bi sa da ido ya shiga driver seat ya tada motar ya bar layin, a hanya aka yi ta kiran wayarsa, ya daga daga karshe, calmly yace "Kun ga Ahmad ni ba yaro bane da xa a wani jera dani kafin in shiga gidana, this isn't my first marriage, my first marriage ma babu wanda yayi min haka, i went home my self, don haka duk sanda nayi niyyar shiga gida xan shiga, yanxu ina wani sabgar ne..." Ahmad yace "Ohh really?" Abuturrab yace "Yes Ahmad, bana anguwan ma ni" Ahmad yace "To idan kaje gidan sai ka sallami kawayenta..." Abuturrab yace "Sun wahala in dai sallamata suke jira... xa mu yi magana good night" daga haka ya katse wayar, dai dai kofar gidan Umma yayi parking ya kashe motar, Jiddah da taji wani relieve ta bude motar ta sauka tana kallonsa tace "Sai da safe" Daga haka ta shiga gate din gidan ya bi ta da kallo. Gidansa ya wuce daga nan, Aneesah da kawayenta na daki banda complain babu abinda take, Fauziyya tace "Nima ban ta6a ganin haka ba wai kannin ango su wani xo gidan amarya suce xa su kwana ranan da aka kawota, wllh sai kinyi da gaske wajen tattaro hankalin mijinki gaba daya gareki ya share kowa ya daina ganin kowa sai ke, don wnn dangin nasa baxa su bari kiji dadin rayuwar aurenku ba" Aneesah tace "Baxa su bari in ji dadin rayuwar aurena ba??" Wani dariya tayi tace "Lokacin da shigowa gidan nan xae fara gagaransu xan kira in sanar maku, ni fa Captain da ku ke gani nawa ne ni kadai wllh, haka plan din yake dama" Naja tace "Atoh, dama wa xai xauna ya xuba ido, barin ma miji irin naki, wllh kar kiyi sanya Aneesah... Kowa tashi tsaye yake" Aneesah tace "Ni nasan bani da matsala da yan mata tunda nasan wanene captain, nasan root din matsalata a aurenmu
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 39 Chapter of 57