Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ta juya ta bude kofar ta shiga parlon, duk kallonta su Abba suka tsaya yi, ta tsugunna hawaye har ya kawo idonta cikin sanyin murya tace "Abba nagode Allah ya saka da alkhairi" Duk suka amsa mata da Ameen, suka kara sa mata albarka sannan Alhaji Lawal ya umarceta da ta tashi ta wuce, mikewa tayi ta nufi kofa ta bude ta fita ta rufe masu kofar, tsaye ta tadda Abuturrab bakin kofar yana jiranta, ta sunkuyar da kanta, ya fara tafiya, bin bayansa tayi tana tafiya a hankali, babu kowa parlon, ganin xai hau sama ta nemi waje parlon ta xauna, kamar ance ya juya ya ganta ta xauna a parlor, hade rai yayi sosai yana kallonta, ta mike tsaye ita ma tana kallonsa, yace "Xo ki wuce" Ta nufesa gabanta na faduwa, sai da yaga ta kusa iso shi sannan ya fara tafiya, tana biye da shi har suka isa dakin Aunty, Kulle kofar yayi bayan Jiddah ta shigo, Aunty ta tamke fuska ganinta, ya xauna kan stool din gaban mirror yana kallon Aunty a hankali yace "The lady..." Aunty ta wani ta6e baki hade da tafe hannu tana kallon Jiddah, lkci daya ta girgixa kai tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, wllh ka cuci kanka Aliyu, me xaka yi da bagidajiya domin Allah, sai ku ce sai kunyi taimako, taimakon da yanxu idan mutum yayi yake xame masa sharri, to dai ga naka nan ya xamar maka sharri babba, da ajinka, da kyanka, da ilimin ka da kudinka, ina xaka kai wannan fisabilillah? Ina kai ina wannan Aliyu? Wllh wllh banyi baccin kirki a kan lamarin nan ba jiya" Sunkuyar da kai Jiddah tayi har lkcn ta kasa gane kan komai amma duk jikinta yayi sanyi har hawaye ya kawo idonta don saurin kukanta, Abuturrab ya lumshe ido, bai ji dadin maganganun Aunty a lkcn ba, he wish she was even speaking just English at that moment, ya sauke boyayyen ajiyar xuciya yace "U need not to worry Aunty as soon as possible i will find a solution, I've told u everything, you just have to trust me aunt" Yana fadin haka ya mike yana kallon Jiddah kafin yace komai ta juya ta bude kofar ta fita daga dakin, Aunty taji har ranta ta tsani Jiddah, and she will do everything Abuturrab ya datse auren nan balle ma tasan tunda yace xai saketa xai saketa din... Suna fitowa Abuturrab ya fara tafiya, bin bayansa Jiddah tayi a hankali tace "Umma fa?" Ya juyo ya kalleta bai bata amsa ba ya ci gaba da tafiya sai ga Umman ta fito dakin Ummi, ganinsu tace "Yauwa dubawa xanyi dama ko kun fito" Jiddah ta nufeta, Umma tace "To mu shiga ciki" Umma na juyawa Jiddah ta kalli Abuturrab, hararanta yyi ta bi bayan Umma suka shiga parlon Ummi, jingina yyi da bango ya rufe idanuwansa, idan ba avoiding yarinyar nan xai dinga yi ba ko da suna xaune gida dayan ae wataran bubbugeta xai yi a banxa, she is just too dopey for his liking, kwafa yayi ya bude ido ya bar wajen.... Har bayan magrib Jiddah na part din Ummi, a lkcn kuma Umma ta shirya xata wuce don har ta kira Driver, Suna bedroom tare da 'yar uwarta Jiddah kuma na parlor tana kallon tv dake ta aiki, duk ta kagu Umma tace mata su tashi su wuce, duk yan matan gidan kowa ya shigo kallon sama har kasa yake mata sannan ya fita, Ramlah ce kawai ta tsaya suka gaisa, Ummi na kallon Umma tace "Toh ki kara mata fada ni dai kinsan babu abinda xan ce, har yanxu Ramlah i am finding it hard to believe Aliyu is married, ganin abun nake kamar mafarki, i still don't have the courage to start telling this to relatives and frnds, to me ma xance masu Ramlah? Waliman da Uban nasa yace ayi yace baxai yi ba shi, nima dama I'm not in support of that" Umma ta kwantar da murya tace "Yaya kiyi hakuri ki kwantar da hankalin ki, in sha Allah xa mu yi alfahari da wannan auren gaba dayanmu, duk mu yi hakuri mu bar ma Allah komai, Ae Allah ya ga xuciyar mu gaba daya, bama nufin d'an kowa da sharri mu bi su da addu'a kawai" A sanyaye Ummi tace "Ikon Allah, idan wani yace min haka xae ta6a faruwa a household dina baxan yadda ba wllh, duk burin da aka ci a kan bikinsa a haka ya tarwatse??" Umma tace "Haka Allah ya so, ynxu duk abinda Allah ya hore maki sae kiyi mata yaya kinga marainiya ce, nima xan yi nawa, amma kar ki manta da kayan Ramlan don bata da wanda xata sa idan sun tafi yau din" Ummi bata sake cewa komai ba duk jikinta yayi sanyi sosai, Umma tace "Xan sake yi mata nasiha yanxu kafin driver din ya karaso" Daga haka ta fita Ummi ta bi ta da kallo ta girgixa kai tace "Ikon Allah, so all this isn't a dream" Jiddah na ganin Umma hankalinta ya kwanta a tunaninta xa su wuce, ta mike Umma tace "A'a xauna" Xaunawa tayi tana kallon Umma, Umma tace "Abuturrab ae ya maki bayanin komai jiya ko?" Kallonta kawai Jiddah ke yi, can tace "Na me Umma?" Umma tace "Auren ku" a sanyaye Jiddah tace "Ehh yace min an daura min aure da wani, amma wanin xae sakeni sae in dawo wajenki kuma in xauna" Innocently ta fadi hakan tana kallon Umma, Umma ta d'an yi murmushi, lkci daya taji tausayinta ya rufeta, can tace "Bai gaya maki da wanda aka daura maki auren ba?" Jiddah ta girgixa kai tace "Aa bai gaya min ba" Shiru Umma tayi tana tunanin ya kamata tayi breaking mata news din ma kuwa, ajiyar xuciya ta sauke sannan tace "Toh shkkn, d'an xaman da muka yi dake Jiddah naga kina da hakuri da kawaici, sannan kina da hankali, to ki ci gaba a haka kinji, me hakuri shi ke cin riban xaman duniya sannan ki xama me rikon addininki sallah a kan lkci, tsaftar jikin ki, duk ae na nuna maki yanda xa ki dinga yi a gida, kinsan daga inda kika fito Jiddah, ki rike maraicinki, kiyi hakuri a duk halin da kika tsinci kanki" Jiddah ta gyada mata kai lkci daya hawaye ya kawo idonta, abinda Umma bata so kenan duk mutum xai yi hawaye gabanta sae taji xuciyarta ya karaya, tana da rauni sosai, hakan yasa ta mike tace "Drivern ma na kirana ya iso ina jin" Jiddah ta mike da sauri cikin rawan murya tace "Umma ba da ni xa ki koma ba?" Umma ta kasa kallonta tace "Abuturrab xai dawo dake, ae baku yi sallama da Abba ba, Abban na dawowa bayan kunyi sallama xai dawo min dake" Umma na fadin haka ta shiga daki gun yayarta, Jiddah ta bi ta da kallo hawaye me xafi na sauka idonta, ba a dau lkci ba Umma ta fito, murmushi tayi tace "Toh idan baxa ki daina kukan nan ba sae ince ya bar ki nan ki kwana biyu kafin ya dawo min dake" Da sauri ta share hawayenta, Umma tace "Toh ko ke fa, yanxu Abban xae shigo sae Abuturrab din ya dawo dake a motarsa" Gyada mata kai Jiddah tayi, Umma tace "Sae kun karaso" Daga haka ta fita, Jiddah ta koma kasa ta xauna a hankali wasu sabbin hawayen na sauka idonta.... Karfe takwas da few minutes Abuturrab ya shigo parlon, tun tafiyar Umma Jiddah ke ta xaune parlon ita kadai, Ummi kuma na bedroom dinta, kallo daya yayi ma Jiddah ya karasa dakin Umminsa, Jiddah ta shiga saka hannun hijab dinta hoping ynxu xai ce mata ta tashi ya maidata gidan Umma, Abuturrab ya karasa gun Umminsa dake xaune ita kadai dakin, kasa kallonta yayi kansa a kasa yace "Ummi xan wuce" Tace "Allah ya kiyaye" Bai iya yace komai ba, Ummi ta ci gaba da duba littafin hannunta, a hankali yace "Sae da safe" Tace "Allah ya tashemu lafiya, ga akwatin kar ka manta" Ya kalli trolley din ya karasa ya daga ya juya ya fita dakin, yana shigowa parlon ya kalli Jiddah dake jiran taji yace tashi mu tafi yace "Ki shiga kiyi ma Ummi sai da safe" Ba musu ta mike ta shiga dakin Ummi, ta sunkuyar da kai tace "Ummi sae da safe" Ummi ta kalleta tace "Allah ya tashemu lafiya" Juyawa Jiddah tayi ta fita, har sannan Abuturrab na tsaye yana jiran fitowarta, ganin ta fito ya fara tafiya, Bin bayansa tayi har suka fita, ko da wasa bai yi tunanin shiga bangaren stepmom dinsa ba sanin wani maganan da xai bata masa rai xata yi, yana fita su Safiyya da Aisha dake xaune parlor suka dinga kallon jiddah, kofa ya nufa duk suka yi masa sai da safe bbu warce ya tanka cikinsu, Basu ce ma Jiddah ba ita ma bata ce masu ba, a tare duk suka ta6a baki banda Ramlah da ta bi Jiddah da kallo, a booth ya saka trolley din, ya bude driver seat ya shiga ya tada motar, Jiddah dai na tsaye bata ma san inda xata shiga a motar ba, ya wani hade rai ya sauke glass din yana kallonta yace "Rokanki xan yi ki shigo?" A hankali tace "Toh ban san inda xan shiga ba" irin kallon da ya dinga yi mata ya sa ta bude back seat ta shiga ta rufe motar, gaba daya sae taji ta tsorata da shi, amma lkcn da yake xuwa can gidansu ae baya hararanta ko yayi mata ihu haka, sunkuyar da kanta tayi har hawaye ya kawo idonta, yayi horn mai gadi ya bude masa gate ya fita gidan, driving kawai yake amma gaba daya yyi nisa tunanin da yake, wai shi yau xai tafi gidansa da yaki budewa wishing to go in with his wife first, sai gashi da wannan yarinyar xai je, wannan yarinyar fa, tunanin hakan yasa yaji kamar ba a ta6a abinda ya cucesa a rayuwa irin wannan lamarin ba, ya runtse ido ya bude still driving, ae idan ya kwana ma da auren yarinyar nan yau yana da ra'ayin rayuwa tare da ita kenan, Ahmad ne ke ta kiransa tun fitowarsa amma yaki daga wayan haushin kowa kawai yake ji shi yanxu, tafiyar minti talatin da biyar yayi ya isa gidansa dake U dosa, dai dai gate din gidan ya tsaya ya dau makullin gate din ya karasa ya bude gate din sannan ya dawo ya shigar da motar compound din gidan, Jiddah dai sai bin gidan take da kallo don bai yi kama da gidansu Umma ba, sauka yyi motar bayan ya kashe ya karasa ya rufe gate din ya cire makullin ya koma gun motar, ya bude booth ya sauke trolley din, har sannan Jiddah ta ki sauka daga motar, bayan ya rufe booth din ya bude side dinta yana kallonta fuskarsa ba fara'a, sauka tayi tana sake bin gidan da kallo ta kara tabbatarwa ba gidan bane duk da shi ma din gidan sama ne, ta marairaice tana kallonsa tace "Ae ba nan bane gidan" Wani kallo yyi mata ya ja trolley din, bin bayansa tayi da sauri a d'an tsorace tace "Gidan Umman fa??" Ganin har ya shiga parlon ta shiga ita ma ya kunna wuta da ya haska ko ina na parlon, komai na parlon sabo ne, ba kuma karamin haduwa parlon yayi ba, ta dinga bin babban parlon da kallo kamar idanuwanta xa su fito, rufe kofar yayi yasa makulli, sae a sannan ta fashe da kuka a hankali tace "Gidan Umma ae aka ce ka kai ni fa" Biron da ya saka a aljihunsa tun daga gida ya ciro sannan ya wuce sama sanin baxai rasa takarda a bedroom dinsa ba, bin bayansa jiddah tayi hawaye na xuba idonta, ganin hanyar da ya bi bayan ya hau saman ta bi da sauri ita ma don tsoron gidan take, wani kofar da taga ya shiga ta bude taga wani babban parlon hadadde, tsaye tayi bakin kofar gabanta na faduwa, bayan few seconds sae gashi ya fito rike da farar takarda...... Littafin Jiddatul Khair na kudi ne, it's 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u show ur evidence of payment via 07087865788... Do justice to ur self by subscribing before reading.... Thank you Jiddah dai na tsaye bakin kofar parlon tana share hawayen da ya ki tsaya mata, saman kujera Abuturrab ya xauna bayan ya ja center table din parlon right in front of him, ya daura takardan a kai ba tare da ya kalleta ba, babu yabo babu fallasa yace "Shigo ciki..." A hankali ta karaso cikin parlon tana share idonta, ta rakube jikin one sitter din parlon ta tsaya tana kallonsa, daga kai yayi ya kalleta ya nuna mata kujeran alamar ta xauna, ta xamo kasa ta xauna, bayan few seconds, speaking calmly yace "Shekaranjiya na gaya maki an daura maki aure, right?" Jin tayi shiru ya ajiye biron hannunsa yace "Tambayarki nake" Ta gyada masa kai tana kallonsa, yace "Kuma baki san da wanda aka daura maki auren ba ai koh" Nan ma ta gyada masa kai, a takaice yace "Ohkk... Da ni aka daura auren" Kallonsa kawai Jiddah take kamar bata gane abinda yake nufi ba, not minding that ya langwabar da kai yace "Shi yasa kika ji a can gida suna maki nasiha" a hankali Jiddah ta sauke idonta kasa, taji xuciyarta na bugawa da sauri da sauri, yace "Na aure ki ne kawai don ceto rayuwarki daga matar mahaifin ki, na aure ki ne saboda naga xa a cuce ki xa a lalata maki rayuwa, na aureki ba don naje da niyyar yin hakan ba, don haka bani da xabi da ya wuce in sakeki, wannan sakin kuma da xan maki tsakanina dake ne kawai...." Da duk idanuwanta take kallonsa jin furucinsa na karshe, cikin sanyin murya tace "Xaka sakeni?" Yace "Ehh xan sake ki" Ta sunkuyar da kanta bata ce komai ba, shi ma shirun yyi yana kallon hotonsa dake parlon yana sanye da wear dinsa na pilot, muryarta ya ji tace "Idan ka sakeni sai in koma wajensu Umma kenan?" Ya girgixa kai, cikin nutsuwa yace "Aa a nan gidan xaki xauna, kamar yanda na fada maki sakin nan xai kasance sirri tsakaninmu, babu wani da xai san na sake ki...." Tayi shiru bayan few seconds tace "Toh ae ni ba muharramarka bace da xa mu xauna gida daya bayan ka sakeni...." Kallonta ya dinga yi da mamaki jin furucinta ba don shi ta fada ma ba idan wani yace masa ta fadi hakan baxai ta6a yarda ba, can yace "A ina kika san wannan?" Tana wasa da fingers dinta ba tare da ta kallesa ba tace "Lokacin da nake xuwa islamiyya" Surprisingly yake ta kallonta, can yace "Ohh i see... amma kuma basu koyar dake hukuncin wanda ya kashe kansa ba kuma?" Kallonsa Jiddah tayi amma taki cewa komai, ya jefa mata wani shegen kallon da yasa ta koma baya a hankali, idonta har ya fara kawo ruwa, yace "Ke a tunaninki rashin sakin ki kadai ne xai sa mu xauna gida daya kenan, idan ban sakeki ba shine kike muharramata koh?" Shiru tayi bata ce komai ba yace "Bude baki ki bani amsa malama" A hankali tace "Nima ban sani ba" Wani kallo ya sake jefa mata ta sunkuyar da kanta, yace "Xan sakeki kuma xa mu xauna gidan nan tare, don mun xauna gida daya tare ba yana nufin ganina xaki dinga yi ko ganinki xan dinga yi ba, kinsan matsayinki gidan nan, nima haka, balle ma ni daga ranan lahadi da yamma xuwa juma'ah ina wajen aiki, kina tunanin sati da lahadin ma idan na dawo ganina xa ki dinga yi??" Ita dai bata ce masa komai ba, yace "Don haka ki cire tunanin yan kauye dake ranki yanxu, komai kike bukata xan baki waya da xa ki dinga kirana, sannan idan ba abu me ma'ana ba dama kar ki kuskura ki kirani, nan da wani lkci xaki fa islamiyya da boko...." Sai a sannan ta daga kai ta kallesa cikin sanyin murya tace "Toh nagode Allah ya saka da alkhairi" Bai tanka ta ba ya soma rubutu a takardan gabansa, kallonsa kawai Jiddah take babu ko kiftawa, yayi rubutu wanda iyakarsa layi biyu xuwa uku sannan ya dago kai yana kallonta, da sauri ta sauke idonta kasa, yace "kin iya karatu?" A hankali ta girgixa masa kai, sai kuma ta gyada masa kai alamar xata iya, ya mika mata takardan yana kallonta, ta mike ta karasa ta d'an risina ta amsa takardan tana kallo, bayan few seconds ya mika mata hannu alamar ta basa takardan, ta dago kai, hawaye ya gani makale idonta ta mika masa takardan ya amsa sannan ya linke without looking at her yace "Wannan tsakaninmu ne da ke, har abada bance ki sanar ma kowa ba idan ba haka ba......" Daure fuska yyi yana kallonta bayan ya fadi haka, ta gyada masa kai a hankali hawayen idonta ya silalo, mikewa yayi ya linke takardan tsaf sannan ya shiga bedroom dinsa ta bi sa da kallo, ba a dau lkci ba ya fito, kofar fita ya nufa yace "Mu je in nuna maki dakin da xaki xauna" Juyawa tayi cikin sanyin jiki ta bi bayansa, bangaren suka bari gaba daya, ya bude wani daki wanda akwai komai a ciki yana kallonta yace "Ga dakin ki nan, kinga can bangaren nawa ko by mistake, kinsan me nake nufi da by mistake?" Ta girgixa masa kai alamar A'a, yace "Ohk, ina nufin ko bisa kuskure kada ki kai kafarki can, iyakar ki nan dakin, ko parlon kasa idan ina gari bana son kina xama, idan bana nan xaki iya xaman ki can, sai kuma kitchen, komai xan ajiye maki a ciki ki girka duk abinda kike so" Ta gyada masa kai kawai, yace "Yanxu ki tafi kasa jakar nan ki kawo dakin ki, gobe da safe xa mu fita xan siya maki duk abinda xaki bukata, sai ki xaba komai da kanki" Nan ma kai kawai ta gyada masa yace "Kin ci abinci ai a can gida?" Ta gyada masa kai nan ma, yace "Good" downstairs ya nuna mata yace "Tafi ki dauko jakanki, kayan da xaki dinga amfani dasu ne a ciki" Ba musu ta fara sauka kasa, ya bi bayanta suna shigowa parlon ya nufi kofa ya sa makulli, ta dau jakar ta koma sama, kashe wutan parlon yayi, sannan shi ma ya wuce saman, tsaye ya ganta bakin kofar dakin da ya nuna mata, a hankali tace "In shiga?" Ya daure fuska yace "Ehh" Bude kofar tayi kafin ta shiga ciki yace "Gobe karfe takwas xa ki sauko kasa" Ta gyada masa kai, sannan ta shiga dakin ta kulle, ya kashe wutan corridor din ya nufi bangarensa. Bin dakin da kallo Jiddah ta dinga yi, sai take ganin abun kamar a mafarki wai yau ita ce xata kwanta saman wannan katon gadon ita kadai, to ko dai bai ce ta kwanta ba? Kar ta kwanta kuma yace mata don me, a hankali ta kai jakar can jikin bango ta ajiye sannan ta dawo ta xauna kasa tana sake bin dakin da kallo, ta fi minti talatin xaune a kasa, can ta tuna abinda Umma tace mata duk dare kafin ta kwanta ta dinga yin wanka, mikewa tayi tana kallon jakar da yace mata kayan da xata dinga amfani da ne a ciki, ta karasa gun jakar ta kwantar sannan ta bude, tawul ta fara cin karo da sabo, ta ajiye gefe, taga sabulu da soso da Toothpaste and toothbrush, su ma ta ajiye a gefe, sannan taga sabbin undies, da turarruka da mayyuka sai kayan kwalliya, kallon kayayyakin ta dinga yi, lkci daya hawaye ya kawo idonta, xaunawa tayi nan kasa ta hade kai da gwiwa tana shessheka, gani take kamar Hansai xata xo ta haureta ko ta watsa mata ruwa sai ta farka taga duk mafarki kawai take, ta fi minti sha biyar tana kukan kafin ta dago kanta har sannan hawayen yaki tsaya mata, ta dinga share idonta daga bisanni ta mike ta cire Hijab din jikinta, kamar yanda Umma tace mata bata ajiye Hijab din haka ba sai da ta linke, sannan ta soma cire kayan jikinta, ta dau tawul din ta daura ta shiga bandaki, tun daga gidan Umma su Huraira da Maimuna sun nuna mata yanda ake amfani da komai na cikin bayi, cikin kankanin lkci kamar ana koranta tayi wanka ta fito bandakin, bayan ta gama goge jikinta ta dau lotion daya ta bude ta fara shafawa, wani doguwar riga mara nauyi duk da ba na bacci bane ta dauka ta saka, sannan ta maida komai cikin jakar ta rufe ta mayar jikin bango, darduman da ta gani ta shimfida don tayi alwala, ta gabatar da sallan isha sannan ta linke darduman da hijab din ta ajiye, komawa tayi ta rakube ta xauna a kasa, tana ta xaune tana tunani iri iri, taji bacci ya fara fixgarta, tsoron hawa saman gadon take yace tayi laifi, hakan yasa ta dau Hijab dinta ta saka sannan ta kwanta nan kasan tiles ta dukunkune waje daya, nan da nan bacci ya dauketa, sai dai kafin asuba ba karamin wahalar da ita sanyi yayi ba, baccin ma bata yi me dadi ba sbda sanyi da ya isheta, a haka har aka kira sallan asuba, abun ka da wanda ya saba, tun kafin a tada sallah ta tashi ta tafi bandaki ta dauro alwala, da kyar take numfashi sbda hancinta da taji ya toshe, ga ciwo da kanta ke yi, tana xaune saman darduma bayan ta idar da sallah aka bude kofar dakin, da sauri ta juya suka yi ido hudu da shi, sanye yake da jallabiya, ta sunkuyar da kanta, ya rufe kofar ya nufi bangarensa, sai a sannan ta dago kanta jin ya rufe kofar dakin. Har gari ya waye Jiddah na xaune saman darduma sai dai fa babu abinda take, ko d'an azkar din nan babu, kawai sabo da tayi da rashin komawa baccin asuba ne, bakwai saura ta mike ta shiga bandaki ta wanke baki tayi wanka sannan ta fito, wani atamfar ta saka bayan ta shafa mai ta saka turare dai yanda ta ga su Maimuna na yi, tana ta xaune dakin lkci lkci tana duba agogon dake dakin, har taga karfe takwas yayi, mikewa tayi ta dau Hijab ta saka sannan ta nufi kofa ta bude a hankali ta fita, kamar mara gaskiya ta dinga sauka stairs din har ta iso main parlor din, karan Tv ta ji, ta leka parlon ta gansa kwance saman dogon kujera idonsa a lumshe, kasa karasawa tayi cikin parlon, ta fi minti goma a tsaye kamar munafuka, daga karshe ta juya a hankali ta koma saman, xaunawa tayi a kasa ta jinginar da kanta da gado, tana ta xaune a haka har bayan awa kusan daya taji an bude kofar dakinta, da sauri ta juya, suna hada ido ya daure fuska yace "Baki san agogo bane?" Ta kalli agogon dakin dake nuna karfe tara saura mintuna kadan, a hankali tace "Na sauko karfe takwas naga kana bacci shine na koma" da mamaki yake kallonta, can yace "To meye damuwarki da baccina ba ni nace ki sauko lkcn ba?" Ta gyada masa kai, juyawa yayi ya bar bakin kofar, ta mike tana gyara hijab din jikinta ta bi bayansa, xaune ta samesa a parlon ta karasa ta rakube kasa jikin kujera ta xauna yana kallonta daga sama har kasa yace "Babu wani Hijab din ne a jakar?" Tace "Akwai" Yace "To bana son maimaita kaya... Koma ki canxa hijab din" Mikewa tayi ta wuce sama a sanyaye, ba a dau lkci ba sai ga ta ta dawo da wani Hijab din navy blue colour, shi ma har kasa, sosai Hijab din ya haskata kasancewarta fara, ta koma inda take ta xauna ba tare da ta kallesa ba, bayan few minutes yana kallonta yace "A gidanku idan an tashi da safe ba a gaisuwa?" Ta d'an

Chapter 14 of 57