xai biyo baya matar da ba mutunci gareta ba kowa ya san da haka..." Abuturrab ya d'an saci kallon Aneesah, lkci daya ta sake fashewa da kuka tace "Wllh baxan kwana gidanka ba yau Aliyu, ni ai bansan bayan duk hakurin xama da nake da kai a yanda kake akwai wani kalubalen dake tunkaroni ba...." Tana fadin haka ta wuce sama kamar xata tashi sama, Hajja tace "Oho dai Allah ya ishi Jiddah, kai kuma kayi ta istigifari don wnn ba karamin laifi ka aikata ma mahaliccinka ba ya jarabe ka da mata kazama, ni wllh kawai nayi shiru ne amma tun daxu da na shigo parlon nan naji yana wari" Tana fadin haka ta juya ta koma sama, Abuturrab ya d'an yi murmushi, shi dai ya ki tashi har sannan, Aneesah na komawa sama ta saka kayanta ta dau kaya kala biyu a karamin akwatinta ta dau hand bag ta yafe gyalenta ta fito, tana saukowa downstairs bata ko kalli Abuturrab ba ta nufi Kofa, ya bi ta da kallo yace "Ina xaki je Aneesah?" A mugun fusace tace "Wllh baxan kwana gidan nan da tsohuwar nan a ciki ba, baka ce min bayan hakurin da xanyi da kai har ita ma xanyi hakuri da ita ba, sannan ita wannan yar iskar mara asali da ta kawo min gida...." Dakatar da ita yayi yace "Tafi kije, Allah ya tsare" Bude baki tayi tana kallonsa, tace "Kace in tafi inje?" Fuska daure yace "Ehh, sai da safe" Kofa ta nufa fuu ta fice, ko kulle kofar bata yi ba ta nufi gate, ya mike ya karasa kofar ya kulle ya sa makulli. Hajja na komawa daki ta tadda Jiddah kwance ta takure waje daya, Hajja tace "Kiyi hakuri duk ni na ja maki don uwar rikon ki ma da kyar ta amince kika biyoni, ban san gidan er iska xa mu xo ba da ban fara xuwa da ke ba, amma kema wannan simi simin da kike baxai fissheki ba, gwara ki samu kiyi baki ki dinga kwatar kanki, naga kin cika wani sanyi kamar kankara, ai yanxu idan kace xaka yi sanyi sanyi a duniya kullum cikin cutarka ake, da kin gaggasa mata magana kin gaya mata irin kazantarta ai da ta kama kanta amma kin wani taho sama kina kuka kamar er yarinya, ni sai yanxu ma kika bani haushi wllh, da ba don Allah ya takaita aurenku da Aliyun ba ai kishiyarki fa xata xama, to a haka xa ki xauna kina mata kuka kullum??" Jiddah dai tayi shiru bata ce komai ba, har sannan xuciyarta bugawa yake, scene din abinda Abuturrab yayi mata ya ki daina dawo mata, ganin abun yake kamar afresh, Cike da damuwa Hajja tace "To ko dai wani mugun abun ta maki naga duk a firgice kike wllh, ki gaya min gaskiyar me ta maki Jiddah" Jiddah ta lumshe ido ta bude a karo na farko ta bude baki a hankali tace "Bata min komai ba" Hajja tace "Oho dai ita da Allah ni dai na gaya mata duk abinda ya kamata ta sani" Tana fadin haka ta sake fita daga dakin, Jiddah ta ji hawaye ya kawo idonta ta kai hannu bakinta da take jin kamar bai cire nasa ba har sannan, ita idan ba a tv ba bata ta6a sanin ana haka a reality ba ma, hancinta ta kai kayanta jin kamshin turarensa ya cikata, ta wani turo baki ta mike ta fara cire kayan, sai da ta cire tas sannan ta saka hijab ta kwanta tayi lamo saman gadon, scene din da bata so na sake dawo mata kamar a lkcn yake faruwa. Aneesah na xaune parlon kawarta Chef Salma, Salma tace "Kan bala'i!!! to ai ni duk a xancen ki babu abinda ya tsaya min irin yarinyar da kika ce ta biyo kakar tasa... Ita yar kauyen da ya saka ce ake miki sintirin xuwa gidan ki da ita? Sannan kuma ta bi ki da sharri haka? To me hakan ke nufi?" Aneesah ta fyace majina da handki din hannunta tace "Ai shine nake jiran kiran stepmom din tasa, wllh ni rabona da su gaba daya tun xuwansu da rana da nayi shigewata parlonsa, ban ganta ba balle har wani abu ya hadani da ita, amma ban san me taje ta gaya ma makirar tsohuwar ba ta shigo har bangaren mijina tayi min wankin babban bargo ta ci min mutunci" Salma tace "To kuma ai kinyi wauta barin gidan da kika yi, bar masu gidan fa kika yi kenan" Aneesah ta fashe da kuka tace "Captain din fa ce min yayi in tafi sai da safe" Salma tace "Toh ai dadi kakar da ita tsinanniyar yarinyar xa su ji, ke dai wani lkcn idan kinyi wani abun kamar er fari, ke da gidanki kawai ki hado kaya ki bar masu, wato sun ma ci nasara a kanki, sannan karyar da ita yarinyar tayi ma kakar Captain din ya xama gaskiya kenan tunda har kika bar gidan" Aneesah tayi wani murmushi tana girgixa kafa, Salma ta ta6e baki tace "Wllh sakwa sakwan da kike ma wnn pilot din yayi yawa, sai kace shine autan maza? Shi yasa har ya iya budan baki ya maki maganar banxa, banda kilan suna da wani kudurin a ransu meye na xuwa da yarinyar da ya saka gidan tun tale tale? Me ya kawota bayan ga kanninsa da cousins dinsa da xasu iya rako tsohuwar, to wllh ki farka daga wnn slumber din naki kina da aiki ja a gaba, da kyar idan ba sake cusa masa me dankali da doyan xa su yi ba" Aneesah ta sakko da kafarta daga saman kujera da sauri alamar xancen ya gigitata tana kallon Salma, er dariya tayi tace "Ka ji ki da wani xance, to babu wani aure tsakaninsu sai in ta sake wani auren, ya mata saki sau uku kenan, daya a lkcn auren na farko farko, sannan suna tare ma ya saketa, sai na karshen da Abbansa ya umarcesa da ya saketa kuma ya saketa din" Salma tace "Ke wa ya gaya maki haka?" Ta gyara xama tace "Aunty, kuma Aunty Safara'u ma taje wani waje haka aka ce mata babu aure tsakaninsu har abada, don haka mu kwantar da hankalinmu, balle ma captain ba class dinta bane shi ma ya sha fada, me xai ci da ita?? yar hayin rigasa ce fa bama birnin hayi ba kauyen hayi, ko numfashinta baxai so ya shakka ba balle wani abu ya hadasu" Salma tace "To har naji hankalina ya kwanta maki, da kika ce babu auren, amma duk da haka sai kin taka burki a daina taho maki da ita gida gaskiya, ba fa dangin iya ba na baba" Aneesah tace "Ita kanta tsohuwar xuwanta na farko da na karshe kenan tayi idan anyi duniya don manzon Allah, wllh ko da kudi aka hadota ta taho gidan Aliyu baxata sake xuwa ba" Salma tace "Yauwa, haka nake son ji dama, ki tashi xaune daga kwancen da kike wllh... Yanxu kowa ta kansa yake duk inda kika ji ance aiki na kyau ki cire kyashin kudi kije" Aneesah ta jawo wayarta ta daga ganin Aunty ke kiranta ta kai kunne da sauri, kuka ta sakar mata, nan kuma ta bata labarin duk abinda ya faru, Aunty da ta kakance idonta tace "Kina nufin tare da shegiyar taje maki gida?" Aneesah tace "Wllh kuwa" Aunty tace "Toh ke banda shashanci meye na barin gidan, wato Hajjar taji dadi kenan ma kin bar masu gidan" Aneesah tace "Aa wllh Aunty ni baxan iya xama ba suna ci mun mutunci kuma babu abinda Aliyun yace, sannan da kansa yace in tafi" Aunty tace "Toh abinda xai faru yanxu ki dauko jakar taki ki taho nan gida, Abbansa na gari ai, maza ki taho yanzu, kuma wajen maida magana duk ki san abubuwan da xaki kara a xancen, ai in sun san wata basu san wata ba" Aneesah tace "Toh" Aunty tace "Wai ya ma baki wannan kudin kuwa?" Aneesah ta tabe baki tace "Ina fa, ce min yayi sai sabon wata da xa a shiga..." Aunty tace "Anya Aneesah kinyi amfani da maganin karshen da na baki a daren ku na farko kuwa?" Aneesah tace "Aunty sai dai na xo gidan, yanxu xan fito dama gidan Salmah na taho" Aunty tace "To na gane, taho gidan maxa yanxu" Driver Salmah ta saka ya kai Aneesah can gidansu Abuturrab. Har wajen karfe sha daya Abuturrab na xaune downstairs tare da Hajja da babu irin labarin Masar da bata masa ba, with much interest yake sauraronta yake biyeta duk da labarin ba dadi yake masa ba, ya gyara xama yana kallon agogo yace "To ai nan ma akwai turarruka masu kamshi ba can kadai ba" Hajja tace "Inaaa har yau banji turare me kamshi irin ta Masar ba, akwai wani turare da Usman ya bani wai dubu hamsin ya siya ni dai yana can na jefa cikin kwambodi.... to ba kamshi" Yace "Toh bari in dauko maki wani turarena yanxu ki ji kamshinsa ko ya kai na Masar din" Mikewa yayi yace "Ki jirani yanxu in dauko maki" Hajja tace "Toh yi maza, kaga idan kamshin ya min sai ka bar min kawai" Yace "Ba damuwa" Daga haka ya haura sama, gently ya murda kofar dakin ya bude, kwance take saman gadon ta rufe duk jikinta da hijab dinta idonta a lumshe, ya karasa cikin dakin ya kulle kofar, kallon switch din dakin yayi kafin ya nufeta walking slowly ya tsaya kusa da gadon yana kallonta, ya kalli kayanta da ta linke ta ajiye sannan ya kara kallonta, daga hijab din da ta lullube jikinta yyi yaga babu abinda ke jikinta sai undies, lkci daya ya sake hijab din ya juya ya fita dakin ya tafi bangarensa yana shiga bedroom dinsa ya kashe wutan dakin ya fada saman gado yayi rub da ciki. Hajja ta gaji da xama, ta sha gyangyadinta har ta gode Allah sannan ta mike wajen karfe daya ta wuce sama tana cewa "Gantalallen ba sai yace min bacci yake ji ba sai da safe, me hali dai baya fasa halinsa kawai..." Tana bude kofar daki taga Jiddah durkushe kusa da gado ta hade kanta da gadon, Hajja tace "Meye haka?" Ta dago da kyar tana kallonta ta girgixa mata kai, a fusace Hajja tace "To meye kika wani rungume gado kamar me nakuda?" Jiddah dai ta kasa ce mata komai, Hajja tace "A gaskiya da na sani baki biyoni ba, daga abun arxiki? Me ya sameki?" Jiddah ta kara girgixa mata kai kawai, Tabe baki Hajja tayi ta Kashe wutan dakin tace "Baxan iya da wahalanki ba bacci xanyi wllh, babu wanda xai shiga hakkin bacci na" Tana fadin haka ta kwanta daga kwanciya kuma sai minshari, Jiddah tayi ta juye juye... tun tana daurewa har ta kasa ta dinga hawaye tana yarfe hannu, rabonta da irin ciwon nan da take ji yanxu tun tana gun Babaarta, har karfe biyu Jiddah na durkushe yanda take, da ya lafa mata sai ya fara kuma... Shesshekarta ya farkar da Hajja, Hajja ta mike xaune sai kuma ta tashi ta kunna wutan dakin, xaro ido tayi ta kalli agogo ta kalli Jiddah sannan ta bude kofa ta fice, bangaren Aliyu ta nufa ta buga kofa, Abuturrab dake xaune saman kujera a parlon ya rike kansa ya juya da sauri yana kallon kofar, Hajja ta sake bugawa, xai mike daga kan kujeran yayi kicking ruwan Lipton din lemun tsami dake cup a ajiye daga kasa kusa da shi, lkci daya ya malale saman carpet din parlon, tsallakewa yyi ya nufi kofar ya bude, cikin tashin hankali Hajja tace "Aliyu awa uku kenan wancan yarinyar bata ko rintsa ba, sai kuka take na rasa me ke damunta, ni fa tsorona Allah tsorona tijaran da Ramlah xata min a kanta" Da mamaki yace "Me ya sameta?" Hajja tace "Ina xan sani Aliyu ko kwanciya taki yi, tana can duke kamar me nakuda nayi nayi ta gaya min meye taki" Abuturrab yace "Ina xuwa" Daga haka ya koma daki ya dau jallabiyarsa ya saka sannan ya fito, yana gaba Hajja na biye da shi suka isa dakin, Yana bude kofar dakin suka ganta durkushe kofar bandaki tana kwarara amai, Hajja tace "Na shiga uku ni Dije ta kashe bandakin, wani aman arxiki ne baxa ta shiga can ciki ba sae a bakin kofa?? Tirrrrr" Abuturrab ya karasa da sauri ya duka kusa da ita yace "What's wrong with u?" Ta kasa basa amsa ya dagata xuwa cikin bandakin, Hajja ta fice daga dakin hankali tashe tace "Baxan iya ba wllh, ko ni ya na kare da nawa aman balle na wani..." Abuturrab ya wanke mata fuskarta bayan ya xuba ruwa gun aman, xai cire mata Hijab din jikinta ta rike gam tana xaro ido amma taki yarda ta kallesa, hade rai yayi yace "Cire hannunki" Da kyar cikin kuka tace masa "Aa bana so wllh" lkci daya ya fixge hijab din a jikinta da karfi, ta turasa ta durkusa a kasa hankali a tashe tana cewa "Wayyo na shiga uku don girman Allah ka bani hijabina ka fita" Yana kallon ko ina na jikinta yace "Me yake damunki?" Duk a gigice take tace "Ai naji sauki" Yace "Saukin me" Taki yarda ta kallesa tace "Don girman Allah kayi hakuri ka fita" Sai kuma ta fashe da matsanancin kuka tana kara rufe jikinta, shi dai kallonta kawai yake, can ya d'an shafa kansa ya ajiye mata hijab din saman washing machine ya juya ya fita bandakin, banda rawa babu abinda jikinta yake, tun da take bata ta6a ganin irin wannan iskanci ba, ko a gaban mace bata ta6a tsayawa a yanda take yanxu ba, gaba daya ta nemi ciwon cikin da take ta rasa, ta kalli jikinta ta kara takurewa waje daya xuciyarta na bugawa, ta fi minti biyar a haka kafin ta mike da sauri ta figi hijab dinta ta saka gabanta na faduwa, ta makale jikin kofa sannan ta leka dakin a hankali, ido hudu tayi da shi yana tsaye har lkcn a dakin, da karfi tayi banging kofar bandakin ta sa makulli, ganin haka ya shafa kansa ya juya ya fita, xaune yaga Hajja a corridor din ta shimfida darduma sai xuba gyangyadi take, yayi mata kallo daya ya wuce bangarensa, throughout daren nan Abuturrab bai rintsa ba, banda juye juye babu abinda yake, idan ya gajiya da kwanciyar saman gadon ya koma kujera a parlor, har aka kira sallah. Karfe takwas Jiddah ta lallaba ta saka kayanta da Hijab tana kallon Hajja dake kwance kan darduma tana bacci, ta dau jakarta ta nufi kofa a hankali ta bude ta fita, kallon direction din bangaren Abuturrab tayi kafin ta sauka downstairs da sauri, mai gadi ne ya bude mata gate ta fice fittt daga gidan....
Littafin Jiddatul Khair na kudi ne, it's 500 via
3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u show ur evidence of payment via 07087865788... Thank you
Fareeskinglow is a last bus stop do u wanna have a fairer skin or u wanna glow up ur skin here is the last bus stop where u can get ur desired results, a dream of having auniform complexion, glowing skin nd getting rid of any skin problems
Fareeskinglow karshe ne Ina kuke masu son farar fata ko masu son jikin yayi glowing kawai ga dama ta samu fareeskinglow taso muku da kayan gyara jiki fatarki yayi fari tayi sheki duk Wani tabo irin su konewar rana masu zagayen Baki a ido,masu pimples masu fama da combination skin Nan Baki Nan fari Ina mata masu ciki da masu jego wayanda wuyansu ke Baki duk fareeskinglow tazo muku da kayan gyara Wanda zaisa fatarki tayi sulbi da sheki ki komai kamar tarwada
Instagram -fareeskinglow_89
TikTok-fareeskinglow
Facebook page-fareeskinglow
WhatsApp -08031898240
Har Jiddah ta isa bakin titi waigen layin take xuciyarta na bugawa, tana ta tsaye har ta samu adaidaita ta hau ta gaya masa inda xai kai ta, dai dai kofar gidan Umma mai adaidaita sahun yayi parking ta sauka ta ciro kudin da Umma ta bata jiya a jaka ta mika masa, ya bata canji sannan ta shiga cikin gidan... Babu kowa parlon don su Maimoon sun tafi Islamiyya, ta karasa kitchen don gaida Huraira dake aiki a ciki, Huraira tace "Dama Umma tace sai yau xaki dawo da aka ji shiru har dare jiya" Jiddah ta d'an yi murmushi kawai tace "Umma bata tashi ba?" Huraira tace "Bata tashi ba ko" Juyawa Jiddah tayi ta wuce dakinsu, sai da ta fara shiga bandaki ta wanke baki tayi wanka ta fito ta shirya cikin doguwar riga bayan ta gama shafe shafenta sannan ta kwanta, da ta runtse ido abinda Abuturrab yayi mata kawai take gani, tana ganin hakan kuma sai gabanta ya fadi, ita har yanxu ganin lamarin take kamar a mafarki, da yake bata wani samu baccin kirki daren jiya ba nan da nan bacci me nauyi ya dauketa. Karfe sha daya saura Umma ta fito daga dakinta ta dalilin kiranta da Huraira taje tayi wai tayi bakuwa, Tsaye taga Hajja a parlon sai hura hanci take, Umma ta karaso tana kallonta tace "Lafiya Hajja?? sannun da xuwa" Hajja ta dakatar da ita tayi mici mici da ido tace "Jiddah ta dawo??" Umma ta kalli Huraira dake bayan kujera a tsaye, Huraira tace "Ehh ta dawo tun daxu amma tana daki tana bacci" Umma ta kalli Hajja, Hajja ta rushe da kuka ta nemi kujera ta xauna tace "Toh a gaskiya Allah ya isa, wannan daga min hankali da tayi taje don kanta, idan kuma ke kika koya mata hakan kema kije don kanki... Kuma ni ban san haka take ba da ban fara xura jiki ina kulata tun farko ba, ashe su Maimu da Aisha kananun yan iska ne a inda wannan yarinya jiddah take ban sani ba?? Amma ba komai nasan duk karatunki ne ta dauka ba wani abu ba" tana fadin haka ta fyace hanci, Umma da ranta ya gama baci tace "Kawai sai in xaunar da ita don rashin aikin yi ince ta baro gidan da ku ka je da sassafe ko Hajja??" A fusace Hajja tace "Oho... Xaki aika wllh, waye bai sanki da halinki ba? dama kuma da ya kika bari ta bini, bai sai da na hadaki Allah... annabi ba?? ni dai ai na gode Allah da ta dawo gida lafiya abu bai sameta a hanya ba balle hukuma su garkameni ko jikana, wai kawai ina farkawa daga bacci barawon da ya sace ni da asuba sai naga daki wayam babu mata babu dalilinta, ban kawo komai a rai ba ina ta jan carbi har kusan karfe tara, nace kai bari dai in sauka in duba ko kumallo take nema mana a kitchen, ina sauka naga gidan wayam babu ita babu isilinta, na duba inda takalmanmu suke naga ai babu nata sai nawo kwallin kwal kamar maye, da gudu na koma sama na taso wancan mutumi Aliyu shi ma dai ya fito muka yi ta bulayin neman yarinya a cikin gidan, banda kuka da rokon Allah ya taimakeni babu abinda nake a lkcn, daga karshe ya bada shawaran mu taho nan kilan ta dawo, shine fa na taho ko wanka banyi ba yanxu haka, abinda ban ta6a yi ba a Masar, gudun fitinarki ma gashi can yaki shigowa yana can xaune cikin mota, to yana da gaskiya mana tunda bai san ko yarinyar ta dawo ko bata dawo ba, daga ni har shi sai ki iya sa a garkame mu kadan da aikin ki" Umma ta kalli Huraira tace "Kira min Jiddah" Huraira ta tafi daki, a durkushe taga Jiddah ta daura kanta saman gado idonta lumshe, baccin ma gaba daya ba me dadi tayi ba banda mafarkan Abuturrab babu abinda take, ga ciwon ciki da ya matsa mata, Huraira tace "Lafiya Jiddah" Da sauri ta bude idonta sai kuma ta dago kanta daga saman gadon ta nuna mata cikinta alamar yana mata ciwo, Huraira tace "Subhanallah sannu kinji, xaki iya fitowa kuwa, Umma na kiranki" Jiddah ta daure ta mike ta dau hularta ta saka sannan ta fito parlor, wani kallo Hajja ta dinga mata daga sama har kasa, Jiddah ta kasa kallonta ta karaso parlon ta durkusa, a hankali tace "Ina kwana Umma" Umma tace "Lafiya lau, why did u leave without telling anyone?" Jiddah ta girgixa mata kai kawai bata ce komai ba, Umma tace "Ki bude baki kiyi min magana" a hankali tace "Umma cikina ke min ciwo" Hajja tace "Kaji sharri?? Dama ba gari muke jira ya waye a kai ki asibiti ba? in ni kina tunanin tsohuwar banxa ce don me baki sanar ma me gidan cewar xaki koma gidanku ba xaki tafi ki bar xuciyoyin mu a gantale da fargaba??" Umma tace "To ayi hakuri Hajja, Allah ya huci xuciyarki" Hajja tace "Aa bbu ruwana wllh, sai kinga tijaran da nayi ma matar gidan a kanta jiya, shine ni xata watsa min kasa a ido?" Umma da mitan ya fara isarta tace "Toh ke yanxu ya kike son ayi Hajja? Komawa gidan xa kiyi tare da ita yanxu?" Jiddah da taji gabanta yayi wani irin faduwa ta fashe da kuka ba tare da ta shirya ba tace "Wllh cikina ciwo yake min Umma" Hajja ta rike ha6a tana kallon Umma tace "In koma ina da ita? Matar da ta kashe mana baccin jiya duk a xaxxaune muka kwana a gidan kamar almajirai, aa tunda ta dawo gida lafiya Alhmdlhi, nima xuwa xanyi ya ajiyeni a gida ashe matar gidan yaji tayi daga jin mun xo, to ni ina na sani, sai yau da safe yake gaya min" Umma dai tace "To Allah ya kyauta, kiyi hakuri Hajja" Hajja ta juya ta nufi kofa tace "D'an ba kara, tunda dai ta dawo xan turo Aliyun ya shigo ya gaisheki mu san inda dare ya mana" Mikewa Jiddah tayi ta wuce daki kamar warce aka tsikara jin xancen Hajja na karshe, Umma ta bi ta da kallo, Hajja na fita kofar gida tana kallon Abuturrab dake xaune cikin motarsa tace "So tayi ta tona mana asiri Allah bai yi ba, gata can munafukar tana ciki, ka shiga kawai ka gaida uwarka muyi ta kanmu, mu dai ba ta dawo gidan lfya ba Alhmdlh" Abuturrab yace "Ke kin ganta a ciki?" Hajja tace "To da fa? Wai sai ta fashe da kukan munafurci daga Uwar tace mu koma tare, bata san nima ta sire min ba baxan sake xuwa da ita ko ina ba, har abada kuwa, jiya kaga abinda dai ta dinga mana cikin dare kamar me cikin wata tara" Abuturrab ya shafa kansa yace "To shigo mu tafi" Hajja tace "Aa rufa min asiri so kake Ramlah tayi dani idan mun tafi tace na hanaka shiga ka gaisheta?? Kaje ko minti daya ne ka gaisheta ka fito kawai" Bude motar Abuturrab yyi ya sauka, Hajja tace "Kayi maxa ina jiranka" Umma na xaune parlon tana ma Jiddah dake xaune kasa kusa da ita magana a kan me yasa xata bar gidan da sassafe, ita dai Jiddah bata ce komai, Abuturrab yyi sallama bakin kofa, sosai gabanta ya fadi tayi kasa da kanta kamar me neman allura a kasan, Shi ma tun da ya kalli inda take sau daya bai sake kallo ba, ya dai karaso parlon ya xauna saman kujera yace "Ina kwana Umma" Umma tace "Lafiya lau, an tashi lafiya" Yace "Alhmdlh, ya gida" Tace "Lafiya lau" Kamar yanda Jiddah taki dago kanta shi ma haka ya ki kallon inda take, Bayan few seconds yace "Hajja na jira na Umma" Umma tace "Toh Allah ya tsare" mikewa yayi yace mata sai anjima sannan ya nufi kofa, Jiddah dai taki dagowa ko da wasa, Umma sai kallonta take kamar dai tana son gano wani abu, bayan fitar Abuturrab tace "Me ya sameki jiya da daddare a can gidan?" A hankali Jiddah tace "Ciwon ciki nake yi?" Umma tace "Ikon Allah, amma da sauki yanxu?" Tace "Idan yayi min sauki sai ya fara kuma" Umma tace "Toh Allah ya sauwake bari anjima Ahmad ya xo sai ya
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 45 Chapter of 57