da kai Fahad, yau muka gama magana da Abba akan na maka magana muje mu nemo Maleeka duk inda take, sun yafe mata sun gano qarya aka mata, ashe ba qarya bane gaskiya ne, dole ne na koma a daren nan na sanar dasu ba zan iya bari sai gobe ba,"
Juyawa yayi a sukwane zai fita Fahad ya riqe shi,
"A kwance ka gan mu da kk ikirarin tabbatar da mu maciya amana ne? Ko kuma a jikina ka gan ta? Ko me ya baka tabbacin na ci amanar ka baya, ba wanda ya bamu damar yin bayani aka yanke mana hukunci, a yanzu ma so kk ka yanke hukunci cikn fushi? To bismillah, ka je ka fada masu, Allah baya barin qarya ta zama a sama, zai bayyana gaskiyar mu,"
"Basshi ya tafi, ko ba komai ni na san wannan karon ba zan bar kalaman kowa su haye nawa ba, ina da baki, kuma nayi wayon da ba ba zan zauna a na qaga min maganar da ba ita kenan ba,"
"Ki min shiru maciyiyyiya amana kawai, uban wa y baku izinin dakkon yara? Kun sa na kulle mutanen da ba su suka daukar min yara ba, ku ban yarana na wuce da su kar ku koya masu zaman iskancin da kuke,"
"Ai hukuncin cin amana da qarya suke karba, domin su ne suka ja komai, dik da ta bangaren sakina da kai banji haushin su ba, itace ta dace da kai dama, ban taba son ka ba Anwar, biyayya nama iyayena, Fahad shine zabina, shi nake so tin usul, Abba ya zaban kai, muka.hakura, yanzu da ka saken, ko da sanin su ko ba sanin su zamuyi aure, sai dai ka mutu,"
Dukan gate din yayi da qarfi ya fice, Fahad bai bata lokaci ba ya saka ta da yaran a mota, zatai musu ya nuna bacin ran shi, sannan ya bata umarnin dole fa yau zata gida, kuka ta saka sosai tana ita bata son zuwa, yq taimaka ya mata hakuriya barta, ta hakura da riqon yaran a yanzu yaje ya musu bayani ba sai taje ba.
"Haba my love, bakiji me ya fada ba? Tinda kk tafi Abba bai taba tsayawa anyi maganar ki ba sai yau, dan haka ba zan bar wannan damar ta wuce mu ba, dole muje a warware komai a yau, muje,"
Kifa kan ta tayi tana t kuka, kiran su Ladeefa yayi, yace zasu bishi dan su zama shaidar shi.
Nan da nan suka shige, gudu yake kamar zasu wani garin, a hanya suka ga motar Anwar, nan Fahad ya wuce shi, sai abun na su ya zama kamar masu tsere.
Kusan a tare suka shiga gidan, suna shiga suka fita, Anwae har tuntube yake ya riga su shiga, a can ciki kuwa jin shigowar motoci da gudu ya sa Umman Maleeka miqewa cikin sauri ta daga labule, ganin masu fitowa daga motar sai da ta kusa faduwa, Abban Maleeka ya riqe ta, shima yana tsakanin murna da mamaki, ganin su nayi sun fara takawa zasu fita, a hanya suka hadu da su, zasu shigo, Anwar kamar wani qaramin yaro ya haukace tini ya fara magana ba kai, yana son ya nuna ma iyayen nasu har yanzu Maleeka da Fahad na cin amanar su.
"Kun ga mu je mu zauna muyi komai a nitse, bana son hayaniya, haka ba abinda zamu gane ai,"
Suna zama, Anwar ya fashe da kuka, saboda bai san me yake ji ba, ji yake kamar numfashin shi na fita kadan2, tashin hankali ne tsabar shi a tattare da shi, ga rin ya ma matar shi zata kasance da abokin daya dauka a dan uwa?
"Fahad yi mana bayani tinda shi kuka zai,"
Labari ya basu akan komai, tin daga sanda suka dawo gidan da zama, tin son Maleeka da ya ke tin bata da wayo har ta girma, da yanda Abba ya bawa Anwar ita, da zaman shi a gidan Maleeka har zuwan ta abuja, da dawowar ta Kano da abinda ya faru yau, komai bai rage va, Abba kan shi sai da ya tausaya ma Maleeka dan jin irin hakuri da biyayyar da tai a gidan Anwar, amma kuma suka samu maqiya suka shiga tsakani, ba su tsaya sun saurari hanzarin su ba, ko Anwar sai a sannan ya san wasu abubuwan, jikin shi ne yayi sanyi, amma ya zai yi, sai a yanzu yake jin matsanancin son Maleeka, (ta haramta gare ka, dan ka sake Fahad na kuma so)
Maleeka da yaran ta suka qanqame ta suna taya ta kokawa ta takure tana ta kuka, taqi daga kan ta ta kalli kowa
"Zo nan 'ya ta, ke din abar alfahari ce a gare mu, mun maki mummunar fassara ashe abinda muke zata ba haka bane, kai kuma Fahad Allah ya maka albarka da ka riqe soyayyar ta da amana baka keta alfarmar aure ba, amma munyi kuskure gaba dayan mu koda ma ace kun kusanci juna, laifin mu ne, tinda kun samu kusanci sosai, alhalin ku ba muharraman juba bane, Allah ya kiyaye gaba,"
"Wannan gaskiya ne Abban Maleeka, dan haka muna neman gafarar ku gaba dayan ku, musammab Maleeka, ki dawo gare mu, tinda kk tafi na rasa nutsuwa ta, saboda yawan tinani yanzu haka hawan jini gareni, dan Allah ki dawo gida, Abban maleeka ka sa baki"
Maleeka matsawa tai kusa da mahaifiyar ta har yanzu bata ce komai ba sai kuka, burin ta daya taji Abban ta yace ta dawo gida, zata dawo cikin frin ciki, ba zata sake kwana a waje ba in ba dakin ta ba, dake cikin gidan iyayen ta.
"Abba kace wani abu akan mata ta da yarana"
Sai a sannan Maleeka ta samu bakin magana.
"Matar ka? Matar ka fa kace? Amma dai ina jin ka manta saki nawa kamin ko? And ko ma saki nawa kamin kai koda da auren ka a kaina dole ka saken a yau, saboda kai ma kasan ka gwadamin rashin imanin da ba zan iya fadan shi anan ba, gaba 'ya'yan ka da iyaye na saboda kar su tsane ka, Anwae Fahad nake so tin fil azal, biyayya ce tasa na aure ka,ga yara nan, sai su zaba zasu bika ko zasu bini, banda ja in zasu bika, amma sai ka sake aure, dan ba zasu zauna a hannun ka ba aure ba,"
Kuka ya saka yana ba kowa hakuri, ya tabbata ya cuci kan shi cuta mafi muni, bak riqe auren ta da kyau ba, ga shi yanzu ya rasa ta, ina zai saka kan shi? Kuma tabbas sun fishi gaskiya, miqewa yayi yana hade hanya zai fita, Fahad ya bi bayan shi, ya kama kafadar shi,
"Ya kamata muje mu kwanta, dare yayi, kar ka koma gida kai daya, kaga ba kowa ko ka koma, mu bar abinda ya wuce a baya mu kalli gaba,"
Abba yaji dadin hakan, dan ko ba komai ya masu tarbiyya me kyu dikan su, sai abinda ba a rasa ba na halin mutum da zaka iya zama malami dan ka dan iska.
Gyada kai yayi alamar ya amince, dan haka juyawa sukai Fahad ne ya iya furta musu sai da safe, ya ja hannun Anwar suka wuce.
Maleeka kallon su tayi, ta ji tausayin Anwar dan ta tabbata ya rasa komai, yanzu abin a tausaya masa ne, addu'a ta masa a ranta Allah ya bashi mace ta gari, musamman dan yaran ta su samu mai riqon su da gaskiya.
Daga nan Umma ta nuna masu dakin da zasu kwana zuwa gobe,dan Abba yace dare yayi kar su fita, gobe sun zauna suji ya akai suka hadu da juna.
Umma da kyar ta hakura ta koma dakin ta, dan ji take da za a bata dama da diyar ta zata kwana, amma Alhamdu lilLAAH suna gida daya, in ba aure ba bata fatan su sake rabuwa.
Samha da Ladeefa sai yaba yanayin gidan suke, Maleeka jin ta take kamar sabuwar haihuwa, nan suka baza hira, yara sunyi bacci a jikin su, Maleeka ta kai su dakin da Umman ta ta nuna mata nan suke kwana in sun je, dakin an qawata shi da kayan alatu, kala2 na yara, ya sha adon pink da white, sai wanda ya gani kawai.
Addu'a ta shafa masu ta fito ta kalli parlourn nasu, tana tuno da rayuwar sa sukai a gidan, ta dade a wajen kan ta koma, ta isko duk sinyi bacci, itama kwantawa tayi, tayi addu'a ta kwanta........
*Mujira zuwa safiya muji ya zata kaya inshaa Allah, Much love Fans*โคPage 20
1K 52 0
by Haermeebraerh
Following
Share
๐
๐ผ MIJIN YA TA KO MIJINA ๐
๐ผ
BY HAERMEEBRAERH
Page 20:
Washegari suka tashi a tare suka shiga kitchen, suka taya Umma abinci, sunayi suna hira,anan suke bata labarin yanda suka hadu dikan su, ta tausaya masu sosai, kuma ta qara basu gudummawa sosai na yanda zasu qara nesanta kan su da shaye2, saboda matsalar da ake samu masu shaye2 zuciyar su na fara sanar da su, tinda suka fara fa ba zasu iya bari ba, kuma da dama basu samun goyon baya da kulawa daga wajen dangin su, sai kyara da tsangwama shike sake maida su ruwa.
Sunji dadin shawarwarin su sosai, bayan sun karya, Anwar ya tafi gidan shi, Fahad ya gyara inda yaji ciwo, bakin shi ya kumbura baya son ayi abin dariya, Maleeka data kula da haka sai tai ta labarai na abin dariya, ya riqe vakin shi yana yarfe hannu, nan ita da yaran zasu hadu suyi ta mashi dariya.
Sin yi qoqari suka maida yara makaranta tare da vada hakuri, sosai kan a yarda a karbe su.
โกโกโกโกโกโกโก
Amarci ake sha sosai a gidan Suhail, wata iriyar soyayya ce mai tsafta take wanzuwa a tsakanin su, ya sauya layin wayar shi saboda matan dayake hulda da su na yawan neman shi, ko turo masa hotunan su marasa kyaun gani, da sunan jan hankalin shi dan ya koma masu, Amatullah yanzu kawai yake gani.
Kwance suke da safe, kowa a cikin su yana jin qiwar ya fara tashi, in tace ya tashi ya bata abin karyawa yunwa take ji sai yace ta ina zai tashi ta danne shi.
Tashi tayi, ta miqe, cikin ta ya dan turo gwanin sha'awa, hannayen ta ta dora akan qugun ta, tana masa kallon ka tashi ko wani abun ya biyo baya, sake jan pillow yayi, ya rungume, jikin shi rabi a rufe rabi a bude, kallon ta yake qasa2, qafarshi daya datake lilo ta jawo, sai da yaji ya kusa fadowa ya kame jikin shi,
"Tsaya2 dan Allah tsaya zan tashi, me za a dafa maki gimbiya?"
"To tashi, ni so nake na ci danwake da mai da yaji, da koko, mai dan tsami2,"
Zaro ido yayi, shi bai iya dama koko ba, kuma bai iya danwake ba,ya fada yayi laifi,
"To an gama, yanzu ki zauna,naje na dawo, amma bari na dan fara wanke baki kan na fita,"
"Dan Allah kayi sauri, ji nake kamar zan suma dan yunwa, kuma su nake so na fara ci,"
Fasa shiga bandakin yayi ya fice, yaje ya samu mai share2n parlourn su, ya roqe ta in ta iya danwake, ta tabbatar masa ta iya, roqon ta yayi akan ta koya masa, sannan ta tsaya ya kwaba ta gani in yayi, haka kuwa akai, a kan idon ta yayi komai, sai ga danwake ya hadu, ba laifi yayi kyau, ya soya mai, ya dakko kwalbar da yaji take, ya zuba mata a mazuban da suka dace, koko ne bai san ya zai ya samu ba, kai mata danwaken ya farayi, kamar wata tsohuwar mayya haka yawun ta ke tsinkewa, ta zauna a qasa, ta bude qafa ta fara ci, cema yayi yana zuwa, ya koma wajen megadin su, ya tambaye shi ina zai samu koko, ko kamu ya dama da kan shi, cewa yayi bari yaje ya siyo, kowanne aka samu zai kawo, Suhail ya jaddada masa yafi son ya siyo kamun.
Wajen minti goma,ruwa ya tafasa, har ya fara qasa dan bai saka da yawa ba, maigadi ya dawo, dauke da kamu a kwanon da Suhail ya bashi, nan da nan me aikin ta koya masa yanda zai dama,bayan ya dama yayi guda, saka abun burga miya tasa yayi na qarfe ya burge shi, nan ya yi daidai, ya dau madara d sugar ya nufi dakin, duk ya gaji, a lokacin da yake aiki. Sai jinjinama mata yake, amma a haka mata ke girki kala2, dan kawai su faranta ma maza, amma basu birge wasu mazan, gwanda shi dama yakan dan taya ta watarana, yu kam shi yayi dika, danwake kadai yayi, amma ji yake kamar yayi aikin gidan dika.
You'll also like
DENIAL by helxiq
DENIAL
305K
6.8K
I was drowning in her kiss. The intensity of it filled me with sensations I'd never felt before. I taste her and I realize I've been starving. I have loved before, but n...
๐๐ก๐ ๐๐ข๐ฌ๐ฆ๐๐ญ๐๐ก๐๐ ๐๐ฎ๐ฉ๐ข๐ by ruuxwrites
๐๐ก๐ ๐๐ข๐ฌ๐ฆ๐๐ญ๐๐ก๐๐ ๐๐ฎ๐ฉ๐ข๐
270K
34.5K
๐๐ก๐ ๐๐ซ๐ ๐ฎ๐๐ ๐ฅ๐ข๐ค๐ ๐ข๐ญ ๐ฐ๐๐ฌ ๐ ๐ฌ๐ฉ๐จ๐ซ๐ญ. ๐๐ ๐๐ฅ๐ข๐ซ๐ญ๐๐ ๐ฅ๐ข๐ค๐ ๐ฅ๐จ๐ฌ๐ข๐ง๐ ๐ฐ๐๐ฌ ๐ฉ๐๐ซ๐ญ ๐จ๐ ๐ญ๐ก๐ ๐ ๐๐ฆ๐. ๐๐ก๐ ๐ฐ๐จ๐ซ๐ฌ๐ญ ๐ฉ๐๐ซ๐ญ? ๐๐ฏ...
๐๐ฃ๐ซ๐๐๐ก๐๐ ๐๐ง๐ค๐ข๐๐จ๐๐จ - ๐๐๐๐๐ค๐ฌ ๐๐ ๐๐ค๐ฌ๐จ by Deewanixwriters
๐๐ฃ๐ซ๐๐๐ก๐๐ ๐๐ง๐ค๐ข๐๐จ๐๐จ - ๐๐๐๐...
6M
549K
AKSHAT SINGHANIA - A literature professor in Singania Institute of Arts and Commerce. He is soft and caring person with a tough exterior, who doesn't believe in love or...
The Malhotras by ritikaauthor
The Malhotras
1.8M
152K
This is a story of four brothers. The brothers who are ready to sacrifice their lives for each other in childhood but what will happen when they grow up and find their...
Busy Bee by SummerMaung
Busy Bee
317K
14.5K
แแแบแธแแญแฏแแพแแแปแ
แบแแญแแแบ แแญแฏแแบแแฐแธแแฑแแญแฏแทแแฒ แแซแแฑแแแทแบ แแปแ
แบแแญแแฑแฌแทแแแบแธ แแฐแธแแแฌแแซแแฒ Beeแแแบ Start Date - 13.9.2025 End Date -
My boy friend and His Friend by Angelina5522
My boy friend and His Friend
909K
22.8K
แแญแฏแแบแแปแ
แบแแฒแทแแฐแแฒแท แแฐแแปแ
แบแแฒแท แแฐแแแบ แแปแแบแธ (แ
แฌแแฏแถแธแแแพแฌแธแแซแแฐแธแแแแบแแฑแธแแฌแธแแฌ) Semeแแแญแฏแแบแธแแซแแแบ แแญแฏแธแแซแแแบ แแผแญแฏแแผแฑแฌแแฌแธแแฌแแซแแฑแฌแบ
๐๐๐๐๐๐๐๐๐ ๐๐
๐๐๐๐ โก (Under Editing) by TaleweaverEmber
๐๐๐๐๐๐๐๐๐ ๐๐
๐๐๐๐ โก (Under Ed...
2.1M
152K
๐๐ช๐ฎ๐๐ญ๐ข๐จ๐ง๐ฌ ๐๐ ๐๐จ๐ฏ๐ ~๐จ ๐ฏ๐๐๐๐๐๐๐๐๐ ๐น๐๐๐๐๐๐ ๐บ๐๐๐๐ โขโยฐ.โพโ.เณเฟ*:โ๐ ๐๐๐๐๐๐ โก ๐๐๐๐๐๐๐๐ Ruhanika, a quiet introvert with a pa...
Tana ganin kokon nan, kamar zatai tsalle dan murna,
"Kaiiiii amma Allah ya maka albarka, gaskiya ba namiji kamar ka a duk duniyar nan,kai kadai ne namiji daya tamkar da ba iyaka, Allah ya qara min son ka,ya sa mu dawwama muna farantawa juna,"
(Ina fatan kun kula da yanda Suhail ya zage ya ke fatanta ma matar shi dake dauke da ciki, wasu mazan ba su san su taimaka wa matan su ba,musamman in suna da ciki, mace me ciki na da tsirfa, tace yau wannan take so, gobe tace wancan take so, in aka samu miji mara imani, ko da yana da hali in tace tana son wani abu, wanda kudi zai siya ma ba ya mata da kan shi ba ha yi yake ba, sannan ina fatan mun kula da yanda Amatullah ta nuna ma mijin ta godiyar ta da addu'a da kuma nuna masa jin dadin ta akan abinda ya mata, wasu matan da sun ga an dan fara taya su abu, zasu maida ma mazan abun kamar dole suka saka kuma akayi dole, daga nan miji na ganewa, ko tsinke ba zai sake yunqurin tayaki ba, dan haka godiya da yi ma.mutum addu'a na sa yayi abinda bai niyya bama, kamar ni dai, in ina jin addu'o'in ku sai naji ina sha'awar rubutu๐๐ป)
โกโกโกโกโกโกโกโกโก
Su Samha sun koma gidan su, inda Maleeka take zuwa makaranta daga gidan su, gaba daya ta sauya har wata 'yar qiba tayi, Samha na zaune tana tinani, kowa rayuwar shi ta kyautatu, banda ita marainiyar Allah, hawayen ta ta share, ta miqe dan zuwa yin alwala, ta gabatar da sallar la'asar.
Bayan tayi sallah, ta dau qur'ani ta na karantawa, sabon abinda ta tsara ma kan ta kenan, yawaita karatun alqur'ani dan taji wa'azi wani malami yace, gwargwadon albarkar mumini, gwargwadon karanta alqur'anin shi, in kana da albarka za a same ka mai yawaita karanta qur'ani, dan haka ta dage,sannan taji ance Allah zai kama wanda yake aje qur'ani har yayi qura ba tare da yana karantawa ba, dan haka ta dage sosai, har Ladeefa ta dan fara itama amma ba kamar Samha ba.
Tana karatun taji qwanwasa qofaat the same time Ladeefa ta kawo mata wayar ta, tana sanar da ita Amatullah ke kira,
"K bani, dan amsa qofar nan pls, inna idar na kira ta,"
"Kk"
Tana budewa taga Amatullah bayan ta suhail ne, kan shi na kallon gefe, a zaton shi Samha ce ta bude,kunya yake ji sosai, ganin ba ita bace, yasa ya dan sake kafadun shi, amma still wannan data daure fuska kamar taga mugun abu fa?
"Yah Amatu bismillah shiga mana,"
Shiga tayi, ya daga qafa shima zai shiga Ladeefa ta tsaya bakin qofar, ta tokare da hannun ta, ta kama qugu da daya,ta daga masa gira alamar ina zashi?
"Malama ya dai?"
Samha ce kan Ladeefa tayi magana ta bashi amsa,
"Ka tsaya anan, tinda kai idon ka idon mata, nan gidan 'yammata ne masu kamun kai, ba zan so ka shigo ba ta dalilina ka lalata su,"
"Haba Samha ban sanki da irin wannan halayyar ba, yanzu meye na ririta magana daga zuwa baki san dame muka zo ba"
"Dame kuwa kuka zo? Ina ce mijin ki ya fi ni, koka manta da dikkan alqawarin da muka ma juna, kikai zaman ki daga zan kira ki in ya fita yau kwana nawa ban gan ki ba, ji nake duniyar gaba daya ni daya ce ban da kowa, ban da iyaye,ke din kin juyan baya kin komawa mijin ki da yayi qoqarin rabani da qimata da dataja ta, ya kk son nayi, Inna da kawu kuwa yanzu duniya kawai suka saka a gaba, ba ma zan tinkare su ba sumin maganar aure,"
Tana maganar cikin kuka da daga jijiyoyin wuyan ta, Amatullah ma hawayen tausaya ma qanwar ta take, tabbas ta zama mai sn kai, ta manta da qanwar ta tana can tana shan soyayya da miji, kama hannun Samha tayi,ta zaunar da ita, sannan ta kalli qofa ta daga hannu akan Ladeefa ta bar Suhail ya shiga,harara ta maka masa kan ta kauce.
Yana shiga ya zube a gana Samha, ya daga hannayen sh yana tafa su alamun bada hakuri, dan matsawa baya tayi, sabod abun ya bata mamaki ma,
"Meye haka?"
"Samha hakuri nazo na baki, ยฐakan dikkan abuhuwan da suka faru a tsakanin mu, ina neman zaki yafe mn domin Allah da kuma hakurin ki, Samha na kasance daga cikin maza masu son kai da zuciya, a baya,ama a yanzu na sauya, na gyara rayuwa ta da izinin Allah da taimakon yayar k,"
Kallon Amatullah tayi taba neman qarin bayani, nan Amatullah ta zayyana mata komai, take Ladeefa ta zauna a kujera, ta dafe baki, tana zaro ido, ta ma qanin saurayin ta rashin kunya,
"Dama kai din qanin Heeshaam ne? Ya salam,"
"A ina kk san shi?"
Dan sunkuyar da kai tayi, ta ja gashin ta ta baya, ta kauda kai gefe, Samha ce tayi magana.
"Saurayin ta ne ai,"
Hawaye ne na qaguwa ya gangaro ma Suhail,shekara da shekaru rabon shi da dan uwanshi,
"Ina zan gan shi? Dan Allah ki kaini wajen shi, ko ki kiramin shi nan, ki sanar da shi kin samu dan uwan shi Suhail,ki hada mu muyi magana,"
"Kaga kwantar da hankalin ka, zauna ka nutsu, zan kira shi yanzu,"
Wayar ta ta zaro a aljihun wandon ta, tana kallon Suhail, da yanda ya rude, danna no Heeshaam tayi, bugu uku ya daga,
"Hellooo sweery, yanzu nake da niyyar kiran ki,"
"Koh, barka da safiya love"
Kafin ya amsa Suhail ya amshe wayar, kallo ta bishi da shi, ta bi kamar zata amshe, ta daga hanni ta hade gira,
"Really?"
Daga mata hannu Amatullah tayi, alamar tayi hakuri,
"Broth, dan uwan ka ne, Suhail, ina gidan da Samha take da qawar ta Ladeefa nan na ji ashe ta san ka, ina kk na zo gare ka,dan uwana nayi kewar ka sosai,"
Heeshaam qamewa yayi, ya daga wayar ya kalla ya maida, da gaske muryar qanin shi yake ji? Wani dadi ne ya baibaye shi, ya miqe, tare da daukan key din motar shi,ya fice,yaba sanar da Suhail gashi nan zuwa.
Kashe wayar yayi, yana cike da murna ya kira iyayen su ya sanar da su yanzu sukai waya da Suhail, suma murna suka dinga yi, musamman Mum.
Ladeefa najin ance Heeshaam zai zo, ta diba daki da gudu, taje ta saka riga doguwa da mayafin ta, ta dan fesa tirare,Suhail ji yake dama Heeshaam ya fada masa inda yake, da shi zai bishi, jiran nan ya dame shi, kula da hakan yasa Samha ta ce,
"Yah Suhail ka kwantar da hankalin ka, tinda ya ce zai zo ,zai zo ne inshaa Allah, hakuri kawai zakai, ya kusa ai"
Kallon ta yayi yayi murmushi, tare. Da ce mata,
"Na gode Samha, a gaskiya kudin ba kuda nabiyu a kyakkyawan hali, har kin manta da abinda na miki, kina bani qarfin guiwa, ba dan yayar ki ba nan ma da tini ina nan ina zaune a lalace,na gode maku na gode maku, Allah ya muku albarka, Allah ya saka maku da alkhairi, na gode"
"Ba komai,Allah ya yafe mana dika,"
Suna zaune suka ji horn, da sauri ya miqe, kan Heeshaam ya shigo, ya fita qofa,a hanya suka hadu, wani wawan mari Heeshaam ya sakar ma Suhailllll.............
*Cassssssssss me ya faruuuu๐ฑ๐ฑ๐ฑ๐๐ป๐๐ป๐๐ปwhatever happens naji dadin marin ga wallah๐๐คฃ*Page 21
1K 55 1
by Haermeebraerh
Following
๐
๐ผ MIJIN YA TA KO MIJINA ๐
๐ผ
BY HAERMEEBRAERH
Page 21:
"Ouchhh wannan marin fa?"
Jan shi Heeshaam yayi ya rungume tsam a jikin shi, haka shima Suhail, ji suke wani farin ciki na ratsa zuqatan su,sun dade kafin su sake juna, su kalli juna,
"Ina jiran bayanin marin daka min"
"Kana son na qara maka wanine,"
Ya daga hannun shi aaar zai kai masa wani marin, da sauri Suhail ya rife fuskar shi da dika hannayen shi,
"Allah ya kiyaye, wancan ma da na san da zuwan shi dana tare, kaima kasan ba a dukana ko?"
"Eh ni din ma ba wai daya na so na maka ba, na so na.maka iya adadin garuruwan da nai ta zuwa neman ka ban same ka ba sai anan,ashe anan din ma kana kusa dani ban sani ba sai yanzu,"
"Yeh thanks to Ladeefa and ur love for her, da wataqila sai dai ka jini a Abuja jibi,"
Da murna sosai Heeshaam ya kalle shi, ya sake rungume shi,
"Da gaske zaka je cikin son ran ka ba tare da an maka dole ba? Alhamdu lilLAAH Suhail munyi kewar ka, Mum cewa take Allah kar ya dau ran ta bata sake ganin ka ba,amma ni da zaka taimaka da.mun tafi gobe, dan na ma Mum alqawarin dik randa na gan ka a ranar ko washegari zan kai mata kai,"
"Eh tinda ni kudi ne ba, Alhaji ka bari sai jibi, kawai muje, saurin n meye,"
"A'a Suhail ba za ai hk ba, mu je goben, me mukeyi? B binda zamuyi ai,"
"K Dear dik abinda kk ce,"
"Wait, is she ur wife,"
"Yup kai ba ka qi aure ba, mata ta ce, ga ta nan har da baby,"
"Na kula da hakan ai, masha Allah, tayi gaskiya kawai kaje ka fara parking gobe mu wuce, but i have to go and see ur house,"
"Hakane ya kamata,"
"๐ญ๐ญYau bama a tani,ko kallo ban ishi mutum ba har yana shirin tafiya bai zauna ba ma, shikenan,"
Da sauri Ladeefa ta dauki ha yar shigewa ciki, Heeshaam ya bi bayan ta, yana waige yana kama baki, alamar yayi laifi babba.
"Habaaa Sweetheart kema kin san ba zan manta ki ba ai, kawai ina cikin murna ne mun dade shekara da shekaru bamu hadu da shi ba, qanina ne uwa daya uba daya, plsss smile for me mana, ko naji sanyi,"
"๐shikenan sai aka ce dan kaga qanin ka ka dauki hanyar fita ko kallo ma van ishe ka ba, sai wani leqen ka nake ina sake haqora kai kuma bama ka gani ba, to na gaji da tallata murmushin nawa nima yau kam bazaka same shi ba, kaje kawai,"
"Ni ba inda zani, sai kin yi min murmushi in ba haka ba na kwana a nan,"
Rufe baki tayi tana kallon shi, nan dariya ta kama ta,
"Ka kwana anan fa kace, tabbb tashi maza van isa ba,"
"Me yasa? Baki son ganina a inda kk ke?"
"Ba haka bane,ka bari lokaci yayi, dan kasan komai da lokacin shi, amma ka kwana anan inaaa ba zai yu ba, muje kar a ga mun dade ma ni,"
Dariya yayi, yanda ta nuna da gaske ya tafi dan kar a ga sun dade,
You'll also like
DENIAL by helxiq
DENIAL
305K
6.8K
I was drowning in her kiss. The intensity of it filled me with sensations I'd never felt before.
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 9 Chapter of 13