irin mai fadin nan ta baya, ta gaba ta tsule kai, sai Maleeka da ta saka mayafi, ba abinda ya bayyana a jikin ta sai hannun ta da fuskar ta, a motar Maleeka sula fita, sun saka kida na tashi suna ta bi suna shewa, suna isa ADO BAYERO MALL suka samu waje sukai parking suka fito dauke da sun glasses, masu kama da kwalbar cikin flask, na Samha mai renbow colour na Maleeka mai kalar golden sai na Ladeefa mai kalar silver, sun rataya jaka irin doguwar nan, har cinyar su, maza da dama kallon su suke, kai har matan ma, wani sai ya rantse yaran wani qusan ne a Nigeria, shigewa sukai ko a jikin su, kayayyaki suka fara diba, suna yi suna hotuna, suna vedio ma junan su,kamar daga sama Ladeefa ta juya ta gan su, da sauri tabi ta bayan Maleeka ta boye,ta zare glass din idon ta.
"Kun gan su can, dan Allah kuzo mu bar nan,"
"Su su waye?"
"Mijina da saurayin shi, dan Allah kuzo mu tafi bana son mu hadu, bana son kowa ya san inda nake,"
"Ba zamu tafi ba kuma ba zai gan ki ba, amma mu zamu bi shi mu ga me suke yi a kano,"
"Noooo plsss mu tafi kawai, ba zan iya jure ganin shi da wannan dan iskan ba a matsayin mijin shine ko matar shi ne whatever, plsss lets go,"
Samha ce ta tsaya ta gefen Ladeefa ta sake kare ta ganin suna zuwa ta wajen, sannan tace,
"Ke malama ba inda zamu fa, sai munga uban me ya kawo su Kano,"
Wuce su sukai, abokin na cewa,
"Eh wancan din ma na da kyau ai da ka bari mun dauka,"
"Kar ka damu wannan ma na da kyau mu gwada mu gani,"
Dan dafa kafadar juna sukai sannan suka rabu, ga wanda bai san su ba, zai zata kawai shaquwa ce ta abokai, nan ko ba a san iskancin da suke shukawa ba, suna gama biyan kudi, su Samha suka aje kayan da suka diba suka bi su, motar su suka shige suna jiran su suma su tada tasu su bisu.................
*Wayyoooo Dan Allah Hamy a ci gaba muji ina za a jeeee๐คฃ๐คฃ๐๐๐ sai gobe inshaa Allah, choliiiii*๐
๐ผ MIJIN YA TA KO MIJINA. ๐
๐ผ
BY HAERMEEBRAERH
Page 11:
A baya2 suka dinga bin su, ba tare da sun gane bin nasu suke ba, can nesa da su suka tsaya, ganin sun tsaya a bakin gate din wani gida, mai gate irin mai qarafunan nan, unguwar ta manyan masu kudi ce, manya2n gidaje ne a wajen, ga shuke2, bayan sun shiga gidan, sukuma suka bi su da gudu, suna zuwa bakin qofar suka tsaya dn ba yanda za ai su iya shiga gidan, ba tare da an san d zuwan su ba, ta wajen suka karade gidan, suna leqe, can ta bayan gidan suka hango, maza kala2, da masu shigar 'yan daudu da qananan kaya, da masu wando kawai, sai wanda suka saka boxers suna ta yawo, kamar tsirara, Samha kam ta ga tashin hankali ganin maza haka kamar tsirara,har wani jiri taji na dibar ta, Maleeka ce ta kula da hakan, tace,
"Ya isa haka yanzu mu tafi mu zauna a mota mu dan jira, in basu fito ba muje gida mu yi shawarar yanda zamu tafi da lamarin cikn sauqi,"
Ladeefa kuwa kuka take sosai, dan ko ba komai har yanzu tana son Sammani, dama za a ce zai daina wannan abun ba abinda zai hana ta yafe masa su ci gaba da zama, amma da dikkan alama ya dade yana yi, tafya suk farayi, tsabar waiwaye da Samha take yi ta gurda qafa, qara ta saka mai qarfi, ta kama qafar ta ta, Maleeka ce ta toshe bakin ta, kusan a tare suka zaro ido, da sauri suka kama ta ta kafadun ta suka fara gudu, kan su kai hanyar barin wajen, wasu maza masu six packs sun leqo, suna ganin su Maleeka suka nufi wajen su, ba su tsaya ba suka diba da gudu, mazan na biye dasu, mota suka fada, Maleeka ta wuga Samha ta baya, ta bude gaba ta shige mazaunin Driver, tana ma Ladeefa ihun ta shige, cikin rashin sa'a kuwa suka riqe ta ta hannun riga, ihu ta sake, kan lokaci mai yawa mazan nan sun qaru, wasu sun.fito, Ladeefa na ganin haka ta ce ma Maleeka,
"Maleeka kuje zan zo ba abinda zasu min, kar ki bari a kama mu dika ba zan taba yafe maki ba kk bari suka kama ku, kije kawai i will be fyn,"
Cikin firgici da rashin sanin abin yi Maleeka ta taka motar zata wuce, maza uku suka tsaya gaban ta, a zaton su ko zata tsaya, yi tai da motar ta cikin su suka rabu kowa ya kauce, ta sa gudu, suka bar wajen da Samha, Samha na ta mata ihu akan kar su bar Ladefa a wajen,
"Shut up ! I said shut it up !! Ya kk so nayi? Na tsaya su kama mu dika? Kina ganin in suka kama mu dika akwai wanda ya san ina muke ne? Wa zai kawo mana dauki, plssss let me concentrate"
Shiru Samha tai bata taba jin ihun Maleeka cike da bacin rai irin na yau ba, nan da nan ta fara kuka, saboda kawai hango mazan nan take sun saka Ladeefa a gaba, Maleeka zuciyar ta tayi laushi, rasa ya zatai tayi, suna isa gida Maleeka tace ma Samha ta fito, nuna mata qafar ta tayi, kallon qafar tayi, ta kama qafar zata ja Samha tai ta ihu, amma haka Maleeka ta ja qafar, tana gama ja mata taji dama, ba kamar da ba, ciki suka shiga, Maleeka ta dakko mata doguwar riga ta saka, itama ta saka, nan suka yafa mayafin suka sake fita, wajen 'yan sanda suka nufa,daga kwatancen unguwar da gidan suka sallame su, wai ba zasuje ba, gidan da yaran manya da kuma manyan kan su ba abinda zasu iya yi.
Har dare suna yawo ba wanda ya taimaka masu, a lokacin har Maleeka kuka take, domin rashin sanin abin yi, gida suka kma,Maleeka ta roqi Samha akan ta taya ta kwana tsoro take ji.
Haka kuwa akai anan ta kwana.
โกโกโกโกโกโกโกโกโก
Bayan tafiyar su Samha, mazan nan suka dauki Ladeefa kamar kaza suka shiga da ita gida, mazan dake ciki sunyi cirko2, suna jiran suji me ke faruwa, Sammani da budurwar shi suna can baya sosai, amma sai da Sammani ya gane ta da sauri ya dinga ratsa mutane yana zuwa inda yake hango Ladeefa.
"Ladeefa? Ladeefa me ya kawo...... oh oh oh, kune matan da muka gani a Mall? Amma ban gan ki ba ai?"
"Sammani ka taimaken kawai na gan ka ne naji ina son na sake ganin ka shine na biyo ka, amma ni bani da wani abu a raina, dan Allah ku barni na tafi gida, qawayena na cikin damuwa,"
"Ba inda za a barki kije, tinda kk kawo kan ki, ba zaki bar gidannan ba,zaki zauna kamar sauran matan da suka kawo kan su ki na mana aikatau,"
Kallon shi Sammani yayi da wani kallon da bai taba masa ba,
"Sadam ba ruwan ka, ba mai wahal da ita, abu daya zan mata shine ta koma gida, ko muma zamu huta da qaryar da mukayi, na muna qasar waje, zaman Nigeria ya gagare mu tinda muka rasa ta yau muna can gobe muna nan, kull sai dai ka kashe murya kai magana a matsayin ta, i want my freedom, ta koma gida na sake ta, kawai,"
."ehhhh dan Allah ka saken na maka alqawarin ba zan fadi komai ba, amma nima kar ka doran laifin komai, dan Allah kar ku barni na kwana a gidannan ku maidani gidaaaa"
Ta qarasa qarshen cike da kuka da tsoron ganin ta cikin qattin maza ba riga, ga su wasu a rungume a jikin wasu, wasu ana ma wannan case din kiss suke abin su, ga shi nan dai, ba zata iya zama anan ba kona kwana daya ne.
"Wannan kuma ne baki isa ba, sai dai ki bari ki kwana gobe muje ki ma qawayen naki sallama ba inda zaki tsaya gobe sai gaban iyayen ki, muma muna son mu huta da wannan jarabar qaryar da muke faman yi,"
Sammani ne ya shafa qirjin Sadam din nashi,
"Babe ka daina tada hankalin ka akan wannan yarinya, na fada maka bana son ta ko kadan, kai nake so, i love only u, ka daina zafafa wa akan ta,kaji? Muje ciki, Kaii ku kaita dakin Angela ta kwana zuwa gobe,"
Wani fari Sadam din yayi ya kwantar da kan shi a jikin Sammanin, yana wani karairaya, irin ya yarda da son da Sammani ke masa, tafiya suka fara Ladeefa na qasa, mazan da suke riqe da hannayen ta suka daga ta, suka fara tafiya da ita wani bangare na gidan, juyawa tai taga yanda Sammani ke zuba ma Sadam soyayya kamar wani mace, kuka ta fara mai tsananin qona rai, shikenan ga namiji har namiji amma shaidan yayi nasara akan shi,kwata2 ba Allah a lamarin su.
Haka aka kaita dakin, suna budewa suka wurga ta, suka rufe, wasu mata ta gani, su biyar tsirara, suna ta zuba iskancin su suma, a tsakanin su, kallo suka bi ta da shi, dayar su ce wadda take siririya sosai gata ba ta da tsaho,ta taso tana wani yanga ta kama hannun Ladeefa, da sauri ta janye hannin ta, tana zare ido, bakin ta ya bushe, wani tsoron su ne ya kama ta, wadanan kuma su nasu gang din abinda suke kenan? Tana cikin wannaj yanayin akai waya, sauran matan nata hira a tsakanin su, akan wace ce ita, gajerar nan ce ta taka ta dau wayar, ganin sunan dake jiki ne ya sa ta nutsuwa, ta danna amsawa,
"Yes sir,.... ok sir......an gama sir...to to Allah ya kaimu,...... habaaa ba abinda zan mata kuma zan sa ido sir,"
Tana aje wayar ta dafe kan ta,
"Kassshhh amma oga ya kwafsa min, wannan tsaleliyar kazar ba ta ci bace ta ajiya ce, da mun yagalgala ta, dan ta min,"
Kallon ta Ladeefa tai, taga da ita take ashe, dan da dubawa ta hau yi ko ina kaza take anan din, nuna kan ta tayi da yatsa tana zari ido,
"Nnnniiiii ceee kazar?"
"Yup kece kazar, dan da gani ba ki san harka va, muje na nuna maki dakin da zaki kwana, zuwa gobe, in kuma kina son wani abu ki min magana, ki shiga zan kawo maki abinci,"
Da sauri ta shige dakin tana waigen su, dariya suka saka, tana shiga ta danne qofar, dan ko abincin su ba ta jin zata iya ci, ko ruwa ma ta gwammace ta sha na bandaki.
Bandakin ta shiga, ta ga abubuwan da suka sake tada hankalin ta, wato abinda ya yadu yanzu a cikin al'ummar Annabi muhammad sallahu alaihi wa sallam, al'umma mafi karamci da daukaka a wajen Allah, al'ummar da Allah ke so, ya karrama, amma ta wulaqanta kan ta, al'ummar da ta maida aikata zina da dikkan abinda ya danganci zina ba abakin komai ba, al'ummar da ta maida luwadi, madigo, zina, ba abakin komai ba, a yanzu har ya kai tallata su ake, group ake budawa dan a shiga, a instagram ko facebook, haka ake tallata su ba kunya ba tsoron Allah, abinda ta gani, ne yasa tai saurin bude qofar ta fito, dan ta tabbata wata qila suna amfani da abun ne saboda mazan gidan dik da 'yan uwan su maza suke amfani, zama tai a bakin gadon daf da inda pilo yake, ji tai ta taba wani abu, hannu ta sa ta zaro abun, the same abinda ta gani a bandakin shi ta zaro wurgi tai da shi tana ihu, da sauri Angela ta shigo, ba ko kaya,
"Lfy? Me ne ne?"
Sauran matan na biye da ita, dan ba qaramin ihu Ladeefa tai ba, nuna masu wannan abun tai, tana kuka, me zasuyi banda dariya, har suna riqe ciki, wata ce mai jan ajin cikin su ta shafi bayan Ladeefa, ita kuma ta janye jikin ta da sauri, kashe mata ido tayi, sannan tace,
"Poor gurl, ina jin ko mazan ma bata sani ba, to ke garin yaya, gaki dai da gani kin girmen, amma ace kina nan baki san komai ba har yanzu? To wa kk ajewa wajen?"
Kallon ta Ladeefa tai, cikin jin haushi, tayi tsaki, ta zubda yawu a gefen ta,
"Ke qazama mazinaciya, yar iska, kar ki kuskura ki sake tabani,dan ni ba irin ku bace,na yi wa Allah alqawari daga yau ba zan sake shab kayan maye ba, na san ta nan na zama butulu a wajen mahalicci na, amma na gode masa da bana irin aikin ku, na assha, kuma ina ruwan ki da wanda na aje ma kaina? Meye naki a ciki? Ko haka zan koma ga mahaliccina ba wanda ya karbi budurcina ya fiye min akan shiga halin da kuke ciki, ni sallah nake son yi, in kuna yi ina son a ban hijab ko mayafi sannan ki ciren abubuwan dake dakin nan na banza in ba haka ba, ba abinda zai hana na sanar ma da Sammani,"
Da jin sunan Sammani a bakin ta naga sun nutsu, wasun su ma fita sukai, amma wannan da aka ma rashin mutunci na tsaye tana kallon ta, kallon kin min ban rama ba saboda ba halin ramawar.
Debe abubuwan sukai suka bata abinda ta huqata, suka ja qofar suka fita.
Zama tai tana ta kuka,tare da nadamar shaye2n da ta saka kan ta,ashe akwai 'yan iskan da suka dame su, ashe shaye2n da suke ma su suka saka kan su? Lallai Allah abin tsoro ne.
(Ga mai hankali ne zai ga zunubin da ya fi na shi ya bar wanda yake aikatawa, amma wani in yaga wanda yafi na shi qoqarin shi ya koya shima, shin mun manta akwai mutuwa ne? Mutuwa bata bada notice balle kace akwai lokaci zaka tuba, kana aikata zina Allah zai iya zare dan ka, kana sallah Allah zai iya zare ran ka, komai kk Allah zai iya zare ran ka, kenan ruwan mu ne mu mutu muna aikin Alkhairi, ko mu mutu muna aikin assha, Allah ya bamu dama masu yawa da zamu kubuta daga fadawa tarkon shaidan, Allah ya kare mu daga mutuwar wulaqanci da aikin sabo)
A daren ranar nan gaba daya mutum shida basuyi bacci ba, Samha da Maleeka, yah Amatullah, da Ladeefa, Sammani da Sadam, kowa Allah2 yake safiya ta waye ya dau matakin da yake ganin shine daidai.............
*
*Allah ya kaimu da rai da lfy mu ga me zai farun*๐๐ป๐
๐ผ MIJIN YA TA KO MIJINA ๐
๐ผ
BY HAERMEEBRAERH
Page 12:
Da duku2n asuba, Sadam ya tashi Sammani, wanda yayi daidai a gadon, yana kallon sama kmar mai bacci, kamo Sadam din yayi ya kwantar a jikin shi, yana shafa bayan shi, shi kuma ya fisge,
"Ka ga tashi za kai mu maida yarinyar nan hankalina zai fi kwanciya,"
Ya sauka qasa fuskar shi ba walwala, he is really a jealouse type, fuskar nan ba wani annuri,kallon shi Sammani yayi ya yi murmushi, ya tashi, ya ya mishi kiss a goshi, shi kuma ya wani daga ido sama yana wani harare2 shiga shi ana mai barazanar kwace masa miji,ko mata ko waye ma oho, da wuri suka gama shiri, ana idar da sallah suka nufi bangaren da matan suke, a parlour suka ga 'yammatan a baje,ga abubuwan maza nan a hannayen wasu wasu a jikin su,
"Shegu 'yan bariki ko gajiya ba sa yi,"
Dariya sukai suka wuce suka tada Angela, da magagi ta farka, idon ta na sauka akan Sammani ta wartsake,
"Barka da safiya sir,"
"Ina take? Fito da ita ku bata kaya masu kyau ta saka, tayi wanka,nan da 30mnts muna zaune muna jiran ku anan, ki waya a kawo mana abinci nan, yanzunnan,"
"Yes sir yanzu kuwa,"
Da sauri kamar wadda iska ke kwasa haka take tafiya, bata da wani shape sai tantagaryar iya iskanci a cikin ta, isar da saqon ubangidan nasu tayi ta fito, lokacin da ta shiga wajen Ladeefa sallah ta gan ta tana yi tana kuka a cikin Sallah, tana neman gafara, da qarin shiriya, fita tai tana qunqunin ko ina suka samo wannan mata sai Allah.
"Ke dalla je ki saka kaya kina yawo kamar zakaran da yayi sabon aure,"
Sammani ne ya yi murmushi wanda yafi kusa da dariya,
"Babe kana da wulaqanci, shi zakaran daya yi sabon auren ya yake?"
Matsawa yayi daf dashi yana shafa jikin shi, yana wani kashe masa ido,cikin wata murya wadda za a fi kiran ta data mata, yake maganar,
"Shi zakaran da yayi sabon aure ai lalacewa yake, ko gashin wiyan shi da kyar yake zama, dik figewa yake, saboda jaraba irin ta mata,da a zakarun ma za a samu irin mu da duniya t zauna lfy,"
(Wa'iyazubillah, can u imagen? Su fa masu wannan lamarin gani suke sun fi Allah iya tsarawa halittar da yayi da kan shi, yanda zata tafi da rayuwar su, in ba haka ba, Allah ya ce mace dana miji ne zasuyi aure,su kuma sun sauya saboda taurin kai da nuna wa su zuri'ar yahudawa ne masu qin bin dokar Allah, ko in zasu bi su yi ta ba daidai ba,ko su yawaita tambaya dan qure Annabawan Allah, sun maida bin jinsun su halal, saboda tsabar rashin tsoron Allah a tare da su, Allah ka kare mu daga aikata dikkan abinda zai zama sabon ka ne ya kareem)
Sammani kasa jure ma salon Sadam yayi ya ja shi cinyar shi ya zaunar, nan suka fara romancing junan su, a haka aka kawo abincin, wadda ta kawo tana ganin Sammani ne kan ta a duge ta aje ta fice, shine shugaba a yanzu, ada ne yake da manya, amma yanzu shine oga kwata2 na masu luwadi na Arewa gaba daya.
Abinci aka kai ma Ladeefa bata ci ba ta gama saka kayan da aka kawo mata, dan ko wanka bazata iya tubewa tayi ba a wannan tsinannen gidan, fatan ta Allah ya ara mata rayuwa ta bar gidan kar ta mace a irin wannan gida, gawa ta ta san ko kallo ba zata ishi mutane ba, tsallake kwanukan abincin tayi, bayan ta dora doguwar rigar akan wandon ta dogo ta cire rigar saman ta bar vest din,ta ninke rigar ta ta riqe a hannu, ta yafa mayafin kayan, ta fito, takalman ta ne da ta zo da su, bata sauya da wanda suka bata ba, tayi kyau sosai, sai dai idon ta sun nuna bata samu bacci ba, tana fitowa tai arba da su, amai ne ya taso mata ga cikin ta ba komai, komawa tayi tana kakarin amai, Sammani ya aje Sadam a gefe ya bi bayan ta, da gudu2 Sadam.ma ya bi su,
"Ke meke damun ki? Baki da lfy ne a daga tafiyar?"
"A'a plss, mu tafi yau, dn Allah in baku son na amayar da hanjina ku daina abinda kuke yi a gabana, indai zan gani zanyi amai, coz u guys a r so disgusting,"
Cikin fushi Sadam ya je gaban ta kamar zai make ta ya furta,
"What? We ar disgusting? Ke me kk sani, ina kyauta ta zaton har yanzu namijin ma yaqi neman ki bare 'yar uwar ki mace, banza mara rabo kawai,"
"Ai rashin rabo akan ku ya qare, tinda in ba tuba kukai ba haka zaku koma lahira ku hadu da babbar azabar da Allah ya tanadarwa masu aikata luwadi, da madigo, da zina, dan haka indai wannan ne rabo a wajen ku na bar maku ku riqe rabon wahalar ku,"
Hannu ya sa zai dake ta, Sammani yayi saurin riqewa, yana shafa bayan shi, kallon takaici ya ma Sammani, dan irin protecting din nan nata da yake ne sai ya dinga sawa yaji kamar Sammanin na son ta ne,.ficewa yayi yana fishi, ita kuma ta fito, tsayawa yayi yana tambyar taci abinci? Tayi banza da shi ta wuce shi, ta tsaya a hanyar fita, ta bude qofar, tana jiran su.
Sammani da kyar ya lallashi sadam, suka fice, mota suka shiga, ya tambaye ta kwatancen gidan nasu, ta mishi, ya dau ha ya.
โกโกโกโกโกโกโกโกโกโก
Cikin dare su Samha sun gagara bacci, Maleeka ta dakko masu wani maganin mura a kwalba suka sha, dan haka sai goshin asuba bacci ya kwashe su, suna baccin ne suka ji bugun qofar parlour, cikin mayen da bai gama sake su ba suka farka, Samha ce ta je qofar, cikin shigar ta kamar kullum gajeren wando da vest, tana budewa taga qarti a gaban ta danna qofar tazo yi suka bude da qarfi, da gudu ta koma, tana nuna ma Maleeka su, Maleeka ma jikin ta na rawa take kallon su, cikin dakiya tace,
"Ina qawar mu? Me kuka mata? Na rantse maku in wani abu ya same ta u will all answer to me, ba zan bar ku ba,"
Dariya Sadam yayi ya wurga ta a kujera, yana wani karairaya kamar mace, ya kai fuskar shi daf da ta ta,sannan ya fara magana,
"U little bitch, me kk isa yi mana? Wa yake son qawar taki da har zai damu da mata wani abu? Sallama muka zo ta maku zamu maida ta gabam iyayen ta, dan kar ku dame mune bayn mun tafi muka biyo mu sanar saku, in kuka kuskura kuka yi wani yunquri akan mu,kashin ku ya bushe, dan mun san komai game daku, ba ku kadai musibar zata shafa ba har dangin ku sai mun qarar, kun gane? In ta isa zata maku magana a waya, ba ba byeeee,"
Hanyar waje suka dauka, suma da gudu suka bisu, hango ta sukai sun kulle ta a mota sai kuka take, bude mata Sammani yayi ta fita da gudu kuwa,suma da gudun suka nufe ta suka rungume junan, su na kuka, jansu tayi gefe ta fara sanar dasu abubuwan da suka faru a taqaice bayan tafiyar su sannan ta dora da musu nasiha,
"Dan Allah when i am away, ku daina shaye2, kuji tsoron Allah kamar yanda naji, in da ku kuka ga abinda na gani na san sai kun riga ni barin sabon Allah, naga inda ake tantagaryar shaye2, da zinace2, nayi kuka kamar idona baza su zauna a jikina ba,na fiku son maye amma na bar maye da izinin Allah iya kyautar da zan iya bar maku qawayena shine ku bar maye, ku bar shi bari na har abada, ina son ku, zamuyi waya inna isa,"
"Hey hey hey we don't have all day,ki sauri ki dakko kayan naki mu wuce, jirgi na jiran mu,"
Harara ta zabga ma Sadam din ta bi su, suna ci gaba da hirar da ta dace, sannan tana fada masu ita ta hakura d Sammani, ta cire ran zai shiryu, har ta same shi, saboda a gaskiya ya yi nisa, ta sanar da su muqamin shi, Samha ce ta sa kukan tausaya mashi, a matsayin shi na.musulmi, ace yana aikata zunubi irin na ne.an jinsi, zunubin da me imani ko wanda yake aikatawa ya gani sai jikin shi da zuciya da ruhin shi sun shiga wani hali na tsoron Allah.
Suna gamawa suka rako ta har motar, suna mata bye, suna koka rabuwar su, da gudu Sammani ya ja motar ya tafi, suna komawa Maleeka ta fashe da kuka, yanzu ita daya za a bari awannan gidan, dan ta san Samha komawa za tai, tinani take me zurfi, can naga tayi murmushin jin dadi,wanda ya sa Samha tambayar ta meke sata murmushi?
"Samha 'Ya'yana na tina, kuma na samu.mafita, mafitar da zata fissheni, akan kadaicina, inshaa Allahu, amma nima a yau zan maki sallama, zai zama kamar daga yau zuwa kowanne lokaci zaki nemen ki rasa, muje na baki takardun gidannan, da komai dana mallaka anan, na baku shi, ke da Amatullah, mallakin kune yanzu, in kuna so zaku iya dawowa nan, ku bar wancan dan iskan, har sai ya gane kuren shi, akwai abinda na qudurta a raina,amma sai nayi shawara da Fahad,"
Kallon Mamaki Samha ta bita da shi, me take fada ne, ita fa vata taba kawo musu rabuwa a nan kusa ba, amma gashi a lokaci qalilan kowa zai tafi, a barta ita daya a cikin musibar datake ciki, ga shi sun ma Ladeefa alqawarin daina shaye2, anya zata iya cikawa kuwa, baqin cikin ba wanda zata iya jurew bane ba kayan caji.
Tinda Maleeka ta dawo nan da zama, ba
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 5 Chapter of 13