Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
2 / 13
a cikin shekaru qalilan, amma har yanzu kowa tana riqe sirrin rayuwar ta, wanda ina ganin zama da sirri a tsakanin junan mu ba zai bamu damar zama cikakkun amintattun juna ba, kuma ba laifin kowa bane illa nawa, dan haka nayi maku alqawarin jin labari na a yau, inshaa Allahu, dan yanzu banda 'yan uwan da suka fi min ku" Gyara zaman su sukai, tare da tabbatar mata da abinda ta fada gaskiya ne kuma suna sauraron ta, dan haka ta fara magana.. "Kamar yanda kuka ji suna na, Maleeka, to sunan mahaifina Muhammad Auwal, Mahaifiyata Zulfa'u, mu asalin 'yqn jihar Nija ne,mahaifina attajiri ne wanda ya gaji dukiya wajen mahaifin shi, shi kuma ya gada wajen mahaifin shi, kenan dukiyar gado gare mu, mahaifin na da son talakawa, nice babbar diyar shi, daga ni ba su sake haifr wata ba, har na bar gida, mahaifina anyi2 ya qara aure yace ba zai ma mahaifiyata kishiya ba," "Na taso cikin gata da jin dadi, da kwanciyar hankali, tare da tarbiyya da nutsuwa, na fara primary na a makaranta mai tsada, na gama na shiga makarantar gaba da primary, ina ajin farko, Abbana ya dawo da yaran shi dake kudancin Nigeria suke masa kasuwanci gida masu suna da Anwar Fahad, Fahad saurayi ne kyakkyawa, mai nutsuwa da hankali, sai Anwar bai kai Fahad kyau ba amma ya fishi nutsuwa da tsoron Allah, ga tsantseni, kuma yana gudun maganar Abbana, dik abinda bai so basa yi, daga almajiran ta ya riqe su ya saka su a kasuwanci, sai da suka girma Anwar har ya fara tsayawa da qafarshi ma sannan ya dawo dasu dan ya musu aure" "Tin da aka kawo su, na ke yabon kyau na Fahad, Mamana tai ta min dariya tana cewa quruciya ce, wataran aka ce nayi sai na y kuka ko na musa, nakan ce inaa ai ni ba zan taba musawa ba, sai dai tai dariya ta barni kawai," "Ana haka na kai aji uku a secondary, Abbana yayi alqawarin da yari yar shi ta tasa zai mata aure, ba zai bari ta balage masa a gida ba aure ba, in taje gidan mijin ta ta qarasa, lokacin dana ji labarin a daya daga cikin yaran Abba za a min aure fatana bai wuce a ban Fahad ba, a lokacin mun shaqu da shi, ya san ina son shi, shima kuma na san yana so na, sai dai shi bai fadan ba, amma na gani a littafin sirrin shi, ya rubuta hakan," "Kwatsam muna cin abinci a babban parlourn mu da muka saba haduwa dikan mu muci abinci Abbana ya fadi maganar aure na, da Anwar, wanda hakam ba qaramin razanani yayi ba, ya sa na kware da abinda ke bakina, har na tsahon mintunan da ban san iyakar su ba, idona sun yi jawur kamar yanda na kula idon Anwar ya kada, sannan ya tsaida cin abincin nashi, nan Mamana ta ban ruwa na sha, sannan na kalli Abbana zan magana ya dakatar dani, da cewa," "Maleeka ina son ki zama mai biyayya ga iyayen ta, dikkan mai biyayya baya tabewa, Allah na tare da shi, Allah shine zai jibinci lamarin shi, dan haka kiyi hakuri, na sani irin wannan auren da farko baya da dadi ga ma'aurata, amma daga baya suna samun nutsuwa da gamsuwa tare da so da qauna da kwanciyar hankali," "A nan ma na so na ce masa, wadan da ba su da wanda suke so a ran su ake samun hakan, ba ni danake da wanda nake so ba,amma mamana ta katseni, ba su ban dama.ba ko kadan na fadi ra'ayina, sun yanken hukunci sun aurar da ni ga wanda suka so," "Maleeka kar ki ja da maganar mahaifin ki mai biyayya baya tavewa, maza qarasa cin abincin ki ki wuce daki ki wanka zan aike ki, gidan qawata Hajiya Zainab," "Daga kai nayi kawai na tashi, dan banda abinda zan ce kuma,Fahad ma tashi yayi, Anwar bakin shi har kunne dan murna, shima tashi yayi saboda ba zai iya ci gaba da cin abinci table daya da surukan shi ba su kadai," "In taqaice maku a cikin wata uku akai auren mu, komai da kuka sani ana ma 'yar gata an min, gidan mu sama da qasa ne, kuma Anwar ke da shi, sana'ar daya dauka shine yana sai da motoci second hand,kafin daga baya Allah ya buda ya fara saida sabbi, muna cikin rufin asiri sosai, bamu da matsakar komai, a hankali na hakura na fara sabawa da zamana da shi, ba dan ina son shi ba, Fahad kuwa bai fasa hulda da Anwar ba tinda bai fada ma kowa ba dama, sai ya zamana muna zaune kamar wa da qanwar shi, yana zuwa gidana yaci abinci, ya yi hira da Anwar wataran har dani," "A kwana a tashi mun kai shekara daya, ban.da ciki, a shekara ta uku n samu ciki, a zatona soyayyar da Anwar ke nuna min zata qaru ne inaaa sai naga sabanin haka," "Randa ya fara fiton da asalin halin shi, wanda har yau na kasa gane meye musabbabi, amma ina ta'allaqa hakan da aljanun da ke damun shi, ko kuma ciwon da ke damun shi kowanne iri ne, ya dawo da ga aiki da dare, kamar kullum dama duk soyayyar da zamuyi baya son kiss, baya son duk wani abu daya danganci romance, sai dai kawai a yi sex ba wani armashi, ko tana nan na san da ace auren soyayya ne da zan more hakan, jakar hannun shi na amsa na ki daki, na aje, abincin shi da komai n kan dinning, can ya nufa ya fara zubawa, ina zuwa na amsa na ci gaba da zuba masa, bayan na gama na miqa masa ya fara ci, yana gamawa ya shiga wanka, kan ya fito ina kwance da waya a hannu, a nan naga yanda ake koyawa mata yanda zasu sumbaci mazan su, koda ba su so suma zasu yi masu, nai murmushi, dan na san ina da kissable lips da na mai ko sau daya ne zau fara son abun," "Kan ya fito na jefa sweet dina ta watermellon, ina tsotsa, tashi nai danaji ya fito, naje na rungume shi, ya dan ture ni, ban damu ba, fatana na kauda komai na zauna da shi da zuciya daya, rigar shi da zai saka na dakko na saka turaruka, na fara taya shi fesawa a jikin shi, y kwace tiraren ya fesa, ya aje, nan ma ban damu ba, yana gamawa ya haye gado, ya kwanta, sauya kaya na nayi na hau gadon nima bayan na shafe jikina da turaruka masu qamshi, kwantawa nai daf da shi, na fara qoqarin masa wasanni, ya min banza kamar ina taba gunki, a hankali na dora lips dina kan nashi, kamar yanda aka koyar da mu, kamar abin arziqi ya fara responding kawai naji ya hankade ni, ya tura ni na bugu da jikin gado, a kafada ta, nan da nan kuwa wani azababben zafi ya ziyarcen, hawaye suka fara zarya a idona,na rasa jarabar da take damuna tinda na samu cikin nan, shiyasa kullum na ke son sama mana sabon salon gamsar da junan mu, b tare da na kauce hanyar musulunci ba, amma shi ko a jikin shi," "Wai ke Maleeka me yasa kk fiya naci ne? Nace maki bana son wannan iskancin amma bakiji ba, daga yau sai yau kk qara manne min irin haka dik abinda na miki ki kuka da kan ki, banza kawai," "Haka ya tashi ya bar dakin gaba daya ya koma wani dakin, ya barni kwance da matsananciyar sha'awa, haka nai kuka har bacci ya dauken, ga ciwon kafada da ya ke damuna" "Da safe kamar be min wannan rashin mutuncin ba haka.muka gaisa, ya karya ya shirya ya fita, lokacin da Fahad ya zo, bayan ya fita muka sha hirar mu yayi2 na fada masa meke damuna nayi kuka, dan idona ya nuna, haka na kasa fada, dan a ganina sirrin mu ne, ni da mijina, haka ya gana ya tafi," "Yau daya dawo sai ban kula da sai na manne masa va, bayan mun kwanta, cikin dare wajen qarfe 2 na dare na gan shi zaune, sai kallon waje daya yake, na so na masa magana amma na fasa ban san me zai ce ba, bandaki naje na dawo, abun tsautsayi, har na kwanta na sake tashi, dafa cinyar shi nayi sai ji nai yace," "Dauke hannun ki, bar taba ni," "Ban ji me ya ce va na sake kai hannu na dayan na dafa shi, na ce me ke damun ka ne? Ko k kasa bacci ne, ban sake sanin meke faruwa ba sai jin ruwa nai a jikina, tin wani mari daya wanka min," "In taqaice maku magana sai da ya kai Anwar baya baccin dare,kuma kullum sai ya daken, ga ciki,๐Ÿ˜ญ ga shi ya daina kwanciyar aure dani sai ya so, sai muyi fiye da wata daya ko biyu bamuyi komai ba, sannan gaba daya gaban shi ya daina aiki yanda yake yi da, kwata2 ni dai gani nan ne, nayi baqi na rame, sai kowa yace ciki ne," Tinawa da wannan azabar da ta sha ya sa ta fashe da kuka sosai, Samha da Ladeefa ma hawayen tausayin ta suke, rungume ta Samha tai tana buga bayan ta, "Ya isa haka muyi sallah sai mu ci gaba yau nan zan kwana" Murna sukai da sukaji anan zata kwana, sunji dadi, dan haka tashi sukai domin gavatar da sallah su dawo.......... *Cassss maza kuna sha'anin ku*๐Ÿ’…๐Ÿผ MIJIN YA TA KO MIJINA ๐Ÿ’…๐Ÿผ BY HAERMEEBRAERH Page 4: Bayan sun idar ne, suka dumama sauran abincin su a oven, suka zauna suka ci, suka qoshi, Ladeefa ce ta dakko kwalba wadda da ganin ta na san ta wani abun mayen.ce, Samha ta kwace, "Gaskiya ya kamata just for today mu tsahirta ma komai na.maye har sai mun gama sanin junan mu, baki da aiki sai watsa abun maye kin fimu zalama fa besty," Dariya sukai, ita kuma ta bata rai, dan a ganin ta kadan zata dan sha a ci gaba, murguda ma Samha baki tai ta turo harshe tare da kada idanun ta masu haske, ta.ja hannayen.ta.ta nade, wai ita.tayi fushi, ba wanda ya kula ta, illa Maleeka da ta miqa mata chocolate mai dadi , karba tai ta sake murmushi second weakness din ta kenan in ba kayan maye ba. Zama Maleeka ta gyara tare da.dorawa daga inda ta tsaya a labarin nata. "Ba a jima ba mutanen gidan mu suka san halin da muke ciki, nan Abbana ya ce a kaishi a sibiti, ana.kaishi suka duba shi suka gane ciwon rashin.bacci ke damun shi, nan aka bashi magunguna, wanda na bacci ne, daga nan Anwar baya bacci in.ba maganin nan.ya sha ba, daga baya ma ya zamana ko yasha sai ya yi halin nashi,.wato dukana, gashi lokacin cikina ya girma, ni kuma bani da wani dan uwa danake da shi mace da zai zo ya tayani zama, dan haka na shiga maqotana,.suna da wata budurwar yarinya, mai suna Khairat, a lokacin a iya ganina su ne kadai mutanen kirki a unguwar dika, ashe ban sani.ba sune zasu ja na bar komai nawa na dawo nan da zama๐Ÿ˜ญ" Kallon ta sukai gaba dayan su, ta gyada masu kai cikin hawaye sannan ta ci gaba. "Da farko Khairat komai nace tayi yi take, har wanda ban saka ta ba ma, yarinya ce mai biyayya da hankali, kafin kuce mi na fara dawowa hayyacina saboda ba aikin wahala kamar da, har na dinga jin dama qanwata ce, tinda ya hana daukan me aiki sai tana kwana, dik inda dare yayi hankalina ya tashi dan tafiya zatai, mahaifin ta dattijo ne sai yace budurwa kamar wannan bazata kwana.mana ba, ni kuma ina son ta kwana, mahaifiyar ta da suke kira da Habi itace babbar shu'umar da ban san shu'uma bace sai bayan abinda ya faru ya afku, amma a ido in ka gan ta sai ka rantse ko yatsa aka saka mata ba zata iya cizawa ba" "Abbana.ne ya tara mu a gidan mu watarana, bayan na haihu na haifi yaro na.miji, an saka mishi sunan Abbana, muna kiran shi da Amir, nayi arba'in zan koma gidana, Abba.ya umarci Fahad daya koma gidan mu ya zauna a qasa kafin yayi aure, saboda yanzu ciwon Anwar ya yawaita, jikina kamar yanda kuka ga tabo ko ta ina haka in ciwon shi ya tashi ko giftawa nayi sai na ci duka,ko yayi ta jefe2n abubuwa, kuma ba damar na hana shi, abun ya zama.masa kamar me tabin.hankali, amma da rana sak zaki gan shi.bai da wata damuwa," "Ran da Fahad ya tare na kula da ba haka Khairat ta so ba ita da Habi, amma sai naga su a su wa to? Ko bi ta kan su ma ban ba, na rasa me.na masu haka kawai sai suka fara janye min, nayi tambayqr duniya sunce ba komai, Fahad shike kula da komai, wataran har shara yake mana ta tsakar gida, Anwar ko kula mu baya yi, sannan rabon da ya kusanceni har na manta, a duniya banda wanda nake qanwace da shi ya san sirrina kamar Fahad, dan haka da shi nake shawara, in ya rasa shawarar da zai ban sai yayi ta ban hakuri, yana nuna min yanda matan sahabbai da annabawa ke hakuri a gidan mazan su, saboda haka sai naji hakuri ya shigen, bana sake tada maganar," "Sai da Amir ya shekara daya da watanni, amma Anwar bai sauya hali ba, hakuri na ya gaza,inna zauna ina tinanin da yanda yake tattalina sai naji a da ina da dalilin zama da shi saboda ya na tattalani dik da bana son shi, amma ba zai yu ba.yanzu ba wani abu dake shiga tsakanin mu ga duka da rashin mutunci kuma na zauna, ko shawara da Fahad ban ba na je.na samu Abbana.da Mama na fada masu komai, suka ban hakuri suka ce na dawo zai sauya ne, haka na koma gidana, cikin takaici," "Dake da rabon Amrah, watarana ya dawo aiki, na fito wanka, ya shigo, ina sake da wata guntuwar riga, iya cinya, ina taje gashin kaina, naji ya amshi cumb din, yana tayani, yana shafa wuyana, abin ka da an dade ba a hadu ba, nan da nan jikina ya fara responding, cikin qanqanin lokaci mukayi saduwar aure, yana gamawa ya.miqe, ya.shige wanka, ni kuwa a zatona hakurin da iyayena suka ce naje nayi ne Allah ya sauya min komai, dan haka cikin jin dadi na qanqame pilon dake kusa dani, ina nan kwance naji alamar ya gama wankan tsarki yana na sabulu, tsautsayi ya sa na tashi na shiga.bandakin, domin muyi wanka tare, ina shiga ya qanqame jikin shi, yana min ihu na fita, na fita, dariya ta kamani, nace masa meye hakan?.yanzu fa muka gama sex meye najin kunya, ina karairaya na isa gare shi, da kumfa da komai a jikin shi ko daurayewa bai ba ya hau ni da jibga kamar jaka, sai da nai dana sanin wannan ranar gaba dayan ta, a wajen ya bar ni cikin jini, ta baki da hanci ya wuce, jiki ba kwari nayi wanka na fito, na saka kayana" "Fahad daya ga fuskata da safe, masifa ya fara na ya.gaji da ganina a haka, zai dau matakin da ba zai.ma kowa dadi ba, daidai lokacin Khairat ta shigo, wai ta kawo min kuka daga wajen Maman ta, da suka je qauye, tsayawa tai tana kallon Fahad kan ta ban saqon ta fice, haka na ci gaba da bashi hakuri, daga baya ya min.nasiha ya fice cikin fushi," "Bayan wata hudu ciki ya bayyana a jikina, nan fa mahaifana sukai ta murna, amma banda Anwar, na rasa dalilin dayada baya irin murnanr nan ta iyaye maza in sunji matan su na da ciki, ban damu ba.tinda na Amir ma haka akai, na ci ga a da rainon cikina," "Ranar da ba zan taba mantawa da ita ba a rayuwa ta itace ranar da komai ya faru, ina zaune a dakina, Fahad ya saba shiga ko ina na gidan sai dai zai yi sallama da neman izini, kan ya fita na bashi saqon zogale da rama nai tsami, da quli dakakke, ya dawo yana ta sallama ina bacci, a zaune, nayi tagumi da hannuna, ba ma a dakina bane ba kuma dakin Anwar bane, wani daki ne na daban, a gidan, na dawo nan ne saboda Khairat da take mana share2 tace.yau na musamman zatai, dan haka na dawo nan na zauna, sallama yake tayi yaji ban amsa ba, sai ya leqa kan shi ya ga ina bacci a zaune, tausayina yaji, ya shiga ya dau pilo ya daki qafata da shi, ina bude ido danaga shi ne sai nayi dariya nace masa yanzu fa na zauna baccin ya dauken, bai ce komai ba ya ajen leda ta. Ya nuna min da hannu ya fara tafiya zai fita sai qarar qofar mukaji alamar an rufe ta da qarfi kuma ana saka mata key, da sauri Fahad ya kallen yayi magana da qarfi," "Waye anan? Da mutane a ciki fa a bude," "Ina kyauta ta zaton dariyar Habi da Khairat najiyo, ban sake jin komai.ba,haka muka zauna muna jiran Anwar ya dawo dan ya bude mu, a tamu wautar ai kowa ya san ba abinda ke tsakanina da Fahad sai zumunci, ko a jikina, na kwada zogalena da rama a leda, da ruwan toilete, na ci abuna, Fahad ne ya fara min fada," "Ke fa baki da hankali,me kk tinanin mutane zasu ce daga ni sai ke a daki, kuma a rufe, hankalin ki kwance baki san sharrin da aka shirya mana ba ko?" "Relax bro ba wani sharri, ko sharri aka mana n tabbata Anwar zai yafi kowa sanin halin mu, ba yanda za ai ya zarge mu da komai, musamman in muka masa bayani," "Kauda kai yayi, bai ce min komai ba, muna haka mukaji buga qofar parlour da qarfin gaske, sannan tafiya cike da qarfi ake tafiyar, cikin bacin rai ake qoqarin bude qofar , a sannan zuciyata ta fara bugawa, da dikkan alamu ba mutum daya bane a wajen, qofa na qarasa budewa naga Abbana, Mamana, Anwar, sai Habi da Khairat," "Cikin bacin rai na kalli Khairat zan magana, wasu maruka naji da ban san daga ina suka fito ba, Fahad kuwa shi da Anwar suka dambace, Anwar na kiran shi green snake, da sunaye kala2, yana fada masa ai ya dade da sanin yana sona dama, amma ya zaci komai ya wuce, ashe yana da mummunan nufi, Khairat sai kuka take tana bada hakuri, wai da ta sani da bata bayyana abinda ya dade yana faruwa ba, tsayawa nai cak ina kallon ta dan tsoron mutum daya kama ni, a nan take, naji mutum ba abin yarda bane ashe," "Allah ya isa tsakanina daku, kuma ki nemi uban cikin jikin ki amma ba nawa bane, na sake ki saki uku, bani ba ke, Abba in Fahad bai bar gidannan ba, ni zan bar ku har abada," "Cike da fushi ya bar wajen, Abba ya kalli Fahad ya bashi umarnin ya koma Abuja da zama, gidan shi na can, ya ci gaba da kula da kasuwancin can kar ya sake ganin shi a inda muke, ina ji ina gani Fahad yamin kallon qarshe ya fice,kuka na saki na rashin madafa, Mama ce ta jani kamar akuya har waje, fizgewa nai na dakko hijabina, ta kallen," "Wane hijab kuma zaki saka?bayan kin gama yaye hijabin naki a gaban duniya? Kin cuceni, kinci amanar yandar dana miki, ni da mahaifin ki, meye amfanin ki a duniya?" "Tin ina kuka har na kasa kukan, na so cikin Amrah ya zube, na huta, amma Allah bai nufa ba, haka na koma gidan mu a wulaqance a qasqance, masu aikin gidan mu dana maqota sun fini daraja, gashi sunqi barina nayi bayani, daga baya na gane ko nayi masu bayani ma ba mai fahimta ta, ba zasu yarda ba, dan haka na ja nai shiru, wata tara na yi na haifi Amrah, ban yaye ta ba, Mama ta sa na zama yar aikin gidan, aka sallami ma'aikatan gidan, wahala ta sa na fara shaye2 ganin haka Mama ta ce wataqila ban daina yawon ba ko wani cikin garen, tinda kull bacci nake, da jin haka raina ya baci, da asuba na tattara komai nawa na bar gidan, ga kudi dana diba wanda ni kaina bansan iyakar shi ba, ina da account, kuma cike yake da kudi, tinda Abbana na zuban dukiya ni daya ce diyar shi tall, a da kan Anwar ya sauya hali yana zuban, daga baya ya daina, Fahad ke saka kudi, har yanzu danake mku bayani bai daina ba" "Bayan na bar gidan na kama gida, na zauna, na saka kaina a makaranta, na kammala secondary, dana gana na shiga jami'a shine muka hadu daku, har yanzu inna so ganin iyayena nakan labe na hango su daga nesa, da yarana, Anwar ne kawai bana kalla saboda bana qaunar ganin Khairat a rayuwa ta again," "What! Kina nufin ki ya aure ta?" Murmushin takaici tayi ta daga kai, alamar Eh, Samha lumshe idon ta tai, ji take jikin ta har rawa yake dan takaici, wato saboda ta auri Anwar ta hada ma Maleeka sharrin nan na zina da aure????........ *Duniya kenan, mutanen banza suna sawa ana tsoron mutanen kirki*๐Ÿ’…๐Ÿผ MIJIN YA TA KO MIJI NA ๐Ÿ’…๐Ÿผ BY HAERMEEBRAERH *Ina godiya da addu'o'in ku, ina ma kowa fatan alkhairi, Allah ya kiyaye mu ya kare mu daga sharrin zamani, jazakumullahu bi afdhadul khair* Page 6: "Wai ya naga yau gaba daya ko bacci bamu da alamar yi ne, dare fa yayi," "Wanne bacci mutum yaji wannan labarai na tashin hankali? Sannan ai ba wani daren da yayi sosai akan yanda muke bata lokaci a banza ma" "Besty ni dai yunwa nake ji, ina mamakin masu aiki a gidan redio, wataqila suna gama labarai suke zuwa cin abinci," "Ba wani nan ke dai dake rumbu ce komai a zuba shiyasa kk ji haka," Kokawar wasa suka kaure da ita da kyar Maleeka ta shiga tsakanin su, Ladeefa miqewa tai taje fridge din su ta kwaso masu cimar zaqi kala2, da fruits, ta hado da ragowar cake din da sukai baking, ta zuba a tsakiyar su, ta zauna, cinyoyin ta duk a waje, duka Samha ta daka mata a guda daya ta kalle ta, ita kuwa a furgice ta fara sosawa tana neman ba'asin dukan, "Malama wannan wai banawa bane? Wayace ki dakko da shi," "Shine zaki min wannan dukan kamar an danan iron naji, an dakko din, kuma kin san Allah kin gama ci kenan," "Tabbb ko a ban naci ko na fasa fadan labarin" Da sauri ta tura mata gaban ta har sauran abubuwan da ta debo, dariya sukai, sannan suka fara taba kayan ciye2n at the same time Samha ta fara magana. "Ku kunji dadi koma me ya faru kun taso cikin gatan ku, da dukiya da wadata, amma mu, hummm mu, daga wahala sai baqin talaouci daya mamaye zuri'ar Dan Kano, haka ake kiran kakan mu, wanda yake da yara hudu, maza, Abbanmu shine qarami, a cikin su dika, Abbana shine mafi talaucin cikin su, komai sai 'yan uwan shi sun taimaka masa, hatta aure yi.masa kawai akai, amma ko sana'a ya kama ba abinda ke zama masa, Umman mu itace suke da dan abin hannu, ita da Yayan ta namiji, da yayar ta mace, sun gaji gonaki da wasu kudade wajen iyayen su, dan haka Ummana da dangin ta, Kawu Abu, da Inna Samirah, suna taimakawa, amma muna shan gori sosai, wajen su, su basu da yara a lokacin, dan haka suke cewa Umman mu tana ta zuba yara ga shi mijin ta talaka bai da halin riqe mu, a dole suka kaita aka juya mata mahaifa dan kar ta sake haihuwa, Abbana bai da tacewa saboda da yayi magana za a zage shi tass, saboda talaka ne shi," "Da sanyi ana yawan yin gobara, a wannan lokacin ne gidan su Abbana ya kama da wuta, 'yan uwan shi dika ba wanda ya tsira, har mahaifin shi, sai mu kadai, dake dakin mu ne na qarshe, amma kunsan me mutane suka ce? " Girgiza mata kai sukai, nima da nake rakube na girgiza qaton kaina irin na Mum Sultan๐Ÿคฃ. "Cewa ake tayi Abbana

Chapter 2 of 13