BY HAERMEEBRAERH
Page 17:
"Mum ta dauke ta kamar diyar cikin ta, dan kwata2 bata nuna mata kishi, haka Aunty Amarya ma, kamar yanda muke kiran ta, dan da kadan zata girmi Heeshaam"
"Ni bana ko kula ta, amma ta maqale min, dan iyayi har wani qaramin dana take ce min, Mum in tayi fushi da ni, akan dadewar dare danake, ita zata zauna har sai na dawo ta ban abinci, sai taga na shiga dakina ta kwanta, koda kuwa Dad a wajen ta yake,ta haka ta sake samun waje a wajen Dad, Heeshaam na jin labarin ta a wajena sosai, ina nuna masa yanda take ban haushi, Heeshaam yana min dariya sosai yakance,"
"Broth meye na jin haushin ta, she just want to be frends with u, ko kana son ta dinga maka halin kishiyoyin wannan zamanin, kuna zaune da iyayen ku ta raba ku da su?"
"Kai rabu da ita, a matsayin da take ai ba wani maganar freinds, kawai tai harkar ta nayi tawa,"
"K broth, ka gaida min ita, na duk sanda na zo zaka ga yanda ake abota da matan uba lfy qalaou zamu zauna,"
"K sai ka dawo din ina gefe na sha kallo,"
"Kafin ya kashe mukaji bugun qofa ta, kallon qofar nayi daga jin qamshin na san ita ce,kallon waya ta nayi nace ma Heeshaam, she is here bye,"
"Sallama mukai ta bude ta shigo, wasu masifaffun kaya ne a jikin ta, riga da wando, sun masifar fidda dik wata gaba ta jikin ta, kamar sai da aka auna ta akayi su, gashinnan ta baza shi ya sha kwalliya, ga qamshi tana zubawa, ban san dalili ba duk son matana bata birge ni ba, dan na san itan.mallakin Dad ce, leqowa ta dan yi tana kada qirjin ta,"
"Dinner is ready, ya kamata ka sakko,tin dazu kana daki kamar amarya, ko ni da nake amaryar na fito balle kai,"
"Ko kallon ta ban sake yi ba nace gani nan zuwa, ta qi tafiya wai sai na je mun tafi, wata tsawa na daka mata nace bazan je ba na fasa cin abincin ma dole ne?"
"Kamar mara zuciya haka ta shiga dakin tana son ta ban hakuri na kore ta, fitar ta a dakina Dad ya fito shima, gyara rigar ta ashe ta hau yi, ta ce ma Dad wai kirana ta zo yi cin abinci,amma sai masifa nake, Dad ya rasa me zai yarda dashi, ga yanda ya gan ta, sannan ga gyaran riga tana yi ta kuma.fito daga dakina, ni din da kowa ya san bana ganin mace na kyale, Dad gyada mata kai kawai yayi, ya wuce, a wajen cin abinci Dad baya da wata walwala, na yi ta masa magana kamar yanda muka saba sai dai yace immmm yace a'a, na rasa meke faruwa, gani nayi Aunty Amarya tayi murmushi, dan da alama taji dadin hakan,"
"A taqaice sai da Amaryar Dad ta shekara ba ta da ko ciki, tin daga nan Mum ta fara zargin ko tana son wani abu ne ba zaman aure ne ya kawo ta ba, Mum na fada min ban bada hankalina ba, ana haka na kammalla karatuna, Heeshaam ya dade da fara aiki a asibitin da Dad ya bude mana ni da shi, ni kuma nace sai shekara ta sama zan fara zuwa, Dad ya biye min, Mum tayi2 amma naqi, haka ta hakura, kudi kuwa a account dina basu yankewa, Dad na bamu kudi kamar albashin shi akan mu ya qare, gidaje Dad ya sai mana manya,iri daya, a kus da juna saboda muyi aure mu saka matan mu, ko zan daina shashancin bin mata, amma inaaa, Heeshaam yaqi aure, ni kuma nace sai yayi zan yi, Dad yayi fadan har ya hakura dan dole,"
"Ana haka wata rana na yi dare na dawo, ina tafe ina waya da babe din dana gama harka da ita, tana fadan yanda take ji kamar ta dawo mu kwana, ina tafe ina qara jaddada mata irin dadin da take da shi, kawai ban ga zuwan ta ba na shiga dakina sai ji nayi an fado jikina kamar dama a dakin take, juyawa nayi da sauri zan magana ta rife bakin mu waje daya, magana ta fara a gaggauce tana shafani, tana qoqarin cire kayan ta,"
You'll also like
DENIAL by helxiq
DENIAL
305K
6.8K
I was drowning in her kiss. The intensity of it filled me with sensations I'd never felt before. I taste her and I realize I've been starving. I have loved before, but n...
๐๐ก๐ ๐๐ข๐ฌ๐ฆ๐๐ญ๐๐ก๐๐ ๐๐ฎ๐ฉ๐ข๐ by ruuxwrites
๐๐ก๐ ๐๐ข๐ฌ๐ฆ๐๐ญ๐๐ก๐๐ ๐๐ฎ๐ฉ๐ข๐
270K
34.5K
๐๐ก๐ ๐๐ซ๐ ๐ฎ๐๐ ๐ฅ๐ข๐ค๐ ๐ข๐ญ ๐ฐ๐๐ฌ ๐ ๐ฌ๐ฉ๐จ๐ซ๐ญ. ๐๐ ๐๐ฅ๐ข๐ซ๐ญ๐๐ ๐ฅ๐ข๐ค๐ ๐ฅ๐จ๐ฌ๐ข๐ง๐ ๐ฐ๐๐ฌ ๐ฉ๐๐ซ๐ญ ๐จ๐ ๐ญ๐ก๐ ๐ ๐๐ฆ๐. ๐๐ก๐ ๐ฐ๐จ๐ซ๐ฌ๐ญ ๐ฉ๐๐ซ๐ญ? ๐๐ฏ...
๐๐ฃ๐ซ๐๐๐ก๐๐ ๐๐ง๐ค๐ข๐๐จ๐๐จ - ๐๐๐๐๐ค๐ฌ ๐๐ ๐๐ค๐ฌ๐จ by Deewanixwriters
๐๐ฃ๐ซ๐๐๐ก๐๐ ๐๐ง๐ค๐ข๐๐จ๐๐จ - ๐๐๐๐...
6M
549K
AKSHAT SINGHANIA - A literature professor in Singania Institute of Arts and Commerce. He is soft and caring person with a tough exterior, who doesn't believe in love or...
The Malhotras by ritikaauthor
The Malhotras
1.8M
152K
This is a story of four brothers. The brothers who are ready to sacrifice their lives for each other in childhood but what will happen when they grow up and find their...
Busy Bee by SummerMaung
Busy Bee
317K
14.5K
แแแบแธแแญแฏแแพแแแปแ
แบแแญแแแบ แแญแฏแแบแแฐแธแแฑแแญแฏแทแแฒ แแซแแฑแแแทแบ แแปแ
แบแแญแแฑแฌแทแแแบแธ แแฐแธแแแฌแแซแแฒ Beeแแแบ Start Date - 13.9.2025 End Date -
My boy friend and His Friend by Angelina5522
My boy friend and His Friend
909K
22.8K
แแญแฏแแบแแปแ
แบแแฒแทแแฐแแฒแท แแฐแแปแ
แบแแฒแท แแฐแแแบ แแปแแบแธ (แ
แฌแแฏแถแธแแแพแฌแธแแซแแฐแธแแแแบแแฑแธแแฌแธแแฌ) Semeแแแญแฏแแบแธแแซแแแบ แแญแฏแธแแซแแแบ แแผแญแฏแแผแฑแฌแแฌแธแแฌแแซแแฑแฌแบ
๐๐๐๐๐๐๐๐๐ ๐๐
๐๐๐๐ โก (Under Editing) by TaleweaverEmber
๐๐๐๐๐๐๐๐๐ ๐๐
๐๐๐๐ โก (Under Ed...
2.1M
152K
๐๐ช๐ฎ๐๐ญ๐ข๐จ๐ง๐ฌ ๐๐ ๐๐จ๐ฏ๐ ~๐จ ๐ฏ๐๐๐๐๐๐๐๐๐ ๐น๐๐๐๐๐๐ ๐บ๐๐๐๐ โขโยฐ.โพโ.เณเฟ*:โ๐ ๐๐๐๐๐๐ โก ๐๐๐๐๐๐๐๐ Ruhanika, a quiet introvert with a pa...
"Dan Allah Suhail love ka taimaka min, na auri mahaifin ku gaba daya baya biya min buqata ta yanda nake so, Suhail kai ne namijin da zuciya ta ta amince da shi, ka ban hadin kai, dik dukiyar dana mallaka wajen mahaifin ka zan baka ita,plsss"
Gaba daya ta birkitamin lissafi na, amma a haka na qoqarta controlling kaina, na tura ta baya, ina qoqarin magana kamar mayen qarfe haka ta sake manne mana jikin mu waje daya, tana wani rausaya a jikina, jana tayi na fada jikin ta, daidai nan qofa ta bude, kuka ta saka, ta miqe da gudu ta fada jikin Dad, tana cewa,"
"Dama na fada maka nemana yake, ban amince masa ba, daga dawowa na aje masa abinci ya dakko ni kamar wata yar tsana ya toshe bakina, Allah na gode maka bai ida nufin shi akaina ba kazo, yau dana shiga uku, ina auren uba da na nemana, wayyo Allah, wannan wane irin gida ne dole ne na sanar da mutane su san yanda gidan ka yake,"
"Dan mamaki da tsoron yanayin da naga Dad, kasa magana nayi, iya firgita na firgita, wannan wace irin masharranciyar mace ce haka? Ban tava neman ta ba, amma here she is, tana min sharrin dama na saba, da sauri Dad y furta kalmar da ta yi sanadiyyar qara lalacewa ta, ta sa na ke aikata dikkan wani iskanci dana so, wato nan take Dad ya tsine min,ya koren a gidan shi, sannan ya tsugunna yana bata hakuri, Mum na zuwa taga meke faruwa ta tabbatar ban aikata abinda ake zargina da shi ba, amma ta ja bakin ta tayi shiru,akan umarnin Dad, na in tai magana a bakin auren ta, Heeshaam ma in yayi magana zai bini, Amarya sai kuka take tana jijjiga, ita sai ta sanar da duniya halin da ake ciki, da gudu ta bar wajen, Dad ya bi ta a gujen shima, yana ta rufa masa asiri a matsayin shi na dan siyasa, qi tayi sai da ta nemi miliyoyin kudi sannan ta nemi saki, wai ba zata iya zama da shi ba, kar wataran daya dan ya neme ta, Dad naji na gani ya sake ta saki daya,sannan ya bata million goma, ta saka a akwatin ta ta kwashi sauran kayan ta tayi gaba, a cikin daren, ina ganin ta fita nima na dau key na fice, dik inda ta shiga nima nan nayi, har muka isa wani gida qarami mai kyau, nan naga ta fito, ba ko mayafi, yanda ta fito daga gida haka take yanzun ma, tana shigar da motar ta na shige nima, nan hankalin ta ya tashi, zuwa nai gavan ta nace,"
"Kar ki damu, kawai fitowa zaki ki qarasan abinda kk fara, dan ba zaki min sharri a banza ba ki karbi kudi a banza, tinda kk tadani tsaye sai kin zaunar dani,"
"Cikin takun 'yan duniya ta qaraso gabana, tana shafani daga sama har qasa, kasa jurewa salon ta nai, sai da muka shiga ciki mukayi masha'a da ita, tana bacci na kwashe komai, har da wasu kudin nata na fice, tin daga ranar ta koya min sabon salon neman mata, bayan na koma gidan da Dad ya sai mana, na zauna, daga baya naga zamuyi kusa da mutan gida zamuna haduwa, kawai na saida shi da kudi mai yawa, na tattara kudina na maka account dina, na hau jirgi sai Kano, ina zuwa Kano na sai gidannan, sannan na zama ina neman manyan matan garinnan, naje har gida ko hotels,na biya musu buqata su ban kudi maqudai na dawo gida ko randa muka hadu ma na kwana ne a gidan diyar mataimakin gomnan garinnan ne, ta cika ni da kudi, ina komawa gida muka hadu,"
"Na so dana tashi auren ki, na sanar da Dad, tinda naji labarin ya gano qarya tamin, da satar da ta masa na takardun kadarorin da bai san na dauke ba, yanzu haka suna wajena, ya nemen sama ko qasa,naqi komawa, Heeshaam har canja asibitoci yayi daga gari zuwa gari ko Allah zai sa mu hadu, amma naqi bari mu hadu, ance yanzu haka yana Kano, iyaka ban san ina yake ba ne,"
Yana kaiwa nan ya daga kai yana kallon Amatullah da tai bacci,yana ta zuba, wani haushi ne ya kama shi, anyways ya cika alqawari , ita ta sani, in dai ta tashi tace bata ji ba ba zai maimaita ba.
Taba ta yayi, yace,
"Ashe bacci kk bama kiji me nake ta fada ba,"
Cikin sauri tace a'a naji ka mana, naji sanda kace, Heeshaam na kano,"
Murmushi yayi, ya tabbata ta ji shi, wata qila bata dade tana baccin ba.
"So yanzu dai da dan sanata nake tare;nake aure kuma? Ba tare da na sani ba, to dik naji me kace,kana nufin shine dalilin daya sa bakai tinani ba, baka yi nazarin hakan ya haramta ba, ka nemi qanwata, saboda ka kwanta da wadda baban ka ya kwanta da ita?"
Baiji dadin kalaman ta ba amma ai shi yaja ma kan shi, daga kai yayi, a hankali,
"To a gaskiya zan fada maka wata magana, daga yau sai yau, ina son ka min alqawari, ba zaka sake aikata wannan mummunan aikin va, sannan zamuje mu bawa Samha hakuri, kuma mu dawo da ita gidannan, d kan mu, bayan nan zamu dunguma zuwa Abuja, domin bawa iyayen ka hakuri, ka maida ma Dad kadarar shi, ina son na haihu wajen surukata ta zama uwa a garen, tinda ban da uwa,"
A firgice ya miqe,
"Kina da hankali kuwa? Me zan koma nayi, ko baki san me ake kira da tsinuwa bane? Ba inda zani ni, ina da kudi, ina da dukiyar da zata ishemu rayuwa koda na bar sana'ar danake yanzu, zan iya ci gaba da aikin asibiti na, kima daina wannan maganar,"
"K fyn na daina wannan maganar,ka sani yaune gani na qarshe da zaka min, gwanda na haifi dana ba uba dana zauna da uba kamar ka,"
Cikin tsananin baqin ciki ta tashi ta hau hada kayan ta...........
*Cassssss wace shawara zaku bawa Amatullah in yace ba zasu ba?*
*Dazu diyar ku ta batan caja, wataqila gobe ku jini shiru, ban dai sani ba, in anjini shiru lfy ta qalaou matsalar caji ne, thanks*Page 18
1K 57 0
by Haermeebraerh
Following
Share
๐
๐ผ MIJIN YA TA KO MIJINA ๐
๐ผ
BY HAERMEEBRAERH
*This page is for u my group members, i really appreciate ur comments and du'as, Allah ya barmu tare da alkhairi, much loveโค inji Haermeen Haermmaerh๐๐ป*
Page 18:
"Wai me yasa yanzu kk min abinda kk ga dama ne? Ko dan kin ga ina matuqar son ki? Ko dan kinga yanzu shiriya ta sameni kin san komai nawa shiyasa kk ganin zaki iya ci min fuska ko ki wulaqanta ni?"
Kallon shi tayi tare da sassauta fushin ta, ta aje rigar da take ninkewa zata saka a akwatin ta, ta taka gaban shi, riqe hannayen shi biyu tayi, yaso ya fisge amma kallon da take masa ba zai bashi dama ba, kwantar da kan ta tayi a qirjin shi, tana shafawa da hannin ta daya,
"Suhail ba haka bane, ina son ka gane dik abinda ka lissafa banda burin yi maka daya daga cikn su, ina son ka gane cewar mahaifin ka ya gano kuskuren shi, yana neman ka, mahaifiyar ka da take ta yarda da kai tin fari baka tinanin ya zafin rashin da yake? Ya kk jin zafi a ran ka in ka nemi wani abu ka rasa, ko ka manta yanda ka sha dambe da Samha a gidannan, don neman biyan buqatar ka ka rasa, ya zuciyar ka ta maka,.......
"Plssss Amatullah ki daina dawo da abind ya wuce, tsananin jahilci da son zuciya ne ya kaini neman qanwar ki uwa daya uba daya, dan Allah ko me za ai daga yau ki daina dakko wannan maganar abun na dukan zuciya ta,ni yanzu kunyar hada ido da Samha nake ma, inna gan ta nace mata mi?"
"Ka ce mata Samha koyi hakuro da dikkan abinda ya faru,inshaa Allahu ba zaki sake ganina da wata ba ma balle na neme ki, faqat an kashe boss ko ya kace mijina?"
Ta qarasa maganar tare da dukan qirjin shi da dunqulallen hannun ta, ta daga masa gira.
"Wannan ai wayon duka ne, kice kawai baki huce ba shine kk daken, in bai ishe ki bama qara ga qirjin nan sai na cirs rigar ki daka,"
"Haba? Cire ka gani ban huce ba,"
Aiko cire rigar yayi, vata bata lokaci ba wajen kai ma qirjin shi naushi iya qarfin ta, qara yayi ya riqe wajen, yana tari,
"Auchhhh Amatullah zaki kashe me rai, irin wannan naushi haka, da dikkan alamu kin dade kina imagening yi min irin shi,"
"Ohhhh yes na dade ina hango ni ina kirba maka naushi kamar haka,"
Naushin shi take tayi yana gudu tana bin shi, sai da suka hada zufa ta gaji ya dauke ta ya dora kan cinyat shi, yana shafa bayan ta,sai lumshe ido take tana maida ninfashin ta dake sauri,
"Yanzu dai kin huce ko?"
"Ya dangan ta da inda kace mu fara zuwa sai kaga hucewa ta, dan Allah muje ka min wanka ma, na gaji ba zan iya ba, gashi ka sa nayi zufa๐"
"Yes ma'am ur wish is my command, muje,"
Daga ta yayi, ya sauke ta qasa, ya riqe ta ta gefe anan sika cire kayan su dika suka shiga wanka, a karo na biyu,, anan ma sai da suka taba wasan da tin tana amarya ma basu taba irin shi ba.
(Ina fatan kun fahimci wani abu a wannan fadan na masoya, a dik sanda aka samu sabani tsakanin miji da mata, zama a tattauna matsala na sake saka wani bond mai qarfi tsakanin ma'aurata wanda a da ba a da shi, sabanin a yi ta ririta magana, ba a zauna an tattauna ba kowa ya fuskanci kowa, ko a zontattaunawar kowa ya riqe ego, baya son ace shine baida gaskiya, in ka saukar da kan ka kuka fahimci junan ku kai ke da riba, ga dai Suhail ya samu ribar yi mata wanka, kowa dai ya san yi ma mace wanka akwai ribaaaaa๐คฃ๐๐๐๐๐๐ปโโ)
You'll also like
DENIAL by helxiq
DENIAL
305K
6.8K
I was drowning in her kiss. The intensity of it filled me with sensations I'd never felt before. I taste her and I realize I've been starving. I have loved before, but n...
๐๐ก๐ ๐๐ข๐ฌ๐ฆ๐๐ญ๐๐ก๐๐ ๐๐ฎ๐ฉ๐ข๐ by ruuxwrites
๐๐ก๐ ๐๐ข๐ฌ๐ฆ๐๐ญ๐๐ก๐๐ ๐๐ฎ๐ฉ๐ข๐
270K
34.5K
๐๐ก๐ ๐๐ซ๐ ๐ฎ๐๐ ๐ฅ๐ข๐ค๐ ๐ข๐ญ ๐ฐ๐๐ฌ ๐ ๐ฌ๐ฉ๐จ๐ซ๐ญ. ๐๐ ๐๐ฅ๐ข๐ซ๐ญ๐๐ ๐ฅ๐ข๐ค๐ ๐ฅ๐จ๐ฌ๐ข๐ง๐ ๐ฐ๐๐ฌ ๐ฉ๐๐ซ๐ญ ๐จ๐ ๐ญ๐ก๐ ๐ ๐๐ฆ๐. ๐๐ก๐ ๐ฐ๐จ๐ซ๐ฌ๐ญ ๐ฉ๐๐ซ๐ญ? ๐๐ฏ...
๐๐ฃ๐ซ๐๐๐ก๐๐ ๐๐ง๐ค๐ข๐๐จ๐๐จ - ๐๐๐๐๐ค๐ฌ ๐๐ ๐๐ค๐ฌ๐จ by Deewanixwriters
๐๐ฃ๐ซ๐๐๐ก๐๐ ๐๐ง๐ค๐ข๐๐จ๐๐จ - ๐๐๐๐...
6M
549K
AKSHAT SINGHANIA - A literature professor in Singania Institute of Arts and Commerce. He is soft and caring person with a tough exterior, who doesn't believe in love or...
The Malhotras by ritikaauthor
The Malhotras
1.8M
152K
This is a story of four brothers. The brothers who are ready to sacrifice their lives for each other in childhood but what will happen when they grow up and find their...
Busy Bee by SummerMaung
Busy Bee
317K
14.5K
แแแบแธแแญแฏแแพแแแปแ
แบแแญแแแบ แแญแฏแแบแแฐแธแแฑแแญแฏแทแแฒ แแซแแฑแแแทแบ แแปแ
แบแแญแแฑแฌแทแแแบแธ แแฐแธแแแฌแแซแแฒ Beeแแแบ Start Date - 13.9.2025 End Date -
My boy friend and His Friend by Angelina5522
My boy friend and His Friend
909K
22.8K
แแญแฏแแบแแปแ
แบแแฒแทแแฐแแฒแท แแฐแแปแ
แบแแฒแท แแฐแแแบ แแปแแบแธ (แ
แฌแแฏแถแธแแแพแฌแธแแซแแฐแธแแแแบแแฑแธแแฌแธแแฌ) Semeแแแญแฏแแบแธแแซแแแบ แแญแฏแธแแซแแแบ แแผแญแฏแแผแฑแฌแแฌแธแแฌแแซแแฑแฌแบ
๐๐๐๐๐๐๐๐๐ ๐๐
๐๐๐๐ โก (Under Editing) by TaleweaverEmber
๐๐๐๐๐๐๐๐๐ ๐๐
๐๐๐๐ โก (Under Ed...
2.1M
152K
๐๐ช๐ฎ๐๐ญ๐ข๐จ๐ง๐ฌ ๐๐ ๐๐จ๐ฏ๐ ~๐จ ๐ฏ๐๐๐๐๐๐๐๐๐ ๐น๐๐๐๐๐๐ ๐บ๐๐๐๐ โขโยฐ.โพโ.เณเฟ*:โ๐ ๐๐๐๐๐๐ โก ๐๐๐๐๐๐๐๐ Ruhanika, a quiet introvert with a pa...
Bayan sun fito sun shirya suka shiga kitchen yi ma kan su girki, a tare suke komai cikin so,qauna, tausayi, girmamawa, da kulawa.
Sun tsaida magana akan za su je su dakko Samha, amma sai sun sha amarcin su da ba su mora ba, dan haka tai ma Samha text akan Suhail na gida kwana biyu amma in ya fita zata sanar da ita.
Samha tayi mamakin saqon taso bin diddigi amma ta share, dan ta san yanda Amatullah ke son Suhail, kuma ga alqawarin da ta mata na kare ta a wannan lokacin,wata qila bata son wani abu ya hada si zama waje daya ne, ko dake itama bata son hakan.
โกโกโกโกโกโกโกโกโก
Soyayya ce mai qarfi tsakanin Dr Heeshaam da Ladeefa, Maleeka da Fahad, Fahad ya maida Kano kamar unguwa, zuwa yake anytime,Ladeefa kuwa hae asibiti take kai ma Heeshaam abinci, ya sanar da ita iyayen shi na Abuja da zama, amma bai sanar da ita cewar ya zo ne saboda neman dan uwan shi, tayi mamakin kasancewar shi dan babban mutum amma yana abu kamar ba hakan ba, komai na shi akwai tsari da tarbiyya a ciki, gashi da riqon addini, bayan lalurar allura da ya mata bai taba riqe mata hannu da sunan soyayya ba, yana da qoqarin kiyayewa, ba dan a ran shi ba wannan kwadayin ba, inda za a shiga kan shi a ga me yake saqawa ma da sai dai a kame baki, amma saboda tsoron Allah yana jiran sai randa ya malleke ta zai nuna mata dikkan abinda ke zuciyar shi.
โกโกโกโกโกโกโกโกโกโก
Anwar ne a zaune a qaton gidan shi da ya zamar masa kamar kufai, ba abinda yake tinani illa yaran shi, daga haka ya gangara tinanin Maleeka, wadda yake ganin bai ma kan shi adalci ba daya kore ta, ya sake ta, sannan ya raba ta da iyayen ta, ga shi kuma alaqar shi da Fahad din ba wai ta yanke bane, lallai yayi babban kuskure a rayuwar shi, musamman in ya tina yanda take masa biyayya,ta ke son ta bashi cikakkiyar kulawa da jin dadi, sannan ga shi har da rashin lfyr shi a hakan tana qoqarta biya masa buqatar shi, in ya tina yanda ya dinga gudun ta ko in ta nemi siyi sabon abu dan faranta ran juna, yana gwale ta, sai yaji hawaye na zuba masa, dole ne ya nemo Fahad su yi magana, amma bari ya fara zuwa ya gaida su Abba, daga nan su yi magana da Fahad akan fara neman Maleeka.
Gyara jikin shi ya yi, ya dau key, ya fice, yana isa ya leqa bangaren su Abba da Umman Maleeka sika gaisa, ya dakko masu maganar Maleekan, kamar yanda ya keyi a kwanakin nan,
"Na fada maka ka daina kira min sunan yarinyar nan a gabana, yarinyar d bata san barazana ba,ta aikata laifi an mata barazana, wato ta zama 'yar kan ta, tana da kudi shine bari kawai ta kama gaban ta ta bar gidan, to taje ai dunia ce, na san tana can tana ganin ta,"
"Haba Abban Maleeka, ya zaka dinga fadan wadannan kalaman? Shekara nawa ya ci ace mun yafe mata,na san a qasan zuciyar ka kana son ganin ta, me yasa zaka dinga aibata ta, bayan a yanzu ya kamata ka gane komai ya faru shiri ne dan ta bar gidan a aure mata miji, kuma an samu nasara, to in ma tana da taurin kai kai ta gada, saboda gashi nan qiri2, kana son ganin ta ka kafe, baka so,"
Tana kaiwa nan ta miqe cikin bacin rai, da hawaye a fuskar ta,
"Anwar ka samu goyon bayana akan nemo ta, daka gan ta ka dawo min da yarinya ta gida, nayi kewar ta, in taqi kazo ni ka dauken na je ko fldurqusawa ne zan yi dan ta dawo gareni ita daya na mallaka duk duniya, banda wata sai ita"
Abban Maleeka ya san kalaman ta gaskiya ne, dan haka bai musa ba, yayi shiru, ya kauda kai.
"Abba bari naje naji Fahad yace min ya shigo, zanje mu fara maganar, sai a san yanda za ai,"
Bai kula shi ba, ya sake kauda kai gefe, shi kuma daya ga haka ya san ya sakko kenan, dan haka ya fita,dakin Fahad,dubawa yayi ko ina yaga alamar bai jima da fita ba, dan ga qamshin tutarukan shi nan da ba a jima da fesawa ba, nan da nan ya fita,dan duba shi a harabar gidan, ganin fitar motar shi yayi, shima ya fada tashi, me gadi na ganin haka ya qara qangale qofar, bin bayan motar Fahad yayi, a baya, yana dariya, yace bari ya ga ina zai je dan da alama zance zai tafi, shi da ya ke musa bai da budurwa.
Haka sikai ta tafiya, sai da sukai tafiya ta kusan awa daya da mintuna wajen.ashirin sannan suka tsaya wani gida madaidaici, mai kyau, gani yayi, Fahad ya cire waya, ya yi kira, ba a jima ba sosai, gate din ya fara budewa, ta juya bayan ta, sai d ta gama bude gate din ta daga Fahad ya haske ta da hasken fitilar motar shi, tsayawa tayi tana murmushi, da wani irin salon sace zuciyat dik mai tsautsayin daya kalle ta, doguwar riga ce a jikin ta wadda ta bi shape din jikin ta, har tana ja da qasa, sai daurin dankwalin da ta yi kamar gwaggwaro, ta yafa mayafi ya rufe har qugun ta, gashin ta ya sauka a bayan ta, sai kyalli yake suma.ne kawai Anwar bai ba saboda tashin hankali, wa yake gani? Dama kenan zargin shi na suna neman juna gaskiya ne? Innalillahi wa inna ilaihirrajiun, wannan wane irin mummunan al-amari ne yake shirin faruwa, Fahad ya gani ya fita, yana taku cin annashuwa da jun dadi, Ameer ne ya fito daga parlour da gudu, Amrah na biye da shi, sun sha gayu gwanin sha'awa abun ya masa kama da me gida yayi tafiya,mata da yaran shi sun fito tarbar shi, ya Allah, meke shirin faruwa ne?.....
*Nima ban sani baaaaa sai a next page maji*๐ฑ๐ฑ๐ฑPage 19
960 56 0
by Haermeebraerh
Following
๐
๐ผ MIJIN YA TA KO MIJINA ๐
๐ผ
BY HAERMEEBRAERH
Page 19:
Yana ganin suna qoqarin rufe gate din ya bude motar shi yana wani huci kamar zaki ya taka ya danne qofar da qafar shi ta hagu,mamakin qafar waye wannan Fahad yayi kan Anwar ya bude qofar cikin qarfi, ya fada ciki shima, naushi ya kai ma fuskar Fahad da iya qarfin shi, nan take Maleeka ta kwalla qara, yaran ta suka ruga da gudu suka qanqe ta, ta dafa kafadun su, kafin Fahad ya dago Anwar ya sake kai mishi naushi a baki, jini sai zuba yake, qafa ya sa zai dake shi ya riqe qafar, nan fa sukai ta naushe2, Ladeefa ce uwar dambe tana isa wajen ta shiga tsakiyar su, tana muzurai,
"Kai malam kai waye daga zuwa zaka hau dukar mana Yaya? Ko ka fita ko na maka dukan dahuwar gandar raqumi, kar ka ganni haka bana daukan raini,"
Watsata gefe Anwar yayi, yana nishi, ya zubda yawun bakin shi daya ji ya sauya ya tabbata jini ya zubar,
"Ashe dama zargin dana janye akan ku gaskiya ne, na zaci sharri aka maku, ashe da gaske ne, yau idona ya gane man komai, Fahad dan uwa fa na dauke ka fa, haka zaka min,ba zan taba yafe maka abinda ka min ba har duniya ta nade, ko a lahira bana fatan sake haduwa
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 8 Chapter of 13