Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
4 / 13
jiqa ya kwana biyu, a saka gero daya kwana a jiqe a markada, a saka madara da zuma, a bata ta shanye, gaskiya Inna tayi qoqarin gyara Amatullah, kamar mahaifiyar ta na raye indai ta nan ne, qawayen Inna sun kawo magunguna na ciyayi da ganyayyaki amma ta qi bata tace bata son ta ba ta su su lalata mata rayuwa da wuri, gwanda ta sha abubuwan gida," "A tare akai mana qunshi da gyaran gashin mu, lokacin bamu taba sa mai ba, dan haka lokacin da aka saka yayi kyau sosai yayi tsaho kuma da ban sha'awa, gidan mu ya cika da 'yan uwan su Maman mu na nesa dana kusa, akai ta koka rashn ta, har suka samu kuka," "Amatullah dani mun sakankance tare za a tare, saboda mun san alqawarin da mukai ma juna mu, dan haka muka sake jikin mu,kowa sai raqashewa yake dan Suhail ya sake bakin aljihu ana ta biki mai cike da ciye2 da shaye2 na kayan dadi," "Inna da Kawu ne suka tara mu, suka sanar damu, su suka ma Amatullah kayan daki, wanda sai da suka siyar da gadon su sannan suka hada kudin, ashe Suhai ne y yi komai, nan mukai ta kuka muna masu godiya" "Yau aka daura aure, zuwa yamma za a kai amarya gidan ta, aiko ba qaramin kyau tai ba, kayana na hada nima, Inna da wasu 'yan uwan su suka mana bayani ba fa inda za a dani, sai amarya ta kwan ta hantse gidan ta, wata qila sai ta huta gidan miji, cike da tashin hankali muka kalle su, me sike fada, tabbb za a yi ta maga yanda za a raba mu yau, Kawu na gefe ya kallemu da gudu ya shiga tsakiyar mu yana haki," "Kar ku kuskura ku bar su su hade jikin su, in kuka bar su suka manne ko gum bai fisu mannuwa ba, ba wanda ya isa ya raba su, ku ja Babbar ai mota da ota ai masi daukam Amaryar dama an gama da su an basu ita sai tafiya," "Manyan matan unguwar dake unguwar mu na yanzu sune a matsayin 'yan uwan ango da suka zo daukan amarya, kuka muke ta zabgawa kamar dayar mu ta mutu, kukan rabamu da juna da akai muke, muna tinanin anya zamu sake haduwa kuwa?" "In taqaita maku sai da mukao sati biyu bamu ga juna ba, ni kam harda qarin ruwa, ita kuwa taqi amincewa da shi saboda rabamu da akai,kullum tace in ta rufe ido gano ni take Kawu na son haike min, dan haka sai ta kasa zaune ta kasa tsaye." "Ina zaune mun dawo asibiti, ina cin ayava, Suhail ya shigo cikn fushi, ya dakan tsawa, ko gaida Inna bai ba," "Ke hada kayan ki mu wuce, ki min saur kuma," "Lafiya dai ko Suhail" "Inna ina fa lfy, Amatullah ta na can ba lfy wai na maida mata da qanwar ta, na rasa meke min dadi ni," "Ai ina jin zai kai ni wajen ta na shige daki na hada kayana, sauri2, na fito, bakina har kunne, ko ya taya ni daukan kayan mai nauyi haka ya wuce, na bude boot na.saka kayan na shiga gaba bayan ya bude, haka muka wuce sai gidan Amatullah, da suhail," "Muna shiga mukai arba da juna mu muka rungume juna muna murna harda kukan dadi," "Suhail ba kunya ya janye ni, ya kalle ta, yace ina alqawari na? Sauke kai naga tayi tana kallo na qasa2, nima kallon shi nayi ina neman qarin bayanin wanne alqawari kuma?.......... *pls manage this page, nayi ne dan cika alqawari amma wallah baccin yamma na son kama ni, a ban chocolate na sha na wartsake🀣, Thanks all for ur comments i love u all❀ dan Allah banda tambaya ta pc, ko da tambaya dan Allah a yita group, hakan ba wai wulaqanci bane kamar yanda wasu ke dauka, ni din ba kowan kowa bace ya dillaliyar ayaba, amma ina gudun kar ban amsa ba saboda wasu dalilai aga nan ma nayi shiru, thanks all*πŸ’…πŸΌ MIJIN YA TA KO MIJINA. πŸ’…πŸΌ BY HAERMEEBRAERH *HHHHH niyyata yau na dan maqale nima, tinda Ayusha taqi bamu JALILAH amma ba yawa zan maqale in ba a turo ba yau ma* Page 9: "Kallon shi naga Amatullah tayi ta sadda kai qasa, kama hannuna tai, ta kama akwatina zata kaini dakin da zai zama nawa ne, da qarfi ya fizge hannun ta, cike da fushi ya kalle ta," "Wai Amatu wannan wanne irin wulaqanci ne? Ya na cika maki alqawarin ki ke kin kasa cikan nawa, inq miki magana ma kina kama qanwar ki zaku wuce ku barni tsaye?" "Cikin rawar jiki, da murya Amatullah tace," "Haba dan Allah, ka bari na kaita dakin ta mana, ko a nan zan cika maka alqawarin ne? Kuma dai ai bama wuce mu bar ta anan a tsaye ba ko," "Wani kallon da ban gama gane na meye b ya bini da shi, yana lashe lips din shi, sannan yace," "Dan taji meye? Ai ko bata fara ba yanzu gaba zata sani ne, muje, ke Samha, kinga wancan dakin? Shine naki, maza ja akwatin ki ki shiga, ki sake abin ki nan gidan kine kema, kamar yanda yake na yayar ki kinji?" "Daga masa kai nayi, bai bamu damar zama da Amatullah ba ko mu shiga ta nuna min abubuwan da ban sani ba, dan tinda muke bamu taba shiga gida mai kyau ba musamman kamar wannan, haka na ja akwatina nai dakin, ban jima da shiga ba sosai, dan inajin ko minti biyar ban cika ba na fara jin kukan ta, naso na je naji ba'asi, amma na kyale; tinawa da nai nan fa gidan ta ne, kwantawa nai na rufe ido ina tinanin irin rayuwar da zamu yi a wannan gidan, sannan na dinga hango rayuwar da mukai a baya, fatana na samu na ci gaba da karatu na, inna karanci bangaren aikin asibiti wataqila zan fi samun kudi, ba irin tinanin da ban ba wanda zai kawon kudi inna kammala karatuna, daga baya na miqe na tura qofar dakin sosai dan na daina jiyo kukan Amatullah, ina gama tura qofar na shiga bandaki, na cire kayana na tattaba inda naga alamar pampo ne, na kunna ruwa, a sink, ya taru a kofin bandakin a haka na dinga wanka na na gama, nayi alwala, na fito, sauya kaya nayi, na ninke wancan, na zauna jiran ta ta shigo, ta nuna min gabas, ina zaune na zuba tagumi, naji an bude qofar, da sauri na kalli wajen, ganin shi nai yana wani murmushi cikin nutsuwa da jin annashuwa," "Kije yayar ki na neman ki, ni na fita," "To,shine abinda na iya furtawa, dan mamaki nake,shi yana murmushin jin dadi ita tana kuka,me kenan? Da sauri na fita, har yayi gaba naga ya dawo ya nuna min dakin, da sauri na isa, ina shiga na ganta daidai a gado, in ban bata gani ba, tsirara take, kuma cikin wani irin yanayi, da sauri na kulle idona nayi baya kadan, tana jin muryata na kira sunan ta ta ja mayafin gadon, da sauri,ta rufe jikin ta, umarni ta ban na fita, na so na mata musu amma na fita, dan ko ba komai na gane me ya faru,(a wannan lokacin ai yara qanana ma ba abinda ba su sani ba balle yar secondary)," "Ina fita naji ta fashe da kukan takaici, jingina nayi a jikin bangon dakin, na rintse idona, ina jin zafin yanayin dana gan ta, ya gama abinda zai da ita ya five ya barta, Allah na nan," "Dakina na koma na zauna ina tinanin ina ya kamata ya zama gabas, ina ganowa na fara sallolina, bayan na idar na zauna ina addu'a, ban jima da zaman ba naji motsin qofar dakin da nake, idon ta ya kumbura ya yi sintim, fuskar ta tayi jawur,ga shatin yatsu nan manya, a kuncin ta, sai kaucewa take karna gani, d sauri na rungume ta ina shafa bayan ta, sake jikin ta tai a nawa tana kukan dake dukan qirjina ya tabo zuciyata nima hawayen nake, ba qaqqautawa," "Samha kar ki kuka, nima rashin sabo ne, kowacce mace sai ta wuce wannan siradin, fatana kawai dik abinda mike nema mu samu a wannan gidan, bana son ki saka kan ki a dikkan abinda zaki ji ko ki gani a gidannan, kome ke faruwa ki zama kurma ki zama makauniya, fatana kiyi karatu maruqa, ki jajirce tinda ni ya ce ba zai bari ina fita ba, so zan dora rai a kan ki, zaki iya min alqawarin tsayawa tsayin daka kiyi karatu, dan mu fita daga quncin da muke ciki?" "Da sauri na daga mata kai, ina furta, nayi alqawari Yah Amatullah, na maki alqawarin ba zan baki kunya ba inshaa Allahu, ina son ki ba zan abinda zai bata maki rai ba da izinin Allah sai dai a kan kuskure," "Rungume ni tayi tana kissing goshina tare da shafa kaina, ta furta, ina son ki qanwata, Allah ya ma rayuwar ki albarka, Allah ya bamu hakuri da juriyar zama a wannan gidan," "Ameen Yah Amatullah," "Tashi muje muyi girki,na kuma nuna maki yanda abubuwan gidan suke,kinsha magungunan ki?" "A'a sai can anjima, muje ko?" "K muje," "Fita mukai, mka shiga kitchen,naga na'urorin da ita kan ta karantawa take tana gane komai, wani muyi dariya wani mu tsokani juna, koma dai meye muna cikin farin ciki after so many long years da bamu samu dama ba,ina lura da ita lokaci zuwa lokaci tana yatsina fuska, saboda kamar tana jin zafi, in mukai aiki, ta gaji da tsaiwa sai ta zauna tayi shiru, haka muka kammala,ta wuce daki zuwa wanka, ni kuwa ba abinda na sake, bayan ta kammala ne, ta zo kirana mukaji dawowar shi, sai da naga alamar faduwar gaba a tattare da ita,dakewa tai,ta fadan na fito mu ci abinci, a yanda nake ba mayafi, haka na miqe na fita, tana hango shi ta tafi da sauri ta rungime shi dauke da fara'a mai kyau a fuskar ta, shima tarar ta yayi, ko kunyata bai ji ba ya kama bakin ta yana sha, sai ni na kauda kai, yana gamawa ya quran ido, da wani kallon lust, ko daga kai na kalle shi ban sake yi ba dik da jana da hira da yake, na kula Yah Amatullah ta kula da kallon da yake min amma kuma banga alamar bacin rai a tattare da ita ba," "Samha ya maganar makaranta? Dan na sama maki inda zaki ci gaba, da drivern da zai na kai ki ya dakko ki, ina fatan hakan ya maki, yanzu ma daga makara tar na dawo, gobe zamu je dake, inshaa Allahu," "Ban san sanda na saka murna ba, for the first time zan shiga makaranta ta masu kudi nima, za a na kaini a mota, wooo niii, godiya mukai ta zuba masa jida Yayata, kallon yayata yayi yana shafa dantsen hannun ta da yatsan shi guda daya,yana cije lips din shi na qasa, tare da kafe ta da ido, murmushi naga tana masa wanda bai gama kai zuci ba, alamar ta gane me yake nufi," " Ki daina min godiya u guys ar my responsibility now, kome kuke so zan maku shi, ina fatan kun gane?" "Ni dai da kunya ta kama ni saboda abinda yake yi, da sauri na daga kai na bar wajen, kamar jira yake, ina tashi ya dauke ta cak a hannu yayi daki da ita, sai mutsu2 take tana fada masa bata warke ba da ciwo fa, fada mata yake ba wani abu zan maki ba ai sai kin warke, kawai wani sanon wasa zan koya maki, kwantar da kan ta tayi, suka rufe qofar da qarfi , suna shiga na juya na kalli wajen, na sauke a jiyar zuciya, wannan rayuwa itace rana zafi inuwa quna," "A cikin sati daya na saba da makarantar mu, dan daliban basu da matsi,musamman an kaini dik ajin ko nace kusan a dika makarantar in ba a kirani ta uku a kyawawa ba a kirani a ta biyar, kowa a ajin na son kula ni anan nayi qawa Aneesa, mun saba da ita sosai, amma bamu san komai game da juna ba, na dai san tana da qoqari fiye da kowa a ajin," "Aneesa ce ta fara ban wasu kwayoyi na sha kafin na fara karatu zan samu ya shiga sosai, ai kuwa tin bana damuwa in.ban sha ba ya zamana na fara damuwa, bata gajiya kuwa wajen bani, inna sha na dawo gida sai nayi ta bacci, sai na tashi nayi wanka na yi karatu, sai na ji karatuna na shiga, Yah Amatullah ta fara damuwa da yawan bacci na, da kuma abu danake kamar mai maye, sanar da ita nai meke faruwa, kuka ta sa ta hau min fada sosai, sannan ta sa Suhail ya sauyan makaranta, nan ne rabuwa ta da Aneesa, na shiga damuwa sosai saboda rashin wannan kwayoyin, kamar zan haukace inna so sha ban samu va haka nake ji, da kyar na hakura da su, bayan jinya dana sha," "Randa na kammala secondary school, Suhail ya sai min mota mai kyau, lokacin kowa ya ganni sai ya zaci wata diyar babban mutum ce, Suhail ya lalata mu da kashe kudi, daga mu har su Inna da Kawu, Kawu ya sauya gida, ya zama qaramin Alhaji, ban sani ba ko asiri suka mana, yanzu mugun tsoro. Su muke ji shi da Inna, kome suka ce ma Amatullah ta basu jiki na rawa take diba ta bayar, ko a raina ina son na hana ta,sai na kasa, ga shi ba wuya sunce a basu kudi su sai kayan abinci wai saboda yawan baqi abincin su na qarewa da wuri, in kayan abincin tace zata basu sai suce ta bari in bata yarda da su ba, haka zata dau kudi ta basu," "Ranar dana fara zuwa jami'a har muka hadu daku, kuma kun shigo, dik da kun riga ni shiga da aji daya, a ranar na dawo da dabi'ar shan kayan maye, in baku.manta ba Ladeefa ce ta fara ban Coc. Na sha, akwai maganin mura a ciki, na sha nai ta timbele, kuna dariya, daga nan muka saba, har nake biyo ku gida, " "Suhail ya fara nema na daga ranar da ya leqo kirana dakina ya tarar na fito daga wanka, ba komai a jikina,taqama ta dakina ne, ba mai shigo min, shine dalilin daya sa na ke fitowa ba kaya inna so, sannan kuma ina da dabi'ar saka qananan kaya sosai, musamman qaramin wando da vest, iron mai dame qugun nan, na sake gashina, in ina zaune Suhail ya dawo zan tashi na koma daki, amma innai niyyar wuce su suna zaune hakan ba zai sa na saka wani abu ba dan rufe jikina gani nake ai yayana ne shi, mun zama daya,( wannan shine babban kuskuren da mata ke tafkawa da sunan mijin Yayata ne ai, ba komai, kuga mace ko budurw ko matar aure ta zauna tinqis gaban mijin yayar ta ana ta shan hira, wata qila tafi yayar kyau kamar dai samha da yayar ta,kunga kuwa ana gida daya, shaidan in ya gilma ai ba laifn kowa bane sai na wadda take aikata hakan)" "Muna hada ido da shi, na saki ihu, na qanqame jikina, ina fada masa ya fita, amma yaqi, takowa ma yayi, ya rufe qofar, baya na dinga ja ina qoqarin fadawa bandaki, ya fizgen, qirjina da suke a cike, ya manna da qirjin shi, yana bin su da kallo, tare da daga kai yana kallo na, gannun shi ya kai qasan mazaunai na ya taba da qarfin shi, ihu na saka tin qarfina, vakin shi ya saka anawa, Yah Amatullah ce ta banko qofar ta shigo😱😱😱😱😱😱😱😱😱😱.......... *Much love guys, gaskiya ina jin dadin comments din ku da addu'o'in ku, addu'a ita daya ce zaka ma wanda yake faranta maka ka burge shi, dan haka kuna burge ni Allah ya barmu tare da alkhair*β€πŸ’…πŸΌ MIJIN YA TA KO MIJINA πŸ’…πŸΌ BY HAERMEEBRAERH Page 10: "Tana ganin yanda Suhail yake damqar jikina kamar na ta ne, amma haka naga hawaye a idon ta kamar pampo ta juya ta fita da gudu, a zatona wani makamin zata dakko ta maka masa dan kubutar dani, amma ina sai qarar dakin ta naji ta buga qofar, da qarfi, ta rufe, a tare da qofar na kulle idona, wasu sabbin hawaye naji suna zuba min, Suhail qoqari yake ya kwantar dani akan gado na,wani qarfi ne ya zo min, na sa qafata a qasan shi, da alama dadin hakan yaji ya sake bude qafar shi, yana murmushi, janyewa nai nayi baya da qafartawa na buga masa a tsakiyar shi, wata qara ya sake ya kwanta a wajen yana murgususu, idon shi a rufe,dukan shi nai tayi da qafata, sannan na duqa na ja shi zuwa waje, da ga gani dukan ya shige shi ba kadan ba, ina kaishi waje na danne qofar na rufe, na saka key, maza na zira rigata na fice, da niyyar na zo wajen ku, ina fita ya riqe ni, ya dinga mari na, na sha mari har na gode Allah, yana dukana ina ramawa, haka mukai tayi, har Allah ya ban sa'a na fisge na fada mota, na kulle, gadan2n na nufi gate, da sauri me gadi ya buden, na fice, shine akaro na farko dana zo gidan nan ina kuka,kukai ta tambaya ta dalili ban fada ba, sai da na kwana uku anan, sannan Yah Amatullah ta dinga min waya da text tana ban hakuri,tana nuna min Suhail yayi nadama, d sauran su, harda tina min ashe ba zan iya riqe alqawarin da mukai wa juna ba, zan iya barin ta kamar yanda iyayen mu suka tafi suka barmu? Maganganu kala2 da suka sa dole na koma gida," "Lokacin dana shiga gidan yana zaune a kujera yana kallo, kallon irin finafinan turawan nan, ana ta iskanci a ciki bai damu ya sauya tasha ba, ya shagala da kallo, zuwa nai na wuce shi, kafin na shige dakina naji muryar shi," "Well come back home sweetheart, how was ur loooonnngg vacation, ina fatan kin manta da komai, Yayar ki ta matsa sai na baki hakuri dan ki dawo gida, she don't wanna loose a sister like u, bayan ta rasa iyaye, ok to be honest nima bana son n rasa ki, u ar such a durling u knw," Tsayawa nai cak a lokacin danaji maganar shi ta tsaya a dokin wuyana, ban juya ba, ya sa hannu ya shafi wiyan nawa, sannan ya yi ma wuyana kiss ya koma mazaunin shi, raina a bace yake matuqa, ji nai kamar na dawo wajen ku amma na dake na sa qafa zan shige ya sake magana," "Ko zaki zo muyi kallo ne, na kula rashin sanin dadin abun ya sa kk gudun shi, amma ki zo ki ga yanda ake yi, wataqila zaki bada hadin kai," "Na so na bashi amsa amma ance kulawa ma ai yabawa, da qarfi na rufe qofata, daga ranar ya zamana bana baccin kirki, saboda ban san me zai je ya zo ba, wata rana ya fita na kira kafinta ya zo ya sa min sakata ta ciki, Yah Amatullah bata ce komai ba, har haushin ta nake ji in bata magana akan abinda ya dace ace ta nuna bacin ranta ma ba iya magana ba, gashi tsananin son da take masa komai namu basirri sai ta kwashe ta sanar da shi, gaba daya ta zama kamar wata doluwa, kai ko da period nake sai Suhail ya sani, dik wani zance na ya zama kamar a kan idon shi ne, in kaya na siyo musamman qanana sai tace itama tana son su, zata siya ta sa Allah yasa ya mata kyau kamar ni, shi kuma da dadin baki sai yace ai sai ya ma fi maki kyau, sai da ta kai na daina hira da ita, na daina fada mata dil wani abu nawa, saboda kar naji shi a bakin shi, adadin yanda yake bamu kudi ya ninka shi, kashe mana kudi yake kamar baya son su, a yanzu duk.kulawar shi ta dawo gareni, ya zama ko a gidan yake bai zaman parlourn dakin su, sai dai babban parlour, dik wata wucewa ta a kan idon shi, wataran in zan wuce sai dai na ji shi ya daki duwawuna ta baya yace "Nice Ass babe" da ire-iren kalaman nan na marasa tarbiyya," "Akan abinda yake ya sa mun maida gidan kamar na 'yan dambe, gobe wance za a kai asibiti, jibi shi za a kai, gata ita ko ni, masu aiki kuwa saboda wai sa ido ya kori sunfi biyar, zaman arna kawai ake a gidan, a dalilin haka ne dana koma ya nemi ya ketan mutuncina na kare kaina, ya koma wajen ta, na caka masa wiqa shine aka kaishi a sibiti dan rashin zuciya kuma take masa girki ta kai masa," Cike da tausayawa suke kallon ta, Maleeka kuwa ji take kamar taje asibitin ta qarasa shi. "Allah na tare damu da izinin Allah dik wanda suka cutar damu Allah zai bi mana haqqin.mu, ko anan duniya ko a can lahira, ba dan su ba da mazamu bata kan mu da wannan shegen shaye2n da ni har ya fara isata ma, amma in ba kai ba tinanin banza ya dame ka," "Bari na dan miqe zuwa yamma ina da lecture, kar na makara, munci bashin bacci, and maybe na tafi ba zan dawo ba zan wuce gida naga ya abubuwan suke," "K ni anan zan kwanta dan sai na dan watsa kayan aiki," "Allah dai ya yaye mana amma ke kin fi uban kowa son maye," Tafawa sukai, kowa ta kama inda ta nifa. β™‘β™‘β™‘β™‘β™‘β™‘β™‘β™‘β™‘β™‘ A can asibiti kuwa Suhail na kwance, jiki ya fara sauqi, ba laifi, tinda ya na shan magunguna, ga kayan.fruits da yake faman sha, har yau ya qi sake ma Amatullah fuska, ita kuwa kamar mayya in taje, tai ta surutu ko zai kula ta, tana bashi hakuri, yanda take nuna masa tafi son shi sama da kowa na ta, shima yana son ta, amma sha'awar qanwar ta tafi komai yawa a ran shi, dan bai boye mata ba, ya sanar da ita dik sanda Samha ta amince da.shi, ya biya buqatar shi,ya kauda kwadayin shi, zata samu kyakkyawar kulawar shi, kuma ya mata alqawari ba zai sake kula Samha da sunan wani avu ba sai ita kadai, abin tambaya anan shine ita sokuwar ina ce, kuma ta amince da hakan? Haryanzu danake wannan rubutu banda wannan amsa. β™‘β™‘β™‘β™‘β™‘β™‘β™‘β™‘β™‘β™‘ Samha ta maida hankali wajen karatun ta, karatun ta yanzu shine gatan ta,dan bata son saka damuwa ta samu matsala,harkar lfy ba wasa ba, dik ta wani rame ta wuyan ta kamar a zuba ruwa a ramin wuyan, cikin nan ya qara shigewa, ba dan itan me shape bace da ba zata ganu ba, gashin kanta kan shi ya ragu saboda damuwa, ga su Inna da suka sata gaba akan itama ta nemi miji tayi aure saboda su samu kudin shiga su qaru masu, kasa daurewa tai ta masu tass, wato sun maida su kadarorin su? Kalmar da ta gaya ma Kawu ya sa har ya jibge ta ya farfasa mata jiki itace, "Ba banza ba Allah bai baku haihuwa ba, dan karuwai zaku maida 'ya'yan cikin ku, saboda abin duniya, mu kuma da baku riqe amanar Allah ba da zumunci, amanar Allah sai ta ci ku ko bajima ko ba dade," Tana fada Kawu na dukan ta, sai da ta qarasa fadin abinda tai niyya, da kyar ta iya komawa gidan su Maleeka, a zaton su ko Suhail ne again, har sun fara masifa da niyyar zuwa har gidan su masa rashin.mutunci ta ce Kawu ne, zama sukai sin rasa me zasu yi ma wadannan mutane da suka maida ma su rayuwa mara mahimmanci, suka gurgu ta masu rayuwa, kayan mayen su suka debo sukai ta sha, dan mantawa da komai da kowa, ranar ma anan Samha ta kwana. β™‘β™‘β™‘β™‘β™‘β™‘β™‘β™‘β™‘β™‘β™‘ Shopping suka shirya yau zasu je, gaba dayan su, sun sha gayu irin na matan yanzu da ake yi, da riga irin ta sojoji da farar vest, a saka dogon wando, a sa sarqa, a yafa mayafi akai, Ladeefa ko mayafin bata yafa ba, haka ta gyara gashin ta ta baza a bayan ta, Samha ta saka hula

Chapter 4 of 13