An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels
💅🏼 MIJIN YA TA KO MIJINA💅🏼
BY HAERMEEBRAERH
*Assalamu alaikum, makaranta novels dina ina maku fatan alkhairi a duk inda kuke, saqon gaisuwa ta a gare ku ba shi da iyaka. Kamar yanda novels dina suka gabata guda biyu, MUGUN MIJI, AURI SAKI, n yi su ne akan yanda mazan wannan zamani ke cin kasuwa akan matan su, cikin kwanciyar hankali, ba tare da an dau mataki akan su ba,ko kuma in an dauka din ba zai taba goge azabar da suka ma matan nasu ba, wannan novel din shima kusan akan maza ne zan yi shi, domin labarai ne da ya hada na mata kala2, amma inshaa Allahu zan taqaita shi yanda saqon da muke son mu isar zai kai ga mazaje, yana da kyau ku dinga sharing irin wadannan labaran, ba kiga wani shiririta ki ta sharing va kina barin abu mai amfanin da zai iya gyara rayuwar wani.*
*kamar kullum ina mai roqon ku da tara novel ko baki karantawa wata qila gaba zaki so bi, dan wadda nake tura mata mutane ma yau da gobe ta qi wasa kar mu lalata mata waya😄 and in an ga abu mai amfani a kwafe, a wani wajen, dan Allah banda tambaya ta pc, wayata nada matsala tayu na gani kan na amsa sai aga kamar na share ne, amma network ko riqewar ta ne yasa ba a ga amsata ba. Na gode*
Page 1:
Kidane ke tashi kamar wajen zai fashe, madaidaicin parlour ne wanda iya ganina kayan maye ne a kan center table din, wadan da tinda nake ma ban taba ganin su ba balle sanin sunan su, mata ne matasa su uku, wanda naji suna kiran kan su bestis, kowacce in zata kira dayar su da besty take kiran ta, biyun su masu matsakaicin kyau,amma farare tass, sai dayar su wadda ta fisu kyau, farin fatar ta bai kai nasu ba, kuma ta fisu cika, ga shin ta irin na hausa fulani, saboda gyaran da yake sha ya kwanta har kafadun ta, ta dan zubo da shi ta gaban goshin ta, a buge take kwance a kujera, ko bude idon ta bata iyawa, hannun ta take son dagawa amma sai ta maida shi yaraff,bakin ta na motsawa, da kyar ta yunqura ta miqe ta shige bandakin dake cikin parlourn.
Dariya dayar su tayi, tace,
"Besty, kinga Besty Samha yanda ta tipse ko tafiyar ma kamar a taya ta, yau fa ta hau network kowa zai maida ta gida? Dan dai ba zan je ba na hadu da wannan shegen mijin Yayar ta ta, mayan mata,"
Dariya tai dayar cikin maye itama ta furta,
"Malika besty ai sai dai ta kwana anan kawai, dan nima ba zuwa zan ba, kwanaki dana maida ta, dik da mun dawo hayyacin mu guy dinnan fa nema yake ya haye ni, baqin dan iska ne, mara misali,"
Daga sama suka ji maganar ta,
"Shegu me kuke cewa? Ina jin ku, ai ku bari kawai, Yah Suhail, ya mugun maida ni kamar matar shi, Allah ne kawai bai....."
"Dakata Besty, in zaki shekara rantsuwa ba wanda zai yarda wannan dan akuyan bai hauki ba, ko qur'ani zaki dafa kuwa,ke dai kawai ai sha'ani, Allah ya kyauta,"
Wani baqin ciki ne ya kama ta, babban abinda ke damun ta kenan, sanin cewar kowa kallon da yake mata kenan ya sa take qara jin baqin ciki, da tsanar Mijin Yayar ta da Yayar ta ta ma, amma ba komai, Allah na nan.
Tsaki tai, ta ja doguwar rigar ta ta dora akan riga da wandon dake jikin ta, ta shige daya daga dakunan, ta kwanta.
Ba ita ta farka ba sai wajen isha'i, da gudu2 ta shiga wankata fito, qawayen nata na ta bacci, ta shirya ta aje masu note ta fice,shigewa mota tai bata zame ko ina ba sai unguwar Zoo road, dake garin kano, a wani gida mai babban gate ta tsaya, wanda da gani kasan gidan kudi yaji ko ta ina, parking motar tai ta fita,kanta a qasa, irin ladabin nan na masu shaye2,dakin ta tanufa, dan bata ji motsin kowa ba,ta san auntyn ta na daki ta kwanta, saboda bata dadewa batai bacci ba, in ko ta dade to ana dadi da Yah Suhail kenan, tana koyarwa a makarantar secondary ta Gyadi2, dan haka take bacci da wuri, ga gajiya gashi tana son ta tashi da wuri.
Da sauri ta shige dakin ta,ta yi wurgi da jakar ta, ta fara qoqarin cire rigar ta, tana cirewa ta cire ta cikin da bra din ta, dan so take ta sauya kaya tayi sallah ta kwanta itama.
Cikin sanda ya fito daga toilete din ta da ya shiga ya buya, ta baya taji hannayen shi akan qirjin ta, wani wawan ihu ta sake, yai maza ya juyo da ita ya toshe bakin ta da nashi, a yunwace yake tsotsar vakin ta, ita ko sai qoqarin kwace qirjin ta daya manna hannayen shi kamar a wajen aka halicce su take, cikin sa'a ta kama lips din shi ta dasa mashi wani cizo, taqi saki, sai da ya saka ihu, taji alamun jini a jiki, sannan ta sake.
Kuka ta fashe da shi, tana bin shi da kallon tsana,da qyama, da Allah wadai, shi ko fuskar shi tayu jawur saboda baqin cikin abinda ta masa.
Bai bata lokaci ba wajen damqota da gashin kan ta, ya wurga ta gadon, tana ganin ya fara qoqarin cire wandon shi ta ja rigar ta ta fita wajen dakin a guje, a palourn suk ci karo da yayar ta ta, kallon yayar tai ta daka mata harara ta saka rigar ta tayi waje a guje, kulle su tai ta wajen, da wani qarfe, ta zauna a bakin qofar tana ta kuka, wannan wace irin masifa ce? Ina ma tana da wajen zuwa; da ta bar gidannan ta koma, in tace zata var nan ta koma zaman kan ta ta qara vata wa kan ta suna akan wanda take ciki yanzu,ina zata? Wani tinani tai da sauri naga tana girgiza kan ta.
"Inaaa ba zai yu ba, Ya Allah gare ka nake neman tainako, Allah ka taimaken😭"
"Samha, Samhaa, ki bude qofar nan, nace ki bude qofar nan, kar ki bari na bude da kaina,"
Hararar qofar tai tayi tsaki, ta juyar da kan ta, ta kifa kan a cinyar ta, hawayen ta na zuba ta gefen idon ta.
Yaya Amatullah kuwa tana tsaye jikin dinning tana kallon yanda mijin ta ke rikice akan qanwar ta, baqin cikin dake zuciyar ta bai da iyaka, zuciyar ta ta bushe ko hawayen takaicin da take ciki babu, idon ta yayi jawur, farar fuskar ta kamar garwashi, gashin ta dake sosa mata dokin wuyan ta ta debe ta fara tafiya daki dan ta kwanta.
A iya ganina na rasa gane da Samha da Amatullah wayafi wani kyau, banbancin su daya ta gashin kan su, Samha tafi gashi me kyau, akan Amatullah, kuma da dikkan alamu gyara ne yasa hakan ba komai ba.
Gajiya yayi da bugawa ya koma, daki ya shige, ya tadda Amatullah a zaune a bakin gado, a lokacin taci kuka itana ta gode Allah, tinani daya ne ya sata kuka, tinanin da ke damun Samha kenan har ya sata kuka, tinani ne na ina zasu su tsira daga hannun wannan azzalumin?
Da sauri ta goge hawayen ta, ta gyara zaman ta,a tsorace ta kalle shi, ganin abinda yake yi, yasa kamar baiwa ta fara cire kayan ta tana kuka, isa tai wajen shi, shi kuma ya kashe fitila,ina ganin haka nace to sa idon baida amfani kenan bari na fece😏
Kukan ta kawai nake ji, wanda ashe ba ni daya nake jiyowa ba har Samha dake waje tana jiyowa, itama kukan take, qanqame jikin ta tayi, kamar me jin sanyi, daga baya na ga ta miqe, ta zare qarfen da take rufe qofa in irin haka ta faru, dan maboya ta masa ta musamman.
Kitchen ta nufa direct, ta dakko wuqa, dakin Yayar ta ta nufa, ta bude qofar, ta kunna fitilar dakin, a yanda ta gan su bai hana mata yin abinda tai niyya ba,wuqar ta caka masa ta baya, wata qara ya sake, ya sulale a wajen...............
*Hummmmmm wannan abun akwai rikici faaaa*
*Iya comment din ku iya typing dina, kunsan ina typing da yawa innaji comment sun min kadan za a ga dan neman lalacu wallah, 🤣*💅🏼 MIJIN YA TA KO MIJINA 💅🏼
BY HAERMEEBRAERH
*Page din farko na so a ce ya zama naki Sister Sherryna❤, amma ba komai, ke din ta daban ce ko ba page kina ruhina, Allah ya bar mu tare da aminci, ya kawo miji na gari mumini salihi, Allah ya bada ikon kammala karatu cike da nasarori da sa'a, MUCH LOVE DURLING❤*
Page 2:
Kasa zaro wuqar tai a jikin shi tsabar yanda jikin ta ke rawa, ga halin da take ganin yayar ta ta a ciki, da sauri ta isa wajen ta janyo rigar ta ta miqa mata, cikin kuka da rawar jiki ta karba ta zura, a hankali cikin azaba ya miqe, yana qoqarin kamo Samha, ta zille, ta so tabi ta bayan shi ta qara caka masa wuqar amma ba hali, saboda yanda ya ke qoqarin kama ta ta qarfi, jan hannun yayar ta tayi, suka fice daga dakin da gudu, dakin ta suka shige suka kulle qofa,tare da rungume junan su suna kuka, sai kace wadan da iyayen su suka rasu yanzunnan.
Gani yayi jinin dake zuba a jikin shi yaqi yankewa, zai iya rasa ran shi, cikin jiri ya isa waje, a qofar dakin drivern shi ya tsaya, kwalawa mai kira yayi, a guje ya fito, yana bude qofa yayi tuntuve da maigidn na su a qasa, cike da tsoro ya kama shi yana
"Yallabai lfy? 'Yan fashi ne suka.shigo? Subhanallahi, Yallabai kana buqatar zuwa asibiti fa, muje Yallabai na kaika asibiti,"
Cikin hanzari ya kama Suhail suka bar gidan gaba,daya zuwa wani private hospital dake kusa da su, nan da nan likitan dake duty ya hau duba shi, Allah ya taimaka sun samu blood type din shi, da sauri aka fara qara masa jini, domin jinin shi yayi qasa, Suhail baya gane komai a wannan lokacin, baya sauraron komai, ji yake kamar a mace yake ma, bayan sun yi nasarar zare wuqar ne, suka duba bata shiga cikin jikin shi yanda zata yi ma wani sashe na ciki illa ba, likitan ya dinke, suka barshi a kife, aka maida shi dakin da zai zauna, hannun shi na hanni drivern shi ya riqe masa kar ya taba jinin da ake qara masa.
Suhail bai tashi farkawa ba sai wajen goma na safe, dishi2 yake gani, a galabaice ya bude ido ya ga yana kallon qasa ba sama ba, juyawa yayi qoqarin yi ya kwalla qarar azaba, tini ya koma ya kife,nan take abinda ya faru ya dawo masa, cike da bacin rai ya lumshe ido, yana tinanin irin uqubar da zai saka su Amatullah in ya samu sauqi, musamman Samha.
Driver ya samu dama ya aje masa hannun shi a gefen gadon ya wuce gida, nan ya sanar da Amatullah abinda yake zargi ko barayi ne suka shiga suka caka.masa wuqa,bata nuna masa komai ba ta tambayi asibitin da yake ciki, ya fada mata ta koma ciki ya wuce wajen mai gadi,
"Kai yanzu kana ina jiya har barayi suka shigo sukai aika2?"
"Barayi kuma, da yaushe, me suka dauka?"
"Ina kyautata zaton ba abinda suke so sai ran me gidannan dan kuwa an caka masa wuqa ta baya,"
Gyada kai kawai Me gadi yayi, dan ya san me ya faru, dan tin gidan na sabo suke tare,drivern ne sabo a gidan bai san komai ba,
"Kaga abinnan daya faru, in kana son zama a gidannan na dindindin, to ka ja bakin ka ka ja idon ka ka ja kunnuwan ka ka toshe,ka barshi a barayi ne suka shigo, saboda direbobi da yawa sun rasa aikin su saboda rashin sirri, zaka ci gaba da ganin irin wadannan ta'addancin na faruwa a gidannan, ko a matan ko a mijin, dan haka kai dai naka ido, in bazaka iya ba ina mai baka shawara ka sa kai ka bar gidan tin kan Alhaji ya maka korar kare, ina fatan ka jini?"
Bude baki yayi xai masa tambaya da sauri ya dakatar da shi...
"Kar ka zurfafa a sanin meke faruwa, dan baida amfani, in ma ka sani ba abinda zaka iya yi"
Shiru yayi yana nazarin maganar kan ya wuce bandakin da aka ware a matsayin na masu aikin gidan maza, kama ruwa yayi yayi alwala ya rama sallar asuba da ake bin shi.
Amatullah kuwa na jin haka bata gaya ma Samha me zatai ba ta shiga kitchen ta fara girka abinci kala2 marasa nauyi, a zaton Samha nasu ne, dan haka ta je kitchen din ta tsaya, tana taya yayar ta ta aikace2, ba mai cewa kowa komai, tin jiya suke a haka, in da sabo sun saba, tana gamawa Samha ta dakko masu plates, sai taga ta hado da foodflask, guda uku, ta diddibi abincin nan ta zuba, kunun tsamiyar da ta dama ma ta zuba a flask. Kallon ta kawai tai, can tinani ya shigi kan ta, cike da bacin rai ta kalli yayar ta ta,
"Wai Yaya yaushe zaki daina bautawa wannan azzalumin mijin naki ne? Yaushe zaki daina jin tsoron shi? Dan yana a matsayin mijin ki ba zai bashi damar musguna miki yanda yaso, ya min abinda yaso sannan kina binshi a jiki2 ba, haka. Ke qara masa qarfin guiwa yana ci mana mutunci son ranshi, in ta su kawu ne ki rabu da su, ki kyale su, ba abinda zasu mana wanda Allah bai mana ba,Yaya duniyar nan fa na da girma, in bamu zauna a nan ba zamu iya samun wani wajen, kin sani ba dan bana son barin ki ba, munyi wa juna alqawarin zama a kowanne hali, d tini na raba kaina da wannan musibar, ke baki huta ba ni.ban huta ba,"
Cikin matsanancin kuka ta qarasa maganar, Yayar ta ta ta.matso zata lallashe ta ta fisge hannayen ta ta bar wajen da gudu, dakin ta ta shiga ta fada gado, ta kwanta, tana ta rusa kuka, wannan wace irin rayuwa ce? Ta kula dik halin da suke ciki laifin dangin mahaifiyar ta ne, da kuma yayar ta ta, tinda tsananin son da take wa Suhail shi ya jefa su a dikkan halin da suke ciki.
Tashi tayi zaune ta share hawayen ta, tare da jan hancin ta, ta dakko band ta daure gashin kan ta daya hargitse, kaya ta sauya ta dauki key din motar da Suhail ya sai mata ta fice a gidan, direct gidan besties din ta ta nufa,a hanya ma kukan ta ke yi, dan ta kasa tsaida hawayen ta dake zuba.
Tana shiga ta fada kan kujera ta rintse ido, dan basu nan da key din hannun ta ta bude, ganin table din nasu tai ba wasu kayan da yawa, haka ta ja jiki hannu na rawa, bakin ta a bushe ta fara durawa empty cikin ta kayan mayen nan, tana zubda hawaye, sha tai tayi mankas, sai da ta ji bata jin wani zafin abinda ya faru a qirjin ta sannan ta bari.
Dariya kawai take tana zage2, dan ji take kamar tana hango Suhail tana ta caka.masa wuqar nan a ciki.ba a baya ba, sannan tana fada masa dikkan abinda take son furta masa.
A haka qawayen nata suka shigo, suka same ta,Malika ce ta kalli, Ladeefa, tace,
"My goodness not again,"
"Hummm here we ar, yau kuma ko uban me ya aikata? Ni fa da zata ban dama sai na ci ku........ uban gayen nan, wai shi devil din ina ne? Dubi idon yarinyar nan da alama bata samu bacci ba, kuma da kin kalle ta kin san tare take da yunwa,"
"Je ki dakko madara, ki zubo zuma a ciki,"
Da sauri Malika, ta wuce fridge, ta dakko madara ta dau glass cup dake saman fridge din, ta zuba madarar ta zuba zuma, kitchen taje ta dakko spoon ta juya, da sauri suka daga ta suka dura.mata madarar, bata so, amma haka suka bata.ta shanye tass.
Bata jima da gama sha ba ta fara kwara amai, sai da ta amayar da komai na cikin ta sannan ta koma ta kwantar da kan ta, ko a fuskar su ba damuwar aman da ta kwara, har rige2n dakko abun.gyara wajen suke, kuka suka dawo suka tadda ta tana yi,
"Da kun barni a buge na ni, yanzu.kunsa munyi asarar komai, zuciyata ji nake kamar zata.fashe,"
Basu kula ta ba sai da suka gama.gyara wajen, sannan suka zauna kusa da ita,
"Besty kar ki kashe kan ki akan wannan banzan, ya kamata ki dawo nan, zama da shi ba alkhairi ba,"
"Ya kuke so nayi ne? So kuke na tafi na.bar masa ita ya kashe? Jiya na samu na caka masa wuqa na so ace ya mace kowa ya huta, amma shegen bai mutu ba, bansani.ba ko dan ban caka.masa daidai bane,"
"Wai ke da an magana kice ba zaki iya barin ta ba,ai ita ga shi ta kai ki cikin wahala kuna ta shan wuya dika,"
"Kun san fa alqawarin da mukai wa junan mu dani da ita, sannan koda.mun gudu kawunan mu da Inna Atika ba zasu karbe mu ba, zaman kanmu kuke son muyi?"
Malika ce ta kalle ta cikin fushi tace,
"Kuyi zaman kan naku.mana,sai me? Ni baga ni ba, xaman kan nawa nake tin abinda ya faru dani, me ya samen,"
"Besty dik da har yau kinqi fada mana.me ya.rabo ki da gida amma i have to.be honest, zaman kan nan namu da muke ba abin arziqi bane, bai kamata mu ba qawar mu shawarar nan ba,"
"Stuation ke kawo hakan, ba son rai bane ai, in sona ne na zauna da mijina da yarana da iyayena, amma ba gani ba, me ya samen? Ina zama cikin aminci da jin dadi,"
"Guys, guys ya isa haka, ba zamuyi zaman kan mu ba, ba zan kashe mata aure ba, yanzu abinda zan maida hankali shine neman mijin aure na dauke ta kawai.na kaita wajena, shikenan, bari na koma naga halin da take ciki, dan kwana biyun nan bata da lfy sosai, ga abinda ya faru jiya kuma,"
Miqewa tai cikin ta taji yana qugin yunwa, tin jiya bata ci komai ba sai kayan maye kawai data durawa kan ta.
Kitchen dinsu ta shige, dan kwalam da maqulashen da ke aje ta bude tai ta durawa cikin ta, sannan ta fice.
Binta kawai sikai da kallo,cike da tausayawa qawar tasu.
Ko da ta isa gidan bata ga kowa ba,dama ta san za ai haka, tsaki tai ta shiga wanka, tana fitowa ta sake kaya ta shirya zuwa makaranta, dan tana da lecture da yamma..........
*Nima ina tausaya miki Samha*😭😭😭😭😭😭😭😭😭💅🏼 MIJIN YA TA KO MIJINA 💅🏼
BY HAERMEEBRAERH
Page 3:
Tana tashi daha skul gidan su Malika ta wuce, dan ba ta son su yi ja in ja da yayar ta ta akan kai masa abinci da tai, tana son ta dan huta da komai da yake faruwa da ita kan ta koma.
Kitchen ta gan su, da sallama ta shiga, ta daga masu hannu ta wuce, sai da tai alwala tayi sallah, sannan ta sako dan qaramin wando da vest ta gyara gashin ta ta taho kitchen din itama,
"Wai me kuke yi ne tin dazu, ga gidan ya cika da qamshi, ga shi kun dade baku fito ba,"
Kallon ta sukai,.sannan suka ja hannun ta, qaton cake ta gani, an saka Happy 25th birth day Samha, idon ta ne ya cika da kwalla, dan ita ta manta ma gaba daya yau birthday din ta tana cikin tashin hankali, ya zata samu tinawa, rungume su tai suka dan jima a haka,
"Thanks guys, i love u,"
Ladeefa ce ta kama kumatun ta, ta turo baki kamar tana wasa da yaro,
"Awww u ar so cuteee, we love u more,"
Kwacewa tai ta harare ta, dan ita ce sa'ar ta, Malika ta girme su, lakutar cake din zatai Ladeefa ta make hannun ta, tana kada mata tsaya, sama tai da idon ta ta kwantar da kan ta a bayan Malika, tace,
"Ki mata magana, kar na shaqe mata wuya, ba ruwana ni,"
"Eh ai ni ce qaramar dangar ki kin shaqe ni mana,.baki shaqe shegen Yayan nan naki ba sai ni, matsoraciya kawai"
Kallon ta tayi da fuskar da ta sa suka daina dariyar domin sun san me hakan ke nufi, ta wuce parlour, ta zauna dabar a kujera, tare da limshe idanun ta,
"Da baki mata wannan wasan ba, this is her day, shiyasa tin da muke bana son na zurfafa tambayar kowa labarin shi sai iya abinda kowa ya so mu sani, dan haka u have to say sorry,"
"Ok"
Daukan cake din sukai, suka je parlourn suma, tare da mata waqar BD,murmushi tayi mai kama da yaqe, ajewa sukai suka koma kwaso sauran su pepper chicken da fride race with salad, sai drinks wanda Ladeefa ta so a saka da na maye Maleeka tace a'a yau so take su taba hirar yaushe gamo.
Dan haka cikn dabara da wayo suka hilace ta, suka yanka cake suka zauna suna cin abincin suna hira, cikin raha da shaquwa irin ta qawaye.
A tare suka gyara wajen, suka wanke kwanukan, sauran abincin suka saka a fridge, kiran sallar magariba ne ya sa suka tashi yin sallah, Maleeka da bata sallah tana zaune, tana latsa wayar ta.
Bayan sun dawo ne suka zauna, Maleeka ta kalle su ta yi gyaran murya, sannan ta fara magana,
"Sanin kan ku ne munyi shaquwar da ta wuce ta qawance ta kai ta 'yan uwan taka
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 1 Chapter of 13