Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
6 / 13
ta taba kiran Fahad ba sai dai ya kira ta, yaji ya take, sannan ya turo mata kudi, for the first time kenan data danna no shi dan kira, yana dagawa sukayi shiru, daga baya tayi sallama ya amsa, ta sanar da shi qudirin ta yayi shiru bai ce komai ba, sai da ta dade tana masa bayani sannan ya amince, yace ta je Abujan in ta kammala abun da take, sukai sallama ta kashe wayar. Duba lokaci tayi, sauran 45mnts a tashi yara daga makaranta kasancewar yau juma'a ne, kayan ta ta hada tsaf a akwati, suka sha koke2n su, ta mallaka ma Samha komai, ta zuba kayan ta a boot ta ja mota tayi makarantar yaran nata, jira tai a ciki har aka tashi, fita tayi da Chocolate din data kula Amir din ta na matuqar so, Amrah kuma babyn roba mai kyau ta dakko mata a cikin irin kayayyakin yaran da take siya domin su, zuwa tayi ta df kafadun su, ta ce masu yau Abban su yace tazo daukan su, ita abokiyar aikin shi ce a office, ta zare glass din idon ta,Amrah na ganin ta tace " laaa Amir kaga muna kama da ita, ni dai zan bita," "Ke ba Abba ya hana bin strangers ba? Sai an sace ki an yanka kan ki an shanye romo," ba ruwana" "I am not a stranger. Muje lokaci na tafiya, Abban ku na jira, yace nai sauri na kai ku wai ko zakuje Mall ne na manta," Da jin haka suka fara murna, suna ta murna, da tsalle,da sauri ta saka su a mota,ta fara tafiya dasu, motar ta zata gifta ta Abban nasu na shigowa, da sauri ta wurga masu chocolate da babyn dan su dauka, suna sunkuyawa dauka ta fice," "Woooo that was close," "Kids, yanzu zamu je na aje saqonnan da kuke gani, sai na kai ku inda Abban ku ke meeting da shugavan companyn mu kunji, akwai nisa wajen sosai, daga nan sai na aje ku gida, kuyi wanka kuci abinci, ku je mall din, zaku dani?" "Ehhhhh zamu dake mana, ni dai ina son ki ko kin aje mu ki dinga zuwa gidan mu wataran fuskata da taki iri daya ne," "Nima ina son ku dika," Cikin muryar da zata tabbatar ma da wanda ake ma magana gaskiya aka fada, ta furta hakan, sun jima suna tafiya, yara sun gaji, tini bacci ya debe su, ta rage qarfin AC,ta qara gudun mota, sai ABJ................... *Cassssss waye zashi abujaaaaaa💃🏻💃🏻*[18/11 12:02 pm] Prince-s-square: 💅🏼 MIJIN YA TA KO MIJINA 💅🏼 BY HAERMEEBRAERH Page 13: Basu bude ido ba sai da suka ji mota ta tsaya, sannan suka bude idon su, kusan a tare, Ameer ya riga Amrah tashi, ganin matar da ta dakko su sukai a waje da wani suna magana, ba su san shi ba, "Amrah ina ne nan?" "Ni ma.na sani, wataqila wajen Abban mu zata kai mu, Allah yasa wani gidan aka canja mana mu huta da dukan Aunty," "Ameen, amma ni dai nafi son naga Abbana nan wajen bansan ina ne ba," "Kids kun tashi? Maza muje to gidan da zaku sauya kaya, kuci abinci sannan muje mall, Abban ku ya turo saqo ba zai samu damar zuwa ba, saboda aiki ya masa yawa," Daga mata kai kawai suka yi, ta bi motar Fahad, a baya suka wuce unguwar da yake da zama, wani babban gate suka ga an bude, Fahad ya saka motar shi ciki, bakin ta hude dana yaran tare da kiran "Wowww" Basu sake sakankancewa da kyaun gidan ba sai da ta kama hannun su suka shiga ciki, gaskiya Maleeka tinda take bata taba ganin gida mai kyau haka ba. "Bismillah muje mana, naga kun tsaya," "Yah Fahad wace sana'a kake haka? Wannan gidan...... and all the cars out side.....ban gane ba? Ni yanzu a tsorace nake da kowa, dan Allah kamin bayanin gaskiya, zai yu mu zauna anan ko na kama mana haya har na gama me nake?" Dariya yayi sosai, sanan ya nuna masu wajen zama, ya dauki Amrah ya dora a jikn shi, bayan sun zauna ne yayi gyarab murya sannan yace, "Maleeka ,Maleeka, Maleeka, wato kina zaton ko ina wani sana'a mara kyau kenan? Hhhhh gaskiya kin ban dariya, sana'ar da muke yi ni Abba, Anwar, ita nake yi har yanzu ban sauya ba,in kin kula ni banda iyali, banda uwa banda uba, sai 'yan uwan mahaifana, danake kula dasu, a qauye, da ina da mata da yara shine dukiyata ba zata ba kowa mamaki ba, amma yanzu na tara ba masu cin ta kamar masu iyali, kinga ko dole kiga gida haka," Ajiyar zuciya ta sauke mai qarfi, wadda zata nuna ma kowa cewar hankalin ta ya kwanta. "To ku tashi muje mu ku yi wanka, muje aci abinci, a siyo sabbin kaya, dan a sauya na makaranta ko?" "Dan zo muyi magana pls," "K" Tashi sukai suka je wajen dinning, suka tsaya, kallon yaran take cike da so da qauna, da kuma tausayawa, dan ta na sane da wahalar da Auntyn tasu take basu, da dik wata rayuwa da suke ciki, sun san mahaifiyar su rabuwa sukai da Abban su, dan haka tace ma Fahad, "Yah Fahad shawara nake nema, kana ganin na nuna ma yarana nice mahaifiyar su ko nayi shiru, na rasa ya zan, ga qarya danake ta shara masu, gashi na tabbata ba yau ko gobe zan maida su ba, plsss ya zanyi da ba zai affecting tinanin yarana ba?" "Kar ki damu muje mu sanar dasu komai, yaran nan suna da wayo fiye da yanda kk zaton su, muje," Cikin dari2n abinda zasuyi ta bi bayan shi, zama sukai ta toshe bakin ta da hannayen ta da sukai sanyi, ta qurama yaran ido, tana kallon kuma Fahad. "Kids, ku saurari abinda zan sanar daku da kyau, ku fahimta kunji? Abinda baku gane ba inna gama fada maku komai sai ku min tambaya kunji?" "To uncle," Murmushi Fahad yayi, sannan ya kalli Maleeka da idon ta yake cike taf da hawaye, ya yaran nata zasu karbe ta? "A gaskiya ba Abban ku bane yace ta dakko ku, sannan ita ba mai satar yara bace, itan Mummyn ku ce, na san kun dade kuna tambayar Abban ku ina Mummyn ku, ni na san ku amma kune baku sanni ba, ni abokin mahaifin ku ne,kuma dan uwan mahaifin ku, sanda nake zuwa kunyi bacci, da safe kan ku tashi na tafi, wannan ita ce Mummyn ku, ta dakko ku ne dan tana son kasancewa da ku, kuna son ta? Ko ta kaida ku bazaku sake ganin ta ba?" Da gudu suka qanqame mata wuya, suna murna, mai hade da zubar hawaye, suna kiran. "Mummy plsss kar ki sake tafiya ki barmu wajen Aunty ba ta son mu, Mummy muna son ki kar ki maida mu," Hawaye take.mai zafi, kuma mai dadi, bata taba zaton yaran ta zasu yarda da ita a matsayin mahaifiya ba, rungume su ta sake yi sosai, ba suyi aune ba lokaci ya tafi sosai, miqewa sukai, ta musu wanka, itama tayi ta sauya kaya, ta saka masu kayan da take dan siya, saboda su, sai murna suke, kayan Amrah ne ya dan mata yawa,.shi kuma Ameer kamar an gwada shi, sai murna suke, suna gamawa ya kwankwasa qofa, ya musu magana su je suci abinci, da gudu yaran suka fita, suna ganin shi, suka fara kiran, "Wooow Uncle u ar so handsome," "And so u ar, my durlings, ku je mu ci abinci yuuuunwaaa nake ji," Dariya sukai masa, sannan Maleeka ta fito, kallon ta ya tsaya yi, har bai san yaran na kiran ta ba, a cikin ran shi yana qudurta dole ya bar wannan gidan, ya koma qaramin gidan shi da zama, ba zai yu su zauna gida daya ba inaaa, she is too beautiful, tsohuwar soyayyar ta ce ta dinga dukan zuciyar shi tana taso masa, hannu tasa ta dan kada a gaban idon shi sannan ya dawo daga tinanin daya shiga, "Muje ko?" "Eh...eh muje," Gaba ya shiga riqe da hannun yaran tabi bayan shi, tana masu kallon sha'awa dikkan su, sun mata kyau a tare. Wani babban Mall suka je, abinci suka fara ci, sannan suka yi siyayya, kayan sawa, kayan abinci, da kayan aikin da dole sai sun buqata, wanda shi da dayake shi daya bai dasu. Suna gamawa suka nufi gida, bayan sun shirya komai a mazaunin shi, da shi da ita da yaran, suka dan zauna suka yi hira, can daya ga suna jin bacci yace, "Ni zani gida, ina fatan ba abinda kuke buqata?" "Ahh ba anan zaka kwana ba?" "Eh ba anan zan kwana ba, a gaskiya ba zai yu na kwana anan ba, kema na san zaki fahimce ni, a yanayin da muka tsinci kanmu a baya, ya kamata mu kiyaye dokar Allah,sai Allah ya kiyaye mu, zamana anan, zai bamu kusanci,kuma shaidan ba anesa ya ke ba, a kusa yake, so akwai gidana dake gaba da nan kadan,zan koma can, da safe zan zo nan din, ku kwana lfy," Da kallo ta bishi dan bata da bakin gode masa, ya fahimci hakan, yayi murmushi, ya miqe,ya dau yaran ya kai mata daki, sannann ya dawo, kada mata hannu tare da murmushi,ya bude qofa ya fice. Zama tayi, tana tinanin irin kallon da yake mata mai dauke da tsantsar so da qauna, "Ohhhh Allah,Allah kasa nima bai ga idona a yanda nake kallon nashi ba, wannann abun kunya ne, daga haduwa after so many years, wayyoo kunyata, Allah kasa bai gane ba," Cire dankwalin ta tayi tana yamutsa hashin kanta, a haka ta miqe ta shiga bacci, a nan ma da tinanin shi ta samu bacci. ♡♡♡♡♡♡♡♡♡ Sun isa Zariya, lfy, Ladeefa ta shaqi iskar mahaifar ta, bayan shekaru masu yawa, tate da lumshe idon ta Sammani na kallon ta ta mirrow, cikin tausayawa. Kallon shi Sadam yayi, ya juya ido, ya saka hannu ya shafi hannun sammani, kallon shi ya danyi, motar da tazo daukan su guda biyu ne, suna cikin daya, inda drivern su ya shiga daya motar, suka koma gida, su kuma suka dau hanyar gidan Mahaifin Ladeefa,wani tsoro ne ya kama ta, dan bata san me zai fada masu ba ya raba auren su, ba ta san me zata fada ba, hannun ta ne ke zufa ga shi sai rawa yake, "Ki kwantar da hankalin ki, ba abinda zai faru," "Wataqila bata da gaskiya shiyasa ta damu🙄" "Babe plsss, ka kyale yarinyar nan, banda ra'ayin kowacce mace tinkan ka fara harkar nan, balle da ka fara na san ka, ba qata mace da zata shiga raina bayan kai, ba namijin da zai shiga raina bayan ka, dan Allah ka daina abinda kake, kuma naga daga yau me zai sake hada ku? In dai ba nan gidan su zaka zo ganin ta ba," Ya qarasa maganar da wasa,yana kallon masoyin nashi, hararar shi Sadam yayi, "Allah ya kiyaye akan me?" Itana hararar shi tayi tayi tsaki. "Allah ya nesanta ni da ku," "Ameen muma ba son sake ganin ki muke ba," "Ya isa mun zo," Motar na tsayaw ta fita, tana zare ido, kayan ta Sammani ya dauka,suka fara shiga, sallama sukai tayi, kafin daga baya Maman ta ta fito daga kitche, kallon kallo suka tsaya yi, daga baya mamanta ta....... .. *Amin hakuri, inshaa Allah zuwa gobe zanci gaba, na gode da addu'o'i na gode sosai, Allah ya saka da alkhair, Alhamdu lilLAAH naji dama, ga tabbaci nan na maku page sukutum💃🏻* [18/11 1:06 pm] Prince-s-square: 💅🏼 MIJIN YA TA KO MIJINA. 💅🏼 BY HAERMEEBRAEH Page 14: Da sauri Maman ta ta je ta rungume ta, tana murna, sai qoqarin riqe kwallar dake barazanar balle mata take, Ladeefa kuwa kuka take sosai na farin cikin kasancewa da mahaifiyar ta, "Mama ina Babana?" "Baban ki na ciki," Da sauri ta saki Maman nata tayi hanyar dakin Mahaifin nata, a hanya sukayi karo, bai zato ba kawai yaga gudan jinin nashi, da sauri ya jata jikin su, ya rintse ido, "Ji nake kamar bazan sake ganin ki ba a rayuwa ta, ashe da rabon zamu gana,nayi kewar ki matuqa, naso na bi ki qasar taku tinda kin maqale kullum sai waya, da alqawarin kina nan tafe amma shiru," Cikin kuka take magana, "Babana na dawo ke nan ba zan sake komawa ba sai da izinin ka," "Habaaa bana yi sn kai ba ai kuma na hana ki bin mijin ki, zaki koma a duk sanda yaso," Sunkuyar da kai tayi, a zaton shi na kunya ne,janshi tai suka nufi parlour,inda kowa ke zaune, mahaifiyar ta ta kasa rife bakin ta saboda murna, Sammani kuwa a ranshi ya qudurta ba zai yi abinda suka shirya ba,dole zai fadi gaskiya, ko ba komai,a yanzu qungiyar su tayi qarfin da ko ina aka kaishi aka daure sai ya fito, (daurin mutum ba Sammani, amma ka sani daurin Allah na Allahn ne, ba mai fidda ka sai Allah din,dan haka ka tuba d kai da masu irin halin ka, ko Allah ya muku rahama ya sassauta maku, ko ya yafe maku baki daya). "Lallai da dikkan alamu kina biyayyar aure, domin dik wannan sabbin abubuwan da kk gani gidannan Mijin ki shine ya ke mana har Hajji sai da ya kai mu, na ma zaci zami gan ki can, amma bamu gan ki ba sai da shi da abokin shi ne sula samu zuwa, yace makaranta kk, yanzu kina mataki na nawa kenan?" Kuka take sosai saboda wannan dik qarya ne ai, amma still taji dadin yanda ya kula da mahaifan ta, "Baba ina matakin qarshe, a bangaren medicine, ni da qawaye na, kasan karatun medicine bai da sauqi ko kadan, sai a wajen Allah, zaman mu waje daya bama yawace2 shine babban taimakon mu, yanzu haka.muna matakin qarshe, ba zai yu na zauna anan ba zan koma makaranta daya ce take da dauran shekara biyu," "Masha Allah, lallai ashe babbar likita muke magana da ita," "Inshaa Allahu, thanks tu Maleeka, da yayan ta," "Wace ce hakan?" "Qawata ce Baba," "To Allah ya muku albarka dika, Allah ya saka ma ta da alkhairi," Daga nan Sammani ya gyara zama, ya yi gyaran murya tare da sa hannu shi wajen bakin shi, kamar mai shirin goge wani abun, "Ammm Malam, kai mutumin kirki ne, haka yarinyar ka mutuniyar kirki ce, da dikkan alamu bata watsar da dikkan tarbiyyar da kuka mata ba, a qashin gaskiya ni da yarinyar ku bamuyi zaman aure ba, bamu zauna tare ba, tana garin kano tana karatun ta da qawayen ta, guda biyu, ta bar gidana ne tin lokacin data gano ni din maza nake bi,ma'ana ni din dan LUWADI ne, kuma har aure garen, ga shi nan, Sadam, shine wanda na aura a ranar da aka daura mana aure da Ladeefa, Sadam shine wanda ya bude mata gida ta fita ba da sani na ba, munyi neman ta har mun gaji, kullum da Sadam kuke magana a madadin ta, kullum akan neman ta nake, ban same ta ba, bai shekaranjiya da ta ganmu a Mall ta bi bayan mu, yarana suka dakko ta na gan a she ita ce, na dakko ta yanzu.na dawo maku da yarinyar ku, ban taba dora mata idda ba, dan ban kusance ta ba, na sake ta saki uku ga ta nan, dan ko na zauna da ita ba abinda zata iya min, ko da nayi auren ne dan kare suna na, amma a yanzu danae tare da manyan qasar nan, ba wanda nake tsoro, ko ina za a je ina nan a kan bakana, bana son mata sai maza, na gode da qaunar da ka nuna min da fari ka auramin yarinyar ka daka fi so," Kowa a wajen banda Ladeefa a qame yake, musamman Sadam, ai ba haka sukai zasu yi va, sunyi zasu mata sharri, dan rufawa kan su asiri, su bar ta su tafi, lallai ma Sammani, ashe haka zai masa har ya tanadi wasu kalaman, shikenan ai, nan danan ya bata rai, Sammani ya kula amma ya share, Malam kanshi sai da ya zubda hawayen tausayawa yarinyar tashi, Mama kuwa tinawa kawai take da wayar da sukai da Ladeefa da abinda ta sanar da ita, da yanda ta mata kaca2, akan gaskiyar ta,wani kuka mainqarfi ta saka sannan tace, "Ladeefa ki yafe ni, nice silar komai, ki yafe ma mahaifiyar ki, ba dan matsayina ba a wajen ki, sai domin Allah, da wata hanyar kika fada mara kyau ba zan yafewa kaina ba, Ladeefa ki yafe min;" Da sauri Ladeefa ta je ta zauna a qasan qafar mahaifiyar ta ta dora kan ta a cinyar ta,tana shafa qafar, tana furta, "Mama qaddarata kenan, Allah ya hukunta sai hakan ya faru da ni, n yafe maki, Allah ya yafe mana dika, Mama kin yi kuskure mai girman da da yanzu dana bar gidan Sammani na fada mugun hannu wataqila da kun rasani har abada kenan, ya kamata da dana fada maki sai kice nazo a zauna a tabbatar da me gaskiya a cikin mu, amma kk min abinda kk min, shikenan dai ya wuce, Allah ya yafe mana dika," "Kinyi gaskiya Ladeefa, abbas nice mai babban laifi, kuma ko a hira ban taba sanar da mahaifin ki ba, jin muna waya dake baki sake tada zancen ba, ya tabbatar min qarya kika ma bawan Allahn, ashe ke ce me gaskiya Allah ka yafe min, Allah na gode maka da ka dubi yarinya ta bata da laifi ka kare min ita," Malam ya rasa me zai ce, dik yanda yaso kalma daya ta fita a bakin shi kasawa yayi, Sammani ya kula da hakan, ya miqe tsaye, Sadam ma ya tashi, "Malam hakuri kaima zaka yi, na san kana mamakin ya akai na zama haka, dama tin da haka nake, tin kan haduwar mu, kai na fara so kafin na hadu da Sadam, kai kuma sai ya zamana ba wanda ka tsana irin mu, daga baya dana samu Sadam zamuyi aure sai aka ban shawara nayi aure saboda rufawa kaina asiri, shine ka ban yarinyar ka da ka fi so a duniya sama da komai naka, sakamakon ganin na dade ban aure ba, ka yafe min dik da na san zai wahala hakan, sai watarana," Hannun Sadam ya kama, wanda suke watsawa juna harara shi da Ladeefa, suka fice, sai bayan sun fita da jimawa Malam ya fashe da kuka, Ladeefa ma kukan take, Mama ce ta je kusa da shi tana bashi baki, da kyar yayi shiru, sannan yayi ta godewa Allah da ba wani cutuwa da ta samu yarinyar shi sai dai ma qaruwa tinda tana karatu. Hira sukai tayi,suna nan nan da ita kamar zasu maida ta ciki, addu'a malam ya hada su sukai, Sammani kuwa yace yaje zai gani, abinda ya masa ya ci amanar yardar da ya masa, Allah baya barin maciya amana, ba su kyakkyawan qarshe, Allah na nan a madakata, ba zai yafe ma Sammani abinda ya masa ba. ♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡ Samha kuwa qin komawa tayi gida, Amatullah tin bata damu ba har abun ya dame ta, yau ta qudirta zata bi Samha gidan qawayen nata ta lallashe ta su koma gida. Bayan ta kai ma Suhail abinci, yanzu yaba dan mata magana, amma ba wani mai tsaho ba, tana tafe tana tinanin anya tana ma qanwar ta ta adalci kuwa? Gaskiya ba zata biye ma son zuciyar ta tana yin abinda zai cutar da qanwar ta ta ba, zata gyara komai, bari komai y koma daidai. A waje ta aje motar ta ta fita ta qwanqwasa, shiru taji, alamar ba kowa a gidan,taso ta tafi, ta ce bari ta shiga mota ta jira ta ga ni, tana zaune, bayan wasu mintuna taga motar Samha ta shigo layin, a kusa da tata motar ta Samha ta tsaya,ta zuge glass din motar, fuskar ta ba yabo ba fallasa dan gaskiya tayi kewar yayar ta ta, Amatullah kuwa murmushi tayi, tace, "Ni ban tava sanin qanwa na ma yayar ta yaji ba sai akan ki, muje gida," Bata musa mata ba ta tada mota suka nufi gida. Bayan sun shiga sun zauna, ba mai cewa komai, Samha na ta wasa da cup din Juice din dake hannun ta,Amatullah ta dafa kafadar ta. "Samha i am so sorry, na gano tsantsar son kaina da son da nake yiwa Suhail na neman sawa na manta da kaina gaba daya, dan ke ce ni, kece farin cikina, inshaa Allahu, daga wannan karon Suhail ya gama wulaqanta ki ta hanyar neman ki da yaks, ba an sake bari hakan ta faru ba, inshaa Allahu, i promise u ba abinda zai sake faruwa wanda baki so,ko mene ne shi," "Zan iya yarda kuwa? Kina ma Suhail son da zan iya cewa ya wuce misali Yah Amatullah, anya zan sake jikina kuwa?inaaa sai na ga ya zaki handling komai kafin zuciya ta ta aminta da alqawarin ki, amma ni zan so ki min izini na ci gaba da zama a gidan can, har na gama karatu na in yaso inna gama na dawo,bayan haka ma in kin kula ai ya fi kusa da tafiya makaranta, akan nan, zan dinga leqo ki lokaci zuwa lokaci, in baya ganina ba zai neme ni ba, hakan ma zai baku damar sake shaquwa da mijin ki," "Amma kin san bana son muyi nisa da juna ko?" "Na sani shi yasa ma ba zan dinga kwana biyu ba tare dana zo na gan ki ba, wannan alqawari na ne, zan dinga zuwa akai2," "Shikenan, amma yanzu zamu zauna ai har ya dawo ko?" "Eh zamu zauna ina nan, su Ladeefa ma sunyi tafiya," Nan suka zauna suna ta hira har Samha ke bata labarin asalin qawayen nata, ta ji tausayin su sannan a ranta ta sake qudurta ba zata bar qanwar ta ta shiga gararin rayuwa ba, saboda son zuciyar ta. ♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡ Kwanan Maleeka Uku a gidan, ta yanke shawarar komawa, saboda makarantar ta, sannan tana tinanin sauyawa yaran makaranta,inda Abban su ba zai sani ba, tayi shawara da Fahad, bai so suyi nesa da shi ba, amma ta mishi alqawarin da ta kammala watannin da suka rage mata zata dawo Abuja da zama, sai ta sauya ma yaran makaranta, ba dadi haka suka tattaro, suka hawo jirgi zasu dawo, ta sanar da Samha dan haka Samha ta yi wa Amatullah sallama zata je gyara gida, daga nan ta dakko su. ♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡ Ladeefa ta fara karkarwa saboda rashib kayan maye, tafi sauran shaye2, dan ita bata iya kwana biyu bata sha ba, su kuwa sai damuwa ta musu yawa suka fi sha, dan haka kan asirin ta ya tonu ta shirya komawa makaranta, Maman ta ta fuskanci rashin lafiya a tare da ita, ta nuna ba komai, ta damu da komawa makaranta ne ana ta karatu an wuce ta shiyasa, amma lfyr ta qalaou, Malam ya yi qoqari dan kuwa mota ya sai mata qarama mai kyau, tayi ta murna, tana tsalle, kamar wata qaramar yarinya, su kuwa farin ciki ke lillive su in suka ga diyar tasu cikin murna, a ganin Mama ba abinda zata ma diyar ta ta ta wanke baqin cikin da ta jefa ta a ciki, a kullum cikin kwantar masu da hankali take. Tasha Malam ya je ya samo drivern da zai kai ta a biya shi, da kuka suka rabu da Mama, ji take kamar kar ta bar gidan, amma ta musu alqawarin suna gama karatu zata dawo gida. ♡♡♡♡♡♡♡ Yau aka sallami Suhail daga asibiti, wanda ya ke cike da buri kala2 a zuciyar shi, suna hanyar komawa gida yana murmushi, wanda da ka gani na mugunta ne............ *Ta Allah ba taka ba Suhaillll* [18/11 10:07 pm] Prince-s-square: 💅🏼 MIJIN YA TA KO MIJINA 💅🏼 BY HAERMEEBRAERH Page 15: Suna isa gidan ya tsaya kalle2n harabar gidan, masu aiki na ta masa sannu da dawowa, suna mishi ya jiki, daga kai kawai yake kamar wani me nazari, bai ga motar Samha ba, kallon Amatullah yayi wadda tai kicin2, dan ta kula da me yake kallo, wucewa tayi, ciki, ya bi bayan ta, "Ina take?" "Bata zama anan yanzu," "What do u mean bata zama anan yanzu? Kina hauka ne? Ina kk barta ta tafi?" "Indai Amatullah kk aure ga ta a gaban ka, amma in Samha ka ke aure bata nan, ta tafi inda hankalin ta zai kwanta, ta kammala karatun ta ta tsaya da qafar ta ba tare da wani ya keta mata haddi ba har mijin da zata aura ya raina.ta yace ta gama.lalata da mijin yayar ta sannan tai aure ba," Cikin matsanancin fushin da bai san tana da shi ba take

Chapter 6 of 13