Reading LAUJE CIKIN NAƊI by ZAINAB FALALU Chapter 9 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

fito?
Ya safiya ke kiran ki bani ba" ta juya sukaci gaba da magana da umma ƙarama



Goggo safiya tace "shiru mumtaz banji kince komi ba, bana so kizo kina danasani daga baya"



Shiru tayi bata ce komi ba, umma ƙarama tayi tsulum tace "Ya safayi shifa yaro ba'a mishi dole,
in bata son wancan ta kawo wanda yafi kwanta mata mana"

Taɓe baki mama tayi, badai ta saka musu baki ba

Goggo safiya tace "haka maganar ki take sumayya, ni nagartar yaron kawai nake hangowa
wallahi"

Umma ƙ ta kalli mumtaz cike da kulawa tace " a cikin samarin naki wanne kk so tunda kamar
baki gama aminta da shi khalid ɗin ba"?
Kafin mumtaz tayi magana mama tace "ba se in akwai wasun ba, da bakin ta take korar su,
nasha zaunar da ita ina nuna mata illar hakan amma yarinyar nan ta maidani wata gani can dai,
to ga ranar maganata nan"



Zumɓura baki mumtaz tayi, duk maganganun su sun isheta,

Ga khalid ya jima da zuwa yana jiran ta, gashi su kuma sun titsiyeta a nan.

Suna tsaka da surutun su megadi ya ƙwaɗa sallama a ƙofar palon

Altine ce ta leƙa, ya faɗi saƙon ya juya



Tana komawa ciki tace "Tunɗazu baƙon na jiran ki wai mumtaz"



Salati goggo safiya ta saki haɗe da riƙe baki "yanzu fisabilillahi ajiye shi kikayi yana jira? to
gaskiya baki kyauta ba tashi kije"

Daman maganar su ta ishe ta,
Da sauri tayi waje ta barsu da binta da kallo.




Khalid na zaune a mota yaga fitowar ta,
Ajiyar zuciya me sanyi ya sauke ganin ta fito fuskar ta a sake ba kamar jiya da yazo ba

Da sauri ya fito ya tako zuwa wajen ta

Fuska a washe yace "barka da fitowar sarauniyar kyawawa"

Murmushin ta me kyau ta saki tana sunkuyar da kanta ƙatsa

"muje ciki" tace, tana gaba yana binta a baya har palon baƙi.



Da ƙyar da jiɓin goshi a ranar mumtaz ta yarje wa khalid turo manyan shi kamar yarda ya jima
da nacin tambaya"



Tsabar murnar maganar data yi yasa shi tashi ya fara juyi yana rawa yana mata waƙar "ta kusa
zama tawa, ta kusa zama tawa"



Ganin murnar da yake yasa yasata jin nutsuwa sosai a cikin ranta

Tun tana ɓoye fuska tana dariya har ta dena ta koma yin ta a fili,

Tsabar murna duk abinda aka jera mishi beci ba, time ɗin tafiyar shi ma beyi ba yayi mata
sallama ya tafi cikin zumuɗi da zakwaɗin sanar wa mami.



Tana komawa ciki kusan a tare sukace "har ya tafi?"

Mama tayi caraf tace "ko kuma ta koreshi ba"



Goggo safiya tace "Daɗina dake wani lokacin baki faɗin alkairi zahra'u,"

Murmushi mama tayi taci gaba da danna wayar hannun ta.



Mumtaz ko a jikin ta, seda ta shiga ɗaki ta ciro hijabin jikin ta tukun ta dawo palon, kusa da
goggo safiya ta koma ta zauna

Ƙince ma kowa komi tayi, seda ta mula ta mulmule tukun tace

"wallahi ji nake a raina dama ban amsa mishi ba"

Ta gefen ido mama ke kallon ta, ba dai tace komi ba dan kar tayi tunanin ta matsu taji

Goggo safiya ce ta gyara zama tukun tace "bana son iskanci mumtaz, duk kin bi kin saka mu a
duhu, shin kin ce ya turo ne koko wani taɗin kike yi na daban?"



Tura baki tayi gaba kafin tace "ai shine nace nayi danasanin cewa na yarda ya turo ɗin"



Kusan a tare umma ƙarama da goggo safiya suka saki wata narkekiyar guɗa wanda seda yasa
Altine dake baya shigowa da sauri

Mama kam ajiye wayar hannun ta tayi, haka kurun taji gaban ta na faɗuwa ba gaira ba dalili.
Tsabar haushi mumtaz barin wajen tayi

Kallon yarda mama ke binsu da ido goggo safiya tayi

Cike da murna tace "naga kamar kina wani basarwa zahra'u"

Kafin mama tace komi umma babba ta shigo itama, duk dan saboda yaya safiyar suke yawan
shiga sasan maman, duk da umma babba bada son ranta hakan ke kasancewa ba



Waje ta samu ta zauna, fuska ba yabo ba fallasa ta gaishe da yaya safiyar, sauran ko sannun
ku tace

Jin ana kamar magana me muhimmanci ne yasa taƙi tashi ta tafi

Kowa yasan bata jimawa in tazo, amma yau suka ga saɓanin hakan



Murna nata cin goggo safiya, bata so ci gaba da murnar a gaban umma b ba

Haka nan ta basar ta kalli mama data ci gaba da danna wayar ta tace "Kin dai gani in baki buɗe
ido kin tsaya ma ƴarki ba to ke kika sani, yarinyar da ba ƴar fari bace balle ace zaka ɗanyi
kawaicin wani abun, wasu ma da zasu aurar da na farin basuyi kawaici ba sam"
Kowa yasan da umma b take, dan tana maganar tana kallonta ta wutsiyar ido



Dan haka ki saki zuciyar ki kinuna ma ubangiji godiyar ki.



Umma ƙarama ta amshe da "gaskiyar ki kuwa yaya safiya, Allah dai ya tabbatar mana da
alkairin sa"

Cike da shewa goggo safiya ta taɓa umma ƙ tace "na taɓa ki da alkairi mutuniyar kirki"



Sosai umma babba ta ƙunsa, rai a ɓace ta miƙe tayi hanyar fita
Har ta saka ƙafarta waje ta waigo tace "Duk wanda yayi zagi a kasuwa yasan da wanda yake,
kuma wallahi ya safiya ki kama girman ki tun wuri"
tana gama faɗan haka ta fice fuuuu kamar zata tashi sama.



Umma babba na fita mama tace "kayya ya safiya ni kam bana son irin haka sam wlh"
Banka mata harara tayi, tukun ta waiga saitin umma ƙarama tace "Bazata taɓa sauya ba ita,
daga faɗin gaskiya kinga zata fara jero wa'azin nan nata "

Murmushi umma ƙ tayi kafin tace "zaman lafia yafi komi daɗi ai ya safiya"



Basar da su tayi taci gaba da murnar ta, harda faɗin "tafiya kam ba yanzu ba, se baba ya gani".




******Bayan isha, duka iyayen na nan suka tarbi masu kawo kayan Amal, aka tarbe su kamar
yarda aka tarbi sauran, sosai aka daddara kafin suyi sallama suka tafi.




Ta ɓangaren khalid kuwa yana barin wajen mumtaz gida ya nufa, duk da yasan mami bata nan,
hakan be yana shi komawa gida ba, gaba ɗaya yama rasa me zeyi

Waya ya ciro ya danna mata kira, amma har ta tsinke bata ɗaga ba

Maida kiran yayi ga kiran ƙanwar mamin, da ya sanar mata itama tayi murna sosai, a zumuɗin
ta har ta fara mishi lissafe-lissafen abinda za'ayi.



A daidai lokacin da call ɗin khalid ya shiga wayar mami tana tsaka da kallon videon data zaƙulo
na sanda mumtaz ta ɗaukin abin hannun ta

Sosai abun ya bata mamaki, ta kalli videon yafi a ƙirga

Sosai ta lula tunanin inda tasan yarinyar, daga baya ta gane sun taɓa kwanciya anan.




Kwana biyu da mumtaz ta bashi dama aka saka musu ranar aure, bayan an gabata da komi na
al'ada

Zukatan mafia akasari basu so haɗin ba, to da yake aikin gama ya gamu ba yarda wasun suka
iya dole suka haƙura da bin abun da addu'a.
Ta ɓangaren mus'ab kam ya samu kwanciyar hankali jin har an tsaida magana da khalid ba da
TK ba, sosai ya saamu nutsuwa.




TK tunda aka saka ranar mumtaz aka haɗe da sauran hankalin shi yayi mugun tashi



Takanas ya je ya sami uncle Abbas a guess hause ɗin shi ya tayar mishi da hankali



Da ƙyar da lallami uncle Abbas ya lallaɓa TK haɗe da alƙwari me ƙarfin gaske na mallaka mishi
mumtaz a cikin ƙanƙanin lokaci.



ƘILA KU JINI ANJIMA

ALLAH KASA ANNABI YA CECE MU 🤲
LAUJE CIKIN NAƊI

NA
ZAINAB FALALU(MRS SULAIMAN)

MARUBUCIYAR



👹
MAKIRCI
KISHI DA ALJANA
WANI HANIN GA ALLAH
ƘADDARAR MU
LAUJE CIKIN NAƊI

WATTPAD@ZAINABFALALU8

Pg45-46



Yinin ranar umma b a sama take gaba ɗaya sam Abba babba baya shawara da ita a kan
hidimar nan
Alhalin nata yaran sunfi yawa a ciki waɗan da za'a auras
Tunda ta baro ɗakin shi take yaɓa maganganu marasa daɗi wanda sam bema dace ace tayi su
ba



Amal da shigowar ta kenan daga school ta iske umma b a haka, cike da damuwa tace

"Haba umma, dan Allah kicire wannan abun a ranki, wallahi in kika ga ramar da kikayi se ace
ma jinya kika kwanta"



Wata mahaukaciyar harara ta ballo mata

Aikuwa gumm tayi da bakin ta dan tasan sauran zancen in taci gaba da magana.



Shigowar ya faruk kenan daga tafiyar da yayi ta sati, jakar shi kawai ya aje ya shiga sasan nasu

Nan shima ya taras da banbamin da umma b ke yi

Tana ganin ya faruk tayi shiru ta bishi da kallo

Sama-sama ya gaishe da umma ƙarama dake ta harkan gaban ta, tukun ya shige uwar ɗakan
umma babba



Tsam ta miƙe tabi bayan ɗan nata

Ko gaisuwar shi bata amsa ba ta hau tambayar "ciwo kayi ne acan faruk?"



Tashi zaune yayi tukun yace "aikuwa, zazzaɓin dare nayi"



Zama a gefen gado tayi sannan tace "Allah yasa kaje an duba ka, yanzu haka maleria ce"



Gyaɗa kai kawai yayi,
Shiru ɗakin ya ɗauka, an ɗan jima kaɗan tukun ya faruk yace

"Umma dan Allah ki rage yawan faɗan nan naki, wallahi bana jin daɗi ace sam ba'ajin sautin
muryar kowa a gidan se taki, kuma in anji takin faɗa ne a koda yaushe umma"
Taɓe baki tayi tana kallon shi sama da ƙasa sannan tace

"Ai zanyi mugun mamaki innaji baka tanka ba, ayi tajin muryar tawa mana, shikenan akan
gaskiya ta baza'a barni nayi magana ba?, to wallahi bazata saɓu ba, dole in naga abinda beyi
min ba in tanka"



Dafe gefen kanshi yayi tukunyace "ni ba haka nake nufi ba umma, akwai abunuwan da suna
son a kawar musu da kai, ba komai bane ake tankawa, wallahi mu ƴaƴan ki bama jin daɗi sam,
Baki ganin yarda umma ƙarama ke shanye abubuwa bama kamar akan Abba b, duk zuciya da
fuahin Abba tasan yarda take mishi"



Bata bari ya ƙarasa ba ta miƙe tsaye, idon ta a rufe ta nuna mishi ƙofa tace "Fita kafin zuciya ta
ɗibeni nayi maka muguwar magana"



Jiki a sanyaye ya miƙe, murya cike da damuwa yace "ban faɗi dan na ɓata maki rai ba umma, ki
gafarceni, Allah ya huci zuciyar ki"



Da ƙarfi tace "naji kullum haka kake faɗa, fitar min a ɗaki, kuma Allah ya kiyashe ni zama
micijiya me kan mutum!!"

cak ya tsaya ya kafe umman nashi da kallo jin maganar ƙarshe datayi



Ganin ya kafe ta da ido tace

"bari na maimaita kaji da kyau, cewa nayi Allah ya kiyashe ni zama micijiya me kan mutum!"

Ta juya tayi shigewar ta ciki.



Umma ƙarama na tsaye a wajen dining tana shirya kulolin abincin dare a kai



Kunya sosai ta rufe ya faruk ganin ko kallon inda suke umman bata yi ba

Jiki a sanyaya ya taka zuwa inda take

Murya ƙasa-ƙasa yace "Dan Allah umma ƙ kiyi haƙuri, har yanzu na kasa gane kan umma sam"
Murmushi tayi kafin tace "bakomai faruk, watarana zata gane ni ba mace me zafi bace, kowa da
kalar nashi kishin zaka ga na wani yafi na wani zafi ne kawai"

A ranshi yake faɗin "inama ace haka umman tashi ke da sauƙi hali kamar na umma ƙarama"

Har umma ƙarama ta wuce be dawo daga ɗan guntun tunanin da ya tafi ba.




Beyi niyar shiga part ɗin mama na a yanayin da yake a ciki, amma ganin motar khalid a gidan
yasashi nufar sasan kai tsaye



Mama ce zaune a palon tasha lulluɓi yayi sallama ya shiga

Fuska cike da fara'a mama tace "oyoyo yarona"

Murmushi yayi ya ƙarasa kusa da ita ya zauna, cike da zolaya yace

"Fita zakiyi ne naga kin sha lulluɓi? daga gani ma sabon mayafi ne wannan"



Dariya mama tayi tana kai mishi ranƙwashi, tace "Yaushe ka fara saka wa mutane ido ban sani
ba?"



daidai nan goggo safiya ta fito itama da nata lulluɓin ta samu waje ta zauna

Kallon shi ya maida ga goggo safiya
Be san sanda ya kwashe da dariya ba

Ya hau raba kallon shi a tsakanin su

Be kai ga sake maimaita tambayar shi ma khalid da kamal suka yi sallama duk sun sha
shaddaji suna ta zuma ƙamshi

Kansu a ƙasa suka ƙaraso ciki, fuska a sake goggo safiya ke musu maraba haɗe da nuna musu
waje su zauna



Shigowar su khalid yasa ya faruk gane lulluɓin me suka sha
Yi yayi kamar ze bar palon ya dake ya basar

Ɗaya bayan ɗaya ya miƙa musu hannu suka gaisa, tukun ya koma ya zauna



Cike da girmamawa kai a ƙasa khalid da abokin shi kamal suka gaishe su

Mama dai tunda tace 'lafia lau, ya mutan gidan" bata sake magana ba, haka zalika ya faruk
wayar shi ma ya ciro yaci gaba da danne danne

Goggo safiya ce kawai ke jansu da surutu

Daga gefe kuma Altine tana ta ukin kai kawo tana jera musu abubuwan motsa baki.

Cike da kulawa mama tace "Bisimillan ku fa, ya safiya muje ciki su samu suci"



Da sauri khalid yace "a'a mama mun ƙoshi daga gida muke, zamu koma ne ma yanzu"



Goggo safiya tace "ai ko ɗan lemon kwasha ko?"

Murmushi dukan su sukayi



Ɗan ɗaga murya mama tayi tace "Altine, zoki parckaging musu su tafi da shi"

Hakan kuwa akayi, Altine ta naɗe komi da komi da suka tashi tafiya suka tafi da shi.



Ta ƙofar da Abba ƙ ke shigowa mumtaz tabi ta fita jin sun bar palon

Basu wani jima sosai ba suka ƙara gaba ita kuma ta dawo

A tunanin ta ya faruk ya fita shine ta shigo ta palo

Ido huɗu sukayi da shi

Da sauri ta ɗauke kanta, ko gaishe shi bata yi ba ta shige ciki

Yana ganin shigowar ta ya tashi ya fita

Har mama na faɗin "ka fasa shan kunun ne faruk?"
Yana tafiya yace "Zan sha, anjima zanyi wani aiki a palon Abba ƙ, a saka a flask"



Goggo safiya tace "uban ƴan'iyayi"

Dariya mama tayi tace "ai kuwa yarona bashi da wannan iyayin".




Wajen goma saura na dare ya faruk ya gama tas abinda yake

Farar jallabiya ya saka se gajeren wando a ciki

Laptop da wayoyin shi ya ɗauka tukun ya kulle ɗakin ya wulla keys ɗin cikin aljihun jallabiyar



A kan idon uncle Abbas ya faruk ya fito daga sasan mazan gidan



Ƙara lafewa yayi yaga ina zeyi, dan yau a babban company yaji sanda Abba ƙarami ke waya
yana faɗin wasu mahaukatan daloli da babban companyn ya kawo a iya watan kawai

Shine yake ta bin diddigin yarda za'a fitar dasu ko shigo da su

Ga mamakin shi yaga ya faruk ya shige part ɗin Abba ƙ memakon ya shiga mota ya fita

Kuma a iya sanin shi yasan Abba ƙ ɗin baya cikin gidan

So abin yayi confusing shi ƙwarai

Haka ya gama tsayuwar shi bega shigowar Abba ƙ ba be kuma ga fitowar ya faruk ba

Wayar shi dake ta vibrating tun ɗazu ya ɗaga ya kara a kunne tukun ya juya yayi ciki.



Ya faruk na shiga sasan mama, sama yayi inda a nan suke komi da ya shifi dukiyar Abban

Wani sirrin da ba kowa ne ya sani ba tunda aka gidan gidan shine a sasan Abban akwai gidan
ƙasa a ciki

Daga shi se mama se kuma ya faruk suka san da zaman gidan ƙasan nan
In zaku tuna sanda Abba ƙarami ya fara gini be kawo kowa ba har seda aka kammala komi, so
ba wanda yasan da zaman wannan wajen.



Yana shiga palon ya matsar da ƙatuwar kantar dake manne a jikin bango, inda akayi decorating
palon da ita

To ta bayan kantar ne akwai ƙofar da zata sada ka da gidan ƙasan

Ya shige ya aje kayan hannun shi tukun ya fito ya zauna a palon yana jiran akawo mishi kunun
shi ya sha kafin ya koma ciki



Be jima da zama ba mumtaz ta kawo mishi kunun, tana ajiye wa ta juya da sauri ta fita, ƙaramin
tsaki yaja kafin yaja flask ɗin ya zuba, yana sha yana kallo har ya gama tukun ya sake komawa
gidan ƙasan.




shabiyu ta gota gidan yayi tsit baka jin motsin komi da kowa

Mama na kwance ta rasa me ke mata daɗi sam ga bacci yaƙi zuwa ga kuma rashin daɗin
zuciya

Hijabi ta ɗora akan kayan baccin ta tafito ta nufi palon Abba ƙ

Tana shiga ta juya kantar palon ta shige ƙasa

Ya faruk na tsaka da aiki yaji takun tafiya, duk a tunanin shi Abba ne

Sallamar data yi ne ya kawar mishi da shakku

Kuerar kusa da shi taja ta zauna, bata ce komi ba

Matsar da tarin takardun gaban shi yayi ya maida hankalin shi gare ta
Yace "mama lafia? bakiyi bacci ba?



"Na ƙasa bacci faruk, kawai bana jin daɗin jikina, nasan kuma kana nan kana aiki ga Abban ku
be dawo ba,

Me zan taya ka da shi?"
Da yake ba sirrin lissafin su da bata sani ba, kafin ya faruk yayi wayo ma da ita da Abban suke
abinsu.



Tunda mus'ab yaji muryar mama ya kasa sukuni

Zuciyar shi kawai ke azalzala mishi ya fito yaji ɗumin ta

Daurewa iya daurewa yayi ta, amma sam
ya kasa riƙe kanshi, ji yake kamar ana ingiza shi.



Sosai suka duƙufa da aikin shi da maman, kamar daga sama taji an rungumeta ta baya yana
faɗin "Nayi kewar ki mama!"



Duk da ya faruk ya firgita, amma mama tafi shi shiga mugun ruɗu, tozalin da tayi da mus'ab ba
ƙaramin gigitata yayi ba.



ALLAH KASA ANNABI YA CECE MU 🤲

LAUJE CIKIN NAƊI

NA
ZAINAB FALALU(MRS SULAIMAN)

MARUBUCIYAR



👹
MAKIRCI
KISHI DA ALJANA
WANI HANIN GA ALLAH
ƘADDARAR MU
LAUJE CIKIN NAƊI

WATTPAD@ZAINABFALALU8

Pg47-48

Duk da daurewar da mama ke ƙoƙarin yi na kar ta yi kuka amma hakan ya gagara
Tun da mus'ab ya fara bata kaɗan daga cikin dalilan da yasa ya koma tayuwa a nan

Cikin kuka abinda mama ta fara tambayar shi shine
Mus'ab a ina kake cin abinci to?"

ya faruk najin yambayar da mama tayi wa mus'ab seda tsiga jikin shi ta tashi
A ranshi yake faɗin "uwa daban ce!"



Mus'ab sake shigewa jikin mama yayi sannan yace " da bakwa nan ina cin su biskit da su
goldenmoon, amma kusan kullum dani ake girki a gidan"



Jiki a sanyaye ya faruk yace "bama wannan ba, ya akayi kasan da wajen nan?"

Da sauri mama ta gyaɗa kai, dan itama tana son jin wannan amsar



Kai tsaye yace "a ranar dana fara jin mugun ƙullin da uncle Abbas suke ƙullawa shida waɗanda
ban san ko suwaye ba naji yana maimaita "anya akwai gidan ƙasa kuwa a cikin gidan nan
malam"

Tunda naji haka na fara dube-dube, dan nima ina mamakin wani lokacin da na san Abba na
cikin gidan nan, amma lokaci ɗaya inga ban ganshi ba yasa na yarda da hakan
kuma na taɓa jin sanda Abba ke waya da ya faruk akan ya same shi a gidan ƙasa"

Daga maman har ya faruk ɗi
da rayuwar ki data Abbanmu dakuma Ahmad da mumtaz
bbas ya kamani ina mishi laɓe shine y
Na firgita sosai da naji abinda yn kafe shi da ido sukayi suna sauraren shi



Ya ɗora da "A ranar da uncle Aace min, ya bani kwana ɗaya in ɓace a idon shi, inba haka ba ze
salwantar ace, kuma mama bazan ɓoye miki ba, in har na kusance ki ko Abba ina jin wani
mugun ƙunci da tsananin baƙin ciki a cikin zuciya ta
wani lokacin inajin zuciyata na tunzura ni nazo na shaƙeku ko kuma in burma muku wuƙa

Tsoron kar hakan ta kasance yasa nayi niyar nesanta kaina da ku
Amma ina tunanin kar yazo ya aiwatar da abinda yace alhalin ku baku san da wace irin zuciya
yake zaune daku ba



Shine na rubuta wasiƙa na ba mumtaz ta baki, dalilina na yin haka shine uncle Abbas da ma
wanda duk suke aiwatar da mugun nufin su zasuji na bar gidan

Amma a baɗini shine ina nan gidan ƙasan."



Karkaɗa kai ya faruk yayi yana mamakin hakan, can yace "a ina ka samu keys to?"

murmushi Mus'ab yayi kafin yace "inda kake aje spare keys a nan na ɗauka"



Sosai mama ke kuka, ko bakomai wani nauyi da ƙirjinta yayi mata tun lokacin data ga wasiƙar
nan taji yana sauka a hankali, nutsuwa na ratsata

Kuma ko da wasa batayi mamakin jin sunan uncle Abbas a masu neman ganin bayan su ba

Tsoronta ɗaya shine bata san suwaye sauran muƙarraban shi ba.



Murya a dishe mama tace "faruk ya kake gani zamuyi wajen sanar da Abba ƙ, ko ba komai yayi
taka tsantsan da shi"




Murmushi ya faruk yayi, sannan yace " bazamu gaya mishi ba mama, shari'a saɓanin hankali
ce, zuba ido kawai zamuyi akan komi, sannan kar mu bari ko Abba ƙ yasan da zaman mus'ab a
nan, in da hali ma shiryawa zeyi ya tafi can china ya wakilci Abban kamar yarda nace musu
yana can dama gudun magana"



kan mus'ab a ƙasa yace "Bazanje ba gaskiya ya faruk, wallahi ko kun saka ni na tafi nasan
bazan iya aiwatar da komi ba
Ni kaɗai nasan abinda nake ji a raina"



Dafe ƙirji mama tayi tana kallon su kafin tace "kodai akwai sihiri a lamarin nan ni zahra'u"?



Dan dai kawai ya faruk ya kwantar mata da hankali yace "haba dai, ba wani sihiri mama"

Amma deep down him yasan baza'a rasa sihirin ba,

Yana cikin wannan tunanin mumtaz ta faɗo mishi a rai, haka nan yaji mummunar faɗuwar gaban
da har seda ya dafe zuciyar shi,
Yace "In sha Allah nata ma sihirin ne"

Mama da mus'ab suka kalle shi jin me yace

Ganin kallon tambayar da mama ke masa yasa ya gane a bayyane yayi maganar ba'a zuci ba

Ganin sunji yasa ya waske yace "ina nufin mu dage da addu'a, sannan zuwa da safe zanje
wajen Alaramma Baffa ya bamu ayoyin karya sihiri mu gwada mu gani"



Cikin kuka mama tace "bani da bakin gode maka faruk, Allah yayi maka albarka ya baka mace
tagari warda zata zauna dakai da zuciya ɗaya"



Lumshe ido yayi ya buɗe sannan yace "amin" a kan laɓɓan shi.



Yanzu kullum mama da kanta take fakaitan ido ta kaimishi, ba dan kowa ba se dan itama ta
saka ayar tambaya akan Altine

Bata da tabbas dan zargi take, shiyasa ma ta kore ta ba, ta dai ci gaba da saka mata idanu.



A ɗan tsukinne uncle Abbas ya tsiri tafiya duk da shirye2n biki da aka fara gadan-gadan,

duk iya bin diddigi su sun kasa kama koda hujja ɗaya a tattare da shi

Haka dai suka watsar da magana amma dai ba su rufe idanun su ba.




BAYAN SATI ƊAYA

Ya faruk ya shigo gidan kenan ya hango tawowar mumtaz ita da Amal

Jira yayi har suka ƙaraso, gaishe shi sukayi har sun gota shi yace
"mumtaz kizo ki same ni in kun dawo"

Seda ta zumɓura baki kafin tace "to"

Duk da ya gani besa ya tanka mata ba, dan yaga kamar da bikin nan ya sake ƙaratowa wani
rawar kai ta ƙara, ƙwata kawai yayi ya wuce.
Koda su ka dawo ƙin zuwa tayi, har seda ya ɗaga waya ya kira mama yace ta turo mishi ita



Shima seda tagama nuƙu-nuƙun ta tukun taje

Kallon ta yayi yace "Ki kiyayi ranar da zan miki fyaɗin ƴan kaɗanya wallahi, saboda kin raina
mutane shiyasa kike abinda kk ga dama ko?"

Bata ce komi ba, ta dai tsaya a saitin ƙofa, inta baci tayi waje.



Ƴar ƙaramar farar roba ya miƙa mata,

Karɓa tayi tana jujjuyata,

Ko kallon ta beyi ba yace "gashi nan, kishi kafin ki kwanta, da safe ma kisha, sannan da daddre
ki sha, sha uku zaki mishi"

Ɗan kallon shi tayi tukun tace "to shi wannan ɗin mene?"

Balla mata harara yayi kafin yace "maganin mutuwa ne"

Ta san sarai baƙar magana yayi mata,

Juyawa tayi da niyar tafiya taji ya ce "In kin sha domin kanki ne, dan ina jiye maki tsoron ranar
da wancan wawan ze gane kina ɗauke-ɗauke, duk da dai bani da tabbacin baki taɓa yi mishi
ba"



Acikin zuciyar ta taji dirar kalaman ya faruk, duk da gaskiya ya faɗa amma se taji tayi mugun
muzanta, da kuma ta tuna agogon khalid data ɗauka taji gaba ɗaya wani tsoro da farga sun
lulluɓe ta

Ganin ta tsaya tayi shiru ya faruk yace "fita kija min ƙofa ta malama"

Seda ta harari gefe tukun taja ta fita rai a ɓace.



Tana fita ya sauke ajiyar zuciya, a bayyane yace "Allah ka bata ikon sha".
Mumtaz na shiga ɗaki ta aje robar akan mudubi taci gaba da harkokin gaban ta.



Tunda bikin ya rage saura sati huɗu, kusa ko wani sasa basa zaune, aunty ce kawai take free,
kuma ta ɗan fi shiri da mama akan sauran matan gidan



Gaba ɗaya angwayen sun haɗe waje ɗaya sun san juna

Wanda hafsa zata aura ya kawo shawarar su haɗe duka events ɗin waje ɗaya
Yarda baza'a haɗa ma family gajiya ba

Duk da hafsat taaso ta kawo gardama, amma ganin an rinjayeta yasa ta haƙura shima ba da
son ranta ba

Haka akayi ta shirye-shirye, wanda kaf komi da komi na amaren a hannu Abba ƙarami yake, ya
ɗora ya faruk a kan komi da ya dace ayi



WATA RANA DA DADDARE BAYAN ISHA

Umma babba ta kira ya faruk yazo ya same ta a ɗaki

Yana zuwa ya iske ƙannen shi duk sunzo, duk akan maganar bikin

Zama yayi bayan ya gama amsa gaisuwar su, harda haɗawa da ƴar tsokanar shi "mata sarakan
son biki".



Ba yabo ba fallasa mama ta kalle shi tace "Faruk banji kace min komi ba game da hidimar nan"



Cike da kulawa yace "kamar me umma?"



"Kamar ka ɗebo kuɗi masu kauri ka bani tunda ragamar komi a hannun ka take"



Shiru yayi, yama rasa

Please Login or Register in order to submit comment