Reading LAUJE CIKIN NAƊI by ZAINAB FALALU Chapter 1 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Downloaded From https://tknovels.com.ng LAUJE CIKIN NAƊI.

NA



ZAINAB FALALU
(MRS SULAIMAN)

MARUBUCIYAR

MAKIRCI
KISHI DA ALJANA
WANI HANIN GA ALLAH
ƘADDARAR MU

Page 1

Cikin sanɗa ta tura ƙofar ɗakin, ganin ƙofar ta buɗe yasa ta sauke ajiyar zuciya me nauyi



Seda ta waiwaiga taga ba motsin kowa tukun ta saka kanta kai tsaye cikin ɗakin



Seda ta gama ƙare ma ɗakin kallo ta lumshe ido tana shaƙar mayen ƙamshin turaren da ko a
bacci taji shi ta san na waye, tukun ta ƙarasa inda taga agogunan shi a jere



Tas ta gama ƙare musu kallo,
seda ta darje tukun ta ɗauki wanda suka fi ko wanne tsada a ciki, ta ɗaga rigar ta saƙa ta ɓoye
su



Motsin data ji ne ya sa bata kai ga taɓa sauran abubuwan ba ta fice da sauri



Tana fitowa daga ɗakin ta hango shigowar shi gidan

Da sassarfa ta kwasa tayi hanyar part ɗin su tana tallafe da agogunan data ɗakko tana jin yarda
gaban ta ke dukan uku-uku a duk sanda tayi dafe




La haula wala ƙuwata illa billah! yanzu inda ban ankare dake ba da shikenan kin min illa kin sa
na yanke,
ki sabauta ni haka kurum mumtaz



Mumtaz da ake maganar domin ta tuni ta ƙule can cikin bedroom dan ko waiwayowa bata yi ba,
ballanta na tasan me tayi



Tana shiga ta banko ƙofar da ƙarfi sannan ta murɗa key



Ta window taci gaba da leƙen ya Faruƙ dake tafe hankalin shin na ga wayar da yake,

Kamar walƙiya yaga giftawar mutum da gudu amma hankalin shi be kai ga kowaye ba, waya ce
me muhimmanci yake amsawa shiyasa be wani damu da ya san waye ɗin ba.




Seda taga shigewar sa tukun ta sauke ajiyar zuciya tana komawa da baya ta zauna




Ɗaga rigarta tayi ta ciro agogon, ƙare mishi kallo tayi sosai sannan tace



"Daga gani zasuyi mugun tsada, Komi na ya Faruq me kyau ne wallahi,



Jakar islamiyar ta tajanyo ta saka agogon tukun ta rufe ta maida sannan ta fito palon inda
mama take




Zama kusa da Mama tayi ta zabga tagumi ta kafe ta da ido



Maman tana kallon ta tayi fuska kamar bata san da zaman ta a wajen ba taci gaba da yanke
farcen ta tana magana da atine dake kitchen tana haɗa kayan shan ruwa, da yake yamma ta
gabato ana gab da a kira sallar magriba.




Murya a sanyaye Mumtaz tace
"mama yau ba aikin da zan yi ne ni?"



ko kallon ta bata yi ba ballanta na ta saka ran amsa mata

Ganin ba amsa mata maman zatayi ba yasa ta miƙe jiki a sanyaye ta koma ɗaki tayi kwanciyar
ta dama ba ƙaramin jin azumin yau take ba,
ko gudun data yi ɗazu shima dan ya zama dole ne dan in har ta kuskura ta shiga hannun yaya
faruƘ to tabbas se dai buzun ta dan tsaf se ya sauke mata waɗan nan yatsun nashi kamar itace
bama biyar ɗin ba goman duka ze sauke mata



Juyi tayi ta gyara kwanciyar ta, tayi shiru tana tunanin wannan muguwar halayyar ta
ɗauke-ɗauke datake yi

kan kice me hawaye suka cika idanun ta kamar zasu zubo,

Da iyakacin ƙarfin ta tahanasu sauka ta maye gurbin su da murmushi, cikin zazzaƙar muryar ta
me daɗin sauraro tace



"Komi yana da lokaci, Allah ka yaye min wannan ɗauke-ɗauken da nake yi na ba gaira ba dalili'



kiran sallar magriba ne ya fito da ita palon inda aka jera komi da komi na buɗa baki

Dabino uku ta ɗauka ta taci tukun ta wuce toilet ɗin palon ta ɗauro alwala



Seda ta gabatar da sallar magrib kafin ta ƙaraso ta zauna kamar yarda kowa da kowa ke zaune
ana shan ruwa.



Sama-sama ta tsakuri abincin, ita she ƙarshe zama kuma itace ta fara tashi



Ba wanda ya kula ta, kusan haka ɗabi'ar ta take, bata fiya son cin abinci ba, tafi auki a kayan
ƙwalama, shiyasa gata nan bata da wani auki na azo a gani.




Gaba ɗaya gidan suka hallara a babbar harabar gidan inda anan yaya faruƙ yake jan su sallar
asham in har yana gari



Manyan su da yaran su, kowa na wajen amma banda mumtaz, sakina ce dake zaune kusa da
mama kawai ta lura da rashin ta a wajen,

A hankali tace

"Mumtaz bata fito ba mama"

Kafin maman ta buɗe baki suka ga tawowar ta da sauri

Bawanda mumtaz ta kalla ta samu gefe ta shimfiɗa dardumar ta tabi sahu



Tunda suka ɗago daga sujjada ta ƙella ido akan carbin dake aje a gaban umma babba ta rasa
sukunin ta gaba ɗaya,

Salla ake amma ita tunanin gaba ɗaya ya tafi ta inda zata ɗauke carbin

Har aka sake komawa sujjada mumtaz bata ankare ba



Can ƙasan zuciyar ta tace

"bari a tafi sujjadar ƙarshe, ai nasan ya faruƙ jimawa yake, har in ɗauke shi ma ba lale ne a
ɗago ba"



Haka tayi ta fakon wannan carbi har aka kai sujjadar ƙarshe



Cikin sanɗa ta janye jikin ta, ta matsa kusa da umma babba, cikin ƙwarewa a harkar ta saka
yatsar ta ƴar manuniya ta janyo carbin, seda taji shi gaba ɗaya a hannun ta tukun ta juya a
hankali bayan ta cusa shi a cikin rigarta tkun ta koma kan dardumar ta tayi sujjada kamar yarda
taga kan kowa a ƙasa.




Sosai Umma babba tayi mamakin rashin ganin carbin ta, har Aunty dake gefen ta take
tambayar ta da "lafia umma babba?"
Da mamaki tace

"na rasa ina na wurga carbi na wlh, abun mamakin da shi na fito ba"



Kyaɓe baki aunty tayi, bata sake cewa komi ba taci gaba da tasbihin ta tana ɗan dudduba
wayar hannun ta sama-sama



Itama umma babban shiru tayi, taci gaba da mamakin ta ita kaɗai a cikin ranta




Ɗaya bayan ɗaya ahalin gidan suka rinƙa watsewa kowa na kama gaban shi, kowa ya kama
hanyar part ɗin su



Ya faruƙ na zaune be kai ga tashi ba, mumtaz na ɗago kai taga ya rage daga ita se ya faruƙ se
kuma ya Tk dake waya tayi saurin miƙewa da sauri zata bar wajen

Tsautsayi wannan carbin na umma babba data ɗauka ya faɗo

Caraf akan idon ya faruƙ da ya kafe ta da kallon tuhuma yana kallon carbin yana kuma kallon ta
at thesame time




Wuri-wuri mumtaz tayi da idon ta tana kallon shi, gaba ɗaya rashin gaskiya ya bayyana a tattare
da ita



A hankali ta saka hannun ta ɗauke carbin sannan ta kwasa da gudu tayi hanyar part ɗin su,
tana yi tana waiwayen shi ganin har lokacin be ɗauke idon shi a kanta ba.



Seda ta ƙule ma ganin shi tukun ya kauda kan shi yana mamakin rashin nutsuwa sam na
mumtaz kusan so biyu kenan yana kama ta da makamancin abubuwa shigen wannan



Ƙwata ya ja tukun yace

"zan saka miki ido kuwa"
Tashi ya faruƙ yayi ya wuce ɗakin shi waya kare a kunnen shi yana sauraron saƙon da Abba
babba ke bashi akan rabon kayan masarufi da za'ayi ma bayin Allah saboda alfarmar watan
ramadana da ake ciki.



Mumtaz na shiga part ɗin su ta wuce palon mama,

Tana shiga ta iske yayun ta da suke uwa ɗaya uba ɗaya zaune a palon suna fira mama na daga
gefe tana duba list ɗin sunayen ƴan'uwa da abokan arziƙi masu ƙaramin ƙarfi tana fidda list ɗin
wanda ya kamata ayi ma kayan salah



Ɗago kai mama tayi ta kalli mumtaz da alamun rashin gaskiya ya bayyana a gare ta

Cike da kulawa mama tace



"zo nan mumtaz"



A tsorace tace

"ina zuwa mama, futsari nake ji" ta yi hanyar ɗakin su da sauri tana ƙara damtse carbin hannun
ta.



Seda ta adana shi tukun ta fito ta zauna kusa da mama tace "gani"



Kafe ta da kallo mama tayi tace

"Anya akwai alamun gaskiya kuwa a tattare dake mumtaz, ƴan watannin nan sam na kasa gane
ki, kwata-kwata baki da nutsuwa kullum in aka ganki a zabure kike, kodai basir ɗinki ya tashi ne
mumtaz?"



Shiru mumtaz tayi tana kallon, ya Ahmad da yake dariyar basir da mama tace



Jiki a sanyaye ta girgiza kanta, sannn tace

"be tashi ba mama"
Sosai mama ta hauta da nasihar ita ƴa mace da nutsuwa aka santa, ba wai komi ta rinƙa yin shi
a hauka-hauka ba



Abinda mama bata sani ba shine duk maganar nan data ke ma mumtaz yana shiga ta kunnen
dama ne ta fice ta kunnen hagu, hankalin ta gaba ɗaya na kan ɗayar wayar ya Ahmad da ya aje
a hannun kujera



Lissafin ta kawai yarda zata ɗauki wayar ba tare da an samu matsala ba,



Ganin yarda mumtaz tayi shiru kamar tana sauraron abunda maman ke cewa yasa mama taci
gaba da kawo mata misalai da sauran ƴammatan gidan da suke sa'annin ta

Nuna mata take saboda tsabar rashin nutsuwar ta yasa ko saurayi yazo wajen ta baya sati uku
ze kama gaban shi, tun suna zuwa har sun dena zuwa




Murmushin ta me kyau mumtaz tayi, kallon mama tayi tace



"Saboda haka kenan suka dena zuwa waje na mama?"



Sosai mama ta buɗe ido akan ta, sannan tace



"ai duk ɗa namiji yana sonbya samu mace nutsatstsiya me nutsuwa sosai, amma a yarda kike
yin abubuwa haka ai dole saurayi ya gudu"




Murmushi mumtaz tayi, bata sake cewa komi ba, sema kishingiɗa data yi tana jiran sa'ar ya
Ahmad akan wayar data ƙwallafa rai akan ta.



KAMAR YARDA NACE, IN SHA ALLAH NAN KUSA ZAN FARA SAKIN SHI,

SABODA MASU TAMBAYA NA DAN ALLAH IN ƊAN GUTSIRA MUSU KAƊAN DAGA CIKIN
LABARIN, TO GASHI NAN, INA MUKU FATAN ALKAIRI



ALLAH KASA ANNABI YA CECE MU 🤲
LAUJE CIKIN NAƊI

NA
ZAINAB FALALU
(MRS SULAIMAN)

WATTPAD@ZAINABFALALU8

Pg2

Tana a nan zaune jiran tsammani bacci yayi awon gaba da ita, har su ya Ahmad suka tashi bata
sani ba



Wajajen goma mama ta tashe ta tawuce ɗaki

Da wannan wayar ta farka, tunda ta buɗe ido taga wayam sun tashi ranta ya ɗugunzuma ya
ɓaci

Haka tayi ta zumɓure-zumɓurenta ta haƙura ta shige ɗaki.



WASHE GARI

Ƙarfe takwas da rabi na safiya ƴammatan gidan suka fito kusan a tare

Dukkan su sanye suke da blue dogayen hijabai



Su shida ne kyawawa da su ma sha Allah



Parcking lot suka wuce inda bala driver ke jiran su

Kowa ya shiga mota banda najwa data waiga ba ta ga mumtaz ba

Da sauri tace
"Ina zuwa mlm bala, bari in taso kira mumtaz

Bata jira cewar su ba ta juya da sauri har ta na haɗawa da ɗan gudu-gudu

knocking ƙofar part ɗin su mumtaz da basu buɗe ba tayi cikin nutsuwa



Cikin bacci Altine me aiki taji knocking ɗin, da sauri ta taso ta zo ta buɗe ƙofar



A ladabce najwa ta gaishe da altine tukun ta shige ciki

Direct ɗakin mumtaz ta wuce tana kiran sunan ta



Mumtaz na tsaye gaban mirrow tana saka nata hijabin najwa ta shigo



Ganin ta a tsaye yasa ta tsaya itama, tace

"nasha baki tashi ba ai"



Fuska a sake mumtaz tace

"Tun asuba ban koma ba, sam na kasa komawa se yanzu da lokacin islamiya yayi nake jin
baccin wallahi"



Dariya najwa tayi tace

"na saba jin wannan zancen naki malama, koya ya shiga mota fa, muje"



Tana gama faɗin haka ta juya ta fice



Jakar islamiyar ta dake ajiye gefe ta ɗauka, seda ta buɗe jakar ta ga ajiyar ta na nan tukun ta
rufe ta sagala sannan ta janyo ƙofar



Ɗakin mama ta leƙa taga bata tashi ba ta wuce bayan ta sallami altine
Mumtaz tasan sarai jiran ta suke, tunda ta fito suka haɗa ido da hafsa taga yarda ta banko mata
harara yasa ta koma tafiya ɗai ɗai kamar bazata taka ba, ba dan komi ba se dan ta sake ƙular
da hafsa



Daga ƙofar part ɗin su zuwa wajen parcking lot ɗin seda tayi mugun ɓata musu lokaci kafin ta
ƙarasa,

Da ka gani kasan da gangan take, tsabar neman magana ne



Abunda bata sani ba shine, tunda ta fito ta fara tafiyar ta ya faruƙ ke kallon ta da mamaki a
fuskar shi, sarai zaka ga zallar neman fitina da neman saka su suyi latti a fuskar ta



Kasa cewa komi yayi yana jiran ganin gudun ruwan mumtaz ɗin har ta ƙarasa wajen motar inda
suke jiranta



Daga can ya hango yarda take murguɗa ƙaramin bakin ta, da dukkan alamu rashin kunya take
ma hafsa dan tana gaba da ita a shekaru



Seda ta gama murguɗe-murguɗen ta tukun ta buɗe baya kusa da najwa ta zauna, tukun bala
driver yaja suka tafi.



Seda ya faruƙ yaga fitar su tukun ya maida idon shi kan systerm ɗin shi dake ajiye akan stool
ɗin gaban shi yana shigar da wasu bayanai.




Suna shiga aji mumtaz ta kalli najwa dake ƙoƙarin zama a gaba tace



"hour ɗaya kafin a tashi ki tashe ni dan Allah"



Balla mata harara najwa tayi kafin tace

"wai da gaske baccin zaki yi yau ma?"
Seda mumtaz ta rama hararar da najwa tayi mata, kanta tsaye tace

"kina da damuwa ne a ciki?"



Banza najwa tayi da ita, dan ta san ba ƙaramin aikin mumtaz bane tasa su raba hali



Ganin najwa ta juya yasa mumtaz sake maimaita mata tafa tashe ta kafin a tashi, tukun ta juya
ta koma can baya ta zauana.



Tun kafin a fara tafsir bacci me nauyi yayi awon gaba da ita, ba itace ta farka ba har seda aka
tashi sannan najwa ta tashe ta suka fito



Tunda suka fito mumtaz ke mata ƙorafin taƙi tashin ta



Da dai najwa ta gaji da ƙorafin mumtaz tace



"inda na tashe ki ina zaki je to?"



Tsaki mumtaz taja, tukun tayi gaba inda anan bala driver ke ɗaukan su ta barta a nan



Sosai mumtaz ta haɗe rai har suka kai gida, bata ce ma kowa uffan ba ta wuce part ɗin su duk
ba haka ranta yaso ba.




Bilkisu da hafsa na ganin wucewar mumtaz har wani rige rigen tambayar najwa suke da "me
akayi ma warcan mara kunyar ne?"



Murmushi kawai najwa tayi, bata basu amasa ba, itama ta ɗauki jakar ta tayi nasu part ɗin.
Sosai rana ta take, kusan kowa na side ɗin shi yana bacci, dan azumin yau yana ƙwala jama'a



Tunda mumtaz ta shiga part ɗin su ta tabbatar da kowa bacci yake bata yi ƙasa a gwiwa ba ta yi
maza ta cire hijabin uniform ɗin ta tasauya wani,

Jakar makarantar ta buɗe ta ɗauki wannan agogunan da ta ɗakko a ɗakin ya faruƙ ta saka a
hand bag ɗin ta, se ƙaramar wayar ta nokia data saka a ciki, sam bata lura ba ko sisi a ciki ba,
haka ta fice sauri-sauri tayi waje, ko ta kan mama dake bacci bata bi ba tayi waje tana waiwaye
kamar warce za'a ce ma tak ta kwasa da gudu.




Dai dai ya faruƙ ze tashi daga wajen da yake zaune yaga fitowar Mumtaz da sauri, tana yi tana
waige, rashin gaskiya ƙuru-ƙuru a tattare da ita



Shiru yayi yana kallon ta har ta fice ta ƙaramar ƙofar gate ɗin gidan,
Cikin ɗaga murya malam ado yace

"Sauka lafiya zankaɗaziya"

Haka ya ke kiran Mumtaz tun tana ƙarama



Cuno baki mumtaz tayi ta ƙarashe ficewa da sauri, dan kar tsautsayi yasa wani a gidan ya
ganta.




Ya faruƙ har ya juya ciki, amma zuciyar shi sam ta kasa nutsuwa, a rayuwar shi be cika shiga
abinda ba ruwan shi ba, amma sam ya kasa nutsuwa da yarda yaga fitar mumtaz.



Haka ya danne ya buɗe ƙofar ɗakin shi ya shige,
Amma me?, kwata kwata ya kasa samun nutsuwar rai



ganin ya kasa nutsuwa yasa ya juya ya fice da sauri yayi hanyar fita shima



Wayam layin, ba alamun mutum ko ɗaya a layin, yanayin layin dama bana jama'a bane, da
wahala kaga mutum tafe a ƙafa
Haka ya gama wurwurga manyan idanun shi da suka zama na gado ya haƙura ya juya cikin
gidan da niyar shima ya ɗan kishin giɗa zuwa yamma, lokacin ranar ta ɗan yi sanyi.



Seda ya watsa ruwa tukun ya kwanta, amma sam ya kasa baccin da yayi niyar yi, al'amarin
mumtaz na daɗa ɗaure mishi kai, shi ya san kaf yaran gidan nan babu warce ta kai nutsuwar
ta, amma wannan dawowar da yayi yaga saɓanin haka daga gare ta



Can daga ƙasan zuciyar shi tace

"Ka sani ko dama lumbu lumbu take, dan ba'a shedar mutum"



A sanyaye ya faruƙ yace

"Haka ne, amma ya zama dole in saka mata ido, ba mamaki mugayen abokai tayi"

Da wannan tunane tunane bacci yayi awon gaba da shi.



ALLAH KASA ANNABI YA CECE MU 🤲
LAUJE CIKIN NAƊI

NA
ZAINAB FALALU(MRS SULAIMAN)

WATTPAD@ZAINABFALALU8

Pg3

Babbar kasuwar seye da sayarwa na diamond da gold na garin mumtaz ta nufa kai tsaye



Seda suka isa tukun ta tuna da bata da ko sisin da zata ba me keken data ɗakko



Nan fa ido ya raina fata,
Me kekenapep ya kafe ya tsare, kai da fata besan wani zance ba in ba na kuɗin shi ba
Mumtaz na tsaye ƙwale da idanu kamar zata fasa ihu akan tereren da me keken ke mata



Murya ƙasa-ƙasa tace

"Da Allah fa nake haɗa ka bawan Allah, wallahi ban san ba ko sisi a cikin jakar ba"



Cike da hargowa ya yunƙuro kamar ze make ta, da sauri ta ja da baya tana ƙara danƙe jakar ta
tamau



A fusace yace

"Wallahi tallahi in baki bani haƙƙi na ba se ba miki tsinannan duka a wajen nan, se in ga uban
da ya tsaya miki"



Fuska a ɗaure Mumtaz ta ɗaga mishi hannu tace

"ah, dakata mlm, zagin ya tsaya kaina kar ya kai can, inda yanzu zaka ga waɗan da suka tsaya
min da bakin ka ba ze ƙara furta ko da kalma ɗaya a wajen nan ba, kawai ka nutsu muyi sulhu
tunda ni na kawo kaina"



Ta ƙarashe maganar tana jujjuya manya idanun ta na gado.




Da zafin nama me keken ya sakko yayo kan Mumtaz da ke tsaye



Ƙiris ya hana ya sauke mata yatsun shi biyar a kumatun ta Allah ya kawo wani matashin saurayi
da tunda suka fara dramar kuɗin yake kallon su




Da sauri saurayin ya riƙe hannun me keken, fuska a sake yace



"Haba kai kuwa, ya zaka daki mace kamar ba na miji ba?"
A fusace ɗan keken ya ƙwace hannun shi, cike da kumfar baki yace



"Banda tsabar wulaƙanci ɗakko yarinyar nan nayi, duk da zafin ranar nan da kuma ƙishirwa be
sa na kwanta ba, na fito neman halali na amma dan ta raina min hankali se da na kawo ta zata
ce min bata san babu kuɗi a jakar ta ba"



Nunata yayi sannan yaci gaba

"To wallahi ko waye ya tsaya mata yau ɗin nan se ta bani haƙƙi na, ko kuma na daki kuɗi na"




Cikin nutsuwa saurayin ya waiga inda mumtaz ke tsaye tana wani karkaɗa jiki,

Murmushi yayi, sannan ya waiga yace wa me keken

"To nawa ne kuɗin naka?"



Baki a bushe yace

"Ɗari biyar ne".



A aljihun rigar shi ya saka hannu ya ciro sabuwar dubu ɗaya ya miƙa mishi



warce dubun yayi ya juya ya shiga keken shi yana mita



Da sauri Mumtaz tace

"Ɗari biyar ce haƙƙin ka malam, se ka kawo canjin na samu na komawa gida"




Duk yarda me keken nan ke ɗaurewa seda maganar Mumtaz ta bashi dariya
Shi kuma saurayin na gefe yayi folding hannuwan shi a ƙirji yana kallon Mumtaz cike da
mamaki da kuma ban dariya




Mumtaz kam har ga Allah da zuciya ɗaya tayu maganar,

Daga bayan su suka tsinkayi muryar saurayin yace



"Ki barshi ya tafi, ke se in maida ki gida a mota ta" yayi maganar yana nuna inda yayi parcking
motar shi da hannu.




Ko tsayawa me keken ya ƙarasa jin zancen beyi ba yayi gaba abun shi.




Seda ya ɓace ma ganin mumtaz tukun ta waigo da fuskar ta inda saurayin ke tsaye yana kallon
ta tun daga sama har ƙasa



Tana juyowa idanun ta suka sauka a cikin nashi,
Da sauri ta sauke kanta ƙasa tana wasa da hannun jakar ta dake cikin hijabi



Murmushi ya sakar mata,
Cike da ƙwarewa a magana yace



"im khalid, and u?"



Kanta a ƙasa kamar ba zata ce komi ba,

Har ya fitar da ran jin wani abu daga gare ta, can dai tace

"MUMTAZ"



can ƙasan numfashin shi ya maimaita "mumtaz"
Murmushi sosai ya sakar mata a wannan karon, sannan yace

"unique name"



murmushi itama tayi sannan tace "nagode".



Tana gama faɗin nagoden tayi gaba



Da sauri khalid ya bita a baya yace



"Ah ya zaki tafi kuma ki barni bayan bamu gama magana ba?"

Be jira cewar ta ba ya sake cewa

"ina ma zaki je tukunna?"



Yana mata wannan tambayar ta tsaya cak gaban na dukan uku-uku, sarai zaka ga hakan ga
fuskar ta



Kafe ta da kallon ƙurilla yayi yana jiran jin me zata ce



Ganin bata da niyar cewa komi yasa yace



"tunda ba zaki faɗa min ba, muje to na rakaki"



Da sauri Mumtaz tace



"na fasa, gida zan koma"



Shiru khalid ya sake yi yana kallon ta
Can yace

"Muje na sauke ki to"



Da sauri ta girgiza kanta tana yin gaba da sauri



Haka khalid yayi ta binta yana roƙonta akan ta tsaya ya sauke ta amma firr mumtaz ta ƙi yarda



Badan yaso ba ya sake tsaida mata ɗan keke



Yana ji yana gani ta tafi, ko arzikin number wayar ta be samu ba.




****Duk a tunanin mama mumtaz sun dawo tana ɗakin su,



Yau da yake a general kitchen za'ayi abincin buɗa baki yasa tun da akayi sallar azzahar matan
gidan suka hallara a babban kitchen ɗin dake ta can ƙarshen makeken gidan dake ɗauke da
ahalin gaba ɗaya



ko wacce mace da ƴan aikin ta, se ɗaiɗai ku na daga cikin ƴaƴan gidan da suke ɗan taɓa wani
abun a wajen.




Cike da haɗin kai suke aiyukan su,

Yawanci duka matan suna zazzaune akan kujeru suna basu order abubuwan da za'ayi



Sun jima suna aikace-aikacen su suna taɓa fira sama-sama

Ganin duka yaran gidan sun fito waje, mama ta kalla taga mumtaz ce kawai babu

Atine ta ƙwala ma kira daga can in da suke
Da sauri atine ta tawo tana amsawa



Kallon ta mama tayi tace

"Je ki taso min mumtaz, bacci ya isa haka"



Da "to" atine ta amasa tukun ta wuce part ɗin maman kai tsaye



Mumtaz na cire hijabi atine tayi sallama a ɗakin



Da sauri mumtaz ta waiga tana kallon ta,

Seda ta sauke ajiyar zuciya, duk a tunanin ta mama ce, tukun tace



"ya akayi ne?"



Atine tace

"mama na kira" ta juya ta fita.




Seda Mumtaz ta adana waɗan nan agogunan sannan ta gabatar da salla tukun ta fito zuwa
kiran maman.



A hanya kafin ta ƙarasa kitchen ɗin suka yi kiciɓus da yaya faruƙ da ya kafe ta da kallo tun
fitowar ta daga part ɗin su



Ita sam bata lura da shi ba seda ta kawo daf da shi



Fuska a ɗaure bayan ta kawar da kai gefe tace a taƙaice
"ina wuni"



Be bi ta kan gaisuwar ta ba yace



"After asham kizo ki same ni a ɗaki"



Ko kallon ta be kuma yi ba ya wuce abun shi.



Jin kalmar ta same shi a ɗaki ba ƙaramin ɗaga mata hankali yayi ba, sosai tsoro da fargaba
suka kamata



Murya ƙasa-ƙasa tace

"ko dai ya duba bega agogunan shi bane ni mumtaz"?



Ta jima tsaye a wajen tana saƙa da warwara, can dai ta yanke hukuncin ƙin zuwa kamar yarda
ya umarce ta.



Ƙarasawa tayi inda su mama suke a ka ci gaba da aikin da ita.




Wajen biyar da rabi na yamma suka kammala, su Mumtaz, Najwa, Bilkisu da Hafsat ke ta
kwasan manyan kulolin suna kaiwa kan babban dinnig ɗin gidan suna jejjerawa,

inda lokaci zuwa lokaci ake haɗuwa duka iyalan aci abinci



Seda suka gama tas, tukun kowa ya koma part ɗin shi domin yin wanka kafin kiran sallah.



SHARE PLS.

ALLAH KASA ANNABI YA CECE MU 🤲
LAUJE CIKIN NAƊI
NA
ZAINAB FALALU(MRS SULAIMAN)

MARUBUCIYAR



👹
MAKIRCI
KISHI DA ALJANA
WANI HANIN GA ALLAH
ƘADDARAR MU
LAUJE CIKIN NAƊI

WATTPAD@ZAINABFALALU8

p4

Ahalin gidan gaba ɗaya kowa da kowa ya hallara a babban ɗakin cin abincin da yake
musamman sabida lokuta irin haka dama



Cikin nutsuwa kowa ke cin abinci, baka jin motsin komi sai cokula, se kuma waya da wasu daga
cikin ƴan mazan dake amsawa lokaci zuwa lokaci.




Ba wani abincin kirki Mumtaz taci ba,

Ƙaramin bowl ta ɗauka ta zuba pepper soup ɗin cat fish ɗan madedeci ta fakaici idanun kowa
tukun ta fece zuwa part ɗin su, duk dan gudun kar su ƙara arangama da ya faruƙ

Bata san yana lura da duk wani motsin ta ba, duk da a zahiri zaka ce besan da wanzuwar ta ba
a wajen, amma kar yake kallon ta.



Tana fitowa ta sauke ajiyar zuciya, a bayyane tace



"Na sha a wannan karon, sallar ma a ɗaki zanyi ta tunda ba'ace dolen dolen mutum se yayi ta a
cikin jam'i ba"

Ta ƙarashe maganar haɗe da murguɗa baki.
Ɗan karkatawa Abba ƙarami yayi saitin kunnen mama yace



"Wani abun kika daka Mumtaz halan?"



Saitin ƙofa mama ta kalla sannan tace



"Ba abunda na saka ta, ƙila ta ƙoshi ne, kasan bata fiya zama taci abinci kamar yarda kowa keyi
ba"



Abba ƙarami ba sake cewa komi ba, sema ɗan yatsina fuska da yayi yana streaching wuyan shi
da kwana biyu yake ɗan sagewa, kamar irin be kwanta da kyau ɗin nan ba.




Ya faruƙ ne ya fara tashi,
Sannan ɗaya bayan ɗaya ƴan samarin suka fara watsewa daga teburin cin abincin suna ficewa,



Cike da isa Umma babba tace

"Hafsa, ku tashi ku kwashe plates ɗin nan, uwayen son jiki" Ta ƙarashe maganar tana miƙewa
haɗe da kara wayar ta dake ringing ga kunne




Tas su Najwa suka gyara wajen kamar yarda suka shirya shi a ɗazu, kowa da abinda ya ɗauka
yake yi, banda Hafsa dake ƙorafin bata ga Mumtaz ba, ai ba su kaɗai ya dace su rinƙa aikin ba



Da yake ƙasa-ƙasa take ƙorafin ta yasa Umma babba

Please Login or Register in order to submit comment