Reading LAUJE CIKIN NAƊI by ZAINAB FALALU Chapter 10 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

amsar da ze bata

ta sake cewa "magana nayi fa bakace komi ba"
Tallafe gefen fuskar shi yayi sannan yace "ai maganar ce naga tafi ƙarfi na umma, amanace fa a
hannun na kin fi kowa sani, kuma ni a halalin da nake samu daidai gwargwado na baki kusan
4m ki yi wani abun, ni kam ban gane ba gaskiya"




Ɓata rai umma tayi tace "nasan ka bani 4m, amma babu wani abu da zasuyi min game da
hidimar nan wallahi, ka mance bayan hafsa da Amal harda bilkisu a ciki?



Ya faruk da maganar ta fara isarsa yace "na sani umma, duk abunda ya dace ayi wa yaran nan
Abba ƙ yayi, ko cokali be barku kun siya ba to me kuma ya rage?"



"hmmm" tace, sannan ta ɗora da "Duk baƙar wahalar da yake saka ka ai baka gani kullum cikin
goyan bayan shi dana matar shi kake, inda bani na haifeka ba banjin ko kallo na ishe ka a cikin
gidan nan ba"



Ya maryam tayi karaf tace "haba umma, dan Allah kidena kawo ma zuciyar ki irin wannan
abubuwan, be dace ba gaskiya"

Tana gama faɗin haka ta bar ɗakin ita sam bata ƙaunar abinda umman keyi, abun na mugun
ɓata mata rai



Sakin baki tayi tana binta da kallo

Ya sabiha da ita ce ke bin ya faruk itama tace "gaskiya ne umma, dan Allah ki rinƙa hanga
abubuwa mana, in baki fahimci ya faruk ba waye ze fahimce shi, wallahi yana a tsaka ne, kuma
abun alfaharin ki ne ace ɗanki nada amanar da har aka yarda dashi akan maƙuden kuɗaɗe har
yake kula da su bako wani shakka, wallahi bama jin daɗin yarda har ita maman kike nuna mata
abubuwa marasa daɗi" itama miƙewa tayi kafin ta fice tace "Amma in maganar mu ta ɓata maki
rai ki yafe mana" ta fice.



ya sabiha na fita, ya faruk ya miƙe shima, cikin ladabi yace "kiyi haƙuri, zan ƙaro miki 2m yanzu
in sha Allah" shima ya fice



Ɗakin su hafsat ya nufa dan yasan basu wuce can
Yana shiga ya iske ya maryam na kuka ya sabiha na bata baki

Shima zama yayi sannan yace "uwa uwace dole muyi haƙuri da ita a duk yarda take, sannan
muriƙa tausasa kalaman mu a garesu domin dacewa gobe alƙiyama

Nasan yarda kuke ji a ranku, to duk mu haɗu muyi haƙuri, muna haƙuri muna nusar da ita a
hankula se muga ta sauya" yana gama faɗin haka ya miƙe ya fice.

ALLAH KASA ANNABI YA CECE MU 🤲


LAUJE CIKIN NAƊI

NA
ZAINAB FALALU(MRS SULAIMAN)

MARUBUCIYAR



👹
MAKIRCI
KISHI DA ALJANA
WANI HANIN GA ALLAH
ƘADDARAR MU
LAUJE CIKIN NAƊI

WATTPAD@ZAINABFALALU8

Pg49-50

A haka zaka ga kamar umma b tayi laushi

Hakance ke kasancewa duk sanda yaran suka mata gyara akan halin ta.



Ya faruk be jima da fita ba yayi mata transfer sannan ya shirya ya bar gidan.



Sati ɗaya kawai Ahmad da mus'ab sukayi suna sha addu'a nan suka fara jin canji sosai a jikin
su

Babbar alama kuwa itace yarda yanzu har Ahmad na iya kusan yini a palon mama in har bashi
da wajen zuwa

Ita da kanta taga canji sosai, wani lokacin ma har surutun shi ya dameta



Ta ɓangaren mus'ab ma haka, da bakin shi yace "mama, kwana biyun nan ina jin zuciya ta na
sauka, wani nauyi datayi min shima se sauka yakeyi"

Murmushi mama tayi tukun tace "ai duk wanda ya riƙe Allah bashi ba taɓewa, shike yi shike
sakawa kuma shi ke hanawa, Allah ya warware mana komi cikin sauƙi da salama"



"Amin" yace ya ci gaba da aikin shigar da takardun da ya faruk ya bashi yayi tun shekaranjiya".



Ta ɓangaren mumtaz kuwa tun da ya faruk ya bata nata maganin ƙin sha tayi, anan kan mudubi
ta ajiye shi, Altine kuma data tashi shara ta haɗa da shi ta share



Da ya faruk ya tambaye ta tasha maganin? eh kawai tace ta barshi a hakan.




Wasa wasa biki nata matsowa, rayukan wasu fes wasu kuma gasunan dai



Tun biki na saura wata ɗaya Ya sabiha ta kira umma babba a waya tace "umma su hafsat zasu
iya tawowa zuwa jibi, me gyaran jikin na hanya itama"



Cike da fara'a umma b tace "aikuwa anjima zan kira Bilkisu ta dawo"

Ya sabiha tace "bata nan ne?"



"eh, taje wajen mahaifin ta tun shekaranjiya"



Cike da ɗan shakku ya sabiha tace "ehnn dama ina ta son in sanar da ke nayi wa mama da
mummy magana subar Mumtaz da Najwa su biyo su hafsan suzo tare se ayi musu gyaran
duka"
Umma nadaga kishingiɗe dama suke wayar, jin abinda ya sabihan tace yasa ta miƙewa zaune
Ƙanƙance ido tayi kamar tana ganin ta tace

"ohh, seda kika aiwatar tukun kike sanar dan saboda ban isa dake ba?"



Cikin rashin jin daɗi sabiha tace "ba haka bane umma, a matsayina na babba a cikin su be dace
ace na kira ƴan ɗakin mu ba kawai na bar sauran alhalin dukan su rana ɗaya za'a aurar da su,
kuma.."

Bata bari ta ɗora ba ta dakatar da ita da sauri tace "Su da kike kumfar baki akansu kika san me
iyayen su ke musu ba tare da sun haɗa da su Amal ɗin ba?"



Shiru sabiha tayi tana danasanin sanar mata data yi, data sani tayi shiru sedai daga baya taji
labarin dasu suka tafi



Cikin fushi umma tace "ba magana nake miki ba kikayi banza dani?"

Kasa cewa komi tayi sedai tace "kiyi haƙuri ban san bazakiji daɗin hakan ba"



Tu zaburar farko da umma b tayi ta fara sababin ta mumtaz ke tsaye jikin ƙofa,

Hannun ta riƙe da leda me ɗauke da sauyoyi na maganin sanyi da goggo safiya ta bata ta kai
mata ita da mummy

Tas ta gama jin me suke faɗa ita da ya sabihar kafin ta ƙwanƙwasa ƙofar

A sama umma tace "waye? shigo" a tare

Seda mumtaz ta taɓe baki kafin ta tura ƙofar bakin ta ɗauke da sallama ta shiga



Umma na kallonta ta sake haɗa fuska

Ɗan rissinawa tayi ta gaishe ta,
Ta amsa ba yabo ba fallasa

Mumtaz bata jira komi ba ta miƙa mata babbar ledar tace "gashi inji goggo safiya, wai ki tafasa
da jar kanwa ki ba su Amal su rinƙa sha"
A yatsine ta karɓi ledar ta leƙa sannan ta ɗago kai
Har mumtaz ta kai ƙofa taji tace "Kuma tace maganin mene?"

Ko waigowa mumtaz batayi ba tace "na sanyi" a taƙaice ta fice ta nufi sasan mummy(matar
uncle Abbas)




Seda tayi knocking me aiki tazo ta buɗe mata

Tayi niyar taba me aikin saƙon, jin muryar mummyn tana tamvayar waye yasa ta ƙarasa shiga
cikin palon



Cike da fara'a mummy ke faɗin "Ah lallai ɓatan hanya kika ne ko?"



Murmushi mumtaz tayi ta ɗan ɗosana mazaunan ta a bakin kujera tace "ina wuni mummy"



Tace "lafia lau mumtaz"



Bayan gaisuwan bata sake cewa komi ba ta miƙa mata ledar hannun ta tace "goggo safiya tace
na kawo, a dafa Najwa ta rinƙa sha"



Allah Allah take ta bar sasan saboda wani mayen kallo da Tk ke binta da shi

Mummyn na ankare da rashin nutsuwar ta, a wayance ta kalli Tk da ido tace "meye haka?"



Murmushi kawai yayi ya kashe mata ido ɗaya

mumtaz na gama faɗin saƙon ta miƙe tace "se anjima mummy"



Cike da fara'a mummy tace "shikenan tunda kinƙi zama, kice mata angode"



Tana fita ya Tk yayi wuf ya biyo bayanta da sauri, ko maganar da mummy ke mishi be tsaya yaji
ba yayi gaba



Sauri kawai take zubawa ta bar wajen kar ya cin mata,
Hakan be samu ba seda ya sha gaban ta

cike da shaƙiyanci yace "ina fatan kema ana gyaramin ke yarda ya kamata?"



Ɗaure fuska tamau tayi ta kewaye shi tayi gaba abinta, a ranta tana faɗin " Ɗan iska, Allah yayi
min tsari da kai"



Beyi yunƙurin binta ba ganin kallon da Ahmad ke mishi, duk da ya girmi Ahmad amma hakan be
hana shi jin ɗan shakka ba, tunda yasan ba Allah acikin kalaman bakin shi.




BAYAN KWANA BIYU



Ya sabiha da su ya maryam da ƙyar suka shawo kan umma b ta yarda da maganar zuwan
mumtaz da najwa.

Randa ya dace su tafin, akai-akai da mumtaz ta shirya su tafi, ba abinda ya fito bakin ta se
cewa tayi "Wallahi ko waye yazo kanta bw zata je ba, ita bata son gyaran jikin tunda be zama
dole ba"



Da bayan hannu goggo safiya ta make mata baki, kafin tace "dan kanki tunda kin raina kowa"



Mama kam tunda tace "meyasa ba zaki je ba" tace mata "ka kurum" bata sake magana ba,
tasan sarai tana da dalilin ƙin zuwan, in akai duba da tun randa sabiha tayi maganar bata musa
ba.



Haka Amal tayi nacin har tayi fushi ta rabu da ita,

Da dai taƙi zuwan, haka zuka tattara sauran suka tafi.



Ko da ya sabiha taga ba mumtaz a cikin su ta ɗauki waya ta kirata, bugun duniya taƙi ɗagawa
daga baya ma kashe wayar tayi.




BAYAN SATI BIYU, ANA SAURA SATI BIYU ƊAURIN AURE

Kayan funitures suka iso tun daga turkey ya faruk yayi order bisa ga zaɓin ko wacce a cikin su



manyan stores ɗin dake gidan aka buɗe aka shaƙare kayan duka a ciki tukun aka rufe



Duka su biyar ɗin saiti ɗai-ɗai Abba b yayi musu, wanda yaga ze ƙara ma ƴarshi shikenan
shidai yayi nashi




A sanda akayi order kayan mama itama ta yi nata order har sun so sufi wanda akayi musu duka
tsada,



A ranar da akaje ganin gidajen amaren aka ga gidan mumtaz ɗaki uku ne, nan Mama tayi wa
Abba magana ya bada wasu kuɗin aka siya saiti ɗaya.



Kamar Najwa da Bilkisu su dama dangin mahaifin su sun masu ɗaya, sun tashi da bibbiyu
kenan



Ranar da za'a je jere raba tafiyar akayi

Umma babba da aunty suka tafi na mumtaz tare da ƴan'uwan mama



Mummy tabi wasu daga cikin ƴan'uwan umma b suka tafi na Amal

Umma ƙarama tabi wasu suma daga cikin dangin umma b ɗin zuwa gidan hafsa



Mama tabi zuwa na Bilkisu, inda kuma dangin mummy duka suka ɗunguwa zuwa ga Najwa.
Ganin dukiyar da aka narka ma mumtaz a ɗan madedecin gidan ta hankalin umma babba yayi
masifar tashi tunawa data yi bayan saitin da Abba ƙarami yayi musu, Abba babbar ƙananun saiti
ya ƙara musu da shi

Duk da tana basarwa, amma indai kayi mata farin sani zaka san bata cikin nutsuwar ta



Gefe taja bayan ta fakaici idon mutane ta ɗaga waya ta kira ya sabiha tace "Duk yarda za'ayi
kar ajera saitin da Abba babba yayi musu, a samo mota a kwashe su a maida store ɗin da aka
siya zatayi ciko a zaɓo musu waɗan da suka fi wannan tsada"



Cike da mamaki ya sabiha tace "saboda me umma?, har fa mun gama da gidan hafsat mun
wuce na Amal"

Cikin fushi umma b tace "haka nake so ayi sabiha, nan da awa ɗaya zan kira"

Ba ta jira jin komi ba ta tsinka wayar.



Haka suka haɗu aka ɓalle gadon aka loda su a mota
sannan suka wuce gidan hafsa aka ciro nata suka kama hanyar store ɗin da aka siya kayan



Tsabar gasa da umma ta saka a cikin ranta seda ta siya musu wanda yayi shige dana mumtaz
tukun hankalin ta ya kwanta, amma fa aljihun ta ya girgiza.

ALLAH KASA ANNABI YA CECE MU 🤲
LAUJE CIKIN NAƊI

NA
ZAINAB FALALU(MRS SULAIMAN)

MARUBUCIYAR



👹
MAKIRCI
KISHI DA ALJANA
WANI HANIN GA ALLAH
ƘADDARAR MU
LAUJE CIKIN NAƊI

WATTPAD@ZAINABFALALU8
Pg51-52

Gadan gadan shieye shirye sun fara kankama,

Ta ɓangaren mumtaz taƙi yarda da duk wani gyaran jiki da mama Asiya tasa azo ayi mata

Abu ɗaya ta yarda da shi shine turaren jiki da ake mata, shima dan tana son ƙamshi ne, irin
haɗin nan ne mesaka jiki yayi laushi kamar fatar jariri

Wannan bata fashin shi, ko ba'ace tayi ba takan ɗauka tayin

Ana sauran kwana goma sakina ta haɗo yanata yanata ta dawo nan gidan, duk da ka kalle ta
zaka san akwai abu a ranta

Ganin vatayi nasara akan khalid ba yasa tun da ta iso da zaran sun keɓe se ta fara kusar kalid
ɗin

Jinta kawai mumtaz take, abinda bata sani ba khalid ɗin da bakin shi ya gaya mata tayi hankali
da ita.



Fitowar su daga ɗaki kenan suka iske ya faruk zaune kusa da mama

Cike da damuwa mama ke faɗin "Memakon ka bari se bayan biki se ka tafi faruk? ko dai wani
abunne baka sanar dani ba?"



Murmushi yayi yace "ko ɗaya mama, nema ne kawai ze fitar dani"



Shiru mama tayi, haka kurin take jin wani yanayi mara daɗi a tattare da ita.



Sakina har ta kai ƙofa amma mumtaz bata tawo ba

juyowata tayi tace "ko mun fasa ne?"



Bata san me yasa jin wani iri ba jin ya faruk zeyi tafiya

Jiki a sanyaye tace "bamu fasa ba ina zuwa"

Da sauri ta haura sama, ɗakin da aka loda layan lefen ta tashiga
Bubbuɗe akwatunan tayi ta rasa me zata ɗauka ma a ciki

Shiru tayi ta zuba wa kayan ido kafin idanun ta sukai ga akwatin turaruka



Bata yi la'akari da cewa turaren mata bane, haka ta ɗakko wata ƴar madedeciyar jaka ta kwashi
kusan guda huɗu ta saka a ciki, se lip balm guda biyu

Tusa jakar tayi a hijabi bayan ta rurrufe komi tukun ta sakko

Bata iske kowa a palon ba se sakina data gama cika



Da sauri mumtaz tace "sakina su ya faruk fa?"



Seda tayi mata kallo ɗaya tukun tace "gashi a baya na"

Tsaki mumtaz taja tayi waje da sauri

Tana fita ta iske bala driver na saka jakar shi a mota

Ƙarasawa tayi tace "Bala ya faruk fa?"

Yanzun nan umma babba tayi kiran shi

Jakar hannunta ta miƙa mishi tace "in ya fito ka bashi kace nace Allah ya tsare"



Karɓa yayi ya aje a kujerar gaba sannan ya shiga ya kunna motar



Sakina na ƙarasowa suka fice zuwa neman head ɗin da ze hau kayan da zata saka ranar kamu.




Seda suka isa cikin airpot sannan bala ya miƙa ma ya faruk ledar da mumtaz ta bayar

Da alamun tambaya a fuskar shi yace "na mene wannan?"



Kai tsaye yace "Mumtaz tace a baka, kuma tace nace Allah ya tsare"
Akaro na ba'adadi da yaji faɗuwar gaba, karɓa yayi be tsaya ya buɗe ba ya saka a jakar hannub
shi yayi sallama da bala ya shige.




Ta duka ɓangarorin kowa shiri yake ba ji ba gani



Yau ya kama saura kwana biyar ɗaurin aure, yayin da zasu fara biki daga jibi



Duka ƴammatan da suka tafi gidan ya sabiha sun dawo, ko wacce ka kalla zaka ga tana sheƙi
da ƙamshin amarci

Randa suka dawo da goggo safiya taga yarda suke sheƙi gunin ban sha'awa, aikuwa ta tasa
mumtaz tayi ta caccakar ta tana dungure mata kai



Ɗaya daga cikin dangin mahaifiyar mama tace "banda abinki ba wanda ze ganta yace ba tare
akai musu gyaran ba"



Da sauri ta gyaɗa kai tace "ƙarya haram, hasken fata daban sheƙin ta daban, in kika ga yarda
suke sheƙi ba zaki ma fara haɗa su da wannan ba"



Matan dake palon suna ta kakkare mumtaz, anayi ana dariya




Gida sosai ya ɗau harama malam, saura kwana uku ɗaurin aure amma zakayi tunanin ranar
ɗaurin auren ce.



WASHE GARI

Tunda safe wajen goma masu decoration ɗin wajen da za'ayi kamu suka iso

Ɓangare ɗaya na gidan aka shirya, kayan gargajiya da ake kamu dasu aka danka gunun ban
sha'awa
Ta ɓangaren amaren kuwa akan gama sallar azzahar aka fara musu kwalliya

Masu kwalliya mutum biyu aka kira dan asamu yin sauri



Hafsat aka fara ma, se najwa, se bilkisu se Amal sannan akai ma mumtaz da seda aka kai ruwa
rana kamar wacce za'aiwa auren ƙi




Ta ɓangaren gidajen angwayen kuwa sun shirya tsab domin halartar taron kamun, wanda a
al'ada suke zuwa su kama amarya.



Mutum shida mami ta wakilta daga ɓangaren khalid

Bayan la'asar kamal da wani abokin khalid suka je ɗakko su, mota biyu sukayo



Sosai sukayi shiga ta alfarma ta kuma kece raini



wajen biyar saura duka dangin angwayen suka iso, an jima da nisa wajen farawa

Masu kiɗin ƙwarya da aka gayyata sun baje kolin su, mata na ta rausayawa

Su kansu iyayen amaren ba daga baya ba, karma ku hango shigar da mama tayi, tuni wasu da
dama suka fara raina tasu shigar alhalin suma ɗin ba daga baya ba



Dangin angwayen ma zuwa suka gabatar da al'ada na feshe feshen turaruka da kuma sauran
abubuwa



Ana gab da kiran magariba aka tashi, na tafiya suka tafi, wanda kuma dama sunzo se bayan
biki kowa ta kama inda ya dace ta zauna.




Wajen sha biyu saura na dare da yake gidan biki ne, bama zaka taɓa cewa dare yayi haka ba,
shewace shewace da guɗa da kuma hirarra ki ke tashi ta ko wani lungu da saƙo na gidan, uwa
uba ga hasken fitulu ta ko'ina

mumtaz ta ƙwanƙwasa ƙofar ɗakin Abba ƙ inda take kyautata zaton maman na nan tunda bata
a ɗakin ta



Fitowar mama daga wanka kenan taji bugun ƙofar

Zuwa tayi ta buɗe, ganin mumtaz a tsaya yasa ta matsa ta bata hanya ta shigo, sannan ta
maida ƙofar ta rufe

Kan kujera ta wuce ta kwanta bata ce wa maman komi ba



Maman ma bata ce ba taci gaba da abinda take

Seda ta gama tas tukun ta mayar da hankalin ta ga mumtaz da har ta fara bacci anan kan
kujerar

Kafe ta da kallo mama tayi, ta jima tana kallon ta kafin ta tashi ta fito

kitchen ta nufa, shayi ta haɗa sannan ta ɗauki cake gudu uku da su Altine keta parckaging
rabon da za'ayi a gobe wajen walima

Saman ta koma, a gefe ta aje shayin tukun ta fara tashin mumtaz
"Tashi mumtaz daga ganin ki na san bakici komi ba, tashi kisha tea"



Da ƙyar mama ta samu ta tashin, ko rabin kofin bata sha ba tace "mama ya ishe ni"



Cike da lallami maman tace "daure ki shanye dai, ko ɗaya ne kici cake ɗin shima"

Tusa mata shi tayi tayi har seda ta kusa shanye shi tukun ta rabu da ita, kafin daga baya tace
"anan zaki kwana ne?"



Gyaɗa kai tayi tace "Mutane sun cika ɗakin ba wajen kwanciya"

Bata sake cewa komi ba ta juya tayi kwanciyar ta bacci yayi awon gaba da ita.



Mama kam tun ranar da aka fara taruwa ta ƙarasa rasa sukuni gaba ɗaya,
Maman sakina tasha ta titsiye ta tana tanbayar ta "lafiyar ta kalau kuwa"

Amsa ɗaya ce kodayashe itace "lau" ko kuma tayi murmushi kawai

Dan ko an titsiyeta ta faɗi meke damunta ba zata iya kwatantawa ba.

Daga baya kawai take alƙanta abin ga kewar mumtaz da zata yi.

Daga wannan saƙe-saƙen bata san sanda bacci itama yayi awon gaba da ita ba.




WASHE GARI

Biyar saura na yamma harabar gidannan a shaƙare take da ƴan'uwa da abokan arziki, wasu
sun sha Abayoyi, wasu sun sha jalbab ɗinsu wasu kuma normal hijabai ne a jikin su,
Wasun su da niƙab wasun su kuma haka nan



SHAIKA ZAINAB MAHMUD ADAM na tsaka da fara muƙaddima amare suka fara shigowa,
dukkannin su sunsha tsadaddun Abayoyin su, banda mumtaz da ta naɗe kanta da jar laffaya
me tsaɗar gaske



Ɗaya bayan ɗaya suka samu waje suka zauna a kujerun gaba-gaba



Sosai shaika zainab mahmud Adam tayi shikekken wa'azi game da haƙƙin mace akan mijin ta

sosai wa'azin ke shiga dukkan mahalukin dake wajen, bama amaren kaɗai ba, harda waɗan da
sun jima a cikin auren dama wanda basu kai ga shiga ba



Shaika zainab mahmud ta ɗau lokaci me tsayi kafin ta rufe

Ɗaya daga cikin malaman da suka zo tare ta fara rero waƙa cikin harshen larabci,

Tana tafi tana waƙen,
wasu a ciki da suka iya suka hauyi suma

Anata tafi ana waƙen gunin ban sha'awa.
Note: waƙe ne da musulunci ya yarda dasu, don't come and attack me 😎
Sosai walimar tayi armashi, aka ƙaru sosai, waɗan da jikin su yayi sanyi saboda tsoratarwan
datayi duk suka warware wajen waƙe da kaɗa kai.

Shima gab da magriba aka watse, bayan an gabatar da hotuna, ciye ciye da shaye-shaye.



WASHE GARI



RANA BATA ƘARYA SEDAI UWAR ƊIYA TAJI KUNYA!!!



Tunbatsar da gidan yayi ba'acewa komi, mata ne ta ko'ina,

Tsabar cikar gidan har seda ta kawo da an buɗe makeken gate ɗin gida

Runfuna ne da kujeru ta ko'ina, karku mance biki ne na masu shi masu ƙubar susa

Matane hawa hawa, waccen wace wannan, wannan wace wancan



Kowa kaga fuskar shi zaka san yana cikin murna da farin ciki banda ƴan tsiraru daga ciki

Ciki kuwa harda mumtaz da mama da har shi Abba ƙarami da faɗuwar gaba ta same shi a
safiyar ɗaurin auren



Haka zalika kalid,
Daga wayewar gari zuwa yanzu ya ƙira mumtaz a waya yafi a ƙirga, kuma in ya kirata abu ɗaya
yake tambayar ta shine "Ba wani abun dai ko" har ma ta gaji da amsashi.



Sanda ya faruk ya tafi, se washegari ya buɗe jakar turarukan da mumtaz ta bayar a bashi

seda abun yaso bashi dariya da yaga duk turarukan mata ne

Ɗaya bayan ɗaya ya hau shinshinar turarukan, yanayi yana lumshe ido tsabar yarda sukayi
masa daɗi

Yana tsaka da jin daɗin shi zuciyar shi tace "Allah yasa ba satar su tayi ba dai"
Nan da na mood ɗin shi ya sauya haɗe da jin wata mummunar faɗuwar gaba.



HMMMMM.

ALLAH KASA ANNABI YA CECE MU 🤲
LAUJE CIKIN NAƊI

NA
ZAINAB FALALU(MRS SULAIMAN)

MARUBUCIYAR



👹
MAKIRCI
KISHI DA ALJANA
WANI HANIN GA ALLAH
ƘADDARAR MU
LAUJE CIKIN NAƊI

WATTPAD@ZAINABFALALU8

Pg53-54

Tunda garin Allah ya waye mumtaz ke zauna a bedroom ɗin Abba ƙ

Ita batayi wanka ba, ba ta kuma da niyar tashi tayin.

Kusan tashi uku mama na shigowa ɗakin, a inda ta barta a nan take isketa,

Har ita maman tayi wanka ta shirya duk mumtaz na nan zaune, ta muskata nan ta muskuta can



A shigowa ta huɗu ne mama tace "Kalli agogo fa mumtaz, sauran duk sunyi shiga ta bibbiyu
amma ke ko ɗayar bakiyi ba, ni shin gaya min gaskiya, kodai kina da wata damuwar ne da kika
kasa gaya min"?



Sadda kanta ƙasa tayi ta kasa cewa komi, se hawaye da suka fara tsere akan kumatun ta



Jikin mama dama a sanyaye yake, nan da nan ganin hawayen ɗiyar tata yasa jikin ta ya sake
yin sanyi
Kayan dake hannunta ta aje sannan ta matsa kusa da ita

A hankali ta janyota ta rungume ta, cike da tausayi da kuma ƙauna irin ta uwa ta fara shafa
bayanta, a hankali tace "Ki gaya min ko dai kun samu matsala da khalid ɗin ne?"

Tana cikin jikin ta ta karkaɗa kai,
Maman ta sake cewa "To gaya min menene?"

Cikin sheshekar kuka tace "Kawai bana jin daɗin jiki na, kuma gabana na yawan faɗuwa
akai-akai"



Murmushin yaƙe mama tayi ta ɗago da kanta daga jikin ta

Sosai ta fuskance ta tukun tace "Wannan ba wani abu bane mumtaz, duk amarya a ranar auren
ta takan fuskanci abubuwa makamancin waɗan nan da kike ji, daurewa ake da zaran an ɗaura
auren zakiji kin dena ji"



Mumtaz tace "Amma mama jiya a wajen walima seda na tambayi Amal ko itama tanajin hakan
tace min a'a"



Shiru mama tayi can tace "ai shine nace miki ya danganta, ta yuwu ita ba kalar naki take ji ba,
wani daban take ji"



Bata sake cewa komi ba,

Seda maman ta sauya kaya tukun tace
"Maza kije kiyo wanka, ga akwatin kayan ki nan, zan turo me kwalliyar zuwa palo se ki fito tayi
maki"



Ɓata fuska mumtaz tayi tace "yau ba zanyi kwalliya ba mama"



Kai tsaye maman tace "zakiyi, zance ayi maki light one" ta juya ta fice tana amsa call.




Gida ta ko'ina ba matsaka tsinke, kowa ka gani ya cike da murna da kuma fara'a
Wasu sunyi group ana ta fira wasu kuma suna ta harkokin su

Daga can gefe sautin waƙar gwanja ne ke tashi

Duk da ba rawa ake ba amma daga gani kasan sautin na kaima kowa




Ta ɓangaren amare kuwa ko wacce daga cikin su ta gaji da haɗuwa



Babban palo aka ware musu su da ƙawayen su,

Sakina ce keta tarbar ƙawayen mumtaz dabata fito ba haryanzu

Sauƙinta ɗaya ma ƙawayen nasu ɗaya ne da Amal, amma ko wacce in tazo bataga mumtaz ba
se ta tambaya

Da dai Amal ta gaji da tambayoyin yasa ta janyo waya tayi dialing no ɗin mumtaz

Ana tsaka da mata kwalliya call ɗin Amal ta shigo,
Ganin an kusa gamawa yasa bata ɗaga ba dan dama tasan ƙorafi ne.




Ta ɓangaren angwace ba'acewa komi, in ka kalli wannan sekace yafi sauran kyau, da ka kalli
wani shima se kaga kamar yafi wancan kyau,



Khalid na zaune kusa da kamal yana ɗaure igiyar takalmin ƙafar shi

Waya kare a kunnen shi yana sauraren mami dake ƙorafin kar ya wuce wajen ɗaurin auren ba
tare da sun biyo taga wankan shi ba

Murmushi kawai yake zubawa, sannan yace 'na san yarda mamina ke sona da kuma son nayi
aure tabbas zata so ta ganni for the last time a matsayin saurayi kafin na zama ango kokuma
ince magidanci"



Dariya da salati a tare mami ta hau yi kafin tace "naji ka dai zo in ganka" tana gama faɗin haka
ta ajiye wayar taci gaba da saka ɗankunne a ɗayan kunnen.



Khalid na aje wayar mami abokan shi suka hau tsokanar shi da mummys boy

Shidai murmushi kawai ya ke ta faman yi yana jin azalzalar ayi a ɗaura

Please Login or Register in order to submit comment