Reading LAUJE CIKIN NAƊI by ZAINAB FALALU Chapter 19 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

cewa komi yayi, duk da daman yasan zesha fama da Abba ƙ kafin ya amince
da maka su a kotu

A cikin ranshi yace "in an san wata ai ba'a san wata ba wallahi"

Ficewa yayi daga ɗakin rai ɓace

Mama na hango shi ta yafito shi da hannu

Duk da ya sassauta fuskar shi hakan besa ɓacin ranshi ɓacewa ba

Mumtaz kanta kallon shi take tana so su haɗa ido taji meke damun sa.

Kusa da mama ya zauna ya sadda kan shi ƙasa

Jiki a sanyaye tace "nasan hukuncin ba daɗi ze maka ba yaro na,
mu barsu da aniyar su, mukuma gode wa Allah da ya taƙaita mana abun, ko a haka aka tsaya
Allah ya warware mana kaikaifen LAUJEN da ke CIKIN NAƊI"

Bece komi ba sema sake jin wani tausayi da ƙaunar ta a cikin ranshi.

Gyaɗa kai goggo safiya tayi itama tace "hakane abinda zahra'u tace faruk, koda amanar
zumunci da suka ci aka barsu ya ishe su"

Umma babba ta ɗora da "mugunta kuma ai fitsarin faƙƙo ce, suje can su ƙarata da matsalar
dake a tsakanin su ma ta ishe su"

Aunty tace "Allah yayi mana maganin abinda bamu iyawa"

Haka suka haɗu sukai ta ba ya faruk baki da kalami masu daɗi har sanda su Abba babba da
uncle ƙasim suka fito da niyar zuwa duba Tk dake kwance shima har yanzu.
Gaf da azzahar aunty da umma babba suka wuce gida aka bar goggo safiya da mama se
mumtaz da ke bacci tunda ta samu ta shiga ta gaida Abba ƙ ta bi lafiyar ɗayan gadon da mama
ke kwana a kai ta kwanta

Ba wanda ya tashe ta aka barta tayi baccin ta.



***Sosai ya faruk ya fuskanci mus'ab da Ahmad yace

"Ku saurare ni da kyau kuji, tunda har su Abba suka yanke wannan shawarar to babu yarda
za'ayi mu ja da su, abinda zamuyi yanzu shine, zan yi write up akan uncle Abbas da uncle
junaid harma da umma ƙarama akan cin amanar da sukayi, mu yaɗa su a duniya"

Tun ɗazu se yanzu mus'ab yayi murmushi, dan gaba ɗaya wannan tunanin bezo mashi ba sam



Ahmad yace "yes, shiyasa nake alfahari da kai ya faruk"

Murmushi ya faruk yayi sannan yace "zamu haɗa duka da pictures ɗin su, yarda har fita ma
seta gagare su saboda kunya, sannan ko su Abba sunji zamuce bamu san yarda akayi ba"

Dariyar farin ciki mus'ab da Ahmad suka saka haɗe da rungumar ya faruk dake ta murmushin
jin daɗi shima.



BAYAN SATI ƊAYA

Khali na kwance yana ta scrolling a facebook yaci karo da dogon rubutu me ɗauke da hoton
umma ƙarama da uncle Abbas da kuma uncle Junaid

Ganin fuskokin su da kuma rubutun da akayi da manyan baƙi daga sama ya sa shi miƙewa
zaune da sauri haɗe da ƙurama rubutun ido, inda ka rubutu "MACIYA AMANA UKU"

Tiryan-tiryan khalid ya karanta labarin tas, inda babu wani abu da aka ɓoye akan irin cin amanar
da sukayi, har da asirin da akayi wa Abba ƙarami na sata da be kamashi ba ya kama ƴarsa
mace ɗaya tilo

A sukwane khalid ya fito ya hau kiran sunan "mami" da ƙarfi

Mami na zaune ita da aunty hajara suna firarsu sukaji mahaukacin kiran da kalid ke kwaɗa mata

A firgice har suna rige*rigen fitowa
Mami tace "lafia khalid"

Fuska shaɓe-shaɓe da hawaye yace "mami na cuci kaina, na shiga uku, ni dama nasan
mumtaz mutuniyar kirkice wallahi"

Kallon kallo mami da aunty hajara sukayi kafin mamin tace "me yafaru kake kira ma kanka
shiga uku?"

Cikin kuka kamar wani ƙaramin yaro ya miƙa mata wayar

Hannun ta har rawa yake wajen ƙoƙarin ƙarɓa

Shiru tayi tabi wayar da kallo, bata san mutanen dake cikin hoton ba, amma content ɗin saman
yaja hankalin su ita da aunty hajara har suka tsunduma cikin labarin

Tun kan mami ta kai ƙarshe take furta "innalillahi wa'inna ilaihirraji'un!!"

Aunty hajara kanta jikin ta yayi sanyi tana tuno fuskar mumtaz

Kukan da khalid keyi ya karyar musu da zuciya, se ga mami itama shaɓe shaɓe da hawayen
nadama da danasani

(SHIYASA BINCIKE YAKE DA KYAU KAFIN KA YANKE HUKUNCI

KUMA GAGGAWA AIKIN SHEƊAN CE)

Ranar haka khalid da mami suka yini cikin juyayi da danasani.



Kamar yarda kalid yaga wannan rubutu game da su incle Abbas, haka ya karaɗe lungu da saƙo
na ƙasar.

Uncle ƙasim na gani yayi murmushi, a fili yace "Nasan ba kanwar lasa bane kai faruk, kayi
ƙoƙari"



Gaba ɗaya fita ta gagari uncle Abbas da uncle junaid, ga tsiyar dake tsakanin su data kunno kai
me zafin gaske.

Umma ƙarama kam tun sanda Abba babba ya bata tikitin sallama taƙi yarda ta sanarwa da
iyayen ta abinda tayi

Seda wannan rubutu me ɗauke da hotunan su ya bayyana aka san komi,
Abin duniya suka taru sukai mata yawa, ga tsana daga wajen ƴaƴan cikin ta, ga kuma tsana
daga nasu gidan, rana zafi inuwa ƙuna kenan.



Abba ƙarami tun yana hospital yasa aka gyara mashi ɗaya daga cikin maka makan gidangen
shi

Kai tsaye yace "ya gama zama da kowa, nesa nesa tafi"

Hakan kuwa ba ƙaramin daɗi yayi wa mama ba, dan sanda ya sanar da ita kasa ɓoye murnar ta
tayi seda ta rungume shi.

Haka ya faruk yayi ta up and down har seda gidan ya shirin gidan ya kammala sannan aka
sallami Abba ƙarami

Direct sabon gidan suka wuce

Seda aka kwana ɗaya tukun mama taje can gidan

Ta kwasa abinda take so daga nan, ta rabar da wanda bata so.



Duk da ƴan'uwan nasa basu ji daɗin huƙuncin da Abba ƙ ya yanke ba, amma hakan besa sun
hana shi ba, sanin irin haƙurin da yayi da kuma ɗawainiyar da yake kan yi dan ba denawa yayi
ba.



BAYAN WATA TARA DA ƳAN KWANAKI

Ya faruk na kwance waya kare a kunnen shi suna magana da mus'ab da ya fita shigo da wasu
kaya na ɗaya daga cikin companyn Abba ƙ dashi ke managing yanzu a maimakon uncle Abbas

Mumtaz na zaune akan darduma tayi zaman tahiya ga uban tirtsetsen cikin ta a gaba haihuwa
yau ko gabe

Ta gama karatun tahiyar tana so ta miƙe tsaye amma ta kasa,

Ya faruk hankalin sa na can kan wayar da yake

Hannun ta tafa alamar magana

Shiru beji ba
Sake tafa hannuwa tayi a karo na biyu sannan ya faruk ya farga da tafin nata

Sallama sukayi da mus'ab ya taso ya matso kusa da ita yace "menene"

Alama ta sake yi mishi da hannu,

shiru ya faruk yayi ya bita da ido dan har ga Allah be fahimci me take nufi ba

Da dai mumtaz taji kamar bayanta ze ɓalle tace "Ai se ka ɗaga ni tunda kasa na ɓata sallah ta"

Kwashewa da dariya ya faruk yayi ganin yarda har idonta sun cika da ƙwalla

Seda ya miƙar da ita tukun yace "yanzu dai in kin huta kiyi sallar a zaune tunda in kin yi sujjada
baki iya ɗagowa ta daɗi"

Banza tayi da shi ta wuce can gefen gado ta zauna tana maida numfashi.

Kallon ta yayi cike da so da ƙauna haɗe da tausayawa yace "in sha Allah kin kusa sauke su ki
huta kema, Allah yayi maki albarka matata!"

Lumshe ido tayi, a koda yaushe ya faruk na sata jin nutsuwa a rayuwar ta

Ko kallon shi tayi takan tsinci kanta cikin farin ciki haɗe da godiya wajen ubangiji

cike da shauƙin so ta ɗora kanta a kafaɗar shi, shi kuma ya zagayo da hannun sa kan ƙaton
cikin ta yana shafawa.



A GURGUJE.

Mom Asiya data samu ta anshi nata tikitin daga wajen incle junaid taje ta maka Tk a kotu tana
nemar wa ƴarta saki

Haka akaita tafka shari'a har Allah ya basu sa'a ta samu sakin, sedai ba'a jima da sakin ba cikin
Tk ya bayyana a jikin sakina

Hankalin sakina ba ƙaramin tashi yayi ba, haka sukai ta fama wajen ganin bayan cikin nan,
amma da yake duk abinda Allah yayi niyar halitta babu makawa seyayi haka suka haƙura har
ƴar Tk tazo duniya ba dan ransu yaso ba.
ALHAMDULILLAH!!!

DUKKAN GODIYA TA TABBATA GA UBANGIJIN TALIKAI

NAGODE WA ALLAH DA YA NUNA MIN FARKO DA ƘARSHEN LITTAFIN "AKWAI LAUJE
CIKIN NAƊI" ALLAH UBANGIJI YASA MU AMFANA DA DARASIN DA KE CIKI, KUSKUREN
CIKI YA YAFEMAN, YASA MUYI TARAYYA A LADAN!



❤️
GODIYA DA JINJINA TA MUSAMMAN GA MIJI NA ABIN ALFAHARI NA, ƘAUNAR KA TA
DABAN CE A RAINA, ALLAH YA BAKA KARIYA ADUK INDA KAKE



JINJINA GAREKU IYAYE NA, ALLAH YA SAKA MAKU DA ALKAIRI.

SANNAN INA MIƘO GAISUWA DA FATAN ALKAIRI GA DUK WANI MAKARANCIN LITTAFI NA

😊
MUSAMMAN ƳAN CIKIN GROUP ƊINA, ALLAH YA BAR ZUMUNCI YA HAƊA MU A BOOK
ƊINA NA GABA DA ALKAIRI

ALLAH KASA ANNABI YA CECE MU 🤲
30/5/2023

ZAINAB FALALU
08145225540

Downloaded From https://tknovels.com.ng


Please Login or Register in order to submit comment