Reading LAUJE CIKIN NAƊI by ZAINAB FALALU Chapter 13 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

cikin ƴan'uwan maman tace "ƙila mijin ne ze kaita, dan da muka fito naga an rufe
gidan ma"



Kamar daga sama suka ga faɗowar mumtaz a firgice
Dan har tsoro taso basu



Ganin yarda kowa ya watso mata idanu, ga kuma palon da yayi tsit kamar ruwa ya cinye su
yasa ta haura sama da gudu ta shige ɗakin mama ta danna key



Shigowar goggo safiya a hautsine itama ya sake kaɗa hantar cikin mama, nan da nan cikin ta
ya ƙulle taji kamar zata zagaya toilet



A tsorace mama ta miƙe tsaye tace "Lafia yaya safiya?"

Goggo safiya na zama tace "Se alkairi"



Gulma kecin kowa dake palon, tambayiyi fal baki, amma sun kasa tambayar ta

Zaman goggo safiya kenan ta miƙe tace "muje sama zahra'u"
Kasa miƙewa mama tayi, karkarwar da jikin ta keyi kawai ze nuna maka ba ƙaramin tashin
hankali take a ciki ba

Cike da ƙarfin hali goggo safiya ta temaka mata suka haura saman.




***UMMA B

Wallahi ka fitar da kanka acikin lamarin nan,

Kuma ba zan zaman babbar banza ba tunda har a gaba na komi ya faru to wallahi babu abinda
zan rage se na faɗa wa Abban ku, ai in har nayi shiru da maganar nan na ha'inci kowa.



Kan faruk a ƙasa ya ce "naji ki sanarwa da Abban amma dan girman ubangiji bayan shi kar ki
bari wani yaji maganar nan daga bakin ki umma"



Taɓe baki tayi kafin tace "saboda ga munafuka ko?"



Da sauri ya faruk ya ɗaga kanshi yace "subhanallah, Allah ya tsare ni da furta mugayen kalami
a gareki umma, kawai dai alfarman hakan nake nema, duk wanda ka rufa ma asiri kaima Allah
ze rufa maka a ranar da kaima kake da buƙata"

Banza dashi tayi, can tace "buɗeni na fita"

Jiki a mace ya saka hannun ya danna lock ɗin motar

Har umma b ta saka ƙafarta waje ta waiga ta nuna shi da yatsa tace "wallahi kar naji kar kuma
na gani, ko uffan bana so ka tofa"

Gyaɗa kai kawai yayi, yana jin tsananin zafi da kuma suya da ƙirjin shi ke mishi.



*****MAMA

Kuka take me sauti, kuka irin na yaya zanyi, daga wannan se wannan

Ta maimaita kalmar sata yafi a ƙirga
Tayi kuka tayi kuka har muryarta na neman dishewa

Goggo safiya na gefe, bata hanata kukan ba sam,
Da barin shi a zuciya babbar matsala ce



Mumtaz na daga gefe, itakam idanun ta a bushe suke

Da rarrafe ta matso kusa da mama dake zaune dirshen ta mimmiƙar da ƙafafuwan ta a ƙasa

Dafa ƙafar ta tayi tace "Mama dan girman Allah ki yafe min, bansan me ke damuna ba nima,
tsoro nake ji mama wallahi tsoro nake ji!"

Tana maganar jikin ta na rawa kamar mazari

Cikin kuka mama ta janyo ƴarta ta rungume ƙam a ƙirjin ta

Bata ce komi ba, amma rungumar data yi mata shine ke nuna komin



Sunfi minti talatin a haka kafin mama tace "Baki kyauta min ba mumtaz, ni mahaifiyar ki ce, in
baki sanar dani halinnda kike a ciki ba wa zaki faɗa ma? inda na sani ba zan taɓa bari ki tozarta
ba mumtaz ba zan bari a kai ga haka ba" ta sake fashewa da kuka tace "Allah kana kallo kana
gani kana ji ya Allah, bana nufar ɗan kowa da sharri ya ubangiji amma ga ɗiyata a daren
amarcin ta an koro min ita saboda wani dalili na bayin ka masu son zuciya da son ganin bayana

Ya Allah wannan tozarci ne a gareni da ɗiyata dama ahalina gaba ɗaya, Allah na kawo ƙarar
kowa gareka, bani da sani sedaga abinda ka sanar dani ya ubangiji, ka shiga cikin lamarin nan
da gaggawa, kabi mani haƙƙin tozarcin nan me muni da aka yi min ya ubangiji,

Allah ƙarfi na ya ƙare haka zalika dabara ta taƙare"

Kuka yaci ƙarfin ta, seda ta koka sosai kafin tace "Alhamdulillah ya rabbi, kayi mani kuma
nagode da ni'imarka"



Tunda mama ta fara addu'ar nan ya faruk ke tsaye, bata ganshi ba, amma mumtaz da goggo
safiya sunga tsayuwar shi

Shi kanshi neman maɓuya yake ya samu ya sauke nauyin da zuciyar shi ta ɗauka



A hankali ya ƙaraahe shigowa ciki
Kusa da mama ya zauna, se a sannan ta ganshi, da sauri ta saki mumtaz ta kama ya faruk tace
"kaji ko? ita kuma sata takeyi, faruk ko iya haka aka barni ai na gama tozarta ko?"



yatsun hannun shi ya saka ya goge mata hawayen fuskarta sannan yace "Allah baze taɓa barin
iyalan Abba ƙ su tozarta ba mama, haka zalika Allah ba zeyi watsi da wannan roƙa da kika yi
mashi ba, an zalunce ku kuma kin kai ƙara wajen wanda shi ya halicci ɓoyo, dan haka ki
kwantar da hankalin ki mama, ƙaddara ce kuma ina da yaƙini zamu cinye ta nan kusa"

Ajiyar zuciya take saukewa babu abinda take faɗa se "nagode faruk, naji sanyi a raina da na
ganka"



Waigawa wajen goggo safiya yayi da gaba ɗaya ta wani susuce a lokaci ƙanƙani yace "dole su
Abba su san dawowar mumtaz, abinda nake son sani shine sakin ta yayi kokuwa cewa yayi ta
dawo gida, dan mu san ya za'a tunkari su Abban da maganar"



Murya a dishe tace "ban sani ba wallahi faruk"

Mumtaz na lafe a jikin mama idonta a rufe, ya faruk yace "me mijin naki yace, saki ko ki koma
gida?"



Bata ko kalle shi ba tace "Bansani ba nima"



Miƙewa tsaye yayi yace "bani number shi"

Mumtaz tace "ban san inda wayar take ba"

Da sauri goggo safiya ta buɗe jakar hannun ta ta ɗauko nokiar ta tace "nemo shi a nan, da
kanshi ya saka ta"

Amsa ya faruk yayi, direct sunan kalid ya nemo, kwashe no ɗin yayi a wayar shi sannan ya miƙa
mata ya fice



Yana fita mota ya faɗa, har yayi niyar kunna motar ya hango uncle Abbas na tahowa

Cike da fara'a yaji yana faɗin " Kin kawo babban albishir wallahi, bari na koma gefe nayi gum
muji ta ina maganar zata fasu
Ina me tabbatar miki da in har Abubakar(Abba ƙarami) yaji wannan batu se zuciyar shi ta buga,
daga nan kuma ai kin san sauran, shi kuma wancan shashashan a daren nan zan sa yazo ya
sakar ma junaidu ƴarsa, in huta da tashi barazanar tunda ga babban kamu nan, yarda maganar
zata fasu kowa yaji banjin akwai wanda ze sake zuwa neman auren ta ba, zanyi amfani da
wannan damar ni in tausasa kaina se in nema wa Tk auren ta ba tare da anzargi komi ba"

Lafewa ya faruk ya sake yi, duk dan ya jiyo wacece wannan ke magana da shi

Kai tsaye zuciyar shi ta bashi da "umman kace, yo inba ita ba waye yasan da maganar" kan
kace me zufa ta lulluɓe faruk da ya fara tsoron abinda ranshi ke gaya mishi.

Kasa tada motar yayi yaja seat ɗin baya ya kwanta, yana ta farfasa maganar uncle Abbas dalla
dalla.



Gyaɗa kai yayi kafin yayi dialing no ɗin khalid, haka tayi ta ringing be ɗaga ba har ta katse

Ya faruk be gaji ba ya sake danna mishi kira a karo na biyu

Khalid na kwance a ɗakin mamin shi, abun duniya yayi mishi cak ya rasa meke damun shi

Cike da tausayi mami tace "dole zaka je gobe ka ɗakko ta, amma tabbas zaka auri macen kirki
wanda zata haifa mata nagartattun ƴaƴa

Tana gama faɗin haka kiran ya faruk ya sake shigowa

Mamin tace "ka daure ka amsa khalid, ko wani bawa fa da kalar tashi jarabawar"

Idon shi a rufen yana daga kwance ya janyo wayar, ko number be duba ba ya ɗauka ya buɗe
speaker,



Daga can ya faruk yayi mishi sallama

Da ƙyar kalid ya amsa jin muryar waye

Ya faruk beyi fushi ba yace "Naji duk abinda ya faruk khalid, amma yanke hukunci a cikin fushi
ba halin mumini na ƙwarai bane, komi yana buƙatar bincike kafin hukunci"

Tsaki da ƙarfi khalid yaja sannan yace "malam ka faɗi abinda kayi niya ina da abunyi"

Shiru faruk yayi, yana danne zuciyar shi sannan yace "okay, abinda yasa na kira ina so inji shin
da wata manufa mumtaz ke zaune a gida? in ba wata manufa to zan dawo maka da ita yanzu
dan munfi buƙatar sulhu akan wani abu daban"



Da sauri khalid ya miƙe zaune yace "Dalla malam dakata, karma ka kuskura ka dawo da ita ku
rubuta ku ajiye se Allah yayi mani sakayya akan ha'intata da akayi, kuma har abada bazan taɓa
iya zama da mumtaz ba, NA SAKE TA, NA SAKE TA, NA SAKE TA!!!!!"



Salati me ƙarfi mami ta saki haɗe da faɗin "Baka da hankali ne dan ubanka!



ALLAH KASA ANNABI YA CECE MU 🤲
LAUJE CIKIN NAƊI

NA
ZAINAB FALALU(MRS SULAIMAN)

MARUBUCIYAR



👹
MAKIRCI
KISHI DA ALJANA
WANI HANIN GA ALLAH
ƘADDARAR MU
LAUJE CIKIN NAƊI

WATTPAD@ZAINABFALALU8

Pg63-64

Cikin zafin nama ta kashe wayar, ta hau zazzaga mishi bala'i, cikin fushi tace "Maza-maza ka
janye sakin nan nace maka"

Ido jajir yace "mami wallahi ko na zauna da ita cutar ta zanyi, kuma bana so Allah ya kamani da
laifin cutar da wani"



Cikin kuka mami tace "su Baffan ka in suka ji abin zeyi muni, dama suna cewa na sangarta ka
kalid, yanzu kuma suji labarin ko tarewa da yarinyar baka yi ba kayi mata sakin wulaƙanci, babu
wanda zeyi la'akari da ɗan halinta"
Da ƙayar yake iya buɗe idon shi tsabar nauyin da kanshi yayi mishi, ya fice a ɗakin



Dafata aunty hajara tayi tace "Karki tilasta mishi, addu'ar ki yafi buƙata a yanzu, kuma tunda
yace ko sub zauna ze iya cutar da ƴar mutane kinga ba zamu sa ya kai kanshi ga halaka ba,
Da kaina zan kira su Baffan nayi musu bayani, gara ɓacin ran lokaci ɗaya akan na har abada"

Da kalar wannan kalaman aunty hajara ta kwantar wa da mami hankali

Gidan biki kam basu san me ke faruwa ba banda ƴan tsirari.



YA FARUK

Tunda khalid ya ɗaga wayar shi ya danna record saboda sheda

Har ga Allah da ya faruk yaji kalmar kalid ta ƙarshe baze iya fasalta yarda yaji ba

Daga sama kawai yaji kalmar beta tunanin hakan cikin sauƙi ba

Ta wani ɓangaren kuma beji daɗi ba sam ko dan saboda bakin duniya

Ya faruk na tsaka da wannan tunanin kiran Abba babba ya shigo mishi

Ba ɓata lokaci ya ɗaga
Kan yace komi Abba b yace " Kana ina?"

Har yayi niyar cewa yana cikin gida ya fasa,yace "ina wajen dr jamal Abba"



Jim kaɗan yayi yace " kaje gida ka ɗakko min Hajiya zahra'u da yaya safiya ku tawo da mumtaz
ma"

Da mamaki ya faruk yace "ina zan kawo su Abba?"

Kai tsaye yace "guest house ɗin Abubakar, kayi maza karka ɓata min lokaci kaima"



Huci me zafin gaske ya fesar daga bakin shi



Number dr jamal ya kira, yana ɗagawa yace "Be farka ba?"
Daga can dr jamal yayi dariya yace "ai na gaya maka se gobe kuma shi da ya buɗe idon shi"



"good" ya faruk yace, sannan ya ɗora da "kar ka bari ya gane kaine pls, in da hali ka barshi a
motar ya kwana da safen masan yarda zamuyi daga nan"



Dr jamal yace "no baza'a barshi a mota ba, tun ɗazu nasa aka shigar da shi ciki, kawai sanda
kake da buƙatar shi kayi min magana"

Daga haka sukayi sallama.



Seda ya sake ɓata time kafin ya fita ya shiga sasan mama, inda ya barsu anan ya iske su

Suna ganin shi suka zubo mai ido

Goggo safiya tace "Yace a maidata ko?"



Basar da tambayar yayi yace "Abba b yace ku shirya na kaiku yana son ganin ku"



Tafa hannu goggo safiya ta hau yi haɗe da faɗin "nasan dama tunda akayi komi a gaban
uwarka bazata rufa ba se ta fesar ni safiya, nasha zamuyi rufa rufar mu a mayar da ita ba tare
da kowa yaji ba"

Murya a dishe mama tace "Ba magana bace da zata ɓoyu ba ya safiya, muje kawai komi ze
faru da sanin ubangiji"



Ƙwale mumtaz tayi kamar me shirin hawa bori

Cike da tausayawa ya faruk yace "Tashi mana"

Hawayen da take maƙalewa suka sakko murya na rawa tace "tsoro nake ji ya faruk"



Da sauri ya runtse idon shi, be yarda ta gane halin dayake a ciki ba,
Seda ya juya yace "keep on praying, nothing will happen kinji ko?"

Taji shi ne amma bata yarda ba, har ji take a ranta inama tana da layar ɓata, ta ɓace kowa ma
ya huta
Mama ce kaɗai ta shiga ta ɗauki lulluɓi
Tukun ta fito.



Baƙi suna ta harkokin gaban su, dukda da ka kalli kowa zaka san akwai tambaya a bakin shi.



Mumtaz na gaba mama da goggo safiya baya,

Motar tayi tsit baka jin komi

Mintuna ba su fi sha biyar ba suka isa guest house ɗin Abba ƙ

Mumtaz na fitowa daga motar gaban ta ya hau lugude ganin motar Abban ta data Abba b, uncle
ƙasim, ga kuma motar Ahmad a gefe
Se ɗayar motar da bata san ko ta waye ba

Da sauri ta koma bayan goggo safiya, murya na rawa tace "Na shiga uku, nan ma mutanen aka
ƙara tara min"

Gam goggo safiya ta riƙeta, ya faruk na gaba mama na biye da shi se su daga baya suka kutsa
har cikin palon

Dukan su ciki-ciki suka yi sallama inma bakaji da kyau ba balale ka gane sunyi ba

kusan palon a cike yake,

Abba b, uncle Ƙasim, Amir(me bima TK) Ahmad, Fadil se kuma ALHAJI SULE(Mahaifin su)

kowa yayi zuguɗi ran kowa babu daɗi

Kan mama a ƙasa ta gaishe da sirikin nata, goggo safiya ma ta gaishe shi

Mumtaz bamata da courage ɗin gaisar da kowa, tunda ta lafe kusa da goggo safiya ko ɗaga
kanta bata sake ba



Waigawa Abba b yayi gaba ba Abba ƙarami a wajen
Ya ciro waya ya danna mishi kiraz gab da zata tsinke ya ɗaga

Abba babba yace "jiran ka muke"
Ko minti ɗaya ba'ayi ba suka jiyo takun saukowar shi daga sama

A fakaice mumtaz ta saci kallon Abban nata, sosai gaban ta ya faɗi ganin yarda idanun shi suka
yi jajir, sun ɗan kuma tasa alamun wanda yayi kuka dai



Yana sakkowa amma idanun shi na kan mumtaz



Yana shigowa palon yayi kan mumtaz da bugu, duka yake kaimata tako ina



Banda ihu da neman agaji babu abinda take



Da sauri ya faruk yayi kan Abba ƙ yana riƙe shi, shima ya samu tsarabar nashi dukan

Abba babba na daga zaune yake faɗin "ya isa Abubakar mana"



Alhj sule faɗi yake "Abubakar kar ka sake taɓa ta, baka ji ina maka magana"

Maganar mahaifin shi ce kawai ta dakatar da shi, yaso yayi mata lilis yarda bazata moru ba
sam.

Yana huci ya koma ya zauna.




Gyaran murya Alhj sule yayi kafin ya buɗe taron da addu'a

Nasiha ya fara yiwa mama da Abba ƙ akan muhimmancin haƙuri da kuma ɗaukar ƙaddara,
seda ya tabbatar da nasihar ta shigesu kafin yace

"Ba wani sauran dawo da maganar data wuce tunda munji komi, Faruku" ya nuno ya faruk da
hannu "kace min ka kira shi mijin mumtaz ɗin ko?"

Jinjina kai ya faruk yayi ya ciro wayar shi daga aljihu

Kunna maganar da sukayi da khalid yayi,

Tsit wajen ya sakeyi kowa najin abinda yake faɗa
A ƙarshe da ya ce NA SAKETA, har sau uku

Alhj sule yace, "Sake kiran shi ya tantance mana, saki nawa yake nufi"



Da sauri uncle Abbas yace "Baba ai bama buƙatar ƙarin bayani, sau uku ya furta"

Alhj sule yace "a kira shi dai, ta iya yuwuwa ɗaya yayi"



Badan ya faruk yaso ba ya sake dialing no ɗin khalid

Duk ringing ɗin data yi tana yi ne da faɗuwar gaban shi, bama shi kaɗai ba har uncle Abbas
dake ganin ta leƙo ta koma mishi

Gab da zata tsinke khalid ya ɗaga

Murya ƙasa-ƙasa yace "ehen, inaji?"

Seda ya faruk yayi gyaran murya kafin yace "na kira ne naji tabbacin saki nawa kayi wa
mumtaz?"



Shiru khalid yayi kamar baya kan layi, seda ya faruk yace "kana jina kuwa?"

Kai tsaye khalid yace "uku gaba ɗaya" ɗif ya tsinka wayar.



Seda wajen ya ɗau shirun mintoci kafin Abba ƙ yace "Good tunda haka kika zaɓar ma kanki,
Allah shine shedata ban rageki da komi ba amma kika tashi kika saka kanki a abu mafi ƙasƙanci
da har wanda be isa ba yake tozarta mana ahali, to wallahi ba zan zauna inuwa ɗaya dake ba,"

Da sauri mama ta ɗago kanta ta kalli Abba ƙ da mmaki da kuma tsoro, tasan mutum ne me
haƙuri amma in yyi fushi a abu yakan kafe akai.



Nan da nan uncle Abbas ya sauya fuska zuwa ta tausayi yace "Hannun ka ba ze taɓa ruɓewa
ka yanke ka yar ba, dole babu yarda zamuyi haka zamu haɗu mu rufa ma junan mu asiri
Abubakar, tunda dai babu wata idda akanta ni ina nemar wa TK auren mumtaz"



A firgice mama ta ɗago kanta, tana kallon uncle Abbas
Haka zalika ya faruk da beyi expecting jin maganar a yanzu ba

Karaf uncle ƙasim yace "Gaskiya be kamata ayi hakan ba Baba, karfa ku manta Tk na auren
sakina ƴar gidan yayan zahra'u(mama kenan)
Be kamata a haɗa mishi mata biyu ba a lokaci ɗaya kuma daɗin daɗawa ƴan'uwan juna, kunga
anyi ba'ayi ba kenan, nan mun gyara zumuncin mu can kuma mun haɗa tsiya"



Cikin hargowa uncle Abbas yace "to ai ba haramun bane ko malam"



Ɗaga musu hannu alhj sule yayi yace "Duk ya isa akira min Tukur ɗin muji ta bakin shi

Se asannan ya faruk ya sauke ajiyar zuciya, dan yasan ba yarda za'ayi a samu no ɗin Tk kuwa

Kafin ma ayi dialing no ɗin mama tace

"Baba ayi mun afuwa abani dama nayi magana"

Tacan uncle Abbas na ta aiko mata da harara ta ɓangare ɗaya kuma yana ta danna wa Tk kira
amma shiru bata shiga



Alhj sule yace "ina jin ki zahra'u"

Seda ta kalli Abba ƙ da ya zabga tagumi kanshi a ƙasa kafin tace
"ina neman alfarmar ta farko kar ayi mana wannan haɗin ko dan saboda girman zumunci, duk
da nasan ba haramun bane,

Sannan alfarma ta biyu kuma, INA NEMAN WA YARONA FARUK AUREN MUMTAZ ƊIYAR
ALHJ ABUBAKAR BISA WAKILCIN UNCLE ƊIN SA ƘASIM"



Da sauri Abba ƙ ya ɗaga kanshi ya kalli mama, idanun shi na ciccikowa da hawaye



Alhaj sule kam dariya yanayin yada mama tasa maganar ya bashi, banda kaɗa kai babu abinda
yake

Uncle ƙasim ma murnar shi na gaf da bayyana, a ranshi yake jinjinawa jarumta irin ta mama

Mumtaz kam daskarewa tayi a wajen gaban ta na dukan tara-tara
Yayin da goggo safiya ta kasa riƙe kukan ta sam

Oga ya faruk kam lumshe ido yayi yana sauraren amsar da Alhj sule ze ba mama

Haka Abba babba ma jira yake yaji me baban nasu zece

Jin shurun da yayi yasa Abba babba faɗin

"Ni ALIYU SULE NA BAMA ƊANKI FARUK AUREN ƳATA MUMTAZ



Dariya me haɗe da kuka mama ta saka

Da sauri ta janyo wayar ta tace "zan biya sadakin ɗana yanzu"

Sosai taba wasu ɗariya

Uncle ƙasim yace "zaki iya bayarwa"

A take ta saka dubu ɗari biyu cif a asusun bankin uncle ƙasim



Uncle ƙasim na faɗin "kuɗi sun shiga" uncle Abbas yayi fuuuu yafice daga palon



Alhaji sule dake kallon iyalan nashi cike da jin daɗi yace

"Tun da akwai shedu har sama da mutum shida a ɗaura shi a yanzu kawai"

Abu kamar wasa ya zama gaske a take!!!

Da ƙarfi ya Ahmad yace "Allahu akbar"

Mama da ya faruk kusan a tare suka yi sujudushshukur, banada mumtaz data kasa ɗauke
idonta ga kowa dake palon.

ALLAH KASA ANNABI YA CECE MU 🤲

LAUJE CIKIN NAƊI
NA
ZAINAB FALALU(MRS SULAIMAN)

MARUBUCIYAR



👹
MAKIRCI
KISHI DA ALJANA
WANI HANIN GA ALLAH
ƘADDARAR MU
LAUJE CIKIN NAƊI

WATTPAD@ZAINABFALALU8

Pg65-66

Saɗaf-saɗaf Abba ƙarami ya tashi daga palon yayi sama,

Tsabar sauri bema san a bibbiyu yake taka matakalar benen ba

Yana shiga ɗaki ya kalli gabas ya kabbara sallah

Nafila yayi ta godiya ga Allah,

Acikin addu'o'in da yayi yake faɗin

"ya Allah ban taɓa tsammanin wannan abu ba, ada munso hakan amma ganin waɗanda
mukeyin dan su basu da ra'ayi, haka muka danne zuciyoyin mu muka haƙura, ashe akwai shirin
da kayi mana Allah, Allah na gode maka, kacika mana burin mu nida nagartacciyar matata
alokacin da muke tunanin an mana tozarci mafi muni a rayuwar mu,

Allah ikon ka ne kuma yardar kane ya rabbi, kai kayi mana kuma mun gani, Allah ka ƙara tsira
da aminci ga shugabanmu kuma masoyin ka annabi Muhammad"

Haka Abba ƙ yayi ta wa ubangiji godiya da wannan sauyi da yayi musu a lokaci ƙanƙani.



Mama na ɗagowa daga sujjadar datayi ta rungume ya faruk da shima ɗagowar shi kenan

Jin yarda jikin shi ke rawa yasa tayi ƙasa da murya tace

"Bi a hankali yarona, kar ka kunna kanka fa"
Dariya yayi, a karo na farko da kunyar mama ta kamashi a kaf rayuwar shi

Ƙeyar shi ta mangara sannan ta yunƙura ta tashi, har gaban Alhj sule taje ta tsugunna

Gwiwowinta a ƙasa haka zalika kanta a ƙasa tace "Nagode Baba, Allah ya ƙara girma, arziki da
wadata"

Murmushi yayi yace "Amin, Allah kuma yasa ace gara da akayi, ya kaɓe sharri da fitina"

Da "amin" ta amsa, sannan ta tashi.



Uncle Abbas na fita dama uncle ƙasim yabi bayan shi da sauri ganin abinda yayi be kyauta ba,
dan kamar raini ne ace mahaifin su na zaune dan ba'ai mishi abunda yake so ba se ya tashi ya
fice

Yana fita ya iske shi zaune a mota yana waya cike da tashin hankali a fuskar shi

Uncle ƙasim na ƙarasawa wajen yayi saurin datse wayar yaci gaba da muzurai yana wani ɓata
rai



Jinjina kai kawai uncle ƙasim yayi sannan yace "Yanzu ka kyauta abinda kayi Abbas?,
Ai ko baka ɗaga ma kowa ƙafa ba ka ɗaga wa Baba da shine silar zuwan ka duniya"



Cikin hargowa uncle Abbas ya fara magana daidai kuma Abba babba da ya faruk sun sako Alhj
sule a tsakiya zasu maida shi masaukin shi suka ji yana faɗin

"Ai ɗaya bayan ɗaya zan same ku, banda toshewar basira irin taku ai wani kusancin yafi wani,
kuma komin lalacewa kusanci na da Abubakar yafi kusanci shi da Aliyu"

Cak Alhj sule ya tsaya jin wannan furuci da uncle Abbas yayi

Kafin Alhj sule ya magantu, Abba ƙarami dake bayan su yace "ka tafka babban kuskure Abbas,
akan abinda be taka kara ya karya ba kake wani tada jijiyoyin wuya haka?

To bari kaji abinda baka sani ba, wanda kake cewa kafi kusanci dani akan shi, shi ya fara shan
nonon mahaifiyar mu kafin mu musha, haihuwar shi ce kawai inna batayi ba, amma tundaga
shayarwa zuwa raino, cin kashi da fitsarin shi duk itace

Sannan kuma abinda yayi mahaifiyar Aliyu shi yayi inna in baka sani ba na sanar da kai
Kuma wallahi inda inna zataji wannan furucin daga bakin ka tabbas da zaka ga mummunan
fushin ta"



Waigowa Alhj sule yayi yace "wannan bayanin ma ya ishe shi haka Abubakar, kuma har gobe
ina alfahari da jinin Bilkisu da Zainab(Bilkisu itace mahaifiyar Abba babba, zainab kuma
mahaifiyar su Abba ƙarami)"

Shiru uncle Abbas yayi yana muzurai har su Abba suka bar wajen shi yana nan tsaye.



Cike da fargaba mumtaz tace "mama haka ake ɗaurin auren wai?"

Daga mama har goggo safiya kwashewa da dariya sukayi

Goggo safiya tace "Kinga yardar ubangiji ko?"

Gyaɗa kai mumtaz tayi hawaye na sakko mata tace "wallahi kashi na ya bushe in dai da gaske
an ɗaura min aure da ya faruk"

Sakin baki suka yi suna kallon ta, goggo safiya tayi ƙarfin halin cewa "Kamar ya mumtaz, mudai
kiyi shiru kar ki janyo mana wata lukutar masifar bamu jima da fita a wata ba"

Mama kan kafe mumtaz tayi da ido tana nazartar ta.

Tsaki Ahmad yaja kafin yace "yo ya faruk befi wancan sakaran ba so ba adadi?"

Cikin kuka mumtaz tace "To wallahi baku san halin ya faruk ba, ku rubuta ku aje kullum se ya
narkeni tunda ba dena ɗauke-ɗauken nayi ba"

Gaba ɗaya jikin kowa yayi sanyi, harda shi kanshi ya faruk ɗin da dawowar shi kenan daga kai
Alhj sule masauki yaji ma kunnen shi.



Jiki a saɓule goggo safiya tace "Allah ze rabaki da ita in sha Allah, kema ki daure ki rinƙa kai
zuciyar ki nesa dan Allah mumtaz"

Shiru mumtaz tayi tana share hawayen fuskar ta,
Amma tsoro na nan danƙare a zuciyar ta, bayan tsoro ga tsananin mamakin wai an ɗaura mata
aure da ya faruk.



Murya ƙasa-ƙasa goggo safia tace "Ni ba kowa nake ji ba se tijararriyar uwar faruk wallahi"
Tagumi mama tayi kafin tace "babban damuwa ta da kikace a gaban ta akayi komi a can gidan"
can ta nisa tace "mu bar ma Allah kawai, kuma ina fatan zuciyarta tayi sanyi ta karɓi abun da
hannu bibbiyu".



Ɗan komawa da baya ya faruk yayi, kamar zuwan shi kenan yayi sallama

Da sauri mumtaz ta juya baya tana dafe ƙirji jin yarda gaban ta ya yanke ya faɗi

Yana lura da actuons ɗinta, basarwa yayi yace "mama ku taso na maida ku gida"



Kallon shi mama tayi cike da fara'a tace "su Abban naku fa?"

Yace "Alhj ya tsaida su duka"



Tashi tayi tace "ku muje to"

Ita ta fara fita sannan goggo safiya, se Ahmad dasu fadil

Mumtaz kuma ta tsaya neman warin takalimin ta da ya shige ƙarƙashin kujera

Duk tabi ta ruɗe jin kowa ya fita se ya faruk da ya rage

Daga inda yake tsaye yana hango takalmin, Daburcewar datayi ne ya bashi mamaki

Dan ya sake tabbatar da ta ruɗen ne ya

Please Login or Register in order to submit comment