Reading LAUJE CIKIN NAƊI by ZAINAB FALALU Chapter 8 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gidan nan kamar da fushin kowa ya shigo".




Juyawa cikin ɗaki umma b tayi, wayar ta da ke kan mudubi ta ɗauka tayi dialing nombar ya
faruk

Wayar nata ringing be ɗaga ba,
Seda tayi mishi kira uku be ɗauka ba tukun ta aje wayar haɗe da faɗin "zuciyar gadon ta motsa
kenan".




Ta ɓangaren ya faruk kuwa yana shiga ɗakin shi ya shige wanka, yana wankan ne yaji kira nata
shigowa, sauri-sauri yayi ya gama wanka duk a tunanin shi calls ɗin daga asibiti ne

Yana fitowa yaga missed calls ɗin ummar har uku
Be kira ta ba seda ya gama shiryawa tsaf tukun ya maida mata da kiran



Umma b kamar daman jiran kiran nashi take ta ɗaga, kafin yace wani abu ta riga shi faɗin
"meke faruwa ne faruk?"



Cike da basarwa yace, "a ina umma?"



Sakatoo umma b tayi da baki tana sauraron rainin hankalin ɗannata, cikin ko in kula ta maida
mishi da "ohhh, hakane fa ba kai nayi niyar kira ba fa"

Murmushi ya faruk yayi jin yarda ta ƙule nan da nan, kafin ta aje wayar ta sake faɗin "ayi jinyar
kumatu lafia"

Wannan karon he can't hold it seda ya dara, duk da raɗaɗin da zuciyar shi ke mishi kuwa



Sosai ya faruk yayi nutsu cikin tunanin shi, gaba ɗaya ya rasa inda ze kama, ya kuma rasa da
wa ze tattauna akan wannan matsalar

Saƙon da'aka tura mishi a jiya ya buɗe ya sake karantawa "ya faruk kar ka bar su mama su
kaɗai"

A bayyane yace "waye wannan?"

Can kuma ƙwaƙwalwar shi ta koma ga likitan ɗazu da ya danne Abba da pilo

Gaba ɗaya kanshine ya hau hautsinawa yana juya mishi, alamar in mutum ya cika tunani.

Zumbur ya faruk ya miƙe, still a bayyane yace "wallahi AKWAI LAUJE CIKIN NAƊI, dole ma"



Sanda ya fito harabar gidan ba mutane kamar ɗazu, dan har su Abba b da uncles ɗin shi duk
basa wajen

Ahmad ua hango can wani lungu zaune shi kaɗai ya haɗa kai da gwiwa

Tsayawa sosai ya faruk yayi yana kallon shi, duk a tunanin shi wayace a hannun shi

Ya kai kusan min biyu yana kallon shi kafin ya ƙarasa kusa da shi
Sam Ahmad beji zuwan shi ba har seda ya faruk ya dafa kafaɗar shi tukun ya ɗago da sauri

Zazzaro ido ya faruk yayi ganin yarda fuskar Ahmad tayi ruɗu-tuɗu tsabar kukan da ya sha

Cike da fargaba ya faruk yace "me ya same ka Ahmad?"



Murya na rawa Ahmad yace "ina son zuwa inga su Abba, amma sam na kasa ya faruk, zuciya
ta na min ƙuna da zafi duk sanda na kusance su"

sunkuyar da kai ya faruk yayi yana faɗin "innalillahi wa'inna ilaihirraji'un" yana tunowa da abinda
mus'ab ya rubuta sak da da abinda Ahmad yace a takardar shi lokacin da ze bar gida



Gaba ɗaya jikin shi yayi mugun sanyi,

Bayan kalmar innalillahi da ya furta be sake cewa komi ba,

Miƙewa yayi tukun ya kamo hannun shi ya miƙar da shi shima

Janshi ya hau yi har bakin motar shi, se a sannan yace "shiga ka jirani"

Ya juya yana amsa call ɗin dr jamal

Yana cikin amsa call ɗin dr jamal ya fauza(babbar ƴar umma ƙarama) ta fito ɗauke da manyan
kuloli

Yana a inda yake tsaye ya buɗe mata booth ta saka na hannun ta, sannan fadil ma ya saka
nashi.

Kaf a gidan babu warda suke zama suyi magana ta fahimta kamar fauza, tasu tazo ɗaya tun
suna yara

Ya faruk na gama wayar ya dawo jikin motar inda ya fauza ke tsaye tana jiran shi

Da ɗan damuwa a fuskar ta tace "ya faruk me yayi zafi wai ɗazu har Abba b ya mareka"?

Hannu ya saka ya shafi kumatun shi kafin yace

"nima dai nayi mamaki, daga na sauya ma su Abba ƙ hospital shikenan fa" har yayi niyar sanar
da ita abinda ya faru, ɓangaren zuciyar shi ya gargaɗe shi, waskewa yayi da maganar yace
"bari in dawo dai mayi magana"

Da "to" ta amsa, ta shige ciki, shi kuma ya shige mota.



Daga shi har Ahmad ba mece ma wani komi har suka isa asibitin

Har yayi parking ya fito bega Ahmad nada niyar fitowa ba

Kallon shi ya faruk yayi yace "fito"

Jimm ya ɗanyi tukun ya fito jiki sam ba ƙwari



Booth ya buɗe ya ɗauki kulolin da ya fauza ta saka

Yana gaba Ahmad na binshi a baya

Jiyake kamar yayi ta zunduma ihu tsabar zugin da ranshi ke mishi



Amir dake zaune a ɗan harabar wajen ya hango su, da sauri ya taso yazo ya karɓi kular hannun
shi yayi ciki da su

Amir na shigewa Ahmad yayi saurin faɗin "ya faruk ɗan riƙe min, fitsari nake ji"

Karɓa yayi tukun yaci gaba da tafiya zuwa ciki.



Ba wani fitsari da Ahmad keji, kawai yakasa riƙe kanshi ne sam shiyasa yayi haka

Ya faruk na shigewa, Ahmad ya zagaya ta bayan windows ɗin ɗakin,

Laɓewa yayi ya rinƙa leƙen iyayen nashi dake zaune bama zaka taɓa cewa sunyi accident ɗazu
ba, bama kamar mama ita ko ƙwarzane babu a jikin ta, Abban ma ƴar buguwace kawai a kafaɗa

Cike da so da ƙauna yake kallon iyayen nashi,

Abinda be sani ba tun da ya leƙo na farko mama taji ajikin ta ana kallon ta

A wayence ta kalli windon, ganin Ahmad ne ke leƙen su hakan ba ƙaramin karyar mata da
zuciya yayi ba.
Kusa da mama ya faruk ya zauna, cike da kulawa yace "mamana ya jikin?"

Murmushi mama tayi kafin tace "naji ƙarfi sosai yanzu, mumtaz ce har yanzu tun baccin daka
tafi ka barta tanayi bata farka ba, Allah yasa dai kan yarinyar nan be taɓu ba"

Da sauri goggo safiya tace "ah tuf da baƙin yawu, in sha Allah garas zata miƙe kamar yarda
kuka miƙe kuma"

Kowa seda ya murmusa wa yarda tayi maganar

Tsam ta taso daga inda take ta matso kusa da ya faruk, ƙasa tayi da murya tace

"waɗan nan masu kakin fa faruk?"

Kai tsaye yace "saboda tsaron lafiyar su na aje su goggo"

Taɓe baki tayi kafin tace "kamin daidai faruk, ni kaina ban gane ma wasu abunuwan ba wallahi,
tunda na iso garin nan na fara gane-gane masu ban tsoro wallahi"

Tsit wajen yayi jin abinda goggo safiya ke faɗi

Cike da son jin me tagani ya faruk ya ce "me kika gani ne goggo?"

Shiru tayi bata sake tanka kowa ba, daga baya ma miƙewa tsam tayi ta nufi gadon mumtaz
dake mutsu mutsu.



Se asannan mama tace ma faruk "In yasan ba ze shigo ba mene na zuwa yana leƙen mu?"

Da sauri ya faruk ya kalli window ido biyu suka yi da Ahmad dake laɓe

Da Ahmad yaga sun ganshi yayi saurin barin wajen yana jin azalzala acikin ranshi

Murya ƙasa-ƙasa ya faruk yace "mama akwai matsala babba wallahi, ban san daga ina take ba,
amma kowa ya kalli yarda abubuwan nan ke tafiya zaka san akwai wani abu a ƙasa,"



Murmushi me cin rai tayi sannan tace "Tabbas AKWAI LAUJE CIKIN NAƊI FARUK, Amma mubi
komi a hankali mu dage da addu'a Allah ze warware mana komi"



Kafin ya faruk ya sake magana goggo safiya ta dawo tace "faruk zo ka kamamin mumtaz in
saka ta fitsari kar ta jiƙe shimfiɗar"



Dururu yayi, cikin ƙinƙina yace "ni kuma?, ah bari a kira nurse tazo ta tayaki dai"



Goggo safiya tace "kai bana son shashanci, yo kafin nas ɗin tazo ai ta gama fitsare wajen"



Murmushi mama tayi tace "muje na kama miki ita yaya safiya"

suna shiga yayi wuf ya bar wajen ya nufi office ɗin dr jamal.




*******KHALID

Yinin ranar yayi shine cikin rashin sukunin maganar da sakina ta gaya mishi game da mumtaz

wani ɓangaren na zuciyar shi yaso ya yarda, amma wani sashin ya gargaɗe shi da kar ya
kuskura yayi sake na dafe da mumtaz

Da ya zauna yayi tunani me kyau, yayi la'akari da irin yanayin rayuwar da akeyi a yanzu,
hassada, baƙin ciki, da zallar zagon ƙasa da yayi ma al'ummma katutu yasa ya dawo daga
rakiyar maganar sakina

Dan tabbas a rayuwar nan wanda kafi kusanci da shi se ya cuceka, ko kuma ya nemi ganin
bayan ka, kuma haka kurum siddan ragadan baka tare mishi komi ba, zallar hassada da
tsananin baƙin ciki ya ginu a tsakani.



Bayan wannan dogon tunanin da yayi ne yasamu sukuni a cikin ranshi

Beyi fushi ko zuciya ba ya sake kiran sakina, da ƙyar da ɗan wulaƙanci ya samu ta gaya mishi
asibitin da aka maida su



Aikuwa beyi ƙasa a gwiwa ba yaja abokin shi kamal suka nufi hospital ɗin

Sanda isa an shiga sallar isha, seda suka tsaya a masallaci sukayi kafin suka fito

Suna fitowa suka sake haɗuwa da uncle Abbas shima da fitowar shi kenan, cike da girmamawa
su khalid suka sake gaishe shi da tambayar masu jiki

Uncle Abbas da kan shi yayi musu jagora zuwa ciki

Inda Allah ya temakesu kenan, dan jami'an tsaron wajen bazasu taɓa barin su shiga ba saboda
tsaro

Direct ya wuce da su ciki

Abba ƙ kam be sheda shi ba, duk da yayi mishi bayanin a cmpnyn shi yake aiki

Ganin basu ga mumtaz a wajen ba yasa shi tambayar uncle Abbas "an sallami mumtaz ne sir?"



Uncle Abbas yace "ohh, gadon ta na ciki, ai tafisu jin jiki kam, ku shiga"



Suna shiga suka isketa zaune goggo safiya ta tasata a gaba tana cin abinci

Kalid na yin sallama mumtaz ta ɗago kanta da sauri, a take agogon data ɗauka a cikin motar shi
ya faɗo mata, da sauri ta sunkuyar da kai ganin yarda ya kafe ta da kallo

Murya ciki-ciki mumtaz tace "goggo bani hijabina pls"

Baki sake goggo safiya tace "Ah lallai kin fara dawowa hayyacin ki ƴannan da har kike neman
hijabi"

Ganin ba bata hijabin zatayi ba yasa taja ɗankwalin goggo safiyan dake ajiye a gefe ta yafa a
jikin ta



Hannu bibbiyu goggo safiya ta karɓi su kalid jin bayanin da kamal yayi mata

Nan suka zauna suna ta fira kamar irin sun saba ɗinnan

Ita kam komawa tayi ma tayi kwanciyar ta, sedai kaf firar da suke tana jin su.



Kiran da uncle ƙasim yayi mata ne yasa ta tashi a wajen

kamar dama jira kalid yake ta fita, matsawa yayi kusa da mumtaz data juya baya yace

"ya jikin naki?"
Ƙin amsawa tayi, in da ta waiga fuskar ta ya koma, ido huɗu suka yi
Da sauri ta rufe nata tana jumɓuro baki gaba

Murmushi kalid yayi kafin yace "nagode ma Allah da ya takaita abin nan a iya haka mumtaz,
yanzu kam zan iya bacci me daɗi tunda na ganki na kuma ga yanayin jikin ki"

"hmmm" kawai take cewa

Cike da damuwa yace "ina wayar ki?"

Se a sannan tayi magana tace "kamar an sace fa"

Yace "toh bakomai, gobe in zanzo zan tawo miki da wata, amma yanzu ba wani nonba da zan
same ki kafin safe?"

Girgiɗa kai kawai tayi,
Daidai nan goggo safiya ta dawo

Basu sake wani jimawa ba sukayi mata sallama, bayan sun aje ma goggo safiya 20k agaban
ta.



Sun fita kenan ya faruk ya shigo hannun shi ɗauke da takarda, kusa da Abba ya zauna, miƙa
mishi takardar yayi kafin yace "dan dai ka matsa ne Abba, amma da kun zauna kun sake
warwarewa tukun"

Cike da kulawa Abba yace "gara mu tafi gida tunda Allah yasa ba wani matsala, kuma na gaji
da tambaye tambayen da ake min akan waɗan nan ƴan sandan da ka zuba, kuma hankalina
baze taɓa kwanciya ba a nan"



"Hakane Abba, amma waze zauna da mumtaz?"

Se a sannan mama tace "Ya safiya zata zauna da ita mun gama wannan maganar, gwara muje
gida a sauƙaƙa ma jama'a dake ta sintirin zuwa"

Ba yarda ya iya, haka suka tattara suka koma gida aka bar mumtaz da goggo safia a asibitin.




****gaskiya ya kamata kije ki gaishe ta mami, wallahi taji jiki sosai
Cike da zolaya mami tace "ohh khalid bako kunya?, in na dawo daga tafiyar da zanyi gobe
zanje in gaishe ta,
Amma dai zuwa gobe ka samu binta da azima suje su dubata(binta da azima ƙannen mamin
ne)
Se su sake tabbatarwa da gaske kake



Cike da jin daɗi khalid yace "yauwa mami na, kin kawo shawara me kyau wlh"



Haka suka yi ta firar su irin na uwa da ɗa, sun jima suna fira kafin mami ta sako maganar abun
hannun ta data nema ta rasa "Wai khalid har yanzu shiru ba wani labari game da abun hannun
nan?"



"Mami, tunda kikaji har yanzu ba wanda ya kirani to wlh ba satar shi akayi ba, maybe ya faɗa
wani wajen ne, ki sake dubawa dai"

Taɓe baki mamin ta kafin tace "ko ɗazu seda na sake dubawa wallahi, ɓatan shi yayi min ciwo
sosai"

Da sauri khalid yace "mami ba akwai CCTV a office ɗin ba?"

Mami tace "akwai mana"

yace "ki duba to, ƙila kiga inda ya faɗa"

Da ɗan murna mami tace "aikuwa danaji daɗi, sam na mance da wata CCTV a office ɗin'

ya ɗan jima a wajen mamin kafin yayi mata sallama ya wuce ɗakin shi.




*****wajajen ƙarfe biyu da rabi na dare, ya faruk na kwance sam bacci yaƙi zuwar mishi ya rasa
mafita ga wannan matsalar da ke neman fin ƙarfin su
Yaji ana ƙwanƙwasa ƙofar shi kaɗan kaɗan

Nutsuwa yayi yaji da gaske nan bugawar ake

Seda ya tabbatar da bugawan ake, da sauri ya zira riga haɗe da kallon agogon wayar shi

lokacin da ya gani ne yasa shi jin faɗuwar gaba, haka ya dake ya matsa jikin ƙofar, a dake yace
"waye?"



Daga can akace "MUS'AB".



NAGODE DA CALLS ALLAH YA BAR ZUMUNCI ❤️
ALLAH KASA ANNABI YA CECE MU 🤲
SHARE PLS.

LAUJE CIKIN NAƊI

NA
ZAINAB FALALU(MRS SULAIMAN)

MARUBUCIYAR



👹
MAKIRCI
KISHI DA ALJANA
WANI HANIN GA ALLAH
ƘADDARAR MU
LAUJE CIKIN NAƊI

WATTPAD@ZAINABFALALU8

Pg 41-42

Babu inda jikin ya faruk baya rawa jin mugayen maganganun da mus'ab ke bashi labari,

Cikin kuka mus'ab yace "shiyasa na yanke shawarar nisantar su gaba ɗaya, dan muddin ina
kusa da su komi ze iya lalacewa".



Sam ya faruk ya kasa magana, ajiyar zuciya kawai yake saukewa yana tuna yarda uncle Abbas
ke gaggaya mishi magana akan sauya ma su Abba hospital da yayi



Da ƙyar maganar ya faruk ke fita yace yace

"Mus'ab zaka iya tunawa, bayan shi se wa?, baze taɓa zama cewa shi kaɗai ne ke wannan
aika-aikar ba"



Kan mus'ab a ƙasa, yaƙi yarda sam ya ɗago kanshi, ga alamar yana son cewa wani abu, amma
sam yaƙi ya furta



A zuciye ya faruk ya finciko shi, murya a murmurɗe yace "ka gaya min mus'ab, kar kaji
shakkata, se kuma wa ka gani?"



Ƙin cewa komi mus'ab yayi banda haɗiyar zuciya da yake ta faman yi



Sun jima a haka, har wajen asuba tukun mus'ab yace

"Zan tafi, tsayawa ta babbar matsala ce anan ya faruk"

Ya faruk be hana shi ba, sema dafa kafaɗar shi da yayi yace

"Ko shine silar zama ƙarshen numfashi na zan kare ahalin Abba ƙarami in sha Allah"



Mus'ab be seke minti ɗaya a wajen shi ba ya fice.




BAYAN SATI ƊAYA

Sosai jikin mumtaz yayi sauƙi dan suna saka ran sallama a yau ko gobe

A ɗan zaman asibitin da tayi wata soyayya suke zubawa ita da khalid da tuni yayi watsi da
maganar sakina

Ɗari bisa ɗari goggo safiya na goyon bayan hakan, itama ba ƙaramin son haɗin nasu take ba

Zuwan aunties ɗin shi biyu haɗe da shatara na arziki suna zuwa dubata



Wasa wasa, wani lokacin kafin khalid ya wuce asibitin se ya fara zuwa gaishe da mama har
gida tukun yake wucewa can
Mama tayi murna, ko ba komi ta yaba da hankalin shi, balle ma maganar da sukayi da Abba ƙ
akan aurar da su na nan maƙale a ranta, dan ma wannan tsautsayin da ya faru ne akayi shiru
da maganar, yanzu kam ta fara samun kwanciyar hankali.



Tafiyar khalid kenan ya faruk ya tura ƙofar ɗakin ya shiga

Da fara'a sosai goggo safiya ta tarbe shi, haɗe da faɗin

"Oh kana nan faruk? tunda aka sallami iyayen ka mu kuma ka ɗauke mana ƙafa"



Ɗan murmushi ya saki kafin yace "nima banji daɗi bane goggo, amma Alhamdulillah"



Ta gefen ido mumtaz ke kallon shi, tabbas ko be ce baya jin daɗi ba zaka hango hakan, ramar
da yayi ta nuna ƙarara a fuskar shi



Jajanta mishi goggo safiya tayi kafin tace "To ga kayan marmari a miƙo maka?"



Kallon tulin ledojin gaban su yayi yace "wannan shirgin fa"?



Cike da jin daɗi goggo safiya tace

"Hmm kaima dai ka faɗa, yarone mara ƙyashi wallahi, kullum in zezo baya zuwa hannu bibbiyu
se kaga ya riƙo wani abun yazo da shi, Allah dai yasa hat cikin gida ba maƙeƙe bane ba"



Idon ya faruk na kan wayar shi yace "wa kenan goggo?"



Baki buɗe, tace "khalid sunan shi, kuma wallahi baka ga yarda yake kula da mumtaz ba, abin
har birgeni yake"



A hankali ya faruk ke furta sunan khalid, be sake cewa komi ba yaci gaba da danne dannen shi

jin yayi shiru yasa goggo safiya tashi ta ɗauki komi bibbiyu ta aza akan plate ta tafi wanko mishi

Tana fita ya kalli mumtaz data juya baya yace
"Tunda har kin samu damar yin soyayya kina jinya kin warke kenan?, duk da na lura bayan
halayyar ki har rashin gaisuwa ma kin iya"

Bata ce komi ba, bakuma ta gaishe shin ba



Suna a haka goggo safiya ta dawo, kusa da shi ta aje plate ɗin sannan ta kabbara sallar isha'i

Ko kallon plate ɗin beyi ba ya fice daga ɗakin



Direct office ɗin dr jamal ya nufa, ba wani ɓata lokaci ya karɓi takardar sallamar da yasa akayi
ta dole.



Ya jima a cikin mota yana amsa wayar mus'ab kafin ya koma ɗakin

Goggo safiya na ganin shi tace "au nasha ka wuce ne ba ko sallama"



Kujera ya ja ya zauna tukun yace "a'a, nayi waya ne, ku haɗa kaya ku same ni a mota an
sallame ku"



Sakato goggo safiya tayi tana kallon shi bako ƙiftawa, can tace "yo haka ake sallama da dare
tsaka mutum ya gama sadaƙarwa kwana zeyi?"

Murmushi ya faruk yayi kafin yace "To mene abun ɓata rai goggo, ai komin daɗin asibiti gida yafi
shi ko? tunda naga kamar daɗin zama kuke ji" ya ƙarashe maganar yana kallon mumtaz ta
gefen ido



Be jira amsarta ba ya juya ya fice

Aikuwa suna haɗa kaya goggo safiya na mita, wai khalid zezo yaga basa nan

Mumtaz da se yanzu tayi magana tace "Rabu da shi goggo, zan kira shi a waya yanzu ma"



Saboda yawan kayan su seda goggo safiya ta kira masu goge goge suka taya su ɗauka
Suna zuwa wajen da yayi parking ya fito, ɗaya bayan ɗaya yake kallon kayan da suka jido

Beyi wata-wata ba yace wa warda ta tayasu ɗakko kayan "kwashi wannan da wannan ki tafi
dasu"

Nan tayi ta zabga godiya, goggo safiya na gefe tana zuba ƙorafi.

ƙofar baya ya buɗe mata ta shiga, sannan ya zagaya shima ya shiga

Mumtaz na tsaye ita bata shiga ba, sanin waye ya faruk yasa ya zagaya ta shiga gaba



Suna tafe yana ayyana abubuwa da yawa a ranshi, bin diddigin uncle Abbas da yake har yanzu
ya kasa gane komi, gani yake kamar ma incle Abbas ɗin ya gane yana bin diddigin shi



Dai dai wajen shagon da ake seda fura ya tsaya, sanin goggo safiya ta shaƙa da yawa yasa
yace "Bari na karɓo miki fura goggo"

be jira cewar ta ba ya fice a motar ya barsu a cikin raɓa.



Tunda mumtaz ta shiga motar idon ta ya sauka ga zoben azurfar da ya faruk ya aje domin ya
gwadata ya gani se kuma bandir ɗin ƴan dubu dubu guda uku dake gefen zoben



Ba wani dogon tunani mumtaz ta saka hannu ta ɗauke zoben nan, sannan duk a bandir ɗaya ta
zari goma goma a ciki ta saƙe a hijabin ta



Be daɗe ba ya dawo, kallo ɗaya yayi ma wajen ya ga babu, abunda bata sani ba saboda ya
gwada yaga ko ta dena halin ne yasa ya ajiye

Bece komi ba yashiga yaja suka tafi.



Goggo safiya na sauka ya waiga side ɗin mumtaz dake saurin sauka itama, fuska a ɗaure yace
"bani abinda kika ɗauka a nan"!



Duru duru tayi tana wani kauce-kauce, kunya da tsananin nadama na baibayeta

Gani kawai yayi ta sauke kai ƙasa ta fashe da kuka haɗe da ciro zoben da kuma kuɗin
Duk da yarda ranshi ke tafasa ganin yarda tayi yayi mugun ɗaga mishi hankali da kuma
mamaki,

Kasa ce mata komi yyi, da yaga bata da shirin sauka a motar yace "you can go, Allah ya shirye
ki ya kuma rufa miki asiri"

Jin yarda yayi maganar cikin sanyin rai da batayi zato ba yasa ta ɗago fuska da sauri tana
kallon shi

Kashe motar yayi, ya fice ya barta.



Seda ya ɓace wa ganin ta tukun ta fito bayan ta share hawayen ta tas, tayi cikin sasan su inda
take jin hayaniyar mutane sosai.




****Da asuba bayan sun dawo daga massallaci duk suna tsaye a harabar gidan Abba babba
yace
"Inajin zuwa gobe duka yaran su aiko da samarin nasu se asan abun yi ko?"

Amsawa sukayi da "hakane" Tukun suka ɗora da firarrakin su na ƴan'uwa

Sun ɗan jima sosai kafin kowa ya nufi sasan shi.



Uncle Abbas na shiga nashi part ɗin ya iske duka nashi ahalin a dinning suna breakfast

Amir ne ya fara gaishe shi kafin Najwa da Tk

Shima kujera ya ja ya zauna,

Mummy da kanta ta tashi ta fara haɗa mishi tea, tana haɗawa take faɗin

"Yaudai firar nan ta jima"

Seda ya kai mug ɗin bakin shi kafin yace

"Aikam" yana tsaka da cin abincin ya kirayi sunan najwa da ke gaf da barin dining ɗin
Kanta a ƙasa tace "na'am daddy"

Kai tsaye yace "ki sanar ma wanda ke zuwa wajen ki yazo gobe muna son ganin shi"

Duk da tasan da zancen amma hakan be hanata jin faɗuwar gaba ba, jiki a mace tace "to
daddy" haɗe da barin wajen.



Cike da jin daɗi mummy tace
"abun ya taso kenan"

Yace "ya taso fa, in sunyi daidai da ra'ayin mu ba za''a ɗauki wani dogon lokaci ba, kin san
bama saka biki da nisa"

Cike da jin daɗi mummy tace "hakane, Allah ya tabbatar mana da alkairi"



Uncle Abbas na gama cin abinci ya tashi ya nufi palon shi, kasancewar asabar ce ba ranar aiki
bace

Tsum ya Tk ya miƙe shima yabi bayan sa

Uncle Abbas na zama Tk ya shigo ya zauna kusa da uban nashi



Fuska ba alamun rahma Ya Tk yace "Daddy, na kasa gane me kake nufi gaskiya, na gaya maka
nifa ina son yarinyar nan, nace zanyi magana ka hanani da niyar kai zaka nemar min auren ta,
kuma ga ƙishin-ƙishin ɗin da nake ji na daban, nifa gaskiya an saka ni a duhu"



Murmushi uncle Abbas yayi tukun yace "Daɗi na da kai gajen haƙuri, akwai damar da nake jira
ne TK, kuma nafika sanin muhimmancin mumtaz a gareka, just trust ur dad, haƙƙata ta kusan
cimma ruwa soon!!!

Kamar wasu sa'anni haka suka tafa suna kwashewa da dariya.

Mus'ab na gama recording maganar yayi saving, har yayi niyar tura ma ya faruk ya fasa, ya
koma yayi kwanciyar shi haɗe da rufe fuskar shi.



😊
Sorry for the late update, kunsan jiki da jini

ALLAH KASA ANNABI YA CECE MU 🤲
SHARE PLS.
LAUJE CIKIN NAƊI

NA
ZAINAB FALALU(MRS SULAIMAN)

MARUBUCIYAR



👹
MAKIRCI
KISHI DA ALJANA
WANI HANIN GA ALLAH
ƘADDARAR MU
LAUJE CIKIN NAƊI

WATTPAD@ZAINABFALALU8

Pg43-44

Da yamma lis, yau baƙi masu zuwa gaisuwar sallah da kuma dubiya duk sun ɗauke ƙafa

Gidan an samu sauki mutane sosai

Mama da goggo safiya na zaune a palon ƙasa suna firar kayan sha tara na arziki da aka kawo
na saka ranar hafsa da bilkisu da kuma najwa

Goggo safiya tace "naji Ƙassim yace yau da daddare za'a kawo na Amal itama"



Mama tace "hakan Abban su ke gaya min kafin ya fita"



Can goggo safiya ta sake cewa "mumtaz fa? ko har yanzu ta kasa tsaida zuciyar ta akan yaron
kirki nan"



Gyara zama mama tayi kafin tace "a dai gaban ki jiya muka titsiyeta ya safiya, na kasa gane
kan yarinyar nan sam, ɗazu da safe da na sake mata magana ma fashe min da kuka tayi,
Na rasa yarda zanyi ni kam"



Da mamaki goggo safiya ta sake cewa "kuma fa naga kamar tana son yaron, nikam wallahi na
yaba da hankalin shi sosai, duk yafi min samarin sauran kamala da nutsuwa"
Ta waiga wajen da mumtaz ɗin ke zaune ɗazu taga bata nan

Altine ta yafito tace "shiga kira min mumtaz"




Altine na shiga ɗakin ta iske mumtaz tsaye gaban mudubi tana saka kwalli

Ta cikin mudubin take kallon ta, fuska a ɗaure tace "lafia?"

"ana kira" kawai tace ta juya



A fili mumtaz tace "munafuka kwanan ki sun kusa ƙarewa a cikin gidan nan, ki gama raɓe-raɓen
ki"

Seda ta gama tas abunda take tukun ta fito

Wannan karon harda umma ƙarama a palon

Kusa da mama ta zauna haɗe da faɗin "gani hajiya mama"
Yarda tayi maganar ya basu dariya, a da mumtaz akwai iya shege sosai, amma tunda ɗabi'ar
sarface-sarface ta kamata ta sauya gaba ɗaya.



Dundu mama ta sakar mata kafin tace "seda kika gama shanya mutane tukun zaki

Please Login or Register in order to submit comment