Reading LAUJE CIKIN NAƊI by ZAINAB FALALU Chapter 2 | TKNovels


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

bata jiyo ta ba, dan ita ta mammake
mutum ba wahala yake mata ba



Macece me son iyawa da kuma kamewa, bata ɗaukar raini balle shashanci, kuma bata fiya
shiga sabgar mutane ba, in abu be shafe ta ba da wahala kuga ta saka baki, amma tana da
mugun kishin zamantakewa, se ka zauna da ita sosai zaka fahimci hakan.
Mama, aunty, umma ƙarama da mummy suma suka kama gaban su, kafin lokacin sallar isha
yayi, ko wacce tayi part ɗin ta suka bar iyayen maza kawai a babban palon da tun bayan gama
cin abincin suka koma cikin palon.




Cike da kulawa Abba babba ya kalli Abba ƙarami yace



"Ina lura da yanayin ka se streaching baya kake, badai ciwon bayan bane ya dawo?"



Murmushi Abba ƙarami yayi, yana lumshe idanun shi dake nuna tsabar gajiya tukun yace



"Ɗazun nan na fara jin alamun shi dai, amma ina tunanin gajiya ce, in nayi bacci zan warware in
sha Allah"

Da "Amin suka amsa dukan su



Seda suka gabatar da sallar isha'i suka ɗora da asham kafin kowa ya kama gaban shi.




Tunda ya faruƙ ya shiga ɗaki yaƙi cire riga saboda yana jiran Mumtaz



Ɗabi'ar shi ce sam baya son zama da riga, komin sanyi kuwa



Haka ya zauna tun yana kallon agogo har ya gaji da jiran ta

Se a lokacin ya fara recalling befa ganta a wajen salla ba



Ƙwata yaja tukun ya tashi ya cire rigar shi,

List ɗin da Abba ƙarami ya bashi ɗazu ya janyo ya hau duddubawa yana fitar da wanda ya
dace ya fitar ya bar wanda ya dace ya bari,
Ba shine ya gama ba, se wajen sha biyu saura, tukun ya kishingiɗa.




Tun da mama ta koma part ɗinta ta hau Mumtaz da faɗan rashin fitar ta salla da kuma tashi
data yi bata tsaya an gyara wajen cin abincin da ita ba




Marairaice murya Mumtaz tayi sannan tace



"kaina ne ke fa ciwo shiyasa ban fita ba mama"



Taɓe baki mama tayi, tace

"Da dai ban san halin ki ba, in bakiyi sharar masallaci ba ai kya yi ta kasuwa" ta juya tayi
ficewar zuwa palon Abbah ƙarami da shima shigowar shi kenan.




Direct kitchen ɗin palon ta nufa, butar shayi ta ɗora akan gas bayan ta zuba kayan ƙamshi da
ruwa

Seda ya dahu tukun ta juye a ƙaramin flask golden colour tukun ta ɗora a tray ɗan madedeci
bayan ta ɗora ƙananun cups biyu da kuma glass ɗin sugar akai, tukun ta fice zuwa palon Abba
ƙarami



Zaune yake ya kafa kai da gwiwa mama ta shiga, tana ganin a yanayin da yake seda gaban ta
ya faɗi

Jiki a sanyaye ta ƙarasa ciki, ajiye tray ɗin hannun ta tayi sannan ta zauna a kusa da shi

Jiki a sanyaye ta ɗora hannun ta a kafaɗar shi, bata ce komi ba se ɗan shafa bayan shi data ke
alamar rarrashi.




A jejjere Abba ƙarami ke sauke ajiyar zuciya, sun ɗan jima a haka kafin ya ɗago idanun shi da
suka yi jajir



Kafin yace komi mama ta rigashi faɗin



"Dukkan tsanani yana tare da sauƙi yallaɓai, tunda har warcan shawarar da na baka ba zatayi
aiki ba, dole mu rungumi haƙuri sannan mu ƙara ƙaimi wajen kaima Allah kukan mu, shine
yasan abunda muka sani da wanda bamu sani ba"



Murya a sanyaye Abbah ƙarami yace



"Maganar ki haka take, amma can ƙasan raina ina jin wani mugun yanayin da ke ƙoƙarin taɓa
min zuciya, faɗuwar gaban da nake ji sam bata barina na aiwatar da komi cikin salama, amma
ba komi ƙila dalilin hawan jinin nan ne yasa nake jin hakan" ya ƙarasa maganar yana ƙirƙirar
murmushi.



A hankali mama tace

"shima ze iya sawa"



Flask ɗin shayin ta janyo ta zuba mishi.




Suna a haka Ahmad da mus'ab suka shigo a tare bakin su ɗauke da sallama



Akan laɓɓa Abba ƙarami ya amsa musu yana jiran yaji me kuma suka zo da shi.



"Mus'ab ne ya fara magana cikin inda inda



"Abbah, dama akan maganar tafiya umarar ne, mun gama shiryawa ni da Ahmad gobe da
yamma zamu wuce"



Mama na gefe ta zuba musu idanu da mamaki sosai a fuskar ta
Abba kuwa murmushin da yafi kuka ciwo yayi, yasan ze iya jin abunda yafi wannan ba daga
bakin su, wannan zuwan ma da suka yi yasan ba da son ransu suka zo ba



Duk da haka a matsayin shi na uba be kamata yayi musu shiru ba akan muguwar ɗabi'ar rashin
shawarar da sam basayi da shi ko da mahaifiyar su ba



Gyaran murya Abba ƙarami yayi yana ajiye mug ɗin hannun shi a kan table ɗin gaban shi



Ɗaya bayan ɗaya yake kallon Ahmad da mus'ab da ke zaune kansu a ƙasa

Ɓacin ranshi keson fitowa fili, amma ya danne ya kalle su ya ce



"Yanzu kun kyauta akan wannn halin naku?" be jira cewar su ba ya ɗora da



"A matsayina na mahaifin ku ai naci arizikin a sanar dani kafin ku aiwatar da komi zakuyi,
dukkan ku ina lura da sabbin halayen da kuka tsiro da su,

So har kunyi arzikin da zaku iya biyan ummara, kuma har kk biya se zaku tafi muke da arzikin ji
ko?"



Kansu a ƙasa suka haɗa baki wajen faɗin

"a'a Abbah"

Murmushi ya sake yi sannan yace

"Yanzu nayi asarar kuɗin da na biya harda ku kenan?"



caraf mus'ab yace

"zaka iya sawa ayi refunding maka ai Abbah, mu mun riga da mun gama shiri"



Shiru yayi ganin mama na gaf da fashewa da kuka a gaban su yasa Abbah ƙarami saurin faɗin
"ku tashi kuje, Allah ya kaiku lafia"



Kamar wa ɗanda suke kan ƙaya haka suka tashi har suna gwaren fita.



Aikuwa suna fita hawayen mama suka ɓalle, sam ta kasa riƙe su tsabar yarda zuciyar ta ke
mata zafi



Abba bece komi ba, ya kamota ya rungume ta tsam a jikin shi yana shafa bayan ta alamar
rarrashi.



SHARE PLS

ALLAH KASA ANNABI YA CECE MU 🤲
WALLAHI YAWAN SHARHIN KU YAWAN SAMUN UPDATE AKAI-AKAI 😎
LAUJE CIKIN NAƊI

NA
ZAINAB FALALU(MRS SULAIMAN)

MARUBUCIYAR



👹
MAKIRCI
KISHI DA ALJANA
WANI HANIN GA ALLAH
ƘADDARAR MU
LAUJE CIKIN NAƊI

WATTPAD@ZAINABFALALU8

Pg5

Seda yaji mama na sauke ajiyar zuciya akai-akai tukun ya buɗe baki a hankali kuma cike da
rarrashi yace
"Kiyi haƙuri ina a kan umarnin hajiya ne, abu ɗaya na sani shine komi yana da lokaci"



Kasa cewa komi mama tayi, sema ɗan zamewa data yi anan kan kujerar ta kwanta haɗe da
lumshe idanun ta.

shayin da Abba ƙ be ƙarashe sha ba kenan, shiru yayi yana ci gaba da tunane tunanen da suka
aure shi tun shekarun baya.




WASHE GARI

Abba ƙ na zaune a ɗan madedecin palon shi na sama inda ba kowa ke shigar shi ba



Hankalin shi da na mama ya tafi ga tafsirin da akeyi a sunnah tv,

Baka jin motsin komi sena tv, se kuma air con da take aiki



Kusan 1hr suna sauraron tafsirin kafin a gama



Sama-sama suke ɗan taɓa hira, can Abba ƙ yace



"Miƙo min warcan yawar"



Tashi mama tayi ta ɗakko mishi duka wayoyin a inda ya aje ta kawo mishi



Yana karɓa kai tsaye dialing no ɗin ya faruk yayi.




Fitowar ya faruk daga wanka kenan yaji ringing ɗin wayar shi

Ganin sunan Abba ƙ a kan screen ɗin wayar yana yawo yasa yayi saurin ɗagawa ya kara a
kunne haɗe da sallama
Abba ƙ najin ya ɗaga yace

"In baka komi kazo ka same ni a palona"



Cike da girmamawa ya faruk yace

"To Abba"



Yanayin zafin da ake tsugawa yasa ko mai be shafa ba,

roll on kawai ya shafa se body spray, tukun ya saka kayan shi ya fice zuwa kiran da Abba ƙ yayi
mishi




Tunda ya fito daga ɓangaren su na samarin gidan Hafsata ta hangoshi ta windown ɗakin mama



Kamar zata kifa wajen saurin juya tace

"Umma, zo ki gani"



Fuska a ɗaure Umma babba tace

"me zan gani?"

Da sauri hafsat ta sake cewa "ze shige wallahi"




Da ɗan sauri umma babba ta ƙaraso jikin windown itama, akan idon ta ya faruk ya ƙarashe
shigewa part ɗin Abba ƙ



Ƙwata tayi ta koma ta zauna, fuskar ta ba yabo ba fallasa tace

"Bani waya ta hafsat"
Juyawa hafsat tayi ta ɗakko mata wayar, har ta miƙa mata ta tsaya tace



"karki kira shi umma"



Kallon ta umma Babba tayi tukun tace

"wa kenan?



Dariya Hafsat tayi, wani lokacin halin umma babba mamaki yake bata, wani lokacin kuma dariya



Kafe tan da ido da umma b tayi yasa tace



"na sha ya faruk zaki kira ai"



Tsaki umma b tayi taci gaba da danna wayar hannun ta.




Mumtaz na kwance taƙi tashi tayi komi wai azumin yau na bata wahala taji sallamar ya faruk



A guje Mumtaz ta miƙe tayi hanyar ɗakin su, sam ta mance da yunwar data ce tana ji



Tana shiga ta banko ƙofar da ƙarfi ta murɗa key tana maida numfashi da ƙyar



Gaba ɗaya seda hankalin su sakina ya dawo kanta, har altine dake kitchen seda ta leƙo jin
ƙarar ƙofar da aka buga




Karkaɗa kai ya faruk yayi, can ƙasan zuciyar shi yace



"Zanyi maganin ki, da gangan kenan kika ƙi zuwa kiran da nayi miki"
Sama-sama ya amsa gaisuwar su sakina, tukun ya nufi stairs ɗin da ze sada shi da palon Abba
ƙ.




Ya jima sosai a wajen Abba ƙ kafin ya sakko, da ka ganshi kasan ranshi a mugun ɓace yake,
amma in bakai mishi farin saniba ba lale ka fahimci hakan ba.



yana shiga ɗaki ko zama beyi ba, wayar shi ya ɗauka da niyar kiran Ahmad

Missed calls ɗin Umma b ya gani kusan biyar,

Saka wayar yayi a aljihu ya juya ya sake fita zuwa part ɗin Umma b.



Har bedroom ɗinta ya same ta, tana zaune riƙe da carbi a hannun ta tana ja yayi sallama ya
shiga



Zama yayi kan kujerar dake kallon gadon ta, Hafsat na zaune akan 1 seater dake kusa da
window tana duba handout ɗinta, kai kace gaba ɗaya hankalin ta na ga handout ɗin, da yake ya
faruk yasan halinta sarai, kuma yasan umma b babu ruwan ta duk maganar data ga damar faɗa
zata faɗeta koda kuwa a gaban ƙannen shi ne



Fuska a ɗaure yace



"Tashi kiba mutane waje"



Tasan sarai da ita yake,
Da sauri ta hau tattare takardun ta tanayi tana zumɓure-zumɓure ta fice a ɗakin




Seda yaga ta fita tukun yace

"Umma gani"
Juyawa tayi ta ajiye carbin hannunta ta fuskance shi da kyau,
Seda tayi gyaran murya tukun tace



"Tun last week nake jiran naga saƙon da kace amma shiru, banji daga gare ka ba"



Murmushi ya faruk yayi, a ranshi yana faɗin

"Taga shiga ta part ɗin Abba ƙ kenan"



Kafin yayi magana ta ɗora da



"Ni ba shiru na kira ka kayi min ba faruk, ko manzon Allah (SAW) yace uwa tana gaba da kowa"



Cike da kulawa ya faruk yace

"Haka maganar ki take umma, ban mnta da saƙon ba, zuwa anjima nake sa ran za'a kawo se a
fitar ma da kowa na shi dana mutanen shi"



Taɓe baki umma b tayi, kamar ba zata ce ƙara cewa komi ba, can dai tace



"In dai kana son ganin farin ciki na, to tabbas a fara girmama ni kafin waɗan da ke wahalar da
kai da sunan nuna kulawa"



Shiru ya faruk yayi ya sunkuyar da kan shi ƙasa, yana jin maganar da umma b keyi wani iri

Seda ta kai ƙarshen maganar ta tukun yace



"Toh, mu kasance masu yawan kyautata zato umma"



Da mamaki umma b tace

"Fassara abinda kk nufi faruk"
Murmushi ya sake yi, sannan yace

"Umma kenan, bari inje kar in rasa jam'i"



Kafin ta sake magana ya fice daga ɗakin ranshi a jagule.



Aljihun shi ya laluba yaji ko da key ɗin motar shi a jiki

Tsaki yaja jin be jishi ɗin ba, part ɗin su ya koma domin ya ɗakko, yana shiga su mus'ab na
ƙoƙarin fita,



Kauda kai gefe mus'ab yayi yace

"barka da rana ya faruk"



Ko kallon shi beyi ba, har ya tura ƙofar ɗakin shi ze shiga ya waiwayo yace



"Ku kawo min passport ɗinku kai da Ahmad yanzun nan".

Ya ƙarashe shigewa ɗakin.



Ya faruk na shigewa suka kalli juna shi da Ahmad



Murya ƙasa-ƙasa mus'ab yace



"mu gudu wallahi"

Tsaki Ahmad yayi yace

"Ba inda zamu, mu kai mishi ya gani, nasan in yaga yaune tafiyar ze bamu kayan mu"



Shiga ɗakunan su suka yi suka ɗakko passport ɗin su,
Mus'ab na fitowa ya miƙa wa Ahmad na shi yace

"ka kai ni bazan shiga ba"

Ansa yayi ya haɗa da nashi, knocking ƙofar ɗakin yayi

Seda ya bashi izini tukun ya shiga



Tsaye yayi bayan ya miƙa mishi passport ɗin yana jira ya gama dubawa ya bashi



Duk da ya faruk yasan me Ahmad ke jira hakan be hana shi faɗin



"Tsayuwar me kake yi kuma?"



Ido waje Ahmad yace

"ya faruk baka date ɗin bane?"



Kan gado ya wurga passports ɗin ya miƙe tsaye bayan ya ɗauki keys ɗin shi, da ido ya faruk ya
nuna ma Ahmad ƙofar fita



Ba musu ya juya sum-sum ya fice, ran shi baƙiƙƙirin



Akan idon su ya faruk ya rufe ƙofar shi ya wurga keys ɗin shi a aljihun wandon shi yayi gaba
abinshi ya barsu da ƙamshin shi me daɗin gaske.



SHARE PLS

ALLAH KASA ANNABI YA CECE MU 🤲
LAUJE CIKIN NAƊI

NA
ZAINAB FALALU(MRS SULAIMAN)
MARUBUCIYAR



👹
MAKIRCI
KISHI DA ALJANA
WANI HANIN GA ALLAH
ƘADDARAR MU
LAUJE CIKIN NAƊI

WATTPAD@ZAINABFALALU8

Pg6



Rai a ɓace mus'ab yace

"wannan ai mulkin kama karya ne wallahi, na gaji ƙarar shi zan kai wajen umma b wlh" yayi
gaba a fusace ze fita



Da sauri Ahmad ya damƙo shi, murya ƙasa-ƙasa yace



"Baka da hankali mus'ab ya faruk ɗin ne zaka kai ƙarar shi?
Malam ka dawo hankali ka"



Banda huci babu abinda mus'ab keyi



Hannun shi Ahmad ya kamo suka fito harabar gidan

Suna fitowa suka yi kiciɓus da ya faruk zaune a kan boot ɗin motar shi waya kare a kunnen shi
Kallo ɗaya yayi musu ya kauda kanshi gefe yaci gaba da wayar shi




Har sun gota shi Ahmad ya sake yin ƙasa da murya yace

"Ko dai muje mu bashi haƙuri ne?"



Tsaki Mus'ab yaja yace
"wallahi ba zanje ba, sedai kai kaje"
Yana gama maganar yayi gaba fuuu kamar wanda ze tashi sama.



Murmushi kawai ya faruk yayi, dan sarai yaji me mus'ab yace.




Mus'ab ne ya fara shiga part ɗin su fuska a ɗaure yana wani ciccin magani



Sakkowar mama da Abba ƙ kenan suka gan su a tsaye cirko-cirko kamar wasu zakaru



Rai a ɓace mama tace

"Lafia kukai mani tsaye a palo?"



A fusace mus'ab yace

"Gaskiya mama an fara saka mana ido a cikin gidan nan, kuma gaskiya ba zamu ɗauka ba"



Ba mama kaɗai ba, hatta Abba ƙ dake tsaye seda yaji wata mummunar faɗuwar gaba ta
ziyarce shi jin furucin rashin ɗa'a a karo na farko daga bakin ɗan nasu me kunya da tsananin
biyayya gare su"




Kafin Abba ƙ ya buɗe baki yayi magana mama ta rigashi faɗin



"Mus'ab me kake nufi da an fara saka muku idanu?
Mu iyayen ku ne ke saka muku idanu ko kuwa me kk nufi?"

Ta ƙarashe maganar tana zaro mishi idanun ta da suka kaɗa suka yi jajir.



Watsa hannayen shi yayi alamun oho ɗin nan, sannan yace

"Ai ba se na ambaci suna ba mama, kawai dai ku dena ɗaure ma ya faruk ƙarƙashi yana mana
abunda yaga dama bayan mun kauce mun bar mishi komi da ya dace ace mune akai"
Cikin zafin nama mama ta sauke wa mus'ab wasu mahaukatan maruka a kumatun shi



Mumtaz dake zaune itama mamaki ya gama kashe ta na jin abunda mus'ab ke faɗa,
kamar ƙiftawar ido taga tafiyar marin nan, muguwar zabura tayi taja baya tana dafe kuncin ta
kamar ita aka zabga wa marin,




Ahmad kuya ja da baya yayi ganin yarda mus'ab ya samu tsarabar tagwayen maruka



Ido jajir mus'ab ke kallon mama, har wani huci yake



Abba ƙ kam dafe kanshi yayi ya samu gefen kujera ya zauna.



Ganin kallon da mus'ab ke mata yasa ta matso kusa da shi,
Cikin ƙaraji da kuma fushi tace



"Kallon nan ba ze gamshe ni ba har se naji yatsun ka guda goma a fuskata tukun dan ubanka"



Dunƙule hannu mus'ab yayi, kamar ze kai wa mama duka, ya fasa ya fice daga palon a fusace,
a mugun firgice Ahmad yabi bayan shi



Mumtaz kuwa ganin yarda komi ya birkice yasa tuni ta fara kuka tana wa mama ɗan kira




Su mus'ab na fita mama ta juya da gudu ta koma sama



Tana shiga palon Abba ƙ ta fashe da kuka tana dafe kanta da take ji yana juya mata

Sunan Allah kawai take ambata jin yarda numfashin ta ke neman gagarar ta gaba ɗaya.
A daddafe Abba ƙ ya bi bayan ta, shima riƙe da kanshi.



A hankali altine ta koma da baya bayan ta sakayo ƙofar kitchen ɗin tana sauke ajiyar zuciya.




Se wajen bayan la'asar mama ta sakko, da ka kalle ta kasan bata cikin nutsuwa, ƙarfin imaani
ne kawai ke riƙe da ita



Tsabar yarda ta sha kuka yasa muryar ta bata wani fita can sosai,

Ɗakin su Mumtaz ta nufa, tana shiga ta iske ta kwance akan darduma bacci ya ɗauke ta

Seda mama ta gama ƙare ma ɗakin kallo tukun ta taɓa mumtaz tana kiran sunan ta



Seda tayi da gaske kafin mumtaz ta haƙura da baccin ta tashi zaune

A muryar bacci tace

"Wallahi ina jin azumin yau mama"



Juyawa mama tayi zata fita tace

"sannu uwar raki, ki taso ki taya Altine aiki bana jin daɗi"
Ta ƙarashe ficewa.



Seda Mumtaz ta sake ɓata lokaci kafin ta fito zuwa kitchen inda Altine ta fara aikin abincin buɗa
baki.




BAYAN AN SHA RUWA



Wajajen tara da rabi na dare, ya faruk na kwance yana ƙara nazarin maganar da suka yi da
mama da kuma Abba ƙ, abun na ƙara ɗaure mishi kai matuƙa

Waigawa yayi inda ya watsa passport ɗin su Ahmad yayi yaga suna nan
Daga can ƙasan ranshi yace

"Ƙila sunyi trying ɗaukar abun su fa"



A hankali ya sauka daga kan gadon shi ya nufi inda laptop ɗin shi ke ajiye

Seda ya koma gefen gadon ya zauna tukun ya buɗe

A hankali ya rinƙa kallon yarda mus'ab ke wani muzurai yana magana



Shiru yayi ya kafa wa screen ɗin idanu yana tuna irin kunya da kuma biyayya na yaran,
Seda ya gama kallo tas, kamar ance ya duba wasu vedios ɗin da CCTV CAMERAr shi ta ɗauka

A hankali ya rinƙa scrolling yana kallo,

Wata muguwar faɗuwar gaba ce ta same shi a take



Hannun shi har rawa yake wajen maida vedion baya, me idanun shi zasu gani?

Mumtaz ce a lokacin da ta shigo ɗakin shi ta ɗauki agogunan shi na diamond masu mugun
tsada

Tsayar da vedion yayi ya tashi da sauri ya nufi wajen safe ɗin shi

Sanin ba me shigo mishi ɗaki ne yasa be wani damu da rufe shi ba

Ilai kuwa, yana dubawa yaga babu waɗan nan agoguna da ya gani a hannun ta



Da baya da baya ya koma ya zauna haɗe da maimaita sunan ubangiji



A hankali ƙwaƙwalwar shi ke tuno mishi ganin ta da yayi tana abubuwa irin na marasa gaskiya



Da ƙarfi ya runtse idanun shi yana hasasho kirkin Abba ƙ da kuma maman kanta, kusan kowa
inuwar arzikin su yake sha a cikin gidan nan.
A bayyane yace

"Nata yafi muni akan nasu Mus'ab
Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un!! ya Abba ƙ da mama zasu ji in suka ji wannan mummunan
abun?" astagafirullah!"




A wannan dare ya faruk ya jima be rintsa ba, gani yake kamar wasa kamar kuma a mafarki
abunda ya gani



Alwashi kala-kala ya ɗauka a wannan dare, har barci mara daɗi yayi awon gaba da shi.



ALLAH YA ZAƁA MANA SHUWAGABANNI NA GARI.



ALLAH KASA ANNABI YA CECE MU 🤲
YAWAN COMMENTS, UPDATE AKAI-AKAI 😎
LAUJE CIKIN NAƊI

NA
ZAINAB FALALU(MRS SULAIMAN)

MARUBUCIYAR



👹
MAKIRCI
KISHI DA ALJANA
WANI HANIN GA ALLAH
ƘADDARAR MU
LAUJE CIKIN NAƊI

WATTPAD@ZAINABFALALU8

Pg7

Kusan kwana biyu kenan ya faruk ke fakon mumtaz da duk wasu motsin ta

So yake ko ta wani hali ya ritsata amma be samu zarafin yin hakan ba
Mumtaz kam kamar ta so ta ɗago ya faruk, sam taƙi yarda ta fita balle har ya ritsata, ko da
yaushe tana ɗaki kwance

Da mama ta matsa akan zaman ɗakin data tsira, shine tayi ƙaryar ciwon kai ne ke damun ta
Shiyasa mamar ta rabu da ita ba dan ta yarda ba.




Zaune ya faruk yake a palon umma b yana dudduba tickets yana siya ma kowa




Fitowar Umma b kenan daga side ɗin Abba b, da yake ita ke da girki shiyasa bata yi ma ya
faruk titsiyan da ta saba mishi ba



Tana fitowa yana gamawa, cikin nutsuwa ya ɗaga kanshi ya kalleta tukun yace



"Barka da fitowa umma"



Seda ta zauna tukun ta amsa da

"yauwa, kana nan ashe, su hafsa sun kawo maka kayan buɗa baki ko?"



Idon shi akan screen ɗin wayar shi ya amsa da "Nace a kai min ɗaki na"



Taɓe baki umma b tayi, so take tayi magana amma tana ɗan jin shakkar yi

Can dai ta daure tace

"Halan kayi banbancin da ka saba yi?



Da mamaki ya faruk ke kallon mahaifiyar shi, bece komi ba seda ya miƙe har ya kai ƙofar fita ya
ɗan dakata yace
"Gida uku na kasa ku umma, ko wani kashi ɗaya jirgi daban, be dace ace duka ahali ɗaya su
haɗe a jirgi ɗaya ba, babban kuskure ne,
Tunda har Allah ya hore yarda za'a rarraba ɗin ai gara a rarraba, ki duba na tura miki naki a
wayar ki"

Yana ƙarashe maganar ya fice yana jin ba daɗi sam a cikin ranshi na yarda umma b ke mishi.




Yana shiga ɗaki bayan ya zauna, wayar shi ya ciro ya kira mama dake zaune gefen Abba ƙ tana
yanka mishi apples a plate wayar ta tayi ringing

Seda ta kammala tukun ta kira shi

yana ɗagawa yace



"Mama yau akwai kunun gyaɗar nan kuwa?"



Murmushi mama tayi tana gyara zamanta kafin tace

"So sorry yaro na, na mance shaf ba'a kawo maka ba"

Kafin yace a ba mumtaz ta kawo mishi, mama tayi saurin faɗin



"Bari mumtaz ta kawo maka yanzun nan"



Godiya yayi mata suka aje wayar



Number mumtaz mama tayi dialing, bugu biyu ta ɗaga tana wani shaƙe murya kamar me ciwon
gaske, a tunanin ta wani aikin mamar zata saka ta



Ilai kuwa mama tace

"Ki duba kan dinnig flask ɗin yayan ku na nan ki ɗauka ki kai mishi yanzu"
Da sauri mumtaz ta wuntsulo daga kan kujerar da take kwance tace

"mama kuma kince nice zan kawo mishi?"



Tsaki mama ta ja tace

"in sakko inga baki kai mishi ba, zan baki mamaki ke da baki son a more ki sam"

Ta tsinka wayar ta, tana ci gaba da mammatsa wa Abba ƙ ƙafar shi.




Cikin marairaicewa mumtaz ta kalli sakina dake waya da saurayin tace

"Dan Allah sakina ki kaima ya faruk kunun shi"

Mumtaz bata gama rufe baki ba sakina tace



"caɓ, wallahi ba zani ba, salon inje ya rinƙa mun kallon wulaƙancin nan da ya saba"



Kamar mumtaz zatayi kuka tace

"Baki fahimce shi bane, haka yake shi, ni wlh jiwa nake gani shiyasa nace ki kai mishi"



Tsaki sakina ta sake yi, seda ta gyara kwanciyar ta tkun tace

"Haka nan zaki daddafa ki kai malama, thank God ba'a gidan nan nake ba da za'a kwashi ƴan
kallo dani"

Ta maida wayar ta a kunne taci gaba sa firar ta.




A zuciye mumtaz ta yayimi hijabin ta tasaka tukun ta ɗauki flask ɗin kamar shine me laifin, ƙiris
ya hana shi suɓucewa daga hannun ta tasamu ta taro shi
Tafi minti goma a tsaye tana jiran taga ko zata ga wani daga cikin yaran gidan ta bashi ya kai,
haka nan ta gaji da tsayuwar ta tayi shahada kawai ta nufi ɗakin




Ya faruk na zaune a gaban laptop ɗin shi, vedion mumtaz wanda ta ɗauki agogon nan ya kafa
ma ido yana kallo,
har yanzu ya kasa yarda da abun, se yake gani kamar ba nutsatstsiyar mumtaz ɗin da ya sani
bace



Knocking ɗin ƙofar da tayi ne yasa yayi maza yayi pausing vedion ya juyar da laptop ɗin zuwa
ɗayan ɓangaren da ba lale wanda ze shigo ya gani ba



Seda ya kimtsa tukun yace

"Come in"

A hankali mumtaz ta tura ƙofar kamar warce ƙwai ya fashe ma a ciki



Tunda ta shigo ya kafe ta da manyan idanun shi yana kallon ta,

Gaba ɗaya wani mugun tausayin Abba ƙ da mama ne suka lulluɓe shi, for the first time da yaji
kamar ya fashe da kuka tun bayan ya mallaki hankalin shi.



Tana sunkuyawa zata ajiye flask ɗin ya faruk yayi saurin tashi ya rufe ɗakin da key



Tana ganin haka ta juyo a tsorace tana niyar kware baki ta kurma ihu



Kamar yasan me take da shirin yi kuwa, manyan idanun shi ya zazzaro waje ya ɗora yatsar shi
ɗaya a kan laɓɓan shi yace

"shiii, kina fasa ihun nan zan sauya miki kamanni wlh"



Ƙut mumtaz ta haɗiye ihun ta, taci gaba da rarraba nata manyan idanun
Belt ɗin jikin shi ya zaro, tana ganin haka ta tsugunna ta dunƙule waje ɗaya tana ɓarin jiki




Rufe ida ya faruk yayi ya zambaɗa mata ɗaya a jikin ta

Kuma ya hana ta ihu



Sosai mumtaz ta tsorata da yarda taga ya faruk ɗin, a iya tsawon rayuwar ta bata yaɓa gani ya
ɗaga hannu ya daki wani a cikin gidan nan ba se yanzu, yanzun kuma a kanta




Cikin tsananin tsoro mumtaz tace

"Dan

Please Login or Register in order to submit comment