ya tashi sai a yanzu yake jin kunyar abinda ya aika ta ma yaran da mahaifiyar su ya yayi da na sani sosai.
Yaya Muhammad ganin kamar Abbi Baya cikin hayyacin sa ya sa ya ce "Abbi ina ta magana kayi shuru."
Sai lokacin ya dawo daga duniyar tunanin da ya faɗa aɗan firgice!
Ya ce "alhamdulilahi Muhammad fatan mun same ku lafiya?"
Yaya Muhammad ya ce "lafiya lau Abbi amma naga fuskarka kamar da damuwa?"
Murmushin da yafi koka ciwo ya yi murmunshin da yake tafi da abubuwa da yawa danasa wanda aka ce yafi dare duhu.
Abbi ya ce" Muhammad ina jin kunyar kune da wani ido zan kalle Mahaifiyar ku da yan Uwan ka?"
Yaya Muhammad ya ce "kada ka taɓa tunanin zamu juya maka baya Abbi mun san ba haka kake ba a ɗa ka dauka komai yana cikin kaddarar mune kuma bawa baya wuce ma kaddarar shi."
Maganan Yaya Muhammad ita ta sanyaya ma Abbi Zuciya.
Duk wannan abinda ake Eshan na jingine jikin mota shi duk ya damu su shiga ciki dan tunda Yaya Muhammad ya rungume Amira ya ke jin hau shin shi.
Cikin gida kuwa munatane sai zuwa ake ganin su Amira..
Ammi kam ganin mutane baza su daina shiga cikin gidan ba ya sa ta kama hannun Amira da Amir suka tafi ɗakin Yayan ta
Hafsat da Farha suna zaune tunda suka ga Ammi ta rungume su Amira suna kuka jikin su ya yi sanyi.
Hafsat ta ce "Allah sarki su Amira dole Ammi tayi kuka saima taji labarin abinda ya faru da su."
Farha ta ce " Walahi koni sun ban tausayi san da Yaya Eshan ke bani labarin halin da suke ciki ban yarda ba saboda ina mamakin rashin imani na wasu matan uban."
Ammi bayan sun shiga ɗakin dasu Amira suna ta kuka Amir ne ya ce "Ammi ba kuka ya kamata kiyi ba farin ciki zaki yi yanzu haka muna tare da sirikin ki."
Ammi ta ce "wai da shi ku ka zo?"
Amir ya ce "Eh Ammi ai Yaya Eshan bazai iya yin haƙuri mutahu bada shi ba."
Dariya Ammi tayi ta ce "ni kam ina son na ganshi na gode mashi"
Dariya Amir ya yi ya ce "ai haɗa ƙanwar muka zo da abokan shi guda biyu da ƙawar Adda Amira."
Ammi ta ce " kardai ka cemin wainda muka wuce a falo tare kuke da su?"
Amir ya ce "tare muke su."
Ammi ta ce "yau naga ikon Allah amma she baku faɗa min ba."
Amira tayi dariya.
Ammi ta ce "dariya ma zaki yi ta ce ma Amir je kace su zo nan."
Da gudu Amir ya fita daga ɗaƙin ya tafi falon dasu Farha suke.
Ya shiga ya ce "Aunty Farha Ammi ta ce kuzo."
Da murmushi Farha ta kalle Hafsat ta ce " muje."
Suka tashi hannun su sarƙi dana junna Amir na gaba sukuma suna baya sanda suka fita a falo lokacin su Abbi suka shigo ciki.
Amir ya ce "Yaya Muhammad ka girma."
kallon shi Yaya Muhammad suka kwashe da dariya.
Su Farha suka wuce ɗakin da Ammi take sukuma suka shiga falo.
Da sallama suka shi ga falo tunda suka shiga Eshan ya sa ido ko zaiga Amira Amma bai gan ta ba.
Su Farha suna shiga ɗakin Ammi ta jawo su ta rungume su tana masu Barka da zuwa sunji daɗi sosai.
Amir ya ce " Ammi su Yaya sun shigo."
Ammi ta ce " ku tashi mu tafi can mu gaisa."
Suka amsa da Toh
Suka fito suna shiga falo Eshan ya kafe Amira da idanu har sai da Ahmad yayi ma shi magana duk wannan abin da ake Abdul yana kallon shi dariya kawai yayi a zuciyar ya ce Eshan sai addu'a.
Gaisawa suka fara yi Ahmad ne ya gaishe da Ammi ta ɗago ta amsa suka haɗa ido a sukwane Ammi da Ahmad suka tashi suna nuna juna Bakin Ahmad na rawa ya ce Aunty dama kina nan ita kam Ammi ta ƙasa Magana.
Meke shirin faruwa ne meye tskanin Ammi da Ahmad kardai ace yan uwane
DAFIN ZUCIYA
By Fatima Binta Hussain
https://chat.whatsapp.com/CBtvAeshrDyAlqXRA7d4sM?mode=ac_t
https://whatsapp.com/channel/0029VbBbXTM3GJOxiUfRPn1U
[8/15, 06:43] hiameera437: *https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
🦚🦋THE NOBLE WRITER'S TEAM🦋🦚
(🦚✊DEDICATION IS OUR STRONG✊🦚)
[8/16, 06:05] hiameera437:
Bisimilahi Rahamanur Rahim
DAFIN ZUCIYA
By Fatima Binta Hussain
Page 49
://chat.whatsapp.com/CBtvAeshrDyAlqXRA7d4sM?mode=ac_t
https://whatsapp.com/channel/0029VbBbXTM3GJOxiUfRPn1U
[8/15, 06:43] hiameera437: *https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
🦚🦋THE NOBLE WRITER'S TEAM🦋🦚
(🦚✊DEDICATION IS OUR STRONG✊🦚)
[8/16, 06:05] hiameera437:
Bisimilahi Rahamanur Rahim
Ahmed bakin shi na rawa ya ce "Aunty dama kina nan?"
Ammi ta ma kasa Magana tana jin jina ikon Allah da ya haɗa ta da ɗan ɗan yar uwata kuma aminiyata.
Da kyar ta iya ce wa "Ahmad ko?"
Ya ce "eh Aunty."
Ammi ta ce "ina A'isha tu ta ke?"
Ahmed ya ce "tana port Harcourt."
Ammi ta ce "me ya Kaita port horcout?"
Dariya Ahmed yayi "ya ce tana lafiya labarine me tsowo ki bari zuwa anjima sai mu zauna tunda ba yau zamu tafi ba".
Ammi taji daɗi maganan shi hakan yasa ta ce "shekenan ku zauna ga abincinan kuci ku huta amma kafin nan ka kira min yar uwata."
Dariya ya yi ya ce "Tom aunty."
Ya Dan nama Ummin shi kira video call.
Tana ɗagawa ya ƙara a fuskar Ammi u
Ummi naga nin fuskar Ammi a ruɗe ta tashi tana nuna wayan.
Umma rayuwa ta juya masu a yan kwanakin da suka yi gidan gyaran hali bata taɓa tunani zata shiga wannan halin a rayuwar ta ba sun rame sosai sun fita hayyacin su Bama kamar Mama.
Ciki sanyi jiki Mama ta kalle Umma ta ce "gaskiya da an dawo Shari'a zan faɗi gaskiyar abin da ya faru nayi da na sanin kasan ce wata haka ban san me ya rufe min ido ba gwara ayimin hukunci ko kashe ni za'a yi a kashi ko na samu sauƙi wajan ubangijina."
Umma na jin ta tana magana amma babu alamun nadama a tare da ita.
Umma tayi nisa.
Ladidi da kyar ta faɗa ma su yaya abinda ya faru inalilllahi wainna ilaihi ra'ji unm kawai suke faɗa dan Ladidi ta basu mamaki ta ɗaure masu jijeyoyin kainsu saboda tsabar tashin hankali sai da yaya ya faɗi shi kam shi Malam kawai daure wa yake yi.
Ladidi ganin yanda hanakalin su ya tashi yasa ta durƙusa ƙasa tana neman yafiyar su.
Yaya ne ya kamata da duka bana wasa ba yana cewa "waliahi sai dai in kashe ki wannan wani kalar bala'i ne shirka a matsayin ki na musulma."
Allah sarki Malam duk ya ruɗe ya kasa yin komai.
Matar Yaya ce ta shigo da gudu da kyar ta amshe Ladid daga hannun shi.
Wani hauri Malam ya kai mata a ciki nan ta fara zubar jini.
Mommyn Yusurah taga rayuwa itama tana ji tana gani ta koma me ƙafa ɗaya ta yi da na sanin rayuwar ta sosai amma ta gode ma Allah da ya bata damar tuba.
Haidar ne zaune a falo suna fira ya kalle Yusurah ya ce "nifa na kusa ayi bikin nan in killa ce ki a ɗaki."
Dariya ma maganan shi ya bata tayi shuru bata ce komai ba.
Ganin tayi shuru ya sa ya ce "ya aka yi ki ka yi shuru ko ke baƙi ƙosa ki shiga daga ciki ba ki fara haifa na bebes masu kama da ke."
Ciki da jin kunya ta ce "Ummm nifa sai kunya kake bani Please kabar maganan."
Haidar ya ce "Tom ambarta yaushe zamuje ki gaida Mama?"
Yusurah ta ce "duk ranar da ka kai ni a shire nike."
Amaryar Daddyn Yusurah tana ta fama da rashin lafiya wanda an rasa me ke damun ta idan aka ce tazo su je asibiti sai ta ce ita baza ta ba.
Yau Daddy ganin jikin babu daɗi yasa ya ce ta shirya ta rakashi unguwa ita kam bata kawo komai a ranta ba ta tashi suka tafi kai tsaye suka wuce NISA HOSPITAL LIFE CAMP asibiti ne naasu hali gwajin farko aka ga tana da juna biyu wata uku wayo Allah zukuga murna wajan Daddy Allah ya bashi abinda yake nema nan ya faɗi yayi ma Allah sujadar sukur.
Amira ita ta shiga zuba ma kowa abinci da lemuka tana jikin zubawa Babban Yaya ya shigo Yaya Faruk da gudu ta tafi ta rungume shi a bazata ya ɗago yana kallon ta dan shi bai san da zuwan su ba.
Amir ne ya taho shima ya rungume shi kuka kawai suke yi kukan da suke yan taɓa kowa a falon amma Malam Eshan kam ya kumbura.
Da kyar Yaya Faruk ya ce "ya isa haka."
DAFIN ZUCIYA
BY FATIMA BINTU HUSSEN
Fir,Aug22 08:26 hiameera43
https://chat.whatsapp.com/CBtvAeshrDyAlqXRA7d4sM?mode=ac_t
*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
🦚🦋THE NOBLE WRITER'S TEAM🦋🦚
(🦚✊DEDICATION IS OUR STRONG✊🦚)
Allah ya jiƙan magabatan mu😭
Bisimilahi Rahamanur Rahim
Page 50
Ammi ganin yanda ummi ta ruɗe itama Ammi sai ta fashi da kuka tana barin falon ta shiga wani ɗaki dake falon duk da kallo suka bita jikin su duk yayi sanyi.
Ammi na shaga ɗaki ta zauna da yake a kwai wutar nefa ko ina suna samun wuta sosai.
da kyar Ummi ta ce " A'isha dama kina raye dama zan ƙara ganin ki?"
Ita ma Ammi ta ce "ashe zamu ƙara ganin juna?"
Sai kuma suka ƙara fashewa da wani sabon kuka.
Ummi ta ce " ya kuƙa haɗu da Ahmed"?
Ammi ta ce "wannan labarin yana da tsawo amma bari na baki yarda zaki fahim ta."
Nan Ammi ta faɗa mata haɗuwar Eshan da Amira da bikin su da akasa sa har zuwa yau da sukazo....."
Farin ciki ya cika Ummi tama rasa me za tace kawai sai ta ce ma Ammi "kina lafiya???".
Dariya abin ya ba Ammi sun manta duk wannan abin da ake basu gaisa ba.....
Itama Maryam dariya tayi ta ce " kullum hankali na na kanki ina tunanin halin da kike ciki kusan kullum sai nayi kuka nayi maku addu'a Ashe Allah ya amsamin gaskiya zan yi azumi na gode ma Allah..."
Ammi tama rasa me zata ce kawai sai ta sura mata idanu da wayan tana kallon ta tana tunanin wace irin kauna ce wannan baiwar Allah take mata me zata mata dan taji daɗi ita kam.......
Ummi ta ce ma Ammi " wai me ya faru dake bayan tafiya ta....?
Ammi ta ce " Maryam labari ne me tada hankali bayan tafiyar ki nan dai Ammi ta bata labarin rabuwar ta da Abbi ta Kuma iririn zalin cin da Umma tayi ma su Amira Bata ɓoye komai ba ta faɗa mata.....".
Sosai Ummi take kuka kamar zata shuɗe Ammi ta ce " yanzu ba lokacin kuka bane lokacin farin ciki ne dan Allah ki daina wannan kukan..."
Ummi ta ce " dole zan yi kuka DAFIN ZUCIYAR wannan matar har ya kai haka."
Ammi dai lalaɓa Ummi ta daina kuka san nan Ammi ta ke ce ma Ummi ashe Kuna port Harcourt.?
Ummi ta ce "muna can amma mun kusa dawo wa Abuja kin san ɗanki soja ne shida Eshan yanzu hakama Eshan yakai matsayin ganeral
Kuma sun neme taransupar zasu dawo Abuja da aiki sun samu."
Ammi tayi masu addu'a sosai san nan ta ce "zata kira ta numbern ta kamar kar su rabu haka suka yi sallama.
Ammi ta fito daga daƙin ta miƙa ma Ahmad wayar shi...
Allah sarki abbi ganin Yaran sa sai hankalin shi ya tashi ovar....
Da kyar suka daina kukan ya yakama hannun su suka shiga cikin falon duk wannan abin dake faruwa Yaya Faruk bai kula da Abbi ba sai da ya zauna san nan ma ya kula da mutanan falo cikin girma mawa ya taso suka yi musabaha suka gaisa yana ganin Abbi ya tamƙe fuska amma haka ya daure ya meƙa mai hannu suka gaisa....
Yaya Faruk shine Babba a ɗakin su Amira Amma yana da wani murdaɗen hali me wuyar fassarawa dan idan baku zauna da shi ka fahin ce shi ba zaka yi tunanin girman kai gare shi kuma kayi mashi kallon miskili amma ba haka bane dalilin da ya sa mutane ke mai wannan kallon baya shiga abin da babu ruwan shi indai ba saka shi a ciki kayi kuma ba komai yake bama mahimci ba.
Suna gaisawa da Abbi ya koma ya zauna suka ci gaba da cin abinci bayan sun gama ci.
Ammi ta ce ma " Yaya Faruk ya kai su Eshan gidan shi suyi wanka su huta."
Abbi Kam dama ɗan garine ya ce "Shema zai je gidan su ya huta anjima zai dawo."
Ita dai Ammi bata yi magana ba Yaya Muhammad ne ya ce "to Abbi sai ka dawo."
Yaya Faruk ya ce ma su Eshan "su ta shi su wuce"
Suka yi ma Ammi sallama akan anjima zasu dawo.
Nan aka bar su Farha
Allah sarki Daddy duk ya zauce ya yi ma mutane alkairi sosai haka suka dawo gida bayan an sama mata duka ta kiyaye wasu abubuwan.
Haka suka dawo gida koda suka dawo gida da aka faɗa ma Mommyn Yusurah tayi farin ciki sosai daga baya ta shiga ɗaki tayi kuka sosai ta kuma yi dana sanin rayuwar ta baya kuma yarda da duk abin da kayi ma Allah kutse baka ganin dai dai a rayuwar ka."
Mansur suna ta shiri ranar Monday za'a koma court za'a cigaba da Shari'a
https://chat.whatsapp.com/CBtvAeshrDyAlqXRA7d4sM?mode=ac_t
*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
🦚🦋THE NOBLE WRITER'S TEAM🦋🦚
(🦚✊DEDICATION IS OUR STRONG✊🦚)
THE HIDDEN TREASURE OF TH HEART
DAFIN ZUCIYA
BY FATIMA BINTU HUSSEN
Sun,Aug24
03:18pm
Bisimilahi Rahamanur Rahim
Page 51
Abbi bayan fitar shi kai tsaye gidan su ya wuce inda Ammi ta fara zama tunda ya fito suke ta gaisawa da mutane tunda ya daɗe baije garinba hakan ya sa mutane ke marmarin shi kuma bugu da ƙari Abbi Ya na da kyuta hakan ya sa koya yake rabar shi haka su kai ta gaisawa da mutane kuma kusan kuwa sai ya yi mashi ihisani.
Su Eshan bayan su fita koya da tashi motar hakan ya sa Yaya Faruk ya ce "kowa ya hau motar shi idan suka je gidan shi sai su ajiye a can."
Sunyi na'am da shawarar Yaya Faruk kowa ya hau tashi suka tafi.
Masha Allah gida ne ya haɗu iya haɗu ba'a magana daga gani an kashi mashi dukiya ta ban mamaki bayan me gadi ya buɗe ma get su suka shiga suk ayi paking motocin su.
A yaune Yusurah zataje ta gaida Maman Haidar.
Haidar ne ya zu ya dauke ta suka tafi suna tafiya suna firar su ta soyayya.
Haidar ne ya kalle Yusurah ya ce " kin tuna farkon haɗuwar mu ina kain titi ina sai da ruwa?"
Yusurah tayi dariya ta ce "dan Allah ka bar wannan maganan ya na tuna na min wani abu wallahi."
Dariya ya yi ya ce " to shike nan amma Ni kam bazan manta da wanan ranar ba saboda a ranar na haɗu da Matata."
Yusurah ta shagwaɓa fuska ta ce " Please mana kabar wannan maganan Allah fah bana so."
Ya ce "shekenan an barta."
Su Farha kama Ammi ta sa su ka yi wanka san nan ta kaisu wani ɗaki ta ce " su kwanta su huta kafi anjima suma."
Ko da suka shiga ɗaki sai suka bige da fira suna cikin fira sai ga Aunty Fatima ta shigo tare da Auta dama basu nan sum fita unguwa ne.
Dagudu Aunty Fatima ta faɗa ɗakin tana kiran "Amira Amira Amira." Kam tana jin ta bari ta yi ta ƙara so ciki tana shiga ta haɗa su duka ukun ta rungume tana murna duk da su Farha Basu san ta ba haka suma suka rungume ta suna murna.
Amira ta ce "i miss You Aunty duk da ta muna tare duka na kike."
Dariya tayi ta ce "kinsan daga baya har kuka nike me yasa nike dukan kin ki."
Suka kwashi da dariya Amira ta ce "ina ɗiyata tazo na ganta?"
Auta Minal kam sai hararan Amira take wai ai tunda suka zo yanzu Ammi zata dai na son ta.
Amira da ta lura da Auta na hararar ta ta tashi ta tafi ta bige mata baki ta na cewa "dan ubanki baki murna da ganin mu sai harara?"
Auta kam ta fasa ƙara tana kukan taɓara.
Aunty Fatima ta ce "kace har yanzu masifar nan me hali baya fasawa."
Dariya Amira ta yi tace "nidai Ina takwatata."
Aunty Fatima ta ce "bacci fa take ma kwantar da ita."
Amira ta ce " bari to sai ta tashi."
Aunty Fatima ta kalle su Farha ta nuna Hafsat ta ce "ya sunan ki?"
Hafsat ta faɗa mata.
San nan ta nuna Farha ta ce "kefa?"
Farha ta ce "sunan Fatima amma ana ce min Farha."
Aunty ta ce "sunayen ku masu daɗi."
Kiran Eshan ne ya shi go wayan Amira amma saboda Aunty Fatima taƙi ɗagawa tayi shuru.
Aunty Fatima ta ce "kodai sirikin ne ke kira kike ƙi ɗagawa?"
Amira ta ce "ummm."
Dariya Aunty tayi kawai ta ce "bari na fita na barku ku huta."
Eshan haushi ya ishe shi ganin yana kira bata ɗagaba bako kunya ya fara magana agan ban su Yaya Faruk su kam duk sun zuba mashi idanu suna kallon ikon Allah.
Ahmad ne ya ce "kai wallahi naga soyayya na neman maida ka mahukaci dama kuma ba a maganar kunya tunda baka da ita."
..
THE HIDDEN OF TREASURE OF THE HEART
DAFIN ZUCIYA
BY FATIMA BINTU HUSSEN
https://chat.whatsapp.com/Jp93APpPrfe9IezRu9zH91?mode=ac_t
https://whatsapp.com/channel/0029VbBbXTM3GJOxiUfRPn1U
*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin
BIBLE WRITER'S TEAM🦋🦚
(🦚 ✊DEDICATION IS OUR STRONG✊🦚)
Bisimilahi Rahamanur Rahim
Page 52
Eshan wata uwar harara ya maka ma Ahmed san nan ya ce " laifi ne dan na damu da matata."
Tsaki Abdul ya yi ya ce "wallahi duk ka lalace."
San nan ya kalle Yaya Faruk ya ce "Dan Allah kada ku bashi auren nan duk yabi ya dani mutane."
Dariya Yaya Faruk ya yi ya ce "ai ina ga haka za a yi."
Dariya duk su ka yi san nan Yaya Faruk ya ce "ya kamata mu tashi mu fita lokacin Sallah ya yi daga masalaci sai mu wuce wajansu Ammi."
Daga nan suka tashi suka fita yanzu a motar Yaya Faruk suka fita.
Amira suna ta fira tskanin su daga nan bacci ya dauke su ana ta zuwa dubasu amma Ammi tace suna hutawa ne dan dama tasan mutane baza su barsu ba.
Su Amira sai da suka sha baccin su kayi wanka san nan suka fito.
San da suka fito sun iske falon ya cika da yan uwan Ammi ma sha Allah sunyi kyau sun sa abaya kowa da kalar tasa kuma duk ta amshe su.
Tunda suka fito mutane ke binsu da kallo wasu ma gulma ce ta kawo su suna su suga Wanda Amira zata aura.
Bayan sun ƙara so suka zauna san nan suka gaishe da mutane nan wasu suka fara tambayan Amira wai ance basu jin daɗi a gidan Abbi jin wannan tambaya ya sa Ammi ta gane dama wasu ba haka nan suka zo ba Amira Kam sai dai tace su lafiya lau suke zaune don Yaya Faruk yayi masu gargaɗi karsu faɗa ma kowa wani abu dan yasan halin mutane za'a iya zuwa a tarbi Abbi da maganan.
Abbi yana tafiya suna gaisawa da mutane a haka yar ya isa gidan su mutanan gidan sunyi murnan ganin shi sosai dan son san tunda ya zo basu babu cin mara daɗi .
Bayan an gama gaisawa ya shiga Part ɗina da Ammi ta zauna a gidan shigan shi falon sai zuciyar shi ta kare har sai da ya zubar da hawaye yana tuna kalar rayuwar da suka yi a wannan waji ƙaddara ta zo ta dauƙe shi ta maida wani gari wanda hakan yayi sular rabuwar shi da masoyiyar shi amma bai fidda ran zai maida ta ba tunda yaga alamun sauƙi tattare da ita part ɗin yayi datti sosai hakan yasa ya fara kaƙaɓe korar bayan ya gama ya share ya gyra ko ina ya shiga wanka da ya fito ya shiga ɗaki har ya kwanta sai kuma ya fars ma tunanin yaran shi da Umma ta tafi da su ɗan shi bai samu labarin suna gidan gyaran haliba.
Tuna wa da su yasa ya dauƙi wayar shi ya kira wani abokin shi ɗan garin su Umma ya ce ma shi "Dan Allah yaje gidan su Umma ya duba mashi yaran shi koma ya dauko su ya daura su a mota aka wo su funtuwa."
Abokin shin cike da mamaki ya ce "yan zu bakasan abinda yake faruwa ba?"
Gaban Abbi ne ya faɗi ya ce "subuhanal me yake faruwa?"
Nan abokin shi mai suna Sani ya faɗa mashi abinda ya faru ya ce " ranar Monday ma za'a koma Cotu."
Sosai Abbi ya girgiza da jin abinda ya faru san nan ya ce "dan Allah ina son ka dau ko min yaran ba tare da kowa ya sani ba."
Abokin shi ya ce "kana funtuwa ne?"
Abbi ya ce "eh na shigo funtuwa."
Abokin shin ya ce "gobe zai kawo su dan zai zo wani aiki a funtuwa kuma yau zai ɗauko zu su kwana a gidan shi gobe sai su taho tun da safe."
Sosai Abbi yaji daɗi ya ce "ya tura mashi da account number ɗin shi zai sa mashi kuɗin da zasu yi na mota."
Abokin shin ya ce "haba ɗan Allah wani kuɗi zaka bada ai duk ɗayane."
Daga haka su ka yi sallama san nan abbiy ya kwanta yana mamakin abinda yaji Umma tayi ita da uwar ta.
Ladidi koda suka je asibiti da kyar
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 9 Chapter of 14