"wai kai dan uban ka baka da kunya? ko ina ka koyo wannan rashin kunya a gaban surukar ka ka saki baki kama ta kwaso zance."
Kunnuwan shi ya kama ya na cewa "Please Mamen mu dan Allah kiyi haƙuri na dai na."
Ammi dake kallon su tana murmushi ta ce "ai Ni na saba da wannan taɓargazar ta shi tun ina jin kunya yan zu na daina."
Dariya Mame tayi ta ce "kin san halin yan fari."
Abdul ne ya yi sallama ya shi go suka amsa kai tsaye wajan su Ammi yaje suka gaisa san nan ya kalle Eshan ya ce "Malam lafiya ka kirani?"
Marai raice fuska Eshan yayi yana cewa "unguwa zaku raka ni."
Ahmed ya ce " to ba'a zuwa."
Eshan ya ce "kada kaje idan baka je ba kai kayi ma kanka."
Abdul ya ce "to ba sai ka faɗa ma mutane inda za'a je ba."
"Wajan su Amira zamu je muje yanda za'a gudanar da shirin biki muji idan da abinda suke buƙata."
Mame ta ce "sai da ku kira su a waya dan ko kunje baza ku gan su ba na faɗa maku."
Amira saboda gyaran jikin su me gyran jiki aka dauko daga Nijar gyara ake masu bana wasa ba ko fita waje basa yi komai sai dai ayi masu a ɗaki idan ka gansu za ka yi tunanin an chanza su ne su ukun da yake harda Farha Aunty Fatima ce taje har gidan su ta ruƙi Mami akan za'a haɗa dasu Amira ayi masu gyran jiki baki ɗaya.
Yaran Umma koda aka faɗa masu halin da mahaifiyar su take ciki sunbyi kuka Sosai da daga baya basu saki jikin su da Ammi ba suna tunani zata yi masu abinda Umma tayi masu Amira amma sai suka ga ba haka ba domin Ammi kula take da su sosai da sosai hankan ne ya sa suka son ta suka dauke ta kamar itace ta haifisu,
Wannan abu da Ammi tayi baƙara min ƙaramin daɗi yayi ma Abbi ba hakan yasa yake jin kome Ammi ta ke so indai bai fi ƙarfin shiba zayayi mata.
Bayan sati ɗaya
Mariya ɗiyar Ladidi ce kwance a wani asibiti an kawo to ashe bayan rasuwar Mahaifiyar ta wani Alhaji ne ta bi ƙasar waje wai zata rakashi holiday Babu wanda ya sa ni ta bi shi suka tafi ashi babu wata ƙasar waje da zasu ji suna shiga mota za su je aripot ya hura mata wani abu nan da nan ta fara barci ganin tayi bacci ya kai ta wani gida ya mayar da ita matar shi ta karfi da yaji sai da ya gama lalata mata rayuwa gashi ya shafa mata cutar ƙarya garkuwar jikin ɗan adam HIV,
Ganin bata cikin haiyacin ta yasa wani daga cikin yaran shi ya kawo ta asibiti ya bada kuɗi masu yawa a yi mata komai shi kuma ya gudu.
Yanzu ta farka ganin ta a wani ɓakon waje inda bata san ko ina ne ba ita tunanin ta ma ko mutuwa tayi ne ma tana cikin wannan tunanin wata likita ta shigo ta kalle ta ta ce "sannu ya jikin."
Ta ce "da sauƙi."
Likitar ta ce "ina ke maki ciwo?"
Ta ce "kaina ne kawai."
Likitar ta ce "to alhamdulilahi yan zu ina family na ki?.
Kuka ta fashe da shi tana cewa "suna nan amma ina tsoron koma wa wajan su nasan idan naje Baba yaji abin da ya faru kashi ne zai yi."
Likitar ta ce "subuhanal me yayi zafi haka?"
Mariya ta ce "inda kin san abinda na aiki ta ke kan ki baza ki kulani ba yanzu."
Likitar ta ce "kin man ta karin maganar da ake ce wa "ciwon ƴa mace na ƴa mace ne ki faɗamin in Sha Allah nayi maki alƙawarin zan sa san taki da iyayen ki."
Kuka ta fashi da shi.
Eshan duk yan da ya so yaga Amira abin ya gagara har ce ma me gyran yayi ta bari ya gan ta zai bata kuɗi masu yawa amma fafar matar nan ta hana haka ya gaji ya yi hakuri sai dai suyi video Call.
Mame ce ta shirya zata je giɗan wata yar uwar ta da za ta aurar da ɗiya rana ɗaya dana su Ahmed shene zata je tayi mata Allah sa alkairi ta dau wankan ta tayi kyau baza kace ita ce ta haifi Ahmad ba.
A motar Ammi ta fita kai tsaye gidan su Yusurah ta tafi da sallama ta shiga cikin gidan amarya ta amsa mata tana mata sannu da zuwa bayan su gaisa ta raka ta ɗakin Mommyn Yusurah mommyn Yusurah naji sallamar ta ta fashi da kuka Mame kam ganin an yeke ma Hajara ƙafa amma an sama ta ta roba cikin tashin hankali ta ƙara sa tana kuka itama tace "Hajara me zan gani haka?"
Cikin kuka Mommyn Yusurah ta ce "Maryam kinga yanda rayuwa tayi dani ko kinga yanda na koma ko."
Maryam ta ce "kin sani a duhu meke faruwa me ya faru da ke."
Hajara bata ɓoye mata komai ba dangane da zuwan su wajan boka ita da ƙawar ta har zuwa yanzu da take da ƙafar roba.
Cikin ɓacin rai Maryam ta wanke ta da mari takuma ƙara mata ta ce "kin san marin me nayi maki?"
Kai ta girgiza ma ta.
Maryam ta ce "wallahi Hajara kin bani mamaki duka da wannan ƙaddara ki na cikin sai an yanke maki ƙara uban me ya kai ki wajan boka uban me ya kai ku tsaɓa ma Allah baki rasa ciba baki rasa shaba saboda za 'ayi maki kishiya Yan zu Ina amfanin mutuwar da ƙawar ki tayi ki gode ma Allah da ya baki damar gyara ra kuskuren ki."
Hajara ta ce " wallahi ban san me ya shiga kaina ba da har na ai kata haka sai gashi warda nike haukan akai ita ce me min komai ta dauƙeni kamar Yayar ta ta maida Yusurah kamar ita ta haife ta."
Maryam ta ce "yan zu sai ki yi hakuri ki dau komai a matsayin ƙadddar amma wani abun mune da kanmu muke je kawo shi cikin rayuwar mu."
Daga nan suka shiga yan firar su ta bayan rabowa .
Hajara ta ce ma Maryam "yau za'a kawo lefe."
Mame tace " she ne baki faɗa min ba ai da naje idan da wani aiki sai na taya ta."
Daga haka ta fita daga ɗakin zuwa part din Amarya tana zuwa ta same su suna ta aiki ita da yan uwan ta cikin su ta shi ga suna aiki ana fira itama take faɗa su rana ɗaya da bikin ɗanta wasu daga cikin suka ce zasu zo mata.
Da yamma aka kawo lefin Yusurah akwati ashirin da hudu lefe ne na manya an kashi kuɗi iya kuɗi yan unguwa akai ta zuwa kallon lefin wasu na cewa YUSURAH ltayi goshi masu baƙin ciki nayi masu farin ciki nayi sai da yamma Mame ta koma gida.
Abubuwa sumn masu Eshan yawa ga hidimar biki gata ƙarin girma da za'a masu washi garin biki kan su yayi zafi sosai dan ko time ɗin kiran su Amira basu da wani shi ga shi zasu Event da yawa za'ayi deenah za'ayi mother's day ga kauyawa day da za'ayi sanan za ayi fati sai daga baya ayi walima.
Likitar ta jawo Mariya jikin ta tana lalashin ta a haka ta faɗa mata duk abinda ya faru daga mutuwar auren da da yawon barikin da take yi har zuwa rasuwar Ladidi da kuma bin wannan alhajin da tayi.
Sosai likitar tayi mata faɗa kamar zata ari baki daga nan kuma ta koma mata nasiha ta ce ta Bata number wayar Baban ta.
Bayan ta bata number wayan Baba ta Kira shi Baba yana ɗaki ya na ta tuna nin abin duniya yaji ƙarar wayar shi ganin bakuwar number ya sa ya ɗaga da sallama.
Daga can bangaren likita ta amsa ta ce "muna magana da Malam Sa'idu ne? mahaifin Mariya?"
Gaban shine ya faɗi kafin ya ce "eh nine Allah yasa lafiya?"
Likitar ta ce "Lafiya lau Baba ka kwantar da hankalin ka idan babu damu kazo asibiti."
Cikin tashin hankali ya ce "asibiti kuma! Dan Allah ki faɗa min abinda yake faruwa?"
Ta ce "babu komai Baba ta faɗa mashi sunan asibiti."
Yaje ya faɗa ma amarya abinda ya faru ita ma hanakali a tashi ta ce "ai bai ka ma ta ka tafi kai ɗaya ba mu tafi tare."
Haka suka fito suka tafi asibitin suna zuwa suka kira likitar ta zo ta shiga dasu har ɗakin da Mariya take ciki tun da suka ganta sun san babu lafiya daga ganin yana yin jikin ta.
Sai da suka gaisa da likitar ita kuma Mariya kunya tasa ta ka sa cewa komai sai ta juya masu baya ta rufe ido kamar me bacci.
Likitar ta ce ma Baba "nasan kai musulme ne? Kuma zaka dauka ƙaddara ka ko wace kala ce."
Ciki sanyi muraya ya ce "in Sha Allah."
Nan likitar ta faɗa masu abinda ya faru da Mariya tana gama faɗa ta tace "ka ganta nan kunyar ku take ji yau kusan satin ta biyu a asibitin nan sai yau dana takura mata ta faɗa min abinda ta aikata dan Allah kayi haƙuri ka rungume ɗiyar ka."
Baba ya ce "shikenan yan zu zata warke da wannan cutar kam?"
Likitar tace "in Sha Allah zata warke bada daɗi wa ba."
Amarya ce ta ce "ya jikin naki?"
Da kyar ta ce " da sauƙi."
Zuwaira ta ce "kada ki sama kan ki damuwa ki daukeni kamar mahaifiyar ki ni zan kula dake."
Mariya ta ce "yanzu duk abinda Mama tayi maki kice Zaki kula dani."
Zuwai ta ce "kibar tuna wannan komai ya wuce.
Ammi ce ta ce ma Abbi "ya ka ma ta akai yaran nan suga mahifitar su."
Abbi ya ce "shi dai ba zai je ba kuma yaran shi baza su je ba."
Sai da Ammi tai ta lalashin shi san an ya yarda ya ce "zai kai su amma sai bayan biki."
Ana ta shirye shirye za'a kawo lefen Amira da Hafsat.
Sai da aka fara kawo lefen Amira akwati 24
San nan na Hafsat itama 24
San nan na Farha itama 24
Komai kala ɗaya ne babu abin da aka ban banbanta ma sha Allah kaya sun yi komai yayi sai dai maƙiya yaune za'ayi kauyawa a wani gidan gonar Abbi da ya basu key ya ce suje su yi acan.
Mata sun sa riga da ban zani da ban.
Maza kuma sun saka wando da ban riga ba dan ko ina a wajan zagaye yake da sojoji.
An dauko DJ da photographer abin dariya ana kiran amarya da ango suyi rawa Ahmad ne na farko suka fara shiga shida Hafsah aka kuna masu waƙar TSIRE TSIRE DUNIYA KANYA DAƊI ALLAH NAGA GANI BA ZAN BAR TSIRE BA Kowa da tsrire a hannun shi ita Hafsah kunya ta hana ta rawa shi kuma gogan rawar ka wai yake abin shi kamar ba soja ba an zuba masu kuɗi sosai.
San nan aka kira Abdul da Farha suma aka kun na masu waƙar suka kama hannun su suna rawa suna sha Abdul rawa Farha rawa suma anzuba masu kuɗi sosai.
San nan ka zo kain su Eshan Amira dai juyawa kawai take dan kar ace bata yi shi kam Eshan yi kawai yake yanda yake rawar kwai zai baka dariya.
Wasu ƴan family ɗin Ammi da Abbi Yan funtuwa sai yau zuka iso gida fa ya cika ko ina ka shiga mutane cike daya de Shema Ahmad anan za'a yi taron bikin na shi Eshan ma gidan su a ciki yake ko ina.
Haka gidan su Yusurah suma yau aka yi ƙauyawa day.
Haidar ne ya Kira ta Yana so zasu gaisa da wasu yan uwan shi maza da suka zo daga Kano da wasu abokan shi.
Bayan sun gaisa tayi masu sallama zata tafi haidar ya tsayar da ita
Ya ce "ina zaki je ko fira bamuyi ba."
Yusurah ta ce "wallahi na gaji ne."
Haidar ya ce "Ni kam ban gaji da kallon ka ki ba."
Yusurah ta shagwaɓa fuska ta ce "Please kayi haƙuri abinda nakusa zama taka baki ɗaya."
Tana gama faɗa haka ta shige gida.
Kai kawai ya girgiza.
DAFIN ZUCIYA
BY HIAMEERA43
MON,1SEP 2025
20:38pm
https://chat.whatsapp.com/Jp93APpPrfe9IezRu9zH91?mode=ac_t
*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
"Jajirtattu mu ne ƙarfi zuciya, hikima a magana, jajircewa aiki. Ba mu ja da baya, ba mu faɗuwa. Mu ne tarihi da ake ginawa!" 💪🔥✨
🦚🦋THE NOBLE WRITER'S TEAM🦋🦚
(🦚✊DEDICATION IS OUR STRONG✊🦚)
NA KUSA KAWO KARSHIN LITTAFIN NAN A PAGE DIN GARSHE DUK WANDA YA FAƊA MIN ABINDA LITTAFIN NAN YA KUNSA DA COMMENT MA ZAFI YANA DA KYUTAR DATA KO KATI ALLAH YA BA MA ME RABO SA'A
PLEASE MU SANI ADDU'AR KU DA BAKUNAN KU MASU ALBARKA YAN UWA
Bisimilahi Rahamanur Rahim
Page 55
> Kai kawai ya girgiza ya juya ya koma mota suka wuce.
Sai kusan mangariba su Eshan suka koma gida sai da suka kai kowa ce gidan su san nan suka wuce suma.
> Amira ko da ta koma gida ganin family na ta ya sa ta ji wani irin farin ciki har sai da tayi kuka ganin yan uwa ko ta ina koma kowa da abinda zai kawo na gudum Muwa gaskiya family ɗin Ammi da Abbi sun taka rawar gani.
Wasu daga cikin ƴan uwan Hafsat ma duk sun zo gida dai ya cika ta ko ina tun da nan ake bikin Hafsah da Ahmad ga Amira Kuma shima Eshan kusan za'a ce nan ne Farha ce kawai da ba'a nan za'a yi ba.
> Eshan da Ahmed yanzu an basu security's masu kula da lafiyar su haka ya sa duk inda zasu ji yanzu suna tare da security.
Eshan ne ya kalle su Ahmed ya ce "Allah sarki wai yan zu saura ƴan kwana ki mu rabu mu dai na kwana waje ɗaya ko?"
> Eshan ne ya yi wannan tambayar yana kallon su.
Dariya Abdul ya yi ya ce "haba mana Brother Kar ka damu idan baka man taba gidajen mu waje ɗaya suke kaga ai bamu rabu ba tun da ba nisa mu kayi ba."
> Ahmed ne ya ce "nima kam banga abin damuwa ba farin ciki ma za mu yi kaga Malam ka kwantar da hankalin ka ko shekarae zuwa ka zama Daddy."
Yanda da Ahmad yayi maganar ne yayi mugun basu dariya.
> Cikin dariya Eshan ya ce "wallahi Ahmad kai ɗan iskane Ni ga abin da ya damuna amma kai buri ka kawai yan da zaka zama Daddy kake tuna ni ko kar dai kaje ka kashi masu ɗiya wallahi."
Abdul ne ya ce "to Malam Muhammad zauna kai ta kallon ta kai ta gadin ta."
> Eshan ya ce "ai Ni tun da har kuka ji nayi shuru bana wannan maganar kun san hummm."
Abdul ya ce "ya kayi shuru? Ka ƙara sa mana."
> Eshan ya ce "a bar kaza a cikin gashin ta kawai yo aini idan maganar nan tada min hankali take ji nike kamar na jawo ranar."
Dundu Ahmad ya yi mashi ya ce " amma wannan yaron ko ɗan banza ohk dama shiri kake baka faɗa mana ba shirin me kake wallahi yanzu naje na ce ma Ammi kada ta baka yar ta dan kashi mata ƴa zaka yi."
Hararar shi Eshan ya yi ya ce "kar ka fasa baka ga wance da yasan yanzu na zama surukin shi shiya sa ya ke ta min biyayya dan ya san zan iya ɓata komai."
> Tsaki Abdul ya yi ya ce "kan ka ake ji."
Amira ɗakin ta suka shiga ita da Hafsat dan su samu suyi wanka su huta suna zuwa ɗakin suka ga ƴan mata gusan guda goma wasu na latsa waya wasu na fira suna ganin su suka tasu suka rungume su.
Ita dai Hafsat ta gane ɗaya daga cikin su ɗiyar uncel din ta ce ta wajan mahaifi dan tun da baban ta ya rasu basu ƙara haɗuwa ba duk da an dau ka lokaci.
> Murmushi zainab ta sakar ma Hafsat ta ce "fatan kin gane ni?"
Hafsat ta mai da mata murmushi san nan ta ce "eh nagane ki."
Dariya tayi ta ce "to ma sha Allah wannan ɗiyar uncel Abba ce wannan kuma ƙanwa ta ce."
Nan ta gabatar da sauran.
> Hudu daga ciki ƴan funtuwa ne Amira ta gani su da ɗiyar Yayar Ammi sai ɗiyar ƙanwar ta sai kuma ɗiyar Yayan Abbi da ta biyo su dan sauran sai ana jibi biki za su zo.
Dariya Amira tayi ta ce "ashe da gaske kuke zaku zo."
Ɗaya daga ciki ta ce "haba kina tunanin ba zamu zo ba to gamu munxo."
Dariya su ka yi Amir ta ce "tun yaushe ku ka iso?"
Nabila ta ce "wajan ƙarfi 5:30pm."
Amira ta ce "shine baku ce a kai ku wajin ƙauyawa ba?"
> Mariya an sallame ta har sun koma gida aka gyara mata ɗakin Ladidi aka yi yan zu ta natsu kullun cikin idaba ta ke yi na roƙon Allah ya yafe ma mahaifiyar ta san nan itama Allah ya bata miji na gari indai zai kula da ita kuma me addini za ta zauna dashi alhamdulilahi yanzu cutar ta warke dama can ba wani yawa tayi ba.
Zuwaira ta dage tana kulawa da Mariya kamar yarda tayi alƙawari dan yanzu kusan komai Mariya zata yi sai ta nemi shawarar ta yanzu ita ce ƙawar ta abokiyar shawarar ta.
Shima Malam Sa'idu yan zu hankalin shi ya kwanta sosai duk da a kullum ya tuna da abin da Ladidi tayi sai yaji ran shi ya ɓaci amma sai ya ɗanne ya nima mata yafiya wajan ubangiji.
> Yusurah bayan ta koma gida ɗakin ta ta shige cikin ƙawayen ta sun ta fira wasu na bata shawara akan ta riƙe mijin ta yanzu mazaje wahala suke tayi mashi biyayya wasu kam cewa suke yi zasu zo gashi idan an gama komai sun sa Yusurah gaba gashi ita ta rasa yanda za ta yi masu kawai sai ta fashe da kuka su kuma suka sa dariya wata daga cikin su ce ta ce "ai ni banga abin kuka a nan ba koda yake kukan daɗi take yi."
Wata kuma ta ce "ku ka sani kukan rabuwa da gida ta ke yi..
Sa'adatu warda suke ce ma ta batulu ita ce tayi saurin ce wa "a'a fah ni na San kukan da take dan wannan mijin na ta daga gani zai yi jaraba kuma wallahi na san ba zai raga mata ba dan na san manta wa zai yi da soyayya ya tumurmushi sakin sa."
Dariya suka kwashi ta ita yusurah kam sai ta tashi tana kai mata duka
> Pending Amarya ce ta ce "kinga Malama gaskiya aka faɗa mana wama ya sani ko kukan ƙosa wa kike dan na san ki da jaraba kema sai ku haɗu ku ta cuɗa juna."
Ganin Yusurah tayi ban za da su yasa suka gaji suka ga ma.
Umma yan zu Alhamdulilah haukan nata yayi sauƙi saboda Malami aka dauko na addini suna mata karatu dan ana so ita ma a san abin yi.
Washe gari
Yau za'a yi Fulani day ta bangaren ko wace amarya za'a yi a wani gidan gonar Abba da ya Bama Eshan shi Abba ya ce ma shi "akwai ɗiyar abokina suma anan gidan gonar za su yi nasu sai ku haɗu kuyi a tare."
Eshan ya ce "shike nan dama kuma Abba Ina son muyi magana."
Abba ya ce "ina jin ka."
Eshan ya ce "akwai security's mota uku zasuna kulawa da lafiyar ka duk inda zaka je suna tare da kai."
Dariya Abba ya yi ya ce "haba Muhammad kada ka wani damu kan ka da wasu security's Allah zai tsare ni."
Eshan ya ce "duk da Allah ya ke tsarewa amma Abba ka daura kaga an kusa mana ƙarin girma dole kowa na kusa da ya kasan ci cikin tsoro saboda maƙiya."
Numfashi Abba ya sauke ya ce "Tom shike nan Allah ya tsare mu baki ɗaya kuma ya taya ku riƙon wannan miƙami da za'a ba ku."
Ciki da jin dadi Eshan ya amsa da "amin dan shi babban abin da yafi so a rayuwar shi iyayen su suyi mashi addu'a sheke birgi shi koma yan alfahari da hakan."
Sallama su kayi kowa ya kama gaban shi.
> Gidan su Ammi ya ƙara haɗawa da mutane yo Kam bikin mutum uku wasa ne.
Tun wajan ƙarfi biyu aka fara shiri dan da anyi la'asar
za'a fara daukar mutane zuwa inda za'a yi.
Amir kam komai zai yi da ƴan uwan shi ya ke yi yaran Umma abin sai wanda ya ga ni komai tare aka yi masu hatta kayan da zasu sa da takalma komai kala ɗaya abin dai sai son barka.
Bayan la'asar abinku na manya ba'a afirecan time karfi huɗu dai dai motoci suka zo na alfarma ko wace mota bayan ta akwai motar sojoji motoci ne iya ganin ka dan ko ni ban san iya yawan su ba.
> Motar amarya ta daban ce mota ce kamar jirgin sama dan har tashi take sabowa ce dal harda lidar ta ba'a cire ba amarya aka fara sawa a motar tana shiga taga Eshan a ciki ya san ya kayan Fulani rigar su da hula sai sanda a hannu shi tun da ta shiga ya kafe ta da ido ganin kallon da ya ke mata yasa ta ce "ta ce ƙado."
> Wata dariya ce ta zo mashi aikam ya kama yi ya ce "wallahi kayan Fulani sun yi maki kyau Amma kuma babu abinda kika sani sai kaɗo."
Murguɗa mai baki tabyi ta ce "ai dai nayi ko."
Ganin yan da ta murguɗa mai baki ya sa ya ce "humm ina tausaya maki du ranar da muka haɗu zaki gane sha yi ruwa ne Ni kike murguɗa ma baki ko?"
Jin maganar da ya dauko ya sa ta ce "a'a kayi haƙuri Ni dai."
Ya ce "bazan hakura ba sai kin faɗa min kalma me daɗi."
Shagwaɓa fuska tayi ta ce "Yayana kuma mijina."
Akam yaji daɗin maganar ya washi baki kamar gonar audiga.
> Bayan Amira ta fito aka fito da Hafsat itama cikin shigar Fulani aka kai ta mota kalar wadda aka sa Amira ta na shiga itama taga na ta gogan sanye da Kayan Fulani ƙurawa juna ido suka yi suna kallon juna kusan minti 2 san nan ya ce "kallon fa?"
> Hafsat ta ce "naga shigar tayi maka kyau."dariya ya yi ya ce "amma ban kai ki ba ko?"
Abdul shima yana can da tashi tawagar gidan su Eshan suna jiran a fito da amarya da wainda zasu je dan sai sun je wajan su Eshan san nan su wuce tare.
> Farha ce aka fito da ita cikin shigar Fulani itama Ma sha Allah tana shiga ta ga Abdul da kalar shigar baki ta saki na kallon shi ta ce "baka ga yan da kayan nan suka yi maka kyau ba Allah kamar ɗan fulanin gaske wanda zaije kiwo.
> Dariya yai ya ce "Allah ko nayi kyau to muyi PHOTO suka yi photo nan su kafin agama shirya wa.
Bayan sun gama motoci ne a jure ke tafiya har suka ƙara so ƙofar gidan Abbi aka matsa ma motar amarya ta shiga bayan ta su Ahmed ana gama shirya wa komai a tsari san nan suka tafi.
> Ma sha Allah wajan ya haɗu an ƙawata shi da bukoƙi ga shanaye a wajan ga wasu na tsar nono nan shanaye ga wasu kuma na dakan fura ga zabi na taya wo kai Ma sha Allah abu kamar a rugar gaske.
San dan da suka isa sun iske zugar motocin su Haidar na jiran su dama tunda Abba ya ce akwai ɗan ɗan abokin shi da zasu yi a ciki Eshan ya neme numbern haidar suka tsara
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 11 Chapter of 14