Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ya ce "ana ne manku daga ciki." Baba ya ce mashi "bisimilah muje." Sanda suka shiga cikin kotun duk wani wanda ke da labarin mutuwar shi sai da ya razana! Ladidi ganin Boka yana neman yi ma wulaƙan ci ya sa ta ce " Allah ya isa banza ɗan iska ɗan damfara kuma wallahi sai na kawo karshin ka." Wata shigiyar dariya Boka ya yi ya ce "mu zuba mugani idan kura na maganin zawo tayi ma kan ta mu gani." Daddy yace "kai yau Haidar ne agidan?" Cikin jin kunya ya ce "dama nazo wa jan yu su rah ne....." Ya faɗa a rairaɓe. Cikin farin ciki Daddy ya ce "shi ne baka faɗa min ba?" Yana sosa ƙeya ya ce "kayi haƙuri Daddy." Daddy ya ce "ma yusurah ta zauna." Bayan ta zauna yayi addu'a san nan ya kalle yusurah ya ce "kina son shi?" Jin tambayar da Daddy ya yi mata tayi ƙasa da kanta ta kasa cewa komai. Daddy ya ce "to alhamdulilah shurun kiya nuna min kina son shi." Sanan ya koma kan Haidar ya ce "kana son ta?" Shi kam babu kunya ya ce "eh Daddy Ina son ta Kuma zan aure ta." Shi kanshi Daddy amsar da Haidar ya bashi sai da ya ji kunya. Daddy ya ce " to alhamdulilah naji daɗi sosai Allah yayi maku albarka." Duk suka amsa da Amin. Daddy ya kalle Haidar ya ce " na baka dama ka aiko da magabatan ka." KOTU Kai tsaye wajan binci ya tsaya idan ake tsayawa cikin natsuwa ya fara bayani. Nan fa jikin kowa ya ƙara yin sanyi. Barester Kamal ya ce "ina so kotu ta bani dama nayi magana da Malam Umaru." Alƙali ya ce "wannan kotu me Albarka ta baka dama." Cikin iya makirci Barester Kamal ya ce "duk wannan abinda ya faru kana nufin baka sani ba?, Ko kuma baka da damar da zaka iya takawa matar ka birki akan abinda tayi ba daidai ba?" Malam Umar yayi murmushi ya ce "tabbas duk abinda ake min wani na sani bana iya yin magana koda nazo zan yi magana sai kaina ya yi min nauyi wannan dalili ya sa wasu mutane ke cewa akwai asiri a jikina amma ban taɓa yarda ba" Wani abun kuma bansan ina yin shiba. A ranar ƙarshe da muka yi faɗa da ita wanda ya sa na fita aranar suka sa Malam Sani ya je ya buge ni da mota na mutu,. Ni kuma a lokacin da na fito da niyar na bar garin baki ɗaya sai Mansur ya sameni ya ce "min yana da gidan da yake ganawa zan iya zama acan kuma zai kular min da komai nawa, Bayan na aminci ya kaini gidan shi ya dinga kular min da komai nawa ba a daɗe ba shima ya zo min hankali tashi wai shi ma ana so a kashe shi, Eshan ya kira Abbi ya ce "sunan gida sheda abokan shi." Abbi ya ce "yana zuwa dama ba nisa yayi ba." Bayan suna gama waya Amir ya ce "mu shiga falon Abbi." Bayan sun shiga Amir ya kawo masu ruwa da abinci ya ce "ga abincin Yaya nan Allah ya sa abincin yayi daɗi." Eshan ya ce "ai kam baku cin shi kuma dani kuke magana." Amira naje sun shiga falon Abbi ta kira Hafsat a waya ta ce "tazo gida gabe zasu tafi wajan Ammi." Hafsat najin haka ta ce "ganinan zuwa." Ladidi cin ɓacin rai ta fita daga gidan boka tana ai yana abinda za ta yi mashi kuma tayi da na sanin wanan rayuwar ta ta kai tsaye gidan su ta wuce Yayan ta yayi mamakin ganin ta sai yanzu ma ya lura da change dake jikin ta dan cikin ta har ya fito kuma ga rama da tayi cikin mamaki ya ce "ya dai lafiya ki ka shigo a harziƙe?. Haidar bayan sun gama magana da Daddy ya ce " bari na shiga ciki"? Daddy na fita ɗakin Haidar ya taso ya koma kusa da yusurah ya ce "ɗago ki kalle fuskar angon ki ko kunya ta kike je ne." Cikin sanyin jiki ta ɗago suka fawa yi ma juna kallon soyayya cikin nishaɗi ya ce "soyayyar mu ta daɓan ce kamar yanda ke ka biyo wajan nuna min soyayya a ɓoye tunkan na ganki naji kin kwanta min a rai dana ganki kuma sai naji na mutu akan soyayyar ki. Yusurah bata san sanda ta sauke wata ajiyar zuciya ba. Hafsat ce ta shigo cikin gidan da sallama cikin natsuwa jin hayaniya a falon Abbi ya sa tayi tunanin ko suna cikin falon cikin natsuwa tayi sallama,. Ahmad cikin natsuwa ya ɗago yana kallon ta san nan ya amsa sallaman ta shiga suka gaisa dasu Eshan, Bayan sun gaisa take cema Amir "ina Amira ya ce tana ɗakin ta." Cikin natsuwa ta tashi ta shiga ɗakin Amira ta same ta tana danna wayar ta da Abbi ya bata karamar waya ce amma bata ji jiki ba. Da gudu ta shiga ɗakin ta amshe wayar cikin jin haushin wanda ya amshe mata ta ɗago ganin Hafsat ce ya sa ta maka mata harara ta ce "Malama lafiya zaki amshe min waya." Hafsat ta ce " ban sa ni ba baki san kinyi baƙo ba?" Amira ta ce "na sani haushe ya bani shi yasa nayi mashi shuru." Hafsat ta ce ma ta"gaskiya ba haka ake ba ki tashi ki tafi dan kin ga ya damu dake ko to bari yayi maki yaje." Ahmad bayan fitan Hafsat ya bita da kallo sai da Eshan ya buge mashi baki ya ce "lafiya ka wani saki baki kana kallon ɗiyar mutane." Abdul ya ce ma Amir "je kace ma Amira tazo Ina kiran ta." Amir ya tashi ya tafi ya na shiga ɗaƙin ya same su suna dariya kome suke ma dariya oho. Amir ya ce "kuzu ana kiran ku." Amira ta ce kaje kace muna zuwa." Bayan fitar Amir sai da amira tayi shafa san nan suka fita DAFIN ZUCIYA BY FATIMA BINTU HUSSEN https://chat.whatsapp.com/CBtvAeshrDyAlqXRA7d4sM *https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ *(J.W.A)* _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ YA ALLAH YAN UWA KU TAYANI DA ADDU'A DA BAKU NAN KU MASU ALBARKA YAU INA DA JARABAWA IN SHA ALLAH PLEASE ASANI ADDU'A A SALLA ALLAH YA BANI SA'A DA WAINDA MUKE YI BAKI ƊAYA Bisimilahi Rahamanur Rahimi Page 45 Amira da sallama suka shiga falon Abbi tunda suka shiga Ahmad ya tsare Hafsat da idanu kamar wani maye. Yusurah jin abin da Haidar ya ke faɗa ya sa ta saki baki tana kallon shi. Cikin mamaki ta ce "kada ka yaudare ni da daɗin baki." Cikin mamaki ya ce "wallahi babu daɗin bakin da zan maki inda ban sonki to bana sanki kuma da ban ban kamu da sonki ba ba za ki ganni anan ba." Yasurah ta ce "to Allah ya zaɓa mana abinda yafi alƙairi." Haidar ya amsa da "Amin." KOTO Cikin natsuwa Baba yake yin bayanin shi wanda da ka gani ka san babu karya a ciki san nan a iya gariman shi da haibar dake fuskar shi ya wuce da ya yi ƙarya. Kowa ya gamsu da bayanin da yayi wanda hakan ya sa lauyoyinsu Umma cikin su ya yi sanyi bayan Baba ya gama bayani aka ɓuƙaci su kawo shiɗarsu. Eshan she ne ya amsa sallaman da su Amira su ka yi dan shi Ahmad ya shagala da kallon Hafsat shi kuma Abdul hankalin shi yana kan waya suna chat da Farha. Bayan sun shiga sun zauna suka fara gasaisawa. Eshan ya kalle Amira ya ce"ai ni fushi nike da ke?" Amira ta shgwaɓe fuska ta ce "Haba Yaya me nayi? ai nice nike fushe da kai ma." Eshan sankare wa yayi ganin yanda Amira ke zuba mai shagwaɓa. Da kyar ya ce "to bake bace za ki tafi ki barni ba." Cikin jin tausayin shi ta ce " nima bana so na barka. Ina so naga Ammi ina kishin ruwan ganin ta ina begin ganin ta inason naji muryar ta Ina son naje ɗumin jikin ta wallahi Ina kewar ta ban san irin farin cikin da zan yi idan na ganta ba." Ta ƙarshi maganan da saƙin wani irin kuka me cin rai ganin kukan da take ne ya sa Amir ya zo ya rugume ta shima ya na saƙin nashi kuka ya na cewa "munyi kewar Ammi muna son ganin ta ko ki daina kuka in Sha Allah gobe kamar yanzu muna tare da Ammin mu." Sosai suka basu tausayi da sha'awa. Eshan ya ce "nima za'a je dani wajin Ammin ko?" Yayi mata tambayar in serious. Amira ta ce "ai na san baza ka je ba?" Yayi dariya ya ce "in Sha Allah dani za'a je ni zan kai ku ina so naga irin farin cikin da zaki yi idan ki kaga Ammi ina son naga farin cikin nan a gaba na." Amir ya ce "Yaya da gaske ka ke?" Kafin Eshan ya bada amsa Abdul da Ahmad kamar haɗin baki duk suka ce zasu je. Amira farin cikin da suke ciki baya musal tuwa gani suke kamar a mafarki dama suna da masu son su haka da zasu ajeye komai da kowa nasu dan so biso suga mahaifiyar su. Abbi ne yayi sallama ya shigo su duka suka amsa mashi ya shiga falon ya zauna suka gaisa san nan Abbi yake sanar masu da maganan tafiyan a nan ne Eshan ya ke sanar masu da suma zasu je sosai Abbi yayi murna kuma Eshan ya ce "in Sha Allah gobe mu zamu kai ku da motocin mu." Abbi ya ce "bana so na ɗura maku hidima idan bakuda hali ku bar shi." KOTO Baba ya ce "ina da sheda shi ne me motan da suka tura ya bi ta kaina." Alƙali ya ce "ida wannan bawon Allahn ya na kusa ya ƙara so domin jin ta bakin shi?" Da ga inda ya ke zaune ya tashi ya ƙara sa wajan Mama ga nin komai take a mafarki ya za'a ce wannan abin da ke faruwa a gaske ne. Bayan ya ƙara sa wajan cikin natsuwa yayi sallama san nan Barester Kamar ya ce "ka ce kaine wanda suka tura ka kashe Baba? Ya ce "eh nine." Barester Kamal ya ce "ko zamu iya sanin dalilin da ya sa ka fasa kashi su Baba bayan an biya ka kuɗin aikin ka da komai"? Mai mota ya ce "eh hakane sun bani kuɗi akan na kashi shi bayan na koma gida sai ga kiran su wai ya fita na bishi a baya baya haka nai ta binshi har suka haɗu da Mansur na tafi kansu na bigi su duka amma cikin ikon Allah hakan bata faruwa nan dai ya faɗa masu yanda komai ya faru da ga in da suka yi magana da Mansur har zuwa yanzu." Barester Jamal ne ya tashi ya ce "ko wannan shiɗar ya isa agane ba ƙazafi aka yi masu ba kawai aba ma me gaskiya gaskiya abama mara gaskiya hukuncin da yakama ta." Barester Kamal Kam yayi shuru dan shi yanzu bai san me zai ce ba. Alƙali ne ya ce ma Mama idan tana da sheda ita ma zata iya kawowa dan babu yanda za'a yi shara'a ta bangare ɗaya ba'a saurari ɗaya ba dan haka alƙali ya ce anɗaga Shari'ar "sai nan da sati ɗaya me zuwa." Daga nan aka watsi amma kuma an gargami Mama da Umma. Please kuyi haƙuri da wannan DAFIN ZUCIYA BY FATIMA BINTU HUSSEN https://chat.whatsapp.com/CBtvAeshrDyAlqXRA7d4sM *https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ (J.W.A) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️* Bisimilahi Rahamanur Rahim Page 46 Eshan bayan sun daidai ta da Abbi akan zasu yi tafiyan tare. Amira sosai abin ya ƙayatar da ita gakuma wayan da Eshan ya bata ba ƙaramin daɗi taji ba. Ahmed shima sun sai ta da Hafsat ida suka saita kuma babu musu Hafsat ta aminci yaji daɗin hakan sosai. Hafsat haka nan taji ya kwanta mata arai hakan ya sa bata yi ƙasa agwaiwa ba wajan amince mashi kuma nan take ya bata waya inda itama ta ce zataje wajan Ammi. Koda Amira ta ji itama Hafsat ta ce zata je saboda murna tarasa inda zata sa kan ta sha kam Amir ma ba'a magana dan shi cewa ma ya yi su Yaya Eshan zai bi ya kwana. Hafsat koda ta koma gida ta faɗa ma Maman ta bata hana ta zuwa ba saboda tasan yanda suke da Amira dayake Baban su Hafsat din ya rasu hakan ya sa komai yan uwan ta ne ke kula da ita dan ma Allah ya sa sunda rufin asiri. Umma tunda aka ce za'a rufe su a kargame ya sa hankalin ta ya tashi sosai har tayi dana sanin zuwan ta garin. Yusurah soyayya suke sha sosai da Haidar babu kama hannun yaro ko yanzun ma suna tare. Haidar ya kalle yusurah ya ce "gaskiya Beby na bana gajiya da kallon ki amma har yanzu kin ki ki sake dani?" Yayi mata tambaya cikin shagwaɓa wanda ya sa yusurah ta ɗago da kanta ta na kallon shi ganin kallon da take mashi sai ya ɗaga mata gira guda ɗaya alaman tambaya? Eshan tare da Amir suka tafi suna isa gida suka je wajan Mame suka gaisa bayan sun gaisa take tambayan waye wannan? Eshan ya yi mata bayanin ko waye sosai Mame ta ji daɗi har take yi ma Amir wasa ta na ce wa "baza'a je da kai ba tare da kai zamu zauna." Amir maƙe kafaɗa ya yi alman be yarda da maganan ta ba dariya tayi ta ce mashi "to shikenan tunda baza zauna da muba." Eshan ne ya ce "Mame Albishirinki." Harara ta watsa mashi san nan ta ce "kai dalla bar ni da wata gulmarka can Malam ka dameni." Ji yayi kamar ya fasa kuka jin abin da ta ce mashi. Cikin shagwaɓa ya ƙara ce wa "Please mame ki saurare ni." Mame ganin ya takura mata ya sa ta ce "ina jin ka." Ya ce "magana ta farko ni da Ahmad na ne mana taransupar mu ta fyanzu aikin mu ya dawo Abuja. Ba mame ba har Ahmad sai da ya kalle shi da mamaki dan shi bai san da wata maganan taransupar ba hassali ma idan yayi mashi maganan su ne ma sai ya ce a'a nan yafi besan dalilin da yasa ya chanza shawara ba. Washi gari Babu wanda ya san da Farha za'a yi tafiyar ba sai da suka ganta da akwatin ta hakan ya sa kowa ya kalle ta da mamaki. Eshan ya ce "Malama ina zaki?" Kallon shi tayi san nan ta ce "ai ƙafa ta ƙafan Yaya Abdul." Dariya Abdul ya yi ya ce "yawa beby na dama kamar kin san zan yi kewarki." Eshan ya maka mai harara san nan ya ce " ita kuma Mame a barta dawa?" Daga bayan su suka je Mame na cewa "babu komai ku yi tafiyar ku ban damu ba nima sai mu sha ƙauna da mijina." kunyar duniya ta kama su babu wanda ya iya wata magana duk suka shiga mota suka yi mata sallama daman sun riga sun yi da Abba hakan ta sa suna fita kai tsaye kai tsaye suka wace gidan Abbi. San da suka isa kowa ya shirya babu wani bata lokaci suka firfito da kayan su. Inda Amira da Farha da Hafsat suka shiga motan Eshan Amira ce a gaba sai su Hafsat a baya idan Abbi da Abdul suka shiga motan Ahmad da Amir suka kama hanyar Katsina ta dukko ɗakin ƙara kunya gare mu ba tsaoro ba TO SU ESHAN SAI DA MUCE ALLAH YA KAIKU LAFIYA DAFIN ZUCIYA BY FATIMA BINTU HUSSEN https://chat.whatsapp.com/CBtvAeshrDyAlqXRA7d4sM *https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ (J.W.A) _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajir ILIMIN HASKE NE SANAN KUMA JAHILICI DAHU NE TUNANI ME KYAU BAIWA NE RASHIN TUNANI KUMA CIWO NE KYUTATAWA A KULLUM ARZIKI NE ITA KUWA ROWA MUSIBA CE ZAMAN LAFIYA A KULLUM WALWALA NE SHE KO RASHIN ZAMAN LAFIYA KUN CI NE ITAFA IBADA GUZURI CE RASHIN YIN IBADAR KUWA AZABA NE Bisimilahi Rahamanur Rahim Page 47 Amira tunda suka fita Abuja gabanta ke faɗuwa ta rasa dalili she kanshi Eshan ya lura da haka. Hafsat ce ma suke ta fira da Farha. Can motar su Ahmad ma fira suke Abbi Ya na ta yi masu addu'a suna ta fira. Abdul ne ya ce ma Abbi "Dan Allah Abbi ko zamu iya sanin wani abu game da Hafsat?" Ahmad jin tambayan da Abdul ya yi ma Abbi ya sa yayi ƙasa da kan shi yana jin kunya. Abbi ya ce "gaskiya abinda zan faɗa maku shine bata da wata matsala san nan ta na tarbiya da hankali. kuma mahaifinta mutumin kirki ne." Sosai Ahmad ya ji daɗin jin yanda ake ta yabon Hafsat. Abdul ne ya ce "ma sha Allah gaskiya mun ji daɗi yanda ka ke ya ba wa da tarbiyan ta." Abdul ne ya ce "daman Ahmad ne ya ganta kuma ya na son ta." Sosai Abbi ya yi murana dan ya tabbata Shema Ahmad mutumin kirki ne FUNTUWA Ammi ce a kicin ta dafa wannan ta dafa wance murna ta ishe ta gani take komai kamar a mafarki wai yau ita ce zata ga Amira da Amir bugu da ƙari kuma harda wasu ƙarin mutane da suka samu.. Umma bayan an kaisu gidan gyran hali an kulle su sai suka yi sa'a aka haɗa su ɗaki ɗaya. Suna zaune Umma ta kalle Mama ta ce "gaskiya ni na yi dana sanin biye maki. Kuma idan aka zo zama na gaba zan faɗi gaskiyar komai duk abinda za'a min sai dai ayi min kuma da na fita daga nan kai tsaye zan kuma gidan mijina na gyara zaman mu mu rungume yaran mu." Mama ce ta kalle ta ta ce "hummm Ummul kairi nima kai na nayi dana sani." Yusurah yau aka kawo kuɗin auren ta da Haidar sosai tayi murnar daga ka ganta kasan tana cikin farin ciki da wal wala. Mommy jikin ta ya yi sauƙi sai da muce Alhamdulilah dan an basu sallama sun dawo gida. Ladidi ce zaune gaban Yayan ta ta na kuka bayan Malam Sa'idu ya gama mashi bayanin abinda ta ai kata sosai ya yi baƙin ciki yaji inama ace Ladidi ba yar uwar shi ba ce ina ma ace baizo duniyar nan ba ya rasa me zai yi kawai sai ya fashi da kuka. JAN HANKALI YAKE YAR UWATA YA KAI ƊAN UWANA MEYE AMFANIN WANNAN RAYUWRAR KAZO KANA ABIN DA ALLAH YA HARAM TA AMMA MUN DAUKE SHI SHENE ABIN YI A WAJAN MU ABIN DA ALLAH YA UMARCE MU DA MUYI MUN WATSAR BAMU TSORON MU BAR MA YARAN MU Yayan Ladidi ya ma rasa me zai yi kawai sai ya kamata da dukan ta yake ya na surutai alman ya fita daga haiyacin shi. Malam Sa'idu ganin duka banayi bane ya kama shi ya na shafa bayan shi cikin lalashin ya ce "duka ba shi bane in har dai muna so muji wanda ya yi mata ciki to sai dai mu bita a hankali." Yaya jin maganan Malam Sa'idu sai jikin shi ya yi sanyi. Eshan ganin shurun Amira ba me ƙare wa bane ya sa ya ce "me yake damun ki?" "Babu komai." Ta bashi amsa. Farha ce ta ce "sister ya da wannan rayuwar kin yi mana shuru kamar ruwa ya cinye ke kodai Ya Eshan ne yai miki wani abin?" Murmushi ta yi ta ce "ba bu komai ina tunanin wani hali zanga Ammi." Farha ta ce "in Sha Allah lafiya lau za mu ga Ammi karki sa ma kan ki damuwa." Daga haka suka ci ga ba da fira. Ammi ta na can gida ya cika da mutane kowa ya na taya ta murnar dawo War yaran ta. Zamfara Gidan su Umma duk wanda ka kalle fuskan shi zaka fahimci ya na da damuwa shi kan shi Mansur ya shiga damuwa. Abbi kam ya ma manta da wata Umma can dan yasan idan ta gaji zata dawo da kanta. Haidar ne zaune a gaban Mama suna fira akan kuɗi aikin da aka kai na yusurah. Mama ta ce "gaskiya wainan mutane suna da kirki duba kaga kalar tarbar da aka yi ma yan uwanka." Murmushi ya yi ya ce "nima nayi mamaki Mama." Hafsat kam chat suke da Ahmad ya ce mata "ko zata dawo motar su yana so ya ganta?" Hafsat ta ce "so kake ace bani da kunya ko?" Eshan ganin motar Abdul ta wuce ta su ya sa ya fisgi motar shima da mugun gudu dan ya san da biyu Abdul ya yi haka. Abbi ganin Eshan ya wuce su da mugun gudu ya sa ya tambaya "lafiya kam naga Muhammad yana wannan gudun?" Ahmad ne ya ce "ai shi wani lokacin haka yake gudu sosai." Abbi ya ce "Allah ya kyuta ni kam sai nayi mashi faɗa ya dai na wannan gudun." Ladidi cikin daka tsawa Yaya ya ce "ina tambayan ki waya yi maki ciki?" Ladidi ta ce "abin da zan faɗa maku kan ku bazai iya dauka ba shi yasa bazan iya faɗa maku ba." Yaya ya na mamakin taurin kai kalar nata dama har yanzu tana da wannan kafiyan. WELCOME TO FUNTUWA Amira ganin wannan sanbol ya ƙara sata cikin faɗuwar gaba har sai da ta ambaci sunan Allah. Amir kam murna yake har da cewa i miss You wallahi nayi kewar garin nan. Eshan waya ya kira Abdul ya ce "yazo yayi gaba tunda suna tare da Abbi kuma shi ya san gidan." Abdul ya shiga gaban Eshan Abbi na nuna masu hanyan. Sanda suka isa kofar gidan ya yi daidai da isowar Yaya Muhammad daga makaranta ya samu hutu ya dawo. Amira na cikin mota ta hango shi zai shiga gida ta kwala mai kira. A ɗari uku da sitin ya juyu dan bazai taɓa manta Muryar yar uwarshi ba kuma abin son shi abokiyar faɗan shi. Sororo yabi motan ta kallo har san da suka gama paking Amira ce ta fita da gudu tayi wajan shi shi kuma Yaya Muhammad ganin gaske ita ce ya sa yayi watsi da kayan shi ya taho yayi kan ta shima. Amir kama ya na fita ko kallon Su Yaya Muhammad be yi ba ya ruga da gudu yayi cikin gidan yana kiran "Ammi" Ammi ina kika shiga gani? Ammi na ɗaki jin Muryar Amir ta fito da gudu tayo kan shi kafin ta ƙara sa taja ta tsaya tana kallon Amir ganin kamar bashi ba ya rame ya fita haniya cin shi a hakan ma wai sun samu sauƙin rayuwa. Amir ne ya ce "Ammi baki murna da ganin mu ko?" Jin tambayan da yayi mata ya sa ta ƙara sa wajan shi dan dan da ta tsaya shima sai ya tsaya ƙara. Da gudu Ammi ta ƙara sa ta rungume shi tana sakin kuka me cin rai. Amira ganin mutane sun zagaye su anata kallon su yasa ta kama hannun Yaya Muhammad suka shiga ciki ganin Ammi da Amir rungume suna kuka itama ta ƙara sa ta rungume su tana kuka. Eshan ya na can ya kumbura ganin wani ya rungume Amira ya na ta huce. Yaya Muhammad ganin Ammi ta ma manta da baƙin da ke waje ya ce ma Ammi "bari nace ma wainda suke tare su shigo." Abbi tunda suka iso hankali shi ya tashi ya ma kasa fita daga motan Addu'a kawai yake Allah ya kawo mai sauki akan tambayoyin da Ammi za tayi mashi DAFIN ZUCIYA By Fatima Binta Hussain MRS NASIR https://chat.whatsapp.com/CBtvAeshrDyAlqXRA7d4sM?mode=ac_t *https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ *(J.W.A)* _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ 🦚🦋THE NOBLE WRITER'S TEAM🦋🦚 (🦚✊DEDICATION IS OUR STRONG✊🦚) Alhamdulilah Allah na gode maka da ka bani ikon cigaba da rubuta wanan littafin ya Allah ka bani ikon gamawa lafiya ina me miƙa godiya ga wainda ku ka ƙarfafa sani gaba akan na ida wanan litattafin na gode sosai Allah ya saka da alheri Bisimilahi Rahamanur Rahim Page 48 Abbi tunda suka iso hankalin shi ya tashi yama kasa fita daga motan Addu'a kawai yake Allah ya kawo mai mafita dan ya san zai sha tambaya wajan Ammi. Yana cikin wannan tunani sai ga Yaya Muhammad ya zo ya buɗe motan. Jiki a sanyaya ya ce "Abbi ina wuni fatan kun zo lafiya ya hanya?" Jikin Abbi ba ƙaramin sanyi ya yiba hankalin shi duk

Chapter 8 of 14