gidan ganina cikin tashin hankali nace sun kashi min Baba na suma cikin tashin hankali suka ce me kake nufe ya ce wani me motane ta takashi kuma gawar bata ganuwa daga can an rufe shi ko wanka ba ayi mashi ba iya tashin hankali sun shi geshi amma su Umma sun nuna tashin hankali ne saboda kada wani ya zarge su,
kwana biyu da rasuwar shi su Umma suka tada fitina araba gado jin abinda su Umma suka ce ya sa na fara shirin kwashi duk wata dukiya ta mahaifina babu wanda yasan bai mutu ba sai ni kaɗi sai wasu abokan aikin shi bayan yaje wajan Baban ya faɗa mashi su Umma sun fara maganan rabon yasa hankalin Baba ya tashi hakan ya sa ya ce ma Mansur ya na so ya kwashi duk wani abinda yake nashi ya dawo dashi hannun shi haka Mansur yaje yayi aikin nan cikin sirri babu wanda ya sa ni rana guda aka tashi da wani abun al'ajabin duk wani abinda Baba ya mallaka babu komai an kwshe su Umma sun so su tada fitina amma ganin babu wanda ya biye masu ya sa suka haƙura suka bar maganan amma basu hakura a zuciya ba
DAFIN ZUCIYA
BY FATIMA BINTU HUSSIN
https://chat.whatsapp.com/CBtvAeshrDyAlqXRA7d4sM
*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
PLEASE KU YI MIN ADDU'A BANDA LAFIYA
Page 40
Bisimilahi Rahamanur Rahim
Mama da Umma su har ga Allah basu yarda da kwashe dukiyan Baba aka yi ba su suna zargi da sa hannu wani haka suka shirya suka je wajan boka amma abin da basu sani ba duk wani motsin su ina kula da shi.
Haka rayuwa ta ci ga ba da tafiya in da ni da Baba muke kula da dukiyar shi nima har Baba ya ce na kawo wani abu dan a haɗa mu ƙara ma kasuwan cin ƙarfi haka na haɗa duk wani abu da nike dashi na Bama Baba muka haɗa hannu cikin ikon Allah Allah ya sa mana albarka yanda ba mu yi tunani ba,
Wata rana naje gida da yamma ba bu kowa a gidan sai Mama tana ɗaki tana waya abin da naji ya tada min hankali,
Naji Mama na waya da Umma akan ni ma za su kashe ni kuma su kwashi abin da na ke dashi daga nan sai su yima sauran mutanan gidan asiri dan a rufe baƙin su,
Alƙali ya ce "ɗanyi haƙuri duk mutune biyu ke wannan aikin? Kuma ace uwa da yar ta me ya sa tunda ta ne mi kashe mahaifin ku baku ɗau mataki ba?"
Wani Murmushi me cin rai Mansur ya yi san nan ya ce " kada ka manta ina cikin baka labari ne za ka ji komai."
Alƙali ya ce "ciga ba."
Tana ta maganan ta da yanda zasu shirya yarda za a kashe ni sai wata dubara ta zomin,
Na ɗauki wayata na kunna record ina yi babban abin da ya tada min hankali shine yanda suka shirya idan sun kwashi komai su sama gidan wuta kowa na ciki ya kone, ina jin zata gama waya ya sa ma lalaɓa na fita ba tare da taje motsina ba,.
bayan na fita na samu wasu abokaina amintatuna na faɗa masu komai da yake faruwa?,
nace ina son na ɓoye adaina ganina kwata_kwata saboda waɗan mutane ba imani ne da suba gashi yanzu suna so suga bayana Ina so ku kulamin da family na dan Allah.
Suna amsamin da insha Allah bazu su bani kunya ba
kuma na faɗa masu inda niki ba garin zan bari ba.
Muna gama magana dasu na koma idan Baba yake na faɗa mashi abin da naji da record din da nayi sosai hankalin shi ya tashi!
Ya su ya fita amma sai na samu na ganar dashi akan idan ya fita wani abu zai iya samun shi.
Kusan wata guda ana nemana amma ba a gan niba har an gaji an bar ma Allah Mama babu kalar maganan da bata faɗa ma Mamana har ce wa take natafi yawon duniya
amma Mama na bata mai da hankali kan suba kullum tana addu'a Allah ya baiyanar dani
Su Mama basu fasa zuwa wajan bokayen suba da yan tsubbu da yan asiri amma komai yaƙi yi sai abu ya yi kamar zai yi sai ya ƙi yi
Gashi kwata kwata Mama ta ɓata Umma bata ganin darajar kowa har mijin ta bata ganin girman shi.
Bayan wasu shekaru kasuwan cin mu yayi Albarka kuma duk da haka ina sa hankali akan komai na gidan mu batare da kowa ya sani ba sai abokai na.
Mun saɓa da rayuwar ƙaɗai ci nida Baba duk da muna son mu dawo cikin a halin mu ganin abin na damun Baba yasa na shira fitowa domin na ɗau mataki akan abinda ya faruwa da ma wanda yake faruwa.
Sanda na zo kai tsaye gidan mu na wuce tun a hanya kowa yake kallona da mamaki har wasu na ce min fatalwa amma ban kula kowa ba na wuce gida sanda naje gidan ban samu kowa ba sai wasu ƙanine na tamabaye su ina mutanan gidan su ka ce min suna asibiti,
Nace waye baida lafiya su ka ce Mamace aka harba na kama hanya na tafi asibiti lokacin Mama na cikin hauka hakan ya sa na shiga ɗakin kowa da ke cikin ya yi mamakin ganina saɓanin Umma da ita ba mamaki bane a fuskar ta ba firgice ne,
Ina taƙaice maka ninna ɗau nauyin kula da Mama har ta samu lafiya a tunani na zata yi sauƙi sai naga abinda gaba yayi saboda haka na yanke shawarar zuwa koto a amsar mana haƙin mu aba me gaskiya haƙin shi.
Alƙali numfasawa ya yi cike da Al'ajabin wanan lamari yace ranar goma ga watan 10/9/2014 wanda yaka ma ranar Litinin za a shiga koto.
DAFIN ZUCIYA
BY FATIMA BINTU HUSSIN
https://chat.whatsapp.com/CBtvAeshrDyAlqXRA7d4sM
*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
NA GODE DA ADDU'ARKU ALLAH YA SAKA DA ALKAIRI ALLAH YA BAR ZUMUNCI WANNAN SAHAFIN NA MASOYAN LITAFINA NE
Bisimilahi Rahamanur Rahimi
Page 41
Yusurah tana fita ta ga ba ta ga Haidar ba ganin wata mota kaɗai a layin ta fara tunanin ko shine amma sai wata zuciyar ta ce kai ina zai samu mota mutumin da ko keke baya dashi
Haidar shi fa har ga Allah ya manta da kamanin Yusurah ganin wata na dube dai ya yi tunani ko itace ganin bai da me bashi amsa ya sa ya ɗauki wayarshi ya kira numbern ta ya na kira sai yaga wannan ta wajan ta ɗaga hakan ya sa ya fita ya tsaya jikin motar.
Eshan yau Ahmad ya iso bayan jirginsu ya sauka a aripot suka je suka ɗauko shi kai tsaye gida suka wuce suna zuwa suka iske Mame a falo ita da Farha bayan sun gaisa Mame tace ga" abinci can an shirya masu." Eshan ya ce "bari yayi wanka sai su fito." suka wuce part din Eshan bayan yayi wanka Ahmad ya kalle Eshan ya ce "my man yaushe zamuje wajan mutuniyar ne ?"Eshan ya ce "kai ɗan gulma ina ruwan ka kai zaka sa ni na kai ka?"
Ladidi bayan sun isa gida Malam yaka ma ta yayi mata duka ya ce "sai ta faɗi uban da yayi ma ciki ɗan shi ba zai zauna da mushiri ka ba."
Kuma ya ce "ta tafi gidan su sai ya neme ta kuma idan taje ta faɗi laifin da tayi."
Ladidi babu kalar roƙon da ba ta yi mashi ba amma fafaru ya ce shi bai san da wanan zancan ba.
KOTU
Yau ta kama 10/9/2014
Za a shiga kotu shara'ar da ta tara manyan mutane da ga kan y'an siyasa sarakuna da kuma mutanan gari kowa ya taro inda Mansur ya samu lauyoye masu ilimi da sanin abinda ya kamata kuma suna aiki bil haƙi da gaskiya.
SATI ƊAYA DA YA WUCE
Mama na zaune aka aiko ana kiran ta waje bayan ta fita taga wani mutum tsaye babu sallama ta ce "Malam lafita kake nemana ko naci bashin kane?"
Wani Murmushi ya sakar mata na zakiyi bayani cikin basarwa ya ce "saƙo ne daga Kotu takardar sammaci ya bata ya ce anane manki a kotu ranar Litinin.
Cikin masifa Mama "ta ce to ni kuma me nayi ake nemana?"
Wanda ya kawo saƙon ya ce "kinga Malama Ni saƙo ne aka aiko ni."
Bayan ya tafe Mama ta shiga gida tana zuwa ta kira Umma ta faɗa mata abinda ya faru.
Cike da firgice! Umma tace "wayo Allah na Mama komai ya chaɓi min gashi Abbi ya bada auren wannan yarinyar ba tare da sanina ba yanzu baya tsorona."
Mama tayi dariya tace "kar ki damu bari mu gama da wannan kafinmu koma kan wancan zamu je wani bokan zai yi mana aiki me kyau fatan Allah ya dafa mana".
NIKAM NACE ABIN ALLAH KUKE YI DA ZAKUCE ALLAH YA DAFA MAKU.
Umma ta ce "to yanzu ya za'a yi?"
Mama tace "kawai zamu samu lauyoye mu biyasu kuɗi masu yawa nasan zasu yi mana abinda muke so san nan muje wajan bokayen mu suma su bamu nasu taimakon nasan mu zamuci riba kinga da komai ya daidaita sai mu kashe su a boye."
Hakan kam aka yi sukaje suka samu wasu lauyoye suka biyasu kuɗi masu yawa suka tsara masu abinda zasu faɗa da yarda Shari'ar zata tafi.
Haka sukai ta tsare tsaren su har Litinin ta zagayo.
TO KUNJE TA YANDA SU UMMA SUKA YI NASU SHIRIN AMMA MUJE ZUWA ANCE SANU SANU BATA HANA ZUWA SAI DAI A DADE BA'A JE BA ZAMU GA WAYE ZAIYI NASARA A WANNAN TAFIYAN KUDAI KWAI KU BANI HAƊIN KAI.
Eshan bayan Ahmad ya fito wanka ya chanza kaya suka shirya suka fito falo suna cin abinci suna fira Mame da Farha kuma suna kallo a TV babu wanda ya kula da kallon da Abdul yake ma Farha sai Eshan tun ɗazu yana kallon su harda kashe ma juna ido suke cikin zolaya ya ce " ku yanzu saboda rashin kunya a gaban mu zaku yi soyayya ba kuji kunya ta ba kuma baku ji kunyar Mame ba."
Daga Abdul har Farha wata kunya ce ta kama so dan basuyi tunanin wani yana kallon suba.
Farha ta ce "Yaya Eshan kai dawa kuma?"
Ya ce "ban sa ni ba saboda rashin kunya a gaban mu kuke wannan abin ana ai kawa juna kallon LOVE."
Mame ta ce "wai kai meye naka a ciki ɗan sa ido kada ka manta yayan ta ne fah so ba bu abin mamaki dan ya kalleta."
Eshan to "Mame idan baki sa ni ba ki sa ni wannan yaran soyayya suke."
Ciki da farin ciki da kuma fatan abinda Eshan ya faɗa ya zama gaskiya ya ce " gashinan a tambaye shi idan ƙarya nayi mai?"
Cikin zumuɗi Mame ta ce "abinda nike ji gaskiya ne?"
Cikin jin kunya Abdul ya ce "eh mame gaskiya ne.''
Saboda murna Mame kamar ta zuba ruwa a ƙasa ta sha haka ta ji.
https://chat.whatsapp.com/CBtvAeshrDyAlqXRA7d4sM
DAFIN ZUCIYA
BY FATIMA BINTU HUSSEN
*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
Bisimilahi Rahamanur Rahim
Page 42
Mame ta ce "Kai amma naji daɗi wallahi amma me ya sa baka faɗa da wuri ba ai da sai asa lokaci ɗaya dana wan can mara kunyan ta faɗa mana hararan Eshan."
Ganin hararan da Mame ta yi mashi ya sa shi tashi daga inda yake ya koma kusa da ita ya zauna.
Mame ta ce "kai Malam kada ka kuskura ka matso inda nike aini babu ruwana da kai."
ya shagoɓe fuska kamar wani yaro ya ce" ummm kiyi haƙuri na tuba."
suna cikin haka Abba ya shigo falon.
Ganin Eshan tsaye gaban Mame tana ta hararan shi ya sa ya ce "Kai lafiya ka?"
cikin shagwaɓa ya ce "ba Mame ba ce ta ce bata sona ba."
Mame ta saki baki tana cewa " ikon Allah Ni zaka yi ma sharri ko?.
Abba yayi dariya ba ƙaramin daɗi yake ji ba idan ya zo ya iske family nashi na farin ciki haka.
Ladidi koda malam ya ce ta tafi gida bayan ta fita kai tsaye wari boka ta tafi.
KOTU
Bayan alƙali ya shigo ciki kowa ya meke aka gaishe da alƙali ya fara kiran sunan masu ƙara da wa inda ake ƙara ya ce ina masu ƙara su fito. su faɗi abin ke tafe da su.
Haidar ganin Yusurah ta ɗaga wayar yasa ya ɗaga mata hannu.
Ya ƙara so inda take kowa na bin kowa da kallo ganin kallon da yake mata ya sa ta ce "bisimilah mu shiga daga ciki?"
Murmushi ya sakar mata san nan yace okay mu shiga."
Tana gaba yana baya ahaka har suka isa falon Daddy.
KOTU
Mansur ne ya fita ya fara bayani ya faɗi duk wani abin da ya faɗa ma Alƙali bai ɓoye komai ba.
Kowa jikin shi yayi sanyi dajin bayanin Mansur.
Lauyan su Umma ne ya tashi ya ce 'ya me girma me Shari'a ina neman alfarma abani izinin magana da Malam Mansur?"
Alƙali ya ce am baka Barester Kamal ya ce "daga jin bayanin wanyan bawon Allah ansan ba gaskiya bane wannan shari ne ake so ayi masu."
Alƙali ya ce "wannan ne korafin na ka kada ka ƙara magana akan bayanin dayake yi kabari aji ta bakin kowa."
Barester Kamal ya ce "ina neman afuwa."
Amira yanzu komai yayi sauƙi soyyaya suke zubawa ita da Eshan kamar ba gobe idan baya wajan ta ko kuwa suna maƙale a waya.
Abbi ne ya kira Eshan ya ce "ya zo suyi sallama don gobe zai kai Amira gida."
Amira da ke a gabanta Abbi ke wayan cikin farin ciki ta ce ma Abbi "Dan Allah Abbi da gaske kake"
Abbi ya ce "eh in Sha Allah."
kuzo kuga murna wajan Amira.
Eshan dayeke suna tare dasu Ahmad ya ce ma Ahmad "tafiya ta kamani."
Cike da mamaki su Ahmad suka ce "tafiya kuma?"
Eshan ya ce "eh PRINCESS ce zata je wajan Ammi gobe kuma sai naje dan baza ta barin ba."
Abdul ya ɗaka mai duka
DAFIN ZUCIYA
BY FATIMA BINTU HUSSEN
https://chat.whatsapp.com/CBtvAeshrDyAlqXRA7d4sM
*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
https://whatsapp.com/channel/0029VbAho5W8V0tlD03a4Q1g
NA GODE DA ADDU'ARKU ALLAH YA SAKA DA ALKAIRI
WANNAN SHAFIN NA SADUKAR WA MASOYIYA TA KUMA AMINIYA TA MARYAM UMAR STAR
Bisimilahi Rahamanur Rahimi
Page 43
Ahmad ya ce "wai kai yaushe ka koma mara kunya ne?"
Abdul ya ce "ai indai wannan ne kaɗan ma kagani."
KOTO
Ana ta fafatawa.
Bayan Mansur ya gama bayanin shi jikin kowa ya yi sanyi.
Kotu ta ɗau hayaniya da ƙyar Alƙali ya sa mutane yi shuru bayan komai ya lafa
Baresta Jamal ya ce " ya na so Mama ta fito zai mata wasu tambayoyi".
Bayan mama ta fito tazo wajan benci ta tsaya Barester Jamal ya ce "kada ki tsaya bata mana lokaci ki faɗa mana gaskiya domin koda kin ɓata mana lokaci dole zamu gano gaskiya."
Cikin rawar jiki Mama ta ce "duk abinda ya faɗa ba gaskiya bane Sherri aka yi min hasalima ban san da faruwar komai ba sai da aka kawo min takardar sammaci."
Daga yanda take maganan zaka fahimci akwai rashin gaskiya ya bayyana.
Barestar Jamal ya ce " kina nufin duk abin da ya faɗa ba gaskiya bane kina nufin Ƙarya yayi maki shiko wani riba zai ci idan ya yi maki Ƙarya."
Barester Kamal ne ya tashi ya ce ma Barester Jamal "ya na da kyau ka tsaftace kalaman ka."
Wani shigen murmushi Barester Jamal ya yi ya ce mashi " bangane na tsfatace kala mai na ba."
Ganin abin zai zama cecekuce ya sa alƙali ya buga gudumar sa ya ce "odar."
Barester Kamar ya ce "ina so wannan kotu me alfarma ta bani damar yin magana da me ƙara Mansur?"
Alƙali ya ce "an baka."
Barester Kamal ya ce "ina Malam Mansur?"
Mansur cikin natsuwa ya taso ya zo ya tsaya.
Barester Kamal ya ce "meye shedar ka wanda zai tabbatar mana da abin da ka faɗa gaskiya ne?"
Ladidi haka ta koma gidan Boka ta na zuwa ciki ɗaurewa Boka ya ce me "ya kawo ki?"
Ladidi ta ce "bangane me ya kawo ni ba In ce kasan abinda ke tafe dani?"
Boka ya ce "ni yanzu babu ruwa na dake tunda har kika karya mana doka."
Cikin jin haushi Ladidi ta ce "ban gane ba?"
Boka ya ce "a ƙa'ida ta ba a yin ciki duk abin da zai shiga tskanin mu kuma sai da na faɗa maki gashi yanzu kinyi ciki dan haka ko fita ki bani waje bani da abin da zan iya yi maki."
Tashin hankali
Yusurah bayan sun shiga ciki ta kai shi falon Daddy dama an gama shirya komai na abinci.
Yusurah ta ce "ka ci abinci ina zuwa."
Bai ce mata komai ba kawai ya ɗaga mata kai ne.
Yusurah na fita ta kira ƙawar ta khadija bayan layin su take ita kaɗai ce ƙawar ta tunda abin nan ya faru Daddy ya hana ta taraiya da wasu ƙawayen.
Bayan sun gaisa da khadija yusurah ta ce "mata Please ki shigo ga shinan ya zo."
Khadija ta ce mata " yanzu ina ɗan aiki ne amma zan shigo."
Suna gama waya taje ta faɗa ma Ummi matar Daddy sosai Ummi tayi murna ganin yanda Yusurah ta ɗauke ta kamar uwa.
Ummi ta ce mata " taje ta kula dashi ta na zuwa."
Yusurah na fitowa falon Daddy ta koma ta na zuwa ta same shi yana shan ruwa ta shiga da sallama.
Jin sallarta ya sa ya ɗago ya kalle ta san nan ya amsa.
Yusurah ta ce "naga bakaci abincin ba?"
Jin tambayan da tayi mashi yayi murmushi ya ce "ai bari nayi dai Gimbiya ta zo ta bani."
Jin abin da ya ce ya sa ta kwalalo idanu ta na kallon shi.
Shi ma kallon ta yake ganin iri kallon da yake mata ya sa tayi ƙasa da kanta.
Suna a haka Daddy ya shogo turrs ya tsaya ganin Yusurah da Haidar.
Amira ba ƙaramin farin ciki take ba abubuwa sun zo mata lokacin ɗaya sanda Abbi ya ce masu su shirya zasu je wajan Ammi gani take kamar a mafarki babban abin da yaƙara ma ta farin ciki kuɗin nagani ina so na auren ta da Eshan da aka kawo.
Amir kamar wani mahaukaci haka ya koma jin ance za a kaimu wajan Ammi ya zo ya samu Abbi ya ce mashi "amma Abbi idan ka kaimu wajan Ammi bazamu dawo nan ba ko?"
Abbi ya shafa kan shi ya ce "baza ku dawo ba kun koma can kuma can za'a mai daku makaranta."
Amir ya rasa me zai ce kawai sai ya kwanta yana birgima ya na ce wa "wayo Allah na zama ɗan gayu zan koma wajan Ammi na duk abin da nike so shi zata yi min Allah sarki Amminah nakusa ganin ki."
Amira banda dariya babu abin da ta ke mashi.
Shi kuma Abbi tausayin su ne ya ƙara kamashi.
Amira ta ce ma Amir "ai kai nan zan barka wajan Umma."
Amir a sukwane ya yo kanta ya na dukan ta ya na cewa haba "ai koda cewa Abbi ya yi nan zan zuna na san bazaki bari ba."
Abdul ya ce "kaga Malam ka tashi muje muyi mata sallama"?
Eshan "ku dai yi mana sallama dan ni dai da ni za'a je."
Ahmad ya ce "wai yau genaral Eshan ne ya faɗa hannu haka gaskiya ko wacece wannan ta cika me sa'a."
Abdul ya ce "kaima dai ka ce Mutumin da ko maganar mace baya so ayi mashi mata basu gaban shi amma yau she ne yake....... Wani uban dundu Eshan yayi mashi a baya ya ce " zaku yi min shari ni daman can ba cewa nayi bana son mace ba cewa nayi ban samu warda tayi min ba kuma yanzu ba samu."
Abdul ya ce "Allahu Akbar mun je wannan kaga Malam ta shi muje."
Haka suka tafi gwanin birgewa suna tafiya suna fira sai da suka biya wani ƙaton shopping Eshan yayi ma su Amira siyayi ya daga nan ya sai mata waya kirar infinix hot 10t.
Abdul ya ce "kai masha Allah ka fitar min da yar ƙanwa."
Abdul ya ce "kai nima bar na sai ma my Farha na kai mata."
Ahmad ya ce "ni zaku ware ke nan ni ma bari na siya na aje ye ko Zan samu me soma ."
Sai da suka gama shiriri tar su san nan suka bar shopping din suka kama hanyar gidan su Amira.
KOTU
Mansur ya ce "ni kam ke da shidu saboda mahaifina shi kan shi sheda ne da me motan da suka tura yaje ya taka Baba ya kashe shi."
Cikin kiɗima Mama ta ɗago tana kallon shi jin abin da ya ce dan ita tskanin ta da Allah tayi tunani da ya ce ma su Baba ya mutu ƙarya ya faɗa masu.
Barester Kamar ya ce "ko zamu iya ganin shedunka?"
Mansur ya ce "eh su na waje san da suka zo waje ya cika."
Alƙari ya bada umarnin a shigo dasu.
NICE TAKU HAR KULLUM BINTU HUSSEN
DAFIN ZUCIYA
BY FATIMA BINTU HUSSEN
https://chat.whatsapp.com/CBtvAeshrDyAlqXRA7d4sM.
*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
YA ALLAH DUK WANI ME DAMUWA ALLAH KA CIRE MASHI ALLAH KA JIƘAN MAGABATAN MU MARASA LAFIYA NA GIDA DANA ASIBITI ALLAH KA BASU LAFIYA MATA MASU JUNA BIYU ALLAH KA SAUKE SU LAFIYA
Bisimilahi Rahamanur Rahim
Page 44
Abbi ganin su Amira suna ta shiriri ta ya sa ya ce bari ya ɗan fita dan yana so gobe da wuri zasu kama hanya.
Bayan Abbi ya fita Amira suka shiga cikin ɗakin su suna shirya yan kayan su wani abu Amir ya fito cikin jakar shi yana nuna ma Amira da gudu tayo kan shi tana mashi masifa shi kuma ya yi hanyanar fita daidai lokacin su Eshan suka shigo cikin gidan da gudu Amir ya tafi ta ɓoye bayan Eshan,
Ita kuma Amira idanu sun rufe da masifa batan gan su ba ta ci ga ba da ce wa "Ai walahi sai kabani takarda ta kokuma na faɗa ma Abbi yanzu ka rai nani ko?"
Amir daga bayan Eshan ya ce "Kai Yaya ta kiyi haƙuri kinga ni yaro ne ko."
Cikin masifa ta ce "idan na kama ka za ka yi bayani."
Eshan baki ya buɗe yans kallon ta daman ta iya faɗa haka.
Amir ya ce "shi ke nan tunda ba za ki haƙura ba ga takardarki nan ya jefa mata."
Kafin ta ɗau takardar Eshan ya ɗauke ita tunanin ta Amir ne ya ƙara dauka amma ganin wanda ya ɗauka ya sa ta ruga da gudu ta yi ɗakin su.
Eshan ya ce "oho baki da gaskiya ne? Da zaki gudu ko ai kam zan ga ko meye ya haɗa ku faɗa."
Ya na gama faɗin haka Amir ya ce "wallahi Yaya Eshan report ɗin tane da tayo na goma bata son kowa ya gani koda Abbi ya tambaye ta sai ta ce mashi ba a basu ba.?
Eshan ya kwashe da dariya ya ce "wai dama saboda report ke ke ma wannan faɗan ai kam baki bashi dan nayi nawa."
Abdul ya ce "kai Malam ka bata abunta ai tamayi koƙari kai fah kai ne ka keyi na karshin aji."
Ahmad ya ce "ashe baka manta ba aka mashi a duka amma baya ji."
Cikin jin haushi ya ce "ni kuke ma shiri ko ai kam ku shirya shiga gaduroom."
Su duka suka kwashi da dariya.
Umma dama da yaran ta ta tafi sanda suka isa gidan babu kowa duk suna kotu,
Yaran kawai ta ajiye a gida ta tafi kotu,
San da ta isa lokacin aka ce a kira su Baba dama tana isowa bakin ƙofan taga su Baba tare da me motan da suka sa ya kashi Baba cikin kiɗima da razana!,
Tayi baya baya kamar zata daɗi sai kuma ta kama bango dake kusa da ita ta tsaya tana karan to duk Addu'ar dake bakin ta.
Duk abinda take yi Baba suna kallon ta murmushi kawai Baba yayi ya ce "kaɗan ma kika gani."
Suna cikin haka sai ga Police din da akasa ya kira su Baba ya zo wajan cikin girmama wa ya gaishe su sanan
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 7 Chapter of 14