Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
aka amshe ta likitoci sun sha wahala Sosai kafin suka tsaida jinin dake zuba san nan suka mata allurar bacci. Yusurah tayi mamakin ganin irin gidan su Haidar amma ta ɓoye mamakin ta. A tunanin ta zataga Maman Haidar tsohuwa amma ta ganta Ma sha Allah kamar ba ita ce ta haifi Haidar ba. Sosai Mama taji daɗin ganin Yusurah tazo gaishe ta nan tasa masu aiki suka fara haɗa mata abinci kala-kala dan dama Haidar bai faɗa mata zai kawo Yusurah ba. Ita kam ganin yanda Mama take ta nan nan da ita ya sa taji Mama ta kwanta mata a rai sosai. Cikin jin kunya suka gaisa da Mama tana ta yin ƙasa da kai wai ta tana jin kunyar Mama sai da Mama ta ce "niki bar jin kunyata ni Mamar ki ce." Yusurah tayi shuru ita dai Haidar ne ya ce "wai ke kunyar Mama kike ji ko?" Shuru tayi mashi Mama ta ce "ka wuce ka tafi kada ka takura mata." Dariya yayi ya ce "Mama saboda kinga ƴarƙi kike kora ta." Mama tace "an kora ɗin ka wuce ka bamu waji." Fira yayi yana dariya. Yusurah yau kusan a nan ta wuni sai bayan la'asar yazo su tafi sosai Mama ta haɗa mata kayan aziƙi irin su turare atamfa main shafawa haka ta haɗa mata su a jaka me kyau. Yusurah tai ta godiya koda suka taho sunzo wani ƙaton shopping Haidar yace "zu shiga ciki." Allah sarki Ladidi jikin ta yayi tsana ni sosai bata gane wanda yake kan ta shi kan shi Yaya ganin halin da take ciki jikin shi ya yi sanyi sai yayi dana sanun dukan da dama tun farko yafi ta malam da ya ce abin komai a hankali. Saboda cikin ya ɗanyi girma hakan yasa yaron cikin ta ya mutu wanda haka yasa sai an mata CS za fitar da gawar yaron. Amira nan falon suka zauna ana ta fira bayan mutane sun tafi Aunty Fatima ta zo ta zuna suka ci ga ba da fira nan Amira je faɗa masu abubuwan da suka fuskan ta a gidan Abbi har su Farha sai da su ka yi kuka jin wannan abin ganin Aunty Fatima ta dauki zafi yasa Ammi ta ce "kada suyi komai su bar mai Allah zai saka masu daga haka aka kashe maganar." Su Eshan daga masalaci suka ɗan zagaya gari daga nan suka tafi gidan su Ammi. Su Amira ana ta fira ta ɗauka ɗiyar Aunty Fatima takwarar ta ta rugume kusa da ita kuma Minal ce ta isheta da surutu. She Kam Amir yana kan cinyar Ammi Minal tayi kuka ta gaji wai sai ya ɗaga mata cinyar Ammin ta. Suna ta fira su Eshan suka shigo da sallama duk suka amsa. Suka ida sa suka zauna san nan a ka ci ga ba da gaishe gaishe Ammi ita fa kunyar Eshan take ji sai sunar da kai take amma shi kam Eshan babu batun wata kunya a tare da shi saima ai kama Amira harara da yake. Aunty Fatima ce ta ce "ina sirikin nawa?" Eshan aka yi ƙasa da kai ana sosa ƙeya wai yaji kunya. Dariya Aunty Fatima tayi ganin Eshan yana sosai kai yasa ta gane shine. Ta nuna shi da hannu ta ce "kace kaine sirikin nawa?" Ga mamakin ta sai taji ya ce "eh wallahi." Ido ta zo a zuciyar ta tana cewa sannu mara kunya. Ammi kam tashi tayi dan ta lura kwata kwata babu kunya a gareshi. Yaya Faruk ne ya ce ma Aunty Fatima "kin san wannan?" Ya faɗa yana nuna Ahmed. Kallon shi take kamar ta san shi amma ta mata. Dariya Ahmed yayi ya ce "ai dama ba lailai ta gane ni ba." Yaya Ahmad ya ce "Ahmed ɗun Aunty Maryam." Zumbur Aunty Fatim ta muƙe tana maimai ta suna Ahmad tana ce wa "Yaya Ahmad dama rai kangare." Dariya ya yi ya ce "wallah kin ga ikon Allah ko." Daga haka suka shiga fira har Ahmed ke cewa nan da kwana huɗu Mame zata zo. Sosai suka ci ga ba da murna. Suna cikin farin ciki ɗiyar Aunty Fatima ce ta fara kuka Aunty Fatima ta ce "to yanzu ai sai ki kawo ta duk kin kama ta kin riƙe kin hana kowa." Tashi Amira tayi tana zumbura mata baki taje ta kaima ta ita ta masa ta shayar da ita Amira ta taso ta dauka sai taji Eshan yace " kawo ta nan." Zuwa tayi ta miƙa mashi. Su Hafsat kunya duk ta ishe su ganin Aunty Fatima tana falon zaune kuma ga yaya Faruk a wajan. Sallamar Abbi suka ji DAFIN ZUCIYA THE HIDDEN OF THE TREASURE OF THE HEART BY FATIMA BINTU HOSSEN https://chat.whatsapp.com/Jp93APpPrfe9IezRu9zH91?mode=ac_t *https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ *(J.W.A)* _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ 🦚🦋THE NOBLE WRITER'S TEAM🦋🦚 (🦚✊DEDICATION IS OUR STRONG✊🦚) ALHAMDULILAH NAKUSA SAKA THE END Bisimilahi Rahamanur Rahim Page 53 Sallamar Abbi Suka ji su duka suka amsa ya shigo ya zauna duk suka gaisa. Amir ne ya taso ya zo ya zauna kusa kusa da Abbi Yana ce wa "Abbi Ina ta neman ka." Dariya Abbi yayi ya ce "naji na huta ne nima." Abokin Abbi bayan sungama waya da Abbi ya tafi unguwar su Umma yana zuwa ƙofar gidan aka yi Sa'a yaran sun fito waje. Suna ganin abokin Abbi Suka ruga wajan shi suna murna shekam abokin Abbi ya ce "kuje ku dauko kayan ku zan kai ku wajan Abbi." Suna murna suka tafi dama ba wani jin daɗin gidan suke yiba bayan sun dauko kayan su suka kama hanya suka tafi gidan Malam Sani. Abbi ya ce "ina Ammin ta ku?. Aunty Fatima tace "bari na yi mata magana." Aunty Fatima ta tashi ta tafi ta kira Ammi. Tare suka shigo falon tunda ta hango Abbi ta kura mashi ido tana kallon shi she ma ita yake kallo har ta ƙara so . Bayan ta ƙa ra so ta gaida Abbi. Bayan ya amsa yayi gyran mura ya ce "ina son kowa ya maido da hankalin shi kaina zamu yi magana kuma ina so zan baki haƙuri akan abinda ya faro." Eshan da Ahmad da Abdul sai su Farha suka tashi zasu fita dan gani abin na family ne amma Abbi ya ce su dawo su zauna ayi dasu an zama ɗaya. Abbi ne ya ce "Assalamu alaikum." Sukuma suka amsa da wa'alaikum salam. Abbi ya ce "zan fara da Amira da Amir dan Allah ku yafe min ina me neman yafiyar ku wallahi duk abin da yake faruwa ban sa ni ba hasa li ma bana a cikin haiyaci na dan Allah ku ya fini." Ya ƙara sa maganar da hawaye a fuskar shi. Su duka jikin su yayi sanyi Amira Sarkin kuka har ta fara kuka ganin mahaifin su yana kuka yana neman yafiyar su. Ciki kuka ta ce "wallahi Abbi mun yafe maka duniya da lafira mun da ma bamu riƙe ka a raiba kuma ina yawan faɗa ma Amir kada ya riƙe ka a rai asiri ne akai maka." Kowa da mamaki ya kalle Amira jin ta ce asiri ne aka yi ma Abbi. Ta ciga ba da cewa "nasan zaku yi mamaki ko?" Ta ce "wata rana Umma ta ce nazo na raka ta wani waji bayan mun fita muka kama hanya wani daji ne mukai ta tafiya a ciki dan ni nayi tunanin wani abu Umma zata yi min sai naga mun hau wani ɗutsi babba muka shiga wani ramin a dutse wani mutum muka gani babu kyaun gani gashi ƙazami sai wari yake har sai da na tushe hanci na, Amma wani abin mamaki wannan mutumin yana gani na naga ya tashi hankalin shi yayi mugun tashi yana nuna ni da hannu ya na ce we wannan ita ce warda kike so ayi aiki akan ta to ki sani babu wanda ya isa ya taɓa wannan yarinyar donmi akwai wani haske a tattare da ita duk wanda yace zai cutar da ita akan shi abin zai ƙare ya ƙara sa maganar ciki tsawa, sosai hankalin Umma ya tashi jin abinda boka ya ce hakan ya sa ta ce to tunda ni aikin ba zai yi a kaina ba to sai a maida shi kan uban su shida ma namijin na san yanda zan yi dashi na san shi idan ya girma zai yimin amfani haka tasa boka yayi aiki akan ka ya bada wani abu ya ce tazo ƙasan gadon ka ta sa ta ka kwanta zaka manta damu duk abin da tace shi zaka yi muna fitowa tayi min kashe di tace ida taji wannan maganar ta fita to sai ta kashi ne." Ta nufa fasa ta ce "tun ranar da muka dawo tayi maka wannan abun tun daga ranar naga ka daina kula mu baka damu damuba babu ruwan ka idan munci abinci ko ba mu ciba sutarar mu duk ta kwashi komai na mu haka ta mai damu ma ra sa galihu bamu da ƴan cin kan mu wata rana ƙawarta Ladidi tazo naji tana bata labarin yanda aka yi ta raba ku da irin aikin alfashar da suka da farko abbi ka fara da tsar mu wanda daga baya ta kaiga kun rabu hankali na ya ƙara tashi sosai, Gashi banda wanda zan faɗa mawa kowa gudun mu yake na rasa inda zan sa kaina rana zafi inuwa ƙuna gashi a lokacin Amir ba wani wayo ne da shiba watara na munje islamiyya wani malamin mu yana mana karatu ya ce idan mutum yana da damuwa ya tashi da daddare yana Sallah ya faɗa ma Allah damuwar shi In sha Allah zai samu sauƙi kuma Allah zai amsa hakan yasa kullum sai na dinga tashin Amir munayi yin sallah muna roƙan Allah ya fitar damu halin da muke ciki tun Amir baya son tashi har ta kaiga wani lokacin she yake tashi mu wata rana bamu san dalili ba Umma ta hana mu zuwa makaranta ta koma daura mana tallah azaba ta ƙara mana yawa wanda duk abinda ake baka iya yin komai akai wani lokacin har dukan mu kake amma bana damuwa saboda nasan ba'a hankalin ka kake ba wata rana muna zaune kazo kace mu shirya zaka kaimu makarantar boko ta kalle Abbi tana cewa "ka tuna?" Abbi ya ce "tabbas na tuna." Amira ta ci ga ba da cewa bayan ka kai mu makarantar wata rana munyi ma Malamin mu laifi ya ce ba zamu koma gida ba sai kowa ya ga ma tafiya hakan yasa bamu dawo gida da wuri ba ina dawo wa Umma ta kamani da duka tana cewa na tafi yawon iskanci sai ta karyani ta bugamin wani ƙaton ƙarfi a ƙafa, Kowa hawaye yake Eshan yakasa tsare ta da idanu. Ta ci ga ba da cewa tun san da ta buga min wannan abin ƙafata naji kamar bata jikina kwana na uku a ɗaƙi ban iya taka ƙafar ta kumbura Sosai Umma ganin yan da ƙafata ta koma hakan ya sa tace maka ai na ɗine. Saosai Amira ta faɗa masu irin azabtar War da Umma tayi masu har zuwan sanda Abbi ya fara dawo wa dai dai da sanda Umma tabuga mata abu akai wanda hakan yasa ta man ta komai da haɗuwar su da su Eshan har zuwa yanzu. Amira na kaiwa karshen maganar Wasu daga ciki suka fashi da kuka har da su Farha Ammi kam ta sanƙare jin abinda Umma tayi masu dama ita tasan Abbi bazai masu ha ka ba yaya Faruk ma saida yayi kuka. Abbi ne ya tashi ya tafiya ƙama ƙafar Amir da Amira Yana kuka yana cewa "su yafe mashi dan Allah." Yaya Faruk ne yazo ya kama shi yana cewa "haba Abbi ƙaddara ce tana kan kowa mun san bayin kain ka bane ka dauka wannan abin a matsayin ƙadddar ka kowa da ƙalar tasa ƙadddar wata ƙaddarar zata zo maka da sauƙi wata kuma akasin haka yanzu da kayi haƙuri Baga shi ka cinye jarabawar kaba ta wannan bangaren gashi duk wani abu da ake ɓoyewa ya fito." Yana gama maganar abbi ya rungume shi san nan ya koma wajan Ammi yana cewa "dan Allah A'isha ki yafeni wallahi ina sonki." Ammi ta ce "nima na sani nasan cewa ƙaddara ce." Babu ɓata lokaci Abbi yace ma Ammi "ta yardda a maida auren su ita kam tace sai tayi shawara." Abbi ya dauƙi wayar shi ya kira Mansur yace ya haɗa shi da Babansa bayan ya haɗa su ka gaisa cikin girma mawa Abbi ya ce yana so a faɗa ma Umma ya sake ta. Koda Baba yaji abinda Abbi ya ce bai wani tada hankalin shi ba ya ce "Allah yasa hakane ya fi alkairi." Daga nan kuma suka ci ga ba da fira kamar sun saba amma idan ka kalle su zaka fahinci akwai damuwa aƙasan zuciyar su. Abbi wani zazzaɓi ne ya kama shi nan yakama rawar sanyi cikin tashin hankali suka dauƙe shi suka tafi asibiti suna zuwa aka ce jinin shi ya hau kuma zuciyar shi na ciwo sosai hankalin su ya ƙara tashi sun san ba komai ne ya jefa shi wannan halin ba abinda Amira ta faɗa ne. Yusurah koda suka shiga shopping din amma taƙi daukar komai sai da shi Haidar yake dauka ganin abin ya fara zama hauka yasa ta da Katar da shi dan harda su akwati sarƙa atamfofi lass shadda pant pat Babu kunya yake ta dauka wasu abubuwan kamar wanda zai haɗa lefe bayan ya gama siya aka sa masu a but ɗin mota sanan suka kama hanyar gidan su Yusurah suna tafiya suna fira. Yusurah ta ce "gaskiya wainan kayan sunyi yawa rage wasu kasa a lefe don idan Daddy yaga wainan uban kayan zaiyi faɗa kuma zai sa amaida su." Dariya ya yi yace "idan yayi magana kice mijin kine ya Baki." Harara ta watsa mashi tace "tunda ce maka aka yi bani da kunya da za ka ce na ce haka." Dariya yayi yace "to shekenan sai ki rage." Ladidi bayan an fito da ita CS ana ta jira ta farka abu shuru har kusan awa uku bata farka ba ganin shurun yayi yawa yasa a ka kira babban likita yana zuwa ya duba ta yace "sai dai kuyi haƙuri Allah yayi mata rasu wa." Inalilllahi wainna ilaihi ra'ji un KULU NAFSIN ZAIKATUL MUT. Hankalin su ya tashi kowa ce wa yake "inalilllahi wainna ilaihi ra'ji." hankalin yaya yafi na kowa tashi san gani yake kamar shine ya kashe ta saboda duka da yayi mata. Malam ne yai ta kwantar mashi da hankali yana cewa "ya daina cewa haka Allah ya ruba tanan aljalin ta yake." Aka yi ciki ciki aka amshi gawar daga asibi kai tsaye gidan Malam aka wuce da gawar. Amarya ganin gawar ladidi yasa hankalin ta ya tashi kamar ta hauka ce haka ta koma dan mutuwar ta shige ta sosai. Nan aka yi ma marigayiya Ladidi wanka aka yi janiza aka kai ta gidan ta na gaskiya. Sai bayan andawo jana'iza sai ga ɗiyar Ladidi Mariya ta dawo daga yawon ta bata san ma an yi rasuwar ba koda akafaɗa mata rasuwar bata wani damuba sai cewa tayi ma ita ta sani. Nan mutane akai ta zaginta ita kam ko a jikin ta. Bokan dake masu Ladidi aiki yan cikin wannan ɗutsan yana haɗa tsaface tsafan ce wata ta kama a cikin wajan kafin ya fito watar tagama cin jikin shi. Inalilllahi wainna ilaihi ra'ji unm wannan wani kalar bala'i ne ka mutu kana saɓa ma Allah ya kada kasa muyi mummunar ƙarshe ya Allah kasa mu mutu muna bauta maka. Wasu mutane ne zasu je gona suka ga gawar Boka dayake kusan kowa ya san shi sunyi ko kore shi daga garin abin ya gagara hakan yasa suka yi murna suka zo cikin gari aka faɗa ma mutane suka zo babu wankan gawa babu komai suka yi rami su rufe shi. Abbi da kayr jikinshi ya dawo dai dai bugun zuciyar shi ya sai tu san nan suka samu hankalin su ya kwanta duk suna waji daga Ammi sai Abbine a ɗakin da wannan damar Abbi ya ƙara roƙan ammi akan tayi hakuri ta koma gidan shi dam ɗazu kunyar su Eshan ne ya hana ta ce ta amince ta ce mashi ai ita yarda sosai yaji daɗi dan haka ya kira yayan Ammi ya faɗa mashi babu ɓata lokaci ya ce da asuba za a maida auren. A daren aka sallami Abbi daga asibiti suka wuce gidan yaya Faruk bayan sun aje su Ammi a gida . Washa gari sunje sallar asuba kasa sanar da daurin aure jin auren da aka daura yayi mugun basu mamaki dan basa da masaniya aka anan sukai ta murna har suna tsokanar Abbi. Gidan yari Umma sun fita suna aiki kawai aka ga ta fasa ƙara ta yanke jiki ta faɗi haka aka dauke ta aka kaita asibiti amma an duba ba a ga abinda ke damunta kuma gashi tana hauka abinda basu sani ba duka asirin da Umma tayi ma mutane ne ya koma kanta ya haukatar da ita. Abokin Abbi kam tunda asuba suka kamu hanya she dasu kalil. Monday KOTO Yau ta kama za'a koma koto bayan anji koto aka gabatar da shedu inda aka gane su Umma babu gaskiya aka yanke ma Mama daurin rai da rai inda ita kuma Umma aka kaita gidan mahukata idan ta samu lafiya a yanke mata nata hukuncin. Mutanan gidan duk da haka sunji babu daɗi amma dole sai ana yanke ma irin su hukun ci idan ana barin su haka ba'a yanke masu hukunci za aita samun ɓata gari. Yau ne aka kawo kayan Sa rana Yusurah inda babu ɓata lokaci aka saka sati biyu. Yau su Eshan kwanan su uku kuma a yau zasu koma Abuja harda su Ammi dasu Yaya Faruk. Koda abbi ya ji labarin abinda ya faru da Umma ya tausaya mata sosai sukuma yaran Umma koda aka kawo su ganin su Amira yasa suka basu hakuri akan duk abinda suke masu Umma ce ke sasu. Ammi kuma ta ce zata riƙe su amana kamar ita ce ta haife su sosai hakan ya faran ta ran abbi. Bayan sun isa Abuja wani ƙaton gidan Ammi taga ankai su tunda suka shiga gidan take ta mamaki ina Abbi ya sa wannan ƙaton gidan. Bayan sun shiga gidan ya haɗu ga wasu manyan motoci kusan guda biyar kowa Abbi yake kallo da mamaki ganin suna kallon shi yasa ya ce su shiga ciki sai ya yi masu baya ni. Suna shiga suka ga an jera masu manyan kolili na abinci ga katan katan na ruwa da lemuka ciki da mamaki Amira ta buɗe baki zatayi magana. Abbi yace " kibari kici ki ƙoshi sai kuyi min tambayan." Babu yanda suka iya haka suka haƙura. Bayan sun gama cin abinci Kowa yayi wanka suka hutu dama su Eshan nan. Falo suka fito suka zauna Abbi ya ce "nasan bakin ku da tambayoyi yanzu zan ba ma kowa amsar shi amma kafin nan bari na fara magana ta." Abbi ya ce shekara biyar da suka wuce wani abokina me sai da motaci babbane kusa duk motocin da dasu shigo Najeria na shine wata rana yazo ya samin da shawara ya ce me zai hana na saka hannun jari mu haɗa hannu a kasuwan cin mu da naji tsoron kada ya ci amanata amma hakanan na yardda da farko na fara sa miliyan 10 gonaki na na sai da na bada wannan kuɗin sai gashi Allah ya sa mana albarka har ta kaiga nima na mallaki Company na na kai na amma babu wanda yasan nawa ne kowa ya bushi da kallo yace yan zu haka inda Company's guda uku akwai Al hussin Company Al Barka Company Amira and Amir company. Kowa ya bishi da kallon mamaki mutumin da keda wannan dukiya ya zauna a wata unguwa. Abbi ya ce "wannan gidan da kuke gani ina da kamar su guda goma banda gonaki na da na maida yanzu wannan gidan ya dauko keys din gidan ya bama Ammi wannan gidan na mallaka maka shi halak malak a cikin moto cin can ki dauka guda ɗaya Faruk ɗaya Muhammad ɗaya Sadik ɗaya Fatima ɗaya ɗaya kuma a bar ma yara ɗayar kuma hidimar gida. Saboda murna su rasa me zasu yi. Daga nan su Eshan suka tafi gida anan Hafsat zata zauna. Washa gari Aka kawo kayan Sa ranar su Amira inda aka saka sati biyu. Yau ne mahaifiyar Ahmed zata zo zasu dawo Abuja baki ɗaya. Ahmed da Eshan sun koma bakin aiki inda aka basu masu kula da lafiyar su dan ana shirin ƙara masu girma. Amaryar Daddyn Yusurah kam suna ta kula da cikin su sai hamdala Yusurah ta ma fi kowa son cikin tunda bata da ɗan uwa ita ƙadai ce. Yau aka yi sati da rasuwar Ladidi yau an tashi zaman gaisuwa Amarya duk sai taji gidan wa Ni kala babu daɗi tana tunanin rayuwar da suka yi da Ladidi ta na nema ma ta gafarar Allah. Maman Ahmad ta iso harda Ammi aka je dauko ta suna isa aripot jirgin su ya iso suna tsaye har aka fara fitowa Ammi na hango Mamen Ahmad da gudu ta tafi wajan ta itama ta taho da gudu tana sakin kayan hannun ta suka rungume juna suka saki kuka me cin rai amma kuma du sun burgi wasu sai da suka gama yan koke koken su suka tafi gidan Ammi DAFIN ZUCIYA THE HIDDEN OG THE TREASUER OF THE HEART BY FATIMA BINTU HOSSEN https://chat.whatsapp.com/Jp93APpPrfe9IezRu9zH91?mode=ac_t https://whatsapp.com/channel/0029VbBbXTM3GJOxiUfRPn1U *https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ *(J.W.A)* _Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️ "Jajirtattu mu ne ƙarfi a zuciya, hikima a magana, jajircewa a aiki. Ba mu ja da baya, ba mu faɗuwa. Mu ne tarihi da ake ginawa!" 💪🔥✨ 🦚🦋THE NOBLE WRITER'S TEAM🦋🦚 (🦚✊DEDICATION IS OUR STRONG✊🦚) Happy jumma 'atu Mubarak Fri,agu2025 08:17 Hiameera43 Bisimilahi Rahamanur Rahim Page 55 Bayan sun isa gidan Ammi sai da tayi wanka ta huta san nan suka zauna cin abinci nan aka shiga firan yanda biki zai kaya shiri ne ake na musan man bikin da ba'a taɓa kalar sa ba. Eshan ganin tunda suka zo bai ga Amira ba kuma bada ita akaje aripot ba ya sa ya cema Amir "ina Amira ta ke?" Amir ya ce "sun je gidan wata yar uwar mu ita da su Aunty Fatima za'a yi masu gyran jiki." Eshan ya ce "kasan gidan?" Amir ya ce "eh amma ko mun je baza 'a bari mugan suba wai dokar ce." Eshan ya ce "ai kam zan karya dokar tashi mu tafi." Ahmed kam tunda yaga Mamen shi ko kallo Eshan bai ishe shi ba yana kananaɗe da Mamen shi yan zuma yana kwance ya dau ra kansa a cinyar ta ita kuma tana sha fa mashi sumar kanshi ya lumshe ido. Eshan ne ya zo ya finciko shi ya ɗaka mai duka ya na cewa "ƙaton banza kazo ka haye ta a haka za'a yi maka aure amma har yan zu baka girma ba." Hararar shi Ahmad ya yi ya ce "wai na cikin masai ke ce ma na waje ya taka kashi yo kai akwai ma Wanda ya kai ka taɓara." Murmushi Eshan yayi ya ce "ai ni yanzu nayi hankali tunda na kusa ajiyi iyali." Mame ce ta shi ga taɓa hannu ta dauƙi wani kofi ta jifi Eshan da shi tana cewa

Chapter 10 of 14